Books Reviews & FAQs

Uwa Uwa Ce Hausa Novel Complete

UWA UWACE…

Bismillahir Rahmanir Rahim

Batul Mamman

SANARWA: Ina mai bawa masu jiran wannan littafi hakuri game da canjin da zaku gani a tare da labarin. Wasu dalilai sun sa na canja tsarin labarin sabanin yadda na fara shafin farko watannin baya. Allah Yasa mu amfana da darussan ciki Ya yafe min kurakuran da ajizancin dan Adam ba zai barni na tsallakesu ba. Amin

 

Shimfida

 

KIRIKASAMMA, JIGAWA
1983

Nishi take mai kama da gurnani saboda tsananin ciwon da take ji. Ko da wasa bata taba tsammanin ciwon nakudar da mata ke yawan fada ya kai haka ba. Mace ta kasa gane a wace duniyar take. Idan ba ta kama bakinta ba sai dai ka ji tana sumbatun da basu da kan gado. Addu’a kuwa bata san nawa ta kama ta saki kafin ta kai karshe ba. Yau Kulhuwallahu, Falaki da Nasin da ko cikin bacci basu bace mata ta kasa kai karshen ko daya. Sai ta karanta ayoyi biyu a nan ta kama wata. Halilala ma da kyar take cijewa ta kai karshe. Iska take furzarwa akai-akai ta baki ta hanci. Ashe shi yasa Malamin makarantar darensu ya ce duk wadda ta rasa rayuwarta wurin haihuwa tayi shahada. Ladanta daya da wanda ya rasu a wurin yaki. Mahaifiyarta ce ta fado mata a rai a wannan yanayin.

“Allah Ya jikanki Inna. Inna idan na yi miki laifi ki yafeni. Innata bani da kamarki duk fadin duniya.” Ciwo na tasowa ta ce “Inna ki ceceni.”

“Allah dai Ya ceceki Mari kada ki yi sabo mana.”

Ba da niyya ba ta kalli idanun surukarta Inna Mairo cikin radadin ciwo ta ce “kin san irin ciwon da nake ji ne Inna Mairo? Nan…” ta nuna mararta “…ne yake rabewa gida biyu. Yanzu kema a haka ki ka haifo Inuwa?”

Dan murmushi Inna Mairo tayi saboda sanin cewa Mari ba a hayyacinta take ba. Ita da ta sha wannan wahalar sau goma sha uku sai dai ta bada labari.

Wani irin ciwo ne ya damki mara da bayan Mari ta kai hannu ta cafko hannun Inna Mairo. Gani take kamar ba za ta tashi ba saboda azabar ciwo.

Harira unguwae zoman ta sake danna gefe da gefen cikin sannan ta kuma lekawa. Kai ya taho amma da alama hanyar tayi masa kadan. Sabuwar rezarta ta dauko ta ce da Inna Mairo ta matso kusa da tochilan ta haska mata da kyau. Acibalbal din da aka kunna bata da hasken da zai wadaceta tayi abin da ya kamata.

Mari ciwo bai barta taga abin da ake shirin yi mata ba. Harira ta saka tochilan din a cikin dankwalinta ita kuma Inna Mairo ta rike hannuwan Mari. Rezar ta dan kara a jikin wutar acibalbal din ta dauke ta danna kowane gefe a jikin zaninta. Ji ka ke kit-kit ta kara Mari ta hagu da dama. Wannan izaya bata da kalmar kwatance. A kan ce mata basu ganewa idan an karasu saboda ciwon nakuda amma Mari kam taji komai.

Budar bakinta za ta yi ihu wani nannauyan nishi ya taso mata. Da dan sauran kuzarin da ya rage mata ta cije baki tayi nishin. Hamdala Harira tayi tare da karfafa mata gwiwa akan ta kara wani domin ga kan jariri nan ya kara turowa gaba. Ta daddage tayi kuwa sai ji tayi an canyara kuka irin na sabbin haihuwa bakin duniya. A take ta nemi wannan azababben ciwo ta rasa sai son ganin abinda ta haifa.

“Sannu Mari. Sannu da kokari. Allah Ya raya shi Ya baki lafiyar shayarwa.” Inna Mairo ta furta tana share mata gumi.

Kunya taji ta lullubeta da ta tuna cewa ba don dan ya fito ba sakon tsinuwa da Allah Ya isa ta shirya bata domin ta isar ga Inusa maigidanta.

Harira ta nade jinjirin a zani ta mikowa Inna Mairo. Da saurinta ta mika hannu za ta amshe shi hannun ya yi ‘yar kara. Fuskar Mari wadda ta dago kai tana son satar kallon dan nata ta kalla tayi murmushi ganin Marin ta kawar da kai gefe.

“Da dai korafin karya min hannu zan miki amma na fasa. Dauke shi ku ji dumin juna kafin na dawo.”

Da hannu Mari ta rufe fuskarta mai dauke da murmushin da ya gagara buya. A hankali ta bawa Inna Mairo hakurin rikon da tayi mata wanda da alama ya janyo mata rauni. Wani murmushin ta sake yi mata sannan ta tashi domin dora ruwan wanka tana murza hannun da take jin ya yi mata nauyi. Tana tausayin matar dan nata saboda ta tashi marainiya mara gata a wurin danginta. Shi yasa bata yarda an tafi da ita wankan jego ba lokacin da matar kawunta ta matsa akan hakan.

Harira ma fita tayi aka bar Mari da jaririnta. Sai da ta tabbatar babu sawunsu a kusa ta matso dashi kirjinta ta rungume. Hannunta yana dan rawa ta bude fuskarsa da kyau. Hawaye taji ya ciko idanunta saboda kaunarsa da ta shigeta farat daya. Bata jin za ta iya hada shi da kowa sai dai idan a gaba ta sake haihuwa. Tunanin kadai sai da yasa tsigar jikinta tashi da ta tuna halin da take ciki mintuna kadan da suka wuce. Addu’a tayi masa ta neman tsari da kariya tare da albarkar rayuwa. Kafin a fara shigowa dakin har ta gama kissima rayuwarsa har aure. Burinta ya zama da nagari abin kwatance. Ya yi ilimi mai zurfi irin wanda taga ana yi a birni lokacin da take aikatau kafin tayi aure. Idan so samu ne ma ya zama babban likita ko lauya.

“Dinkin nan zan zo in cigaba in tara kudin siya maka duk abin da za a nema a makaranta na karatun.”

Ta fada masa kamar yana fahimta. Guda ta jiyo ta tabbata yanzu duka matan gidan sun sami labarin haihuwarta. Yanzu dakin zai cika duk da asuba ce da matan ‘yan uwan mijinta da sauran kannensu da basu yi aure ba. Ajiye jaririn tayi da sauri kar a ganshi a hannunta a kirata mara kunya. Can kasa kamar mai yi masa rada tayi magana tana murmushin tsananin farinciki da jindadi.

“Bi’izinillahi sai kayi arabi da boko. Kayi sauka sannan kayi digirin digirgir irin na dan Hajiyar da na yiwa aiki.”

Rana na soma fitowa ruwan wanka ya yi zafi. Matar kanin Malam wato kawu ga mijinta Inuwa ce ta zaga bayan gida da ita inda za’ayi mata wanka. Jaririn kuma saboda hannun Inna Mairo da alama ya sami gocewa ko targade sai matar wan Inusa ce tayi masa wanka. Tana murnar rabuwa da ciwon haihuwa ashe akwai wani a gaba. Ruwan wankan da zafi sosai ake yarba mata darbejiyar da take ciki. Tun tana daurewa har ta hada da ihu. Ciki da baya sun sha matsa da dannawa. Bayan an gama wankan ta miko mata wani kwabi da kyallen kunguzu. Kallon kwabin da yafi kama da lalle tayi ta tamutsa fuska.

“Me zan yi dashi Gwaggo?”

Idan bata yi da gaske ba take taken Mari ba za ta saka ba saboda haka ta amshe ta ce yaba mata da kanta. Lalle ne aka kwaba da kauri da wani garin magani aka cusa mata. Mari sai gumi kawai take yi na wahala da ciwo. Bayan an gama sakawa kuma aka toshe wurin da kyallen kunzugu sannan aka bata zani ta daura.

Tare suka fito tana taku da kyar zuwa daki. A haka aka ce ta shayar da jaririn bayan ko zaman kirki ta kasa. Haka aka cigaba da yi mata kwabin lallen nan na tsahon kwana shida sai ta nemi tsagar wurin karin ta rasa. Ciwo ya hade tsaf ya warke (don Allah kada wacce ta gwada).

Ranar suna jariri yaci sunan kakansa Auwalu aka yi masa lakabi da Abbati.

***

DALA, KANO
1985

Kukan ya ishe shi. Idan ya bari suka kara minti biyar a dakin yana da tabbacin zai sami tabin hankali. Bai so Innayo ta karbi girki daga yin arba’in ba. Jiya ma haka suka kwana jaririyarta Hasiya tana ta canyara kuka. A fusace yasa kafa ya haureta tana baccin da ana gani za’a gane cewa a gajiye take likis. Da yake muryar Hasiyan ba karfi gareta ba shi yasa bata ji kukan da ta shafe mintuna tana yi ba.

“Dalla can malama tashi ki dauki ‘yarki.”

Bugun ya shigeta sai dai kukan da ta ji ya dauke zafin dukan. Hannu ta kai da sauri ta lalubi ‘yarta cikin hasken farin watan da ya ratso ta tagar dakin. Rarrashinta tayi nata idanun suna yi mata yajin bacci ta soma shayar da ita. Jin yarinyar tana ta ajiyar zuciya yasa ta jin babu dadi a ranta. Maganin mura ta sha ya saka mata nannauyan bacci ga kuma gajiyar aikin da tayi.

“Baiwar Allah kin dade kina kukan nan da alama ban ji ba. Ayi hakuri” ta kare maganar tana shafa mata kai.

“Mtsew” Alh Rabi’u ya buga tsaki.

A cikin duhun dakin ya tashi ya lalubo wandon kayan da ya dawo dasu daga kasuwa ya saka hannu a aljihu. Sautin sulalla na karo da juna Innayo taji ta kalli bangaren da yake tsaye.

“Alhaji idan wani abu kake nema bari ta gama na kunna maka fitilar kwan. A duhun nan ba ganin…”

Kasa karasawa tayi ganin ya nufota. Duk da ba ganin fuskarsa take yi ba amma ta fahimci ransa a bace yake. Hannunta ya kama ya zube mata sulallan da bata san ko nawa bane.

Da kakkausar murya ya yi mata magana cikin fushi.
“Gashi nan na saya sai ki tashi ki koma dakinki.”

Sam bata fahimce shi ba.
“Me ka saya?”

Daurewa ya yi saboda dare ya raba ya bata amsa ba tare da ya kara daga sautin muryarsa ba.

“Kwananki na saya Innayo! Ki dauki ‘yarki ku koma dakinki. Zan dinga biyanki daga yau har ki kara wata arba’in din.”

Hankali a tashi ta fara tambayarsa laifin da tayi masa. Lokacin kuma Hasiya ta zabi ta sake bare baki tana kuka. Kan Innayo har wani sarawa yake saboda rashin isasshen bacci da gajiya. Wuni take a gaban murhu ga fama da yara. Biyar nata har jaririyarta ga kuma hudu na matarsa ta farko da ya saka shekara biyu da suka wuce.

A yanzu su biyu ne a wurin maigidan nasu Alh Rabi’u kuma ita ce matsayin uwargida. Amaryar tasa Asabe ma ta dan kwana biyu tunda haihuwarta biyu yanzu. Iyakarsu da shi ya aunawa maigirki hatsi ga icce jingim a gidan. Sauran abin da za’a hada da hatsin a tayar da abinci kuwa sai dai mace ta nema. Asabe ko wata bata cika ba ta fitittike ta nemi ya raba musu girki. Kowacce tayi nata. Wadda miji ke hannunta ranar tayi da shi. Ita da ta zo cin arziki gani tayi sadakinta ma idan bata yi wasa ba a cefanen ciyar da ‘ya’yan koshiyoyi zai kare. Haka kuwa akayi. Ya amince ya raba ya bar masu ‘ya’ya da wahala. Bayan rabuwarsa da uwargidan taki daukar ko guda cikin ‘ya’yanta. Har yau basu san me ya hadasu ba amma ko tantama laifin ba zai wuce nasa ba. Mahaifiyarsa ya kaiwa yaran da fari yayansa ya ce bai isa ba. Ga tsufa da tayi ga sanin halinsa na son banza. Jibge mata su zai yi sai an ganshi. A dole ya dawo dasu gidan ya rabawa matansa. Asabe tayi tsalle ta dire a gaban yaran ta ce ba za ta dauki ko daya ba. Tausayi suka bawa Innayo ana rabonsu a tsakar gida kamar ba mutane ba ta karba ta hada da nata. Zancen irin wahalar da take sha wurin ciyar dasu ma bai taso ba.

“Nufinka bani da girki har sai mun kara wasu kwanaki arba’in din?” Ta tambaye shi da mamaki.

“Ashe kin fahimta ki ke wani neman ba’asi.” Shimfidar Hasiya ya tattaro mata “tashi ki tafi bacci ne a idona. Kuma ki kwantar da hankalinki ba wai Asabe zan baiwa kwanakin naki ba. Kukan nan ne kawai ba zan jura ba.”

Maganganunsa sun bata mata rai amma ta daure taki bashi amsar da za ta sa taji sauki a zuciyarta. Tashi tayi jiki ba kwari ta fice ya kada kai a wurin ya kwanta.

Kamar kullum washe-gari karfe bakwai a bakin murhu tayi mata da goyon Hasiya. Da safe ‘yar tsala take sayarwa da kuli-kuli. Da rana kuma dambu. Daidai lokacin tasowar yara daga islamiyya kuma tayi danmalele. Don ciniki kam sai dai tayi hamdala. Kudin ne dai duk yawansu basa isarta. Yara tara ne a gabanta da ita kanta cikon ta goma. Ga kudin laraba ga sayen abinda ba a rasa ba na boko.

Ta sallami yaron karshe da bokiti cike da ‘yar tsala da zai kai kasuwa taga fitowar Asabe daga dakin Alh Rabi’u da danta a hannu. Suna hada ido ta gatsina fuska gami da murguda mata baki ta shige dakinta. Bata bi ta kanta ba ta sauke tandar ta dora ruwan wanka. Yaran gidan duka sun tafi makaranta sai wadda ta yaye tana bacci a daki.

Alh Rabi’u ta gani ya fito cikin shirin tafiya kasuwa. Dauke kai tayi kamar ba za ta yi masa magana ba saboda haushin abin da ya yi mata, sai kuma dai ta daure ta ce,

“Sannu Alhaji.”

Da yake ba shi da gaskiya sai ya hau sababin borin kunya.
“Na dai biyaki kin kuma cake kudin bare ki ce an ci amanarki.”

Zama tayi akan tabarma ta kwanto goyonta kafin tayi magana cikin rashin jindadi.
“Wani abin kaji na ce?”

Hannuwan babbar rigarsa ya nade fuskar nan tasa a hade. Bai so haduwarsu ba shi yasa ya zauna a daki niyarsa sai ta bar tsakar gidan ya fito. Daina jin motsinta da suka yi ne tasa shi cewa Asabe ta duba musu. Ita kuma don ta tura mata haushi ta fito sai ya zata ta gama suyarta ta shige daki ne.

Muryarsa a sama tunda ya san yaran masu wayo suna makaranta yake mata magana.
“Banda fitina ma irin taki Innayo daga yin arba’in ringidi-ringidi kin kwaso jiki kin dawo turakar maigida…”

Maganganunsa a take suka fara tunzura ziciyarta domin ta fahimci ci mata mutumci yake son yi. Kalamansa na gaba basu bata damar yin wani tunanin kirki ba sama da zubar da hawaye.

“…karfe takwas da rabi don bala’i duk kin saka yara bacci kin taho dakina ke mai girki. To magana ta gaskiya ni ba zan dinga kwana da wannan yarinyar tana yi min kuka ba.” Ganin tana ta zubar da hawaye yasa shi cewa “Idan arba’in din ne baki son maimaitawa sai ki dinga barinta a dakinki ko ruwa A’i ta dinga bata. A shekarunta yanzu yaci a ce za ta iya kulawa da jinjinya.”

Ido sharbe da hawayen bakincikin wannan terere da ya yi mata kuma a kunnuwan Asabe ta ce “yanzu Alhaji kayi min adalci kenan? Ka dakeni kuma ka hanani kuka. Ita Asaben ba goyo gareta ba?”

“Ban san kina kishi da namijin da ta haifa min ba sai yanzu. Yaro dan wata biyar da an kwantar dashi baka sake jin kukansa sai gari ya waye. Wai ma da ki ke zancen adalci ke shi kika yi min da kika haifi mata har biyar?”

Zancen kenan kullum! Ita da babarsu A’i sun haifa masa ‘ya’ya mata. Asabe ma ta farkon ta mace ce cikon ta goman matan. Na shadaya ne ya fito namijin da ake muradi.

Idan ta biye masa ita zai cigaba da konawa zuciya a banza. Tashi tayi ta shige daki ko amsa bata bashi ba. ‘Ya’ya mata Allah Yaso bata kuma ta gode. Sake kudurin ganin ta inganta rayuwarsu tayi. Idan ta kama ta kara wata sana’ar za ta kara. Burinta a rayuwa su ginu su zama mutanen da sai dai a rabesu a sha inuwarsu. Ta yarda ita kadai ta gama shan wahalar rayuwar duniya indai ‘ya’yanta za su jidadi a gaba.

***
BARNAWA, KADUNA
2000

Zazzage akwatin da ta ajiye akan gadon tayi ta sake bin kayan ciki daya bayan daya tana jerawa a nutse. Tafiya ko da unguwa ce mara nisa tana da wani abu guda, sai mutum ya bincika kayansa sau goma kafin ya bar gida amma yana zuwa inda zai je sai ya tuna wani abu mai mahimmanci da ya manta. Hayaniyar yaranta ta ji daga falo da alama fada suke yi. Ba sai an fada ba kusan kodayaushe suka yi fada mai laifin daya ne.

“Lilu zo nan”

Ta daga murya tana kiran danta na uku. Bai zo din ba kamar yadda tayi tsammani sai ma ambaton “sai na rama” da yake yi cikin kuka. Sanin halinsa na rashin kunya yasa ta tashi da kyar saboda nauyin ciki ta bisu falon. Babban mai suna Suhaib akwai saurin fushi. Farha mai binsa sarkin tsokana. Sai Khalil da kowa yake kira Lilu mara kunya, ga taurin kai da saurin kuka.

“Allah nagode Maka” ta ce tana kallon yadda suka hargitsa falon kamar gidan mahaukata. Abubuwa kalilan ne a muhallinsu na asali. Yaran na ganinta suka shiga taitayinsu don sun san hali. Tana sonsu tana tattalinsu amma bata yarda da sakarci ba. Cikin hikima ta iya bi dasu duka da halayensu. Idan kayi abin fada ko duka kuma baka tsira. Khadija mace ce mai zafin nama da sanin ya kamata. Idan suka yi kiriniyar ta gama fadan sai ta koma gefe tana yi musu addu’ar shiriya. Fatanta kowannensu yana girma halinsa mara kyau yana raguwa har ya barshi gabadaya. Yanzu ma sulhu tayi musu ta kuma ja kunnen Farha akan tsokanar kaninta saboda raini da ya gama shiga tsakaninsu. Falon ta sake kallo sannan ta cira kafa ta taka kitchen ta leka ta dawo.

“Ina Nasima?”

“Ban ganta ba.” Yaran suka hada baki wurin fada.

A falo ta bar ‘yar budurwar mai aikin nata tare da yaran ta tafi sake hada kayan tafiya asibiti. So take ta tabbatar komai yana ciki kada ayi irin na haihuwar Lilu. Sai da aka gama shirya yaro babu shawul babu zanin nade shi saboda tana tsakar nakuda ta hada kayan.

“Ku taso ku kwashe tarkacen kayan wasanku kafin na kira Nasima ta zo ta share falon.”

“Wash Mami hannuna…” fadin Lilu yana yarfe hannu.

Hade rai tayi tun kafin tayi magana ya mike tsaye “tashi makyuyaci. Idan aikin baki ne naka yafi na kowa tashi. Amma da an ce za a more ka sai ka dinga langabewa.”

Fita tayi tana cije lebe jin kafarta tana rikewa ta zaga bayan gidan tana kwalawa Nasima kira.

Nasima tayi matukar razana da jin muryar uwardakin nata a kurkusa da inda take kwance. Hannuwan mutumin da suke bin jikinta ta doke da sauri tana mikewa tsaye. A razane shi ma ya dauki jakar da ya dawo da ita daga office yana gyara zaman necktie dinsa. Gaba ya yi yana yiwa Nasima inkiya da ta dakata kada ta biyo bayansa. Bata bari ya tafi ba ta bishi da sauri ta ware hannuwanta a gabansa. Mamakin karfin halinta ya yi a wannan yanayin da matarsa take gab da kamasu ya yi saurin zaro kudin da ya san su take nufi ya dora mata.

“Yaya Tahir?” Khadija ta kira shi da mamakin rashin sanin dawowarsa.

Da saurinsa ya tareta ya kama fadan borin kunya. “Me ya fito dake kina jan kafa ke da likita ya ce kina bukatar absolute bed rest? Meye amfanin Nasima a gidan da ba zaki huta ba?”

Murmushi tayi tana yabon irin kulawar da yake bata a ranta.
“Nasima nazo kira.”

Hararar Nasiman ya yi “idan kin gaji da aikin ne sai a nemi wata.”

Hakuri ta bawa Khadija kai a kasa cikin sassanyar muryarta ta makiran yara. Duka duka da kadan ta haura shekara sha shida, amma fitinarta a boye tafi ta wata ‘yar arba’in din. Tamkar hawainiya haka ta kware wurin boye halayenta. Sumumu kasau, macijin sari ka noke shi ne tashenta a wurin saurayinta na farko wani Alhaji a kasan layin.

Sai da suka shiga daki yake cewa Khadija wai yau yaji wa’azin da ake cewa kayi kyauta da dama hagu ba sai ta sani ba.

“Shi ne fa ina shigowa na hango wannan kazamar ‘yar aikin taki tayi baya. Da yake kanta kamar dusa aka zuba maimakon kwakwalwa inata kiranta na bata sadaka bata ji ba. Ni kuma na riga nayi niyar yi da fatan Allah Ya saukeki lafiya. Shi yasa na bita bayan.”

Kwalla taji ta sauko mata ta farinciki. Tana alfahari da mijinta domin ta san sai an tona ake samun irinsa. A da kam ta wahala akan ‘yan matansa amma da dabara ya nuna mata ya bari. Baya son ta wahala kuma baya son damuwarta. Tana cewa wash zai bar duk abinda yake yi yazo gareta. Ga saurin bata hakuri idan ya bata mata rai. Kulawa sosai yake bata duk da mai aikin da ta dauko ‘yar makotansu tun tana laulayi. Da zarar ya dawo gida bayan yara sun tafi Islamiyya yake turata daki tayi bacci. Wai nan so yake ta huta da kyau kafin su dawo. A wannan lokacin yake samun kebewa da Nasima ba tare da saninta ba. Nuna mata yake ya tsani yarinyar domin kada ya bar kofar zargi a tsakaninsu.

“Nagode Yayana amma don Allah ka rage hantarar Nasima. Kaga amana take a hannunmu.”

Ruwa ya tashi watsawa jikinsa ya nuna mata kamar baya son zancen. Yana bandaki shi kadai yake tsakin zuwanta bayan gidan dazu. Bin mata sana’arsa ce tun yana matashi. Khadija ‘yar kanwar babansa ce aka hadasu wai ana ganin idan ya yi aure zai rage. Babu wanda ya bata zabi kawai aka ce ta auri dan uwanta don ya shiryu. Ya kuwa nuna musu shiriyar tasa kamar gaske saboda yana son Khadijan. Da yake kwararren dan duniya ne babu wanda ya san ya cigaba da harkokinsa a waje.

Dawowarsu unguwar nan abin nasa ya kara baci tunda ya ga Nasima komai ya kwance masa. A zahiri yake nuna mata kyama amma a badini tafi kowa. Ita ce kawai a gabansa kuma bashi da burin da ya wuce ganin lokutan da suke samun kebewa a gidan ko a wuraren da ya saba kai ‘yan matansa.

Khadija bata san wainar da ake toyawa ba. Da zuciya daya take zaune da kowa. Gidansu Nasima a can kasan layinsu yake kuma sun fi kowa karamin karfi. Abinci a rana bai fi su ci sau daya ba idan an sami faraga. Shi ne fa ta nemi Nasima ta dinga tayata aiki suna biyanta karshen wata.

A ranar da daddare ta sake yi masa maganar dauko kanwarta ko tasa su tayata zama ko da zuwa tayi arba’in ne idan ta haihu.

“Na fada miki ba zuwansu ne bana so ba amma a gani na me zai hana ki dauko waccan yarinyar?” Ya ce da sigar laluma.

Dan jim tayi tana tunani kafin ta fada masa dalilinta na neman ta gida.
“Na fara tunanin sallamarta ne kawai.” Gabansa ne ya fadi zai yi magana ta dora da cewa “ka san ko Lilu da yake dana muna fada akan rashin kunya balle Nasima. ‘Yan kwanakin nan sai tayi zamanta a baya taki aikin. Idan na kirata a murya sai ka ji lafiya amma a fuska sai in ga kamar tana hararata.”

Dariya ya kwashe da ita duk kuwa da fargabarsa ta cikas da korar Nasiman zai kawo masa.
“Shi yasa nifa bana sonta. Ke kuwa da anyi magana sai ki ce marainiya ce. To kema dai naga alama kin gaji da aikin ladan kenan.”

“Ba gajiya nayi ba.” Ta amsa masa ganin kamar yana ganin asarar kudi yake da biyanta bayan aikin nata babu yawa.
“Zan yiwa mamanta magana ta fara kwana. Idan ta cigaba da halinta sai mu rabu.”

Zuciyarsa kamar an zuba ruwan sanyi don farinciki. Nasima tana gara shi a ‘yar haduwarsu ta bayan gida. Minti biyar idan tayi sai ya biyata. Idan ta fara kwanan zai fi samun lokaci tare da ita.

Bayan ya tafi aiki washegari Khadija ta je gidansu Nasima da misalin shabiyun rana. Lokacin yara suna makaranta ta barota ita kadai tana wanke-wanke. Tarba ta girmamawa ta samu daga wurin mahaifiyar Nasima. Bayan sun gaisa ta fada mata abinda ya kawota.

Ladidi ta dan bata rai “haba Mamin Suhaib? Yanzu don kina son Nasima ta dinga kwana
har sai kin fito a wannan yanayin da kike? Ai cewa za ki yi kawai ta fada min magana ta zauna.”

Dan murmushi Khadija tayi tare da girgiza kai. Don tana taimaka musu ba shi ne dalilin da zai sa su juyata son rai ba.
“A’a gara dai na zo da kaina. Ban fada mata ba ma na ce sai naji amsarki.”

“Allah Sarki Mamin Suhaib. Yasin shi yasa nake kara ganin girmanki. Kina da mutumci kuma kin san mutumci. Allah na tuba banda ma kin dage ai da ko kwandalarku ba zan karba a matsayin albashinta ba. Ciyarwar da kuke mata damu kanmu ta wadace mu.”

A zatonta sai washegari ko nan da kwana biyu Nasima za ta taho sai gata ta dawo da kaya niki-niki kafin magariba. Lokacin ko cikakkun mintuna talatin bata yi ba da tafiya. Da mamaki Khadija take kallonta tana turo katuwar jaka da wata karama sai ghana must-go.

“Ashe da shirinki.”

Tabe baki tayi Nasima tayi ta ce “uhm”.

Khadija ta daure zuciyarta daga take taken fitsarar da take gani a wurin Nasima. Shirin nata cikin kankanin lokaci ya bata mamaki ganin bata san da zuwan ba sai da ta gama aiki za ta tafi ta fada mata. Ita kuwa tuni sun gama shirinsu da Tahir.

Mamakin Khadija ninkuwa ya yi da taga Nasima ta nufi dakin baki da kofarsa take a cikin falon da kayanta. Idan tayi tunanin ko mamanta ce ta hada mata kaya kafin ta koma gida to da ya akayi ta san dakin da za ta zauna bayan ko su Suhaib basu sani ba. Kama bakinta dai tayi tana kallon ikon Allah.

Nasima kuwa tana shiga dakin ta buga wani uban tsaki. Ta lura Khadijan sai wani fiffika take yi ita mai miji. Mijin da yake a tafin hannunta matarsa har wani daga kai za ta yi mata? Sake yin tsaki tayi da ta kula tsohuwar katifarsu Lilu ce aka ajiye mata a dakin da wankakken bedsheet da pillow.

“Kut! Ai wallahi gado za ka zo ka saka min a dakin nan ko na kama gabana. Lallai ma Khadijan nan kin rainani.”

Shu’umin murmushi tayi da ta tuna tuggun da ta shirya mata. Lokaci ya yi da Tahir zai bata nata ‘yancin ko ta kwata ta karfi. Ba zai yiwu bane ya cigaba da raina mata wayo. A gaban matarsa ya fada mata magana a bayan idonta kuma ya dinga lallabata. Da Tahir ya dawo Nasima tana daki ta ji hayaniyar yaran.
Da saurinta ta mike ta gyara kwalliyarta ta fesa turare ta fito.

Shirt dinsa ce a jikinta ta hada da zani da dankwali iri daya.

“Daddy oyoyo” ta ce da karamar murya kai a kasa.

Kallonta ya yi sama da kasa wani abu na fizgarsa gareta. Ba don idon yara ba da sai ya biya ladan wannan ado. Gwalo tayi masa karaf a idon Khadija wadda ta fito daga kitchen da tray a hannu. Nasima sai ta wayance ta kuma yin gwalon.

“Nima na rama Lilu.” A zuwan wasa suke yi dashi.

Tahir sai ya karbe da cewa “anya Khadija ba rainon mutum hudu ki ke ba? Ita da ta zo taimaka miki ta buge da wasan yara.”

Bai bawa Khadija damar yin magana ba ya bukaci ta tara masa ruwan wanka. Daki ta nufa zuciyarta cike da wasi-wasin abin da ba ta son zargi. Abincin ma daki ta kai masa a ranar. Sai da suka kwanta ta sako zancen shirt din.

“Ni fa kamar shirt dinnan taka da nayita nema wancan wankin na gani a jikin Nasima dazu.”

‘Jaraba sai da ta gane’ ya ce a zuciyarsa.
“Oh ashe bamu yi maganar ba. Rannan na tsinceta a bayan mota tayi datti. Ina jin daga kayan wankin ta fado. Na dauko zan yar shi ne da ta gani ta ce tana so.”

“Ka dai san ina bata kaya. Idan kari take bukata ai da sai kayi min magana. Rigarka ai ba abin sawarta bace.”

Da bacin rai take magana ya soma bata hakuri. Zuciyarta sam babu dadi har wani zazzabi taji yana neman kamata. Abubuwan da take ta son turewa game da Nasima sun sami wuri sun manne mata a rai.

Bayan kamar minti arba’in tana fama da guntun ciwon marar dake tsungulinta taji kamar hannun Tahir a saman fuskarta. Da alama karkada hannun yake ya gani ko tayi bacci. Da gangan tayi motsi ai kuwa ya dauke hannu ya kwanta da sauri. Juya mata baya ya yi ta bude ido ta tabbatar baccin karya yake yi. A hankali tayi kwafa ta sake rufe ido. Ba afi minti goma ba ya sake kada hannun. Wannan karon luf tayi takaici na nukurkusarta. Akwai abin da yake boye mata. Fatanta Allah Yasa ba Nasima bace. Tana jinsa ya tashi ya shiga bandaki. A cikin kunnuwanta taji ana bude dakinsu shi ma ya bude bandakin. Sannu a hankali ta bude ido kadan don kada a san ta farka ta hango Nasima a bakin kofar. Abin ya daina bata mamaki ma tunda har take da karfin gwiwar zuwa dakin. Da yatsa Nasima take yafito Tahir da ya fito daga bandaki, shi kuma yana nuna mata Khadija wadda duhun dakin yasa basu gane ta bude ido ba. Barazanar shigowa Nasima tayi masa ya yi murmushi yana yi mata inkiya ta karaso mana. Ba kunya ta sako kafa a kofar dakin ya yi saurin karasawa ya dagata a kafadarsa suka yi gaba. Kememe Nasima taki yarda a koma dakinta wai ita a gadonsa za ta kwanta. Sanin rigimarta yasa ya ce da Khadija su kwana a nata dakin.

Rufe kofar da ya yi a hankali ya yi daidai da matsanancin bugun zuciyar Khadija. Hawaye take yi ba tare da ta sani ba ta tashi da kyar ta bude kofar ta fita. Dakin Nasima ta nufa bata same su ba sai ta nufi na Tahir. Daga bakin kofa take jin dariyar Nasiman tana rokonsa ya daina yi mata cakulkuli. Shi kuma yana cewa ta rage murya.

Sai da ta tsaya ta hadiyi wani yawu mai daci sannan ta murda kofar da karfinta. Ganin da tayi musu yasa komai na jikinta tsayawa cak. Murdawar cikinta ce ta dawo da ita duniyar mutane ta rike cikin tana salati.

 

 

Wattpad: https://my.w.tt/Fae5U4oHh8

UWA UWACE…2

Batul Mammanđź’–

 

Duk hukuncin da uwa za ta yanke akan ‘ya’yanta tana yi ne da tunanin hakan shi ne maslaha a rayuwarsu ko da kuwa a gaba shi zai zamto mafarin kukansu.

***
Kwakwalwarta babu abin da take hasko mata sai yanayin da ta ganshi tare da Nasima lokacin da ta farfado. Idanunta a rufe amma hawaye yana sintiri daga kwarmin idanun zuwa kunne ya sauka akan pillow. Daga kamshin da take ji na dakin kadai ta fahimci a gadon asibiti take. Sakayau take jin jikinta babu wani nauyi sai na zuciyarta da ta koma tamkar dashen dutse. Cikinta ta shafo a hankali taji babu tokarewar nan ta dan da ya kusa zuwa duniya. A firgice ta tashi wani irin radadi na ban mamaki ya soki mararta.

“Bar garaje Khadija jikinki da danyen ciwo.” Cewar Yakumbo mahaifiyar Tahir.

Da yake bata san da ciwon ba tashin bai wahalar da ita ba kamar komawa ta kwanta. Ita ba a kwance ba ita kuma ba a zaune ba haka ta saka hannuwanta ta dafe gefen gadon don kada ta fada da karfi. Yakumbo ce ta taimaka mata ta koma ta kwanta tana rarraba idanu. Tambayoyi ne akan harshenta ta kasa amayar dasu saboda sabon al’amarin da take ji a jikinta.

Yakumbo ta sake cewa “Bari na fadawa nos kin farfado” har ta kusa kofa ta dawo ta dafa mata kai “sannu kin ji. Allah Ya baki lafiya.”

Khadija ta kula da hawayen da Yakumbon ta dauke daga gefen idonta kafin ya sauko. Jikinta sai ya kara yin sanyi da tunanin ko me yake faruwa ba alkhairi bane.

Yakumbo bata jima da fita ba Mamanta ta shigo tare da kannenta da su Farha. Kowa sannu yake yi mata tana amsawa da ka. Sallamar Tahir taji ta dawo mata da duk wasu lokuta da sai a yanzu take fahimtar raina mata wayo suka yi shi da Nasima. Runtse idanu tayi tana jin Mamanta tana tambayarta ko cikin ke mata ciwo ta girgiza kai. Shi kan shi Tahir din ganin idonta biyu sai da yaji kamar ya koma saboda firgici. Saukinsa daya yaransa da suke wurin Mama jikinsu a sanyaye da yanayin Maminsu. Yana da tabbacin ba za ta yi wani abu a gaban ‘ya’yanta ba.

“Ku bashi wuri mana ya zauna kun yi ÄŹare-ÄŹare akan gadon.” Mama ta furta tana nunawa kannen Khadija hanyar fita daga dakin.

Mutum biyu ne dama suka zauna a gefe sai suka tashi amma basu fita ba. Tahir ya kalli Khadija ba shiri yau shi ne da sauke kai kasa. Tsoronta ne ya mamaye masa zuciya saboda irin kallon da take yi masa babu komai a cikinsa sai tsana da disappointment.

Mama kuma ta kara masa zafi da cewa “Ina mai-aikin taku yau? Kodayake ya kamata yau ta huta.”

Dawowar Yakumbo da likita ce ta taimaka masa bai bayar da amsar da za ta zama zallar karya ba. Kukan jinjiri ne ya biyo bayan shigarsu dakin a hannun Matron. Da dan murmushinta ta nufi gadon bayan gaisawa da jama’ar dakin.

“Ina nan ni dai. Doctor ki gama dubata ta bawa bebina abincinta mun gaji da shan madara.”

Kallon kunshin shawul din Khadija take yi a lokacin da likitar ke yi mata tambayoyi game da jikinta. Babu abin da take fahimta sai gyada kai da take yi idanunta fal hawaye akan dan da bata ganin fuskarsa.

Likitar sai ta kalli Yakumbo da alamar tambaya “Maman Khadija ya naga kamar bata san me ya faru da ita ba?”

“Farfadowarta kenan na taho kiran Nos sai na hadu dake.”

Da ido Maman ta kalli kannenta suka fice tare da su Suhaib. Tahir kamar ya nutse ya kasa kallonta. Likitan ce ta karbi bebin ta dora mata a cinya.

“Khadija kin san cewa tun farkon cikin nan akwai matsala har kina yawan zubar da jini ko?”

Bata amsa ba sai bin fuskar yarinyar da har kunne an bula mata take da kallo.

“Yau kwana kenan…” da sauri ta daga kai ta kalli likitan jin cewa kwananta biyu bata hayyacinta “maigidanki da mai-aiki sun kawoki cikin dare kina ta zubar da jini a sume. Ta ce zamewa ki ka yi a toilet wurin faduwa cikin ya bugu da sink. Kafin ki farfado faya ta fashe ga jinin bai tsaya ba.”

“Hummm” ta ce da guntun murmushi idanunta akan Tahir. Yakumbo tana kallonsu ta kuma ha yadda yaki daga kai ya kalli matarsa.

“Ba cs din bane kadai Khadija harda mahaifar muka cire.”

Sautin da taji ya ziyarci kunnuwanta ga dukkan alamu shi ake kira saukar aradu a yanayin tashin hankali. Zabura tayi za ta tashi a karo na biyu tana fama dinkin kasan mararta.

“Kwanta don Allah kada ki yiwa kanki rauni. Kaddara bata wuce kowa. Gashi an ciro miki jaririyarki lafiya kalau.”

‘Yar ta rungume ta fashe da matsanancin kuka.

“Ki yi hakuri Khadija. Mun yi iya yinmu amma jinin yaki tsayawa. Taimakon Allah ne kawai muka sami baby din tunda sun ce basu san tun yaushe ki ka fada kan cikin ba.” Likitar ta karasa yi mata bayani.

Kukanta bai tsaya ba kowa na dakin ya tausaya mata. Yakumbo kuwa haka kawai tun farkon labarin dama bata wani yarda ba. Yanayin Khadijan a yanzu sai ya karfafa mata zarginta. Don ta tabbatar sai cewa tayi da Tahir ya rarrasheta mana. Mugun kallon da Khadija ta watsa masa wanda ya dakatar dashi ya bata amsarta.

“Mijin naki ki ke yiwa wannan kallon don rashin hankali kamar shi ya dora miki lalurar.” Mama ta ce da ita cikin fada.

“Allah sarki” inji Matron “kar ki ga laifinsa da kyar ya yarda yasa hannu. Yarinyar da suka zo tare ce ma ta dinga tausarsa akan ya amince a cire saboda kada a rasa ki.”

Numfashinta neman daukewa ya yi a wannan lokaci. Wato duka karairayin zuwanta asibitin sai da Nasima ta ingiza shi ya yarda aka cire mata mahaifa. Bata san me za ta yi musu ta huce ba. Ya ci amanarta ya kuma cutar da ita.

Gani tayi su Mama na fita daga dakin tayi murmushin takaici. Ta san irin abin nan ne ace a basu wuri ita da mijinta. Ana rufo kofar ya taho gareta da sauri.

“Nasima don Allah kiyi hakuri ki rufa min asiri. Na san ban kyauta ba amma don Allah in ci darajar ‘ya’yanmu.”

Tahir ya cika babban munafuki har tana mamakin yadda akayi ta kasa daukan haske ko sau daya. Saboda nisan da ya yi shi yasa bai ji kunyar kiranta da sunan mai-aikinta ba.

“Khadija. Suna na Khadija.” Ta ce dashi muryarta a dake.

Bakinsa ya doke da sauri ya sauka kan gwiwoyinsa.

“Ki yafeni Khadija.”

Ba shi take kallo ba. ‘Yarta ta karshe a duniya take kalla tana nadamar biyayyarta a baya. Da bata amince ta aure shi ba da basu hada jini da mazinaci ba.

“Na yafe maka tun kafin ka roka duk da baka yi nadama ba.”

“Nayi. Wallahi nayi nadama sosai.”

“Baka yi ba. Na rantse da Allah da kayi nadama da baka taho da ita kawoni asibiti ba. Da bata zauna jinyata har ana cigiyar rashin zuwanta a yau ba.”

Busassun labbansa ya lasa a hankali. Ya san ba za ta taba yarda ba amma shi ya san cewa ya yi nadama. Yana dai yiwa Nasima irin son da ba zai iya hakura da ita ba. Idan kurar nan ta lafa aurenta zai yi ya kama mata gida daban. Zai cigaba da zama da Khadija saboda wani sashe na zuciyarsa yana ganin girmanta. ‘Ya’yan da ta haifa masa kuma duk munin halinsa yana sonsu kuma ya san suna da hakki a kansa. Muryarta ce ta katse masa tunani.

“Kafin a sallameni ka rubuta min takardar saki. Ba zan tona maka asiri ba saboda bana son duniya ta nunawa ‘ya’yana yatsa akan halinka. Kai dai ka tanadi abin da za ka fadawa iyayenmu tunda karya a jininka take. Sharadi na daya ne.” Kallonta ya yi “kada ka yarda ka dora min laifi a matsayin dalilin rabuwarmu. Ina fata ka fahimceni.”

“Ba zan iya sakinki ba. Khadija ina sonki.”

“Ka daina yiwa kanka karya akan abin da baya zuciyarka.”

Zancen gabadaya baya so ayi shi a asibiti amma ya san ba shi da hurumin cewa tayi shiru. Yana son cigaba da zama da ita amma ba ya jin zai zama adalci gareta ya tursasata ta cigaba da zama tare dashi bayan yanzu ya fara son Nasima. Tunda dai za ta rufa masa asiri ya san komai zai zo da sauki. Juyawa ya yi zai fita ta kira sunansa.

“Tahir! Za ka yi nadama a nan gaba sai dai ina tsoron kada ta zo a lokacin da komai ya lalace. Ina gudun kada hakkin ‘ya’yan da ka batawa rayuwa ya rataya a wuyan ‘ya’yana.”

Da yake maganar ta tsorata shi bai san lokacin da ya ce “wallahi ba ni na bata Nasima ba a haka na sameta.”

Kallon da tayi masa ne ya sa shi jin nauyin furucinsa. Sunkuyar da kai kawai ya yi yana jiran ya ji me za ta ce sai yaji shiru. Juya masa baya tayi tana zubar da zazzafar kwalla. Ta so Tahir a lokacin da bata da zabin da ya wuce bin umarnin iyaye. Ta sadaukar da farincikinta na son waninsa saboda tsira daga azabar Allah. A yau ta rasa mahaifi da kuma igiyar auren da take jira ya datse duk a dalilinsa. Ita mai iya tsaya masa ce ya kara aure idan yana so. Shi yasa take mamakin dalilinsa na yin zina. Zinar ma ta fuskar wulakanci gareta. Kalaman mahaifiyarta take tunawa a wani lokaci da ya wuce tana yiwa kaninta fada zai tafi jami’a a wani garin.

“Zina masifa ce. Idan ka yi da ‘yar wani kai ma sai ta zagayo jikinka inda za ka ji ciwo mai radadi. Ko ni, ko ‘yan uwanka, ko iyalinka ko ‘ya’yan cikinka”

Addu’a ta soma yi musu tana fatan Allah Ya karesu daga wannan mummunar dabi’a. Za ta sadaukar da rayuwarta wurin kula da tarbiyarsu da fatan rufowar asirin mahaifinsu. Aure kuwa ta yi ta gama. Abin da ya yi saura ba rayuwarta za ta yi amfani dasho ne wurin ganin yaranta sun sami ingantacciyar rayuwa.

Bayan kwana biyu suka sake kebewa da Tahir a dakin. Tuni tayi masa akan takardar sakin ya ce da ya saketa gara ta tona masa asiri. Amsarsa ta tayar mata da hankali ta kuma sanyata tunanin dalilinsa na sauyawa bayan da ya amince.

Yanayinta ya kalla a ransa yana yabon kaifin basirar Nasima. Yana fada mata zai saki Khadija ya aureta ta fitittike ta ce sam bata yarda ba. Nuna masa tayi duniya za ta zagesu idan suka yi haka. A ranta kuwa gudun kada ya bata rikon ‘ya’ya take yi. Tafi son ayi auren a gaban Khadijan ta ganta suna masu matsayi daya a gidan. Ita ta bashi shawarar wadancan kalamai domin a cewarta Khadija za ta zauna don ‘ya’ya. Tunda aka kai yanzu maganar ganinsu bata tashi ba to ya sani cewa indai akan ‘ya’yanta ne za ta rufa masa asiri.

Ga zahiri ya gani. Sai ga Khadija tana kuka tana rokonsa saki kamar ba ita ya yiwa laifi ba. Da aka murda kofar dakin da sauri ta share hawayenta harda karyar ciwo ke cinta. Da wannan barazanar ya samu ya rufe bakinta har aka yi sallama. Da wani ya san abinda uban ‘ya’yanta ya aikata ko da kuwa mahaifuyarta ce gara ta cigaba da zama dashi ko babu soyayya. Ba za ta so labarin gamon da tayi ya taso a lokacin da wani alkhairi ya doso rayuwar ‘ya’yanta ya wargaza ba.

KHADIJA: A jerin ire-iren iyaye mata ta fado a jinsin masu shanye komai domin ‘ya’yansu. Ta yarda ta fanshi zubar hawayensu ta hanyar sadaukar da farincikinta. Karesu zata yi muddin rai kada kazantar mahaifinsu ta wargaza rayuwarsu a gaba.

*****

KIRIKASAMMA
1995

Ta san ya ji ta sarai amma bata sare ba ta cigaba da binsa da roko da laluma saboda muddin ya sa kafa ya fita yau to magana ta kare. Kiran sunansa tayi da dan karfi ganin ya kusa kofar fita. Indai bukatarta za ta biya tayi alkawarin jure duk wani jan rai da wulakanci daga Inuwa.

“Malam inata magana baka ce komai ba har za ka fita.”

A fusace ya juyu kamar zai mangareta ya soma fada.

“Ke dai Mari da mayya ce ki ka kama mutum Yasin sai buzunsa. Haba! Ni na taba ganin bakin naci irin wannan? To duk jarabarki sai ya tafi yadda ake tura ‘ya’yan kowa.”

Hargaginsa ya fito da sauran matan gidan daga bangarorinsu. Zaman kauye babu abin yi har jiran barkewar rikici suke don a bawa ido abinci. Gidan nasu kuwa an sami karuwar jama’a, kama daga matan da ake kara aurowa zuwa hayayyafar da ake yi kusan duk shekara.

“Rigimar me ku ke yi da rana tsaka Inuwa?” Mal. Sa’idu babban wa ga mazam gidan ya tambayesu amma aka rasa mai bashi amsa.

Mari sadda kai tayi kasa zuciyarta tana bata cewa hakuri kawai za ta yi wannan karon a tari gaba. Mal Sa’adu da sauran ‘yan uwan Inuwa babu mai goyon bayanta. Maganar nan kuma ko Inna Mairo ba bayanta za ta bi ba.

“Kya yi shiru kuma yanzu? Ai sai ki bude baki ki fada musu abinda ki ke rokona” cewar Inuwa yana duban yayansa “wai makaranta ce bata so a tura Abbati.”

“La haila ha illallahu…”

Mata sai tafa hannuwa kamar sun ji gagarumin sabo. Shi kuwa Mal Sa’adu cewa ya yi maganar ba ta tsaye bace su biyo shi sashensa.

Durkuso Mari tayi a gefen tabarmar da Inuwa ya zauna. Bata ma yi niyyar zama ba domin rashin kunya za ace tayi. Mal Sa’adu ne ya yi magana cikin jimami.

“Yanzu ke Mari karatun Muhammadiyyar ne ba kya so? To ko dai kin canja addini ne bamu da masaniya?”

Kai da hannuwa ta karkada a tare “a’a Malam. Cewa nayi a barshi ya cigaba da karatun a nan ba sai an kai shi Kano ba almajiranci ba.”

Matan gidan dama ba kaunarta suke sosai ba saboda fifikon da Inna Mairo ke nunawa a kanta. Gashi tayi karatu har matakin aji uku a firamare kafin Inuwa ya aurota. Su kuwa babu arabi ba boko. Anyi musu baiko tun tana shekara goma. Sai ta tafi aikatau Dutse inda ta sami wayewar kai. Gidan da tayi aikin suka saka ta a makaranta. Sun so a barta ta karasa amma gidan su Inuwa suka ce idan bata dawo anyi auren ba a dawo musu da kudinsu. Haka nan tana ji tana gani aka rabota da ilimin da ta fara jindadinsa. Wannan ne yasa ta dage aka kai ‘ya’yanta firamaren garin sannan suna zuwa makarantar allo da ta dare. Da sana’ar dinkimta da take dan samun kudi take yi musu hidimar makaranta. Su biyar ne yanzu. Abbati babba da mai binsa Sani sai ‘yan mata uku. Al’adar gidan ta tura yara maza almajiranci kwatakwata bata burgeta. Ta ga yadda almajirai ke watangaririya idan sun tafi karatu, bata marmarin ‘ya’yanta suyi irin wannan rayuwa.

“Lallai Mari. Ke ko ‘yar kunyar nan ta dan fari ma ba kya ji har kike kallon idon Malam kina cewa a bar miki da a gabanki?” Uwargidan Mal Sa’adu ta furta da sigar nuna tayi ba daidai ba.

“Ko ma dai mene ne wannan sabon abin da ki ka zo dashi ba al’adar gidanmu bace. Zuri’ar gidan nan suna zuwa almajiranci tun talan-tale. Naki dan da bai fi na kowa ba shi ma zai je. Sai dai kuma idan zaki sake masa uba.” Mal Sa’adu ya kare da tsorata ta.

Idan aka ce ta sake masa uba tamkar ana tuhumarta da laifin haifar dan da ba na sunna bane. Muryarta a karye ta bashi hakuri “Allah Yasa hakan shi ne mafi alheri.”

“Karatun allo hairan ne! Abbati zai je kamar sauran ‘yan uwansa ya rubuce sittin kuma ya haddace shi.”

‘Nima haka nake fata’ Mari ta ce a ranta tana mikewa tsaye. Jiki ba kwari ta shiga dakinta tana jin kamar an zare mata laka. Wannan karon an mata fin karfi amma ba za ta yarda badi a kai Sani ba.

Kafin ranar tafiya ta shanya kanzo gari guda ta gyara masa. Man gyada ma ta soye shi da albasa ta kuma daka masa yaji. Tayi kuli-kuli, carbin malam, hallaka kwabo da duk wani abu da take tunanin zai ci daidai karfinta. Nasiha kuwa har ya soma gajiya da ji.

“Ka yiwa malaminka biyayya Abbati.”

“Banda kwadayi ko dauke dauke.”

“Idan an turaku bara ka ce na hana. Ga kayan abinci nan ina ta hada maka hatsi. Zan fadawa Babanka ya bawa malamin. Idan ya so in sun dora sanwa a dinga dibar maka.”

“Abbati kada ka je bara fa. Daga cikin gidan wani zubin sai an zageka an zagi uwar da ta kawoka duniya kafin a baka kwantai.”

“To Baaba” yake cewa ga duk nasihar da fadan nata. Har yanzu bai san ma’anar karatu da ake cewa za’a kaishi tare da sa’ansa dan yayan Inuwa ba. Yayyansa da suka tafi garuruwa daban daban yake sha’awa. Idan zasu zo suna dan kullo tsarabar birni su kawo. Kuma shi da Baaba ke son ya zama likita yanzu ne zai yi karatu na ‘yan birni ya fara allura.

Mari tayi kuka sosai ranar da zasu tafi. Bai taba nisa da ita ba musamman saboda tsoron fadansa. Indai rigima ake yi da wuya ka ga Abbati a ciki. A gidan manya da yara idan ka cire mahaifansa da ‘yan uwan babansa ana tsokanarsa da Abbati solobiyo. Rashin kuzarinsa yana daga cikin manyan dalilanta na son ya zauna a gida. Kazalika shi ne ya kara rura wutar kiyayyarta da zuwansa almajiranci. Banda iyayen sun riga sun farlantawa kansu kai yaransu maza akwai makarantu yanzu a garin nasu na ilimin islama.

Har soro ta fito tana kuka da zasu shiga a-kori-kurar da ta zo daukarsu. Hawaye take wani na bin wani tana ta nanata masa abubuwan da ta fada masa.

“Mu kuwa kamar tsinar namu ‘ya’yan muke bamu san zafin nakuda ba.” Cewar guda cikin faccalolinta.

Wata ta amshe da cewa “mu da aka jima ana daukar namu ba.”

“Wai kuma a haka fa don dan fari ne. Wannan da Sani ne zai tafi sai tayi mana karamin hauka.”

A gigice ta kalli amaryarta da ko haihuwar fari bata yi ba tana neman ballo mata ruwa. Ranta a bace ta ce,

“Bakin ki ya sari danyen kashi. Sani ba zai je bara ba da yardar Allah. Wannan ma don anfi karfina ne.”

“Ai kuwa zan nuna miki babu dan da za ki fi karfinmu a kansa. Kai Inuwa..” Mal Sa’adu dake bayan matan ba tare da saninsu ba ya yafito kaninsa “tsayar da direban nan ka hado kayan Sani.”

Ba Mari ba shi ma sai da ya razana. Sani shekararsa tara ga karamin jiki kamar dan bakwai.

Mal Sa’adu ya juya a fusace ya kira ragowar kannensa. Duk wanda dansa sai badi zai tafi ya ce a hada masa kaya yau. Sauran matan basu ji dadi bane saboda basu shirya ba. Mari kuwa da ta gama magana da kanwar Inuwa dake aure a Kazaure sai da ta kusa haukan da ake kira mata. Sun gama shiri za ta dawo ta ce a bata Sani saboda bata da namiji sai ta tura mata kudi a kaishi bodin.

A buhu Inuwa ya cusa kayansa tana kuka tana tumami amma Mal Sa’adu ko gezau. Inna Mairo ma tayi masa magana ya ce babu matar da za a auro tafi karfinsu. Idan bai yi haka ba sauran ma zasu raina mazajensu ne.

Kukan Mari a kofar gida har makota ana ji. Ana saka Sani a mota ta sauko dashi tana magiyar a barshi ta yarda a tafi da Abbatin. Ita a nufinta ko shi kadai ya yi bokon ya zama wani abu a gaba zai taimakawa yayansa. Shi kuwa Abbati da zuciyar kuruciya sai ta ayyana masa mahaifiyarsu bata kaunarsa tafi son kaninsa. Kukan shi ma ya saka ta mika hannu za ta sauko dashi Inuwa ya daka mata tsawa.

“Ki mayar dasu ko su sauko ku kama hanyar gidanku tare.” Ransa ne ya baci da jama’ar da ta tara musu ana ta gulmarta wai bata da rikon addini.

Mutanenmu da matukar tsoron kalmar saki. Ba arziki ta saki yaran tana zaman ‘yan bori a kasa. Tana ji tana gani motar nan tayi gaba aka tafi da ‘ya’yanta. Abbati za’a sauke shi a Kano shi kuma Sani da sauran yaran a Zaria saboda can ne suke da manyan yayye.

MARI: Ga Mari ba mutuwar auren kadai take tsoro ba harda inda za ta kai yaran. Iyaye basa raye ga talaucin kauye. Idan aurenta ya mutu kannensu ma masomin tagayyarar rayuwarsu kenan. A wannan lokacin maslahar da ta hango bata wuce ta sadaukar da mafarkin cigaban manyan ‘ya’yanta akan rayuwar kannensu ba.

*****
KANO

1995

“Masu gida. Magadan Alhaji. Ku zo ku dauka na gama rabawa” Asabe ta kira ‘ya’yanta tana rangwada murya.

Gajeren tsaki gami da murmushi Innayo tayi ta cigaba da barar albasar gabanta. Ina abin gado a tattare da Alh Rabi’u har da mutum zai yi tinkaho? Tabbas arzikinsa ya karu a shekarun nan haka kuma tsiya ta rashin son wadata iyalinsa ta kankama. Innayo bata sake haihuwa ba tun Hasiya. Asabe kuwa ta jera maza uku bayan wanda suka yi goyo tare lokacin Hasiya. Salon kishin Asabe ya dade da dena bata mata rai. Ita bata yarda bane sai ta cusa mata haushi ta kowane hali. Innayo kuma bata da wannan lokacin. Har yanzu da ta aurar da duka ‘ya’yan uwargidan Alh Rabi’u bata hakura da dena neman kudi ba. Yadda ta gina su haka take ta fafutukar gina nata. Dukkansu sai da suka gama sakandire da guminta aka yi bikinsu.

Abu daya ke yi mata ciwo a rai wanda yasa ta dada jajircewa akan ‘ya’yanta. Tun lokacin bikin A’i babbar ‘yar Alh Rabi’u mahaifiyarsu ta sake bayyana a rayuwarsu. Mijinta Kansila ne a lokacin suna ta damashere da dukiyar talakawa. Innayo bata son auren ta kuma fadawa A’i, amma sai ta tsallake ta sanar da mahaifiyarta Laraba. Ita kuma ta tsaya mata sun ga mai arziki. Alh Rabi’u dama tuni ya mika wuya ya yi mubaya’a ga wannan hadi. Tana ji tana gani akayi auren. A’i da kannenta suka koma jikin mahaifiyarsu. Ita dai bata fasa yi musu komai da ta saba ba amma tsakaninsu babu wannan mu’amalar ta uwa da ‘ya’yanta. Komai nasu na shawara da Laraba suke yi. A ranta ta kan ce uwa uwace! Shekara na zagayowa Kansila ya biyawa A’i, Alh Rabi’u da Laraba hajji. A gabanta kannen A’i suka shigo da tsaraba mai tarin yawa ita kuwa da ‘ya’yanta aka bisu da dan madina da bagaruwa. Alh Rabi’u kuwa ‘yan mazansa ya gwangwaje ya bata robar zam-zam irin ‘yan kulalan nan adadin ‘ya’yanta.

“A sha a sami tubarrakin Annabi Isma’ila.” Ya ce lokacin da ya ajiye mata a gefen katifa.

Idan ta ce wannan abu bai yi mata ciwo ba tayi karya. Ita ma za ta so nata ‘ya’yan su zame mata inuwar hutawa a gaba. Auren irin su Kansila da ta san dukiyar yawanci zuwa take ta tafi da an gama gwamnatinka ne bata so. Sai ya zamana bata da dare bata da rana. Sana’ar abinci ta iya kuma ita ta kara fadadawa.

Muryar Zara ta ji wadda Hasiya take bi tana magana bakin tsiwar nan a gaba ta zumburo shi.

“Ni dai gaskiya ki canja sana’a Innayo wallahi gulmarmu ake yi a makaranta. Ko? Ko Hasiya?” Ta waiga bayanta inda Hasiya ta tsaya jikin kofa.

“Ni dai ban sani ba.” Hasiya ta ce tana ja da baya gudun fadan Innayo.

Haushi ya turnuke Zara ganin Hasiya za ta bata mata shiri ta harareta.

“Banza kawai. Ke kin fi so a dinga jin tsamin geron ‘yar tsala a jikinki duk safiya a makaranta”

Ita da gaske take son mahaifiyar tasu ta sami wata sana’ar ba ta abinci ba.

Sai da Innayo ta gama barar albasar ta daga kai “yau ke ce da yin danmalelen dare. Ga albasar nan ki yanka kanana Hasiya za ta karbo tumatir ki hada.”

“Innayo” Zara ta kira ta kamar tayi kuka.

“Mai abinci ta fi almajira kuma ta fi mai shiga makota tana bani bani. Idan kin raina min sana’a ni ki ka raina.” Ta bata amsa ko kadan muryarta bata daga ba.

Daga gefensu Asabe ta tsoma baki tana dariyar shakiyanci “sunan wani wai shi girkau. An tasa yara a gaba ana ta kone musu sinadarin kyau da wutar icce ai dole su yi bore. Shiga makota bani bani kuwa dabara ce sai mai wayo. In mutum ya isa ya gwada mana.”

Innayo bata kula ta ba sai ‘ya’yanta da ta bi da kallo daidai suka fahimci ma’anar kallon. Daki suka shige Zara tana botsarewa ita a dole bata son aikin.

“Tara ki nake yi Zara. Idan ki ka kaini bango kin san sauran” cewar Innayo daga bakin kofa.

Zara bata kara cewa komai ba. Innayo na fita kamun bikin ‘yar kanwarta da yamma ta turawa Hasiya aikin da jan kunnen kada ta sake ta ce ita tayi.

Bayan Hasiya ta gama ta fita waje kiran almajirin da yake kai musu bakin hanyar wata makarantar dare tayi. A kofar gidansu yake zama da an yi magariba. Tana jiran karasowarsa daga daya tsallaken layinsu a-kori-kurar da ta dauko su Abbati ta zo ta wucesu zuwa makarantar dake cikin unguwar.

“Kai ina Munzali?” Suka ji muryar Asabe daga bayansu. Rabonta da shi tun kafin ta sauke abincin rana. Shi ne babban danta namiji.

“Ban gan shi ba” yaron ya bata amsa.

“An ce min tare ku ke zuwa filin kwallo.”

“Bai je ba yau. Su Shazali ya bi yawo.”

Da ta bi ba’asi sai ta gane su Shazalin wasu matasa ne almajirai kamar yaron Innayo din. Hankalinta ne ya soma tashi saboda an kusa Isha’i.

***
“Cire wandonka na ce” Shazali ya ce da fada saboda bata masa lokaci da Munzali ke neman yi.

Idanu a waje cike da tsoro Munzali ya sake kama wandonsa ya kankame.
“Na ce maka bana jin komai. Ni gida zani Asabe za ta dakeni idan ban koma ba.”

“Kai ma ka tsaya sai wani lallaba shi kake yi. Dalla bani wuri na nuna maka yadda ake yiwa sababbin shiga.” Cewar wani dan kwaya abokin Shazalin.

Matsawa ya yi ya turo masa Munzalin da ya fara turjiya gabansa. Shi ya rike hannuwan abokinsa kuma ya dauke Munzali da mari kafin ya zare wandon ya yi wurgi dashi.

Dariyarsu ce ta fara karade kangon kafin ihun azaba da Munzali ya saka yana kiran Asabe ta cece shi.

 

Leave a Comment