Hausa Novels

Sahibul Amrat Hausa Novel Complets

*SAHIBUL AMRAT*

🕊️👑🤺🎺

*Zainab Habib(Mom Islam*

*Bismillahir rahmanir rahim,Allah ina roƙonka ka bamu aron rai da kwanciyar hankali ,inda na fara littafinnan lafiya Allah kasa in kammalashi cikin ƙoshin lafiya amin ya rabbi.*

_Banyishi dan wani ko wata ba 🙅‍♀️ so in yazo dai-dai da labarinki/ka , arashi ne kawai_.

__________________________P 1-2

Safiyar assabar ta kasance safiyace mai cike da ni’imomi mai tarin yawa , kasancewar zafin dayayi yawa a gari sbda damina tana shirin sauka ,
Yau kam alhmdulilh antashi da iska kowa sai hamdala yake.

Cikin iko na uban giji ruwa ya sauka kamar da bakin ƙwarya , mutanen garin sunyiwa Allah godiya da wannan ni’imar da suka samu.

Tashi ɗaya ruwan ya ɗauke ya zamo sai yayyafi , hakan yayi dai-dai da fitowar wata mata daga wani gida mai ɗauke da katangar galan-galan , ginin gidan ginin ƙasa ne ,kai dakaga gidan zaka gane ba wasu masu hali bane .
Budurwar da bazata gaza shekaru 20 ba taci gaba da tafiya tanayi tana wai-wayen bayanta , gyara zaman kwalin dake hannunta tayi tare da share ƙwallar data zubo mata ta kalli jaririyar dake cikin kwalin tana wasa da ƴan yatsunta biyu a baki , jaririyar na ɗiban kama da matar dake riƙe da kwalin hakan zai tabbatar maka da cewa itace mahaifiyar wannan yarinyar.
Tayi nisa sosai da gidan da take ,taje kan wata bola mai cike da ledoji da tarkace na ƙazanta ta ajiye kwalin tare da ajiye wata farar takarda a gefe ta sunkuyo tare da tofe yarinyar da adu’oi , batayi tsoron komai ba ta juya tabar jaririyar da ganin babu mahaifiyar tata yasata fara kuka .
Kasancewar babu wanda ya biyo hanyar bare yaga matar ,hakan yasata arcewa da gudu ta koma anguwrsu , zama tayi a kan dakalin dake jikin ginin gidan nasu ta rushe da kuka mai ban tausayi ,
“Allah sarki Norr kiyi haƙuri bazan iya cigaba da ganinki a gabana ba , gara in nisanta kaina dake ko naji sanyi a cikin zuciyata , sake share zafafan hawayen dake ambaliya a kyakkyawar fuskarta tayi kana ta kunto gefen zaninta ta kuma goge fuskarta ta miƙe ta shiga gidan ,tabbas mutum ma rahama ne ,ko kukan jaririyar nan yana tayata hira yanzu kam babu ita .
Wani ɗaki dake kallon gabas ta shiga tare da sakin labulen ƙofar tana mai cigaba da yin kukan .

Gidane babba amma bashi da yawaitar ɗakuna sosai ,dan ɗakuna huɗu ne ,kuma duka ɗakunan a kulle suke da kwaɗo sai guda ɗaya wanda Zainab take ciki wato wannan budurwar wacce ta fitar da yarinya .
Hular yarinyar Zainab ta hango ,a hankali ta miƙe tare da zuwa gaban ɗan kwandon da kayan yarinyar yake ,ta ɗago hular da hannunta ta kuma fashewa da matsanancin kuka ,da sauri kamar wacce aka zabura ta fice taja mayafinta dake rataye a igiyar dake tsakar gidan ,fita tayi tabi layin da takai yarinyar .
a tunaninta taje ta ɗauko ƴarta ,a fili tace “nayi kuskure Norr nayi dana sanin ƴardake a juji “tana tafe tana magana tana share hawaye .
Dik inda ta gifta yara ne ke kallonta sbda shigar da tayi ,riga da zani ne a jikinta koɗaɗɗu sai wani mayafi ja wanda tsabar jin jiki dayayi shima ya koɗe , bata damu da kallon da yaran suke mata ba ,taci gaba da tafiya , layin data ajiye Norr tabi tun daga nesa take hange tana cewa “ina ɗaukoki Norr zan dinga baki kulawa ba irin ta daba , dana hofantar dake ba .
jin tayi tuntuɓe da ledoji yasa ta tabbatar da ta iso bolar , kallon dai-dai inda ta ajiye Norr tayi taga babu kwalin balle Norr ko zanin data kwantar da ita , wata rufaffiyar takadda taci karo da ita wacce ko ba’a faɗa mata ba ,zatace wanda ko wacce ta ɗauki Norr itace ta ajiye wannan takaddar .
Jiki na rawa ta sunkuya , ta ɗauka tashi ɗaya jiri ya fara ɗibanta da sauri ta sauka daga kan bolar ta nemi wani itace dake gefe nesa da bolar ta zauna tare da rafka uban tagumi , yanzu kam tama kasa kuka bata ma san yaza’ayi kukan yazo mata ba ,sai uban faɗuwar gaba dake ziyartar ta .
Lahaula walaƙuwwata illa billa ,ta dinga mai-maitawa ,a hankali wasu siraran hawaye masu ɗumi suka fara sintiri a kyakkyawar fuskarta , ajiyar zuciya ta sauke tare da damƙe takardar dake hannunta.
Cikin rashin ƙwarin jiki ta miƙe taci gaba da tafiya kamar ƴar maye ,
Tana isowa gidan nasu ta zube a tsakar gida tare da ɗora hannu a kanta ta tsala uban ihu tace “Norr !!” idan kaga inda Zainab take kuka dole zai baka tausayi sbda kukanda takeyi muryarta ma bata fita sosai.
A hankali ta rakuɓe jikin bango tare da rafka tagumi gunani iri-iri ne ya ziyarci zuciyarta.
Wane hannu Noor ta faɗa ?,shin waye ko wacce ce ta ɗauki Norr ?” Allah kaga halin da nake ciki Allah ka dawomin da Norr dan isar annabi ” ta ƙarashe maganar tana share hawaye .

Ƙiran sallahar da taji ne yasata miƙewa ta ɗauro alwalar azhar ta dawo ɗakin nata ta kabbara sallah ,bayan ta idar ta ɗaga hannunta sama taci gaba da kaiwa Allah kukanta , bayan ta idar da sallah ta ninke sallayar tare da jingina kanta da bango taci gaba da rera kuka .
Sallamar da taji ne yasata share hawaye tare da goge fuskarta da hijab ɗin dake jikinta , ta amsa sallamar tace “wa’alaikumussalam “ta buɗe gefen labule ta leƙa tace “sannu da dawowa baba “.
Baban dake sanye da rigar shadda ruwan goro ,hannunsa riƙe da magirbi yace “yawwa Zainabu me kika dafa mana ne ?” kanta a ƙasa sbda wasu sabbin hawaye ne suka fara zubo mata tace “shinkafa da mai da yaji ” baban yace “masha Allah ina fatan kinci kin ƙoshi ko ?”
Gyaɗa masa kai tayi alamar eh ta miƙe taje ta kawo masa ,lokacin ya shiga ɗakinsa ya zauna yana ƙirga wasu kuɗaɗe .
Da sallama ta shigo ta ajiye masa abincin kana tace “babu ruwa a gidab fa ” baban yace “haba Zainabu koke bazaki fita ki ɗibo ba? ” shiru tayi masa tare da sunkuyar da kai ƙasa a zahiri Allah kaɗai yasan inda takejin zuciyarta,ta miƙe ba tare da tace masa komai ba .

4:37pm yayi dai-dai da fitowar baba daga ɗakin da Zainab ta kai masa abinci , bankaɗa labulen ɗakin da Zainab take yayi ,har zaiyi magana sai yaga tana sallah ,ya fice .

Koda ta idar da sallah ta cire hijab ɗinta ta shiga kitchen , bayan ta haɗa wuta tayi murhu biyu , ɗaya na tuwo ɗaya na miya ,bayan ta gama zuba kayan haɗi ta rufe tukunyar miya ta gyara wutar tuwo ta koma ɗaki .

“Zainab ga pampas kisawa Aisha ” da sauri Zainab ɗin ta fito gudun kar baban ya zargi wani abu yasata miƙewa da sauri har ta kusa faɗuwa ta zo gaban baban tace “to angode “sai kuma taji tsanar mahaifin nata nayi mata mamaya a ranta .

Ɗaga kwandon kayan Norr tayi ta ajiye can ƙasa ta kuma fashewa da kuka yinin ranar dai haka ta yishi babu daɗi ko kaɗan , bayan ta gama girki tasa nata ta sawa mahaifinta ta zuba ragowar a roba ta kawo ɗaki , lokacin anata kiraye-kirayen sallahar magrib ,gari yayi duhu sosai kasancewar ruwan da aka yi kuma har yanzu da hadari sosai .
Bayan tayi magrib ta janyo tuwon ta da dama ta riga ta zuba miya ,tayi tagumi ga faɗuwar da gabanta keyi babu ƙaƙƙautawa, bayan ta gama cakular abincin ta ɗauko murfi ta rufe tare da ɗaukar buta ta kuskure bakinta ,ta dawo kan sallaya ta kabbara isha’i ,bayan ta idar tayi adu’ointa data saba ,ta shafa kana ta miƙe taje ta ɗauko takardar ɗazu wacce ta ganta gurin kwalin data ajiye Norr , gabanta na tsananta faɗuwa ta buɗe takardar tare da fara karantawa ,saƙo ne ta gani kamar haka…

_Aslamu alaikum nice na ɗauki yarinyarki ,dama na rubuta ne koda zakici karo dashi kai koma ba keba ina mai sanar muku wannan yarinyar ta zamo mallakina ,kuma yau zanbar ƙasarnan da ita _.

A zabure Zainab ta miƙe tare da kurma ihu tana cewa “wlhi bazan yarda ba , Norr zaki dawo gareni “karaf a kunnen baba lokacin ya dawo daga masallaci sallahar isha’i ,ya taho da gudu ya buɗe labulen ɗakin Zainab kana yace “Zainabu me kuma ya faru ?”

Ƙin kulasa tayi sai da yayi magana har sau uku sannan tace “Norr aka sace “ido waje baba ya dafe ƙirji kana yace “dama ansan kin aihu ne” butar dake gefenta ta wurgawa mahaifin nata Allah yayi taimako ya kauce da ya sameshi tace “baba ka cutar da rayuwata ,tunda mamana ta rasu kaƙi yarda a kaini dangin su ,yanzu gashi rayuwata ta lalace ,mutanen garinnan zasu kasa sani ne ?ni gara in shiga duniya da zama a gidannan !”

Ɗiff numfashin baba ya kusa ɗaukewa ,ya sami guri ya zauna kana yace “Zainabu aini na ɗauka komai ya wuce tunda har an shekara ,kuma inhar mijin aure kike tararradi ninan ,nizan kawo miki shi har gida karki sami damuwa “.

Da sauri ta miƙe tare da janyo jakar kayanta ta fara haɗawa tana kuka mai ban tausayi .

Kasancewar baban ya fito ya ganta kana yace “ni yanzo neman Aisha zani ki zauna inje in dawo ” Zainab tace “dangin mamana zani “tana maganar tayi wurgawa mahaifinta kallon tsana ,kalmar da ta doki dodon kunnenta itace “zan tsine miki inhar kika sanya ƙafa kika bar gidannan “rass gabanta ya faɗi bawai dan ta karaya ko taji tsoro ba ,sai dan tana shirin ƙetare maganarsa a halin yanzu babu mai faɗa mata ta saureshi ,yana fita ta fice tare da zuwa bakin titi ta tari mota zuwa , Abuja.
Koda baba ya dawo gida ya samu bata nan ,ya jingina kansa da bango tare da .
Hawayen baƙinciki suna zarya a fuskarsa,a fili yace .”na cutar da rayyuwarki Zainab son zuciya ya jani na tarwatsa miki rayuwa ,tabas da wata ƴar ce ƙarata zatakai gurin hukuma .

Su Zainab sunyi nisa sosai ,ta ciro wayarta ƙirar Nokia ta danna kiran ƙanwar mahaifiyarta , bayan ta ɗauka ne Zainab tace “momy yau ina hanya “ƙanwar mahaifiyar tata tace “kodai ƙarya kike ?nasan mahaifinki bazai barki zuwa ko nan da can ba”Zainab tayi murmishin ƙarfin hali kana tace “momy mun ma kusa sauka gashi bani da kuɗin mota “daga can ɓangaren momyn tace “bari in kun kusa tasha ki kirani Affan zai taho miki da kuɗi ya ɗaukoki “to momy “Zainab tace “cikin sanyin murya .

Cikin ikon Allah suka iso KEFI ta kuma kiran momy ,gyan gyaɗi ne ya ɗauketa ba ita ta farka ba sai da taji ana cewa “waye mai sauka a INTANATIONAL MARKET ta farka a zabure tare da cewa nice anan zan sauka “. driver na parking sai ga motar Affan nan ta tsaya , ta glass ɗin mota Zainab ta hangosa kasancewar an buɗe motar da take ciki yasata sauka tare da cewa “driver dan Allah barin karɓo maka kuɗi a gurin waccan ,dai-dai lokacin da Affan ya fito tare da isowa gurin ɗrivern ,yace “gashi mungode “babu komai “driver yace , Zainab dake tsaye kasancewar ba wani shiri suke da Affan ɗin ba tun bai kai haka ba ,idan suka zo gidansu ita da mahaifiyarta ya dinga yi musu iskanci kenan sbda baya ƙaunar talakawa ko kaɗan ,dan yaga momynsa ta auri mahaifinsu mai kuɗi .

Affan ya kalli Zainab dake tsaye ,irin kallon wulaƙancin nan kana ya ɗan taɓe baki kamar mace ,yace “zaki iya shiga wlhi daga yau kika sake yimin haka ni dake ne ,sai lokacin da kika kusa garin mutane zaki kirasu kice su baki kuɗi ?”.
Ita dai Zainab ita tasan abinda ke damunta duk ba wannan bane a gabanta .
Kai tsaye ta shiga motar abda a halin yanzu ba buƙatar dogon surutu take ba ,koda yaci gaba ba jinsa zatayi ba.

Affan dogo ne fari matashi a ƙalla zaikai shekaru talatin a duniya ,ya kammala karatunsa a halin yanzu aiki yake a company na dad ɗinsa ,inda suke sarrafa aduga izuwa kayayyaki na moruwa masu kyau

Kasancewar tsakanin kasuwar da aka sauketa da anguwar tasu da nisa ,hakan yasa sai da suka sha tafiya sannan suka iso anguwar su Affan Wuse two G.R.A.

Gaban wani haɗaɗɗen gida naga yayi parking , kai da ganin gidan zakasan nera tayi kuka ,duba da yanayin tsarin gidan da kuma nerorin da aka narka. sai da ya jira mai mota gadi ya buɗe masa get sannan ya shiga ,bayan sun shiga yayi parking a inda aka tanadar dan ajiye motoci ya fito ,tare da ƙare mata kallo kafin yace .” saura idan mun shiga ki faɗawa momyna komai kema kinsan sauran “.
Bata kulashi ba ta fito daga motar tare da gyara zaman wuyan hijab ɗinta da yaɗan yi mata yawa kana ta rufa masa baya suka ƙarasa ciki.
Da sallama ta shiga tare da faɗawa jikin momy da gudu ,kasancewar momyn na tahowa sbda taji ƙarar motar Affan kawai taji Zainab ta rungumeta tare da sakin kuka mai cin rai .
Momy ta kamo hannunta tace “zomuje kiyi wanka kiyi alwalah kiyi sallah kinga ana zafi a garin kyaji daɗin jikinki “cikin jin daɗi tabi momy ɗakinta ,tana shiga ta zube kan kujerar dake bedroom ɗin guda biyu a jere ta lumshe ido hoton fuskar Norr ɗinta na dawo mata ,da sauri ta fashe da kuka tare da cewa “innalilahi wa inna ilaihir raji’un ”
Momy da ta fito cikin sauri taga Zainab ta sunkuyar da kanta ƙasa ,taɗan ƙare mata kallo kafin tace ” daughter maza tashi na haɗa miki da ɗan zafinsa…..!

Wannan littafin na kudi ne normal grp 300 VIP 600 special 1000 zaki turo da kud’inki ta wannan account d’in 3175689751 Zainab Habibu first Bank shedar biya ta wannan number 08241799224

Idan kuma kati ne zaki d’auki hoton katin ki turomin ta wannan number 08141799224
[5/12, 12:06 PM] Mom Islam Ce: 🪂🪂🪂🪂🪂🪂
*SAHIBUL AMRAT*

🕊️👑🤺🎺

*Zainab Habib(Mom Islam*

_Banyishi dan wani ko wata na ,inhar yazo dai-dai da labarinki arashine👌_

 

_____________________3-4

A hankali ta tashi ta shiga toilet ta watsa ruwa tare da ɗauro alwalar magrib ta fito , tana fitowa taci karo da Affan a zaune ,bata ma san ya shigo ba sai ƙafarsa data buga ne ya tabbatar mata da hakan , a faɗace ya wurga mata harara kafin yace “karki ɗauka kinzo zama ne komawa gidanku zakiyi “ya miƙe ya fice .

Yakai kamar 10mins da fita ,momy ta shigo tare da cewa “tashi kije ga dadynku ya dawo ki gaishesa ” cikin bin umarnin momy ta sanya hijab tafita ,kana taje ɗakin dadyn ,sai da ta tsaya a bakin ƙofa tayi sallama bayan ya amsa ta shiga .
Kasancewar yana sama a kan kujera hakan ya bawa Zainab damar zama kan kafeta tace “sannu da dawowa dady ina yini ”

Cikin sakin fuska dady yace “lpy lou uwata yau kece a gidan namu ?”
Murmishi Zainab tayi kafin tace “dady sai anjima ”
Dady yace “to Allah ya tashemu lafiya amma dai zaki kwana mana biyu koh ?”
“Eh” tace tare da yin gaba.

Dagannan ta koma bedroom ɗin momy sukayi sallama ta wuce ɗakin da idan sunzo da mamanta suke kwana .
Tana fita momy ta zauna a bakin gado tare da yin tagumi a fili tace “to me ya sami Zainab ?kodai ta gudu uban nata zeyi mata auran dole ne ?tana tsaka da tunani taji Affan na cewa “momy nadawo daga masallaci sai da safe ”
Ba tare da ta tashi ba ,tace “Allah ya tashe mu lafiya my son “.
Koda Zainab ta kwanta sana’ar tata takeyi wato kuka ,sai dai yanzu babu ruwan hawaye sosai sai matsosu take amma sun ƙafe ,ga idanunta nayi mata zafi ,ta daɗe a haka batayi bacci ba har ƙarfe (1:10 am) na dare ,bata san lokacin da bacci ya ɗauketa ba.

Washe gari ranar ta kasance Juma’a ,ranace da mutanen gidan suke breakfast ƙarfe (8:00am) taƙwas ,bayan sun yi sallah Zainab ta fito gaishe da momy ta samu bata ɗaki tana kitchen “kai tsaye Zainab ɗin ta bita kitchen tare da durƙusawa har ƙasa tace “momy barka da safiya ”
Cike da farincikin ganin ɗiyar tata tace ” daughter barka ina fatan kinyi bacci ya isheki ?”sadda kanta ƙasa tayi kana tace “eh momy nazo tayaki aiki ne “flaks ɗin ruwan zafi momy ta miƙo mata tare da cups guda uku tace “kai dinning ” tom “Zainab tace takai dinning ta ajiye ta kuma dawowa ,a karo na biyu momy ta bata food flaks mai ɗauke da farfesun kayan ciki tace shima takai dinning ,daganan momy tace “an gama zanje wanka ki zauna ki fara ci “.
Batare da tayi musu ba taje ta ɗauko plets guda uku ta ajiye da cokali ta ɗauki guda ɗaya tasa kana ta haɗa tea ta ɗauki bredi .
Bata wani jima tana breakfast ɗinba ta kammala tare dayin hamdala ,tana shirin tashi Affan ya shigo cikin takunsa na ƙasaita zai zuba ƙamshi yake yace “keee ! ina momy ?” ko ɗago kai Zainab batayi ta kallesa ba tsawar daya daka mata ne yasa momy fitowa da sauri dan taɗan tsorata tace “lafiya Affan ?” yana wani cumo baki tare da harare -harare yace “momy wannan yarinyar nake tambaya ke amma bata bani amsa ba “murmishi momy tayi kana tace “ai ka fita sanin inda nake haba Affan yaushe zakayi hankali ? dole momy ta zauna shima Affan ɗin ya zauna ,dady daya fito yanzu suka gaishesa ya zauna sukayi breakfast , ganin Zainab bataci abinci ba ,yasa dady cewa “ƴata meyasa bakici abinci ba ?”kanta a ƙasa tace “dady ai tun ɗazu naci ”
“Ok ”
Dady yace “kana ya kalli Affan yace “yau bazakaje hospital ɗin bane ? ” Zani ” Affan ya faɗa kai tsaye ,inda abin da ya tsana bai wuce zuwansa aiki ba ,yafison a nemo a bashi yaci dady na gama yi masa magana yayi musu sallama ya fice.
Zuwa ƙarfe (10:am) Zainab tayi wanka ta taya momy gyara gidan suka dawo palo suka zauna , cikin sigar lallashi da ɗan tsokana momy tace “my daughter me yake saki kuka ko yanzu alhinin mutuwar mamanne ?” Zainab da kanar jira take , ta ɗago kai ta kalli momy ta fashe da kuka ,bayan ta share hawayenne tace “momy baba …baba … cikin rashin fahimta momy tace “to me baba yayi ?cikin kuka Zainab tace “momy akwai wata rana , lokacin watan mama biyar da rasuwa .

Ranar baba ya shigo ya sami ƴan matan maƙotanmu ƙawaye na su uku ,muna zaune kan tabarma muna hirar islamiya ,cikin faɗa ya fara korarsu har yana iƙirarin duk yarinya ko matar data sake shiga masa gida sai ya illata ta ,haka suka fice da gudu ,tun daga ranar ko an aiko yara basa zuwa gidanmu , da yamma da misalin ƙarfe (4:20) pm ,baba ya shigo hannunsa riƙe da lemun roba ,ya miƙamin tare da cemin inje in kwanta , to ni ban zargi komai ba ,tunda nasan tsakanina da mahaifina ko wasa bamayi , ina gama sha naji jikina ya mutu gabaki ɗaya , daƙyar na rarrafa naje ɗakina na kwanta jikina babu ƙwari ,gashi ina ganina a duniya ne ko a lahira ,sbda gabaki ɗaya bana ganin komai sai duhu ,inaji ina gani baba ya rabani da komai na jikina gashi na kasa ƙwatar kaina sbda koda hannuna bana iya ɗagawa , gashi yaƙi bari inzo gurinku ,tunda abin ya faru na daina fita gashi babu wanda yake leƙo gidanmu suna gudun masifar baba , har nakai wata biyar da faruwar abinda kullum cikin laulayi nake ni a zatona rashin lafiya ne ,ashe shi yasan ko meye yake faruwa ,cikin yana wata bakwai ,ya fito sosai a wata na tara da kwana goma naƙuda ta kamani da safe ƙarfe bakwai( 7:00)am , ranar banyi tsammanin zanci gaba da rauwa a duniya ba ,baba ya kirawo wata likita bama a anguwarmu take ba ,sai ji nayi baba na cewa “likita ki dubata mjinta ne ya tafi ya barta tun cikin na ƙarami ,wasu zafafan hawaye ne suka zubomin badan azabar da nakeji ba babu abinda zaisa ban yiwa baba maganar da zai daɗe bai mance ba”.
Tana kaiwa nan ta fashe da kuka ,momy ma da kukan take tace “Allah zai saka miki insha Allah zakiga sakamako tun a duniya ,to yanzu ina abinda kika haifa ?” momy ta tambayi Zainab cikin ɓacin rai ,baki na rawa Zainab tace “na yar da ita a bola satinta biyu ma lokacin “tasss tasss momy ta wanke Zainab da mari kana tace “ke wacce irin dabba ce wacce irin mara lissafi ce ?halitar Allah abin wasa ne ehe ?”Zainab na riƙe da kumatu tace “momy ki yafemin nakoma ban ganta ba “.
Momy kam ta rasa inda zata sanya ranta taji daɗi gumi ne yake karyo mata ta ko ina duk da AC da fanka dake aiki a ɗakin amma kamar babu , Zainab ma kuka take sosai sbda bata ma gama nadamar abinda ta aikata ba sai yanzu da momy ta tsinka mata mari .

Ƙarfe (2:pm) na ranar Juma’a ,momy ta mance dady ya fice sbda jinta take kamar mara lafiya ga jiri da yake neman yarda ita ,kuma batason gayawa kowa .
Ring ɗin watarta ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin data shiga ,ta amsa tare da sallama ,daga can ɓangaren naji ance “Nasir ne fa na sauya layi shiyasa baki gane ba ”
Ƙaƙalo fara’a momy tayi kana tace “ayya ɗan uwana ai naɗau murya ” uncle ɗin yace “Zee tazo koh ”
“Eh ”
Momy tace kai tsaye.
“Gani a kusa da gidanku nakusa shigowa ” tom momy tace “ta miƙe da sauri taje ta wanko fuskarta ta shafa hoda tazo gurin Zainab tace “maza jeki gyara fuskarki ” a hankali Zainab tashi taje toilet ta wanko fuskarta tasa kwalli ta fito.
Sallamar uncle da su momy sukaji ne yasa momy ƙirƙiro murmushin dole tace “oyoyo da autan Hajiya ganinka sai shekara-shekara “dariya uncle yayi kana ya gaishe da momy suka gaisa da Zainab yace “ya ƙarin haƙuri ?”sukace masa alhmdulilh ,uncle yace “amma dai kin dawo mana kenan ko ? kan Zainab a ƙasa ta kasa cewa komai sai momy da tace “insha Allah kam ta dawo ” uncle yace “masha Allah ni ina Affan ne ?rabona dashi wata shida kenan “momy tace “ɗazun nan dadynsa ya gama yi masa faɗa akan zuwa gurin aiki inaga ya tafi “daganan momy ta tashi ta kawo masa kayan motsa baki ta janyo tebur ɗin gilashin dake ajiye a tsakiyar palon ta ajiye tare da cewa “ina Farida amarya “uncle yace “ai da taso biyoni nace tazo ita kaɗai “momy tayi murmishi kana tace “Allah sarki “.
Daganan suka ɗan taɓa hirarsu har wajen ƙarfe (3:pm) uncle yace zai tafi ya ajiyewa momy 20k yayi musu sallama ,har bakin motarshi suka rakashi sai da ya ɓace suka dawo gida ,suna komawa momy ta ciri 10k taba Zainab tace koda zata buƙaci wani abun.
Suna zaune suna kallo kowannensu da abinda yake saƙawa a ransa , momy batason kaf familynsu kowa yasan abinda ya faru da Zainab dan haka take ta tunani iri-iri , gadai T.V nayi amma kaf ɗinsu babu wanda hankalinsa ke gurin , zuwa ƙarfe( 3:50pm) anshiga sallahar la’asar kasancewar juma’a tanada ƙurarren lokaci , momy ta fara tafiya sallah Zainab ma ta tashi ta wuce ɗakinta ,bayan Zainab ta idar da sallah ta ɗan kushingiɗe bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita .
Har momy ta kammala abincin dare bataji motsin Zainab ba ,ta taho bakin ƙofar tata ta ɗan buɗe kaɗan ta ganta a kwance a kan sallahaya ta girgiza kai ta koma gyara kitchen , sai da ta gyarashi tsaf ta fara ɗibo abincin tana jerewa a dinning , bayan ta kammala ta wuce ɗakinta tayi wanka ta shirya tsaf cikin doguwar riga baƙa mai adon golden ɗin duwatsu masu kyau sai sheƙi suke ga wasu ɗan kunne da sarƙa da momy tasa sunyi mata kyau sosai , kasancewar daga daren ranar Juma’a har assabar da lahadi ,dady baya fita aiki sai ranar litinin yasa momy take bawa ranakun muhimmanci gurin gyara jikinta da fitinannun turaruka masu ɗaukar hankali .
Kiran sallahar mgrib da aka ƙwala ne ya farkar da Zainab daga bacci tayi mamakin baccin da tayi ,ta tashi ta ɗauro alwalah ,sai da akayi isha’i sannan ta fito palo ta zauna kan sofa tare da cewa momy “sannu da aiki momy “sai kuma tayi murmishi tace “momy kinga inda kikayi kyau kuwa ?…!

Wannan littafin na kudi ne normal grp 300 VIP 600 special 1000 zaki turo da kud’inki ta wannan account d’in 3175689751 Zainab Habibu first Bank shedar biya ta wannan number 08241799224

Idan kuma kati ne zaki d’auki hoton katin ki turomin ta wannan number 08141799224 y’an Niger suyi magana ta wannan number +22784506476 .

MOM ISLAM
[5/12, 12:06 PM] Mom Islam Ce: 🪂🪂🪂🪂🪂🪂
*SAHIBUL AMRAT*

🕊️👑🤺🎺

*Zainab Habib(Mom Islam*

 

 

 

_____________________5-6

Itama momy tayi murmishi kana tace “aikuwa nagode “sukasa dariya .
sai da akayi isha’i sannan dady ya shigo ,kai tsaye bedroom ɗin momy ya wuce ya sameta zaune a kan sallaya tana adu’a , sai da ta shafa shima ya shafa sannan tayi masa sannu da dawowa yace mata yawwa , sukaɗan taɓa hira ta shiga toilet ta haɗawa dady ruwan wanka ya shiga .
Bayan ya fito ta taimaka masa ya shafa mai ta ciro masa kayansa yasa ta fashe shi da turare mai ƙamshi suka fito a tare ,cike da soyayyarsu wacce ko kaɗan bata tsufa .

*ƊAN ƊANO*
Bayan shekara 19
Wata hamshaƙiyar mota fara ƙirar Bugatti Chiron: 261 mph. ce ke sharara gudu a tsakiyar titin Hanwa low-cost , baƙar mota ce mai ɗauke da baƙin gilashi , yayinda wasu motoci haɗaɗɗu sharon guda biyu ke biye da motar , gudu suke sosai kamar zasu tashi sama , motar dake tsakiya ce taɗan rage gudu , leƙawa nayi na hango wani farin saurayi amma ba fari sosai ba , yana ɗauke da fararen idanuwa gashin kansa baƙi sosai gashi kamar na larabawa hancinsa dogo shi kansa yana da tsayi amma madai-daici yana da faffaɗan ƙirji ,shafo baƙin sajen fuskarsa ɗan rausayar da kansa kafin ya kalli wayarsa ƙirar iPhone 13 ya duba agogo ,ƙarfe(4:00 pm) na yamma ya gani kana ya mayar da wayar tasa aljihu kafin yace “Abdallah kaini gidan gona mu juya “an gama ranka shi daɗe Allah ya taimaki yarima mai jiran gado “Abdallah yace tare da juya akalar motar zuwa tudun wada ,motocin dake biye dasu a baya suma suka juya tare da bin bayansu , a wata anguwa sukayi parking motocinsu gaban wani farin get ,horn sukayi get man ɗin yazo da gudu ya buɗe musu , motar tsakiya ce ta fara shigewa mai gadi har ƙasa ya durƙusa yana cewa ɗan sarki jikan sarki Allah ya taimaki yarima mai adalci “murmishi kawai saurayin yayi kana suka tsaya a gurin ajiye motoci , bayan an yi parking aka buɗewa prince Khalil mota ,ya ziro kyawawan fararen ƙafafuwansa wanda suke cikin takalmin sarauta , gyara zaman alkyabbar jikinsa yayi kana ya juya ya kalli dogawaransa da suke masa kirari ya kalli Abdallah wato abokinsa da ya zamo masa driver a yanzu yace “bana buƙatar a biyoni Abdallah muje ciki “ci gaba da kirarin sukaci gaba dayi har prince Khalil ya ɓace daga ganinsu ma’ana sun shige ciki.
Da shigarsu Abdallah ya janyo wata haɗaɗɗiyar kujera mai ɗauke da sunan prince Khalil yace “ogana ka zauna man “sai da prince Khalil ya gama isa da taƙamarsa wacce kowa yasansa da hakan sannan ya zauna kafin yace “bismillah”
Wannan hali na prince Khalil yana birge mutane musamman ma mahaifinsa mai martaba abu ɗaya ne yasa mai martaba yake yawan yi masa faɗa shine , yayi aure yaƙi yayi dan har sun fara shawarar haɗashi da wata yarinyar ƙanin mahaifiyarsa shikuma yace a’a Allah ya taimakesa maganar bata isa gurin sarki ba .
Abdallah ne ya kalli Khalil kana yace “prince ya maganar Hindu ne “rai a ɓace prince ya kalli Abdallah kana yace “pls karka taramin zafin kai ba wannan maganar nakeson muyi ba so kayimin shiru “.
Murmushi Abdallah yayi wanda yasan dole suyi faɗa tunda ya takaloshi akan maganar ,
Prince ya kalli agogon hannunsa kana ya ɗan lumshe ido sbda iskar dake ɗan kaɗashi yana jin daɗi kafin yace “Abdallah so nake ka rakani gidan marayu akwai abinda zanyi a can so daga nan sai mu koma gida ” tom an gama prince nawa “Abdallah yace “yana murmishi .
A hankali prince ya miƙe shima Abdallah ya miƙe suna fitowa prince yakai dubansa ga dogarai yace “zamuje anguwa so inaso ku koma gida” da sauri suka kalleshi kasancewar a durƙushe suke sukace “Allah ya taimaki yarima mai martaba yace “mu daina barinka kana fita kai kaɗai saboda abinda ya faru rannan “Abdallah dai yana gefe yana gudun yayi magana a tsigeshi , sai da prince ya ɗauki tsawon lokaci kafin yace “yanzu dai bazaku iya tafiya ba kenan “da sauri suka kuma sadda kansu ƙasa kana sukace Allah ya taimaki yarima umarninka zamubi “Abdallah yace “a kira da security “harara prince ya gallawa Abdull wacce ta sashi sunkuyar da kai nan da nan dogarai suka shiga mota suka bar gurin .
Bayan tafiyarsu prince ya kalli Abdull fuska a tamke yace “wai ni ƙaramin yaro ne da zasu sani a gaba suna gadi ?”kai kuma kaci gaba “.
Ya nuna Abdull .
Ba tare da Abdull ya kulasa ba ya shiga mota mazaunin driver shima prince ya shiga ɗayan side ɗin suka bar gurin , gaban wani katafaren plaza prince yasa akayi parking yace “Abdallah ya siyo duk wani abu da marayu suke da buƙata “cikin bin umarni prince yace “an gama “ya fito ,ganin prince ɗin ya fito shima yasa Abdallah cewa “haba ka koma man “no nima zanga gari “prince ya faɗa fuska a tamke “haka suka jera cikin harabar gurin suka shiga plaza ga mamakinsa bai san kaf mutanen gurin ba amma sai ji yayi ana cewa “ga yaron sarkin garinnan mai yawan zuwa gidan marayu ai ana nunoshi talabijin “kan prince a sunkuye Abdallah ne ke ƙare musu kallo har suka shiga cikin shagon , Abdallah ya fara lisaafa abubuwan da akeda buƙata , bayan an gama loda musu a bayan mota prince ya biya kuɗin suka fito dan shiga mota , karo sukaci da wata yarinya doguwa bata da ƙiba tana da kyan diri gata da hips da pink lips gashin idonta ya ɗanyi ja yayinda gashin girarta yake baƙi wuluk ,ikon Allah kenan .
Wayar dake hannunta ƙirar Gionee mai ɗan ƙaramin kuɗi wanda a ƙalla zaiyi 20k .
Faɗuwar da wayar budurwar tayi ne ya sata waro kyawawan idanuwanta tare da ɗorasu a na prince ,tashi ɗaya ta tako daf dashi tana huci suna iya jiyo nunfashin juna tace “sai na nuna maka kai ɗan ƙaramin ɗan iska ne !” da sauri Abdallah yace “ke bakisan ko dawa kike magana ba koh ? tsaki budurwar tayi kana tace “ba damuwata bane insan koshi waye amma wannan wayar daka lalata wlhi sai ka biyata ko in nuna maka inda ake tashanci ” tunda ta fara magana prince ke kallonta yana wani killer smile tashi ɗaya ya dake yaja da baya kana yace “Abdull muje kawai ” da gudu tabi bayansu cikin rashin sa’a har suka kai ka shiga mota suka rufe bata cimmasu ba ta bugi gilashin motar da hannunta kana tace “wlhi kokai waye kaci bashi ” taci gaba da tafiya idonta yayi jajir kamar tayi kuka , a hankali suka dinga tafiya har sai da sukaga gidan data shiga sannan prince yace su wuce .
Sun kusa zuwa gida wayar prince ta fara ring , da sauri ya ɗaga cikin girmamawa yace “tuba nake mai martaba insha Allah bazan ƙara ba ” sai kuma naga ya ajiye wayar ransa a jagule ,
Abdallah yasan a halin yanzu koda ya tambayi prince bazai faɗa masa abinda ya faru ba sai dai dan kansa in yaso .
A wani katafaren gida naga Abdull yayi parking gidane da ganinsa kasan gidan sarauta ne , duba da yanayin zane irin sarauta tun daga wajen gidan har i zuwa ciki ko ina yana ɗauke da tambari irin na sarauta , kirarin da ake musu ne yasa Abdull tafiya a hankali yana amsawa fuska a sake ,yayinda shi kansa yariman fuskarsa take a tamke babu alamun wasa ,dama yawan fara ‘a ba aikinsa bane ko yawan magana miskilanci yafi masa yawa .
A hankali suka ƙarasa ciki naga Abdull yayi parking a inda aka tanadar dan ajiye motoci ,yana zuro ƙafafuwansa dogarawa suka fara yi masa kirari suna cewa “Allah ya ƙarawa yarima lafiya ɗan sarki jikan sarki .
Ko uffan baice musu ba ya wuce kai tsaye fadar mai martaba , a bakin ƙofar ya ƙirƙiro murmishin dole kana ya shafa fuskarsa tun daga goshinsa har haɓarsa tare da yin sallama .
Da shigarsa dogarawan dasuke zaune suka fara kwasar gaisuwa ,amsawa sukayi ciki harda mai martaba ya sadda kansa ƙasa ya kwashi gaisuwa gurin mai martaba kana shiru yaɗan biyo baya .
“To Alhmdulilh dama maganar da nakeson yi dakai shine , mai yasa kakeson fita kai kaɗai alhali kasan hatsari ne yin hakan ?”
Kan prince a ƙasa yace “tuba nake Abbana insha Allah bazan sake ba ”
Murmishi mai martaba yayi wanda ba lallai ne ka gano hakan ba ,sbda rawani daya rufe masa ilahirin gefen fuskarsa “zaka iya tafiya ” mai martaba yace yana kallon Yarima Khalil .
A hankali prince ya tashi tare da ɗan sadda kansa yace “na barka lafiya ya Abbana ” prince ya fita.

Wani gida naga ta shiga ,gidane madai-daici yana ɗauke da ɗakuna uku daga gefe kuma wata matace wacce a ƙalla zatayi 40yrs tana sanye da dogon wando na jeans hannunta riƙe da kuɗaɗe masu yawa , shigowar budurwar da tayi ne da gudu yasa datijuwar cewa shamsiyya mai ya faru na ganki haka ? wacce aka kira da Shamsiya tana huci tare da cuno baki tace “mama wani saurayi ne ya bigeni na fasa wayata nayi ƙoƙarin binsa ya gudu “tsaki maman tayi kana tace “ke nifa banason ki dinga yawan fushi inhar waya ce sai wacce kika zaɓa amma kafin muci gaba da magana inaso kiyi sauri kije ki sallami alhaji Ubaid “waro ido tayi tare da dafe goshi kana tace “ni walhi bani son zuwansa mama dan Allah kice bana nan ” waro ido maman tayi kana tace “ai kuwa baki isa ba ,ko kije ki bashi abinda yake nema ko inci miki mutunci “wata budurwa ce ta fito daga ɗakin dake kallon nasu tana ɗan yamutsa fuska tace “mama Sadiƙ fa yana ƙofar gida kuma yau dai Allah yayi taimako zai ƙaramin 20k ya zamo 50k “tafawa sukayi da maman tace “yawwa ƴar gari kinga irin abin da nakeso gashi ita wannan tana neman wancan attajirin ya gudu mana “ɗagawa budurwar hannu mama tayi kana tace “baby a dawo lafiya ”
Da ƙyar Shamsiya ta yarda da zuwa gurin Alhji Ubaid sbda bata ƙaunar irin kwashen mutane haka ,hannunta mama taja tare da kaita wani ɗaki ,ɗakin cike yake da kayan kwalliya da kayan sawa kama daga turaruka mayuka da shu’umar humra da idonka idona da sauransu ,
Tasha mutsika aka sauya mata kaya i zuwa shadda ruwan madara tasha aiki ja tayi kyau sosai tasa mayafi ja da takalmi ta fito ,ganin fuskar babu fara’a yasa mama cewa “haba shamagirl ki ɗayi murmishi man “murmishi tayi badan taso ba wanda yasa point ɗinta dake kumatu loɓawa ta wuce gurin Alhji Ubaid ,tana shiga ta samesa zaune kan sofa wacce inhar sunyi baƙi to ɗakuna biyu nasu ne koda kwana zasuyi , hannunsa riƙe da kofin gilashi yana shan ruwa , jin shigowarta ya sashi ajiye cup ɗin hannunsa yaje da sauri ya rungumeta kasancewer shi ba wani mai ƙiɓa bane amma yana da ɗan jiki badai irin sosai ɗinnan ba, fuskarta a ƙirjinsa ta ɗan…!

Wannan littafin na kudi ne normal grp 300 VIP 600 special 1000 zaki turo da kud’inki ta wannan account d’in 3175689751 Zainab Habibu first Bank shedar biya ta wannan number 08241799224

Idan kuma kati ne zaki d’auki hoton katin ki turomin ta wannan number 08141799224 y’an Niger suyi magana ta wannan number +22784506476 .

MOM ISLAM
[5/12, 12:07 PM] Mom Islam Ce: 🪂🪂🪂🪂🪂🪂
*SAHIBUL AMRAT*

🕊️👑🤺🎺

_Funny love and romantic story_

 

 

*Zainab Habib(Mom Islam*

Free page

 

 

 

_Ina mai baku haƙuri akan soyayyar da zaku gani a cikin littafin sbda haka labarin yazo ,ina fatan zaku fahimceni _

 

 

 

 

 

_____________________7-8

 

 

 

 

Ɗan goga kana tace “barka da isowa “.
Alhji Ubaid dake ƙare mata kallo kamar yau ya taɓa ganinta yace “baby wannan wankan duk ni kaɗai ?” murmishi Shamsiya tayi kana tace “eh naka ne ”
Bayan sun zauna tunanin wayar dake hannunta ya faɗo mata ,a zuciyarta tace “duk da farfashewar da gilashin wayar yayi bai hanata yimin amfani ba , sai ta zuba tagumi .
Alhj Ubaid dake karantar yanayinta sbda yaga damuwa ƙarara a fuskarta yaɗa dada matsawa daf da ita kafin yace “mai ƙamshi na tunanin me kike ?” cikin sigar shagwaɓa Shamsiya tace “uhm uhm ba wani mutumi bane ya bigeni wayata ta faɗi ta fashe gashi taƙi kawowa ”
Alhj Ubaid dake tsananin son yaji anyi masa shagwaɓa ,ya ɗan jijigata alamar rarrashi kana yace “karki damu inhar waya ce kin samu baki da matsala amma kafin nan a bani abin ”
Farr tayi masa da ido kana tace “yanzu kam ai ina period i promise jibi har sai ka gaji “bai wani damu ba ya tuntsire da dariya kasancewar a inda tayi masa magana dole ta ɗauke masa hankali .
Hannunta ya kama suka fito tsakar gida , mama na zaune da redio a hannunta ,duk da Alhj Ubaid yaga mama bai sake mata hannu ba ,itako mama sai murmishi take na jin daɗi.
Suna fita suka nufi gurin motarsa ,haɗaɗɗiyar motace mai kyau har wani fitar da raɓa take fara sol.
Alhj Ubaid ya buɗe mata gaba ta shiga ya shiga mazaunin driver ,bayan sun rufo motar a hankali ya fara driving  yanayi yana satar kallonta ,a wani katafaren shagon siyar da wayoyi naga yayi parking da sauri ya buɗewa Shamsiya ta fito ,ya rufe suka shiga shagon da sallama , amsawa mutanen shagon sukayi tare da yi musu sannu da zuwa , wani daga cikin masu zama a shagonne ya ajiye musu kujerar roba guda biyu , bayan sun zauna Alhj ya kalli Shamsiya kana yace “mai ƙamshina wace iri kikeso ?”murmishi tayi kana tace “duk wacce na samu ” Alhj ya girgiza kai kafin yace “ba girmanki bane dole sai wacce kikeso kamar inda nima na zaɓo tauraruwa ” miƙewa tsaye tayi tare da nuna wani kwalin waya a jiki an nuna google pixel 2 , murmishi kawai Alhjn yayi tare da miƙa ATM ɗinsa , bayan sun miƙa masa pos yasa code aka cire iya adadin kuɗin wayar , jikin Shamsiya har wani tsuma yake tsabar farinciki da jin daɗi , a gurin ta rungume Alhj tare da manna masa kiss aka sanya musu a leda suka fito , kai tsaye hanyar da zata sadasu da gida suka nufa yana driving yana kallonta a karo na biyu yana murmishi , kafin yace “, Me ƙamshi na ” na’am tace “masa fuskarta yalwace da fara’a kasacewar ta kasa ɓoye farincikin dake ranta , Alhj ya nisa tare da rage gudun da yake ya kamo hannunta kafin yace “ada nasan kinyi taraiyya da mazaje da yawa ,a halin yanzu na haneki da kula ko wanne namiji ,bana son tarkace pls ki kiyaye inahar kinaso mu zauna lafiya “tashi ɗaya idon Shamsiya ya sauya i zuwa ja jawur ta share ƙwallar data zubo mata kana tace “ni ban taɓa amimcewa da kownne namiji ba !babu saurayin da yasannni duk wanda ya gaya maka haka wlhi yayi ƙarya ” da sauri Alhj yai parking a gefen hanya a zuciyarsa cewa yake “maganar wannan yarinyar ba abin yarda bane ko kaɗan ,uwarta fa gogaggiyar ƴar bariki ce  , babu wanda bashi da tarihin UWAR BARIKI ta shahara gurin tara maza a gida ,gashi yanzu ƴaƴanta sun gajeta tun kafin ta mutu , tsinkayo muryar Shamsiya yayi tana magana tana cewa “nasan ko ita maman namu bazata amince ba bare kai da kasan gidanmu yayi suna a gari ”  uhm ” Alhj Ubaid yace kana ya kalleta ya kuma kallonta sai kuma yace “nidai ki ajiyemin kanki karki bawa kowa kimin alƙawari yin hakan zai sa in tabbatar ke masoyiyace ta gaske “kallon wayar hannunta tayi ta tuno tsadarta ta kalli Alhjn kafin tace “nayi maka alƙawari ” okay yace dan shi har yanzu yana ganin she is not… a haka suka ƙarasa ƙofar gidansu ta fito shima ya fito , har zata wuce ya tsayar da ita ,kashe mata ido yayi kafin yace “idan kuɗin acct ɗinki sunyi low ki kirani pls ” murmishi tayi kana tace “insha Allah zan kiraka , ta wuce gida shikuma ya shiga mota .
Tana shiga ta samu mama ta tashi a gurin , ta shige ɗakin maman tana cewa “mama zokiga wayata , mama dake kwalliya a uwar ɗaki kasancewar zatayi baƙo bayan isha’i.
Maman tace “Shamagirl shigo ” da sauri ta ƙarasa tana dariya ta ajiye wayar a cinyar mama ,waro ido mama tayi cikin farinciki tace “bayan 100k ɗin daya baki ?”eh Shamsiya tace ” mama tace “to yanzu ba gashi kin samo arziƙi ba ,ana binki da arziƙi kina gudu , dariya sukasa tare da tafawa ,
Sallamar da baby tayi ne yasa mama amsawa tare da cewa “kinga Shamsiya tayi waya ƴar yayi ” ta miƙawa baby wayar , taɓe baki baby tayi kana tace “aikuwa gashi nan Allah ya sanya alkairi “kasancewar murmishin yaƙe take duk basu lur da abinda take ciki ba , ƙasan zucitarta ji  take kamar an caka mata wuƙa ,gefe koma tanajin wataran sai ta ɓatar da Shamsiya a doron ƙasa.

A take a gurin taba mama kyautar 50k a cikin kuɗin da alhj yayi mata transfer , albarka sosai mama tasa mata kana ta miƙe bayan ta sanya kaya riga da wando mai roba.
Zama Shamsiya tayi a kan kujera mai zaman mutum biyu tare da jona wayar a chaji kasancewar akwai wutar nepa.

Mama na fita ta danna number Alhj mai kuɗi ,ring ɗaya ya ɗaga tare da cewa “gani a ƙofar gida , cikin farinciki mama tace “ka shigo ina ɗakin da muka saba haɗuwa ” kai tsaye ta wuce fridge ta ɗibo faro da fanta da cups , takai ɗakin .
Tana jerewa a kan table taji sallamarsa , kasancewar taɗan sunkuya yasashi rungumota ta baya yana cewa “nayi missing sosai ” dariya taɗanyi kana ta juyo tana jifansa da murmishi mai kashe jiki .
Ihun da aka tsala ne yasa mama ficewa da uban gudu ta nufi ɗakinsu ,sbda muryar Shamsiya taji , tana shiga ta sami Shamsiya riƙe da kanta tana kuka , waro ido mama tayi kana ta buɗe wata samira ta ciro wani ƙullin magani ta ɗibo gaushi ta zuba mata ta luluɓeta , lokaci ɗaya ta dawo haiyyacinta .
Zama mama tayi a gefen kujera tana jera mata sannu  ,a zuciyarta kuma cewa take “meyasa wannan yarinyar take yimin haka ? sai nayi baƙo wanda zan huta dashi sai ciwonta ya tashi anya bazan ɗauki mataki ba ?” duk a zuciyarta take wannan maganar , daga ƙarshe ta tashi ta koma ɗakin Alhj mai kuɗi .
Tana shiga ta samesa a tsaye yana murmishi tare da rungumota kafin yace “Hajiyata ni zan wuce ” cikin rashin jin daɗi Uwar bariki tace “haba alhji baka karɓi tsarabarka ba zaka wuce ?” no karki damu insha Allah zan dawo zuwa gobe yanzu wani mitin ne na gaggawa ya taso min shiyasa ” sam Uwar bariki bataji daɗin hakan ba amma sai ta ɓoye damuwarta , ya ciro bandir ɗin ƴan ɗari bibiyu ya bata tayi masa godiya ya fice.

A Ɓangaren Prince tun da ya dawo daga fadar mai martaba yake jinsa cikin ɓacin rai , ya kasa mancewa da magan ganun da Shamsiya ta yaɓa masa , Abdallah ma ya fice tunda yaga idan sukaci gaba da zama faɗa zasuyi .
Nocking ɗin da akayi ne ya sashi ɗago kai da jajayen idanunsa ,a hankali ya buɗe bakinsa kamar mai koyan magana yace waye ?”
Cikin ƙasa da murya tace “nice ” bai gane ko wacece ba ya tashi kana ya sakko daga gadon ya buɗe ƙofa ,ganin Hindu tsaye ga bayi a bayanta suna durƙushe ita kuma tana jifansa da murmishi yasa Yarima Khalil cewa “meya kawoki part ɗina ? ɗan murmishi Hindu tayi kana tace “ana gaisheka baka amsa ba ” kallon bayin yayi kana yayi musu nuni da hannu alamar su tafi ,suna tafiya ya wanketa da mari ,wanda yai sanadiyar ɗaukewar jinta na ƴan daƙiƙu ,ya nunata kafin yace “nace karki ƙara zuwa inda nake kinƙi ji ko ? a kunyace Hindu ta juya ta kalli dogarawan dake durƙushe ta daka musu tsawa tana ce musu uban me kuka tsaya kallo ku ɓacemin da gani “dakatar dasu prince Khalil yayi kana yace “kai ku zauna kin wuce kinban guri ko saina ƙara miki wani ga dukkan alamu bai shiga jikinki ba ” gudun karya kuma kunyata ta a gabansu yasa ta juya zuciyarta na tafarfasa .
WACECE HINDU?
Hindu ƴace ga Hajiya Rabi amaryar Sarki , Hajiya Amina itace babba , sai da ta shekara Ashirin da biyar shekararta ɗaya da aure Allah ya azurtasu da samun cikin Ibrahim Khalil , tun yana ƙarami ya taso da hazaƙa da wayo ,mai martaba yana ji dashi sosai sbda duk wani abu da yake buƙata inhar baifi ƙarfinsu ba ,baya rasashi ,bayan ya gama primary da secondary ,ya ya nemi mai izinin mai martaba akan ya amince masa da ƙarasa karatunsa a India inda ya karanci Business wato kasuwanci , bayan ya kammala karatunsa ya dawo gida Nigeria ya samu mai martaba ya ƙara aure ya auro Hajiya Rabi ,lokacin yana da 32yers a duniya , ganin Amminsa da Hjya Rabi suna zaune lafiya yasa bai kawo komai a ransa ba , har zuwa neman shawara yake gurinta .
Hajya Rabi harta shekara biyu Allah bai bata aihuwa ba,idan ta matsa akan maganar sai mai martaba yace “akwai lokaci , babban baƙincikinta shine inda taga duk wani taro ko shawara da hidimomi mai martaba sai dai yayi da prince Khalil , hakan yasa ta tsanesa kamar ta kasheshi , bata ƙaunar ganinsa tare da mai martaba .
Ranar wata Laraba da safe ƙarfe( 7:12) aka kirata a waya , da suri ta ɗaga tare da sallama , muryar Hindu taji tana kuka tana cewa “Hajiya momyna ta mutu bata nunfashi “a razane Hjya Rabi ta wuce gurin mai martaba tare da neman izininsa ,bayan ya amsa mata tare da cewa “Allah ya jishemu alkairi ta wuce ita da dogarai biyu da jakadiya a motar da take motar baya kuma ta dogarai .
Suna isa gidan suka sameshi a cike da mutane har anyiwa momyn Hindu sutura an kaita , Hjya Rabi tayi kuka sosai .
Bayan anyi bakwai Hjya Rabi ta nemi a bata Hindu zata tafi da ita ,daga danginta harna mahaifinta basu hana ba ,saima fatan Allah ya tayata ruƙo da suka yi mata ….!

Wannan littafin na kudi ne normal grp 300 VIP 600 special 1000 zaki turo da kud’inki ta wannan account d’in 3175689751 Zainab Habibu first Bank shedar biya ta wannan number 08241799224

Idan kuma kati ne zaki d’auki hoton katin ki turomin ta wannan number 08141799224 y’an Niger suyi magana ta wannan number +22784506476 .

MOM ISLAM
[5/12, 12:09 PM] Mom Islam Ce: 🪂🪂🪂🪂🪂🪂
*SAHIBUL AMRAT*

🕊️👑🤺🎺

*Zainab Habib(Mom Islam*

_Banyishi dan wani ko wata na ,inhar yazo dai-dai da labarinki arashine👌_

_________________9-10

 

 

 

tun daga ranar Hindu ta koma gurin Hajya Rabi.
Hindu fara ce tana da ƙiba amma bamai muni ba ,ba wata kyakkyawa bace amma baza’ace mata mummuna ba.
Bayan dawowar Hindu ,Hjya Rabi ta fara shawarar haɗa Hindu da prince aure ,amma gefe ɗaya bata sonsa ko kaɗan , prince ya lura da irin tsanar da Hjya Rabi take nuna masa hakan yasa ya dena zuwa sashinta koda kuwa nemansa take sai dai tazo da kanta ,
Hajiya Amina mace ce mai mutunci bata jin ƙyashin yiwa kowa abin arziƙi ,
Lokacin da Hindu ta cika 50days a gidan su prince Hjya Rabi ta sami mai martaba akan tanason a haɗa auran prince da Hindu , mai martaba sam bai amince ba sabda rawar kan da yarinyar take dashi , bugu da ƙari tarbiyya bata isheta ba ,amma yace “ni nawa mai sauƙi ne inhar Ibrahim ya amince to nima na amince “cikin farincki ta dinga jerawa sarki kirari daga ƙarshe tabar gurin .
Burinta shine inhar Hindu ta auri prince sun warke sarki na mutuwa prince zai hau mulki idan prince ya mutu yaron Hindu Za’a naɗa , dalilin kenan.
Back to story.
Hjya Amina ce zaune a kishingiɗe jikin wani haɗaɗɗen filo ,gefe kuma jakadiya ce zaune tana ɓarewa Hajiya Amina ayaba , Hajiya Amina ta kalli Jakadiya kana tace “ni kuwa Hindu tana nan ?” Jakadiya tace “ranki shi daɗe ai ɗazu ma na ganta a gurin yarima ,ga dukkan alamu saɓani suka samu “Hjya Amina tace “mai ya kaishi shiga harkarta ?” Jakadiya ta sunkuyar da kai kana tace “Allah ya taimakeki wlhi basan meya haɗasu ba “Hjya Amina tace “shikenan .
Washe gari ta kama Alhamis da misalin ƙarfe biyu na rana bayan anyi azhar ,Prince Khalil ya shigo side ɗin Amminsa ,tun daga nesa dogarai suke kwasar gaisuwa har ya so ɗakin Ammin nasa ,sallama yayi kana ya ɗan sunkuyar da kai cikin girmamawa yace “barka da hutawa Ammi da fatan na sameki lafiya ” Jakadiya dake gefe sai kirari take yiwa prince tana cewa “Allah ya taimaki ɗan sarki jikan sarki takawarka lafiya yarima mai mai jiran gado “Ammi ce ta ɗaga mata hannu alamar ta basu guri , cikin girmamawa jakadiya tace na barki lafiya .
Tashi zaune Ammi tayi ta kalli fuskar prince taɗanyi murmishi wanda ita kaɗai tasan ma’anarsa ,kafin tace “,ubana kwana biyu na lura dakai kana cikin matsala wani abunne ya faru ?”ɗan rausayar da kai Khalil yayi kafin yace “Ammi Hindu ta fita a harkata wlhi zan saɓa mata “Ammi tayi gyaran murya kana tace “ni kaina ba son haɗin nan nake ba ,saboda Hindu bata da kamun kai ko kaɗan ,adu’armu kaɗai ce zatasa mai martaba ya janye da kuma kaima idan baka nuna kana so ba ” hankalin Prince Khalil a tashe yace “Ammi kinsan mama da naci idan ta nacewa mai martaba zai iya amimcewa ” Ammi tace “karka kawo komai a ranka ,kai dai kaci gaba da adu’ar neman zaɓin Allah ,nafilolin daren nan daka saba karka fasa.
Tunda suka fara magana wata baiwa ke tsaye a bakin ƙofar tana girgiza kai , shirun da taji Ammin prince tayi ne ya sata wucewa part ɗin hjya Rabi da uban gudu har tana tuntuɓe ,ta zube gaban hjy Rabi tace “Allah ya taimakeki uwar ɗakina Allah ya ƙara nisan kwana wata magana naji a sashen su yarima mai jiran gado “keeee…! Hjya Rabi ta daka mata tsawa tare da sauke ajiyar zuciya mai zafi tana huci tace “karki sake cemin yarima mai jiran gado dan in Allah ya yarda bazai gaji wannan sarautar da yake taƙama da ita ba inhar ba auren gimbiya Hindu yayi ba ,inhar ina numfashi a doron ƙasa bazan bari Ibrahim ya gaji sarauta ba , inada yaƙinin zan haifi wanda zai zamo sarki ko ta halin ƙaƙa ai mai martabar bawai ya tsufa bane bare ace kwanan nan za’a naɗashi ,ta ƙarashe maganar tana dafe kanta .
Hindu dake kwance a kan cinyar Hjya Rabi tace “to Umma idan har ya kasance mai martaba ya rasu kafin lokacin da zaki aihu fa ?” cikin ɓacin rai Hjya Rabi ta kalleta ,delo yasata yin shiru badan ta ƙarƙare maganarta ba .
Hjya Rabi ta kalli baiwar tata kana tace “Iyami wane zance kika jiyo ne ina sauraronki ”
Baiwa Iyami tace “magana suke akan wai yarima bazai auri Gimbiya ba ” da sauri Hjya Rabi ta janye Hindu daga jikinta kana tace “wlhi ƙarya ne ,ashe ma bacci nake “.
Bayan anyi sallahar la’asar .
Tunda Prince yabar part ɗin mahaifiyarsa ya koma nasa part ɗin , a palo ya sami hadiman nasa an cika dinning table da kayan ciye-ciye , kallonsu ya shigayi ɗaya bayan ɗaya , gaban table ɗin yaje ya tsaya tare da ƙare musu kallo sbda ganin baƙuwar fuska da yayi , haka kawai yaji jikinsa na nunar masa akwai wata matsala ,cikin takunsa na ƙasaita yaje gaban sabuwar baiwar ya tsaya kana ya nan naɗe hannunsa a ƙiji ,shigowar Abdallah ne ya dakatar dashi daga faɗar abinda zaice “Abdallah shine yaron waziri kuma babban abokin prince Khalil , Abdallah ya ƙaraso da sallama yana murmishi ,bayi na kwasar gaisuwa a gabansa ya riƙe hannun prince kafin yace “muje dan Allah kaji wata magana ” sai da prince yaɗau lokaci sannan yace “jeka ina zuwa ” ba tare da Abdallah ya ƙara magana ba ya wuce kasancewar yasan koda yaƙara magana ba lallai ya sami amsa ba , prince ya tako har gaban baiwar wato Iyami yace “a kira masa Jakadiya “cikin sauri ɗaya daga cikin bayin ta tashi tare da ɗan sunkuyawa ta fice “tana zuwa ta sami Jakadiya Hauwa’u wacce ta ke kula da part ɗin yarima Khalil ta zube gabanta jiki na rawa tace “bansan waye ya kawo sabuwar baiwa ba “amma dai yarima yace a kiraki ”
Jikin Jakadiya na rawa itama tace “to a ciki wacece baƙuwa ? bayan kowace baiwa ya santa kuma nike zaɓota ?”.
Suna tafe suke maganar gudun kar suyi babban laifi , suna ƙarasowa babban palon prince sukaci karo da bayin su uku a tsugunne ko wacce da alamun tashin hankali a fuskarta , Jakadiya ta ɗan sadda kanta ƙasa kana tace “Allah ya taimaki yarima mai jiran gado ,fuska ɗaya ce ban santa ba dan bani na kawota ba Allah ya temakeka ” wani irin murmushi prince yayi a zuciyarsa yace “baya rasa nasaba da mama ita zatayi hakan tabbas zan basu mamaki “, a fili yace “,babu komai ku barta , a fili dukkansu suka sauke ajiyar zuciya Jakadiya kam hankalinta bai gama gamsuwa da wannan yarinyar ba .
Sbda Ammin prince ce ta zaɓa masa Jakadiya a matsayin mai kula dashi kasancewar tun yana yaro take kula dashi , kuma indai zatayi abu tsakani da Allah take har yanzu bata yunƙurun cutar da Ibrahim ,dalilin da yasa ya yarda da ita kenan.
Prince yama mance da shugowar Abdallah dan zama yayi aka haɗa masa tea yasha da soyayyan dankali , sai da ya gama ikonsa sannan ya wuce bedroom ɗinsa , su kuma hadiman suka ci gaba da gyara gurin .
Yana shiga bedroom ɗin ya sami Abdallah zaune yana kallon wani indian film , Abdallah ne ya juyo tare da cewa “barka da yamma my prince “barka prince yace yana cire gilashin dake manne a fuskarsa yace “shine da ka tafi sai yanzu ka dawo ? Abdallah yace “tuba nake naje anguwarsu yarinyar nan ne ga dukkan alamu bata da tarbiya ” prince ya gyara zama kafin yace “ka mance a gidan da muka ganta ne ? “Abdallah yace “tabbas gidan da ake cewa na karuwai ne ,amma meya kai wannan yarinyar gidan ?”prince yayi murmishi kafin yace “asara ka sani ko uwartace babbarsu ?, Abdallah ya jinjina kai kana yace “nidai abin da nakeso dakai shine ka yafe mata “a tsawace prince yace “infa yafe mata kace ?yarinyar da ta yimin zagin tozarci ? to barin gaya maka wata magana idan har bakada labarin ,ba’a taɓa prince a zauna lafiya ,saina rama , ina yafiya amma baga wanda ya zageni ba ,waye ubanta waye uwarta wane matsayi suke dashi ?sai tayi nadamar abin data aikata ” cikin ƙasa da murya Abdallah yace “muyi a hankali yarma kar mai martaba yaji komai ya dagule”.
Ƙarfe 6:47 pm ) Lokacin ne da aketa kiraye -kirayen sallahar magrib kama daga masallacin gidan har dana maƙota , bayan Abdallah da prince sunyi alwalah sunyi sallah , suka wuce gurin mai martaba , tunda suke fito ake gaishesu har suka shige fadar mai martaba ,Abdallah ne kawai ke amsawa ,da sallama a bakinsu suka ƙarasa ana ta yiwa prince kirari ,yayinda mai martaba keta faɗaɗa fara’arsa.
Bayan sun kuwashi gaisuwa a gurin mai martaba fadawan suka bar gurin da sauran mabiyansu , Prince ne yayi gyaran murya kafin yace “ya Abbana nazo maka da wani albishir “cikin jin daɗi da ƙaunar ɗan nasa yace “Ibrahim ina jinka “Abdallah dake zaune kansa a ƙasa ya besan me prince zaice ba .
Prince yace “Abba Abdallah jiya ya sameni akan yana son Hindu ! da sauri Abdallah ya ɗago tare da kallon prince irin kallon da bai taɓa yi masa ba ,shiko prince murmishi yake ,yaci gaba da cewa “kuma shima Abdallahn yana sonta ” mai martaba ya faɗaɗa murmishinsa kafin yace “to masha Allah shine Abdallah ya kasa faɗa sai kai ka ari bakinsa kaci masa albas? har yanzu kan Abdallah a ƙasa yake yana mai jin zuciyarsa na dukan uku -uku ,mai martaba ya mayar da kallonsa ga Abdallah kana yace “hakane babana ?” cikin jin nauyi Abdallah yace “Allah ya ƙarawa Abba lafiya da nisan kwana ” hakan yasa mai martaba ci gaba da murmishinsu na manya.
A zahiri dai fuskar Abdallah bata nuna komai ba sbda a sunkuye take kuma ya amsawa mai martaba fuska a sake.
Bayan sun ƙara kuwasar gaisuwa sun fice ,
Mai martaba yayi hamdala dama yana yiwa Hindu adu’ar zaɓin Allah sabda maraicinta , sai gashi yau Allah ya zaɓa mata ɗansa wato ɗan wazirinsa Alhmdulilh a fili yace “yarinya ce mai biyayya nasan bazata bani kunya ba.

Suna fitowa dogarai da fadawa suka dinga jera kirari har suka ɓace , hannun prince Abdallah ya kama ya kaishi bedroom ɗinsa ya zaunar dashi kan haɗaɗɗiyar kujera , cire masa alkyabbar jikinsa yayi kana ya janyo kujera wata marar nauyi ya zauna gaban prince kana yace “haba yarima mai yasa zakayimin haka ?kasan ko me mai martaba yace min bazan iya ƙetarewa ba ?”.
Shafo sajen fuskarsa prince yayi kana yace “kai dan uwarka ni zaka rainawa wayo ,meya kawo hoton Hindu wayarka ?mai yasa duk lokacin da bayi suka rakata gurin shukokin gudannan kake leƙenta ?”.
Tsit Abdallah yayi ,kafin yace “,sai aka ce maka babu so na ƴan uwantaka sai na aure koh ?”
Hararasa prince yayi kana kafin yace “haka dai kace ,inason a haɗa bikina da naka ” ido waje Abdallah ke kallon prince sbda tunda suka taso bai taɓa ganin yayi budurwa ba amma yau shine harda mag

Leave a Comment