TSANTSAR BUTULCI cmpl by Ameera Adam
*بسم الله الرحمن الرحيم*
😭 *TSANTSAR BUTULCI*😭
2020
*Written By:-*
_Ameera Adam_
_AmeeraAdam60_
*@Wattpad*
☀ *FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*____________________________________*
*SADAUKARWA GA MAHAIFIYATA ALLAH YA KARA NISAN KWANA AMEEN.*
1&2
A sanyaye matashiyar budurwar ta shiga dakin cikin yanayin damuwa, kayan jikinta sunyi wuluk saboda datti duk sun tsufa, kyakykyawar ja idan kayi musu zasu iya yagewa, kafarta kamar wacce ta shekara bata ga ruwa ba, hijabin jikinta kamar ankwato shi daga bakin kura, jingi a tayi da kyauren dakin nasu wanda tuni ya jima da karyewa, cikin karyewar zuciya mahaifiyarta take tambayarta.
” farida yanxun ma ba’a dace ba ko”
Dan jim kadan tayi sannan tace, ” wallahi inna naira biyar ban samo ba, duk gidan dana shiga neman taimako sai dai suce nayi hakuri, ga dai danyar taliya guda daya da naje wucewa ta wani layi na samu ana rabawa nima na tsaya aka bani ” ta karasa maganar tana mikawa mahaifiyarta taliyar.
” to ay shikenan, Allah ya rufa mana asiri, dama malam nake ji kar ya tashi ba abinda zaisa abakinsa, amma hakan ma mun godewa Allah, zauna inje ingani ko zan samo mana abunda zamu dafa ko da mai muci ” mahaifiyar tata ta fada.
Farida zama tayi cen kusa da mahaifin nata, wanda yake kwance kan wata yaloluwar katifa wacce bata da maraba da tabar ma duk ta sid’e, har marmashewa take, tana kade masa kudaje, cikin zuciyarta tana tausaya musu irin ‘kangin rayuwar da suke ciki.
Innar farida na fita rasa inda zataje tayi, saboda duk gidajen da zata je kowanne da kudin bashinsu akanta, gidan sahura ne ya fad’o mata, kai tsaye gidan ta nufa da sallama ta shiga cikin gidan, sahura najin sallamar innar farida tayi kicin-kicin ta tsuke fuska, ciki-ciki ta amsa mata sallamar kamar wacce akayiwa dole.
Gefe innar farida ta samu ta zauna cikin sanyi jiki tana fadin, ” sahura mun wuni lafiya ya yaran ”
” lafiya, yara kuma gasu ” sahura ta fada tana dauke kai gefe.
Innar farida tace, ” Dan Allah sahura dama zuwa nayi ki taimaka dan girman Allah ki bani icce dauri daya wallahi zan hado miki da wadancen kudin ”
Kallan tsaf sahura tayi mata sannan tace, ” haba sadiya yanxu bakiji kunyar zuwa karbar wani iccen ba, karki manta kudin da nake binki sun doshi wata uku fa, kullin sai dai akarawa barno dawaki, gaskiya na gaji wallahi wancen kudin ma naga alamar bazasu fito ba kije na yafe miki amma nida ke ciniki ya daina shiga tsakanin mu ”
Innar farida kamar zatayi kuka ta tsugunna tana rokon sahura, ” dan Allah sahura ki taimaka mun wallahi bani da inda zanje da ya wuce nan, ki taimaka sahura kamar yanda Allah ya taimake ki ” innar farida ta karasa maganar tana zubda kwallah.
Sahura bata ce uffan ba fuuuuu ta tashi taje ta dauko wa innar farida icce kullin hamsin ta shuro mata, tana hada mata da kananan maganganu alamar gunguni.
Godiya innar farida ta shiga jerowa kamar wacce aka bawa kyautar gida, ta dauki itacen ta wuce gida.
Kai tsaye gida ta wuce tana shiga inda tabar farida anan ta koma ta same ta, farida na ganin mahaifiyarta ta taso ta tarbe ta, wuta ta fara korarin hura, ledodi da yayi ya tadinga hadowa harta hura ta dora tukunyar girki.
Mahaifin farida na kwance tari ya tirnike shi, ruwa innar farida ta dauko ta tallafo kanshi tana kokarin budewa ta bashi, da kyar yayi kurba daya ya kuma kwarewa sai bayan wani lokaci sannan tarin ya sake shi, shigowa dakin farida tayi cikin hadin baki suka fara jerawa mahaifinta sannu.
Da ido ya bisu da kallo jikinsa na rawa bakinsa na karkarwa yace, ” sadiya nikam na sare rai da wannan ciwon nawa, sai dai kumun fatan cikawa da imani, Allah ya tallafi rayuwarku ”
” haba malam karka dinga fadar haka, kana sare mana gwiwa malam kasan cuta ba mutuwa bace, anyi yafi haka ma Allah ya baka lafiya ” cewar inna.
” kayya sadiya inaji ajikina wannan ciwon bazai barni ba……… ”
Inna ce ta katse shi, ” a’a malam ka daina fadar haka kana karya karyamun zuciya ”
” Baba insha Allah bazaka mutu ba, inka mutu dawa zaka barmu nida inna? ” farida ta fada tana goge hawayen daya gangaro mata.
Tari malam ya karayi sannan yace, ” farida ko yanzu ba ahannuna kuke ba, kuna hannun Allah dan haka idan ma na mutu zan barmu ahannun Allah ” inji malam.
” Insha Allahu ma zaka samu lafiyarka malam ” cewar inna.
Dan jinjina kai malam yayi yace, ” Allah yasa ”
” Farida dubo tukunyar cen ko ta tafasa, inta tafasa sai ki debi taliyar ki zuba ” inna tace.
Tashi farida tayi ta fice daga dakin.
Malam ne ya dan dago da kai yace, ” sadiya ya akayi kuka samu abin girkawa? ”
” awani gida farida ta karbo mana sadaka ” inna ta fada.
” sadiya ki tsaya tayin daka akan tarbiyyar farida, nasan kina yi iya bakin kokarinki, amma ki kara kinsan duk fadin garin nan bamuda wasu yan uwan bare ince ko wani zai tallafa miki ta hanyar tarbiyantarwa, sadiya na bar miki Amanar farida duniya da lahira kiyi iya bakin kokarinki wajen ganin kin dora ta akan hanya mafi inganci, wasiya ta gaba da zan gaya miki itace, idan yarinyar nan ta samu mijin aure ki sanar da mutanen garin mu dukda nasan zaki samu kalubale daga garesu, amma ki kauda kanki mutumcin farida zaki nemo tunda kinsan mutumcin kowanne yaro dangin ubansa, idan bana raye kinga bazai yuwu ace kin aurar da farida ke kadai ba, watan wata rana dole agoranta mata, nasihata daku ta karshe itace, kuji tsoron Allah ku kyautatawa wanda ya kyautata muku, domin dan halak shi ke nuna halarci, wanda ya cuce ku kubarshi da Allah, Allah zai isar muku Allah ya albarkaci rayuwarku ya duba lamarinku ” malam ne yake yiwa inna wasiyya.
Gaba daya jikin inna yayi sanyi da maganganun malam, hawaye ne ya gama wanke fuskarta cikin sanyin jiki hade da kuka tace, ” malam duk naji abunda ka fad’a kuma insha Allahu zanyi iya bakin kokarina akan tarbiyyarta, malam cuta ba mutuwa bace da ikon Allah zaka samu lafiyarka ”
Farida ce ta shigo dakin ganin yanayin da mahaifiyarta take ciki yasa jikinta yin sanyi, gefe ta samu ta zauna tana karayiwa mahaifinta sannu.
” Farida Allah yayi miki albarka, farida kiji tsoron Allah kiyi biyayya ga mahaifiyarki kiyi koyi da kyawawan dabi’u, ki kare mutumci ki dana mahaifiyarki Allah ya tsare miki imaninki aduk inda kike ” malam ya fada yana lumshe ido.
Amsawa mahaifin nata tayi cikin wani yanayi tana karewa mahaifinta kallo.
Tun lokacin da mahaifinta ya kwanta jinya bai taba doguwar magana irin ta yau ba, tabbas duk wanda ya ga yanayin da malam yake cikin yasan yana jin jiki, mutuwa da rayuwa ta Allah ce amma ba wanda zai bawa malam awa guda ayanayin da yake ciki.
Jugum sukayi bame cewa wani uffan kowa da abinda yake ayyanawa azuciyarsa.
Sauran farau-farau inna ta dauko ta tallafo malam tana bashi, kurba daya yayi ya dauke kai, ta maidashi ta kwantar.
Taliyar da farida ta dafa inna ta zubo musu ko mai babu gishiri kawai suka barbad’a suka ci ta a haka.
Farida ce ta kalli mahaifiyar ta tace, ” inna yanxu haka zamu kyale baba cikin wannan halin, ko zamu maidashi asibiti? ”
” hmmm farida kenan idan munkai shi asibiti dame zamu kaishi, kudin da zamu tafi asibitin ma ina muka ganshi kina gani wancen zaman da mukayi a asibitin sai da na saida komai namu hatta sitira saida na saida mana su, gidan nan bamu da komai banda yan tsummo karan mu sai abunda ba a rasa ba, haka muka dinga bara da kyar muka sa mu kudin magani, kina gani aikin da za’ayi masa na ciki baifi dubu saba’in ba amma sun gagare mu ba inda bamu je neman taimako ba, karshe kina gani likitocin da suka gaji da zamanmu a asibiti sai sallamar mu sukayi, farida bamu da karfi bamu da abunda zamu iya biyan kudin aikin malam dasu, kinsan kuma halin dangin mahaifinki sarai, mu cigaba da yi masa Addua Allah ya bashi lafiya, idan kuma ciwon bana tashi bane Allah ya sa ya cika da imani. ”
Ajiyar xuciya farida ta sauke, sannan tace “Aameen ya rabbi ”
Cikin dare ciwon malam ne ya tsananta jikinsa ya rikice, inna ce akusa dashi tana shafa masa ruwa tana tofa masa addu’a, ganin jikin ya kara tsanani yasa inna tashi ta fita, gidan makocinsu mlm maude take bubbugawa sai bayan wani lokaci aka bude kofar.
Da fitila mlm maude ya haske ta cikin mamaki yake tambayarta, ” sadiya lafiya naganki da tsakar daren nan ”
Cikin shashshekar kuka tace, ” ka taimaka mun dan Allah mu kai mlm asibiti jikinsa ya rikice ”
” subhanallahi muje ingani ” mlm maude ya fada.
Tare suka wuce shida inna, yanda inna ta fito haka suka koma suka sameshi cikin mawuyacin hali.
_Vote_
_Comments_
_Share_
MUM ASLAM Ce😉
[8/23, 10:59 AM] Ummou Aslam😍Bint Adam❤️: *بسم الله الرحمن الرحيم*😭 *TSANTSAR BUTULCI*😭
2020
*Written By:-*
_Ameera Adam_
_AmeeraAdam60_
*@Wattpad*
☀ *FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*____________________________________*
*SADAUKARWA GA MAHAIFIYATA ALLAH YA KARA NISAN KWANA AMEEN.*
3&4
Da hanzari mlm maude ya shiga dakin yana kokarin tallafo mahaifin farida, sam baima san abinda akeyi ba saboda baya cikin hayyacinsa, asanyaye inna tace, ” mlm maude dame za’a kai mlm asibiti ga dare yayi ko gidan mlm harisu zan buga ya taimaka ya kaimu?”
Gyada mata kai mlm maude yayi, ya fara karantowa mahaifin farida kalmar shahada, farida ce ta shiga dakin cikin hawaye ganin halin da mahaifinta yace ciki gefe ta samu ta zauna tana goge hawaye.
” inna ce ta shigo ita da mlm harisu, kamo shi sukayi mlm maude ya rumgumoshi suka shiga dashi adaidaita sahu, farida na tsaye mahaifiyarta ta bata umarnin komawa gida saboda babu gurin da zata zauna.
Kai tsaye asibitin murtala suka wuce da hanzari likitoci suka karbeshi, sai dai kafin su fara ma bashi agajin gaggawa rai yayi halinsa.
Wani likita ne ya fito ya sanar musu, inna hawaye ne ya gangaro mata cikin dakiya da jarumta tace, ” Allah ya jikanka ya gafarta maka malam halinka na gari ya bika, oh rayuwa wai yau mutuwa ta dauke mlm ” sai kuma ta fashe da kuka me tsuma zuciya.
Su mlm maude ne suka dinga rarrashinta suna bata baki ahaka har aka basu gawar suka juyo gida.
Lokacin da suka dawo anfara kiraye-kirayen sallar asuba, jin karar adaidaita ne yasa farida tayi farat ta fita waje sai dai ganin andauko mahaifin nata arufe yasa jikinta yayi sanyi bata gama yarda da abinda take zargi ba saida taga mahaifiyarta na share hawaye, da gudu ta tafi ta fada jikin mahaifiyar tata ta fashe da kuka me tsuma zuciya.
Ruk’o hannunta inna tayi suka karasa cikin gida, kan shinfidarsa ta da aka maida shi ka kwantar dashi, su mlm maude su suka sanarwa mutane da rasuwar, kafin wayewar gari gidan ya fara taruwa da matan mak’ota, wajen karfe goma na safe akayi jana’izar malam aka kaishi gidansa na gaskiya.
Duk wanda yaga halinda su inna suka shiga sai ya tausaya musu, sunyi kuka kamar ransu zai fita fuskarsu duk ta sauya kammani abunka dafarar fata tuni fuskarsu ta kumbura tayi jawur.
Tun bayan rasuwar malam makota su suke ciyar da inna itada farida, abinci har bayar da shi inna sukeyi kafin wannan ya kare zakaji wani yaron yayi sallama ya kawo wani kwanon, ita kanta inna har mamaki take tasan dai duk fadin unguwar babu wanda baisan halin da suke ciki ba, amma babu me daukan koda gero ne ya kawo musu da sunan taimako, sai gashi yanxu abinci har almajiri suke bawa.
_Mafi akasari abinda yake yawan faruwa kenan, acikin unguwa zakuga akwai gidan da ansan mabukata ne suna bukatar taimako amma ko gero babu wanda zai dauka ya kai musu, idan ma rashin lafiya ce mutum zaiyi ta neman taimako amma masu taimakawar kadan ne, sai lokacin da mutum ya mutu sai kaga yan uwa da makota anata tururuwar kawowa iyalansa kayan abinci wasu guraren ma harda danye zaka ga buhu-buhu anashigarwa da iyalan mamancin, Allah ya bamu abinda zamu taimakawa yan uwanmu musulmai dan matsayi da isar Annabi muhammad (S.A.W)_
Ahaka har aka shafe sadakar bakwai abinci daga na safe rana dare baya yanke musu, yau da gobe ahankali komai ya fara ja baya, dan kudin sadakar da ake bawa inna su take tarawa da aka daina basu abinci daga makota dasu suke cefane suna cin abinci, bahaushe yace zaa ra bata barin dami akwana atashi dan kudin hannu inna ya kare, su farida suka fara komawa yar gidan jiya.
Malam yau ya cika kwana arba’in da rasuwa, inna da farida na zaune suna dan hira farida tace, ” inna me zai hana ki fara dafa mun abincin siyarwa ina kaiwa bakin titi kinga sai mu rage wata matsalar, amma zaman haka nake ganin bazai fisheshe mu ba”
” farida kinsan dai tallah ba tsarin mu bane nida mahaifinki, kuma tun yana raye kunsan sarai bai lamunci tallah ba, zandai gwada sarar yan kayan amfanin ko su kuku da daddawa ne nagani ko zamu dace, idan ma abincin ne sai dai mu gwada agida ” cewar inna.
” to inna ko kosai zamu gwada ko kuma wainar gero?” inji farida.
” ehto bari mu fara da kosai koda na gwangwani shida ne sai mu gani ko zamu samu ciniki ” inna ta fada.
Farida dan murmushi tayi tace, ” eh to inna kosan ma yafi Allah yasa mu fara cikin sa’a ”
” Aameen farida”
Wata tsohuwar gingimemiyar radio su da wata bulalliyar tukunyar karfensu inna ta fito dasu, farida ta aika gidan hansatu dilalliya ta kira ta.
Hansatu bata dau lokaci ba ta janyo mayafinta tayi gidansu farida.
Kallan tsaf hanne tayi musu sannan tace, ” sadiya gaba daya kayan nan zan siye su dubu daya da dari biyar idan kin siyar ga kudinki ahannu ”
” haba hansatu dan Allah kidan kara mana, tukunyar nan fa me kwari ce bula daya ce ma ajikinta kuma radio ma wlh ko gun masu gyara kika kaita tsab za’a gyara ta ki siyar da daraja ” cewar inna.
” gaskiya nikam haka zan siya na dauka ma na siya da daraja ” inji hansatu.
Inna tace, ” dan Allah kar muyi haka dake hansatu kudin nake da bukata ”
” to na kara dari biyu akai zan baki dubu daya da dari bakwai gaskiya daga haka ba abinda xan kara ” hansatu ta fada tana kallan inna.
Inna bata da wata mafita hakan ne yasa ta karba, amma tasan ba karamar riba hansatu zata samu akai ba, bayan fitar hansaci cefanan kosai inna ta bawa farida taje ta siyo sauran dan canjin ta sai musu abinda ba’a rasa ba, makota inna ta dinga aykawa ana gaya musu zatayi kosan siyarwa.
Kamar yanda inna ta sanar haka suka wayi gari da kosan siyarwa, cikin ikon Allah tas ya kare murna suke inna tana fadin sun samu sana’ar da zasu rike kansu da ita.
Haka inna ta dinga kosai tana ciniki tun tanayin na gwangwani shida har ta dawo yin na rabin kwano da gwangwani biyu, ahankali kuma sai cini ya dinga ja baya, wata rana ma baifi suyi cinikin dari uku ba, ahaka-ahaka inna ta rage mudu ta dawo yin na gwangwani hudu, ciniki sai kara ja baya yakeyi tun abun baya damun inna har abun ya fara damunta.
Wainar gero suka koma yi itama hakan take, wata shawarar suka sake tayin wainar shinkafa, ba laifi itama da farko anfara cini daga baya kuma ko ta dari biyu ba’a zuwa siya.
Ganin haka ne yasa inna ta watsar tunda wataran idan sukayi sai dai su cinye abarsu, rasa abinyi inna tayi komai ta kama da ta fara sai cinikin yaja baya.
_*WATA UKU DA RASUWAR MALAM*_
Su inna suna zaune farida na yi musu kwad’on kanzo sallama sukaji ina kwalawa, hannu farida ta wanke ta leka kofar gida, Alh Ya’u ta gani tsaye cikin manyan kaya, har kasa ta tsugunna ta gaida dashi, cikin washe baki ya amsa sannan yace, ” yanmata ina maman taki kimun sallama da ita ”
” To ” farida ta bashi amsa.
Inna ce ta fito suka gaisa, sannan yace, ” dama tun watan shekaran jiya nake sauraron ku har yanxu naji shiru, ya ake ciki ne kinsan kudin hayarku wata biyu kenan da karewa, dama na d’aga muku kafa ne saboda rasuwar me gidanki, yanxu inasan ko rabi ne ki bani zuwa watan gaba na dawo na karbi rabin kudin ”
Rass gaban inna ya fadi dama kullin da tunanin hakan take kwana take tashi, tattaro jarumta tayi sannan tace, ” dan Allah Alh kayi mana afuwa wallahi dama kullin kudin nan yana raina amma insha Allahu zanyi kokari inhada maka, dan Allah ka dan kara mun lokaci ”
Karkace kai gefe yayi cikin kufula yace, ” wane lokaci kike san na kara miki, dududu nawa ne kudin hayar dubu arba’in kudin gida ashekara banda ni dinma wane gida zaki samu azamanin nan daki biyu adubu arba’in, abinda nake so dake ki rage mun wani abu ko dubu goma ki mikomun na rage zafi ”
“wallahi Alh dubu daya tawa ta kaina bani da ita, dan Allah kayi hakuri insha Allahu zanyi kokari inhada maka kudinka” inna ce tsugunne gaban Alh ya’u tana rokonsa.
Dan jim kadan Alh ya’u yayi sannan yace, ” shikenan na baki nan da wata guda ki hada mun kudina wallahi idan na dawo bansamu ba aranar ne zaki gane asalin kalata ” yana gama magana bai jira cewarta ba ya juya ya hau kan mashin din vespan sa ya kara gaba.
Tashin hankali wanda ba’a sa masa rana, inna ta kusa minti guda agurin tana jimamin maganganun Alh ya’u, gida ta shiga ta zayyanewa farida duk abinda ya faru.
Farida ce ta kalli mahaifiyarta tace, ” inna yanxu meye abunyi ?”
” farida abunyi yanxu fita zanyi neman aikatau agidan masu kudi ” cewar inna.
Yatsina fuska farida tayi tace, ” aikatau inna ”
” kwarai farida, wannan zaman da nake yi bazai kaini ko ina ba, kina gani kinfi wata guda rabonki da zuwa islamiyya duk saboda ba kudin wata, ita dama boko ba’a magana tunda yanzu sa’anninki sun tafi aji daya ababbar sakandire ( SS1) farida idan na zauna kina ganin zaman zai fishsheni? ” inna ta fada tana kallan farida.
” A’a inna ance ne gidan masu kudin wulakanci garesu musamman ga wanda yake musu aiki” inji farida.
” Farida duk wulakancinsu zan jure indai ba duka da zagina zasuyi ba, komai da kika gani na rayuwa me wucewa ne, wata rana zai zama tarihi ilimi shi ne jigo arayuwa, idan bakiyi ilimi ba sai gaba abin zai miki ciwo, insha Allahu farida zanyi duk wani aiki ba gajiyawa indai zai rufa mana asiri ” cewar inna.
A sanyaye farida tace “To Allah ya taimaka inna”
_Vote_
_Comments_
_Share_
_MUM ASLAM Ce_😉
[8/23, 12:47 PM] Ummou Aslam😍Bint Adam❤️: *بسم الله الرحمن الرحيم*
😭 *TSANTSAR BUTULCI*😭
2020
*Written By:-*
_Ameera Adam_
_AmeeraAdam60_
*@Wattpad*
☀ *FIRST CLASS WRITER’S ASSOCIATION* ☀
FCWA
*{Home of qualities and trusted writer’s of The nation}*
https://www.facebook.com/First-class-writers-Association-111719967001810/?referrer=whatsapp
*____________________________________*
*SADAUKARWA GA MAHAIFIYATA ALLAH YA KARA NISAN KWANA AMEEN.*
5&6
Washe gari duku-duku inna ta tashi ta shirya ta fita neman aiki, kudin motar da zata hau ma bata dasu da kafa ta tafi tun daga unguwa uku har na’ibawa cikin layin masu kudin nan tashiga, duk gidan da taje sai dai suce Mata suna da me aiki, yawo take tayi ba nasara ahaka ta hakura ta dauko hanyar gida, agalabaice ta shigo gida kafafunta furu-furu ga yunwa da k’ishirya sun addabeta, adaki ta samu farida na bacci jin Motsin Inna ne ya tashe ta, barka da dawowa farida tayi mata take tambayarta ko andace, duk abinda ya faru haka Inna ta bawa farida labari, sosai ta tausayawa mahaifiyar Tata, sauran dumamen Daren jiya farida ta zubowa Inna, tuni Inna ta cinye shi badan ya isheta ba, ruwan rijiyar da farida ta debo musu shi Inna ta kamfata take ta mammak’a, Sai da Tasha me isarta ta sauke kofin ta ajiye.
Sallar Azahar da la’asar ta gabatar tana tunanin abinda zasu ci da daddare, tunawa Inna tayi da wata ajiyayyiyar ramarta da ta taba siya, Ramar ta dauko suka Fara gyarawa itada farida, haka suka kwadanta Ramar Dan dole ita suka ci suka kwanta bacci.
Inna tun daga ranar haka ta dinga zarya neman aiki Amma yanda take fita haka take dawowa ba sa’a, wata ranar lahadi itace ranar da Inna ta fita na karshe domin taci alwashin muddin ta fita Bata samu ba to daga ranar ta daina fita, sai dai ta gwada wani abun ko zata dace.
Awannan Rana ne Inna ta shiga unguwar kundila ta zagaye gidaje sunfi goma sai ana gaba ne wata mata tace ta amince zata dauketa aiki, alokacin Inna kamar ta zuba ruwa akasa tasha.
Wani hanzari matar ta kawo na cewar ita masuyi Mata aiki kwana suke basa jeka ka dawo, Sam Inna bataji dadin wannan maganar ba.
Alfarma inna ta roki hjy ta taimaka Mata da ta dauko farida suyi aiki tare.
Kin amincewa hjy tayi dan dole Inna ta hakura da aikin wannan ake cewa ga k’oshi ga kwanan yunwa, Inna afadarta bazata iya tafiya aikin kwana da kwanaki tabar farida na kwana ita daya agida ba, hakan ne yasa ta yanke kauna Kai tsaye gida ta wuce jiki asanyaye tana kara mik’awa Allah lamuranta.
Lokacin da ta shiga wanke-wanke ta samu farida tana yi, guri Inna ta samu ta zauna agajiye tana maida numfashin wahala, farida ce tazo take tabaryar Inna halin da ake ciki.
Ajiyar zuciya Inna ta sauke ta zayyanewa farida duk yanda sukayi da hjy.
Farida ce tace, ” Inna meyasa Kika ki amincewa? ”
“Saboda ke farida ” Inna ta fada.
Da mamaki farida tace, ” saboda nifa inna, bangane ba ” inji farida.
” Saboda bazan iya tafiya wani guri inje inyi ta bauta inbarki ke daya kina kwana agidan nan ba, kinsan fa akace kiwon mutum ake ba dabba ba, haka kawai wani yazo ya b’ata Miki rayuwarki abanza da wofi, gwara na hakura Allan daya hallicemu zai San yanda zaiyi damu, haka zalika Allah baya dorawa bawa Abinda bazai iya ba, nasan hakan Yana daga cikin jarrabawar mu, duk tsanani Yana tare da sauki wata Rana wannan rayuwar da muke ciki zai zama tarihi ” Inna tayiwa farida bayani.
Tun daga lokacin Inna Bata kara fita neman aiki ba sai yan kame-kamen sana’ar da takeyi yau suyi wannan gobe suyi wannan ahaka har aka shafe wata biyu da zuwan Alh ya’u, Inna ta saddak’ar da duk irin cin mutumcin da Alh ya’u zai musu, saboda basu da wata kafar samu kudin gidan sa, tabbas Alh ya’u tasan idan yazo ba makawa zai tashe ne tunda akallah sun shafe sama da wata uku basu bada kudin hayar ba, ita kanta tana mamakin yanda Har ya Kara musu kwanaki bai dawo garesu ba kamar yanda ya fad’a.
Inna da farida na daki suka jiyo sallama daga kofar gida, hijabinta farida ta dauka tasa ta fita, atsaye ta sameshi gaisheshi farida tayi, kafeta Alh ya’u yayi da idanu sannan yace, lafiya klau yan Mata kiyi mun sallama da mamanki kinji ”
Farida mamakin Alh ya’u take, gida ta shiga ta sanarwa da mahaifiyar ta, ba karamin firgici Inna ta shiga ba gabanta ya hau duka uku-uku, fita tayi ta sameshi akofar gida, Inna gaisawa sukayi da Alh ya’u sannan ta Fara cewa, ” Alh ya’u Dan Allah Dan Annabi ka taimaka kayi Mana afuwa wallahi kudin nan………….. ”
A zafafe Alh ya’u ya katseta, ” ke dakata mun tashi tsaye kibar tsugunna mun, wallahi ko ki bani kudina ko ku fice mun daga gida na ”
Duk da Inna tasan karshen maganar kenan, Amma ba karamin razanata maganar tayi ba, cikin magiya ta Fara rok’onsa, Alh ya’u kallan tsaf yayiwa Inna sannan yace, ” kina San na yi muku afuwa ? ”
Kamar karamar yarinya Inna ta amsa da, ” Eh”
Shafa keyarsa yayi Yana gyara tsayuwa yace, ” Abu daya Zaki mun, idan Kika yi munshi kuwa ba kudin haya ba gidan nan da kike ciki zan iya mallaka Miki shi baki daya”
Mamaki, al’ajabi da ta’ajibi ne suka kama Inna kamar wata sokuwa haka ta saki baki da hanci tana kallan Alh ya’u, ta kasa cemasa Koda uffan.
Magana ya Kara yi Mata, ” Inna magana kinyi shiru ko inkara maimaita Miki? ”
Ajiyar zuciya Inna ta sauke sannan tace, ” naji abinda kace, meye bukatar taka? ”
” Yauwa wato abinda nake so, so nake ki bani auren waccen yarinyar taki shikenan abinda Zaki mu ”
Kafeshi da ido Inna tayi sannan tace, ” kasan me kake fada kuwa Alh ya’u? Inbaka auren farida fa kace, Kai bakaji kunya ba Dan Allah? Yanxu farida nawa take na tabbata sai anraba shekarunka gida nawa Zasuyi nata, ka dubeka ka dubi farida alalace dai nasan ka yi jika da farida, Alh ya’u shekarar farida goma Sha shida fa, gaskiya bazan iya baka farida ba ”
Azafafe Alh ya’u yace, to kuwa dole ku barmun gida na nida na dauka ke mutuniyar kirkice Ashe ba haka bane, wallahi ayau basai gobe ba sai kun fice mun daga gida ” Yana gama maganar fuuuuu yayi gaba cikin sauri ya haye mashin dinsa yayi gaba.
Hawayen bakin ciki da takaici ne ya zubowa Inna, gida ta juya ta shiga ta zayyanawa farida duk abinda faru harda maganar aurenta da Alh ya’u.
Farat farida tayi tace, ” Inna to meye aciki Dan na aureshi kinaji fa gida zai bamu, Kuma kina gani me kudi ne fa Inna ni wallahi………………. Ke rufemun baki sakarya kawai mara sanin darajar kanta ” Inna ce ta katseta cikin takaici, farida badan taso ba taja Baki ta tsuke Tana mita kasa-kas.
Bayan Awa daya da fitar Alh ya’u, sai gashi ya dawo shida wasu mazga-mazgan samari, Kai tsaye gidan suka shiga, umarni Alh ya’u ya dinga bawa samarin ana fita da kayansu kofar gida, cikin isgili suke musu watsi da kaya.
Gaba daya kayan su inna sai da aka fice dasu, dududu kayan nasu basu fi ajuye su cikin buhu ba sai wata yaloliyar tabarma, fitowa sukayi Inna na kuka ta karasa gurun kayansu, suna fitowa Alh ya’u ya ja kofarsa ya datse ta da kwad’o ko kallan arziki bai musu ya sa Kai yayi gaba.
Su farida kuka sukaci suka godewa Allah, bakin cikin duniya ya ishesu mutane hard sun Fara taruwa, ganin anfara sa musu idanu yasa suka, Inna ta hada musu kayansu Kai tsaye gidan hansatu me adashi ta nufa, gaba daya kayan ta Kai Mata Dan ta siya, hakan kuwa akayi gaba daya tayi musu kudi gaba daya dubu uku ta siyesu, ta mik’awa Inna kudin, ba wanda Inna ta gayawa maganar tashin su daga su sai kayan jikinsu, suka tafi.
Tafiya suka yi me nisa, tafiya suke ba tare da sunsan inda zasu ba, cikin gajiyawa farida tace, ” Inna wai Ina zamu je ne ”
” Duniya zamu shiga farida, muje ko bakin gada ne gwara mu dinga kwana acen.

Leave a Comment