*🅱RILLIANT WRITER’S ASSO…*
_(Pen of freedom home of exceptional and magnificent writer’s)_
*🌺TSAKA MAI WUYA*🌺
@ASM££NT Z££YAN
आिजमषपपपक९८३रुरर
الحمد لله وبه نستعين،وصلي الله علي سيد نا محمد و علي اله و صحبه وسلم تسليما.
_*Kamar kullum xance na d’ayane banyishi dancin zarafi ga kowaba se dan kyautata Alaqa” kana banyarda Ajuya min littafi ta kowace sigaba kasancewarsa haqqin mallakata ne! Idan Baku manta ba munyi littafai kamar haka:-*_
*KUKANA*
*BADAQALA*
*NAMIJI*
*KUYANGAR QUNCI*
*BAKIN GANGA*
*NAMIJI HANTSINE*
*BR.SHA’AWA*
*BAQAR RANA*
*BANKAD’A*
*HUKUNCI*
*D/S*
~Dahaka nake cewa masu karatu kubiyoni sannu Ahankali danjin ~yayaxata~ ~kasance~ A *TSAKA MAI WUYA~*
بسم الله الر حمن الر حيم،
01
Yarone matashi d’an kimanin shekaru Ashirin da ukku Aduniya” yana sanye cikin qananan kaya farare tasssss! riqe da littafai Ahannayensa, tafiya yake cikin yanayin nutsuwa da ginanniyar tarbiya” hankalinsa kwance xahiri bashida wata damuwa” wani gida me qaramin qarfi da rashin yalwar Arxiki yashiga da cewa “salamu Alaikum” amma shiru bawanda ya amsa hakan yasanyashi fad’awa gidan batare da naxarin komaiba” wata dattijuwa ce xaune tsakiyar gidan me kimanin shekaru hamsin da Aihuwa” tana rungome da bahausar shinkafa me jahhh da tsakuwa ta sadda kai qasa batare da tsintar shinkafar da tarunguma ba” cakkkk yajah yatsaya yana naxarinta’ daga bisani yarankwafo cikin yanayin damuwa yace innah!
Firgigit tad’ago tare da yin yaqe tace Muhammad kadawo? Shima yaqen yayi yace Eh nadawo tund’axu! murmushi tayi tace sannu da hanya yakaratun? Uhmu segodiyar Allah innah” shiru yad’an ratsasu nadaqiqu yakatse dacewa Inna haryanxu baki d’ora Abunciba yamma nayi ko bakida lafiya ne!?
Idonta kamar xaikawo qwallah tace lafiyana qalau muhammad’ babu gawayin da xand’ora inajiran qanwarkane tun d’axu nace taje tasamo ledoji naga ko xaidafa mana shinkafarnan tunsafe rabon mu da Abunci” da Alamar damuwa yace haba innah nace kidaina aikenta A unguwar nan tsintar ledoji kidinga bari nasamo ita macce ne bekamata anasakata kowane aiki ba” da yanayin damuwar itama tace Muhammad dolece tasanyani nikaina ba Asan raina bane” littafan sa ya’ajiye be furta komaiba yafita” yanafita yaga qanwarsa tadawo cike da kulawa tace yah muh’d sannu daxuwa! Murmushin sa yafad’ad’a kana yace sannu qanwata yana qoqarin karb’ar buhun da tayotsince tsince dashi!
Bayan yakarb’a sukashiga yana tambayarta me akayi masu A class? Seda ta yatsina fuska tace komai! Xare ido yayi yace komai shin? Tace eh wani malami ne Kawai yashiga yamuna tatsuniya” qwafa yayi da ido aransa yace yaushe nigeria zataci gaba!? ko yaushene talaka zaihuta Aqasar nan? duba da ilmin ma ankasa bashi! Inkaga yaro da ilmi me kyau bincika waye ubanshi? Haqiqa bazakasamu talaka bane” jin shirun Muhammad yayiyawa tace yah meyasa kayi shiru!? Yaqe yayi yace Rayyanah Karatun talaka kebani tausayi yau sati ukku kina zuwa makaranta babu karatun kirki ahaka har qarshen zango yaqare baku gane komai ba” narasa gano bakin zaren shin kodan bayaransu Amakarantun gwamnatine sukayi shiru ilmin maras galihu nazama tarihi!? Kokuma sun manta A kyauta sukasamu ilmi lokacin su sir Ahamd bello” su tafawa b’alewa” su yakubu gawan” se yaji hawaye sun wanke mai fuska…..
Hannuta takai A hankali tashare hawayen tace yah muh’d kayi shiru kadaina zubda hawayenka kullum sekayi kuka innace ba’akaratu makaranta kuma kana koyamun inayi.…rungumota jikinsa yayi yace Rayyana ke in ina koyamaki wasufa?! Dayawa kuke amakaranta Rayyanah! kuma Annabi muh’d yana cewa d’ayanku bazaiyi imaniba harsai yasoma d’an u’wansa abunda yakeso wakanshii..” Shiru yaratsasu duka biyun can mamansu taleqo taga halin da suke ciki A sanyaye tace kuyi haquri muh’d ita duniya haka take wannan Abun da kake gani zezama tarihi duk Wanda kukeji Ana cema wani sedayasan duniya” kuma zaku samu ilmi dukkk dacewa kunxo babin qaddara mai wuyar sha’ani” haka dai sukayi zaune suna jajinta lamarin can innah tace muh’d maganar hajiya rabi kojiya tazoooo.
Iskar bakinsa yahuro yace innah kiyi haquri banason kuyi aikinan zuciyata bazata juri kuna maula gidan waniba, se naga kamar Wasiyar Abbana nake tozartawa bayan qasa tashafe idonsa” kamar tayi kuka tace Muhammad babu wanda yake kauce qaddararsa’ kuma aikin zaifi mana kocikin mu muke cikawa yafi muna Azumin da babu lada….
Gwaron numfashi yasauke yace shikenan innah Allah yasanya kufara cikin nasara yayimun Arxikin samun aikin da zanriqe ku””””Amin tafad’a tare da sanya mashi Albarka.…..
Bayan kwana biyu innah da Rayyanah suka shirya cikin wata shatattar atamfa da qiris takejira ta yage, suka kama hanya sosai suke tafiya ba niyar shiga keke npape har suka kai wata unguwa mabera” unguwar shiru’ kamar bakowa kana kowane gida ka duba kasan na mehannu da miyane da haka suka shiga wani katafaren gida na wani sanannen d’an siyasa A Nigeria” yana saman bene yana kallon masu shige da fice nagidan yahango innah da rayyana” zumbur Alhajin yamiqe yana duban Rayyana da son sanin wacece..? Nan take yakira amuntaccen yaronsa jabeer yace idan sunfito yabimashi sawunsu asan A inasuke…? Jabeer kamar yatafi yadai tsaya yace Yallab’ai tsohuwar ko yarinyar” tsaki yajahhhhh me sauti yace mezanyi da tsohuwar yarinyar dai” galala yasaki baki yace yallab’ai batafi 11 ba fa mezakagane'””” dariya yasaki yadaki kafad’arsa yace jabeer…….jabeer
*🅱RILLIANT WRITER’S ASSO…*
_(Pen of freedom home of exceptional and magnificent writer’s)_
*🌺TSAKA MAI WUYA*🌺
@ASM££NT Z££YAN
आिजमषपपपक९८३रुरर
الحمد لله وبه نستعين،وصلي الله علي سيد نا محمد و علي اله و صحبه وسلم تسليما.
بسم الله الر حمن الر حيم،
02
Yace Jabeer…jabeer ai dodo yafison nariqa Zina da yaran da basahaura15yes ba, shikuma yayitabani sa’a akan harkar siyasana kana sunana na fad’ad’a a bakunan mutanen duniya…! Dan haka aikin kad’aya ka bunciko wacece…?
Sosai yaqyal qyala dariya yace kamar kaikaxon dakanka Alhaji! Koyau kakeson kwana da itah xakasamu! Cikin jindad’i yace nasani jabeer d’ina’ yana dariya Yafice” sukuma sunashiga suka gaisar da hajiya rabi,,, cikin girmamawa da Rashin qyamar talaka takarb’esu kana suka rab’e gefee..! Bayan gajeren shiru da yaratsa su hajiya rabi tace innar rayyana muh’d ya amunce da maganarmu kenan”!? Cikin xumud’i tace Eh hajiya! thommm Masha Allah wanke wanke da share sharene naki sune babu meyi..
Sunkuyar dakai tayi qasa tace ngd hajiya Allah yabar xumunci yaqara arxiki da yalwar lafiya…! Amin tace taredamiqewa ta nuna mata gurin aikinta, bayan taga komai sukadawo suka xauna daga bisani suka wuce gida da Xummar gobe xatayo samakko! Dan fara aikinta.
Koda suka isah gidan muh’d na kuka me sautiii cikin raxani sukayo kanshi” inna dai batace komaiba se rayyanah ce taxame daga jikin innar tace cikin murya me rauni da rawar kuka yah muh’d meyasameka? Wayab’ata maka rai Dan Allah…jikinsa yarungumota yace rayyanah bawanda yab’ata mun rai haka kawai nake tirrrr dakasawata gareku!!!
Hannunsa tariqo cikin sigar hankali tace yaya karkace haka mukam baka kasa mana da komaiba Alkhairanka da tarin soyayyarka muka sani bakasawa ba, kukanka shine tashin hankalina dana innarmu, yah muh’d mu maida Al’amarin mu ga Allah watarana halin da muke ciki xaixama labari….takuma kai hannu tashare masa hawaye sukaxauna xaman tunanin Abubuwa dayawa dasuka faru bayan qasa tashafe jigon su Aduniya…!
wayewar gari tun safe muh’d da rayyanah suka tashi suka share gida tass kana yatayata wanke wanke sunayine yadubeta yace rayyana inaburin nayi kud’i sosai sabida kawai kijj dad’i A duniya.. Murmushi tayi tace nikam banaso kayi kud’i sabida Annabi yanacewa daga cikin fitinar Al’ummata Akwai dukiya banaso tashagaltar da qaunarmu” tagumi yayi yana kallonta tabushe mar idoó yaqyal qyala dariya tare dacewa mekikso nayi tommm inbakud’i ba? Sadda kai qasa tayi tana wasa dayatsanata kana tace mutuwane banaso kayi yah muh’d domin kai nakeyiwa kallon Abbana!… Wani Abu yaji yatokare ransa amma yadake yace baxan mutu nabarki ba rayyana namaki Alqawari se naxama bango agareki xanxama tamkar bawa rayyanah idan harxakiyi dariya.
Yatsanta tamiqo tace muqullah Alqawari bamusu yamiqa mata nashi bayan sun qullah tace yah muh’d dukkkk yadda duniya tarikice da qulle qullen makircinta katuna ranar yau domin kuwa Alqawari Abun tambayane gaban Allah S.W!
Idonnnnsa yaji sunkawo qwallah yace Allah kaxama shaida idan ina numfashi ina da sukuni rayyanah baxatayi kukaba…xatayi magana innarsu takatseta da cewa Rayyanah kishirya lokacin tafiya yayi” cikin girmamawa tace thommm innah bawani b’ata lokaci tamiqe shima yamiqe’ suka shirya atare suka fitoooo muh’d harxaifita se yace xega inda xasufara aiki sannan yawuce makaranta! Inna ba musu tace shikenan muje” haka kuwa akayi…tafe suke suna fira cikin qaunayya harsuka isah……
Bakin gidan yatsaya suka shiga ciki sunashiga Alahji na fitowa sashensa harqasa inna da rayyana suka gaidashi ya amsa but hankalinshi nakan sabuwar harqallar shi datahanashi bacci ganin farko da idonsa suka mata'” jin shirun da yad’auke yasa inna Jan rayyana sukatafi…. tana bada baya yawani had’a yawuuuu da kyar kana A fili yace wajibina ne najawoku jiki domin jiran yahuce shike kawo rabon wani….suko bayan sunshiga aiki suka fara kamar yadda aka nunawa innah kana ba kissa tsakaninta da Allah takeyi! Bayan ta kammalah hajiya rabi tafito tayaba sosai da aikin daga bisani tace taxo tagabatar da ita ga megidan!.
Cike da sakin fuska yaamshe su kana yamata fatan nasara da haquri’ har ga Allah tajj dad’i tayi godiya sosai harxasu miqe yace ke Dota yasunanki….
Cikin sigar yarinta tace Rayyanah wani yarrrrrr yaji kana yakoma namiji yace Abbanki yasamaki suna maidad’i kuma mai darajah..murmushi tayi suka fita yana kallon tafiya me cike da nutsuwa………
*🅱RILLIANT WRITER’S ASSO…*
_(Pen of freedom home of exceptional and magnificent writer’s)_
*🌺TSAKA MAI WUYA*🌺
@ASM££NT Z££YAN
आिजमषपपपक९८३रुरर
الحمد لله وبه نستعين،وصلي الله علي سيد نا محمد و علي اله و صحبه وسلم تسليما.
بسم الله الر حمن الر حيم،
03
Yana kallon tafiya me cike da nutsuwa..!har seda ganin sa yadaina hangota sannan yad’auke kansa!!!!
Gefen muh’d ya isa makaranta lafiya, kana cikin sa’a ba’afara lecture ba, xaune yayi can baya yana “bud’a hand out” d’insa batare da shiga sabgar kowa ba, yana haka wani matashin saurayi da bayawuce shekarunsa” yadaki kafad’arsa dacewa shaihi..” Shaihi” murmushin sa yafad’ad’a tare da cewa bro Ahmad! Ya yau”? dubansa yayi sosai yace lafiya qalau but inaga bakasan wainar da aketoyawa ba shaihi…!?
Cikin miqa nutsuwarsa yace mekefaruwa Ahamad..? Zab’en sossa president xa’ayi..tsaki yajah iya leb’e kana yace su yashafa ni bana cikin kowa Allah basu sa’a…barama nawucewata gida dan yau school d’in ba karatu” dariya Ahamad yayi yace shaihi dagaske wucewa xakayi..? D’an bud’e baki yayi yace ah mexanjira bayan naje neman Abunda xankorewa kaina quda” silent smile yasaki yace gaskiya ne amma tun d’axuuuu naga mutuniyar ka nasafa da marwa yakamata ko gaisawa kuyi!!!!
Gwaron numfashi yasaki yace Ahamad rufamun Asiri ni dukkk Abunda nayi lissafi nakeyi kamar yadda nafad’a abaya gaisuwar musulunci xatariqa sadamu maganar so bayanxu ba inada u’wa da qanwa wanda suke buqatar soyayyata” sannan ko bawannan Salmah tafiqarfina takowane siga…! Dubansa Ahamad yayi yace soyayyar u’wa da qanwa daban, soyayyar saurayi da budurwa daban shaihi” magnar fin qarfi kuma Ajiyeta gefe domin So beduba wannan..! Kana Sanin kan kane dukkk kud’in mahaifin salmah besata shiga jerun watsatsun y’anmata ba! Haka dubun jama’a masu kud’i dagata kebinta suna tsumayin samun tamusu magana ko saud’aya amma batabasu dama ba….! Shaihi kayi naxari akan tayin salmah”””Thom Ahamad xanyi sedai inaso kaima kayi naxarin kasancewar kowace qwarya y’ar uwarta take bi”
Ido Ahamad yaxura masa shikuma yadafashi dacewa nabarka lafiya…! Bayan tafeeyarsa kad’an Salmah taxooo tare da rakiyar qawarta Zareena” cikin sakin fuska tace Ahamad yakukayi da shaihina..? Fuska bayabo yace haryanxu bawani cigaba maganarsa tabaya itace sedai kiyi ta Addu’a…murmushi tayi tace ina kanyi kuma watarana xataxo nayi nasara shaihi yakarb’i soyayyata….
Aransa tausayi tabashi A fili yace hakane salmah domin kin mallaki komai da namiji ke buqata..! Uhmmm wani dai Ahamad bcx nasani ban mallaki komaiba tunda yaushekara d’aya nakasa samun Aron rana d’aya da xanyi magana da shaihina” murmushi yayi batare da furta komai ba” xareenah tamkar xuciyarta tafashe Dan baqin ciki! Wai kamar salmah ace tana maular so gurin yaron da bewuce tataka tawuce ba”” salmah naganin xarina but ko Ajikinta….!
Harseda taqare tace muje xareenah! Batace komaiba tayi gaba” Haka sukayi tafiya med’an tsayi ba mecewa komai seda harsuka shiga mota xareena ta kwanta ta yatsina fuska tace gaskiya salmah A jinki bekammala ba! Seda tad’au mintuna biyu xuwa ukku sannan tace me kikace xareenah..!? Cike da jin haushi tace shaihi nace!!!!
Sanyayyar ajiyar xuciya tasaki tace wow!! xareena kamar kinsan shinake fasalawa da kalar rayuwar da xamuyi gaba…! Tsaki tajah me sauti tace salmah Dan Allah kimanta yaronnan ga maxaje nan dayawa nasonki dai daike masu kud’i domin yau kyau namaxa bayawuce naira!!! Numfashi tasauke tace A gurinki xareenah…but duk duniya bawanda nake gani namiji kamar muh’d maganar kud’i duniya Akesamu kuma nan Akebari, xareena bantab’a ji nafi muh’d da komai ba Dan haka inkinaso mucigaba da xama Alkhairan muh’d sukasance Abokan firarki idan kuwa bahaka ba xanbarki har Abada…!!!!!
Shiru xareeena tayi Dan dagaske salmah ta Afka Tarkon son muh’d kana tace shikenan salmah kicigaba da son shaihi..! A yanayin fushi tace basaikince ba Xareena domin mutuwa kad’ai ke iya dakatar dani….! Ta tada mota suka tafi ba maicewa kowa komai harsuka isah gida, Anan ma parking tayi tafito da qarfi! Abbanta naxaune yana karatun jarida yaga shigewarta fuuuuuuuu,,,,!
Murya yad’aga yace jabeerrrrrrrr! Dasauri yace na’am Alhji lafiya”? hankali tashe yace bi sawun salmah kace ina kiranta…! Dasauri yashiga yace ma hajiya rabi ina salmah..!?
Cikin Rashin fahimta tace tana makaranta jabeer lafiya…?
*🅱RILLIANT WRITER’S ASSO…*
_(Pen of freedom home of exceptional and magnificent writer’s)_
*🌺TSAKA MAI WUYA*🌺
@ASM££NT Z££YAN
आिजमषपपपक९८३रुरर
الحمد لله وبه نستعين،وصلي الله علي سيد نا محمد و علي اله و صحبه وسلم تسليما.
بسم الله الر حمن الر حيم،
04
Cikin Rashin fahimta tace tana makaranta jabeer lafiya..?! Lafiya qalau hajiya Alhajine yace yaga shigowarta raxane! Cikin rashin sukuni tace Raxane..? Eh hajiya! Cikin yanayin mamaki tace ikon Allah Inanan banga shigowarta ba But bara naduba! Thom duba mugani Bawani b’ata lokaci tataka benen da xaisadata da y’arta amma Abun mamaki d’akin wayam! Tana fitowa da xummar bashi Amsa Zareenah tashigo” da wayoyin salam da hand bag d’inta” daga hajiya har jabeer jira suke tafurta wani Abu akan salmah” amma setajah tatsaya shiru yaratsasu…….! Jabeer ne yakatse dacewa xareenah ina salamar!? Dubansa tayi tare dacewa Abunda xantambaya kenan yanxu tashigo ina bayanta…! Numfashi hajiya tasauke kana tace meyafaru kukashigo daban daban!?
D’an saitawa xareena tayi tace cikinta ke murd’awa shiyasa’ murmushi hajiya tayi kana jabeer yace Thom “Alhmdullah yafice” xareena kuma tayi gurin hutawar salmah Dan tasam batawuce can..cikin sa’a kuwa tana xaune dirsha tasunkuyar dakai qasa” xareenah ta marairaice murya tace salmah kiyi haquri bansan maganan xaiyi kauri haka ba! D’agowa tayi tace yawuce xareenah amma dan Allah karkiqara kushe “shaihi” gabana ina sonshi fiye da yadda kike tsammani kitayani Addu’a Allah yabani muh’d!
Rungumeta tayi tace insha Allah salmah namaki Alqawarin Addu’a daganan suka fara fira..gefen muh’d yana isa gida yacire kayanshi yad’auko kayan Rayyana da inna yana wankewa da y’ar omon da yaiqo…! bayan yakammala yad’auki baro da jalka biyu naruwa yadoshi rijjya dan d’aukar Ruwan dayake siyarwa A unguwanni, har magrib tagabato yadawo da cinkin dayayi d’ari da hamsin. naira hamsin yasaka Ah banki, naira d’ari kuma yasiyo gari da quli yaxauna ba’afi mintuna ukku ba Sega Rayyanah da inna washe baki yayi yace sannu innah? Ya aiki..? Lafiya qalau muh’d ta amsa dashi kanaa yamaida kallonsa ga rayyana yaga se haki take Alamar gajiy..matsowa yayi daf da itah yace rayyana ba gaisuwa!? Murmushi tayi seda ilahirin haqoranta suka bayyana tarufe fuskarta tace najira kaqare da innarmu ne!
shima Murmushi yayi yace bakomai kind’ebo gajiya rayyana! Suna haka aka Kira sallah duka miqewa sukayi xuwa ga ubangijinsu bayan sunkammala bacci yad’auke Rayyana! Haka dai lokaci yafara tafiya har 12 biyun dare ganin nepa basukawo wuta ba muh’ d yatada rayyana yace tayi wanka xafi yayiwa’ cikin magagin bacci tamiqe yahad’a mata ruwa tayi wanka yaqara gyara mata shimfid’a ta kwanta yanatofa Mata falaqi da nassss bayan bacci yad’auketa yasanya hannayensa yana dannah tafunan qafafuwanta” Ahankali ta motsa cikin muryar bacci tace yah muh’d kaje ka kwanta kajiiiii! Ngd da kulawarka Allah yasanya mumutu tare!!!
Murmushi yayi yace Amin Amin Rayyanah kuyi haquri dani nikaina takaicin kaina nake da nabarku kuna qangin bauta gidan Wani” xaune tamiqe tana dubansa tace yah muh’d kadaina jin damuwa Dan Allah” kulawarka kad’ai kwanciyar hankaline A garemu!! Shiru yayi yana shafa kanta tausayinta na fisgarshi yamaida kallonsa ga innarsu aransa yace Allah sarki innarmu ubangiji yabani damar kare y’ancinku….! Haka har gwanin iyasata yasacesu suna tsananin tausayin junansu!
Bayan wayewar gari suka shiga shirye shiryen tafiya yauma muh’d seda yamasu rakiya har qofar gidan kana yajuya xuwa makaranfa yana tafe yana tausayin qanwarsa tun A wannan shekarun tanasahan wuyar duniya! Har yaisa Yanashiga sega Salmah da fara’a tace barka shaihi!? D’auke kai yayi yace barka yakike….? Cikin sanyin jiki tace Dan Allah muh’d katsaya kasaurareni..! Cak yatsaya tare dacewa inajinki kiyi sauri….araunane tace shaihi Xanyi tafiya” juyowa yayi yadubeta duban mekikeso idan xaki tafi!? Ta sadda kai qasa tace numberka nakeso!? Banida waya salmah kiyi haquri…d’agowa tayi idooo cike da qwallah tace muh’d turkia xanje nayi degree d’ina Dan Allah kabani kogaisawa mayi…!
Numfashi yasauke yace banida waya salmah ko babu xanbaki..? Kaitagirgixa Alamar A’a! Yace thommm xan iya tafiya!? Muryarta nasarqewa tace Eh shaihi ngd da lokacin da kabani..! Tafiya yayi Tana kallonsa Afili tace muh’d xancigaba da Dakon soyayyarka tsawon lokacin da Allah yaso mukasance Aminan juna..tana juyawa kuma xareena tace muje salmah watarana muh’d xaisoki! Cikin mutuwar jiki tace uhmmm xareena Allah ka amunce min namallaki shaihi kodakuwa shine Ajalina” qwafa tayi batace komaiba se mamakin salmah dake lilo Aqashin xuciyarta……!
Hakadai Rayuwa tasoma tafiya Bayan wattanni shidda inna da rayyana sosai sukejin dad’in Aiki gidan hajiya Rabi” hakama muh’d yabarkomai gurin Allah ita kuwa salmah tana can turkiya xuciyarta na begen shaihi” yau laraba da sanyin safiya innar rayyana takammala shara da wanke wankenta Alhajj yace mata waye wanda yake rakota da safe…?! Cikin jindad’i tace muh’d ne yayan Rayyana! Dafara’a yace haba inaganin hankalinsa wane Aiki yakeyine….!? Duk da begirmeta ba cikin sigar ladabi tace karatu yakeyi Alhaji! Murmushi yayi yace in babu damuwa kice yaxooo yad’an mini wasu Ayukkah kafun yarona jabeer yadawo!!!! Cike dajin dad’i tace babu damuwa Alhaji insha Allah gobe xanxo dashi ngd Allah yaqara sutura…amin yace yanawucewa! Bayan magrib Inna da rayyana cike da farinki suka koma gidah! Muh’d nashigowa Inna talabarta masa Amma seyasha murrrrrrrr!
Itama had’e fuska tayi tace muh’d baka farinciki ne..? Shiru yayi sannan yace A’a inna nibanason walaqanci kuma kinsan masukud’in yanxu gani suke kamar su sukabama kansu babu medarajah A idanuwansu se me kud’i d’anuwansu” Dan haka inaroqonki kisanar mai cewa nagode datayinsa karatun dake gabana ma aikine!!!!
Kallo inna taqare masa kana tace muh’d gobe kashirya fita Aiki gidan Alhaji idan kuma bahakaa ba xansab’a maka! Cikin ladabi yace tuba nake Allah yahuci zuciyar innata kuma xanfita aikin insha Allah yayishiru”
Tausayinsa innataji kana tace muh’d ngd da biyayyarka gareni da dad’i daba dad’i duk kanemun Ina maku fatan nasara dakai da y’aruwarka Allah yaqara shiryaku shirin Addini..! Tare suka amsa da Amin dagabisani inna tafara yaba halayen hajiya rabi da mijinta Alhaji. Bayan wayewar gari suka d’unguma sukaje gidan hajia rabi, muh’d yasha mamaki ganin mekud’i shahararren d’an siyasa da talauci be rab’a ba kana duniya kedamawa dashi baya qyamar talaka” yadda yatarbesu cikin farinciki kad’ai xainuna ma baid’auki duniya da girma ba! Kana cikin mintuna yagabatar ma muh’d kansa dakuma Abunda yake buqata yadinga mai nawani lokaci muh’d fuska fad’ad’e yayi godiya ga Alhaji….! Suka fita waje Inna tayi ciki itada rayyana shiko yatsaya” Alhaji suna fita yasaki shagaltaccen murmushi me ma’anoni dayawa………
*🅱RILLIANT WRITER’S ASSO…*
_(Pen of freedom home of exceptional and magnificent writer’s)_
*🌺TSAKA MAI WUYA*🌺
@ASM££NT Z££YAN
आिजमषपपपक९८३रुरर
الحمد لله وبه نستعين،وصلي الله علي سيد نا محمد و علي اله و صحبه وسلم تسليما.
_For you blood sister ma’u halliru_
05
Shagaltaccen murmushi yasaki me ma’anoni dayawa’ kuma daga Ranar muh’d yafara Aiki cikin jindad’i da walwala” satinsa biyu gidan yashiga rayuwar kowa kasancewar kyawawan d’abiunsa dayanayin nutsuwarsa da kamewa” qauna kuwa da gata bawanda Rayyana tarasa gurin muh’d komai yasamu bayawuce qanwarsa” wanda jama’a da dayawa kejin dama sune!
Wata safiyar lahadi misalin qarfe ukku na yammaci muh’d nagxaune kusa Da Alhaji yanamar tambayoyi A harkar makaranta yanabashi amsa” seyace muh’d xanmaidaku gidannan kaida innarku da qanwarka sabida Akwai wani business center daxanbud’e kuma kana d’aya daga wanda xasukance masukula da gurin…hawaye muh’d yaji sun wankemar fuska” cikin girmamawa yace Alhaji aikin dakabani kad’ai banida kalaman godiya Allah yasakamaka Da Aljannarsa!
Kan muh’d Alhaji yashafa tare dacewa kaina nayiwa karkaji komai domin ita duniya da kake gani Budurwa ce! Yau inada kud’i, mulki, qarshe kuma mutuwa xanyi so muh’d meye amfani mulki da dukiya inban taimaki maraya ba? dame xanyi tutiya gaban Allah inbanyi taimako ba”!? shiru muh’d yayi dagabisani yace Annabi yayi gaskiya dayace harduniya taqare ba’arasa naqwarai Alhaji mungode maganar dawowar mu nan da anbarshi karhidimar tayiyawa….!
Sake dafa muh’d yayi yace kai yarone baxaka gane ina nadosa ba! Kaga kana karatu sannan nace nad’auke ka aiki so fitar isha’ xakayi kadawo shad’aya kaga behana ma karatu ba” kuma behanama aikin gida ba” kana hikimar dawoooo dakunan duniya talalace muh’d kanada qanwa macce da uwa wanda kaine jigonsu wani xaisama fitarka idooo yayi Abunda yagadama so hikimar dawo daku gidana kenan!!!
Shiru yayi aransa yace lallai Abunda babbah yahango yaro ko yahau tsani baxai hangoba…! Afili kuma kalmarnan yafurta da dukkk girman Alkhairi bakii bayawuce furtata! Idanuwansa nasauke qwallah rayuwarsa natunano Abbansu da dukkk kwanan duniya yakemar wasiya dukkk rintsi yaxama mai gaskiya gashi tun ba’aje koina ba yafara ganin “sakamako” dagabisani Alhaji yashige sashensa yabarshi da tunane tunane barkatai Axuciyarsa har lokacin tafiyarsu gida yayi! Tafiya suke kowa yayi shiru Rayyanah tace yah muh’d kayishiru” dubanta yayi cikin sakin fuska yace yau banajin surutu qanwata! Tab’e baki tayi tace ya Akejin surutu yah muh’d..!?
Dagashi har innah dariya sukasa sannan yanayi ciki ciki yace cewa kawai nayi ba’ajinshi dan hakan kawai xaifad’a taqyaleshi” but tasake jefo magana dacewa kuma kace koda wasa qarya haramun ne meyasa kaikayi..!? Sosa qeyarsa yayi yace inmunje gjda xanmaki bayani! Tace meyasa yanxu baxakamun ba!? Dariya yayi yace jarida xaimaki kyau Rayyana sedai naqallafa maraina law xakikaranta” innace tasako Baki dacewa Rayyanatu kam maaikaciyar Assibiti nakeso taxama”! Numfashi yasauke yace inna ko law yanada amfani ga y’amacce ni A tunanina in Akwai mata A harkar sharia xaasamu cigaba fiye da harkar lafiya!..cikin qarfafama d’anta tace meye hujjaraka!? Yace yauwa inna hujjata A harkar lafiya yanxu ansamu mata sosai Wanda suncike gib’in daakecewa y’ayamata su karanci lafiya”
Yakamata yanxu Asama harkar law gaba domin akaratun shima inkayi aiki akan gaskiya xaka ciribar Abunka xanbaki misali yadda wasu mutane kecin xarafin y’ayamata da ma maxa tahanyar miyagun kabairai (xina da luwad’i”) shekaranjiya nagawani case A Court ankawo yaro d’anshekara ukku wani babban mutum yaybita bayanshi Duburar yaron nabada jini sosai” kuma ansani but sabida kud’i lauyan dake jan ragamar yaron se yabari akafishi points tohm ni A tunanina macce da tasan nauyin ciki daxafin Aihuwa baxata bari Ayaudareta dakud’iba! Tace gaskiyakam matar datasan xafin Aihuwa baxatayi wannan taadancin ba” yace yauwa innah shiyasa nake burin ganin Qanwata A matsayi Brr.
Dubansa tayi tace Allah yasanya taxama..Amin yace yana murmushi sukacigaba daxantawar har suka isa gida…suna jajintawa bayan sunkammala yagayama Inna saqon Alhajj” wani farinciki taji yaxiyarceta” Afili tace kai yakagani!? Cixa yatsansa yayi yace na’amunce nace kuma insha Allah sati mexuwa xamu koma! Tace shikenan Allah yasanya shine Alkhairi dama Ina fargabar biyan hayarnan Dan kud’in damukasa A banki baya biya” kuma Bashiru bayayimuna uxurin ko qwandala” murmushi yayi yace innah kibarma tuna lamarinsa komai yayi kansa duniyace”
Hakane ko muh’d je ka kwanta dare yayi kansa yasosa yace thommm bari nayiwa sarkin surutu Addu’a tayi bacci yamata yace seda safe” bayan gari yawaye sukayi gurin aiki kana kwanci tashi Asarar mebegen duniya yau sunkoma gidan Alhaji shikam baki har kunne haqarsa takusa cimma ruwa!!!!..
Haka dai suka soma sabuwar Rayuwa komai wadace harsunfara manata talauci kasancewar rayuwa da manta baya! Lokaci yajah sungama sakankancewa tare da miqa yardarsu ga Alhaji” sirrinsu bawanda sukeshayin gayamasa domin babuko shakka matsayin ubah sukabashi! Yau litanin dasanyin safiya Alhaji yashirya tafiya shida jabeer” Acewarsa xekaiwa tilon y’arsa Xiyara! Muh’d yakaisu harfilin jirgi amma bega tashinsu ba domin Alhaji yamatsamashi akan yaje gida yayi wasu Ayyuka” muh’d na’ajiye mota yayi school acanma besamu dawowaba se 6:pm yatsaya masallacin gidan yayi sallah wanda masu kud’i kenufi da Allah ga naka…!
Dagabisani yashigo yayikwance kanqafafun inna wanda rabonshi damata haka bayatuna Rana..”Inna kansa tadafa tace muh’d bakada lafiya ko..!? Kallonta yayi ido cikin idol yace Eh inna! Dayanayin damuwa tace jikinka babuxafi mekemaka ciwooo!? Seda yayatsina fuska yace gabana ke mugun fad’uwa tunjiya inna kimun Addu’a komenene xaixomin yaxo yadda hankalina xai iyad’auka” murmushi tayi tace komeye Alkhairine yace Allah yasa haka innarmu! Ina y’aruwata!? Dubansa tayi tace wanka take yace thomm Inna komai nakeyi yau ita nake tunawa Allha yasa Alkhairi ne! Amin tace xahiri” aranta kuma roqo take Allah karyaraba xumuntar bayinsa” suna wannan yanayin Rayyana tashigooo tayi face da itah…”Sedai bakamar yadda tasaba ba shigowan ba’ Inna da muh’d duka basuyi magana ba sunsan intaxauna xatafad’i damuwarta intanada”!!! sedai har mintuna goma suka shud’e batace komaiba, muh’d miqewa yayi Ahankali yace y’aruwata meke damunki..!? Dubansa tayi da xara xaran idonta se tayi shiruuuu! Hannunta yajah sukafita yana tambayarta cikin sigar rarrashi dakyar tayi murmushi tace bakomai” aransa yaji wani irri se yabasar kasancewar Rayyana batada xurfin ciki kuma batada qawa se yayanta…..lokaci yafara jahhhhh muh’d yaqitafiya seda inna tatakurashi sannan yatafi yakwanta bacci” solesalin dare yakama mutanen kirki kowa yad’auke sawuuuu Alhaji da jabeer sukayi parking mota tabaya suka shigo tafe suke Ahankali tamkar b’arayi suna matse jikinsu suna bin bangon daxaisadasu da sashen inna……
Daidai wannan lokaci kuma muh’d ya idarda sallah bacci b’arawo yasaceshi” rayyana nackin jikin innarta duk taduqunqune” inna kuma semishari take ba abunda ketashi se sautin fanka gidan yayi duhhhhu sosai sabida sunkashe fitillun lantarki

Leave a Comment