*🫦TSAUTSAYIN TAUNA🫦*
_✨GAWURTATTU BIYAR✨_
*Zainab Babib(Mom Islam*
Kuyi following d’ina a arewabook
https://arewabooks.com/u/momislam22
Ina mik’a sak’on gaisuwa mai yawa, a gareku masoyana, musamman wanda suka nunamin zallar soyayya gurin siyan littafina *GUNTUN GORO* yauma gani tafe muku da sabo wanda nake ganin zakuyi farinciki, labarin yazo da sark’ak’iya, da zallar soyayya, karku manta da sunan fitaccen littafin wato *TSAUTSAYIN TAUNA* dagajin sunansa kunsan akwai cakwakiya over kudai muje zuwa.
Page 1-2
KADUNA STATE
Anguwar Dosa.
Wani irin tsawa ya daka mata tare da cewa ”meyasa kikeson sakani a hanyar da bata dace ba?, sokike inje inyi sata in kawo miki ko Yaya?”,
Matar da zatayi 35yrs bak’a bamai jiki sosai ba, dakaga yanayin jikinta zakasan suna fama da matsanancin talauci,
Ta rik’e k’ugu tana girgiza ta matso gabansa kana tace “inhar bakaje kayi sata ka kawomin ba wallahi baka cika namiji ba”
Rik’e da baki malam Haladu ke kallonta, bai jira me zata sake cewa ba ya fice.
Yana fita ta kalli Aisha yarinya y’ar kimanin shekaru goma sha biyu duniya, sai bala’in rawar kai, Aisha fara ce sbda Wanda baisan iyayenta bama ya ganta zai rantse y’ar masu kud’i ce, Allah ya azurtata da yalwataccen gashi, ga idanuwannan masu d’aukar hankali y’an madai-daita, gashin girarta kuwa luf-luf yake, sai d’an k’aramin bakinta na tsiwa pink kamar ansa masa janbaki,
“Mama wai baba bazai nemi aikin yi bane? Wallahi yanason zuciyarsa ta mutu ne irin na mijin Hansatu mai waina”
Aisha ta fad’a tana ta6e baki,
“Yo ni ina zan sani, muddin yace zai takuramin wallahi bazan zauna ba ai bashine autan maza ba, gashi tunda talauci ya aureshi muka shiga uku,sudai abin kamar a jini yake kaf danginsu matalauta ne”
“Mama ki fara yimin k’osai in mun sami ribar sai mu dinga adanawa kinga ma kya sami jarin siyarda gawayin ko?”
“Amma Aisha baki da hankali, kina ganin ana fama da cefanen gida ki kawomin yin aikin mangyad’a, yanzu komai da yayi tsada sokike ciwon zuciya ya kamani na murk’ushe kud’in da y’an uwana suka aikomin dashi?”
Dajin haka Aisha ta cuno baki kana ta mik’e tare da ficewa waje tana gunguni.
Tunda malam Haladu ya fita, yake neman aiki koda kwa6ar k’asa ne ta masu gini amma Allah besa ya samu ba, zama yayi kusa da shagon wata mata mai abincin siyarwa, wata dank’areriyar mata ce ta fito bak’a, kanan yaji gashin doki kai kace ba musulma ba, cikin d’aga murya take cewa “wai yau ina almajiranne duk kunyi shiru, gashi babu masu wanke-wanken?”
Da sauri malam Haladu ya taso jiki na rawa yace “gani ni zanyi”
Cikin yamutsa fuska tace “sai ka shiga ka d’ibo plets d’in da akaci abinci ga ruwan wanke-wanken nan ga omo can” ta nuna masa inda aka ajiye.
“To” yace jiki na rawa ya nemi leda ya kwashe ragowar abincin da mutane sukaci suka rage ya tara a bak’ar leda, kana ya fara wanke-wanken, yana gamawa cikin d’aga murya yace “hajiya an gama”
D’ari da hamsin ta mik’a masa sai abinci data zuba masa d’an kad’an
Jikin Baba Haladu a sanyaye ya kamo hanyar gida, koda yaushe in zai shigo gida gabansa fad’uwa yake saboda masifar maman Aisha,
Kasancewar akwai abinci a hannunsa hakan yasa ya sami k’warin guwaiwar shiga gidan,
Yana shiga ya sami maman Aisha a d’aki tana sallahar azhar, mamaki ne ya kamashi a zuciyarsa kuwa cewa yake “wai har anyi sallah ni ban saniba?”
“Haladu me aka samo mana ne? kasan idan mukaga bak’ar leda da bayani”
Malam Haladu ya k’arasa d’akin ya nemi guri ya zauna sannan ya kunce bakin leda kana yace “d’auko kwanon a juye”
Jikin maman Aisha na rawa taje ta d’auko kwano ya juye shinkafar, ya had’a da wacce aka bashi, sai gashi shinkafa ta cika kwano,
Cikin fara’a maman Aisha tace “megida a ina aka samo mana beta?”
Malam Haladu yayi jimm kafin yace “zubar da mutunci na nayi,
Ta dafe k’irji kana tace “ban gane ba?”
Malam Haladu yace “wallahi zaman nayi a shagon mai siyarda abinci shine nayi mata wanke-wanken ta bani”.
“Mtsw nama d’auka wani abun ashan kayi, ai wannan ba komai bane naga kamar da nama a ciki ko?” Kallonta kawai yakeyi Amma a zahiri zuciyarsa nayi masa zafi.
Tsince naman cikin abincin tayi kana ta ajiyesu a roba daban tace “in zuba maka ne ko kaci acan?”
Tsabar takaici kasa ce mata komai yayi.
Sai da taci tayi hani’an sannan ta ajiyewa Aisha tunda shikam yak’i kulata,
Cikin takaici ya fice a gidan ya nufi masallaci, Aisha kuma sai dare ta shigo,
Tana zuwa ta fad’a jikin mamanta a shagwa6e tace “mama baban kowa yana siyawa yaransa kayan dad’i niko baba ko biskit baya siyamin”
Maman Aisha tayi murmishin da zata iya kiransa dana takaici kafin tace “bak’in talauci ke dukansa ki rabu da matsiyacin ubanki kawai, yau dai ya kawo mana abinci harda nama”
Da murna Aisha ta mik’e tsaye tana rawa, Dan rabonsu da nama tun watan babbar sallah.
Abinci mai albarka itama Aishar sai da taci ta k’oshi sannan ta tashi, harzata kuma fita Maman tace “jekiyi alwalah rabonki da sallah tun ta asubha”
Cuno baki tayi kana tace “ke ina lissafa miki naki ne? Kin mance lokacin da kikayi sati guda ba sallah ba azumi?”
Waro ido maman Aisha tayi ta bita da gudu tana cewa “yau naji fitsara zuwa gaba Aisha zata zageni”
Sai da ta tabbatar da mamanta ta shiga d’aki sannan ta fito taje tayo alwalah tazo parlo ta kabbara sallah, kasancewar gidan nasu madai-daci ne mai d’auke da d’akuna uku na maman ciki da parlo sai makewayi sai kicin, shikenan tsakar gidan nasu ma ba wani mai fad’i bane, infact ma gidan haya ne duk shekara malam Haladu yake biyan dubu goma sha biyar kud’in wutar lantarki d’ari biyar.
Koda ta shimfid’a sallahya ba sallahar take ba, kana daga gefe kanajin mis-mis-mis d’inta, mamanta na daga d’aki tace “halin naki dai bazaki fasa ba ko?”
Aisha tayi ruku’u tace “duk nai 6atawa mutun sallah wuta zai shiga ni babu ruwana,taci gaba da sallaharta.
Zuwa dare basu wani samu abincin da zasu sake ci ba, haka sukasha ruwan d’umi suka kwanta, Aisha ce ta fara bacci sai mamanta itama kafin malam Haladu ya shigo, yaji dad’i sosai dan baccinsu shine kwanciyar hankalinsa, yahau gadon tare da d’ago Aisha ya mayar gefe ya kwanta kusa da mama,
Can cikin dare mama taji ya fara lalubarta, bige hannun nasa tayi taci gaba da baccinta, malam Haladu dai ya kasa hak’uri ya kuma matsowa murya k’asa-k’asa yace “haba maman Aisha kiyi hak’uri ki bani hakkina wallahi nayi hak’uri har tsawon wata biyu sai kace dutse?”
Cike da masifa ta tashi zaune kana tace “mazan k’warai sune ake yiwa lale marhabun kaikuwa mai matacciyar zuciya mene ne abin faranta maka anan ko ance maka ni ina sha’awarka ne?”
Ta d’auko pilo ta koma Palo, kan wata doguwar kujera da ita kad’ai ce a palon sai kwanukan wanke-wanke da randar ruwa, kwanciyar tayi tana jan tsaki lokaci-lokaci har bacci yayi awon gaba da ita.
Washe gari asubar fari, Aisha ta riga kowa farkawa, waigawa tayi taga babu mama, ta fara dukan baba tana cewa “ina maman? sarai ya jita, dan haramar alwalah yake shirinyi ta tashi,
A hankali Aishan ta sakko ta taho parlo tana ganin maman tace “to kekuma meya kawoki nan?”
Jin shiru bata ansa ba, da alamun baccin har yanzu dad’insa takeji,
Aisha ta d’ibo ruwan randar k’asa ta juyewa mamanta a jiki, da sauri maman ta tashi zaune tana goge fuskarta da gefen zani tace “dan ubanki me yasa baki kwarawa ubanki ba saini da kika Raina?”
Shima ina nan zuwa gurinsa ai, naga kuma taimakonki nayi tunda kinaji ana Kiran sallah kikak’i tashi”
Maman na mik’ewa ta wanka mata mari tare da cewa “gaba ki k’ara”
Tsalle ta dingayi tana 6arin kwanuka had’i da wurgi da tukwane, a ranar dai anyiwa Aisha duka tun kafin gari ya waye.
Malam Haladu na kwance yana jinsu ko uffan bai ceba, har Saida ta gama dukan ya fito,bai kulataba ya wuce gurin alwalah.
Tunda yayi alwalah ya wuce masallaci.
Gari na wayewa ya dawo gida, zama yayi a tsakar gida kan kujera y’ar tsugunno ya zabga tagumi, fitowa mama tayi tana cika tana batsewa, tazo gaban malam Halatu ta tsaya kana tace “mene ne nufinka? mun kwana bamu k’oshi ba yanzu ma sokake ka horamu?” ta k’arashe maganar tana yatsina fuska.
“Uhm maman Aisha bazanso mu zauna da yunewa ba, amman idan bani dashi fa?” wata wawuyar cafka takai masa kana ta shak’e kwalar rigarsa tana cewa “banda mutuwar zuciya irin taka da kanada iyali kana wani cewa baka da kud’i mazan k’warai na zuwa neman aiki kaiko kana gida idan y’an uwana sun bani muci idan basu bani ba mu zauna haka, to wallahi na gaji”.
Malam Haladu dai baima waigo ba bare ya kalli fuskarta,
Zuwa rana wajen 11:34am malam Haladu ya fice daga maman Aisha sai ita Aishar, suna zaune tun safe babu abinda sukaci, sai kame-kame wanda aka sabayi, gurin tukunyar Aisha tayi kana ta bud’e tukunyar tana cewa “mama tsakin ya tsotse”
“Sauke”
Mama tace tana daga zaune, bayan ta sauke ta zuba musu a kwanuka biyu, daga ganinsa ma a iya su biyun koda sunci ba lallai bane ya ishesu, sunfara ci kenan Baaaba Indo ta shigo hannunta rik’e da dubu d’aya, bayan tayi sallama tace “Maman Aisha ko kinada canjin dubu guda?”
Maman Aisha ta rik’e baki kana tace “wuuuu dubu guda fa kikace, d’in mik’o min it’a insa albarka dan rabona da ganinta nakai wata”
“Wallahi ke kikaga dama ga mata nan masu maza wanda suka fiki hali suna bara amma ke kin zauna, aiko zakiga zama, shi mijin da kike tak’ama dashi gayican a k’ofar gida yana zaune gurin y’an kashe wando”
Maman Aisha ta dafe k’irji kana tace “Aiko banga ta zama ba, tunda abinda ya za6a kenan ni na zamo mijin shi ya zamo matar inhar zamuci musha mu tsira da mutuncinmu”
Baaaba Indo tace “wane irin tsira da mutunci a harkar bara nasiyi akuya nasiyi fili ke har zannuwa na samu, ga wani alhji shahararren mai kud’i kullum yazo saiya fillo mana y’an dubu-dubu”
Maman Aisha ta zabura kana tace “aiko zan biki amma bari ya shigo”
Baaaba Indo ta tafi tana mitar cewa “shi mutuwar zuciya kema haka kikeso ki zamo kenan?nikam bazan dinga jira ba” tayi gaba.
Tana fita Aisha tace “wallahi mama Baaaba Indo ta kawo shawara sai ki mak’ale idonki d’aya ki dinga bara ni zanyi miki jagora inmuka tara kud’i mudingacin abin dad’i”
Suna cikin magana malam Haladu ya shigo hannunsa rik’e da bak’ar leda, da gudu Aisha taje ta anso tana cewa “oyoyo baba”
Fuskarsa d’auke da murmishi yace “yauwa y’ar baba d’aukomin kujera in zauna”
Bayan ta kawo masa, mamanta tayi masa sannu ciki-ciki, ba yabo babu fallasa ya amsa yana fito da shinkafa da wake da manja da magi had’i da attaruhu da albasa,yace “ayi maza a d’ora mana abinci Allah ya kawo”
Jikin Aisha na rawa tace “mama yau zamuci shinkafa “maman ta bige bakinta kana tace “dan ubanki tunda kin wuni da yunwa dole kiyi magana, Allahn daya haliccemu yabamu munci munsha, ace tun safiya har 12:pm mutum bai k’arya ba Sai kace d’an boko, gara ma y’an bokon sunacin mai maik’o mukuwa wataran ma abincin babu magi”
“Innalilahi wa inna ilaihir raji’un, malam Haladu ya furta tare da dakatar da ita yace “ya isheni haka!! bakisan wannan gorin da kikeyi min yana konamin raiba bakisan tafarfasar da zuciyata takeyi ba, sam wad’annan kalaman basu kamaceki ba”
Malam Haladu na yin shiru tace “abinda kayi ake fad’a, akwai k’arya a ciki ne?” Ko kanada zuciyar nema? acikin abokanka akwai wad’an da suka yi gida da mota wasu har k’asar waje sunje, kaiko baka ma da muhallin kanka bare asa ran zaka taimaki wasu”
Dafe kai malam Haladu yayi zuciyarsa babu dad’i, yakawo masifa bai kawo bama masifa,
Suna cikin haka Aisha ta fice da gudu, zuwa anjima sai gashi an tasota a gaba wai ta fasawa wani d’a goshi, baba yace “Dan Allah kuyi hak’uri kasoshi a barbad’a masa garin ganyen kurna”
Mama ta mik’e tsaye cike da masifa tace “tsoransu kakeji da zaka wani magiyar basu hak’uri?”
“Idan d’anka ne da laifi dole kai zaka bada hak’uri dan haka ki dakatamin”
Aisha kuwa tanata tsalle inda kasan batasan komai ba,
Yaran na tsaye har malam Haladu ya gama basu hak’uri suka fice.
Aikin Aisha kenan kullum sai an kawo k’ararta gida, duk ranar da ba’a kawo ba kuwa bata da lafiya.
“Zaki d’auki kayan cefanen ki girka ko kuma kina ganin in koma dasu”
Malam Haladu ya fad’a a hassale,
“Yo aiba yau ka fara komawa dasu ba”
Ta fad’a tare da shigewa d’aki.
Gurin had’a wuta yaje ya had’a kana ya kira Aisha yaja mata kunne akan neman magana, sannan yace ta tayashi d’ora girki, babu abinda ta iya sai jajjaga kayan miya, iya shid’in tayi ta fice,
Sai daya gama had’a sanwa sannan ya fice yabar gidan.
Maman na ganin ya fice ta fito tana cewa “ni wallahi sakina nakeso kayi inkuma kak’iji bazakak’i gani ba”
Ta nemi guri ta zauna, da ruwan ya tafasa ta wanke ta zuba ko tsincewa batayi ba,
Sai dare akaci abincin dan hatta Aishar ma sai dai in a yawonta taci dan bata, bata ba.
A wani kwano kamar na bola aka sanyawa malam Haladu abinci itakuma ta cika kwano ta koma d’aki.
Washe gari basuda abincin d’umame, iya kacin ragowar wanda ko Aisha taji ba k’oshi zatayi ba..!
# Love
# Romantic
# Funny
Zazzafan labari wanda yazo da sabon salo, wanda yazo da gwagwarmayar soyayya mai sanyi, mai sanyaya zuciyar masoya, saboda wannan karon mun ta6o lovers.
Domin magana da marubuciyar 08141799224
_Ummu Maheer_
*DINYAR MAKAHO*
_Miss Hajo_
*KHADIJATUL SABREEN*
_Mrs Bukhari_
*ANGULU DAKAN ZABO*
_Ummu Affan_
*SANDAR MAKAUNIYA*
_Mom Islam_
*TSAUTSAYIN TAUNA*
*Ga tsarin yanda biyan yake*
_Guda d’aya 300_
_Guda biyu 500_
_Guda Ukku 700_
_Guda hudu 800_
_Guda Biyar 1k_
Kai tsaye zaku iya turo kuɗinku ta wannan hanya.
0037219728
FATIMA RABIU SUNUSI
StanbicIBTC BANK
Shaidar biya ta nan
0810 433 5144
Masu turo kati MTN ta wannan number.
0702 616 6536
Ƴan Niger zaku turo da naku kai tsaye ta wanna number.
0706 860 6171
*TALLAH*
Ina kuke amare uwayen gida kai har ma da ƴan mata? Ko kun san Mrs Bukhari mai kayan ƙamshi, ai in dai batu na kayan ƙamshi gyaran jiki da na ɗaki to kai tsaye ku ne mi Badi’at domin gwana ce ta ko wanne fanni a ciki. “Wai ƙamshi kina nufin Badi’at dai marubuciyar nan tamu mai nishaɗantar da mu?”
“Tabbas Fati ita take magana, ai kin dai ji yadda ake magana a kai na, hatta me gidana ya jinjinawa Badi’at domin duk wani ƙamshi da zaki ji a jikina tare da gidana to daga ita ne, ke me kankat ma har gyara na nake yi domin gyaran aurena daga gareta ne, shi ya sa bana wasa da gyaran jikina da na gidana har kuke kirana da ƙamshi.”
“Eh tabbas nima na jinjina mata, kuma zaki bani addireshinta domin nima na kwankwati wannan garaɓasa. Ko zaki iya faɗa mini abubuwan da take sayarwa.?”
“Bari na faɗa miki akwai…
Humra
Kulacca
Sudanese Humra
Kulacca ta gashi.
Turaren wuta ɗan gaske, iri daban daban.
Turaren mopping
Room freshner
Turaren turara kaya.
Turaren wuta na toilet
Sannan akwai ingantaccen maganin infection
Ina da magungunan mata, wanda zai gyara amarya da uwar gida.
Wanda zasu shiga daga ciki kuma
Akwai sabulun amare, da dilka ta amare, wanda zaisa amarya ta fito ta haska tas
Kabbasa
Setin kujerar tsugunno
Sannan inayin turaren wuta da kasko, da ashana wanda ake rabawa a taron biki ko suna.
Ina bayar da sari.
Ma sha Allahu to taya zan sameta domin mallakar nawa?
“Kai tsaye zaki mata magana ta whatsApp ko kiranta ta wannan number.
08179523215
*TALLAH*
A yau nazo muku da manya manyan magunguna domin gyaran Auranmu! Saboda yadda zamantakewarmu ta AURE keta kara tabarbarewa. Mata iyayenmu ku fito ku gyara jikinku , domin wallahi har Abadan macen da bata gyara bata isa ta hada kanta da mace me gyara ba har abadan! Mu gane yaku yan uwana mata, ma’aurata! wallahi gyara shine mace Akwai mata dayawa dasuka san magunguna na, a online Suna siya kuma Alhmdulillahi ba wadda ta siya bata dawo tamin godiya ba, Alhmdulillahi!Alhmdulillahi! Alhmdulillahi! Yawancin mata dayawa na nemana ta dayan sim dina sede nayi losing dinsa sede wannan shi yake Aiki 08104335144, A YAU NAZO MUKU DA MAGUNGUNA INGANCI DA IZININ UBANGIJI, WATO AINIFIN HADI Iri ~iri na MALLAKA D’ANA MIJI ALFARMAR ANNABI SAW, ina tabbatar muku da magunguna na babu shamaki base na tsaya bata lokaci a bayaniba zanso ku gwada dan tantance GASKIYA * Akwai cututtukan dake hana maganin mata aiki idan kinason sani ki tuntubeni ta wannan lambar 08104335144 wadannan cututtukan inhar kinadasu wallahi duk maganin daza kisha bazeyi Aiki ba, kuma bazaki taba fahimtar komiba a harkar dadih na magungunan mata.
*MUNADA MAGUNGUNA AVAILABLE KAMAR HAKA*👇🏽
*ingantaccen maganin infection *
Ingantaccen maganin basir
Ingantaccen maganin gyaran nono
Ingantaccen maganin gyaran hips
Ingantaccen maganin kara kiba kiyi dumur~mur dake
Ingantaccen maganin rage tumbi meyi tsakani da Allah
Ingantaccen maganin matsin farji mesa dadin farji ga azzakarin d’ana miji.
Ingantaccen MALLAKA TA DOMIN ALLAH (Bata harkoki) shine sunansa, hmmmm Wannan magani inada tabbaci a kansa shidin hadine kawai na mallakar d’ana miji akwai komi a cikinsa na mallaka hajiya ki gwada kisha mamaki Alfarmar Annabi SAW.
Se matsin (GAMADIDI) wannan matsi in kikayi amfani dashi har abadan abidina mijinki baze kawo a gaban wata ya mace ba in har ba gabanki bane wannan inada tabbaci a knsa 💯 kuma wadanda suka saya ma sun kara tabbatarmin da kyaunsa na mamaki.
Akwai zallan hadi na amarya
Akwai hadi na uwar gida sarautar mata wannan seat ne akwai komi a cikinsa.
Akwai ingantattun gumba iri iri kamar haka 👇🏽
Akwai gumbar Madara
Akwai gumba me rubutu 🤐
Akwai gumbar kankana
Akwai gumbar giginya (sa megida kuka)
Akwai ingantacciyar gumba me suna (BARIN MAKAUNIYA)
Akwai gumbar hasi
Akwai zallar gumba wadda ita ta rubutuce zallarta zaki ganta baka karki damu Aikin kawai zaki duba 😉
Akwai gumbar gero
Akwai gumbar ridi
Akwai gumbar garin gamadidi ita ta mallaka ce zallarta.🤐
Akwai tsumi iri iri sunansu sha yanzu magani yanzu 💯👇🏽
Akwai tsumin kankana
Akwai tsumin baure
Akwai tsumin rubutun Ayar Allah
Akwai tsumin kwakwa
Akwai tsumin giginya
Akwai tsumin GORON SUDAN (wannan special ne dan kudinsa ma daban yake)
Akwai ingantattun magunguna na tada shaawah kama daga na turawa har zuwa na Islamic wato namu na gangajiya. Akwaifa maganin maza madam na hausa dana turawa 😉 duk basuda side effects 👌
Akwai rubutun mallaka
Akwai zoben mallaka
Akwai hayakin mallaka
Akwai zani na mallaka
Akwai hadin ci da kaza
Akwai hadin yan shillah
(Muna dafa kaji da yan shillar ma dade sauran abubuwa da dama,)
Akwai dambun nama na mata wanda ke dauke da magungunan sirri na mata mesa tsantsi da laushi da ruwa a farjin mace 😉
Akwai magunguna na ban mamaki wadanda base na rubutasu ba saboda SIRRI 😉
Muna aika magungunan mu kasa kasa gari gari *UWAR GIDA KI GARZAYO QUEN SANAF Islamic chemist kise magunguna na ingantattun ne insha Allahu kin wuce takaicin d’ANA MIJI * direct to me 08104335144 muna sauraron masu shawarwari a kan zaman AURE insha Allahu, amma in knsan baki shirya siyan magungunan jima’i ba na mata ko na maza pls karki kirani.
*Mun gode da kasancewa da gawurtattu biyar taku na biyu* 🤘🏿
*🫦TSAUTSAYIN TAUNA🫦*
✨GAWURTATTU BIYAR✨
*Zainab Habib (Mom Islam*
Page 3_4
Iya Aishar ta bawa ita kuma ta dama kunun gari,
Zuwa rana malam Haladu ya shigo da fara’arsa, yana cewa “yau dai an bani mashin in dinga kabu-kabu,
Ga mamakinsa sai yaga maman Aisha na fara’a har tana tafi, tare da cewa “Allah ya sanya alkairi kuma Allah ya tsare”
Malam Haladu yace “Amin ya rabbi, ya d’auki hularsa ya fice da niyar zai aiko da kayan cefanen.
Yana fita ta k’walawa Aisha Kira, Aisha na zuwa tace “yau bara zamu Allah yasa Baaaba Indo ta shigo”
Aisha ta fara murna sbda a ganinta zasuyi kud’i su faracin abin dad’i,
Kaya maman ta sauya zuwa had’in gambiza na riga da zani na atamfa ta d’auki sandar da suke dukan 6era ta d’auko wani fasasshen kwano da yagaggen hijabi ta d’aukowa Aisha yagaggen kaya da tsinkakken takalmi maman Aishar ta zumbula hijabi gudun kar a fahimci inda zataje, tana zuwa bakin hanya ta tarar musu mashin suka wuce Kano road, suna sauka a mashin tace ina zuwa malam, ta rik’e hannun Aisha sukaje gurin mabaratan dake zaune a tsallakensu ta aro nera d’ari, bayan tace musu mijinta ya gudu ya barta sam ba’a jin labarinsa.
Tana kawo masa ya wuce it’s kuma ta dawo ta zauna,
Tun safe suke zaune a gurin babu abinda sukaci, gashi har k’arfe goma tayi shiru,
Cikin ikon Allah wata galleliyar mota tazo wucewa suka mik’e da uban gudu har ana ture-ture, Aisha ko sai cewa take “Alhaji ka taimaki mamana bamu da abinda zamuci jiyama da yunwa muka kwana, babana baya kula da ita”
Cikin d’aga murya take maganar,
Rage tsayin glass d’in motar yayi kana yace “ina yarinyar dake magana?”
Aka nunata, mutumin da a k’alla zaiyi shekaru 60yrs ya ciro bandir d’in y’n d’ari-d’ari ta mik’a wa Aisha, sukuma ya mik’a musu na y’an d’ari biyu yace su raba, ya wuce, aka fara danbe da wata budurwa mai yiwa gurguwa kuma makauniya jagora tace ai kud’in su Aisha yafi yawa, Aisha ta fasawa budurwar baki tana cewa “dan ubanki inda zamu dinga zuwa bara kullum sai mun fiku ciniki yasin mtsw taja tsaki tare da cewa “mama tashi mu tafi”
Mabaratan gurin nata kallon su maman Aisha,
Kasancewar sun sami abinda ya kawosu yasa suka fara tarar mai mashin Dan su koma gida, suna tsaye Baaaba Indo ta sauka a mashin hannunta rik’e da buhu da robar bara,
“Wato ni inacan ina jiranku ashe sammako kukayi y’an duniya”
Maman Aisha tace “hmm Baaaba Indo ko karyawa bamuyi ba shiyasa muka fito wallahi gashi munsami na cefane”
Mai mashin d’in daya kawo Baaaba Indo zai juya tasa masa hannu ya tsaya tace ka kaimu Anguwar Dosa, Baaaba Indo na magana maman Aisha ta haye mashin tana cewa “mayi magana a gida idan kikadawo”
Rik’e da baki Baaaba Indo ke kallonsu har sukayi nisa suka 6acewq ganinta,mabaratan gurin sukace wannan mata anyi y’ar bala’i yasin, anbamu kud’i su rik’e saboda cuta da son zuciya, Baaaba Indo dai bata nunar da tasan mama ba sbda shiru tayi, dan suka gano ita tayi mata hanyar zuwa gurin masifa ta auku.
Suna isa gida suka tarar da malam Haladu a zaune ya zabga tagumi, maman Aisha tayi sallama har sau uku shiru ko waigowa beyi ba,
Sai da tace “maa…laam!!” sannan ya d’ago fuska irin ta yanayin cikin damuwa ya sauke ajiyar zuciya kana yace “ina kukaje tun d’azu nake nemanku har can k’asa naje amma ko d’uriyarku babu”
“Nifa bance kayimin tambayar k’wa-k’wa ba, dan haka ka k’yalemu”
Shiru malam Haladu yayi tare da mik’ewa ya shige d’aki ya nemi guri akan kujera ya zauna,
Murya k’asa-k’asa yace “wannan wace irin damuwa ce, sai kace ni kad’ai Allah ya jabarta da talauci, ina zansa kaina, yau na nifa aiki mashin ta 6allomin gyaran dubu uku, gashi ko cinikin dubu d’aya banyi ba” sai ya fashe da matsanancin kuka,
Daga can tsakar gida, maman Aisha tacewa Aisha jeki siyo mana shinkafa mudu d’aya da rabi, ki siyo mangyad’a gwangwani d’aya ki siyo mana kifi na d’ari biyu ki had’o da Maggi da onga kiyi sauri tunda munada itace barin had’a wuta in d’ora sanwa”
Tana bawa Aisha kud’in ta fice da gudu tana murna yau abinci harda kifi shikenan suma sun zamo y’an gayu,
Jiki a sanyaye malam Haladu ya fito, ya tsaya a bakin k’ofa kana yace “maman Aisha a ina kika Sami kud’in cefane?”
“Nifa sa idone bana so, tunda dai kaga an d’ora ai saikayi shiru da bakinka ko? amma zaka wani cikawa mutane kunne da surutu”
Maman Aisha ta fad’a tana gyara wuta,
“Allah ya baki hak’uri”
Kalmar daya furta kenan ya k’ara gaba.
Tsaki taja had’i da buga k’afa tace “wallahi gobe ma saina koma maula ai naga gurin zuwa”
Aisha na dawowa aka gyara kayan miya takai nik’a, zuwa dare ana kiran magrib shinkafa da miya ta kammala danma kafin mai awara ta kawo sunci,
Sai da mama tayi sallah sannan ta raba abinci, yaukam ansawa malam Haladu abincin da yawa, bayan ya dawo daga sallahar isha’i ya shiga da sallama, ga mamakinsa sai yaji tana cewa “oyoyo da mai gida,Aisha mik’a masa abinci”
“Sannunku” kawai yace dan a inda tayi fara’ar sai abin ya bashi mamaki Dan ba kasafai ake ganin fara’arta ba.
Washe gari asubar fari ta mik’e yau babu dogon bacci, kasancewar ta riga kowa tashi hakan yasa ta share gida ta d’umama abinci, taje tayi alwalah sai da tayi nafila sannan ta tashi malam Haladu, yana tashi yayi alwalah ya wuce masallaci, sai da gari ya waye sannan ya dawo, mamaki ne ya kamashi, ragowar shinkafa da miyar jiya harda ragowa kuma cikin kwana, batare da yayi magana ba bare akuma dank’ara masa bak’ar magana, yasa cokali ya fara cin abincin.
Yana gamawa yayi hamdala tare da tura hannu cikin aljihunsa ya ciro wata kod’ad’iyar d’ari biyar ya mik’a mata kana yace “cefanenku na dare da rana wallahi daga fara aiki da mashin d’innan jiya harta 6allomin gyara”
Ko tanka masa batayi ba ta kar6i kud’in tayi d’aki.
Yana fita suka fara shirye-shiryen barin gidan, kamar jiya shigar da sukayi yauma ita suka mai-maita, wato had’in bauta Aisha kuma da yagaggun kaya haka suka haye mashin suka wuce,
Suna sauka ta mik’awa mai mashin kud’i ta kamo hannun Aisha da d’an buhunsu a hannu ta gaishe da matan gurin, suka amsa mata cikin d’agun kai, Baaaba Indo dataga maman Aisha bata hangots ba, ta sunkuyar da kai,
Juyowar da maman Aisha zatayi sukayi ido biyu da Baaaba Indo, maman Aisha ta washe baki kana tace “Baaaba Indo ashe kinzo”
Bayan sun gaisa ko wacce tasa ido a titi, ita kuma Aisha na tsalle tana cewa “a taimakemu babanmu ya gudu yabar mamanmu da yunwa,
Yau dai kamar anyiwa garin shara Dan masu manyan motocin ma basu wani wuce ba bare susa ran samu, har k’arfe ukun rana su maman Aisha ko sisi basu rik’e ba, malam Haladu ya dawo daga gareji yana daga tsallaken titi, ya hango maman Aisha zaune ita da Aishar a layin mabarata, mamaki ne ya kamashi had’i da takaicin, abinda bai ta6a tunanin zata aikatashi ba, ya taho da gudu zai tsallaka titi mota tayi gaba dashi, da gudu mutane sukayo kansa cikin harda mabaratan gurin dasu maman Aisha, wani mai mashin cewa yake “malam Haladu nefa yanzu na ganshi a tsaye, lallai tsautsayi ba’a samasa rana”
Daga jin mai mashin yace malam Haladu maman Aisha ta rugo da uban gudu tana ihu ta watsar da buhun da sandar hannunta tana cewa “mijina ne, indai Haladu ne wallahi mijina ne”
Kaff mutanen gurin mamaki ya kamasu kowanne sai kallonta yake, wai ashema tanada miji mijinma mai K’arfi Wanda ba musaki ba,
Kasancewar motar data bigeshi ta tsaya aka sanyashi a ciki suka wuce Giwa hospital harda maman Aisha da itama Aishar,suna isa aka shiga dashi, likitoci furr sukak’i kar6arsa, sai sun kawo jami’an tsaro,
Duk da ba wani ciwo yaji ba sai kujewa da yayi a goshinsa amman da alamu yana jin ciwon gurin sosai, Wanda ya bige malam Haladu ya d’aga waya tare da matsawa gefe, ba’a jima ba sai ga abokinsa nan yazo aka shiga dashi emergency room, abu d’aya yake ambato wato kansa, idan ka gansa lokacin da akayi hatsarin bazaka ta6a cewa ya bugu sosai ba, sbda kujewa ne kawai, Amma asalin ciwon yana cikin jikinsa,
Sai da akayi masa allurar bacci sannan suka sami lafiya, doctor daya gama y’an gwaje-gwajensa ya sauke nannauyar ajiyar zuciya, kana yace “ku biyoni zuwa office,
Da maman Aisha da mai motar wanda a k’alla zaiyi shekaru 35yrs a duniya, suka shiga office d’in, nuni yayi musu da su zauna kafin ya cire gilashin idonsa yace “wato a gwaje-gwajen da mukayi mun gano zuciyarsa na daf da kamuwa da ciwo, gaskiya yana cikin damuwa, ke iyalinsa ce?”
“Eh”
Maman Aisha tace tana gyad’a kai,
Ya rubuta musu magunguna yace suje su siya a cikin asibitin,
Jikin maman Aisha na rawa tace “likita maganin zekai nawa?”
“Dubu goma”
Likita ya bata amsa a tak’aice,
“Ina zuwa”
Mutumin yace tare da ficewa,
Itama maman Aisha fitowa tayi ta koma kan dogon bencin dake k’ofar d’akin da aka kwantar da malam Haladu,
Cikin yanayin damuwa “Aisha tace “mama baban ya mutu ne?”
Muryar mama a dashe tsabar kuka dataci tace “ciwon zuciya ya kusa kamashi”
Aisha ta toshe baki had’i da cewa “mama mu dena zuwa yawon maula kinga baba zai mutu”
Buff ta bige mata baki kana tace “yawon maulan ba taimakonsa mukeyi ba ki gayamin?”
Aisha tayi shiru kamar mai tunanin wani abun,
Wanda ya bige babanta ne suka taho shida abokinsa, mama ta mik’e da sauri, tare da cewa “bawan Allah ansami maganin?”
“Eh zankoma office d’nne”
Ya fad’a a tak’aice,
Suna tafe abokin nasa yace “Alhaji Kabir meka fahimta game da wannan baiwar Allahn?”
Wanda aka Kira da Alhj Kabir yace “Jamil abinda na lura dasu, suna cikin matsanancin talauci, dan a inda na lura talauci yana damunsu,
Isarsu office ne yasa sukayi shiru da maganar da sukeyi,
Doctor yace “Masha Allah amma bawan Allah na jinjina maka, irin namijin k’ok’arin da kayi gurin tsayawa ceto ran bawan Allah, sa6anin wasu mutanen babu tsoron Allah saisu gudu”.
Murmishi Alhaji Kabir yayi kafin yace “inaso ka tsoratar da wannan matar..”
“Ina jinka”
Doctor yace, yana kallon Alhaji Kabir.
“Inaso kasanar mata da cewar zuciyar mijinta tana daf da bugawa muddin bata dena yawon maula ba”
“Ai wannan mai sauk’i ne, karka damu Alhji temakonta zamuyi sai dai ta yi gaggawa gurin kashe zuciyarta a yawon maula”
Likita ya fad’a yana mik’ewa,
A tare suka shiga room d’in da malam Haladu yake, sun sameshi ya farka yana ta d’aga hannu,
Da sauri likitan ya k’arasa tare da zuwa kusa dashi yace “baba jikinne sannu Allah zai baka lafiya”
Malam Haladu yafara magana a sark’e yana cewa “ka..ki..ra..min matata”
Da sauri likita ya lek’a ta window yace “baiwar Allah mijinki na magana”
Maman Aisha ta rugo da uban gudu ta bud’e k’ofar ta shigo tana cewa baban Aisha yadai jikinne ko kanason wani abu ne?”
Duk jerin tambayoyin data dinga yi masa d’aya ya sami damar amsawa yace “banason komai ki mayar da Aisha gurin iyayenta sai kici gaba da yawon maula!! Yawon maula kawai Aisha taji, kasancewar yanzu ta shigo, ganin mama a yanyin damuwa yasata matsa kusa da ita ta kalli Malam Haladu kana tace “baba ya jikin?”
Hannu ya d’aga mata yaci gaba da cewa “ki mayar da ita gurin iyayenta inhar kika barta a gurinki ita kanta yarinyar ba yafemiki zatayi ba”
Dama ba kune iyayena ba? dama baku kuka haifeni ba?!”
Kukane ya kubce mata ta fice da gudu,
Alhj Kabir da Jamil da doctor ta wuce suna ta tattunawa akan inda zasu taimaki maman Aisha da malam Haladu, ganinta kawai sukayi tana kuka,
“Baiwar Allah jikin baban naki ne?”
Kasancewar ta toshe bakinta da hannu yasa d’aga musu kai kawai tayi sbda kukan dake taho mata.
Alhj Kabir ne ya taso yazo inda take kafin yace “baiwar Allah meya faru?”
“Babu komai”
Aisha ta fad’a a tak’aice.
‘Bangaren Malam Haladu kuwa tari ya sark’eshi hannun maman Aisha a nashi tana rok’on gafara, kalma uku ce ta kuma had’ashi da ita wato, “ki mayar da Aisha gurin iyayenta inyaso kije kici gaba da yawon maula! kamar inda ya fad’a d’azu, sai kuma da yace “ana bina bashin d’ari biyar, sai kuma kalimatu shahada da yayi tare da ambaton lahaula wala k’uwawata illah billah” a gigice maman Aisha tayi waje tana hango doctor dasu Alhaji Kabir tace “ka kasheshi ka huta shikenan dama kaso kasheshi ne shiyasa ka bigeshi, ashe duk maganar da malam Haladu yakeyi suna recording, Jamil ya mayar da waya cikin aljihunsa kafin yace “baiwar Allah inda yayi niyar kashe megidanki wallahi ko saurararki bazaiyi ba, ke bama zai tsaya ku gansa ba Dan haka ki iya kalamanki,
“Wallahi sai ofishin jami’an tsaro ya Bimini hakkina”
Jamil yayi murmishi kafin ya fito da I’d card d’insa yace “shari’a daga nan har kotun Allah ya isa inhar akwai muje tunda ke bakisan tauhidi ba, doctor yaja hannun Jamil tare da cewa “just forget muje”
Kai tsaye suka wuce room d’in suka sami likitoci a kansa, suna zuwa aka rufe masa fuska da farin k’yalle…!
# Love
# Romantic
# Funny
Domin magana da marubuciyar 08141799224
MOM ISLAM
Akwai cakwakiya a cikin labarin, nasan yanzu ba lallai ku fahimci inda muka Dosa ba.
_Ummu Maheer_
*DINYAR MAKAHO*
_Miss Hajo_
*KHADIJATUL SABREEN*
_Mrs Bukhari_
*ANGULU DAKAN ZABO*
_Ummu Affan_
*SANDAR MAKAUNIYA*
_Mom Islam_
*TSAUTSAYIN TAUNA*
*Ga tsarin yanda biyan yake*
_Guda d’aya 300_
_Guda biyu 500_
_Guda Ukku 700_
_Guda hudu 800_
_Guda Biyar 1k_
Kai tsaye zaku iya turo kuɗinku ta wannan hanya.
0037219728
FATIMA RABIU SUNUSI
StanbicIBTC BANK
Shaidar biya ta nan
0810 433 5144
Masu turo kati MTN ta wannan number.
0702 616 6536
Ƴan Niger zaku turo da naku kai tsaye ta wanna number.
0706 860 6171
*Mun gode da kasancewa da gawurtattu biyar taku na biyu* 🤘🏿
*🫦TSAUTSAYIN TAUNA🫦*
_✨GAWURTATTU BIYAR✨_
*Zainab Babib(Mom Islam*
Page 5-6
Wata Norse ta fito da sauri hannunta rik’e da wayar malam Haladu, mama taje da sauri ta k’ar6a tare da karawa a kunne, “ina Haladun”
Akayi magana daga cikin wayar, cikin kuka mama tace “Allah yayi masa rasuwa” ta kuma fashewa da kuka,
Sai da aka kuma magana a cikin wayar tad’au murya tace “Yaya Tanimu ne?”
“Eh nine kuna wane asibitin?”
“Asibitin giwa” ta bashi amsa.
Ba’a jima sosai ba asibitin ya cika da y’an uwa da abokan arziki, duk wani abu da ake bukata Alhj Kabir da Jamil suke gudanarwa har akayi masa sutura aka sallaceshi, sannan aka kaishi gidansa na gaskiya, Baaaba Indo kuwa tariga da tazo ta kasa shiga cikin asibitin, dataga an fito da gawar ne ta bisu aka wuce gida.
Aisha kuwa ta riga kowa dawowa dan anan aka sameta,
Gida ya cika sosai da y’an uwa da abokan arziki, a ranar abinci har neman gurin zubawa sukeyi, Alhj Kabir kuwa dashi ake komai,
Bayan kwana uku an watse daga zaman makoki Aisha ta rame sosai duk da ba wata babba bace Amma tanada zurfin tunani sosai,
Ranar da malam Haladu ya cika sati d’aya, maman Aisha na zaune a d’aki ita da mak’ociyarta, Aisha ta shigo tana sanye da hijabi har k’asa tace “mama dama baku kuka haifeni ba?”
A razane maman ta d’ago, cikin tsawa tace “seme idan bamu muka haifeki ba, idan kika kuma yimin magana mai kama da wannan wallahi saina sa6amiki”.
Sallamar da wasu mata sukayi ne yasa mama yin shiru suka kar6i gaisuwa,
Baaba Indo kullum sai tazo zuwa yamma ta tafi, Alhji Kabir kuwa har iyayensa sai da sukazo sukayi gaisuwa tare da kawo musu kayan abinci.
Rasuwar Malam Haladu da kwana arba’in wato lokacin mama ta fita daga takaba, saura idda, duk da kwanakin da suka kwashe har yanzu abinci bai yanke musu ba,
Wata ranar Juma’a da misalin k’arfe 1:30pm, Zaune Aisha take a cikin d’aki ita kuma maman tana parlo, kamar kullum taci kukanta ta gaji, duk wata tsiwa yanzu babu wani lokacin ma tayi ta rok’on Allah mutuwarta tunda dai batada iyaye meye amfanin zamanta a duniya.
‘DAN ‘DANO💞
Gidane had’adde wanda tsayawa misalta kyawunsa sai mu cika pegi bamu gama ba, zaune suke a babban parlonsu wanda yake da girma sosai, shi kansa parlon abin tsayawa a kalla ne sbda ya tsaru iya tsaruwa, wasu mata ne zaune a kujera guda su biyu, daga can gefe kuma wata tsohuwace wacce a k’alla zatayi shekaru 70 a duniya, sanye take da riga da zani na atamfa ta kwafa d’aurin d’ankwali abindai gunin ban dariya, kallon matan tayi kana ta Kira sunan d’aya daga ciki tace “Sajida kin wani zauna kin zubawa talabijin ido sai kace yau kika fara kallo ga aiki can a kicin kamar zai kashe uwani me aiki” wacce aka kira da Sajida ta yamutsa fuska tare da cewa “Hajiya mama damafa an kawo uwani ne dan mu huta da wasu aiyukan”
“Ah lallai bari kabiru ya shigo zanyi masa magana idan ya koreta sai ku huta”
Takuma cewa “kekuma Nafisa kitashi ki d’orawa Kabiru abin bud’a baki kinsan dai yau ya kammala azuminsa”
Wacce aka kira da Nafisa ta mik’e da sauri tabar gurin tana gunguni.
Alhaji Kabir babban d’an kasuwane, sana’arsa itace siyarda atamfofi da shaddoji, a Kano yanada manyan shaguna har guda biyu, haka ma a jos yanada shago d’aya, a nan Kaduna yanada shaguna biyu, inda Allah ya yalwata masa arzik’insa, bayan rasuwar mahaifinsa ya d’auko Hajiya mama ta dawo gidansa, wato mahaifitarsa, shi kad’ai Allah yaba Hajiya mama, gashi bata son taga ansami koda nera biyar ne a gurinsa, Allah ya zubawa Hajiya mama k’ananun magana ga gori da sa ido uwa uba wataran ta fasa ihu tace baka bata abinci ba, wannan kenan. Sajida itace babba a halin yanzu bata da d’a ko d’aya, Hajiya mama tasa Alhji Kabir k’aro aure akan Sajida bata aihuwa, shine ya auro Nafisa y’ar k’awarta, wani lokacin ta nuna tafison Nafisa wani lokacin kuwa tayi mata tatass, watan Nafisa bakwai tayi 6ari tun daga nan Allah bai sake bata ciki ba.
“Au eyye, harkinyi samun gurin da zaki dinga yimin k’ananun magana kenan nagode babu komai, kuna yaran mata bakusan inda zaku kula da mijinku ba, wani sa’in ina fad’ar gaskiya ana ganin laifina”
Dole suka watse dukkansu suka bar mata parlon taci gaba da surutunta ita kad’ai,
K’arfe 8:pm bayan Alhji Kabir ya shigo, sai da ya fara shiga d’akin Hajiya mama sannan ya mik’e zai fita ta tsayar dashi, dawowa yayi ya zauna kafin yace “Hajiya kinsani na dawo?”
Eh dama dalilin dayasa na dawo dakai shine, gara ka zauna musha hira tunda dai ba wani abun suke tsinana maka ba, aihuwar ma basuga dama ba, yo banga amfanin shiga d’akunansu ba, sai dai suci suyi Kashi su juya d’uwaiwaka dan iskanci”
Kan Alhji Kabir a k’asa yace “Hajiya dole fa aba kowacce hak’k’inta wanda Allah ya ratayamin”
“Kabiru kacemin wa’azi ka koma yi aibansan wa’azi ka koma ba sai yanzu, ni zaka gayawa hak’k’i? to nace yau ka huta maza jeka, d’akinka ka kwanta”
Har ga Allah wani sa’in yanajin haushi idan tana yi masa haka, dayake mahaifiyarsa ce koda yayi fushi dole yake sakkowa.
Yana fita ya shiga d’akin Sajida, sanye take da sleeping dress pink color rigar mai shara-shara, ana iya hango komai na jikinta, da sauri ya k’arasa tare da rungumeta kasancewar tana tsaye tana jifansa da murmishi, yana rungume da ita ta dinga matsawa a hankali suna tafiya har suka zube kan bed, takai bakinda dai-dai saitin kunnensa ta rad’a masa “ina alfahari da samunka, hasken idaniyata anurin raina, tabbas samun miji irinka shine abunda mata da yawa suke fata na sameka hakan ya sanya nakejin kamar nafi ko wacce mace sa’a a duniya, ina alfahari dakai mijina ilove you”
Kiss ya bata tare da cewa “love you too my sweet heart”
Suna rungume da juna wayarsa tayi ring, gyara ruk’on da yayiwa Sajida yayi da hannunsa na hagu ya d’aga wayar da hannunsa na dama, kafin ya d’aga sai da ya duba number yaga babu suna, yana d’agawa, daga can 6angaren akace “hubbil khairi nayi kewarka fa”
Da sauri ya sake Sajida tare da kallon number ya kara wayar a kunnensa ya kuma mayarwa kunnensa a karo na biyu kana yaci gaba da cewa “ban gane dawaye nake magana ba”
Daga can 6angaren wacce ta kirashin tace “kana magana da Safiya, nasan bazaka ganeni ba, amma inaso kasani soyayyarka tana neman hallakani sbda kar in cutar da kaina da yawa yasa nanemi numberka na kiraka pls ka yarjemin”
Ta k’arashe maganar tana jan numfashi.
“Mtsw karki sake Kiran wannan layin ban sanki ba”
Yafad’a ransa a 6ace.
Tare da cilla wayar gefe,
Tashi d’aya mood d’in Sajida ya sauya, sosai kishi ya cika mata zuciya, ta juya baya alamar tayi fushi, a hankali ya isa gareta yana bubbuga mata baya, kana yace “haba sweetheart akwai wani albishir da nakeson yi miki?”
“Ina jinka” ta fad’a batare da ta juyoba,
“Mezai hana muje gidan marayu mu d’auko yarinya koya kika gani?”
Da sauri ta juyo kana tace “ina rok’on Allah ya bani nawa basai munje can ba”
Dole ya hak’ura da shawarar tunda dai batayi na’am da zancen ba.
Sai da yaci abinci ya k’oshi sannan yayi brush yazo ya rungumeta suka kwanta, tayi nisa da bacci sai ta dinga mafarkin wani mutumi na binta da wuk’a, sosai ta firgita ta tsala uban ihu wanda yaja hankalin Hajiya mama da dama rabi bacci rabi sa’a ido takeyi.
Washe gari da asbha bayan sunyi sallah Alhji Kabir ya dawo daga masallaci, dama al’adarsa idan ya dawo daga masallaci sai yaje ya gaisheda Hajiya mama da Nafisa sannan ya koma d’akin Sajida kuma duk wanda yake d’akinta ba itace da breakfast ba, yana shiga ya sami Sajida kwance tanata juyi akan kafet, da sauri ya k’arasa gurinta jikinsa na rawa ya fara tambayarta, “Sajida meke faruwa?”
Toshe bakinta tayi sbda amai daya taso mata, tayi toilet da gudu, amai ta dinga kwarawa kamar zata amayar da y’ay’an hanjinta, sai data d’auraye bakinta ta juyo ta ganshi jingine a bango kamar zaiyi kuka, ” Sajida kifad’amin abinda ke damunki” yayi maganar ne cikin wani irin yanayi”
Ya rungumeta suka dawo bedroom, hijab d’inta ya d’auka kana ya taimaka mata tasa suka fito parlo, samun Hajiya mama sukayi tana zaune tana sana’ar tata wato kallo, “ina kuma zuwa da sassafe?”
Ta tambayesu tana mik’ewa tsaye,
“Hajiya sai amai take zamuje asibiti ne a dubata”
“Ashsha! koda kunje ya wuce suce shawara”
Ita dai Sajida datagaji da tsayuwa ta zauna tana dafe da kanta,
“Honey ina kuma zakaje da sassafe?”
Nafisa ta tambaya tana kallon Sajida,
“Zamuje asibiti Sajida batajin dad’in jikinta”
“Oh Allah sarki barin d’auko hijab sai in taimaka mata” ta k’arashe maganar tana yatsina baki, kafin tace “sannu anty”
Cikin k’arfin hali Sajida tace “yauwa”
“To bazakije ba, nace bazaki ba taje ita da mijin nata taji da kiti fifin munafurcinta”
Nafisa ta sosa kai Dan ba haka taso jiba.
“Allah ya kiyaye hanya”
Hajiya mama tace tana ke6e baki.
Kai tsaye suka wuce parking space, d’aya daga cikin motoci biyun dake jere ya d’auka, suka tafi a ita, kai tsaye suka wuce GIWA hospital, wato asibitin da Malam Haladu ya rasu, kasancewar a iya zirga zirgar da sukayi ya sama da doctor d’in,
Bayan yayi parking ya dinga jerawa Sajida sannu, gyad’a masa kai kawai take har suka isa office d’in doctor,
Bayan sun gaisa ya sanar masa da matarsa ce babu lpy, file aka bud’e musu sannan yace suje test, bayan anyi mata abubuwan daya kamata, Norse d’in tace musu su nemi guri su zauna, bayan wasu lokuta results ya fito ta kai can office d’in kana tace “suje can akwai bayanin da za’ayi musu,
Hanunta ya kama suka shiga office d’in, doctor yayi musu nuni da gurin zama,
“Congrats madam tana d’auke da juna biyu”
Alhj Kabir ya juya yaga babu kowa, a tunaninsa ko da wani doctor yake magana, ganin shi yake mik’awa hannu yasa shi, mik’a nashi hannun da rawar jiki,
Doctor ya kuma nanata “congrats ina tayaka murna ya mik’a masa results kafin yace “mahaifarta bata da k’wari, akwai buk’atar ta dinga samun hutu tare da yawan bacci, da kuma cin y’a yan itace, karta dinga d’aukar abu mai nauyi”
Jikin Alhji Kabir na rawa fuskarsa cike da farinciki yace “insha Allah wannan ai duk mai sauk’i ne, mungode doctor, kuje pharmacy ku kar6i magani ga card, suna zuwa aka basu maganin tare da jaddada mata ta yawaita shan ruwan gishiri da sugar, daganan suka fito, kana suka shiga mota, suna cikin tafiya ta hango mai yalo, “uhm honey yalo zanci” mamaki ne ya kamashi sbda bata cinsa kwata-kwata, tunowa da juna biyun dake cikinta yasashi saurin parking ya lek’a ta k’ofa yace “mai yalo..!” mai yalo ya rugo da gudu yana gaishe da Alhj Kabir,
“Duka na nawa ne?”
“Na dubu d’aya ne”
“Ok juye mana a leda”
Alhj Kabir ya mik’a masa 1500, mai yalo yace “na dubu d’aya nefa”
“Eh nasani wannan na baka ne”
Mai yalo yayi godiya tare da sanya musu a leda yayi musu fatan sauka lafiya.
Suna cikin tafiya Sajida ta kwantar da kanta jikin kujera, har suka iso bata saji ba.
Bayan ya shigo gidan yayi parking, ya dad’e yana k’arewa fuskarta kallo, hankali ya shafi gefen fuskarta tare da manna mats kiss a kumatu, a hankali ta bud’e ido da fuskarta datayi fayau tace “harmun iso”
“Eh barin bud’e miki”
Dariya tasa kafin tace “haba sai kace jinjira?”
“Uhm ai kinfi jinjira babyna”
A inda yayi maganar sai ya bata dariya, suka fito a tare, babu kowa a parlon,
Zama tayi tare da jingina da kujerar, “Hajiya..!”
“Nafisa..!”
“Kufito kuji abin farinciki”
Alhj Kabir ya fad’a muryarsa cike da nishad’i,
Har suna rige-rigen fitowa tsabar son jin k’wa-k’waf,
Hajiya mama tana fitowa tace “to muna jinka”
Nafisa ma haka, fuska ba yabo ba fallasa tace “muna jinka”
“Sajida na d’auke da juna biyu”
Ya mik’awa Nafisa results d’in, mood d’inta ne ya sauya tashi d’aya, ita kanta batasan yanayin natan ya sauya ba, sai kuma ta k’ak’alo fara’ar dole tace “wayo dad’i anty Sajida zata haifo mana baby”
Kasancewar babu wanda ya lura da yanayin data sauya suna can suna firarsu da Alhj Kabir da Hajiya mama, ta kalli Nafisa tace “cikin haryakai wata nawa? Wata d’aya ne Hajiya”
Nafisa ta fad’a tana kuma k’ak’alo murmishi, it’s kam Sajida har bacci ya Kuma gaba da ita,
Wata muhimmiyar fara’a Hajiya take ga wani rawar k’afa da take, bini-bini tana d’akin Sajida tana tayata hira, zaman parlo ma tayi masa k’aura.
Washe gari ta kama, lahadi, tun dare aka fara ruwa har asbha tayi ba’a d’auke ba, kasancewar muna watan ogusta, ruwa ake bana wasa ba, Alhji Kabir bai sami zuwa masallaci ba, tare sukayi sallahr shida Sajida, bayan sun idar sunyi adu’oi sun gaisa, yayi mata ya jiki, “da sauk’i” tace masa, har ya murd’a handle d’in k’ofa zai fita tace “honey inason cin tuwon shinkafa miyar wake” angama my baby” kijira zuwansa insha Allah”
Alhji Kabir ya fad’a jiki na rawa ya fice..!
# Love
# Romantic
# Funny
Domin magana da marubuciyar 08141799124
_Ummu Maheer_
*DINYAR MAKAHO*
_Miss Hajo_
*KHADIJATUL SABREEN*
_Mrs Bukhari_
*ANGULU DAKAN ZABO*
_Ummu Affan_
*SANDAR MAKAUNIYA*
_Mom Islam_
*TSAUTSAYIN TAUNA*
*Ga tsarin yanda biyan yake*
_Guda d’aya 300_
_Guda biyu 500_
_Guda Ukku 700_
_Guda hudu 800_
_Guda Biyar 1k_
Kai tsaye zaku iya turo kuɗinku ta wannan hanya.
0037219728
FATIMA RABIU SUNUSI
StanbicIBTC BANK
Shaidar biya ta nan
0810 433 5144
Masu turo kati MTN ta wannan number.
0702 616 6536
Ƴan Niger zaku turo da naku kai tsaye ta wanna number.
0706 860 6171
*Mun gode da kasancewa da gawurtattu biyar taku na biyu* 🤘🏿
*🫦TSAUTSAYIN TAUNA🫦*
✨GAWURTATTU BIYAR✨
*Zainab Habib (Mom Islam*
Page 7-8
Yana fita kai tsaye d’akin Hajiya mama ya shiga, bakinsa d’auke da sallama, bayan ta amsa ya k’arasa kana ya durk’usa ya gaisheta, gyara zama yayi kana ya kalli agogon wayarsa, “k’arfe 8:30”
“Akwai inda zakaje ne ana tsuga ruwa?”
“Hajiya wallahi Sajida ce tace tanason tuwon shinkafa miyar wake shine nakeson zuwa in sanarwa da y’ar aiki”
“Yo y’ar aikin dana koreta jiya Kuna tafiya?”
Hajiya ta fad’a tana ke6e baki,
Matsalar dai d’aya ce gashi mun Sami k’aruwa dole a nemo y’ar aiki a gidanan kodan Sajida ya’r albarka mai juna biyu”.
Hajiya ta mik’e tana cewa “barinje kitchen d’in in dora mata ahincin”
Da sauri Alhj Kabir ya mik’e shima kana yace “no Hajiya bazakije girki ba zanje in siyo mata”
“Ina babu inda zakaje, jikan nawa zai zo duniya kacemin ba hakaba, kai Kabiru inaga nafika farinciki samun wannan rabo”
Tawuceshi, kai tsaye ya fito tare da shiga d’akin Nafisa, samunta yayi tana waya, yana shiga ta a iye wayar da sauri kamar mara gaskiya, “Nafisa kizo ki taya Hajiya d’ora abinci a kitchen”
Nafisa ta yamutsa fuska kana tace “bacin an kammala breakfast yana dining?”
“Eh nasan da haka kinsan Sajida na d’auke da juna biyu, to shine batason cin komai sai tuwon shinkafa miyar wake shine Hajiya ta shiga kitchen dorawa, kuma ai yakamata kije ki tayata”
“To naji”
Nafisa ta fad’a a tak’aice.
Yana fita ta d’auko wayarta ta danna number Safiya, ring d’aya ta d’aga “Safiya muna cikin waya dake Alhj ya shigo, shin baki kirasa bane ?”
Safiya tayi dariya kana tace “wannan alhjin naku sai ku hmm, yanzu dai me kikeso ?”
“Hmm”
Safiya tace, in inda tayi hakan Safiya ta jiyowa tace kiyi magana kinyi shiru kinsanni bana barin ta kwana,
“Safiya bana son cikin dake jikin Sajida yakai labari bana son d’an data Haifa yazo duniya, saboda zai zamemin ciwo a zuciyata kina sane da bana aihuwa,
Amma na 6oye masa saboda masifaffiyar mahaifiyarsa”
“Nafisa abinda nakeso dake shine, kibar d’an dazata Haifa yazo duniya inyaso sai mubi dare mu kasheshi ba tare da kowa ya sani ba”
Safiya ta fad’a tana tafi alamun duniyar zatayi musu dad’i.
“Nafisa tace “to sis shikenan amma kinsan dole zan ga wulakanci dan har wani rawar k’afa yake a kanta”
Daga nan sukayi sallama.
Har Hajiya mama ta kammala girki Nafisa bata fito ba,
Sai wajen 10:11am, sanye da dogon hijab tayi d’akin Hajiya mama da sallama,
“Antashi daga baccin asarar kenan?”
Hajiya mama ta fad’a tana kai lomar tuwo bakinta,
“Ina kwana Hajiya”
Nafisa ta fad’a batare da koda ruwan fara’a a fuskarta ba,
“Lafiya lau wani abunne ya faru naga kina fushi”
Mik’ewa Nafisa tayi, har tazo bakin k’ofa tajuyo tace “yau zanje gidanmu”
Hajiya mama na sud’e hannu tace “to zuwa yaushe zaki sai in shirya”
“Babu buk’atar kije”
Nafisa ta fad’a tare dayin gaba.
‘Dakinta ta koma ta shiga toilet tayi wanka, tana fitowa ta shafa mai, kai dakaga fuskarta zaka tabbatar yau babu lafiya, don ko fara’a batayi, bayan ta gama kwalliya ta bud’e drowa ta ciro leshi mai ruwan k’asa anyi masa aikin wuta a wuyan rigar, kasancewarta fara, sai leshin yayi mata kyau, a yanayin inda akayi d’inkin ma ya zauna a jikinta sosai.
Humra ta d’auka ta goga a jikinta kana taje gurin mayafai ta d’auki fari mai duwatsu da takalmi fari mai tsini ta d’auki wayarta ta fito parlo, Sajida da Hajiya mama ne zaune a kan doguwar kujera, sai da Nafisa ta ke6e baki sannan ta k’arasa tace “sannu anty Sajida ya jikin”
Fuskar Sajida d’auke da far’s tace “youwa Nafesa anguwa zakije ne?”
Hajiya mama tace “ni naga tijara wai Nafisa ni take cewa bazan bita ba?”
Sajida tayi murmishi sbda ada inda wacce Hajiya mama ta tsana bai wuce ita ba yanzu Kuma tana ganinsu a rana tunda batada hak’k’insu,
“Sai na dawo”
Nafesa tace tare da ficewa batajira amsaba.
Tana fita Hajiya mama tace “shegiya juya”
“Innalilahi, haba Hajiya mama wannan aihuwar da aketa magana a kanta fa Allah mai bayarwa, bawai dan baya son bawansa bane take hanashi, sai Dan gwada imaninsa, wasu zasu d’auki tsawon lokaci basu aihu ba, wasu kuma zakiga kamar a bakin k’ofa suke tuntu6e dashi, akwai wanda sam harsu koma ga mahaliccinsu bazasu aihu ba, to mezasuce?”
Hajiya mama tace “wato kina nufin ni inayiwa Allah butulci kenan?”
Sajida tace “a’a Hajiya mama inhar maganar ta 6ata miki kiyi hak’uri”
GIDANSU Nafisa.
Horn driver yake a bakin wani tangamemen get, ga dukkan alamu gidan yafi na Alhj Kabir, sbda shima d’in an narka dukiya babu laifi, ana bud’e get drivern ya shiga da mota, kai tsaye parking space ya tsaya, fitowa tayi mayafinta ninke a kafad’arta hannun hagunta Kuma ta rik’e hand bag, kai tsaye taje bakin k’ofar da zata sadaka da sashen mahaifiyarta, part-part ne a gidan har guda uku, k’ofar farko itace ta mahaifiyarta, ta biyu kuma itace ta kishiyar mahaifiyarta, ta uku, wato amaryarsu, mahaifiyar Nafisa zatakai shekaru 74yrs kishiyarta kuwa batafi 40yrs ba, amaryarsu kuma 20yrs dan yarinya ce,
Hajiya Sakina, shine sunan mahaifiyar Nafisa, tanada yara uku, namiji mai suna Kalil zekai shekaru 35yrs, dagashi sai Nafisa, sai kuma k’anwarsu mai suna Salma wato autarsu shekararta 18yrs.
Kishiyarta kuwa sunanta Hajiya Hauwa, yaranta hud’u itama na farkon namiji ne mai suna Bashir Yanada shekaru Ashirin da biyar 25yrs yayi irin saurin girman nan ne, Wanda idan ka gansa sai ka rantse yayi 30yrs, Dan har yafi Kalil girman jiki, sai k’aninsa mai suna Usman yanada shekaru 15,sai k’anwarsu mai suna Juwairiyya, shekararta 13yrs me binta Husna, itace mai shekaru 9yrs.
Amaryarsu sunanta Hajiya Amina sbda taje Makkah, bata ta6a aihuwa ba, amman yarinyar Hajiya Hauwa Husna tana gurinta.
Kai tsaye Nafisa tashiga part d’in mahaifiyarta, samunsu tayi suna hira sai dariya suke, da alamu duniyar tayi musu dad’i, ko sallama bata tsaya yiba ta fad’a jikin momynta tana kuka, cike da damuwa suka matso kusa da ita, Kalil yace “haba sister menene haka daga zuwa sai kuka?”
Yana idda magana Salma tace “anty Nafisat keda waye?”
Momyn ma takasa cewa komai sai binta da kallo take, daga k’arshe tace “daughter meke faruwa?”
A shagwa6e Nafisa tace “momy ciki ne da Sajida harya fara girma, ni bansan ya zanyi ba, d’an tarairayata da Kabir yakeyi duk ya dena soyayyar ta koma gurin Sajida akan cikin data samu” ta k’arashe maganar tana kuka.
“Eeeeh” ciki fa kikace ?, kice bokanta yayi nasara to inhar tasan wata batasan wata ba, narantse da Allah baza’a haifi wannan yaron a gidan ba, inhar an Haifa to lahira ce makomarsa”
Momy ta fad’a tana jinjina kai.
Cikin natsuwa da sigar kwantar da hankali Khalil yace “haba momy sai kace ba musulmai ba, ke da girmanki kike wannan maganar, kinsan iya adadin zunuban da zaki kwasa kuwa?”
“Kai Ibrahim.! inhar bazaka kawo taka gudunmawar ba to kayimin shiru, wato harda Hajiyar tasa ake sakarcin ko?”
Nafisa ta gyd’a kai da sauri,
“Za suci ubansu basai an had’a da malamai ba wallahi sai sun gane kuransu”
Sai da suka lafa da zancen sannan Salam tayi magana,
“A ganina momy abata maganin da cikinta zai zube wallahi sbda anty Nafisa ta samu kawanciyar hankali”
“Yauwa y’ar gari, kekam halinki abin a duba ne, baza’a bata maganin komai ba amman dai zasu d’an d’ana kud’arsu wallahi”
Sum-sum Khalil ya mik’e a zuciyarsa yana binsu da adu’ar shiriya,
Wuni sukayi hirar Sajida da Hajiya mama da Alhji Kabir,
Sai yamma taje part d’in Hajiya Hauwa, da sallama ta shiga ta zauna akan kujera tana jiran fitowarta, Juwairiyya da Husna suna jinta suka rugo da gudu suka rungumeta suna cewa “anty Nafesa ashe kinzo”
Fuska ba yabo ba fallasa tace “eh mana ai nayi fushi ko kud’an lek’o gidan nawa”
“Anty Nafisa dad ne ya hanamu wai makaranta”
Juwairiyya ta fad’a, tana dariya.
Suna cikin hira Hajiya Hauwa ta shigo, fuskarta d’auke da fara’a,
“Ah Nafisat ashe kinzo amma dai ba yanzu kikazo ba ko?”
“Eh Hajiya na sauka da ciwon kai ne shine nasha magani na kwanta, sai d’azu na tashi”
Nafisa ta fad’a tana rik’e kanta, alamun dai bata da lafiyar,
“Ayya ubangiji ya baki lafiya mai d’orewa ya su Sajida da Hajiyar?”
“Suna lafiya tace tana mik’ewa,
Hajiya Hauwa tace “harzaki wuce be?”
“Eh Hajiya wlh yamma tayi Kuma nice da girki”
‘Daki Hajiyar ta koma ta d’auko wata leda mai d’auke da turaruka masu tsada da kamashi ta mik’a mata tare da cewa “ki gaishe da mutan gidan,
Godiya Nafisa tayi mata tace bari taje part d’in Hajiya amarya, haka suke kiran amaryar baban nasu,
Da isarta tayi sallama ta k’arasa, Hajiya Amina na ganinta ta kwa6e baki kana tace “walkslm sannunki da zuwa yau kece a gidan namu?”
Nafisa ta d’an yi Jim sai Kuma tace “nice”
Mik’ewa tayi kana tace “zan wuce sai anjima”
Batare data jira amsarta ba ta fice sbda basa jituwa, Nafisa na ganin dad ya auro musu sa’arsu, ita kuma tana ganin bazata d’auki raininsu ba.
Part d’in momynta ta dawo a gurguje tayi musu sallama, tare da ce mata duk halin da ake ciki zata Kira a waya,
Tafe suke suna hira ita da Salma har suka isa parking space, motar gidansu ta shiga ta koma gida, kasancewar drivern nasu ya koma can gida.
Sun isa gidan k’arfe 6:40pm lokacin anata kiraye-kirayen sallah,
Da sallama ta bud’e k’ofar parlon ta shiga, turuss tayi ganin Alhj Kabir da Sajida suna zaune a parlo su biyu, yana zaune akan kujera mai zaman mutum uku, ya mik’e k’afafuwansa ita kuma ta kwanta akan cinyarsa hannunta nakan gemunsa, suna dariya,
Wani masifaffen kishi ne ya taso tare da tokare mata wuya, cikin masifa tace “to dai sallah ake masoyan asali sai a tashi ayi ibada”
Tana kaiwa nan ta shige,
Tana zuwq d’akinta ta cillar da wayarta da handbag d’inta a kan gado, ta ajiye mayafin a gefe ta zame d’ankwalin kanta, cikin yanayin damuwa da tashin hankali tace “wai sosuke su haukatani?, dama haka abun yake? meyasa Kabir ya koma kamar wani Wanda bazai iya control d’in kansa ba?”
Ta fad’a tana juyi a tsakar d’akin, “kodai asiri tayi masa?”
Ganin wankin hula yana neman kaita dare yasa ta d’aga waya ta Kira k’awarta, layin a kashe dole ta hak’ura, ta shiga toilet ta d’auro alwalah tazo ta shimfid’a sallahya ta kabbara sallah,
Bayan tayi sallama ta dinga kwararo adu’a akan itama Allah ya azurtata da juna biyu ko hankalin Alhji Kabir zai Kuma dawowa kanta kamar da sai abinda tace,
Sai da akayi isha’i sannan ya shigo, hannunsa rik’e da babbar leda,
Kasancewar a d’akin Nafisa yake ya sashi zuwa d’akinta kai tsaye, da sallama ya shiga ya sameta zaune akan gado tana latsa waya, mamaki ne ya kamashi sbda ba haka suka saba yiba,
Ganin bata da niyyar tasowa yasa ya k’araso tare da zama kusa da ita cikin muryar lallashi yace “haba Feenat d’ina mekuma yw faru?”
Sai da tad’au lokaci sannan tace “komai ma”
“Kinje anguwa kin dad’e gashi Hajiya bata nan taje gidan,Mama Mero, da ita da Hajiya mama, uwarsu d’aya Ubansu d’aya, tana zaune a tudun wada batada miji shima ya rasu, tanada yaro guda d’aya Hashim yana da super market babba, wanda take a mazaunin mallakinsa,
Dama abinda take jira kenan tace “kenan babu hali inje in gaishe da iyayena?, ita anty Sajidan a kwance take bata motsi?”
Kamar Wanda aka tunzuro, kamar bashine ya fara lallashinta ba yace “kotanada lafiya fa?, Doctor ya hanata aikin K’arfi, kinsani Hajiya Kuma ta kori y’ar aiki shine kikaje kikayi shiru sai dare zaki dawo ko?”
“Duk cin amanata da kayi bai isheka ba? zakazo kana damuna da fad’a”
Alhj Kabir yace “wato Nafisa wuyanki ya isa yanka, zargina ma kika farayi kenan?, A ina kika kamani dacin amanar taki?”
“Amman dai kasan k’arfe shida nayi ka dawo d’akina ko?”
Alhji Kabir daya fara gajiya da surutu yace “ni na hanaki dawowa?”
Daga haka yaje kan loka ya bud’e flaks na ruwan zafi ya d’auki cup d’in dake gurin ya had’a tea ya d’auki bredi ya koma gefe kan kujerar roba ya zauna yana shan tea,
Da kallon mamaki ta bishi, a zuciyarta kuwa cewa take “a haka zamuci gaba da zama yana gasamin aya a hannu dole in samo mafitar abinyi tunda dai wayar K’awata Salma a kashe.
Kwanci tashi asarar mai rai cikin Sajida yanata girma, ga wani kyau da k’iba data sakeyi, Hajiya mama kuwa kamar zata cinyeta, kullum cikin yi mata hidima take,
Nafisa kuwa, kowanne hali ta tsinci kanta a gidan Sai ta sanarwa da mahaifarta.
Bayan zuwanta gidansu da sati biyu, momy ta kirata a waya, da sauri ta d’aga tare da cewa “aslamu alaikum”
Daga can 6angaren momy tace “Nafisa kina ina ne? idan kina kusada mutane ki kauce akwai important thing da zamu aiwatar, da sauri ta mik’e, kasancewar tana parlo suna kallo, tana zuwa d’akinta ta danna key kafin ta kara wayar a kunnenta tace “momy ina jinki”
Cikin k’asa da murya kamar ta marasa gaskiya, momy tace “Nafisa kinada 50k a gurinki?”
Nafisa ta waro ido tare da dafe k’irji tace “momy ina zanga wanan kud’i, yanzu duk k’arshen watan ma da yake bamu 10k yadena bansan dalili ba”
“To nidai na gaya miki duk inda zakiyi ki samo koda 30k ne kizo muje gidan Hajiya Lami”
Da sauri Nafisa tace “ita kuma wacece?”
“Wallahi mai magani ce daga Niger duk taurin kan namiji da jiji da kansa Tasha gabansa, zata dawo miki dashi kamar k’aramin yaro sai inda kikayi dashi”
Murna ce ta kamata sbda taji cikakken bayanin da momy tayi mata, cikin k’arfafa guwaiwa tace “momy zanyi masa magana koda aro ya bani…?
# Love
# Romantic
# Funny
Madarar soyayya tare da cakwakiya
_Ummu Maheer_
*DINYAR MAKAHO*
_Miss Hajo_
*KHADIJATUL SABREEN*
_Mrs Bukhari_
*ANGULU DAKAN ZABO*
_Ummu Affan_
*SANDAR MAKAUNIYA*
_Mom Islam_
*TSAUTSAYIN TAUNA*
*Ga tsarin yanda biyan yake*
_Guda d’aya 300_
_Guda biyu 500_
_Guda Ukku 700_
_Guda hudu 800_
_Guda Biyar 1k_
Kai tsaye zaku iya turo kuɗinku ta wannan hanya.
0037219728
FATIMA RABIU SUNUSI
StanbicIBTC BANK
Shaidar biya ta nan
0810 433 5144
Masu turo kati MTN ta wannan number.
0702 616 6536
Ƴan Niger zaku turo da naku kai tsaye ta wanna number.
0706 860 6171
*Mun gode da kasancewa da gawurtattu biyar taku na biyu* 🤘🏿
*🫦TSAUTSAYIN TAUNA🫦*
✨GAWURTATTU BIYAR✨
*Zainab Habib (Mom Islam*
Page ,9-10
Gabanta na tsananta fad’uwa ta ajiye wayar tare da tunanin kud’in da momy ta fad’a mata, da Kuma mallakar da sukayi magana.
Komowa parlon tayi ta samu iya Hajiya mama ne Sajida ta koma d’aki, Hajiya mama na ganinta tace “yau dai y’ar aiki zata zo, inata zuba ido ma na jita shiru”
Nafisa tace “wow Masha Allah”
Hajiya mama ta ke6e baki had’i da cewa “dama abinda kukeso kenan kuci ku kwanta ai kinga kwayi d’uwaiwaka, dama gakinan dasu hardana siyarwa”
Waro ido Nafisa tayi kafin tace “Hajiya mama cin fuska fa bashi da dad’i”.
Sallahr magrib ne yasa kowa ya koma sashen sa, bayan anyi magrib da isha’i, ta fito Dan cin abinci,
Samun Sajida ta fito tayi, ta zauna akan kafet ta mik’e k’afafu, cikinta yad’anyi girma, plet ta d’auko da kular abincin ta zuba musu shinkafa da miya da nama ta d’auko musu ruwa a fridge ta ajiye tare da saka cokali,
Suna cikin cin abincin Sajida tace “Nafisa..”
“Na’am anty Sajida”
Nafisa ta fad’a tana mayar da hankali ga Kiran da tayi mata sbda tana ganin kamar akwai magana mai muhimmanci da zata gaya mata,
“Gobe idan zanje hospital zaki rakani? Wlhi wancan satin danaje nasha wuya gashi cikin yayimin nauyi”
Cikin tausayawar da a iya fuska ta nuna tace “ayya anty Sajida dama inason rakaki kodan taimaka miki da wasu abubuwan Alhj ne yake cewa a’a”
Sajida tace “kibari zamuje gobe insha Allah”
Daga haka sukaci gaba dacin abinci suna kallo, har k’arfe 8:30pm tayi, yink’urin mik’ewa Sajida tayi, kana tace “Wai kinji abun mai ciki wallahi wainar fulawa nakeso “Nafisa ta yak’e baki kana tace “bari ayiwa y’ar aiki magana saitayi miki”
Ta taimakawa Sajida zuwa d’aki ta dawo,
Kitchen ta wuce tare da sanarwa y’ar aiki tayi wainar fulawa tace “ta kaiwa anty Sajida ta wuce d’akinta,
Hajiya mama kuwa na daga d’aki tana cewa “abin mamaki, Nafisa tayi sanyi da masifarta gashi tanabin Sajida sau da k’afa Allah ya k’ara had’a kansu dama shine fatanmu”.
Nafisa na shiga d’aki tayi wanka, tana fitowa ta shafa lotion d’inta mai k’amshi tare da turaruka, harda shu’umar humra,
K’ananun kaya ta saka riga da skirt rigar pink color rigar ko rufe mata cibiya batayi ba, skirt d’in kuwa iya cinyarta yake black color, ta kuma feshe jikinta da turare mai sanyin k’amshi, zama tayi kan bed kana ta janyo wayarta, number Alhji Kabir ta danna ring d’aya zuwa biyu ya d’aga,
“Hello”
Nafisa ta shagwa6e fuska tare da sauya murya kamar ta mai shirin yin kuka tace “uhm Alhji shine ko ka kirani, ko har yanzu fushi kake dani?”
A inda tayi muryar sai jikinsa yayi wani yarr, kasancewarsa mutum mai son shagwa6a ba k’aramin rikita masa kwanya shagwa6a take ba,
Da sauri yace “haba Hajiya Feenat ni bakiyi min laifi ba, yanzu ma ina hanya ne nakusa gida”
“Allah ya dawo min dakai lafiya mijina”
Alhj Kabir na washe baki yace “amin Hajiya Feenat”
Sake gyara jikinta tayi ta jere masa abincinsa akan table dake bedroom d’in ta ajiye su jug na zo6o da ruwan sanyi a gora ta ajiye plet da spoon ta koma ta zauna,
Driving yake amma hankalinsa gabaki d’aya hankalinsa yana kanta, sbda muryar datayi masa ta haifar masa da feeling, Allah-Allah yake ya isa gida,
Tana zaune taji horn d’in mota da alamu ya iso, 6oyewa tayi a cikin labulen daya rufe k’ofar toilet, yayi sallama shiru, ya nemi guri ya zauna a doguwar kujerar data kasance ita kad’ai ce a bedroom d’in, mai zaman mutum biyu, wayarsa ya ciro a aljihu har zai danna numberta, yaji an rungumeshi, da sauri ya k’amk’ameta a jikinsa yana cewa “haba Feenat kinason tsoratani ko?”
Bin ta yake da wani irin kallo mai d’auke da soyayya, sam yak’i d’auke ido daga kallon shigar jikinta.
“Wanka zaka farayi ko abincin zakaci?”
Cikin cold voice wacce baima san yanada ita ba yace “inda na dawo da zazzafar soyayyarki ai kya bari in nuna miki ko?”
“Uhm ai nafison ka sami nutsuwa ta hanyar cin abinci ko yin wanka”
“Kece nutsuwata pls zo gareni matata”
Bata zod’in ba kamar inda ya buk’ata, ta bud’e kular abincin ta zuba masa shinkafa da miya da nama, ta bud’e wani d’an k’aramin bowl mai murfi ta zuba masa salad, zama tayi gefensa tare da d’aukar spoon ta fara bashi a baki, duk da hakan nutsuwarsa bata tare dashi sosai,
Bai yarda ta bashi shikadai ba, sai da yasata ta d’auko wani spoon d’in sannan yana bata tana bashi.
Bayan sun gama ta rufe kayan abincin ta ajiyeshi a gefe taje toilet ta had’a masa ruwan wanka sannan ta dawo ta taimaka masa ya cire kayansa, ya shiga wanka, bud’e drowa tayi ta ciro masa farar jallabiya mai hula ta ajiye tare da fesheta da turare mai k’amshi, ta d’auko boxes shima ta fesa turare,
Alhji Kabir kuwa, yana toilet baima fara wankan ba, yana tunanin sabuwar soyayyar da Nafisa take nuna masa, sbda rabonsu da hakan tun tana amarya, kawar da tunin yayi ta hanyar yin wankan yanajin wutar sonta a zuciyarsa, yana gamawa ya goge jikinsa da d’an k’aramin towel, ya d’aura wani fari a kugunsa ya fito,
Samunta yayi tana dane² a wayarta, yana zuwa yayi huge d’inta had’i da manna mats kiss, k’amshi sabulun da yayi wanka ya ziyarci hancinta, lumshe ido tayi kana tace “lokaci yayi nisa har k’arfe 10:11pm na dare”
Bai ce mata komai ba, sai iya boxes d’in daya saka ya rage hasken d’akin ya kasance hasken pink color bamai haske sosai ba.
Tsam ya rungumeta a k’irjinsa jikinsa na karkarwa,kamar sabon ango, ita kanta tasan da hakan,sbda turaren da momynta ta bata wato humra Wanda akayi had’e² a ciki, sosai ta rikita masa kwanya Dan har wani mimik’ewa yake, gadon bayansa take shafawa a hankali cikin salo na k’warewa da lallausan hannunta, tana hura kunnensa, daga nan salo da labari ya sauya, zuwa nasu na masoya suka lula duniyar da suka mance da mai ciki can a d’aki.
Sai wajen 11:pm ya sarara mata, ta tashi a gajiye taje toilet ta tsarkake jikinta, tana fitowa d’aure da towel ta zauna a bakin gado kana tace “Alhj wanka fa”
Kuma rarumota yake shirinyi, ta kauce da sauri tare da cewa “uhm ni katashi kayi wanka kokuma muje inyi maka”
Rik’e da hannun juna suka shiga toilet ta taimaka masa yayi wanka,
Bayan sun fito farar jallabiya yasa da new boxes, itama ta sanya sleeping dress suka kwanta rungume da juna, asuba ta gari.
Washe gari, d’akin Sajida zai koma kasancewar yayi kwana biyu d’akin Nafisa, kafin yayi wanka ya wuce gurin aiki sai da aka sakeyin zazzafar soyayya sanan ta barshi ya wuce,
Yana fitowa cikin shirnsa na zuwa aiki ya wuce d’akin Sajida, kwance ya sameta akan sallaya lokacin 7:30am, “Maman twins” sunan dayake kiranta dashi kenan,
Bud’e ido tayi tare da rik’e k’afar gado ta yink’ura tana ce masa “barka da safiya”
Fuskarsa wasai yace “barka mom twins ya kika tashi ya Kuma k’arfin jikin?”
“Da sauk’i” tace tana yamutsa fuska, har zai fice tace “yaune komawarmu asibiti fa”
“Okay akwai kud’i a gurin kayana ki d’auki abinda zai isheki”
A karo na biyu tace “tare da Nafisa zamuje Dan ta tayani wasu abubuwan ina Shan wahala idan naje”
“Okay baby damuwa saikun dawo”
Ya fad’a yana fita, tayi masa Allah ya kiyaye hanya”
Daga nan ya wuce d’akin Hajiya mama, da sallama ya shiga ya sameta ta kwanta, durk’usawa yayi kafin yace “barka da safiya Hajiya”
Hajiya ta tashi zaune kana tace “yauwa barka ya aikin, amman dai ka karya ko?” A’a Hajiya idan naje gurin aiki zan karya”
“Nifa bana son sakarci haka zaka tafi da yunwa? me amfanin matan naka a gidan?”
“Alhji Kabir yace “haba Hajiya suna aikatuwa ba, bawai dan ba’a d’ora bane kawai yau bazanyi breakfast da wuri bane”
“To ai shikenan idan yunwa ta cinyeka zaka nemi maganinta”
Hajiya ta fad’a tana yi masa sababi,
“Na tafi adu’arki nake buk’ata Hajiya”
“Allah ya dawo dakai lafiya Allah ya kareka daga dukkan sharri Allah ya kareka daga sharrin mutum da aljan”
“Amin ya rabbi nagode hajiy nagode”
Ya fad’a, tare da ficewa.
Koda ya shiga mota yana tafiya, mamaki darensu na jiya ya dingayi.
K’arfe 9:11am Nafisa ta farka daga bacci, ta dad’e a kwance bata motsa daga inda take ba, tuno makirci da kissar da tayi masa jiya tayi,
“Hmm inyasan wata ai besan wata ba, zan bari sai ya sake dawowa d’akina sai in kuma janye hankalinsa tare da cusa neman buk’ata ta a zuciyarsa Dan sai ya bada 50k d’innan ”
Tana gama fad’ar haka ta sakko daga kan gadon, tare da shiga toilet ta cire kayanta tayi brush kafin tayi wanka, tana fitowa ta goge jikinta taje gaban mirror ta shafa mai da powder tasa man baki,
Drowa ta bud’e ta d’auko doguwar rigar shadda milk color anyi mata aiki da jan zare, sosai tayi mata kyau Kuma ta zauna a jikinta, parlo ta fito hannunta rik’e da d’ankwali, Hajiya mama ta samu zaune a dinning tana breakfast ita kad’ai, karasawa tayi, kana ta durk’usa tace “barka da safiya Hajiya” Hajiya mama tace “barka dai ya gajiya” Nafisa tace “lafiya lau naga anty Sajida bata fito ba lafiya?”
“Tadai sha shayi ta koma d’aki naji tace yau zakuje asibiti ko?”
“Eh yaune barin duba ko ta shirya”
Nafisa ta wuce d’akin Sajida, sallama tayi kana ta k’arasa ciki, murmishi Sajida tayi kana tace “anty harkin shirya?” Sajida tace “eh dama ke nake jira”
Tana zaune har ta gama shiryawa ta mik’a mata wata y’ar jaka suka fito parlo, Sajida na sanye da riga da skirt na atamfa, super Holland tana d’auke da manyan flawoyi purple da bak’i sai adon fari, mayafin jikinta fari, hakama takalmanta.
Komawa d’akinta Nafisa tayi ta d’auko d’in mayafi da takalmi milk color da hand bag d’inta sukayiwa Hajiya sallama suka wuce,
Driver na ganinsu ya taso yana gaishesu, bayan sun amsa ya bud’e musu suka shiga, ya tambayesu inda zasu, asibitin GIWA hospital,
Suna tafe suna hira jefi-jefi, Nafisa kuwa burinta shine, suna zuwa asibitin ta aiwatar da abinda zuciyarta take raya mata,
Suna isowa yayi parking a harabar asibitin, suka fito tare da ce masa ba dad’ewa zasuyi ba,
Zama Nafisa tayi a gurin da mutane suke zama, ita kuma Sajida ta shiga jerin layin masu ciki lol,
Layi na zuwa kanta ta shiga d’akin awon,
Nafisa ta mik’e da sauri tare da aron pen a hannun wani security, ta sashi ya samo mata paper, yana kawo mata tayi wani d’an rubutu ta buk’aci jami’in tsaron ya nuna mata ofishin babban likitan, yana nuna mata ta shiga tana shiga ta sameshi hakimce akan kujera yana juyi lokaci-lokaci, sallama tayi kafin ta shiga, bayan ya amsa yayi mata umarni data zauna, tana zama tace “likita nazo maka da wata buk’ata ce, inhar ka amince zaka huta nayi maka alk’awari,
Ina cikin talauci ne? kokuma ance miki ni talaka ne?”
Kalmar data fito daga bakinsa kenan,
“Haba likita abin bana fad’a bane Kuma babu dole a ciki so zaka iya amincewa zaka iya k’in amincewa”
Ta k’ara da cewa “na rubuta komai a cikin pepper d’innan wacce nakeson ayi aikin a kanta zan shigo da ita ka ganta koda lokacin ya cika” tana kaiwa nan ta ajiye takardar ta fice.
Har ta dawo ta zauna, Sajida bata dawo ba, sai da ta dad’e a zaune sannan ta dawo, tana cewa “wash nagaji wallahi, kiyi hak’uri na zaunar dake ko”
“La anty Sajida babu wani zaunar dani da kikayi, kin kar6o magani ne?”
“A’a yanzu dai zan shiga kar6a gurin likita acan gurinsu ya k’are”
Sajida ta fad’a tana cirar kud’i a Jakarta,
“Muje in rakaki”
Nafisa tace “tana biyota a baya”
Suna shiga office d’in, doctor ya had’a ido da Nafisa, kashe masa ido tayi, kasancewar Itace a baya, hakan yasa Sajida bata fahimci duk abinda ke faruwa ba,
Tana mik’a masa card ya had’a mata magunguna kana yace “taje ta kar6i allura, tariga Nafisa fita, sai Nafisa tayi kamar ta fita sai ta dawo, tana dawowa tace “zan iya samun numberka?” Yes”
Ya fad’a tare da mik’a mata address d’insa da komai da komai, a wani card.
“Tnks sai naji daga gareka”
Ta fad’a tare da ficewa
Lokacin data fito Sajida ma ta fito suka wuce inda motarsu take,
Suna shiga Sajida ta kalli Nafisa kana tace “kinga irin shan wahalar da nake baki labari gashi ko wani abun bamu siya ba”
Nafisa tace “ai gida zamuje anty maci acan”.
Da isarsu gida driver yayi parking suka fito a gajiya, Allah ya taimakesu yanzu akwai y’ar aiki, ta gama komai.
Sai da sukayi Azhar sanan suka fito cin abinci, Hajiya ma ta fito tayi musu sannu da zuwa.
Suna cin abinci suna hirar asibiti, da yamma kuwa bayan anyi la’asar, Nafisa ta shige d’aki, number momynta ta danna, tana shiga momyn ta d’aga, tare da cewa “an sami kud’in?”
“Uhm momy mafita aka samu kinsan dai babu inda za’ayi ya barni in sake fita amman ki turo Salma zan sanar da ita komai dan ko yak’i ko yaso dole yayi min 6arin kud’i wallahi sai nayi rawa da tsalle duk a lokacin da naso”
Momy tayi farinciki tare da cewa “zatazo gobe da Rana insha Allah”
Daganan sukayi sallama…!
# LOVE
# ROMANTIC
# FUNNY
Domin magana da marubuciyar 08141799224
*🫦 TSAUTSAYIN TAUNA🫦*
*Zainab Habib (Mom Islam*
11-12
Washe gari, bayan sunyi breakfast, Alhji Kabir na shirin fita aiki, Nafisa ta tambayeshi zuwa gidansu k’awarta Salma,
Beyi mata musu ba, saboda yasan aminttakar dake tsakaninsu, k’arfe 10:am ya fito tafiya aiki, lokacin ita Kuma ta shirya suka fita tare.
Suna isa anguwar yayi parking a k’ofar gidansu Salma, ya mik’a mata 3k tare da ce mata karta jima ta koma gida.
Godiya tayi masa kana ta shiga gidan da sallama, wata dattijuwar mata ta samu zaune akan kujera tana gyaran shinkafa, bayan Nafisa ta gaisheta tace “Salma na nan kuwa?”
“Ai sun kwana biyu da tashi, babu wanda yasan anguwar da suka koma”.
Nafisa tayiwa matar godiya ta fito bakin titi ta tari napep zuwa anguwarsu wato anguwar Dosa, bayan mai napep ya sauketa ta bashi kudinsa,
Nocking tayi a bakin get din gidansu, mai gadi ya bud’e tare dayi mata sannu da zuwa, kai kawai ta gyad’a masa kana ta shige part d’in momynta, zazzaune ta samesu, momy da kanwarta Salma.
“Oyoyo anty Nafisa, dafa yau zanzo”
Nafisa tayi murmishi hadi da cire mayafi ta ajiye gefe, tace “momy wallahi na gaji”.
Momy dakeyin waya, sai yanzu ta ajiye wayar tace “ashe kina hanya, gara da Salma batajeba”
Nafisa tace “aikuwa dama na fito ne akan zuwa gidansu K’awata Salm, naje ashe sun tashi”.
Momy tace “subanallah ina suka koma?”.
“Ai babu labari momy”
Nafisa tace “momy kawo kunnenki”
Ni kaina bansan me ta rad’a mata ba, gani nayi kawai suna dariya,
Momy ta daga waya ta kira dadynsu Nafisa, ring d’aya ya d’aga tare da cewa “uwar gida sarautar gida”.
Kai tsaye momyn tace “Alhji inason zuwa anguwa”
Dadyn yace “to Allah ya dawo dake lafiya barinyi miki transfer”
Momy tace “to nagode Alhji Allah ya k’ara bud’i.
Momy ta kalli Nafisa, kana tace “tashi muje gidan Malama Saratu mai mallaka, Nafisa ta ta6e baki kana tace “momy ai ta farkon naji kamar ba wannan sunan bane”,
“Kee tashi maza wata aka samu nima tayimin aiki akan dadynku naji dad’i, shine nakeso kema ki gwada”
Salma ta zaro ido
“Momy kenan kin mallake dady kike nufi?”
“Ke dalla can, tunda Allah yayishi namiji meyayi saura, tashi kije kitchen ki Dora abinci mu fita zamuyi”.
Daga haka momy tashiga d’akinta ta d’auki ATM da mayafi, sai yar k’aramar Jakarta ta dawo parlo suka fito zuwa parking space.
Drivers suna ganinsu suka fara cewa tafiya ne Hajiya, momy ta daga musu hannu alamar a’a.
A ranta kuwa cewa take, nasan irin munafurci na gidannan wallahi muddin ba fitar mukayi muka shiga motar haya ba, sai anbi didigi.
Suna isa bakin titi suka tari napep zuwa anguwar Mu’azu, ana saukesu Nafisa ta biya kudin, momy tayi musu jagora zuwa gidan.
Da shigarsu sukayi sallama, sun sami mata sama da uku a zaune suna jira, zama sukayi suma har sai da mutanen suka gama shiga sannan su momy suka shiga.
Bayan sunyi sallama suka nemi guri suka zauna.
“Sannunku da zuwa”
Malama Saratu ta fad’a tana kallon Nafisa.
“Yauwa sannu ina kwana”
“Lafiya ya gida”
Nafisa ta amsa da lafiya.
Momy ta koro mata jawabi from A to Z kana ta kara da cewa “yatace dan Allah a taimakemu, wannan muguwar kishiyar tata tana wahalata, gashi ta janye hankalin uwar mijin a kanta, ni kaina kawatace Amma yanzu munsau hannun riga.
Saratu mai mallaka, tayi murmishi kana ta daga kasan wata kwarya ta dibo kullun bak’ar leda guda biyu, ta mikawa Nafisa tace “wannan matsi zaki dingayi dashi, daga lokacin daya kusanceki wallahi saiya yabawa aya zakinta, wannan Kuma shafawa zaki dingayi a fuskarki kullum safiya dazarar kin idar da sallahar asbha”.
Nafisa tasa hannu biyu ta karba tana godiya.
Momy tace “ai mutuminki bina yake sau da k’afa, harda yimin kyauta”
Malam Saratu tace “ai na fad’a miki abinda zai baki nan gaba ma zakisha mamaki, kedai kici gaba da gashi”.
Momy ta ajiye mata 20k tare da cewa, ki bani account number d’inki zanyi miki transfer kema kici albarkaci”.
Sukayi dariya a tare, momy da Salma sukayiwa Saratu sallama suka fito.
A napep wayar Nafisa tayi Kara, tana dubawa taga number Salma kanwarta, Nafisa ta kalli momy kana tace “Salma cefa mai Kira,
Momy tace “to d’aga mana”
Nafisa ta amsa, “anty dan Allah kicewa momy ta kar6ar min maganin farin jinin samari, Amma masu kud’i”.
Nafisa tayi tsaki hadi da cewa “dalla rufawa mutane baki taki matsalar karamace”.
Tana fadar haka ta kashe wayar.
“Menene naji kina fad’a?”
“Momy wai yarinyar nan saboda batada kunya take iya cemin wai in gaya miki ki kar6o mata maganin samari?”.
Nafisa ta k’arasa maganar mamaki ya gama kamata,
Momy tayi tsaki mtsw, wawuya shine wani abu, dame yan matan suke tak’ama yanzu ba sai sun had’a da gurin malamai ba?”.
Shidai mai napep nata dariya yana gaba.
Momy ta wuce gidansu, Nafisa ma ta wuce gidanta.
A gajiye Nafisa ta koma gida.
Washe gari.
Kamar inda malam Saratu mai mallaka ta gaya mata, ta shafa wannan magani bayan tayi sallar asbha, ta fito parlo.
Babu kowa a parlon sai ita kad’ai, abinda bata cikayi ba kenan wato fitowa da wuri,
Motsin bud’e k’ofa taji ta gyara zaman mayafinta, burinta Alhji Kabir na shigowa yayi tozali da idonta.
Cikin sa’a yayi sallama, ta amsa ta murmishi, ya d’auka ta zauna domin tayi masa surprise, sai yaji tace “barka da safiya Alhji”
Ya kasa dauke ido daga kanta, saboda fuskarta tana yi masa wani irin haske gami da kwarjini da dad’in kallo, da kyar yayi kiciniyar janye idonsa daga nata, kafin yace “barin karasa ciki”.
Sai daya wuce d’akin Hajiya mama suka gaisa sannan ya wuce d’akin da yake, wato d’akin Sajida.
Yana shiga ya sameta tana shafa powder, tasa doguwar riga irin y’ar kantinnan, ta dameta, cikin ya fito sosai yayi mata kyau, fuskarta ta mugun ramewa, duk Wanda yasan alamun mace ta kusa aihuwa ga yanayin da take kasancewa to a fannin Sajida ma haka ne, saboda fuskarta ta mugun ramewa sosai, hakan bai hana fito da ainihin kyawunta ba.
Hannun Alhji Kabir ta kama, kafin tace “barka da safiya baban twins”
Fuskarsa d’auke da murmishi yace “barka pretty”
“To…an sauyamin suna kenan?”
“Ked’in kyakkyawa ce, kobakiyi kwalliya ba”
Sajida tayi murmishi, kafin tace nagode Alhji”.
Sai daya gama kwantar mata da hankali kafin ya shirya cikin lallausan yadi na boyel baki, sai shek’i yakeyi, sanya wayarsa yayi a gaban aljihu kana ya k’arasa gareta ya shafi cikin tare da kai kunnensa gurin cikin yace “Wai banajin suna yimin bye²?” Sajida tayi murmishi, tace “muje kayi breakfast”
Suka fito tare, yana Kara yin arba da fuskar Nafisa, tunaninsa da kwakwalwarsa suka kusa kaucewa daga jikinsa, k’ok’arin control d’in kansa ya farayi, kar Hajiya da Sajida su fahimci wani abu, itako wacce tayi dominshi ta gano tarkonta ya kama.
Suna gama karyawa ya fice, batare daya Kara wasu tsawon lokuta ba.
After 7 days
Ranar Friday, Sajida ta shirya zuwa gidansu, dakyar Alhji Kabir ya amince zai kaita, da yace ta bari saita aihu, sai da Hajiya mama tasa baki sannan ya amince zai kaita inya dawo daga gurin aiki zai wuto gidansu ya dawo da ita gida.
Koda suka shiga mota suka fita daga gidan, a hankali yake tafiya da motar kamar wanda zaiyi parking a gefe, har suka iso gidan.
A tare suka shiga dashi ya gaishe da iyayen Sajida ya bata 3k ko zata buk’aci wani ,
Gidansu Sajida madai-daci ne, mahaifiyarta ita kad’ai ce, sunanta Hajiya Fatima tun auren saurayi da budurwa da sukayi da mahaifin Sajida har yanzu suna tare, yaranta biyar, Samir, Sajida dakuma Zainab da Lirwan
Samir shine babban yayansu, yana aiki a Gombe, yana harkar siyarda motoci da mashina, Sajida ce mai binsa sai Zainab da take karantar likita, sai Lirwan shine karaminsu, shekararsa biyar Zainab kuwa 17, yaran sun taso cikin gata ilimi da tsoron Allah ga taimakon duk wani mabukaci, mahaifinsu mai suna Alhji Halliru, yana kasuwanci ne a Kano yana siyarda kayan kitchen, shagunansa sunkai biyar, mutumne mai mutane ga kyauta uwa uba rikon addini.
Wannan kenan.
Part daya ne a gidan Wanda zamu iya Kiran gidan da muhadu a parlo, a ciki akwai dakuna, na Ammi dana Yaya Samir, dana Zainab dana Lirwan Dana baki, sai kitchen, kasancewar kowanne d’aki yanada toilet.
Babban parlon nasu kuwa, ya cika da kayan alatu na rayuwa, kama daga kan kayan kallo harzuwa kan su kujeru.
Sajida tayi sallama fuskarta d’auke da murmishi,
Ammi fara ce tass idan ka ganta kamar balarabiya, Amma Sajida bata d’auko haskenta ba, komai na mahaifinsu ta d’auko, Yaya Samir da Zainab ne sukayo farinta sai Lirwan da shima yakeda nashi hasken Amma bai kaisu ba.
Cikin fara’a Ammi ta taso tana mata lale, Sajida ta rungume Ammi da tulelen cikinta, tana cewa “Ammi ko nemana bakwayi ina Zainab?”
Ammi dai na fara’a tace “aikuwa muna nemanki, Zainab tana makaranta”.
Yakice mayafin jikinta tayi kana ta cire riga ya zamo iya d’aurin k’irji tayi, tace “Ammi zafi nakeji zan watsa ruwa”
Ammi tace “ai dole kiji zafi,shiga ki watsa ruwa”.
Tana tafiya, Ammi ta rik’e baki kafin tace “nadai San tanada ciki amma yaushe yayi girman haka?”
Tana tsaka da tunani Sajida ta dawo ta zauna, sai lokacin suka gaisa, Ammi tace “ashe da sai dai muji aihuwa kawai?”
Sajida tayi dariya, sai da Ammi ta tambayeta su Hajiya mama da Nafisa tace “mata duk suna lafiya”.
Sajida tace “Ammi albishirinki?”
Ammi na mayar mata da fara’ar tace “goro fari tass”
“Ammi da mukaje asibiti, scanning sukace yan biyu zan haifa”
Wani irin farinciki ne ya lullu6e Ammi abinda suka dade suna roko a gurin Allah, suka dade suna nema gashi har biyu Allah ya basu, Ammi tayi fatan alkairi tare da cewa “Allah ya nuna mana wannan rana”,
Sajida ta amsa da “Amin”.
Sai wajen yamma yaya Samir ya shigo, haka ma Zainab Lirwan dama yana nan, school d’insu k’arfe 1:pm ake tashi.
Sai da taci abincin dare kasancewar suna gamawa da wuri.
Sannan Alhji Kabir yazo suka tafi.
Suna isa gida anayin sallahar magriba, Hajiya da Nafisa na ganinta suka hau yi mata sannu da dawowa, Sajida na had’a ido da Nafisa taji wani irin sonta da tsoron 6ata mata rai ya shigeta,
Washe gari.
Sajida ta tashi da matsanancin ciwon baya da mara, a ranar cikinta ya cika wata Tara da kwana goma, sosai take rik’e baya da mara, Hajiya mama ta rikice, hatta Nafisan sai abin yaso bata tsoro, saboda bata ta6a ganin mai nakuda ba, a ranta kuwa cewa take “dama haka nakuda take? dama haka zafi da rad’ad’ints yake?”
Tayi saurin cewa “idan na bari tausayi ya shigeni, tabbas bazan aiwatar da abinda nake buri ba”.
“Akira driver”
Muryar Hajiya mama ta qwqdoki dodon kunnenta, da sauri Nafisa fice tayiwa driver magana Alhji Kabir na dawowa daga masallaci, bai jira driver ba, a gigice yayiwa motar key suka bar anguwar, kai tsaye asibitin Giwa hospital suka nufa, suna isa aka wuce da ita d’akin aihuwa,
Likitoci biyu ne a kanta, kasancewar dakunan kamar ciki da parlo ne, Kuma duk masu aihuwa ne a ciki, dukkansu babu wacce take cikin haiyyacinta, sakamakon allurar bacci da kowwacce ta samu,
Cikin hukunci da izza ta ubangiji Sajida ta haifi y’ay’anta guda biyu, namiji da mace, tana aihuwa akayi mata allurar bacci mai nauyi sosai, ko kallon yaran batayi ba baccin ya d’auketa.
Doctors na aiki Nafisa ta kira waya,
Rakube take a hanyar toilet na hospital d’in, a zahiri tace wa su Hajiya mama zatayi fitsari ne, nan ko ba haka bane,
“An kammala komai?”
Likitan ya takice zufar data karyo masa kana yace “da saura”
Ta katse kiran itama gumi na sunturi a fuskarta.
Saida suka d’auki tsawon awanni, kafin suka fito, fuskarsu d’auke da takunkumi, kallon Alhji Kabir sukayi cikin yanayi na ban tausayi kana sukace,
“Alhaji sai dai hak’uri, yaran da aka Haifa daya ta koma namijin yana nan”
Hajiya mama tahau yiwa Alhji nasiha tana cewa “ka fauwalawa Allah komai, yafika sonsa dan haka ka gode masa da baiwar da yayi maka”
Ya rigada ya dorawa yaran buri, hawaye ya zubo a fuskarsa ya share tare da cewa Alhmdulilh”
Nafisa tahau borin kunya tana cewa “Ina Wanda yake nan din zamu iya zuwa ganinsa?”
“Yes zaku iya zuwa”
Suka shiga dukkansu, sun samu ankai Sajida d’akin hutu, yaron yasha kayan sanyi sai neman nono take yana tura yatsunsa biyu baki.
Hajiya mama tace “Masha Allah kaga yaro ya d’ibo kamar gidan babanshi”
Ran Nafisa ya fara 6aci, bataso aka rage wannan yaron ba, taso a had’a dashi koma inane a kaishi, sai likitocin suka nunar mata da asirinsu zai tonu,
Alhji Kabir yayiwa yaron adu’a sannan ya tofa masa, Nafisa kuwa sai uban rawar k’afa wanda, su kansu babu wanda ya gane abinda ke faruwa.
Sai wajen k’arfe 12:pm sannan Sajida ta farka, bakinta d’auke da sunan Allah, likitar dake kanta tayi mata sannu tare da turota d’akin da yaron yake, ana kaita idonta yakai kan yaron, “ina dayar?”
Abinda bakinta ya furta kenan a karo na farko data shigo d’akin.
“Tana bacci shi ya tashi ne”
Hajiya mama ta fad’a tana kallon Sajidar,
Sai wajen k’arfe d’aya na rana sukabar asibitin, tare da gawar jaririya wacce ba tasu ba, suna zuwa gida akayi mata wanka da sutura da duk wasu abubuwan da suka wajabta aka binneta.
Tunda suka dawo gida, mutane suketa sintiri, Zainab k’anwar Sajida ma ta dawo gidan, a cewarta kwana uku zatayi, abubuwan data lura dasu da yawa a gidan, komai za’ayi na dangane da mai jego, sai dai Sajida tace a kirawo Nafisa sai abinda tace, idan akaje gurin Hajiya mama itama hakanne, idan Alhjin nema shima sai abinda Nafisa tace shi akeyi.
*🫦 TSAUTSAYIN TAUNA🫦*
*Zainab Habib (Mom Islam*
Page 13-14
Wannan abu ba k’aramin yiwa Nafisa dad’i yakeyi ba, anyi suna na gani na fad’a, inda yaron yaci sunan Mubarak,
Y’an uwan Ammi sun tambayi wankan gida, Hajiya mama tace “meye amfanin zamanta a gidan?”, dole suka hak’ura suka bar Sajida.
Bayan suna Nafisa na zaune a d’aki tana latsa waya, da misalin k’arfe 4:pm, kiran doctor ne ya shigo wayarta, da sauri ta sauke numfashi tare da gyara zama, tana nazarin magana ko Kuma amsar da zata bashi, dan zancen tasan baya wuce na kud’i.
Kara wayar tayi a kunnenta da sallama.
“Hajiya mun cika aikinki kamar inda kika buk’ata, zamu turo da account number ne?”.
“Eh…eh kuturo zuwa gobe da safe zakaji alert, Amma bakuyimin inda nakeso ba, saboda wannan magajinsa kuka bari”,
Ta katse kiran.
Iska ta furzar mai zafi, had’i da buga k’afa,
Zuwa dare, Alhji Kabir yana d’akinta, kasancewar tunda Sajida ta aihu ya dawo d’akinta, k’arfe 8:20pm ya dawo daga gurin aiki, bayan yayi wanka yaci abinci, yana shirin janyo laptop d’insa ya duba, ta ratayo hannunta a wuyansa, muryarsa k’asa-k’asa yace “Hajiya Feenat ya akayi?”,
“Uhm Alhji, wata matsala ce ta afku da K’awata Salma, y’an garkuwa da mutane sun kamata, gashi basu da isashen kudi, shine hankalina ya kasa kwanciya”, tana kaiwa nan ta manne a jikinsa tare da fashewa da kuka.
“Is okay my wife, don worry, zan taimaka musu insha Allah, ammafa saboda ke”
Yaja kumatunta, kana yace “kamar nawa kikeso a basu?”
“200k ma yayi wallhi sunce zasu kasheta”
Alhji Kabir ya zaro ido, kana yace “sunyi yawa Ina lefin 50k?”
Kuka Nafisa tasa tare da k’ara k’amk’ameshi, tana cewa “kayi taimako inhar kana Sona”.
Suna had’a ido da ita, yaga tayi masa wani irin kwarjini, da sauri yace “zan turo gobe bani account number” jikinta na rawa tace “turamin a nawa inyaso sai inyi musu transfer”
“No, banaso kisa kanki cikin matsala”
Kuma marairaice masa tayi, dole ya yarda zeyi mata ta account d’inta.
Washe gari, bayan anyi sallahr asbha, kowa ya koma bacci banda Nafisa da hankalinta ke tashe, saboda a tsorace take, kar doctor ya kirata, tasan inhar ya kira Alhji Kabir saiya tambayi waye?.
Har gari ya waye tana zaune tana karanta wasik’ar jaki.
K’arfe 9:am Alhji Kabir ya tashi daga bacci yayi wanka, ya shirya cikin k’ananun kaya, sai da yayi mata transfer sannan suka fito a tare, ita ko wankan bata samu tayi ba, kamar inda tasabayi kullum, amma duk da hakan babu wani datti a tare da ita.
Suna isowa parlo babu kowa sai breakfast da aka jere a dinning, d’akin Hajiya mama Nafisa taje, ta gaisheta kana ta wuce d’akin Sajida, tana shiga ta sameta a zaune a kan gado tanacin farfesun kaji, hannunta rik’e da jariri, wani uban kishi da tsanar yaron ne ya lullu6e mata zuciya, dakyar ta yakice ta aro murmishi ta yafa a fuskarta kafin ta zauna tace “barka da safiya anty Sajida dafatan big boy ya tashi lafiya”
Sajida ta mik’a mata yaron, tana cewa “aikuwa gashinan lafiya lau sai tsotso da yayi masa yawa”,
“Kai karfa ka k’arar min da aunty kaji”
Nafisa ta fad’a tana dariyar da iya kacinta fuskarta.
Fitowa tayi da yaron ta kawoshi d’akin Hajiya mama, tana cewa “gashinan kunyi kama sak Hajiya mama”
Hajiya mama tayi dariya kafin tace “lallai wannan y’a, Ina kamar take?”
Nafisa na dariya ta mik’a mata shi ta fice,
Koda ta isa parlo ta samu Alhji Kabir harya fara Shan tea, ta k’arasa tana jifansa da murmishi mai kyau, Wanda ya lullu6e makircin datake shirin k’ullawa.
“Alhji farfesu za’a zubo maka ko yam balls?”
“Zubomin farfesun sauri nakeyi”
Bayan ya kammala ta rakashi, parking space ya shiga mota ya wuce gurin aiki.
Yana mota yana ganin transfer din da yayiwa Nafisa kamar a mafarki, dan kansa har wani sarawa yakeyi, koda ya k’arasa gurin aikin ba wani abun kirki yayi ba.
Alhji Kabir na ficewa, Nafisa tayiwa doctor transfer hankalinta kwance.
After one week da faruwar hakan.
Gidansu Ammin Sajida.
Tunda Zainab ta dawo ta tayarwa da Ammi hankali, sosai Ammi ta shiga damuwa, saboda ce mata tayi “an mayar da anty Sajida kamar gunki, bata da zabin kanta sai Wanda anty Nafisa ta za6a mata”
Ammi cikin sanyin jiki tace “da izinin ubangiji, inma sharri take nema, Allah bazai bata ikon yin galaba a gurin Sajida ba, narasa meyasa wasu matan suke kishin jahilci wallahi.
“Hmm Ammi, bakiga wainar da ake toyawa bane a gidan”
Zainab ta fad’a tana kallon Ammi.
Badan Ammin nason cigaba da saurarar zancen nata ba tace “ya isa haka, shiga kitchen ki d’ora mana abinci”
Zainab ta wuce kitchen zuciyarta babu dad’i, cike da tunanin halin da y’ar uwarta take ciki.
Gidan Alhji Kabir.
Washe gari, hankalin Nafisa ya kwanta, sai dai ba anan gizo ke sakar ba, an kashe maciji ba’a sare kansa ba, tana zaune gaban mudubi, lokacin k’arfe 12:3pm, tana duba wasu takardu, tana sanye da atamfa d’inkin riga da skirt, sunyi mata kyau, rurin neman agaji wayarta ta shigayi, a hankali tajanyo wayar tana duba sunan mai kiran “Doctor”
Ta fad’a cikin zaro ido.
“Mekuma yakeso dani?”
Sai da aka kuma Kira a karo na biyu sannan ta d’aga murya k’asa-k’asa tace “barka doctor ya akayi?”,
“Am madam, munga sako mun gode, tofa ina tunanin kin mance da babyn ko?, tana raye fa, munbawa mai shayarwa ta dinga shayar da ita, dalilin da yasa na kiraki shine, mai shayarwar yau zatayi tafiya zuwa garinsu Niger, shine nace bari in sanar dake”.
“Innalilahi wa inna ilaihir raji’un, meyasa baku kasheta ba? meyasa kuka barta da ranta? sokuke asirina ya tonu?”.
Doctor yace “haba madam, kamar kin mance, munyi dake babu maganar kisa, Ina had’a kowanne irin makirci Amma bana kusa!.”
Cikin in’ina wacce batasan tanada ita ba tace “to….to..zan…zo asi..asibitin anjima”.
Hankale a tashe ta mik’e tare da Zagaye d’akin, tana kaiwa tana komowa, kamar me neman wani abu.
Lokaci d’aya ta tsaya cak, “ina zankai wannan shegiyar yarinyar?”
Ni har na baje k’afa akan komai ya kammala”,
Wayarta ta d’aga ta danna number momynta, kamar jira momyn take, ta amsa kiran,
Cikin tashin hankali tace “momy shikenan an yanka ta tashi, momy asirinmu zai tonu, yarinyar dai tana raye, momy kaina ya kulle, momy ki taimakeni momy zan haukace”,
Ta k’arasa maganar tana fashewa da kuka.
“Haba Nafisat..,kamar bana numfashi a doron kasa, inhar kikaga kin wulakanta to tabbas na mutu ne, koda na mutu ma bana fata inganki a hakan dan saina tabbatar da kafuwarku ta har abada a gidan mazajenku”
Momy ta fad’a tana lallashinta.
“To momy meye mafita? doctor yace muje mu d’auko yarinya”,
“Karki damu, kice masa yayi hak’uri zuwa gobe sai muzo”
Nafisa ta waro ido tare da cewa “momy yau me rainonta zataje garinsu fa”
Momy tace “au kin damu da rayuwarta kenan? idan zataje garinsu saita dawo ki kyaleta wata kila yunwa ma ta kasheta kafin goben”.
Cikin amincewa da zancen momy, Nafisa tace “to Allah ya kaimu”.
A 6angaren momy kuwa, suna gama waya da Nafisa ta kira wata mata mai suna Ladi, cikin mintuna kalilan matar ta iso, tana zuwa bayan an kawo mata kayan motsa baki, taci momy tace “dalilin da yasa na kiraki shine, wata jaririyace mukeson baki ki riketa inhar kinaso?”.
Jikin matar na rawa tace “inaso kai, sanin kanki ne Hajiya Sakina ban ta6a aihuwaba”
Momy tayi murmishi kana tace “to shifa mai gidanku?”
“Shima bashi da matsala ko kad’an”
Matar ta fad’a tana share hawaye,
“Yauwa, wannan ya zamo sirri tsakanina dake, ko zuwa gaba karki alak’anta yarinyar da gidannan,inhar kin amince gobe insha Allah sai muje ki kar6eta”.
Ladi tace “haba Hajiya, nemafa mukeyi ruwa a jallo gashi Allah ya bamu”.
Washe gari, da Nafisa da momy da ita Ladin, sukaje hospital suka d’auko yarinyar, Ladin ta wuce da ita gida, daganan suka rabu.
Da sallama ta shigo gidan nasu fuskarta d’auke da fara’a, malam Haladu na ganinta ya washe baki, kana yace “kamar goyo naga kinyi?, a ina kika samo yaran mutane da almuru?”
“Ah ai malam damuwa mukayi muje daga d’aki, in fed’e maka biri har wutsiya”,
Malam Haladu yace “barinyi magariba tukunna, tunda zancen na zama ne.
Sai da yaje yayi sallah sannan ya dawo, ya shigo d’akin Ladin da sallama, lokacin tana bawa yarinyar ruwan d’umi a kofi, amsawa tayi tare da d’agowa ta kallesa kafin tace “yarinya aka bani, ta kwashe labarin komai ta sanar masa, da yake shima d’in yanason aihuwa amma Allah bai basu ba, yasa ko d’arr beji ba gurin amsar jaririyar, ya kar6eta yayi mata hud’uba da Aisha,
Suna kula da ita iyakar k’arfinsu, duk da ba kullum ake dora tukunya a gidan ba, wataran idan Ladi ta isheshi da masifa, yaje waje yayi kuka ya share, saboda gari babu aiki, dama wani lokacin inya mashinne, kokuma leburanci yakeyi, to yanzu komai ya tsaya cak, y’ar madarar da suke samu su siya mata yanzu ta kara kud’i, da suna siya nera hamsin, yanzu kuwa ta koma saba’in, sosai malam Haladu yake shiga damuwa akan rashin abincin da zasu bawa yarinyar, wani lokacin ya gwammace su zauna da yunwa akan yarinyar tayi ta damunsu da kuka.
Tun daga lokacin mutane sunyi rad’e rad’insu sun gama, ko an tambayi Ladi Ina kika samo yarinya sai tace “ya yarinyar kanwatace, data rasu ta barta shine na d’aukota, ba y’an uwane da Ladin a garin ba, bare su tambaya suji gaskiyar magana, dole suka bar zancen a hakan.
GIDAN HAJIYA SAKINA.
Tun bayan tafiyar, Ladi daga gidansu, momy da Nafisa suka dawo gida.
Nafisa tace “alhmdulilh momy naji dad’i, gaskiya duk Wanda ya rasa uwa to yayi kuka”
Momy tayi murmishi kafin ta shafa kan Nafisa, dake danne² a waya tace “ke y’arnan akwai ragowar aiki a gabanmu, saboda karfa azo wannan likitan ya tona mana asiri, inaso a sake mallake miki Alhji Kabir, saboda inajin gaba, koda komai zai faru bazai ce uffan ba, sai dai ya zuba miki ido sai inda kikayi da lamarin”.
Momy ta k’arashe maganar tana yin makirin murmishi.
“Yauwa momyna haka nakeso wallahi kamar kinsan nafara tunanin hakan, kizo gobe insha Allah muje gurin Saratu mai mallaka”
Nafisa ta tashi zaune, kana tace “momy kinsanfa zai iya cewa fitarnan tayi yawa, ba lallai a satinnan ya barni in sake fitowa ba”,
“Okay to duk inda mukayi da ita zan Aiko Salma saita kawo miki”,
“Nafisa tasa mayafinta tare da cewa “momy akwai wata humra da kika ta6a bani, wallahi tanada kyau, kinga inda Alhji yake kallonta kuwa?”
Momy tayi dariya, kana tace “wato Nafisa yanzu kin dena jin kunyata ma ko?”
Dariya Nafisa tayi tana cewa “momy dan Allah idan akwai ki bani zan tafi”
Suka shiga bedroom d’in momyn tare, momy ta bud’e mata wani akwati, d’an k’aramin mai d’auke da turaruka iri-iri, Kuma ko wanne da amfaninsa,
“Wanne kikeso?”
Nafisa na dariya tace “ai momy ko wanne tsiyayamin za’ayi”
Dariya momyn tayi mata kana tace “aikuwa sai dai ki za6i guda biyu, saboda wad’anan akwai wanda ban gama biyan kudinsu ba”.
Dole badan tasoba ta zabi biyun, momy ta zuba mata a kwalba, sai da tayi sallahar la’asar sanan ta koma gida.
Tana isa ta shiga da sallama, turuss tayi ganin k’awarta Salma a parlo, mamaki da matsanancin tsoro ya kamata, a sukwane ta k’arasa ta lullu6e tsoron dake barazanar karyar mata da zuciya, ta washe hakora tana cewa “oyoyo Salma yaushe kikazo?”
Hajiya mama da Sajida sukayi murmishi, Hajiya mama tace “tun bayan da akayi sallahar Azhar ta shigo, munyita gwada lambarki tak’i shiga”,
Nafisa ta zauna tare da cewa “wallahi na mance tun jiya bansa waya a chaji ba, Ina zuwa gidanmu na tuna, shine na kashe wayar saboda tayi saurin cika”
Salma tace “oh Nafisa ko cigiyarmu babu?”
Nafisa nata fakar idonsu, Hajiya mama da Sajida tanayi mata k’ifce, akan tayi shiru, Amma Salma bata ganeba.
Bayan shiru daya biyo baya, Hajiya mama ta fara tashi ta shige d’aki, daga can d’akin Sajida, ita Kuma wayarta tayi ringing, hakan ya basu damar tafiya d’akin Nafisa domin su tattauna, hakan yayiwa Nafisa dad’i sosai.
Bayan shigarsu d’aki, Nafisa tace “mekikeso a dafa miki?”
“No.. Ina sauka aka cikamin gabana da abinci, a halin yanzu na k’oshi”.
Ajiyar zuciya Nafisa ta sauke, kana ta yiwa k’ofar key, kafin ta dawo kusa da Salma ta zauna,
“Naje gidanku ancemin kun tashi?”
“Eh hakane, wallahi mugun mutumin Wanda muke hayar gidanne ya matsa mana”
Nafisa tace “to Ina kuka koma?”
“Badarawa”
Salma taba Nafisa amsa.
“Yauwa yanzu dai turomin account number d’inki”
Jikin Salma na rawa ta turawa Nafisa, kana tace “Wai kud’i zaki turamin?”
“Yes”
Nafisa ta bata amsa, wow dama jiya garin kwaki mukaci muka kwanta, gashi yauma sai da Umma taci bashi”,
Nafisa tayi murmishi kana tace “karki damu nayi miki transfer na 50k please babu yawa, Amma kafin nan akwai abinda nakeso dake,
Suna cikin magana alert d’in ya shigo, Salma ta daka tsalle tare da cewa “gaskiya kawar arzik’i samun kamarku sai an tona”
A hankali Nafisa tace “Salma koda Alhji ya kiraki yace miki ya mukaji da abinda ya faru, kiyi masa godiya kamar zaki ari baki, kice masa kin gode da taimakonki da yayi, akan in taimaka miki ne yasa na kar6i wannan kudin a hannunsa, ashema kina hanya, kima kirashi yanzu kokuma bari in Kira miki shi a wayata”,
Nafisa ta danna number Alhji Kabir, Ring daya zuwa biyu ya d’aga, Hajiya Feenat ya gida ya kike?”
“Lafiya Lau Alhji ga Salma Allah ya fito da ita, zatayi maka godiya akan taimakonta da kayi”
“Laa ai babu komai Hajiya Feenat yiwa Kaine”
Nafisa ta mik’awa Salma wayar,
Bayan sun gaisa Salma tace “Alhji nagode da taimakona da kayi, ubangiji ya tsare gabanka da bayanka, Allah ya kareka daga dukkan sharri mungode, ta k’ara da cewa “Umma ma tanayi maka godiya kafin tazo”.
Yaji dad’in adu’ar Sosai shima yace “ya gode” sukayi sallama da Nafisa ta ajiye wayar

Leave a Comment