ovels / SADAUKI part 1 to 10
SADAUKI part 1 to 10
Posted by Bashir Sani Fesan on 20 Dec 2016 – 20:27
ba abunda kakeji se gudun dawaki da mutane
wadanda zasu kai kimamin mutum 100 dikansu
dakarun wani azzalumin sardine, dik wannan
angayar mutun biyu ake bi, Gudu suke kamar
zasu tashi sama can Naga wata babbar mace
Mai kimanin 40 yrs tafadi tana haki, acan gefe
wata yarinya tayi magana da Sanyayyar murya
ummy kitashi muje bamuda lokacin Hutu yanzu,
ahankali wadda aka kira da ummy tace no Ajlal
banida wani karfi ko zarafin da Zan iya tashi,
hawaye suka cika idon Ajlal dasauri ta cakumi
ummy tagoya sukayi cikin daji sanadiyyar jin
kukan dawakin na karasowa, Haka suka cigaba
Da yankar DAJI Ajlal na Goya ummy tin tana
bacci harta kasa. tafiya sukayi Mai Nissan gaske
baci basha. Sunaji sunaganin manyan dabbobi se
ummy ce ke firgita amma dazaran suka nufuso
zanga Ajlal takalli sama tayi addua sann tadubi
dabbar komin girmanta dazaran suka hada ido da
Ajlal Zata koma yatsanta biyu take nuna su dashi
yanxun zasu juya ikon God kenan, Kusan 3:00AM
tayi musu basu Dena cin dajiba dayaki karewa ko
alamun mutum babu haka suka samu gu suka
kwanta bayan Ajlal ta musu shimpida da haki
tama ummy filo da cinyanta sann ta tofesu da
addua, Kukan tsuntsaye ne yatadasu hakan
yabasu tabbacin safiya ta Waye ahankali Ajlal
tajanye jikinta taje yawon neman ruwa Amma
bata samuba dole tadawo tasame ummy har
tafara sallah ‘ gefe takoma tana kallon yanda
ummynta Ke kuka Acikin Sallah, bayan tagama ne
tace ummy kintashi lfy, kanta kawai tadaga mata
kasancewar tana lazimi ‘ taimama tayi tayi lullubi
da mayafinta ta tada sallah. Suna gamawa suka
dauki hanya ba Wanda kema wani magana
kowannensu da Abunda yake sakawa aransa,
WANI Kuka kakeji da gurnani dasauri ummy ta
koma bayan Ajlal, wata babbar dabba ce dani
kaina bantaba ganin irintaba ko a film. Ajlal
takurawa wann dabbar Ido Sega ta taduka
murmushi Ajlal tayi Abbu kana Raye har yanzu
abbu kana Ina ne?? Hannun ummy taja suka nufi
dabbar bamusu suka hau gaban ummy nacigaba
da faduwa ba halin magana tinda abbu
yabarmata wasiyar cewa kartayi wa Ajlal
Gardama idan taga wani abun nafaruwa tsakanin
ta da animals. Haka suka hau dabbar segasu
suntashi sama tamkar tsuntsu Bai diresu ko
inaba se wani dajin Mai kyau da haske daga nan
Yakoma inda yafito. Aljal taja hannun ummy suka
cigaba Da tafiya…… Kwance yake kan carpet
gefensa fadawa ne Sekuma yan mata masu
yimasa hidima. Ahankali yake kutsura Apple
rayuwarshi Fal take bashida damuwar komai
anahaka. sega calling din Albina yashiga
murmushi yayi Sannan yadaga wayar gud
morning beautiful one, Murmushi tayi tareda
gyara kwanciyar ta. Takara hugging din pillow
how are you my hero Yabata amsa da fine ya
exam. Alhamdulilah tace tareda tambayar mutan
gida haka suka cigaba Da soyewa nikam Ina gefe
Ina daukar tips na love. Tafiya sukayi Mai Nisan
gaske dik acikin wannan dajin ahankali suka fara
jiyo kukan tsuntsaye tareda sanyi hade da wani
yanayi mai dadi. Ajlal tadubi ummy tace mamana
munkawo inda mutane najiyo kamshin mutum.
Ummy dai batace uffan ba illah tayi murmushi Da
azama Ajlal Taja hannun ummy suka kutsa cikin
gurin ganin ruwa agurin da flowers Mai kyau
yasaka Ajlal yin wani irin Kara tareda sauri taje
gurin ruwan tasha tasha harta kasa tashi ummy
ma tasha Aykuwa a take suka zube agurin bamai
nun fashi acikinsu Tafe yake kan dokinsa yana cin
Apple fadawa ba biye dashi . Zuma naji yafada
dasauri aka basa yasha aka basa tissue yagoge
bakinsa Sannan suka cigaba Da tafiya. Acan nesa
suka hango Kaman mutane Kuma da alama
matane kallonsu kawai yayi hakan yabasu
tabbacin meyake nufi dasauri sukayi kansu tareda
dubawa. Ranka yadade suna nunfashi. Dan tanin
yace ku yayyafa musu ruwa. Haka kuwa akayi
dakyar suke nunfashi Dan tanin yabada order aje
dasu cikin gari sasashen yallabai kan sudawo.
Part 2 Katon gida Wanda yawanashi kadai abun
kallo ne yakai girman wani karamun Kauye. Filine
babba Wanda zaisaka tsawon tafiya acan nesa
nake hango motoci tareda hadiman gidan daga
maza zuwa mata, tafiya Mai Dan nisa takaisu ga
gate din gidan idan kashiga flowers ne birjir
gwanin sha’awa se wasu kofofi kusan uku
kowacce kofa katuwar gaskece sa’Annan ginine
na sarauta ta tsakiyar tafi kowaci girma da kyau
kowace kofa akwai fadawa Akanta tareda
soldiers, Kofar tsakiya nagan sunbi tareda
shugabansu direct part dinshi aka wuce dashi
batareda yabi takansuba. Gurin matar Mai
martaba sukaje wato Nana hauwa wadda kowa
me kira da mama, Dan tanin yayi sallama
jekadiyarta ce ta amsa se masu yimata hidima.
Kozan samu ganin mama kuwa tambayar da jefo
kenan. Jekadiya tace ko alama mama nada baki
sedai ko Gobe, Dan tanin yace just two minute
fah, afusace jekadiya tace wannan Kuma kaikasan
mekake cewa. Murmushi yayi Allah huci ranki
gwaggoji, harya juya Sega mama tafito. Kasa ya
zube yana kwasar gaisuwa, mama tace Dan tanin
bajabakaji koh, saunawa Zan gayama bana San
Ana dukamun nida kai dik matsayinmu daya
agurin Allah it myb ma kafini daraja if kafini
tsoron Allah. Jekadiya tace habawa yoshe Kuma
Dan tanin zaifiki tsoron Allah, mama tace kinjiki
dawani zance Ke harkullum kina tsoron gayamun
gaskiya bana son irin hakan akiyaye gaba, cike da
mutuwar jiki jekadiya tace ALLAH ya huci ranki
shugabata dasauri mama tajuyo mekikace jikin
jekadiya yadau bari tace amun afuwa ranki
yadade cike da takaici ta girgiza kai tamaida
dubanta ga Dan tanin dayake murmushi Meke
tafe dakai? Dan tanin yabata lbrn abunda suka
tsinta wato Ajlal da ummynta. Mama tace
subhanallah shine tindazu Kayi shiru baka saurin
gaya mun ba Ina suke din ‘ Dan tanin gaba mama
baya har inda suke wani zaure fadawa na musu
ferfita Mama tace maza akaisu side dinta
jekadiya kikula dasu abasu sutura da abunci idan
kinga da matsala contact me Inji mezanyi akai
tana kai nan tawuce wasu hadiman suka bita…..
Daki aka basu tareda kyakkyawan masauki bacci
suke hakan yasaka aka kyalesu se kusan magrib
suka farka atare dasauri wata hadimar takawo
musu abunci kyada kai sukayi Ajlal tace Ina
mukene ko mundawo gidane.? Hadimar tace
wannan amsa se wadanda suka tsinto ku yanzu
dik ba wann ba kuci abunci kucanza kaya sann
muji lbrn ku, Ajlal zatayi magana ummy tadafata
“halas binti ” it’s ok daughter. Gyda kai tayi tace
abasu ruwa zasu wanke bakinsu tukun. Bayan
sun gama sukaci abunci bana wasaba sann
sukayi alwala saboda ramakon salloli dake kansu.
After sungama sukayi wanka aka basu sutura
suka saka wani baccin ne yakara kwashe
su…….. impossible taya za’ace ba’agansuba
bayan antsince Dan kwalin Aljal. WANI bafade
Naga yasunkuyadda kai kasa yace Allah huci
zuciyanka wlh ba irin neman daba muyi musuba
Amma ba’a samesuba ko wani Abu Mai kama da
su bamu samuba Se wann Dan kwalin. Sedai
kuwa idan dabbobi suka cinye su. How comes
dabba bata taba Ajlal bare ta cinyeta, I know
something happened I know dunkule hannunshi
yayi tareda dukan kujera too bad… Get out of
here. Dasauri mugu yafita kan ya ballasa Mom
tashigo dakin relax bom boy komai zaiyi dai2.
Mom….. shiiiii tafada tareda nuna masa gado
dole yazauna badan yasoba, Haba shamsu
meyasa zaka tada hankalinka akan abunda
yarigada yagama faruwa, matukar banaso ba
Tokuwa ba Wanda ya isa yaja damu barema wani
zancen Ajlal yo Ina Mai Goya mata baya din? Na
wulgasa lafira Ina jarumatarshi dawani
kwarewarshi yo Ina baiwar dayake taqama daita,
ina baiwar yar tashi dik suntafi abanza Dan
basazu amfanesu dakomai ba, Shamsudden ya
nisa tareda yes hakane but momy matukar
wannan awarwayo yana hannun Ajlal ratuwarmu
tab take da barazana sa’Annan koyaushe
mulkinnan zai iya juyawa akanmu, mutane gari
sunyi obey da wasiyyar da Abbu yabayar ‘ don’t
worry son zanyi clearing komai it’s my pleasure..
okay yadaga kai fuskarka bayabo ba fallasa. Part
3 Jekadiya Zaune agaban mama tace ranki
yadade mutanenan da aka tsinto suna bukatar
taimako Mama tagyara zama kamar name kenan,
jekadiya tace ga dukkan alamu wahala ce tafidda
su daga inda suke, sa’Annan sunce ataimaka
abasu kowani irin ayki zasu iya sudai burinsu su
samu masauki da abunci basu damu da
albashiba. Mama tace Allah sarki zanga Ajlah
idan yana bukatar hadimai abasa nagan ya kori
hadimarshi mace. Jekadiya tace hakane Allah ya
biya Ameen Kwance yake yana karatun jarida
karar kibiya tayi yawa hakan yafidda shi waje
tsaye yayi yana kallon Nura dake faman fafatawa
da yaran Ajlah. Har zai koma ciki, Nura yace hey
maza SADAUKI jarumin maza kozaka Dan Dana
ne, Murmushi yayi yagirgiza kanshi Sannan yace
Nura ka rike girmanka har kullum Ina gaya maka
cewa naga yayi gaba na baya sea labari. Nura
yace adane wlh yanzu kam bana Jin akwai wani
jarumin dazai iya gwabzawa dani, murmushi yayi
yanufi hanyar ciki, kamar mafarki yagan ansako
masa tasoki hannun rigarshi Sannan Kuma ta
kafe da gina zai juyo aka sake halbo wani, cike
da bacin rai yazare su tareda jifa da cup dinda Ke
hannunsa yanufi Nura, Nura na ganin haka yayi
murmushin mugunta yanufesa bil-haqqi fafatawa
takasance tsananin jaruman biyu, bawanda yayi
nasarar kauda wani acikinsu, can Nura dayaga
bada karfi yakeba aykuwa ya manna masa takobi
a gefen hannu Tini jini yafara sintiri, fadawansa
suka yo caaa a take yadaga musu hannu alamar
su dakata tareda soka takobi akasa, sann ya
yaga rigarshi dik kaurinta yadaure inda jinin Ke
zuba, Dubi daya na masa nakoma aguje yanda
yasauya alokaci guda ya rikida yazama wani irin
lion, takobinsa yajanyo yacigaba da fafatawa da
Nura tuni yacire hular dake kan nura ciki Harda
uwar sumar dayake tarawa, sann ya wangale
Abun dasuke karawa ahannu ahaka yacigaba da
ketar nura seda yazare dik wani Abu dake jikinsa
na karfe baibarsaba suka cigaba wani tsalle yayi
yadoki nura awuya segashi a kasa hakan yabasa
damar cira takobinsa da nufin soka masa. Karka
aykata hakan aka fada dawata muryar ta
dattawa, tsohone dazai kai kimanin 70 yrs cikin
shiga ta alfarma se wasu mazan dasuke kamar
twins suna gefensa kowannensu yana Mai jin
haushin SADAUKI dakuma rashin kasance dansa
ne yakeda wannan karfin da jarumta, Hakan yasa
dole yajefar da takobinsa sann ya cakumi wuyan
Nura, “ko a bacci kayi mafarkin zaka fafata dani
to kace karya ne, Ni Ajlah ibn Muhammad ibn
Umar bawanda ya isa yaja dani Ni jarumi ne
nikuma SADAUKI ne SADAUKIn ragwayen maza
yana kai nan yajuya afusace ya nufi room dinshi
dasauri Dan tanin yarufa masa baya Dan tanin ya
bude fridge yadauko masa gorar ruwan faro
yamika masa ya karba ya ajiye Dan tanin plss
leave me for while I want be alone Dan tanin yace
ok sir wish you happy now and for ever. Thanks
yafada tareda fadawa kan gadonsa seda yaji relief
sann ya tashi yadora ruwan zafi dakanshi yayi
dressing gurinda yaji ciyo sann yaje toilet a
gurguje yayi wanka tareda alwala yafito waje Dan
bin jam’I Anan suka Hade kabir dasauri ya sakar
masa murmushi hey kabir saukar yaushe, kabir
yace wlh jiya cikin dare. Ajlah yace toya hanya ya
skull hup dae komai fyn. Kabir yace insha Allah
kagama da takardata nazo har Sun daukeni ayki
a can but bana tunanin Mai martaba zai bari,
Ajlah yayi murmushi hakane fah gamu Nan daga
gida se company’s bara abar mutun da abunda
ya karanta ba, Kabir yace banga kana shirye2
dawowan Albina ba ” cikin rashin fahimta yace
Kaman yah”? Kabir yace kaddai kacemun baka
San da zuwanta ba ” Ajlah yace agunka naji myb
zatai surprising Dina ne ‘ yes hakane inji kabir,
Haka suka cigaba da fira har kofar masallaci
Waye Ajlah miye asalinsu da sarautarsu kubi yo
yar mutan sakkwatawa domain jin amsoshinku.
Part 4 Ajlah SADAUKI Dane ga Mai martaba
Muhammad wanda yagadi sarauta a gun
abbanshi malam Umar su hudu ne gun
mahaifinsu Muhammad babba se gwaggo uwani
sekuma Alh Ibrahim da Alh Suleiman Bayan
rasuwar malam Umar akabawa Muhammad
sarauta kasancewar Shi babba agaresu
kiyayyarsu da Suleiman da Ibrahim tasoma ne
daga lokacin dasuka fahimci cewa iyayensu sunfi
son Shi akansu Ba dan komai Ba sedan kawai
tarbiyarsu ta banbanta saudayawa Abu ke faruwa
Amma sedai Shi ya hakura yabarmusu Bayan ya
karbi sarauta ne aka bukaci dayayi aure ananko
rigima ta taso Dan a iya shekarunsa Bai iya kula
mace ba bare yace yana sonta, Hakan ya Sanya
aka basa nana hauwa yar wazirin sarki wadda
takasance abun yabo ga kowa basu wani dade
waba tasamu cikin maryam wadda takai kusan
shekara biyar Sannan aka Haifi Ajlah bayan Ajlah
ta haifi yaya biyu mata sedai basuda lfy basu
wani jimawaba suka rasu daga Nan Kuma
haihuwar ta tsaya mata. Ibrahim yanada mata
daya Mai suna kulu tanada yaya biyu Albina ce
babba se Nura Sulaiman yanada yaya hudu kabir
ne babba Wanda suke age mate da Ajlah se
sayyid da Kuma nuwaira karamunsu shine jafar
Aljlah Kabir da nura sunyi karatunsu ne a
Indonesia Maryam kuwa tuni tayi aure tana auren
Dan wani sarki. Karatu suke bana wasaba dik
wannan Mai martaba ne yake dauke da nauyin
karatunsu, Albina takasance kyakkyawan gaske
hakan yasaka Ajlah santa tin tana karama, hakan
yasanya aka kulla alqawarin aurensu Soyy suke
cike da tsabta dikda ita tana Turkey gurin karatu
tana shekarar karshe a yanxu, Aljah yakaranci
newscasts, kabir kuwa business, Albina na
karanta micro biology, inda Nura yakaranci
computer science, Ajlah 1 yr kenan dagama
karatunsa amma Mai martaba ya hana shi yiwa
Indonesia aiki cos acan suka daukesa ayki,
acewarsa baiga amfanin yiwa wata kasa hidima
ba ga kasarku, hakan yasanya yake son komawa
domin Karo ilmi sedai har yanxu Mai martaba
yaki bada bakin yaje kullum rigimarsu kenan, Bari
mu leka Ajlah da ummy! Wadanda Zuwa yanxu
Sun zama yan gida ummy tashiga daga cikin ma
aikatan mama tana taya jekadiya bakaramun jin
Dadin zama da ita suke ba ‘ musamman dasuka
fahimci cewa da gaskiya take ayki ba munafukar
ci aciki, Mama takira Ajlah ta nuna masa Ajlal son
ga wata yarinya nan idan kanoso tarika maka
hidima tinda ka kori maimuna ” cike da isa da
gadara yakalli Ajlal da ita kanta Shi take kallo
bakaramun kwarjini yamata ba ” yakatse Mata
tunani da cewa me wannan kwailar Zata mun
Dafa tea ko coffee? Mama tace hava son zatafi
Dan tanin iya gyara maka dakinka dakuma
sauran ayyuka bakowani ayki mace namiji zai iya
ba karka Rena mace komai kankantarta mace
tana da girma da daraja mace…. yakatar da ita
da cewa mama Zan wuce inada baki fah, Harara
ta balla masa Ina magana zaka katseni, momma
yafada cike da tsiwa kibar zancen yarinyar nan
kawai waima daga wani kauye ta fito ne, Ajlal
tadago kanta cike da bacin rai kome ta tuna Oho
Sekuma ta Maida kanta kasa, Ajlah yace momma
you know I hate mace fah mata akwai makirci
bana son abunda yafaru baya yasake faruwa.
Mama tace I promise hakan bazai faruba, sadauki
yace shikenan mama Amma atabbatar mai tsabta
ce Dan tanin check and research her works tell
her my rules bana son rubbish okay, Yana kai nan
yasa kai yawuce fadawansa suka rufa masa baya,
Dan tanin yace zo muje na nuna miki aykinki a
sanyaye ta dauki takalminta ta wuce baya yana
gaba har side din sadauki, tayi matukar mamakin
ganin wannan dakin iya haduwa ya hadu kyace
outside kike, Dan tanin ya Katse mata tunani. Kin
iya girki tace eh gyaran Daki fah wankin toilet
muje na nuna miki yanda ake amfani da komai
kitchen suka fara yana nuna mata yanda ake
kunna gas da kashewa tareda sauran abubuwa
hakama toilet, Ajlal kallansa kawai take aranta
kuwa tace ba abunda bansaniba anan nama fika
sanin wasu Abun, Kinga oga baya San yawan
motsi baya San yawan magana dasafe idan kun
hadu zaki masa Ina kwana shaken ba lallai vane
ya amsa zaki gan yafi yawan magana da jikin sa
like hannu kafa ido and other’s idan zaki fahimta
oga magana nabasa wuya, Ajlal tagyada kai
aranta kuwa tace yo mema zaisa inmasa wani
morning Naga alamar Dan rainin sense ne….. Toh
pha kubi yoni domin jin wannan zaman yaxai
kare. Part 5 Tin safe tamasa knocking Amma yaki
budewa hakan yasaka takoma dakinsu tayi
baccinta bata farka ba se 12 taware ido tareda
taslima agurguje taje toilet tayi brush tawuce side
dinshi kofa abude hakan yabata damar shiga,
muryar sadauki taji yiwa Dan tanin fada meyasa
Baa basa break ba gashi har 12 tayi sann komai
ba’aga gyara ba Adakin, Dan tanin yace Allah
yahuci zuciyar sadauki ba laifina bane mama
tariga tamikawa wannan yarinyar aykinka, Ajlah
yace how dare you where is she? Dole ta
fuskanci fushina a yau har Zata barni da yunwa
irin wannan lokacin, shiru yayi jin sallama da
wata zakakkar murya kanta akasa tace sannunku
da fira tawuce kitchen, sadauki yabita da kallon
mamaki. Dan tanin yace Ke bazaki kwashi
gaisuwa ba kin shigo ko kallon mutane Babu,
Ajlal data shige kitchen ta jepo masa magana da
ba lokacin gaisuwa bane yanzu Banda ishash
shen lokaci sann ba gaisuwa nazo yiba ayki
kawai dafatar kagane yaren. Dan tanin yasaki
baki yana jin ikon God itakuma wannan waye ita
dame takeji? Sadauki yashige dakinsa rai bace
yabar Dan tanin parlor, agurguje ta soya Irish da
kwai sann tadafa ruwan tea ta soya biredi tareda
soyen alaiyahu da egg kitchen din tasake gyarawa
sann ta aza dawuwar ganda takara gass, bata
samesa ba tacigaba da gyaran parlor can taji
fitowarshi bata dago ta kallesa ba kawai tace
ankammala Karin safe Zan shiga bedroom in
gyara idan akwai Abunda Babu zaka iya kirana,
tana kai nan tashige ciki, bata tsaya wasaba
tashiga gyaran dakin har tagama tatsaya tana
kallon tsarin baiyi ba, damara tasha tashiga
kwance Kayan tana sauya jeren dakin dik seda
tacire pics dinda suke dakin da daddaya tana
gogewa tana maidawa pics din Albina Sun
matukar birgeta ta canza masa guri dae dae
fuskar gado sanda tazo goge pics din sadauki
wata kasala ta ziyarceta tareda faduwar gaba ta
takurawa pic dinda Ke hannunta ido yana saye da
suit farare fuskarshi dauke da karamun glass yayi
murmushi yana dauke da wani frem, bakaramun
kyau yayi ba agurin, haka dai tacigaba da sauya
dakin har kusan 1 sann tagama har toilet tiraruka
tagani awata karamar drawer ahankali tabude
tadebo wann da wancan ta hadasu takunna
aykuwa tuni Dakin ya gauraye dawani kamshi it
kanta kamshin yamata, Tafito bata samesaba tayi
kitchen tawanke kwanukan daya gama break dasu
tashiga dafuwar ganda wadda taji Kayan kamshi
kuskus tadafa da veritable sekuma hanci data
zuba akai taduba ba Kayan ruwa bare tahada
lemu tadai gama zuwa 2 komai ready tasake
gyarawa takunna tirare taja kofar tafice, Tin a
baranda yake jiyo kamshin wani tirare Mai Dadin
gaske hakan yasanya yayi saurin shiga, kamshin
abunci Dana tirare dik sun gauraya, Dan tanin
yakira yace asamai kiran yarinyar nan, atare suka
zo yace Ke meyasa zaki fita kibarmin dakina
bakowa kinada hankali kuwa? Aljal tace hankalin
kenan to mezanyi aciki bayan Nagama Abunda
yakawo Ni, tas ta tas kakeji sadauki yadauketa
da Mari nizaki gayawa magana Ke har kinyi
matsayinda Zan fada ki fada, Ajlal tace dikanmu
matsayinmu daya agurin Allah so banga wani
dalili dazaisa in maka biyayyar data wuce wann
ba wuyanta yacukuma zai mannata a kofa Dan
tanin yace relax oga take it easy mana mezaka
raga ajikin wannan kwailar, kalmar Data tsana
kenan Ajlal tace Waye kwailar acikin nida ku, Dan
tanin yace Ke wai wace irin Mara kunya ce? Ajlal
tace wann kuma Seka shiga duniyar tambaya
tana kai nan tajuya tawuce, sadauki yace wai
Waye wann kam meyasa bata tsorona kamar
yanda sauran mata suke meyasa bata shakkata
kamar yanda sauran mutane keyi Kodai niba Ajlah
bane, Dan tanin yace hava ranka yadade shawara
daya ka cire dik wani damuwa ko bacin rai
kacigaba da rayuwanka kamanta da ita yarinyar
akwai manyan kalamai lokacin datake gayamin
magana naso na mareta Sekuma nagan tamun
kwarjini, sadauki yace oho wann Kuma matsalar
kace kanada feeling da itane ” Dan tanin yace
Kutt yaushe hadima Zata shiga raina, sadauki
yace get out plss ” Dan tanin yace koba komai
yarinyar akwai iya girki da tsabta ji yanda kamshi
ketashi , sadauki yaja tsaki u know me but kullum
Sena maimaita I hate long talk, Dan tanin yace
tuba nake yajuya yafita, Randa yashiga dakinsa
bakaramun mutuwar jiki yayiba ganin wann tsarin
nata abun ya matukar burgesa baikara jin Dadi
ba seda yakwanta kan gadonsa idonsa a lumshe
yana shakar kamshin dakin yana bude ido idonsa
yasauka kan hoton Albina wani murmushi Naga
yayi much love for you Albina. Part 6 A hankali
take tafiya hannunta rikeda leda wadda aka Bata
sako takaiwa kulu uwar albina, sallama tayi sann
aka Bata izinin shigowa cike da fara’a takarbeta
sann ta karbi sakon, amma dai ke sabuwar
hadimar gidann ce cos bantaba ganinki ba, Ajlal
tayi murmushi eh Ni sabuwa ce momy, hjy kulu
tayi matukar jin Dadin data kirata da momy
yarinya Mai nutsuwa da hankali bakamar sauran
hadiman ba, Fitowa tayi tana rero wata waqar na
larabci kai tsaye tawuce sashen sadauki bata
samesaba, hakan yabata damar fara girkin dare a
gurguje tagama tagyara komai ta kullo masa kofa
haka aykinta yacigaba da tafiya aduk lokacin
daya San zatazo zaibar dakin gudun kar su hadu
sedai yana mamakin irin kamshin jikin yarinyar
daban yake kowanne turare take using Oho, ”
girmanta na matukar masa dadi harya manta
rabensa dayaje restaurant. Mama ta katse masa
tunani da cewa Ajlah kai kadai yau Ina Dan tanin,
Ajlah yayi murmushi barka da yamma mama Dan
tanin na aykesa ” just bana son hayaniya Shi isa
nafito daga dakin, nd Kuma yarinyar nan na ciki
“mama ta gyada kai ince dai komai normal ta iya
ayki? Sadauki yayi murmushi sosai mama akwai
tsabta by mistake bazaki samu something
rubbish ba akanta sedai fah akwaita da barnar
tirare da kayan abunci, mama tace to ay shikenan
tinda dai ansamu yanda akeso wadannan ba
matsala bane koh? Ya gyada kai but mama
yarinyar yar tsiwa ce Sam batada tarbiya wlh,
mama tace Kutt Ajlah wannan Ajlal nada tarbiya
sosai fiyeda zatonka watakila ka nemi mata
rashin gaskiya ne Shi isa, sadauki yace mekikace
sunanta mama tace Ajlal nace any problem “yace
no, Haka yacigaba da maimaita name din Ajlal
wow nice name I like it, muah yaji anbasa kiss a
kunne baijuyoba baikuma motsaba sanin kowaye,
ta zagayo ta baya honey baka murna da zuwana
ne, sadauki yace of course Indai surprise ne wann
to zero, yana kai nan yatureta yatashi yayi side
dinshi, dariya tayi tabi bayansa, part 7 Wow
honey kamshin menake ji tabi kitchen din dakallo
inda take jiyo kamshin nuggets ne akayi se paten
plantain gakuma soyayyar doya da kwai gefe anyi
zobo, tsayawa tayi bin Kayan da kallo, honey
wayake wann, Yamata banza kanshi tafada hava
love plss my head down, sadauki yaballa mata
harara kisauka ajikina banason hakan, idonta
yaciko da kwalla tajuya dasauri tabar dakin, a
take yaji wani iri Bai kyautaba daga dawowanta
yafara sakata kuka, yatabe baki anyway ma ita
taja kawai seta dawo ba announcement, Kuji
sadauki fah lover’s surprising ne aka masa Amma
yakasa ganewa saboda rigimarsa, Plate yajawo
yazuba abunda zai iyaci yasha zobo sann yawuce
gurin ball ” A dai dai kofa Ajlal tahadu dashi cikin
Kayan kwallo red yana daure takalminsa kansa
akasa baima San da itaba sedai yana jiyo
kamshin turarenta kadan2 ” Ajlal kuwa mutuwar
tsaye tayi tana kallonsa yayi matukar kyau a
wann shigar yabirgeta setana jin wani feelings
sosai agamedashi , ya Katse mata tunani a
lokacin dayace you! Yanamai nuna ta da
yatsansa mekike agabana kin wani tsureni da ido,
Ajlal tawani fari da ido yo in kalleka kai madubine
kokuwa bansanka ba, sadauki yayi fuuu zai
bigeta ta goce cike da mamakin gocewar datayi
tamkar wata jaruma yadago yana Mai jin ciyon
hannunsa daya buge gina, Ajlal tace auu yi hakuri
fah ba laifina bane kaine kakeda zafin hannu,
sadauki ya kuramata ido se uban karuwanci idan
tana magana kamar babyn roba, Ajlal tace waima
tsaya tukunna Ina zakaje ne? SADAUKI yace
gidan ubanki yar iskar yarinya wlh kishiga
hankalinka bana son hayaniya ko yawan magana
meyasa kikeso dole Sekin takurawa rayuwana
meyasa kikeso kizama mace ta farko dazata fara
ban problems arayuwana why? Ajlal tayi shiru
kalamansa suna mata yawo a brain ahankali tace
Kayi hakuri Allah huci zuciyanka, tsaki yabuga
yanufi hanyar sauka step din, dasauri tasha
gabansa tace minti daya, yatsaya cak yana
kallonta jiyake tamkar ya shaketa, Ajlal tace kaci
abincin rana kuwa? Sadauki yace Ina ruwanki
kadai ki girka kawai, Ajlal tace nikuwa nakeda
ruwa, a fusace yace banciba Kuma baci Zanyi ba
and so wot, Ajlal tace aykuwa ba inda zakaje,
mama tace inkula dakai tayadda bazaka taba
neman Abu ka rasaba ta fannin girki Dan haka
kakoma kaci abincin kawai kafun kadawo anyi na
dare, sadauki yace Allah Zan ballaki wlh kikauce
mun karna jimaki ciyo, Ajlal tace bafa inda zaka
sekaci abincin, sadauki ya balain tureta kasa
seda tabuga kara, Dagudu tacimmasa tareda
rikemasa riga Allah kawuce kona gayawa mama
ince Sam yau bakaci komai ba, Ana hakan sukaji
muryar mama nacewa ke ke Ajlal lfy kike rikesa
haka, Ajlal tace mama wai bazai ci abunci ba
zaije gurin ball, mama tace kaikuwa kaje kaci
mana aykinmun dai dai wann yanuna mun kin iya
Kula dashi sosai Sadauki yakasa cewa komai,
mama tace kawuce nace kosena karaso, agogon
hannunsa yaduba remain 15mns yarinyar nan zan
koya mata hankali wlh itakuwa tamasa gwalo
tana dariya. Part 8 Crab cake tareda coconut jus
se chicken pie, bakaramun Dadi abincin yamasaba
yanaci yana yiwa mama firar ball, mama kuwa se
murmushi take tana yaba iya abunci irin na Aljal
Bai ankaraba ashe har yaci 20minute acikin time
din ball, kambuu yafada tareda Dubin agogonsa
dasauri ya goge hannunsa da tissue yashiga
toilet yayi brush yafito aguje, Ajlal tace Ajalin ball,
cak yatsaya tareda juyowa mekikace fuskarsa
adaure, Ajlal tace cewa Nayi adawo lfy, ball dinda
Ke hannunsa yajefa mata aykuwa ta cabketa rass
baki yasaki yana kallon ta, Allah mama Zan Zane
yarinyar nan, mama tace aykuwa dakayi abun
kunya ace kamarka sadauki ya doki mace baijira
mexata Kara cewa yafice yana fadan Sena dawo,
mama tajuyo tana kallon aljal Ajlah nagode miki
yata dakike Kula mun da Dana Kuma kike masa
girki Lafiyayye ko awaje iyakaci kenan Ajlal tace
lah haba dai mama akullum mune da godiya
saboda hallacin da yardar dakuka mana hadida
amana bayan baku sanmuba bakusan Waye
muba, mama ta dafa ta Karki damu da wannan
yata Dan Adam Abun darajarwa wane Allah
dakanshi yafifita halittar Dan Adam akan kowaci
halitta dakika sani mudai namu kawai muji tsoron
sa muhanu daga haninsa, Ajlal tace hakane mama
Albina nagani anci ado kamar wata queen tazo
dakin sadauki Bata samesaba ta Dan kwanta
akujera bacci yasoma dibanta taji motsi a kitchen,
a hankali ta tashi ta shiga sewani yanga da
kariraya take, tace ohh ashe kece aciki, Ajlal tace
ehh, Albina tace baki iya gaisuwa bane? Ajlal tace
ba ita nazo yiba, Albina tace wot kinsan dawa
kike talk, Ajlal tace nasani Ina magana da mutum
kamar kowa, akwai wani abu bayan wannan,
Albina tagama kuluwa tace kee ki iya bakinki wlh
banason raini Ke har kin isa kigaya mun magana
kina matsayin boyata, Ajlal waye boyarki toko
wanda kike kuri dashi yayi kadan yace min
boyarshi bare Ke, kiduba dakyau niba karamar
yarinya bace dazaki kawomin raini kinajina,
Albina tace wlh yau se kin shiga uku Sena
wulakantaki sann zansa a koreki agidann korar
kare wlh, Ajlal tamata banza tacigaba da aykinta,
Albina takoma parlor kan kujera ta Dora kafa
daya kan daya sewani cika take tana batsewa ay
wlh yau Zan nuna miki matsayina da isata
agidannan, Sadauki ne yayi sallama tareda fadan
wow nice one wann kashe colour haka gaskiya na
siye wankan nan dole Zan biya, shiru yayi ganin
kamar ranta abace Ohh”sorry bae of life waya
taba matar sarki waya taba matar sadauki Ajlal
yanzu yafuskanci hukuncinsa kowaye Shi, cike da
Jin dadin kalamansa wadanda suka Dan rage
mata bacin rai tace waccan Mai aykin taka waye
ita daga Ina taxo inaso yau kanuna mata
matsayina agidannan, sadauki yatabe baki
Bansan amsar wadann tambayoyinba sedai ko
mama zaki iya tambayar ta, Ajlal dake kitchen
tana jinsu ta tuntsure da dariya, Albina tace
rashin kunya fah tamun har nitake sa’insa dani
infada ta fada kamar wata tsaranta, sadauki
dayake warware takalminsa yace halinta ne keki
fara gani yau just kimanta da ita kawai ki
fuskanci meke gabanki okay. Albina tace tab ai
Se black stomach yakasheni if ban nuna mata
matsayina ba, sadauki yace okay gaki ga guri
tinda bakyaji, marasa kunya irin wannan banza
akeyi da al’amarinsu kulata zaisa takara miki
wani Abun, Amma idan kika kama girminki
musamman matsayinku na mata seta rika
girmamaki, Albina tace Dan bakasan meta mun
bane, sadauki yace ok kije kiyi dik Abunda kike
ganin yafimiki, ganin yafara fusata yasakata yin
shiru badan yasoba Aljal tashigo dauke da tire
abunci har tagama bawuya tahada cook Kuma
Mai ma’Ana, jin kamshin danbu yasakashi fasa
wankan dazaiyi yafito, Ajlal naganinsa tadawo
tazuba masa komai tace akwai mango jus baiyi
sanyi sosaiba Zan iya saka kankara, banza
yamata kamar baiji ba ‘ Albina tayi murmushi
mugunta, Ajlal tace magana nake oga, sadauki
yadaka mata tsawa kinsan dai dai yakikeso kirika
sakani magana, Karki bari inkara warning dinki,
Ajlal tace Kayi hakuri, Albina tace mekike nufi Ni
bazaki yi saved Dina ba, Ajlal tamata banza
tacigaba da tafiya ‘ Albina tace kee dake nake
Ajlal tace mekikace madam, Albina cike da gadara
tace kizo kiyi saved Dina nace. Part 9 Ajalal tace
lokacin da aka daukeni ayki oga kadai akace
ba’agaban da wata yar tsuma ba, Albina ta Mike
tsaye ke Dan uwarki kin isa, Ajlal tajuyo afusace
karki soma Kuma karki Kara zagina Dan kuwa wlh
zakisha mamaki ban hada iyayena dakowa ba,
Albina tace anfada Dan uwarki da ubank… bata
karasaba kaji tasss Aljal ta wanketa da Mari bata
sauke hannuntaba sadauki yabata bashi har biyu
baya da gaba Aljal tayi baya da gaba yafadi gurin
tsananin zafin Marin yakaimata har cikin
zuciyarta, sadauki kuwa yaja Albina kan kujera
yana lallashinta itama bakaramun zafi tajiba a
take fuskarka tayi ja Abu ga farin mutum, sadauki
yace zaki bar mana guri kosena ballaki Dan kinga
Ana kyaleki Ke har kin isa kimare matata
agabana kizauna lfy, kinci darajar mama wlh da
Sena miki abunda yafi wannan, Ajlal tadago
jajayen idonta dasuka kumbura tace nizaks Mara
akan wannan koh tanuna Albina, sadauki yace
ehh kozaki ramane, Ajlal tace wlh sekayi Andaman
dukana dakayi Sannan inamai tabbatar maka
sedai kanemi wata Mai aykin Amma Ni nafi karfin
wulakanci agurin kowa tana kai nan tafita,
sadauki dayagama kuluwa yace, aykuwa zaki bar
gidannan yau ba’ayi mutun dazai Maida mun
magana ba kowaye Shi afadin garin nan, Albina
tace Kayi hakuri sweet boo, sadauki yakwabe
mata hannu ay dik kece kikaja kowacce Mai ayki
aka kawo sekin saka na koreta akan masifarki,
yanxu wannan kina tunanin za’a samu Mai tsabta
da iya girki kamarta ‘ Albina tace don’t worry Zan
rika dafama, yajuyo yakalleta da mamaki tace yes
Zan iya, Ajlal kuwa tana zuwa tafadi kan gado
tana cigaba da kuka. Ummynta na kallonta Bata
kulataba sedai acikin zuciyarta tana Mai jin zafin
kukan komene yasaka Aljal Kuka tokuwa
bakaramun abu bane, tagama kukanta tajanyo
sallaya ta shimpida taje ta dauro alwala ta tada
sallah, bayan tagama takoma ta kwanta bataci
abunci ba, se alokacin ummy tamata magana,
Ajlal kitashi zanyi magana dake, Ajlal ta tashi
tana kallon mahaifiyarta, ummy tace Aljal kisani
fah wannan halin da muka tsinci kanmu aciki
jarabawa ce babba maimuna wuyar ci ga Dan
Adam idan kika daure muka cinye wann jarabawa
natabbata zamu ribanta anan duniya ko lafira,
mafi a’ala lafirar Karki manta wasiyyar mahaifinki
kirike hakurin nan Dana sanki dashi sann
banyarda kidauki reni ko wulakanci ba a gun
kowa Dan kinfi karfin hakan Karki Ina gargadinki
da karki kuskura fushin zuciya yakaiki ga aykata
dana sani Karki dauki mataki alokacin da kike
fushi sann kisani yanxu badai da bayaba dole kiyi
biyayya wa jama’ar gidannan Indai har kinaso
mutsira da kanmu da mutuncinmu karkiyi abunda
zaisa akoremu Dan Allah yata; Ajlal tace insha
Allah ummy “takwanta kan cinyar ummynta har
bacci yayi awon gaba da ita, Bangaren sadauki
kuwa nadama ce fal aranshi domin kuwa har
yafara ganin banbanci gashi 9 tayi bashida
abunda zaici se Dan tanin yakira yace yahada
masa tea da Irish ‘ Dan tanin yace ranka yadade
Inada tambaya plss, sadauki yace nope banda
amsar ta yanzu ‘ Dan tanin yace Kodai batada
lfy, ne kai anya kuwa agurguje yahada komai
yakaimasa, Amma me yakasa ci dankuwa yaji ban
banci ‘ yariga yasaba da girkin Aljal bazai iyaciba,
Albina tafito dauke da tray din abinci takai masa,
honey ga abunci nakawo maka, ya kalleta yakalli
abuncin yace thank you, tagaji da tsayuwa
tazauna dole ‘ mexan zuba maka yanxu, sadauki
yayi murmushi kibarshi zanci anjima yanxu naci
abunci, aranta bataso hakanba dole ta kyalesa
sanin halinshi baya magana biyu. Aljal kitashi har
8 yayi bakije kin hada masa breakfast ba, Ajlal
tace yau ba ayki ummy, ummy tace kamarka
banganeba Aljal tace kawai bazan Jeba ummy nd
Karki tambaye dalili, gaban ummy yafadi kaddai
wani Abun sadauki yayiwa yarta tinda jiya
tadawo tana kuka, zuciyarta tashiga har bawa
Allah kacecemu kakare mana imaninmu da
mutuncinmu ya Allah, tajuyo da fuskar Aljal tace
yata nashiga duhu kigayan meke faruwa Dan
Allah, Ajlal tayi murmushi karki damu ummana ba
Abunda kike tunani bane baima shafe hakan ba nd
Karki taba tunanin hakan zai faru bi’iznillah,
ummy tayi murmushi shikenan yata Allah yashige
mana, Amma ki tabbatar koma menene kece da
gaskiya, Ajlal tace kinfi kowa Sanina kece mutum
nadauko dazai bada labarina so baki bukatar
wani bayani akan hakan, ummy tace Karki sauya
Aljal kimun al-qawari kudi ko mulki baxasu saka
kimanta koke waceba ‘ Ajlal tace Toh ummyna
Zan kiyaye Albina a kitchen zatayi fanke Amma
me a yau ta kwaba kullum Kuma take tunanin
zaiyi gashi ba rana, se hayaniya take da kaya
takashe Abun glass yafi biyar, sadauki yayi tsaki
yakoma bedroom dinshi, se 12 sann tagama hada
komai takira wata hadimar ta gyara kitchen din
tayi wanke2, yunwa kam tacisa kamar me raben
dayaji irin wannan tin kan yasamu hatsabibiyar
yarinyar nan. Brush yayi yafito tin a daki yake jiyo
Kairi baidai yi magana ba seda yaxo cin fanke
Wanda yayi black tamkar gawayi, a storace yakai
daya abaki ya kutsira ganin ta kura masa ido
wani irin daci yaziyarci zuciyanshi gakuma uban
mai dayasha atake ya furzar beena mekika mun
haka kasheni zakiyi kome miye wannan abun,
baikarasa magana ba amai taxo masa da gudu
yayi toilet yana kwara a man da bakomai acikinsu
se tsabar yunwa gakuma ulcer. Part 10 Yana
gama aman yakai kasa yafadi, Albina da Dan
tanin suka shigo suna taslima kan gado suka
Maida Shi bayan Sun goge masa bakinshi, Albina
tace Dan tanin la gyara masa toilet dinn Ni zanje
Inyi wanka, Dan tanin ya kalleta cike da haushi
yace shikenan, bayan yagama Ne yace Dan Allah
sadauki kabari akira yarinyar nan nafahimta
abuncinta kadai yake iya kosadda kai, nikaina
danake cin ragowar naka wlh 2dyz dinn nakasa
cin kowani abunci se Kayan kwalama, plss oga,
sadauki yace nakoreta ne, Dan tanin yazaro ido
kan wane dalili, ya amsa a kufule Albina bataso,
Dan tanin yaja dogon tsaki wannan yarinyar seta
rabaka da kowa naka aduniya wlh, Mama kam
taga har azahar sadauki baixo gaidataba hakama
Mai martaba dakanshi yaje domin dubo lfyr gidan
dansa atare suka Hade da mama, tace kaima kaji
shiru koh? Sarki yace kema kin sani bazan iya
zama batareda nasan halin da dana yake cikiba
lfy ko rashinta, mama tace hakane Allah yaraya
mana Shi yabashi ikon adalci da rikon amana
tamkar yanda mahaifinsa yayi, sarki yace amin
yakuma kara masa kyawawan halaye irin nakiba
mama tadago idonta tasakar masa murmushi
Wanda yake kara masa sonta azuciyarshi
hannunta yajawo yarike mama ta kallesa fuskar
ta dauke da murmushi muna kan hanya fah, sarki
yace toh ay hannun matata na rike bana wata ba
kokinso na rike hannun wata ne, mama ta girgiza
kai tasauya fuska, dariya yayi aikece farko da
karshe agareni, mama tace Allah yabarmun kai
ogana yakara Nisan kwana, ya amsa da amin
tareda rungumota zuwa jikinsa, Dan tanin suka
sama yana moping se uban ruwa daya zube,
mama tace aa Dan tanin lfy Ina Ajlal? Dan tanin
yace ranki yadade Waye Aljal? Mama tace
yarinyar dake mawa Ajlah ayki mana, se alokacin
yakira taresuke da sarki atake yazube kasa yana
kwasar gaisuwa, sarki yace Ina son meke
damunsa yau ban gansaba, Dan tanin yace
zazzabi ne ranka yadade, subhanallah yasha
magani kuwa Inji mama, Dan tanin yace Ina
tunanin hakan Dan Albina na ciki, Mama ta Bata
fuska metake adakinsa Nifa Bana son irin wannan
takalli sarki da shikanshi ita yake kallo tace ayi
auren Nan kowama yahuta plsss, Yaja hannunta
suka shiga cikin dakin kan dadduma suka sameta
tana Sallah hakan yasanya zuciyarta yin sanyi
dakuma ta mai martaba, tana gamawa tayi da
gudu gurin mai martaba ta rungume Shi abbana
sannu da zuwa ya amsa cike da fara’a idonshi na
kan sadauki, gurin mama takoma mamana sannu
da fitowa mama tace yauwa yar shagawaba ke
har yanxu kinkasa gane kin girma kineda shiga
jikin babba koh nan gaba kadan kema Umma
za’akiraki Albina ta juya tana dariya. Son meyake
damunka? Sadauki yadago yace zazzabi fah ne
abbana Kuma naji sauki insha Allah zanfito
anjima ingan fafatawan jarumai, Gud son Amma
katabbar kasha magani yace zankiyaye ranka
yadade, mama tace yauwa lfy bangan Aljal tazo
aykiba dakinma kamar ba’amsa gyaran safeba
banji kamshi natashi ba, sadauki yace momma
yarinyar nan batada kirki wlh na koreta, mama
tace fuck you. Son bazaka taba samun irinta ba
wlh I’m telling you, tsabta Amana hankali da
biyayya iya girkinma ba wasaba, Saduki yace
anemo wata dai mama ‘ tace Kutt nagaji da
samomaka masu ayki kana wulakantawa, sadauki
yayi fuskar kuka abbana kasa baki mana, sarki
yace nope tsananin da uwa ba’a shiga kaidai ka
gyara halayenka ahakan kake tunanin zaka iya
shugabanci in Bani adoron duniya? Ajlah yasadda
kai kasa, mama tace Ni Kaga fitata Kaine aruwa,
Yau kusan sati daya kenan da korar Aljal dayayi
ko ince data bar zuwa gurinsa ayki harya fara
Rama saboda rashin cin abunci dayake, sedai
Albina takawo masa na ummanta hakanan yake
daurawa yaci badan yasoba, Dan tanin yace
ranka yadade kayi hakuri mezai hana kamaida
yarinyar nan kan aykinta na tabbata baxata ki
kiranka ba, sadauki yace wot kana nufin ni
nameta bazai yuba, haushina daya nakin korarta
Da mama ta hana sekace wasu Dan ginta, Dan
tanin yace Ni Zan Bata hakuri, sadauki yace
kodaya ban sakaba wann yarinyar yar zafin kai ce
gwarama kasamata ido, Dan tanin yace bazan
zuba ido Ina kallo ulcer tamaka lahadi ba daga
sarki hara mama nuzasu tuhuma akan rashin
baka cikakkiyar kulawa yana kai nan yasakai
yafice se gurin mama, bayan tamasa izinin
shigowa ta kore hadimanta, atake yamata
bayanin meke faruwa, Mama tayi shiru tace dama
nasan ita zatasa yakoreta bayan ko ruwan tea
bata iya hadawa ba bare tamasa girki saboda
masifarta yakasa yin ‘yar ayki 1, mama tace jeka
kirata Zan Bata hakuri ‘ Aljal taxo tagaida mama
tasamu guri tazauna kamarma atare suke da
sadauki zamanta keda wuya segashi ya shigo,
Mama tace yauwa gwara dakuka hadu, sadauki
yabi Dan tanin da kallon tuhuma Dan tanin
yashiga Sosa keya, mama tace Aljal kiyi hakuri
kikoma kan aikinki, Ajlal tace kiyi hakuri mama
anema min wani aikin komai wayarshi komai
wahalanshi Zan iya Amma Dan Allah kijanye
zancen sadauk

Leave a Comment