Uncategorized

Sirrin Wasu Gayun Hausa Novel

1💜💚💛💙❤️
Sirrin wasu gayun
💜❤️💙💚💛

 

® zuwairat (ummumaryam)

1️⃣

 

Alhamdulillah,

Free page
If you know you can’t afford to pay than don’t start reading, because after free pages comes payed ones. Thanks.

Wani saurayi né zaune cikin wata lungu sai kuka yake while wasu guys guda biyu na rarrashinshi, da wannan ya taba shoulder dinshi sai ya tureshi da wancan ya taba shi sai ya tureshi
“Wai haba meye haka?.. Sai kace ba namiji ba?..” Inji daya daga cikin samarin,
“Pls ku kyaleni Inyi kukan…ko na fi samun sauki azuciyata…eight years muna tare da khairat amma rana tsaya za’a rabani daita Don an gan ban da kudi…” Saurayin ya fada cikin matsanacin kuka,
“Ai sai ka dauki hakuri…komai sai in Allah ya kaddara…kilan ba itace matarka ba…” Dayan saurayin, idanuwa Mai kukan ya daga ya watsawa Wanda yayi magana harara tare dacewa
“Haka ma zaka ce?…tou Yanzu bani kudin néman aure in Kai in ba’a bani ba?.. Kawai talauci na yasa na rasa khairat…” Yafada still crying,
“Pls safwan kayi hakuri…komai sai in Allah ya yarda ake yinshi…kar ka tada hankalinka…” Inji Dayan,
“Pls ku  rabu Dani…kawai ku tafi ku barni…you guys won’t understand how am feeling…mutuwa ta fi mun komai a Yanzu…” Safwan ya fada cikin kuka,
“Nikam nasan yanda nakeji…ba two months ago akayiwa aliya aure ba?.. Kowa yasan Ina kaunar Aliya amma haka na hakura tunda bani da Abunda zan bata in na aureta…ni saida ya kaiga in yan gidan sun ganni sai suce sun rabu da matsiyaci….kawai muyi hakuri..in Allah ya kawo aiki zamu samu wayanda zasu auremu…”  Inji daya daga cikin su Mai suna usman,
“Yau she zamu samu aiki?… Whole three years da gama degree babu aiki…in mutum baiyi karatu ba ace Don bai da ilimi gashi munyi hustling munyi karatu amma no body is willing to help us and give us a job…Yanzu sai Mai long leg ke samun aiki…” Habib ya fada cikin tsananin bacin rai,
“Ai naka is better…tunda uncle Dinka yana da Hali…” Habib ya fadawa safwan da har lokacin bai bar kuka ba,
“Kodai muje wurinshi mu rokeshi ko zai taimaka ya Baka kudin da za’a Kai gidansu khairat?..” Usman yafadawa safwan, sufwan daga red eyes dinshi yayi yace
“Kawu musan da ko zamu mutu da yunwa bai taimaka mana?.. Shi zai fadawa ya bani kudin néman aure?… Gaskiya ban iya Kai Kaina in sha zagi da yamman nan…” Sufwan yafada cikn bacin rai,
“Amma wannan uncle din naku baiyi ba…haba Dan Allah…bai da tausayi ko kadan…” Inji habib,
“Ai ni ba tun yau ba nasan bai da mutunci..remember lokacin da ya ganmu mun dawo daga school shi kuma ya dauko yaran shi amma yaki rage mana hanya..hmmmallah dai ya kyauta…kilan yana tunanin mu muka darawa kanmu talauci…” Usman ya fada, shi dai sufwan bai Kara cewa komai ba saboda abinda ya dame shi da ban, kawai he’s missing the love of his life, kawai Yanzu yana tunanin saboda bai da kudi ya rasa komai, he loose his two  sisters because basu da kudin da  zasu  biya hospital bills dinsu. Ajiyan zuciya ya saki yana lumshe idanuwa while best friends dinshi suna magana kan habit din uncle dinshi, ahankali ya daga Kai ya kalle friends dinshi yace
“Wai yasuhe wannan wahalal zata Kare?… Yasuhe muma zamuyi arziki kaman sauran mutane?… Yaushe zamu samu daraja a idon mutane…” Duk ya jero masu wannan questions din, ahankali Habib yace
“Mu dai kam ya zaayi muyi arziki?… Wa zai taimaka mana?… Masu kudi kansu kawai suka sani…kalli makocinmu ko zakka bai fiddawa…last Ramadan da akwai days da bamu samun wani abun kirki  muyi buden baki amma su dadinsu suke ji…Kai duniya..Wallahi am tired…” Usman yafada kaman zaiyi kuka,
“I wish Ina cikin masu kudi…da na taimakawa talakawa…dana saka mutane da dama farin ciki…amma sai gashi Allah bai yoni Mai arziki ba…” Inji habib,
“Ni nayi wata tunani…me zai Hana muje wurin makocinku mu fada mashi ya bamu kudi muyi sanaa in yaso sai mu biyashi with gain…” Sufwan ya fada cikin sanyinmurya,
“Anya wannan Mutumin zai yarda?… Da wahala…” Usman ya amsa mashi
“Kawai mu gwada mu gani…” Habib yayi adding, sufwan da har lokacin idanuwanshi is still wet ya goge tare da mikewa ya gada bombom din wandon shi fitowa sukayi saga wannan lumgun da suke,unguwar ba unguwar masu kudi bane, irin area din nan né wayanda in kana da machine sai kabi  ahankali zaka iya tukata ka shiga gidanka, koina hayaniyar yara né da matasa, duk inda suka ratsa sai an kirasu, suna zuwa wurin wata yarin dake saida awara habib ya duka ya dauki daya
“Wallahi yaya hamsin kenan…” Mai awarar ta fada mashi,
“In ban biyaba ki kulleni…” Habib ya amsa mata yana dariya, duk matasan babu Wanda ya wuce shekara ashirin da takwas zuwa da tara, kowannensu na sanye da yadi Wanda bai wuce 500 per yard ba, Kayan jikinshi is not expensive but they look neat,
“Allah yasa yau an ajiyemin abinci.” Sufwan ya fada yana tafiya,
“Ni rabon da a ajiye min abinci a gida har na mance….kullum fadar mama na ki samun aikin yi..Tana ganin kaman da akwai aikin nakiyi…h,mm” habib yafada,
“Ai Nima haka Inna take fadan banason aiki..wai nafison in dau wanka in dinga yawo agari…” Usman Yafada yana dariya,
“Allah dai ya kawo mana iyakan wannan wahalal…” Sufwan ya fada hannunshi biyu cikin aljihu, ahankali suka dinga tafiya har suka Isa wata makeken gida dake bakin titi, duk fadin unguwar babu gidan daya Kai wannan girma da kyau, babu Mai cewa a bayan wannan gidan da akwai gidan talakawa da yawa because the house is all over the place, Nikam I wonder wane Mai kudi né ya Gina wannan katon gida a wannan unguwar, kawai shi yana da access din shiga gidnshi da mota saboda a bakin titi gidan yake amma duk wayanda suke baya basu da hanyar kirki, babu komai sai gutters da sauro da hayaniyar mutane, bakin gate din sukayi knocking after like two minutes maigida ya bude, kallon su yayi from head to toe Sannan yace
“Ya dai…” Ya tambayeshi kaman bai taba ganin su ba dukda he knows them,
“Wurin alhaji mukazo…” Usman   ya fada mashi, kallon banza maigida ya watsa mashi yace
“Ka dai San alhaji bayason hayaniyar ku…” Bai karasa ba sufwan yace
“Malam ba hayaniya mukazo yi ba…kawai munzo ganinshi né..” Maigida juyawa yayi gareshi yace
“To Mara kunya bai nan…” Ya fada mashi,
“Haba Dan Allah ka taimaka kayi mashi magana mana..nasan yana ciki..” Usman Yafada mashi cikin girmamawa,
“Ikon Allah…wai meye haka?.. Na fada maku bai nan..ku tafi dan Allah …”Inji angry maigida.  Usman zai bude baki yayi magana habib yace
“Mu tafi mana…wai dole né?..” Ya fada sounding pissed off,  ahankali usman ya rike shoulder dinshi Wanda hakan ya danyi calming nerves dinshi, tsoki Mai gado yaja ya rufe gate din.
“I suggest mu koma gefe daya mu jirashi, dole zai fito sallah magrub…lokacin ya kusa…” Sufwan ya fada masu, babu musu suka koma gefe daya suka zauna suna kallon titi then suna hira, bayan kaman minti arbain aka Kira sallah, nan bakin titi sukayi alwallah duk idanuwansu kan gate din alhaji Ibrahim, suna gamawa alhaji Ibrahim ya fito da wasu elderly people guda hudu,
“Wannan maigadin bai da mutunci Wallahi…” Inji habib, yana wucewa ta inda suke suma suka bi bayanshi suka isa same masjid sukayi sallah, bayan an idar alhaji ya fito da friends suma su sufwan suka yi saurin bin bayan shi, sallama usman yayi mashi ya juyo ya kalleshi tare da amsa sallaman mashi, da sauri usman yace
“Alhaji tun dazun muna bakin gate Dinka muna jira ka…Mai gadinka yacebaka nan…” Alhaji tsayawa yayi ya kalleshi Sannan yace
“Tou ya akayi…” Ya tambayeshi Kai tsaye, mutane dake tare dashi tsayawa sukayi suka zuba masu idanu suna kallon su, usman rasa abinda zaice yayi, sufwan yayi saurin cewa
“Alhaji so muke ka taimaka mana…” Bai karasa ba alhaji Ibrahim ya daga mashi hannu su kuma manyan mutane dake tare dashi suka saki dariya
“Wai meyasa Baku da tunani?… Wai an fada maku Ina growing kudi né?…kowa ya kwaso tsiyarsa wajena yayo… Dan Allah ni ku bar tambayata taimako…Nima ta Allah na dogara…bani da bushiyar kudi…ko roki Allah shima ya baku…daga yau ki bar damuna…” Alhaji Ibrahim ya fada cikn bacin rai, da sauri  habib yace
“Alhaji ba kyauta mukeso ba…kawai munason ka taimaka mana da wani Abu…mu fara Sanaa sai mu biyaka da riba…” Dariyar da mutanen keyi yasa habib yin shuru
“Just listen to what this boy is saying…” Alhaji Ibrahim ya fadawa friends dinshi dake dariya har da rike ciki,
“Wai kaman ni zasu damfara…”Inji alhaji Ibrahim
“Wallahi sir ba danfararka zamuyi ba…kawai dai …” Sufwan Bai karasa ba wani daga cikin mutanen dake tare da alhaji Ibrahim yace
“Ku kam kuje wajen government…Sannan kullum Ana fada maku kuyi karatu rashin ji bai barin ku…gashi Yanzu tun Baku Kai koina ba kun fara maula…” Habib dake girgiza Kai saboda yanda yake ji cikin ranshi yace
“Alhaji munyi  karatu…we have good result…” Bai karasa ba wani daga cikin su ya ce
“Then good and look for a job…ku bar maula…bai kamace ku…” Mutumin ya fadayana kallon su from head to toe saboda basuyi mashi Kama da wayanda suka da ilimi ba,
“Wallahi alhaji kullum muna néman aiki..samu none bamuyi ba…” Sufwan yafada cikin sanyinmurya,
“then take your problems to the government…ku bar damuna…kullum unguwar na kun maida ni kaman cbn…kowa yazo ya tatsa…” Alhaji Ibrahim ya fada yana juyawa, manyan mutanen suma juyawa sukayi daya daga cikinsu yace
“Ni Wallahi am still wondering yanda akayi bazaka rabu da wannan local area ba…kwata kwata bai dace da Kai ba…” Wani abokinshi ya fada mashi,
“Hmmm Ai wannan wajen wuri né na iyaye da kakanni…Sannan wayan nan mutanen da kake gani they’re are like securities…nothing bad can happens…so I know why am staying here…” Alhaji Ibrahim ya amsa mashi,
“Lallai kam…amma dai kana kokari…” Wani ya fada mashi
“Ba kadan ba…kullum cikin bara suke, iyayen su suyi…matansu suyi Sannan matasansu suyi…duk Kaina ni kadai…” Alhaji Ibrahim ya fada sounding so fed up, daya daga cikin su Mai suna alhaji yunusa da tunda su sufwan suke yi magana bai bude baki ba yace
“To you should try and help mana…ai mu da Allah ya bamu ba wai Don mun fisu bane…he has a purpose for our lives…” Yafada calmly,
“Ai ba wai ban basu ba…kawai suna son in basu duk abinda na mallaka which is not possible…at times Ina siyan buhun shinkafa in Kai nan baya a raba masu…ai Ina iya kokari na…I can’t do more than am doing…” Yafada mashi atakaice, gate aka bude masu suka shiga. Har suka shige sufwan, habib da usman suna nan tsaye duk sun rasa abinda ke masu dadi,
“Ni Wallahi da na sani da kudin da na yi karatu dasu ajiye su nayi na nemi Sanaa dashi…gashi munyi karatun babu aiki…” Habib ya fada sounding so angry,
“Kawai we should be hoping…Allah will surely make way…” Usman ya fada, shi kam sufwan baice komai ba saboda tensions sunyi mashi yawa.  Kan wata dakali suka koma suna hirar how to get out of this absolute poverty, duk mate dinsu dayazo wucewa sai yace
“Yan uku ya kuke…” Daman sunan da ake kirasu dashi kenan…basu hada komai ba amma amincinsu is too much, komai tare sukeyi, they’re birds of the same feather so they flock together, babu Mai taba daya daga cikinsu ya zauna lafiya, kowannensu is cute and handsome but yanayin rayuwa yasa ba’a ganewa suna da kyau, babu Mai jiki cikinsu they’re all slim and tall, they understand each other sosai to the extent da wuya suyi fushi da juna, gasu da kishin junansu, they share each other’s pain and joy, suna rikewa junansu amana, basu boyewa junansu komai, duk faman hustling da sukayi na néman kudin school tare sukayi, duk semester da daya bai samu kudi ba sauran zasu taimaka suyi buga buga su taimaka mashi ya biya kudin school, at times suna tunanin ko matan da zasu aura bazasu sosu kaman ya da suke kaunar junansu ba, dukkan su unguwar su daya sai dai gidan su usman is closer to the road shiyasa suke kiran alhaji Ibrahim neighbor dinsu because he’s closer to him, dukkan su haifaffun garin Kano né, the attended buk and passed out with a flying colors amma basu da aikin yi, duk yanda zasuyi sunyi but no jobs, sun rubuta application wurare daban daban amma ko interview ba’a taba kiransu ba balle su sa ran aiki, yan kudin da suka samu wajen nysc suka hada suka bude shop a unguwar su amma bayan shekara daya yayi liquidating saboda expenses din families atakaice dai dukda ba aiki suke ba their families depends on them tunda iyayen su basu da wani aiki na azo a gani, hamma habib yayi sufwan daya yayi rafka tagumi ya juyo ya kalleshi tare dacewa
“Ya dai…”
“Wallahi bahbah yunwa nakeji…har na mance rabona da abinci…” Habib yayi fada yana Kare bakinshi,
“Ka dai mance…dazun ba mun ci shinkafa a gidan mu ba?..” Usman yafada, dariya habib yayi yana cewa
“Da wannan shinkafa da babu ai duk daya né…ko mi kadai zan cinye bai isheniba …” Dariya sauran sukayi sufwan wace
“Mujira Muyi sallah ishai muje gida kilan mun samu Abunda zamuci…” Ya fada looking at habib,
“Allah yasa…nidai am so hungry Wallahi…” Yafada yana dafa flat tummy dinshi,
“Kullum Baka da aiki sai kukan yunwa…even when muna cikin damuwa…mtwss..” Inji usman, dariya habib ya kasayi yana cewa
“Ai abinci dole né…man most eat…” Yafada sounding carefree, shidai sufwan har lokacin babu abinda yake tunani sai khairat, Yanzu he can’t believe khairat will be the total property of another man bayan duk plan da sukayi na aure, she loves him and he loves her amma Yanzu yana ji yana gani zai rasa ta
“Kai duniya….” Yafada yana girgiza Kai,
“Pls a bar wannan maganar mana…” Usman ya fada mashi, juyowa sufwan yayi ya watsa mashi harara yana cewa
“Pls ku rabu Dani…” Yafada yana mikewa, barinsu yayi nan wajen su kuma suka Mike suka bi bayanshi, bakin masjid sufwan yaje ya zauna yana sauraron Ana kiran sallah ishai, baki suka kuskura suka shiga cikin masjid. Bayan sun idar da sallah suka fita duk gidansu sufwan suka nufa, wata karamar gida suka tsaya sufwan ya dauko keys daga cikin aljihu ya bude makullin dake bakin wata Kofar sake waje su usman da habib suka shiga ciki shi kuma ya koma hanyar Dayan kofar ya shiga yana sallama, gani duhun dake yar zauren yayi yawa yasa ya Fiddo waya daga cikin aljihunshi ya kunna touch light din wayar,  compound din bai da girma sai dakuna biyu né cikin gidan, sai bathroom da wata local kitchen, sallama ya sakeyi yana cewa
“Inna..” Ya fada yana ya ye kabulen dakin, wata middle aged woman nagani Tana sallah, bai Kara cewa komai ba ya saki curtains din ya nufi yar kitchen din, pot ya bude yaga miyan kuka sai kuma wata kwano dake dauke da tuwo, wata kwano ya dauko Sannan ya dauki tuwon, yana daf da zuba wa Inna ta fito rike da chasbaha,
“Inna inawuni?…” Ya gaisheta
“Lafiya….” Ta amsa mashi atakaice Tana kallonabinda yakeyi
“Me kakeyi?..” Ta tambayeshi Kai tsaye,
“Inna tuwo nake diba..” Yafada tare dacigaba da zuba tuwon
“Anya kana da hankali kuwa?… Yanzu wannan uban tuwon zaka dauka kannenka suyi kalaci da me?..” Ta tambayeshi,
“Ai Inna ba ni kadai zanci ba..tare nake dasu usman…” Bai karasa ba Inna tace
“Lallai ma…ku Wallahi Baku da kunya…manya irin ku Baku Jin kunyar ku shiga kitchen ku debi abinci alhalin ba ko sisi kuke kawowa ba…” Bata karasa ba sufwan ya fara turo baki kaman zaiyi kuka ya kwantar da murya yace
“Inna Dan Allah kiyi ahankali karsuji..kinga Nima inaci gidansu…kuma kinsan in Ina dashi ban boye maki…” Yafada kaman Mai rada kar abokanshi su ji saboda yasan duk wata magana Mai karfi yana kunnensu,
,”Kaci ubanka…dallah ka rage wannan Abincin…sauran kannenka dake nemo kudin zasuyi kalaci dashi…” Ta fada mashi atakaice, ahankali ya rage tuwon ya sake cewa
“Rage…ci kawai kuka iya sai kuma gantali cikin unguwa…sa anninku suna chan da iyalensu…” Tafada afusace, ahankali ya sake ragewa, tuwon da ya rage sauran Dan kadan Inna ya zuba mashi Miya dan kadan kuma tayi tsaye Don kar ta bar wajen ya Kara, ahankali ya fita da kwanon abincin su usman da suka gaji da zama cikn duhu    kalleshi, ajiyewa yayi nan wajen ya kallesu yace
“Bisimillah…” Yafada masu atakaice yana komawa kan kwallabati ya zauna,
“Kai fa…” Usman ya tambayeshi yana gyara zama,
“Ni abinda ya dameni daban.. Bata abinci nake ba…” Yafada yana tagumi,
“Ta khairat kake kenan..bari yunwa ta hanaka bacci …” Habib ya fada mashi yana Kai hannu cikin kwanon tuwon, sufwan dai bai fada masu komai ba Illah ya kurawa waje daya Ido yana tunanin what a horrible world is this,. Within three minutes habib da usman suka cinye Abincin wata budurwa tazo shigewa gidan habib ya kalleta yace
“Asiya ki kawo mana ruwa…”
“Tou ” Ta amsa mashi ta shige few minutes later ta kawo masu ruwa. Yau dai sufwan bai rakasu zuwa inda suke hira har goman dare ba, he feels so bad, bai San yanda rayuwa zata kasance mashi ba, he’s become one fed up,
“Wai ahaka zamu kare?..” Yafada cikn sanyinmurya
“At 29 bamu da komai na kanmu?..” Ya fada yana juyawa kan yar katifar dayake Kai,
“Ya Allah ka iyakance mana wannan wahalal…” Yafada kaman zaiyi kuka, yana juye2 ya dingayi har lokacin sallah asuba yayi, mikewa yayi ya shiga cikin gida ya Kama ruwa yayi alwallah yayi sallah, yana dawowa ya dauki jarkoki yaje near by borehole ya bugo ruwa jarka 6  kaman yanda ya Saba duk safiya kafin gari ya waye,  daki shi ya koma ya kwanta sai lokacin bacci yayi gaba dashi. Karfe goma ya farka ya shiga cikin gida yayi wanka, fitowa yayi ya shiga dakin Inna yace
“Dan Allah Inna zan samu wani Abu na kalaci?..”ya tambayeta cikin sanyinmurya, kallon shi tayi from head to toe Sannan tace
“Baka da ko sisi amma kana kwance kana bacci har Karfe goma kaman wani shugaban kasa…ya zaayi ka samu aiki?.. Lokacin da masu néman aiki suna chan suna nema Kai kana nan nannade cikin bargo…to jeka bani da wani abun kalaci…” Tafada mashi cikn bacin rai, kura mata Ido yayi for a moment hawaye na taruwa idonshi,
“Inna kaman Yanzu ganina yana bata maki rai….kiyi hakuri…Wallahi babu yanda naiya né…wata rana sai labari…” Yafada cikin sanyinmurya, tsoki Inna taja tace
“Wata rana sai labari..kilan in na mutu zaka  samu labarin…nidai ka fice min da gani…mata da yawa suna alfahari da yaransu na farko..amma Banda Kai…”
“haba inna…ya kikeso Inyi da Kaina né?… Kina ganin a son Raina nake yawo cikin unguwa?..farin cikina né Ina yawo cikin gidan nan?.. Wallahi Inna bani da farin cikin daya wuce in faranta maku…kullum gurina in samu in Baku amma Allah baisa hakan ya faruba…nidai Inna kawai adua nake bukata daga gareki…Dan Allah kar ki karamin sama da abinda nakeji…pls Inna…” Yafada hawaye na taruwa idonshi, tsokin takaici Inna taja ta juya ta  shiga dakinta Tana cewa
“Allah yasa ba kashin  tsiyar ubanka ka dauko ba…” Tafada kaman she’s not talking to her own son, ahankali sufwan ya fita daga gida ya shiga dakinshi dake Kofar gida ya zauna, kawai sai ya fara hawaye,
“In wacce ta haifeni ta tsananeni because of my poverty Ai kowa ma zai tsaneni…” Yafada cikin hawaye, bude Kofar akayi habib ya shigo, da sauri safwan ya goge face dinshi, zama habib yayi gefenshi yace
“You and Inna?..” Ya tambayeshi Kai tsaye saboda sun San yanda Inna takeyi mashi, suma nasu iyayen suna masu haka but na Inna is worst, kullum fadanta sufwan ya kawo kudi kaman zaiyi sata,
“Wai saboda wannan kake kuka kaman you’re not a man?… Ai inda sabo ka saba…pls stop crying..ka shirya muje néman abunyi…ko Dan garuwane muje wata unguwar muyi…” Habib ya fada mashi, ahankali sufwan ya kalleshi yace
“Dan garuwa fa Kace?….” Sufwan ya fada cikn sanyinmurya,
“To do we have a choice?… Ya zamuyi?.. Yau gidan mu babu komai kuma ni mama taje jira…Yanzu dai dole yau mu nemi wani Abu da zamuyi tunda shagon dinki babu kasuwa…” Habib ya fada mashi,
“Ni ko tafiya ban iyayi sosai…rabona da abinci tun shinkafa da mukaci gidansu usman…”
“Yanzu dai ka shirya muje gidan shinkafa da wake ka siya kaci mu fita”
“Wallahi sisi bani dashi…” Sufwan ya fada mashi
“Muje Ina da Dari…ka saya kaci sai mu tafi…”
“Ina usman…” Sufwan ya tambayi habib,
“Nasan yana daf da shigowa…Yanzu na ganshi yace babanshi ya aikeshi layin jankai…amma daga chan zai zo nan…” Habib ya fada yana kwantawa kan katifar, ahankali sufwan ya Mike ya dauko Vaseline ya shafa Sannan yadauko wata neat blue yard ya saka, takalmin shi ya goge da old labulen bakin kofa ya saka, fita sukayi tare da habib sai suka hango usman karshen layin ya taho,  jawo kofar sufwan yayi ya kulle, usman na zuwa suka gaisa Sannan suka nufi gidan shinkafa da wake, habib ya sayawa sufwan na 70 yaci Sannan suka bar wajen,
“Nifa Allah na gani bazai yu Insha inuwar ceiling in dawo Ina saida garuwa ba…kawai mu nemi wani abunyi…” Usman ya fada not in support of abinda habib yace,
“Me zamu nema Yanzu?… Ai munyi kokarin nema amma hakan baiyuba…kawai muyi garuwa in da rabon mu hole a gaba mun hole…” Habib ya fada, shidai sufwan baice komai ba,
“Gaskiya aa…kawai I suggest mu cikin gari muna bin shaguna ko suna butatan maaika…kilan muci saa…” Shuru habib yayi ya kalli sufwan dake tafiya kaman Ana ingiza shi yace
“Wai Kai won’t you say anything?..” Habib ya fada cikin bacin rai, ajiyan zuciya sufwan yayi yace
“Hmmm me Zance…kawai let’s Allah’s will be done…” Yafada cikn sanyinmurya,  tafiya sukayi har cikin gari which takes them about one hour,  wani katon shigo suka shiga sukayi tsaye suna kallon masu shopping, wajen Wanda ke zaune counter sukaje, habib yace
“Dan Allah Ana samun aiki?..” Ya tambayeshi, Mutumin kallon su yayi from head to toe Sannan yace
“Aa ba vacancy…” Aka amsa masu atakaice.

Cikin wani gida wata yarinya ce zaune gaban wani maguji Tana wanke wanke kwanoni, sai gunguni kawai take alaman she don’t want to wash the plates, wata yarinya ce ta  ta fito da wasu plate kuma yarinya ta juyo afusace ta kalleta Tana cewa
” ke Dan ubanki daukesu ki maida…” Ta dakawa yarinyar tsawa, da sauri yarinyar ta juya kaman zatayi kuka tace
“Mommy..tace batayi” naji yar yarinyar ta fadawa mahaifiyar su, wata fara matar Mai kyau ce ta fito daga daki tace
“Maza ki maida mata…” Ta umarci wannan yar yarinyar, juyowa yarinyar tayi ta taho da plates din, irin kallon da Mai wanke wanke take mata yasa tayi saurin ajiyesu ta bar wajen da alaman she’s so afraid of her, Mai wanke wanken sake juyowa tayi looking so furious, yarinyar na ajiyewa ta Mike Tana cewa
“wai ni baiwace a gidan nan?… Duk aiki ni kadai keyi..Sannan abun takaici inayi kuna turomin wasu kaman jakka…” Tafada kaman zata tashi sama,
“Lallai ma nana…wato Yanzu kin girma ban isa in saki aiki ba…” Matar ta fada, baki yarinyar ta turo Tana cewa
“Na gaji Ai…aiki kullum kaman jakka?… ” Bata karasa ba matar ta nufota
“Maza ki farayi kafin ranki ya mugun bace…” Da sauri yarinyar ta dawo kujera wanke wanken ta tacigaba dayi Tana cewa
“Wallahi ko za’a kasheni a campus zan zauna..ban zaman gidan nan…” Tafada kasan makoshinta.

Share…2💚💜💛❤️💙
Sirrin wasu gayun
💚💜❤️💙💛

® zuwairat (ummumaryam)

 

2️⃣

Free page

“Me kika ce…” Matar ta tambayeta sounding angry, baki nana ta turo tace
“Ba komai ” Tafada Tana magana kasa,
“Nana zagina kike kou?..” Matar tafada cikin tsananin bacin rai Tana takawa zuwa inda yarinyar take, da sauri ta sake mikewa Tana cewa
“Wallahi mommy ba zaginki nake ba…” Tafada Tana cikin kuka,
“Ke dai kika sani….duk abinda kikayi za’a yi maki…ba dai rashin respect ba…komai baki sonyi…Wallahi ni dake né gidan nan…sai nayi ubanki…” Matar ta fada Tana nunata da yatsa, nana sai ja take da baya saboda kar ta doketa,
“Now be fast ki gama Wannan wanke wanken ki shiga kitchen ki hada mana abinci…yi sauri…” Matar ta fada Sannan ta juya ta koma ciki yar yarinya dake biye daita tayi saurin shigewa itama, nana wanke plates ta cigaba dayi sai magana kawai take. Wannan nana kenan, she’s the kind of girl that thinks gidan iyaye is a burden, she thinks gidan iyaye is like a prison da Baka da daman yin abinda kakeso, bata da gurin  daya wuce ta ganta as her own boss, ko kadan bata son damuwa ko ta kura, batason zaman gidansu saboda yanda mommy dinta ke sata aiki, hakan yasa bayan tayi weac ta nemi admission a buk Sannan now she’s ready to stay in campus just because she want to be on her own,she’s the third born of the family dad dinta is not a rich man but he takes care of the family, dad dinta irin mutanen nan né da basu da kudi but their families lacks nothing, he’s a noble man with one wife and 4 children, two boys  sai two girls, boys din sune manya  then nana, sai bayan 12 years da haihuwar nana suka haifi last born dinsu. Cikin bacin rai ta gama wanke plates din Wanda inda saka duba da kyau da akwai dirty jiki saboda yanda take wanke su cikin bacin rai, basket din ta dauko face dinta sam babu walwala ta Kai plates dun kitchen ta jerasu a rank, babu abinda kake ji sai karar plates da nana ke yanda ta gan dama dasu, fitowa tayi daga kitchen din dake cikin compound dinsu dake dauke da dakuna hudu, room and palour guda daya sai single guda biyu, the house is neat and beautiful in its own way, yarinyar na kurawa Ido naga she’s pretty beyond words, she has this dark expensive color Sannan Tana da manyan idanuwa da  kuma  sexy lips, her chest is full of boobs kaman ba yarinya ba, bata da tsawo sosai amma she’s ok, sanye take da skirt da Riga na atampa, style din is so tight that I can see her curve, she’s so perfect. Bayanta nabi da kallo
“Masha Allah …” Kawai na fada, bayan ta gama jera plates ta fito daga kitchen face dinta kaman bata taba dariya ba, room and falo ta nufa ta ya ye labulen Kai tsaye Sannan tace
“Me za’a dafa?..” Tafada cikin bacin rai, mommy juyowa tayi ta watsa mata kallon banza matar ta watsa mata tace
“Ki dafa jelof..in sani yazo zaiyo cefane sai kiyi Miya…” Nana bata tsaya sauraron last statement dinta ba ta juya fuuu tayi kitchen Tana cewa
“Mata sai tayi zaune Tana sani aiki kaman wata baiwa…ba dai zan dawwama a nan ba…” Tafada Tana shiga kitchen, match ta dauko ta kunna ta sa wuta a stove, locker ta bude ta dauko pot ta wulla kan wuta ta zuba ruwa ta fito, yar small phone dinta né yayi ringing tayi saurin fita, picking tayi Tana cewa
“Babe ya kike?..” Ta fada Kai tsaye,
“Albishirinki…” Naji an fada mata
“Goro…” Tafada cikin bacin rai,
“Wai yane nakeji kaman you’re angry…” Aka tambayeta daga Dayan bangaren,
“Wannan matar ce mana…” Nana ta amsa mata,
“Wace mata kenan?..” Aka ta tambayeta
“Hmmm Maryam kenan…wa in ba mommy ba…” Ta amsa mata cikin bacin rai, dariya Maryam tayi tace
“Lallai ma…nidai babu ruwana…daman inason fada maki admission ya fito…” Tsallae nana Aisha ta daka tare dacewa
“Way yo Allah na dadi…am so excited…Kai nagode sosai…at least mutum zai bar wannan gidan Mai cike da abun haushi…Sannan zamu dinga ganin gayu”  tafada sounding so excited, dariya kawarta tayi tace
“You’re so funny…wane irin gayu kuma?..”
“Kema kinsani ai…hot guys with flashy cars…babe Wallahi Ina kaunar rayuwar big girls…” Tafada cikin matsanacin farin ciki kaman she’s not the angry girl da take Abu kaman mahaukaciya ba,
“Ke gayun né matsalar ki?.. Kedai mu Sami time Don muje mu duba ko min samu…shine most important part…”
“Hmm nidai kawai in gani cikin school as a big girl…mingling with big boys…ko ba komai zakayi class…Ni Wallahi I love gayu…” Ta fada kaman zata zauce
“Anya ke karatu zakiyi?… ”
“Eh mana…Kawai I can’t wait to be free né…” Haka dai sukayi hira Sannan ta fita daga single room dake dakinta ta shiga falon mom dinta, da sauri tace
“Mommy an fiddo admission…” Tafada cikin farin ciki, kallon ta mommy tayi for a moment Sannan tace
“Sai akayi me?..” Ta tambayeta Kai tsaye,
“Mommy Dan Allah in na gama abinci zanje gidansu Maryam muje mu dubo…” Tafada mata,
“Tou…” Kawai mommy ta amsa mata, da sauri koma bakin aikinta, she don’t look sad at all again, she’s so happy Don she’s feeling she’s finally getting away from home.

Har karfe biyu su sufwan basu samu mutum daya da ya ce zai basu aiki ba, bakin wata masjid suka zauna, kettle dake cike da ruwa habib ya dauka ya juye ruwan bisa Kanshi, he’s feeling so hurt and tired, ba komai yake tunawa ba sai yanda babu komai da mom dinshi da kuka siblings dinshi zasuci, shi kuma sufwan tagumi yayi yana fatan inama mutuwa tayi gaba dashi, shi kuma usman ya kurawa waje daya Ido bai ko kiftawa,
“Rayuwa…” Habib ya furta hawaye na taruwa idonshi,
“Yanzu duk fadin Kano babu Wanda zai  taimaka mana da aiki?… Babu Wanda zaice ga Dubu daya?… Babu Wanda zaice kuzo in taimaka maku?..” Habib ya fada yana kokarin maida hawayen dake néman zubo mashi,
“Sai Yanzu nagane why people do bad things….shiyasa na gane abinda yasa ake kidnapping…ake sata ake kashe innocent people…” Sufwan ya fada kanshi kasa,
“Wallahi in da Ina da bindiga I will rob this afternoon…” Habib ya fada yana girgiza Kai,
“Hmmm Allah bazai sa muyi hakan ba…” Usman ya amsa ma sufwan,
“Inna lillahi wa’ina ilaihi rajiun….” Habib yafada yana dafa kanshi,
“Wallahi am dizzy….nagaji…” Sufwan ya fada,
“Ni Yanzu me mama da sauran yaran zasuci?.. Nasan ba komai gidan ..nothing at all…” Habib ya fada cikin tsananin tashin hankali
“Yanzu wasu suna chan cikin ac…cikin hutu…abinci kala kala na gidansu…suci duk abinda sukeso..suje duk inda sukeso…suyi duk abinda suke so…me suka fimu?.. Why is it that mu uku namu wahala yafi na kowa?. ..kodai we’re curse?..” Sufwan yafada voice dinshi na rawa, wasu flashy cars né suka wuce kan titi duk suka kalla sai usman yace
“Banzaye Mara tausayi…” Yafadawa motocin dake wucewa kaman they’re the cause of their problems. Zama sukayi wajen bayan sunyi sallah zuhr, dukkan su babu abinda suje ji sai yunwa, da kishin ruwa, ga rana ga gajiya, baya sun Dan huta kaman minti ashirin suka mike, takawa sukayi har bakin zoo road suka nufi wajen wasu yan adaidaita, gaisawa sukayi usman yace
“Dan Allah muna néman taimako né…” Juyowa sukayi daya daga cikinsu yace
“Tou…muna sauraron ku…” Kallon juna sukayi Sannan habib yace
“Dan Allah ya akayi kuke samun adaidaita?… Muma munason muyi aikin..” Habib ya fada ma Wanda ya maida hankali kansu,
“Tou nidai wani né an unguwar mu yake badawa…zai Baka Sannan kullum zai zaka dinga Kai balance har ka gama biya ya zama naka..amma gaskiya bai bawa Wanda bai sani ba…” Saurayin ya amsa mashi, shuru sukayi  for a moment Sannan sufwan yace
“Dan Allah bazaka Kai mu wajen shi ba kilan muma ya siya mana?..Wallahi muna bukatar hanyar samun kudi..Dan Allah…” Sufwan ya rokeshi, matashin kura mashi Ido yayi sai yaji tausayi shi ya kamashi, kallon sauran su yayi yaga yanda duk kode sai sunsha rana sai zufa suke,
“Gaskiya Allah na gani inason kaiku amma da wuya ya amince..,matasan  unguwar su kawai yake bawa…bai bawa matasan wasu area,..” Saurayin ya fada masu,
“Dan Allah ka kaimu..kilan Allah yasa ya taimaka mana..Wallahi muna cikin hali…Dan Allah ka taimaka mana…” Habib ya fada mashi, Dan murmushi saurayin ya saki yace
“Nasan ba zai yarda ba..yana da doka sosai…Dan Allah kuyi hakuri ku fadawa manyan unguwar ku Shima ya siya maku…ku ji…”Saurayin ya fada masu,
“Ai mu bamu da manyan da zasu taimaka mana a unguwar mu…duk munyi kokarin samun Mai taimaka mana bamu samu ba…ka ganmu duk yau basu ci komai ba mun fito néman aiki amma abun kaman an hada baki kanmu…Dan Allah ko ba wannan Dan unguwar ku ba in ka San wani ka kaimu wajenshi ya taimaka mana da abinyi…Dan Allah…” Habib ya fada yana hadiye wani Abu, shuru Saurayin yayi yana kallon shi har sai da ya gama yace
“Wallahi abun né sai hakuri…zaman matashi babu abinyi balai né amma government din mu basu damu ba…amma yanda zamuyi muje in kaiku wajen shi kilan Allah ya Dora ku kanshi…Wallahi duk adaidaita da zaku gani da wannan alaman…” Yafada yana nuna bayan nashi, su sufwan kallon tambarin sukayi Sannan Saurayin yacigaba dacewa
“Wallahi nashine…duk yawancin matasan unguwar mu indai Baka da abinyi zai taimaka maka da wannan amma ba kyauta ba…zakayi aiki Kana Kai mashi balance har sai ka biyashi da Dan rabar da ya Dora maka…” Saurayin yayi mashi bayani
“Mudai Allah yasa ya bamu…” Sufwan ya fada cikin sanyinmurya, ameen sauran suka amsa mashi, Saurayin gama goge adaidaitar yayi su sufwan suka shiga yayi hanyar area dinsu. Har suka is a babu Mai cewa komai saboda kowannensu da tunanin da yake, usman yana tunanin Yanzu as a degree holders zasuyi driving adaidaita, Kai kawai ya girgiza without saying a word, shi kuma habib yana tunanin halin da gidansu ke ciki Yanzu saboda bai da uba babu Mai taimaka masu, Yanzu yasan siblings dinshi suna chan suna bin neighbors saboda su samu abinci, several times suna shiga neighborhood Don yi masu aike saboda a dafa abinci a yan masu,  bashi da bakin cikin da ya wuce hakan, because wasu lokutan korar su ake in Abincin ya kusa dahuwa. Shi kam sufwan babu abinda yake sai aduar Allah yasa a basu adaidaitar, he don’t mind ko daya né a bawa su uku su dinga shifting saboda babu abinda yakeso kaman ya farantawa inna, he’s dad is late too and mom dinshi is a strong woman, Tana sanaar saida haja cikin gida amma daga baya jallinta ya kare, Yanzu kannenshi suna saida yan waina a Kofar gida da yamma, ahaka suka isa gidan da bai da wani girma sosai,
“Ko alhaji Ibrahim bai Kai kudi ba amma yana taimakawa matasansu,,..shi kam wannan shegen sai gori…” Habib ya fada cikin ranshi, fita sukayi suka bi bayan wannan Saurayin zuwa inda wasu mutane ke zaune a gindin Wata bushiya, cikin respect suka gaida mutanen Sannan Saurayin yayiwa wani mutum bayanin abinda ke tafe dashi,
“Yaran waye?.. ” Mutumin da akayiwa bayani ya tambayi Wanda yayi mashi bayani,
“Nima ban San su ba…” Kallon banza Mutumin ya watsawa Saurayin Sannan yace
“Gaskiya Ismail Baka da hankali… Ya zaayi ka kawomin samarin  da bansani ba?… Ka taba ganin anyi haka?… Ko kana tunanin kudin banza gareni…” Mutumin ya fada cikin bacin rai Sannan ya juya ga su sufwan da suka sadda Kai kasa yace
“Kuyi hakuri..ni ban bawa Wanda ban sani ba keke…bawai kudi gareni da yawa ba kawai Ina bakin cikin in ga  matasa suna gararamba a gari…Don nasan hakan yana jawo balai da tashin hankali daban daban…kaman yanda turawa sukace an idol mind is the devils workshop…shiyasa nake Dan. Taimaka masu da keke…” Sufwan da idanuwanshi suka Chanza yace
“Alhaji..muma in har Baka taimaka mana ba bamu San irin halin da zamu shiga ba…Wallahi alhaji ko abinda zamu bawa iyayen mu bamu dashi, ..kullum cikin yawon néman aiki muke..tun muna néman aikin office har mun hakura da certificate din mu mun dawo néman na abinci…Dan Allah ka taimaka mana…” Sufwan yafada kaman zaiyi kuka, daya daga cikin mutane dake zaune a majalissar yace
“Wane irin certificate gareku?..” Ya tambayeshi,
“Degree…” Habib ya amsa mashi
“Inna lillahi wa’ina ilaihi rajiun…” Mutumin ya fada sannan ya cigaba dacewa
“Kasar nan ta lalace da yawa…wai Ashe ta matasa majiyan karfi da son aiki amma su nema su rasa?… Yanzu Dan Allah ku fadamin meye amfanin karatun?.. Wannan government basuyi wa matasanmu adalci at all…Yanzu komai sai ka San mutum…in Baka San mutum ba sai ka mutu a wahale…wannan rashin aikin yi yayiwa…kullum matasan mu sai yawo suke a gari…” Mutumin ya fada cikin bacin rai, shuru kowa yayi yana sauraron su,
“Ai gaskiya abun ba’a magana…wayanda suke son taimakawa basu da halin taimakawa…wayanda suke da halin taimakawa kuma basu taimakawa..sun danne kan kudi billions while wasu suna néman Dari biyu na abinci..Kai Allah yaisa…” Wani ya fada, sufwan daga Kai yayi ya kalli masu maganar yaga ko kilan sun samu taimako daga garesu sai yaga they don’t look rich at all, irin normal civil servants né wayanda suke jiran albshinsu Wanda bai taka Kara ya karya ba,
“Ai ni takaici na daya né…misali Ina da gidaje goma…Ina iya zama cikin biyu lokaci guda?…” Wani ya fada sai wani ya amsa mashi dacewa
“Aa…” Mutumin yacigaba dacewa
“Tou in Ina da Kaya da yawa Ina iya saka biyu lokaci guda?..” Ya sake tambayan su
“Ai ka zama mahaukaci kenan…” Wani ya sake amsa mashi,
“Tou kun gani amma masu kudin nan Don handama kaga mutum da gidaje har kasar waje amma basu taimakawa marasa shi yayi…su dai kawai kansu da zuriar su suka sani…Kai Allah kar ka bamu halin rashin tausayi…Wallahi abun kaman ba’a mutuwa…” Mutumin ya fada sounding so bitter, haka suka dinga tofa albarkacin bakinsu sudai shuru sukayi suna sauraron su, Wanda ke bada adaidaita ya kallesu yace
“Tou daman ni ba kowanne lokaci nake badawa ba…Ina kaiwa wata uku ban saya ba Don kudin da suke kawowa nake tarawa sai in hada da kudin pension na in sayo sabo..saboda haka dukda ban San ku ba kuyi hakuri zuwa nan da wata uku…in Allah ya yarda zan sayawa daya daga cikin ku…” Kai suka sadda kasa Jin ya ambaci wata uku, ganin yanayin su yasa yace
“Kuyi hakuri…Nima ban da yanda zanyi…”
“Ba komai…zamu je gaba nema…Don Yanzu in muka zauna haka yunwa zaiyi ajalinmu da yan uwanmu…in Allah ya amince nan da wata ukun zamu dawo…” Habib ya fada kaman zaiyi kuka, ahankali suka Mike, wani dake zaune nan wajen ya saka hannu cikin aljihunshi ya zaro dubu daya tare dacewa
“Ga wannan kuyi managing…” Da sauri suka durkusa suka amsa tare da godiya, shima Wanda suka je wajeshi Shima ya zaro dubu daya ya basu, ahaka duk Wanda ke wajen suka dinga basu waje wani Dari biyar wani dubu, kasa godiya sukayi saboda mamaki, kawai sai sufwan ya fashe da kukan farin ciki Don sai da suka samu kusan dubu ashirin wajen wannan mutanen, godiya suka dingayi inda Mutumin ya sake tabbatar masu zai saya masu keke nan da wata uku Sannan wani yace
“Kuyi hakuri..wata rana sai labari..kawai ku sani in har Allah ya sa kukayi arziki ku tuna da wannan yanayin da kuke ciki..Don mutane da dama suna cikin Hali, ..”Mutumin ya basu shawara, godiya sukayiwa Mai adaidaitar daya kawo su nan majalissar kuma har dashi cikin masu hada masu kudi. Gefe daya suka koma inda babu Mai ganinsu habib yayi counting kudin suka ga dubu ashirin da dari biyar
“Alhamdulillah,…I will never forget this day…” Sufwan ya fada sounding so excited,
“Yanzu dai ni ku bani dubu biyar da Dari biyar sai ku biyu ku raba sauran..” Usman ya fada masu, kallon mamaki sukayi mashi
“Why?..” Habib ya tambayeshi,
“Ai ku Baku da Mai taimakawa..ni kuma ubana yana da rai…kunga ko kaka nafiku…”  Yafada masu calmly, da sauri suka rungumeshi a tare, dariya kawai suke kaman basu bane that look so dull few minutes back ba,  5500 habib ya bawa usman su kuma suka raba 7500 each, daga nan suka shiga wata shago sukayi siyayyar Kayan abinci da su spaghetti da sauransu, sufwan da habib 4K suka kashe each wajen Kayan abinci, wurin wasu masu saida garau garau sukaje sukaci abinci Sannan suka nufi gida, suna shiga cikin unguwar su kowanne ya kama hanyar gidansu rike da abubuwan da suka sayo amma shi usman bai sayi komai ba. Sallama sufwan yayi yana shiga cikin gidansu, Inna dake zaune cikin compound ko daga Kai batayi ba balle ta kalleshi, ahankali ya wuto  ya ajiye Kayan daya sayo, sai lokacin Inna ta daga Kai Tana kallon Kayan,
“Inna gashi..wasu mutane suka taimaka mana…” Yafada har jikinshi na rawa saboda farin ciki, kallon banza Inna ta watsa mashi Sannan tace
“Wannan shi yasa kake rawar jiki kaman Wanda ya sayo buhun shinkafa?..mtwss…” Tafada Tana mikewa,
“Kiyi hakuri…” Yafada yana saka hannu cikin aljihunshi, 1500 ya Fiddo cikn sauran kudin yace
“Inna gasu…kin dinga cefane har Allah ya Karo wasu…” Kwcewa tayi daga hannunshi Sannan tace
“Kaman wasa Yanzu ka fara bara…” Tafada cike da takaici, wata budurwa ce ta fito daki ta kalli sufwan tace
“Lah yaya Kai ka kawo wannan?..” Tafada sounding so excited, ahankali ya daga mata Kai
“Allah sarki yaya..Ina ka samu kudi?..” Ta tambayeshi cike da so da kauna,
“Wasu mutane suka tara mana…” Idanuwa yarinyar da bazata wuce 18 ba ta lumshe before saying
“Amma mun gode…daman duk yunwa mukeji..Bari in Dora…” Murmushi ya saki yana kallon sister dinshi dake Kama dashi kaman yan biyu saidai age difference
“Tou shikenan…” Sufwan ya fada yana barin gidan.

Shi kam habib yana zuwa gida sai da ya kusa fashewa da kuka saboda yanda mahaifiyar shi ke kwance kan taburma a yar karamar compound dinsu, idanuwanta lumshe kaman Mai bacci amma she’s not sleeping, she’s just hungry, Tana Jin sallaman shi tayi saurin bude Ido tare da mikewa zaune, duk ilahirin jikinta sai kyarma take saboda yunwa, idanuwanta duk sun koma ciki, ahankali ya ajiye Kayan hannunshi nana cewa
“Murja…” Ya Kira sister dinshi, da sauri ya fito, kallon mahaifiyar shi yayi yace
“Mama baki Jin dadi né?..” Ya tambayeta eyes dinshi na Chanza launi saboda bakinciki da tausayinta,
“Yunwa…” Tafada Tana nuna stomach dinta, da sauri ya mikewa sister dinshi Dari biyu yace
“Yi sauri ki sawo biredi…” Ya umarceta, da sauri ta amshi kudin  ta dauko hijab ta fita, mom dinshi jingina tayi da bango Tana sauke ajiyan zuciya kaman Mai asthma, hannunta ya Kama yana shafawa ahankali
“Mama Insha Allah sai kinci gajiyata ko ta halin kaka…sai na sa ki cikn makeken gida da masu aiki..” Yafada hawaye na taruwa idanuwanshi,
“Ameen…” Kawai Ta amsa without opening her eyes, suna haka sister dinshi ta shigo da bread din, da sauri ta amsa ta bude ta fara ci, kallon murja yayi yace
“Ina sauran..” Ya tambayeta
“Suna makota…” Bai Kara cewa komai ba ya sa hannu cikin aljihunshi ya dauki Dari biyar yace
“Maza kiyo cefane Sannan ki sayo itace kizo ki dafa abinci…” Ya umarceta, babu musu ta amsa ta bar gidan. Sai da taci bread din ya debo mata ruwa cikin randa Tasha sanna ta saki ajiyan zuciya tace
“Allah yayi maka albarka…nagode..” Tafada cikin sanyinmurya, murmushi ya saki before saying
“Mama kalli..” Ya fada yana nuna mata Kayan Abincin daya shigo dashi, juyawa tayi ta kalli Kayan ta zaro idanuwa
“Ina ka samesu?..” Ta tambayeshi sounding so excited, nan Yafada mata yanda akayi
“Allah ya saka masu da alkhairi..Allah ya biyasu…”Tafada cikin farin ciki, this is the difference between mahaifiyar sufwan da na habib, she appreciates duk abinda danta yayi, kullum cikin yaba mashi take,  shi kam usman ya tarda abinci gida, sai da yaci ya koshi Sannan ya dauki 2k cikin kudin ya bawa mom dinshi, adua ta dinga jera mashi saboda farin ciki.

Nana kam tana  gama girki ko ci batayi ba ta shiga bathroom tayi wanka ta fito ta shirya ciki. Lace Riga da skirt, brown vail tayi rolling dashi ta dauki bag dinta irin na yanmata ta fito zuwa dakin mom dinta,
“Zan tafi…” Ta fadawa mom dai ta, pause dake kusa daita ta bude ta dauko Dari biyar ta mika mata Sannan tace
“Sauran ki dinga gantali a titi…nasan halinki da son yawon banza…” Ta fada mata,
“Mommy gidansu Maryam kawai zanje sai mu wuce school…”
“Na dai fada maki…” Ta amsa mata atakaice Sannan ta fita jikinta na rawa, takawa tayi Tana sauri zuwa bakin titi, sai kallon flashy cars dake wucewa take Tana imagining inama wani daga cikinsu ya tsaya yace zai bata lift da dagudu zata shiga, she loves class and  riches, wata shiny car yaso wucewa ta kurawa motar Ido tayi har yazo wucewa ta inda take taga wani young guy da wata babe zaune a gaba
“Inama ni…” Tafada Tana biting lips dinta, ganin in ta tsaya kallon cars she won’t go yasa ta tsaida adaidaita ta hau zuwa gidan su Maryam daga nan suka wuce buk, luckily ita da Maryam sun samu admission, tsalle ta dingayi Tana ihu not minding mutane dake kallon ta,
“Wai meye haka Dan Allah?.. Kar ki Bari mutane suyi tunanin am together with a mad person mana…” Maryam ta fada mata amma nana bata bar tsalle ba sai cewa take
“Wallahi su kalleni it’s their business…you won’t understand what am feeling..kawai I can’t wait to get out of that house….” Tafada sounding carefree,
“Ke kam you’re funny…you can’t wait to get out of that house kaman ba gidan ubanki ba?.. Kaman dafa ki ake Ana ci?.. Haba nana ki bar wannan maganar mana kar wasu sujiki…” Maryam ta fada mata calmly,
“Ai inda dafa ni ake Ana ci da yafi min..kullum a wahale nake kaman wata baiwa…Wallahi ko kadan bani da Hutu gidan nan…from this to that haka nake rotating cikin gidan kaman Mara galihu…” Tafada hankalinta kwance,
“Hmmm ke kam Ai iyayen mun Don su bamu tarbiya Mai kyau suke hakan..bawai Don basu kaunar mu ba…ba ki ganin yanda wasu yanmata basu iya zaman aure saboda basu iya komai ba?.. Ai in uwa ta koya maka komai to ta tsirar dakai daga cin fuska nan gaba…ki tuna in dai da rai da lafiya aure zamuyi fa..” Ta fada mata Tana Dora hannu kan shoulder dinta,
“Ke dai baki ganewa Wallahi…inda na nufa daban inda kika dosa daban…kawai nidai I want be free ko da na months né…in zauna babu takura babu command…because kaman yanda kika ce aure zamuyi so Yanzu in ban Dan shana ba babu ranar shanawa saboda bakasan Wanda zaka aura ba…daga takurar iyaye zuwa miji…no freedom kenan fa…” Nana Aisha tafadawa Maryam
“Wai to in tambayeki wane irin shanawa zakiyi…hope it’s not what am thinking…badai runs girl kike son komawa ba…” Bata karasa ba nana ta balla mata harara tare dacewa
“Ke kika San abinda hakan ke nufi…nidai kawai I want freedom…that’s all I don’t want to go from fry pan to fire…” Tafada Tana juyawa
“Allah ya huci zuciyar ki…kawai you should know what ever our parents do is for our own good…” Maryam ta fada Tana biye daita,
“Kanki akeji…” Tafada Tana tafiya da sauri sai sai wining waist dinta take in the name of walking, itama bayan ta tabi trying to keep up with her.

Leave a Comment