Books Reviews & FAQs

Wacece Yafi So Hausa Novel

*🤍🤍WACE CE YAFI SO🤍🤍*
(Gajeran labari ne)

 

TSARAWA DA RUBUTAWA

_Maryam Yusuf Ummu Juwairiyyah {Sahibar👸Royal Star🪄}_

~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
*🌟ROYAL STAR WRITER’S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~

Ban yi alkawarin posting a koda yaushe ba🧏‍♀️

wannan book kirkirarren labari ne idan hali ya zo daya katari ne aka yi.

Deducted to UMMUSALMA SANI SALMAN (Yar lelen royal star🪄)

 

Special gift to (NANA SMILE) ina yinki sosai Aunty Nana a duk in da ki ke, miss you so much

 

Da sunan Allah mai rahama mai jin k’ai amincin Allah su kara tabbata ga fiyyayen hallita Annabi Muhammad (S.A.W) Allah ina rokon ka yanda ka bani ikon farawa lafiya Allah ka bani ikon gamawa lafiya, Ameen

*DON ALLAH IDAN KIN GANI KI TAYANI SHARING*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

Shafi na 1

_________________Zaune su ke su uku, mata ne masu matukar kyan gaske farare sol, yan duma-duma dasu za Masha Allah, ko wacen su na aikawa juna harara matan Ahmad ke nan, daya mai suna Harira daya Hadiza dayan kuma mai suna Hafiza, ko wacen su na matukar son mijinta mai suna Ahmad kullum ko wace daga cikin su burinta shi ne ta aikata wani abu wanda zai burge Ahmad.

 

Dayan tsafta ne da ita fiye da tunanin mai tunani waton Harira, Harira akwai tsafta ba kadan ba, ga ta akwai biyyaya da ladabi idan miji ya ce a’a to shi ke nan a’a din ne, idan kuma ya ce ‘e’ to ‘e’ din ne sam bata masa gardama.

 

Hadiza kuwa idan ana maganar girki to ita din gwana ce a fanni girke-girke idan ta girka maka abinci to ba za ka so wata y’a mace ta sake girka maka ba, kan daddadan dandanon girkinta, ga iya tarairayar miji

Ita kuwa Hafiza akwai iya kwanciyar aure, style kala-kala ba wanda bata iya ba fannin jiyarda miji dadi, idan aka zo wajenta to fa dole a tsara mata, amma kam akwai ta da rashin mutunci sam bata gudun bacin ran Ahmad, wannan ke nan.

 

“Wulakancin banza wulakancin wofi yau mijina a dakina ya ke, to me zai sa ku wani dau wanka tamkar miji a dakin ku ya ke, har dai ke Hafiza din nan, sai wani yauki ki ke tamkar miji a dakin ki ya ke” cewar Harira ta na aikawa Hafiza harara.

 

Idan gina ya tanka ta to Hafiza ta tanka, Hafiza banza ta yi da ita tamkar ba ta san ta na yi ba, kafin daga bisani ko wace ta shige dakinta sanin ce wa lokacin dawowan Ahmad ya kusa, Harira da tuni ta gyara gidan tassss ta gyara ko ina na gidan ta sake daukar tsintsiya ta share parlourn wanda yau ta share shi ya fi sau a kirga tsafta kan idan an zo gun Harira to fa dole adurkusa mata sai ta share gidan sau goma a wuni bata damu ba in har ranar girkinta ne.

 

Share parlourn ta yi fes fes fes ta goge ko ina, ta jona burner, nan ta ke ko ina na gidan yau dau kamshin turarenta mai matukar daddadan gaske, Ahmad shigowa parlourn ya yi dauke da sallama a bakinsa amma Harira ba wani tarairaya ba wani yauki ko shagwaba irin na manyan mata masu aji, shi kuwa Ahmad abun baya masa dadi.

 

 

Amma jin wani irin daddadan kamshin da parlourn ke yi, ya sanya Ahmad mance b’acin ransa, “kai my sweet Harira shi ya sa nake kara sonki a koda yaushe ba dai tsafta ba, wannan irin kamshi kuma fa? yau kuma ya sunan wannan turare naki? gaskiya ni na yi sa’a da mace mai tsafta a rayuwar aure, Allah ya yi miki albarka Harira na” Ahmad ya fada ya na mai rumgumota a jikinsa, nan kuma naga ya cika ta ya shiga dakin Hafiza.

 

 

Hafiza ko gaisuwa babu ta shiga tambayarsa, “Ahmad ina alkawarin da ka mun a daren jiya?” Cewar Hafiza ta na mai mika masa hannunta alamar ya bata “Haba Hafiza ko gaisuwa babu? To ai alkawarin ne na zo na cika miki” Ahmad ya fada ya na mai sakan mata murmushi, “to ka bani” Hafiza ta sake fada fuska a daure, wani sarkan gold naga Ahmad ya mika mata wanda kudinsa zai kai dubu dari biyar, “wowww nagode sosai Ahmad dina Allah ya saka da alkhairi, ina sanar da kai da yardar Allah daren gobe zai fi na jiya dadi Hafiza ta fada ta na mai shagwabe masa murya, “to my sweet Hafiza haka na ke son ji” cewar Ahmad farin ciki bayyane a fuskansa, bai fi minti goma a dakin nata ba ya fito ya shiga dakin Hadiza.

 

Hadiza kwance ta ke saman royal bed dinta domin kuwa acikinsu kusan mahaifinta ya fi na sauran kudi sosai, Hadiza ganin shigowan Ahmad dakinta yasa ta yi saurin saukowa daga kan gado ta na masa oyoyo ya yin da ta kai masa rumguma ta na wani zuba masa yauki murya a shagwabe, ta shiga gaishe shi, ya yin da ta zaunar dashi a gefen gadonta, ta nufe dan karamin fridge dinta da ke cikin dakin, ruwa masu matukar sanyin gaske ta zuba masa a cup ta shiga bashi a baki, Ahmad lumshe ido ya yi, sanyin ruwan na ratsa mishi zuciya, ya sauke wani irin nannauyin ajiyar zuciya tare da ce wa, “Hadiza Allah ya yi miki albarka”………..

 

 

Mu je zuwa💃

Taku a koda yaushe Mom Juwairiyyah😍 Sahibar👸Royal Star🪄 ce
*🤍🤍WACE CE YAFI SO🤍🤍*
(Gajeran labari ne)

 

TSARAWA DA RUBUTAWA

_Maryam Yusuf Ummu Juwairiyyah {Sahibar👸Royal Star🪄}_

~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
*🌟ROYAL STAR WRITER’S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~

Ban yi alkawarin posting a koda yaushe ba🧏‍♀️

wannan book kirkirarren labari ne idan hali ya zo daya katari ne aka yi.

Deducted to UMMUSALMA SANI SALMAN (Yar lelen royal star🪄)

 

Special gift to (NANA SMILE) ina yinki sosai Aunty Nana a duk in da ki ke, miss you so much

 

Da sunan Allah mai rahama mai jin k’ai amincin Allah su kara tabbata ga fiyyayen hallita Annabi Muhammad (S.A.W) Allah ina rokon ka yanda ka bani ikon farawa lafiya Allah ka bani ikon gamawa lafiya, Ameen

*DON ALLAH IDAN KIN GANI KI TAYANI SHARING*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

Shafi na 2

________________Ita ma irin sarkan gold din da ya bawa Hafiza naga ya mika mata, Hadiza da duka hannunta biyu tasa ta karba tare da nuna masa jin dadinta nan da nan ta shiga kwarara Masa ruwan addu’a “Ubangiji Allah ya saka maka da alkhairi mijina Allah ya biya ka da gidan aljanna, Allah ya yi maka katangar karfe tsakanin ka da makiyan ka, Allah ya cigaba da tsare muna kai I love you so much Ahmad dina” Hadiza ta fada ta kasa boye farin cikinta. “Ba komai my sweet diza Allah ya yi miki albarka” cewar Ahmad ya yin da ya bar dakin amma kam ita ya kusan minti ashirin a dakinta.

 

Dakin Harira naga ya nufa kasancewar girkinta ne, Harira har ta shirya ko ina na dakinta fes fes har ma ya fi parlorn daukar kamshi, ko ina na dakin kamshin turare mai matukar dadin gaske ya ke, ita kanta Harira wani irin shu’umin kamshin dadi ta ke, kasancewar ita sam bata wasa da turare, ita fa komai na gyaran jiki idan ka zo gunta to ka gama samu, tsafta kam ya gaji da samun muhhali a wajenta sam bata yarda ka ga wani abu na kazanta a gunta shi ya sa Ahmad a kullum ya ke kara sonta.

 

 

Ahmad ko da ya shigo dakin latsar wayan hannunta ta ke, bata ko kalle gefen da ya ke ba, belle har ya samu wani abu wai shi hug daga wurinta ba, ita dai cigaba ta yi da dannan wayan hannunta, da gani chatting ta ke kuma ya na mata dadi.

 

 

Shi kam rage kayan jikinsa ya yi ya shiga toilet ya sakan ma kansa shower bai fi minti biyar ba ya fito ya haye gadon, rumguma ya kai mata amma sai ce wa ta yi, “wayyo Ahmad ka kyale ni wallahi ba na jin dadin jikina, Allah yau na yi aiki da yawa duk na gaji” ta fada ta na mai marairaice masa fuska” Ahmad lallashinta ya shiga yi, kasancewar bata masa gardama yasa ta amince, amma fa da kyar aka yi sau daya.

 

 

Kuma ko sau daya din ma shi ke kidinsa shi ke rawansa, “Ki yi haƙuri ki bari na kara pls my sweet Harira” cewar Ahmad, “don Allah Ya Ahmad ka yi haƙuri, gobe da safe zan baka ka kara yanzu bacci na ke ji” Harira ta fada, daman Ahmad ya san haka za ta ce, ba tare da ya matsa mata ba ya kyaleta kasancewar ko ba komai ta na yawan masa biyyaya.

 

Yau tunda ya tashi ya ke jin kamshi wani irin delicious food da bai taba jin irin sa ba, sauri-sauri ya ke ya gama shiri ya fito daga dakin Harira, domin zuwa wannan lokaci kam miyan sa har ya fara tsinke, tun kafin ya tashi da bacci Harira ta gyara dakinta ta ci gayu tamkar ba gobe, dakin sai kamshi ke tashi ta ko ina ita ma kanta sai zuba kamshi ta ke, Ahmad wani irin kamshin dadi wanda ya fi na jiya ne ya doke hancinsa, wani irin kallon ‘Allah ya biya ki’ ya watsa mata, Harira sai murmushi ta ke ta faman jefa masa.

 

 

 

Ita ma irin sarkan gold din da ya bawa su Hafiza da Hadiza ya bata. “Kai Masha Allah, Ya Ahmad duka ni ka dai?, Amma dai wallahi nagode sosai Allah ya saka ma da alkhairi, Allah ya faranta maka yanda ka ke faranta mun rai a koda yaushe” Harira ta fada ita ma ta kasa boye jin dadin ta, “ba komai my sweet Harira, Allah ya kara miki lafiya” cewar Ahmad ya yin da ya fice daga cikin dakin.

 

 

Fitowa ya yi parlor, wa ni irin kallon ‘I love you’ ya jefe ta ganin sai faman gyara dinning table ta ke, da sauri ya nufa gun da ta ke ya kai mata rumguma ya na kissing dinta, “ina kwana Ya Ahmad fatan ka tashi lafiya? Ya kwanan ku? Ina ita Hariran?” Cewar Hadiza “lafiya muka tashin my sweet wife fatan kema kin kwana lafiya?” Cewar Ahmad, “lafiya na kwana amma sai dai kasancewar ban ji ka a gefe na ba, sai na ke jina cikin wani yanayi tamkar wata marainiya” Hadiza ta fada ta na mai shagwabe masa fuska, “bari na kira su Harira mu yi breakfast sa bo da kada ka makara” Hadiza ta fada ya yin da ta nufe dakin Harira.

 

 

Sallama d’auke a bakinta ta shiga dakin wanin irin daddadan kamshin dakin ne ya doke hancinta sai da ta ja dogon numfashi ta na mai kara shakar kamshin dakin, a gaskiya ba kadan kamshin turaren ya mata dadi ba, “Harira ki fito mu yi breakfast” haka ka dai ta iya ce mata, ta fito daga dakin.

 

 

Kafin ta shiga dakin Hafiza ita kam tuni har ta fito, ko wacen su zama ta yi saman kujera dake dining din, Hadiza Ahmad ta fara zubawa abincin ba ta ida bude kulan ba wani irin daddadan dandanon girkinta ya doki hancin su, Hafiza har miyau ke diga daga cikin bakinta ta yi sauri ta goge tun kafin su gani, a gun Harira ma haka ne, ita ma ba kadan kamshin delicious food din ya tafi da ita ba.

 

 

Ahmad tun kafin ta tura masa plate din hannunta ya yi maza ya karba daga hannunta spoon daya ya kai baki ya ji wani irin dadin girkin nan ta ke ya shiga zuba mata ruwan albarka, tuni su Hafiza an yi nisa dadin abincin ya ma sa ta kasa gane me Ahmad ya ke fada ita ma Harira haka ne a gunta sai kwasan girki ta ke ta faman yi, ita kuwa Hadiza zubawa Ahmad lolo eye dinta ta yi ta na fadin “Ya Ahmad a ci sannu” ta na fadi ta na dariya, Ahmad din ma dariya ya yi ba tare da ya iya ce da ita ko alif ba, nan kuma ta shiga mishi tatsuniya ta na bashi labarai masu matukar dadi.

 

 

Nan dai ya gama cin abincinsa ya tashi zai fita, Hadiza ta rumgumo shi ta na zuba masa yauki, tuni su Harira har sun bar dining din ko wace ta wuce dakinta, yauki ta shiga zuba masa kun san halin matan nan dai masu katsaita, “Ya Ahmad dina zan yi missing dinka yau idan ka fita ba dani ba, Allah sai ji nake kamar karka ta fi ka bar ni, sai ji nake tamkar ka tafi dani” cewar Hadiza ta na kara da ce wa……

 

 

Mu je zuwa💃

*Don Allah sis ki yi Comment ki yi share, Ubangiji Allah ya faranta miki ya kuma saka miki da alkhairi yanda ki ka tayani sharing🥰💃*

 

Taku a koda yaushe Mom Juwairiyyah😍 Sahibar👸Royal Star🪄ce
*🤍🤍WACE CE YAFI SO🤍🤍*
(Gajeran labari ne)

 

TSARAWA DA RUBUTAWA

_Maryam Yusuf Ummu Juwairiyyah {Sahibar👸Royal Star🪄}_

~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
*🌟ROYAL STAR WRITER’S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~

Ban yi alkawarin posting a koda yaushe ba🧏‍♀️

wannan book kirkirarren labari ne idan hali ya zo daya katari ne aka yi.

Dedicated to UMMUSALMA SANI SALMAN (Yar lelen royal star🪄)

 

Special gift to (NANA SMILE) ina yinki sosai Aunty Nana a duk in da ki ke, miss you so much

 

Da sunan Allah mai rahama mai jin k’ai amincin Allah su kara tabbata ga fiyyayen hallita Annabi Muhammad (S.A.W) Allah ina rokon ka yanda ka bani ikon farawa lafiya Allah ka bani ikon gamawa lafiya, Ameen

*DON ALLAH IDAN KIN GANI KI TAYANI SHARING*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

Shafi na 3

_______________”Allah ya kai ka lafiya ya kuma dawo mun da kai lafiya” Hadiza ta fada ta na kai masa peck a goshi, “Ameen” ya amsa mata shi ma ya mata kiss a goshi, ficewa ya yi daga gidan domin kuwa har ya soma yin latti, Hadiza komawa ta yi dakinta ta haye gado ta kunna datan wayanta ta fara chatting, can kuma naga ta kashe datan da alama dai ta gaji da chatting din, wsp office ta shiga ta fara karanta wani littafi mai suna *RASHIN UWA NE SANADI* domin kuwa kawarta Amina ta bata labarin littafin ya hadu over.

 

*FIVE (5) HOURS LATER {BAYAN AWA BIYAR)*

 

Fitowa ta yi daga cikin dakin, ta nufa kitchen, gas ta kunna ta fara girkin dare, abinci kusan kala biyar ta sarrafa, garin pounded ta fara tuka domin kuwa Ahmad ya na matukar son pounded sosai, miyan agusi ta yi wanda ya ji naman kai sai wani irin daddadan dandano ke tashi daga cikin kitchen din, daga bisani ta dora tuwon semo da miyan okro (guro) nan ma ba kadan Hadiza ta sarrafa miyan ba, ya gaji da jin kifi, nan ta hada lemon kankana ta hada masa kunun aya, ai nan ta ke gidan ya dau kamshin girkinta.

 

 

Hafiza ce ta fara fitowa daga cikin dakinta ta na ta shinshine shinshine tamkar mazurun (cat) da ya ga bera, Harira kam tun daga cikin dakinta ta dinga jin kamshin girkin ya kaurashe gidan gabaki daya, ita dai wannan mata Allah ya hore mata ilimin iya girki, yanzu kuma ko me ta ke dafa muna?” Cewar Harira ya yin da ta fito daga cikin daki ta zauna a dayan royal chair din da ke cikin parlourn, kasancewar dakin ko wacen su jere da juna yake sai parlour da dining area sai kitchen ko wace na da toilet acikin dakinta.

 

 

Harira harara ta watsa ma Hafiza, don kuwa ta fi jin haushinta a gidan, Hafiza kam ko ajikinta domin kuwa bata ma san ta na yi ba, Hadiza ce ta fito daga cikin kitchen dauke da had’adden warmer’s guda biyu a hannunta, Harira murmushi ta sakan mata tare da ce wa “Hadiza sannu da kokari, har kin kammala ke nan? Don Allah ki dan zuba min” cewar Harira ya yin da ta nufa gun da Hadiza ta ke, “to ai sai ki zo ki zuba da kanki” Hadiza ta fada ba tare da ta kalle ta ba.

 

 

Ai kuwa Harira plate ta d’auko ta shiga zuba tuwon semo da miyan guro, ta zuba kunun aya a jug ta wuce dakinta, don kuwa ta san Ahmad baya cin abincin dare a dining area sai dai ya ci a dakin wace ta ke da girki a ranar, shi ya sa bata ma wani jira dawowansa ba, ita kuwa Hadiza kitchen ta shiga ta ɗauko sauran warmer’s din ta shiga dakinta dasu, ita ma Hafiza dining area ta nufa ta shiga zuba nata abincin a plate sai da ta cika plate din din dim da pounded sannan ta zuba juice din kankana da kunun aya a kofi ta shiga dakinta.

 

 

Hadiza ko da ta fito parlour duk basa nan, murmushi ta saki, ta dan gyara parlourn sama-sama, ta na tsaka da gyara parlourn sai ga shigowan Ahmad gidan, Ahmad kallon parlourn ya shiga yi, nan ga pilon kujera yashe can ga remote, ko ina dai kaca kaca ba wani gyara, Hadiza da sauri ta je ta rumgume shi ta na fadin “Oyoyo kalbeee, fatan ka dawo lafiya ya hanya? Cewar Hadiza, bata bari ya amsa mata ba, ta shiga kai mishi kiss ta ko ina ta na wani shishigewa jikin shi, ai kuwa nan da nan Ahmad ya manta da wani zancen ba a gyara parlourn ba, janyo shi ta yi har cikin d’akinta, ta ce “Yaya Ahmad na zuba muna abinci ko?, Da yake ma wanka yakamata ka fara yi” Hadiza ta sake faɗa ta na mishi kallon I miss you.

 

 

“A’a bari ina zuwa” cewar Ahmad, dakin Hafiza ya fara shiga ko sannu da zuwa babu, shi ne ya fara yi mata sannun da gida, sama-sama ta amsa masa, bai fi minti goma ba ya fito daga cikin dakin, ya nufa dakin Harira, as usual ko yau din ma wani irin mugun shegen kamshi ne ya doke hancinsa, wani irin kallon ina matukar kaunar ki ya watsa mata, ita ma Harira fuskanta d’auke da murmushi ta shiga gaishe shi, ita ma bai fi minti goma ba ya fito daga cikin d’akinta ya koma dakin wace ta ke da girki, waton Hadiza.

 

 

 

Abinci ta zuba mishi, ya na ci ya na santi, sai faman saka mata albarka Ahmad ya ke ta yi, ita kuwa duk bayan loma uku sai ta bashi kunun aya ko kuma lemon kankanan da ta had’a mishi, haka dai ta dinga mishi har ya kammala cin abincin, bandaki ya shiga ya watsa ruwa, ya fito wasa ya fara mata amma sam Hadiza bata iya ba, ta ki ta sake jikinta dashi, romance dinta Ahmad ya shiga yi, amma fa ta ki maida masa martani.

 

 

D’aukan ta ya yi cak ya haye gado da ita, ya shiga cire mata kayan jikinta, nan fa Hadiza ta fashe da kuka ita dai kar ya yi having sex da ita ba ta cikin mood, haƙuri Ahmad ya shiga bata da kyar da boni ta iya yarda ya yi sau daya da ita, sai wani hade kafa ta ke ta faman yi, ta ki ta bude kafanta da kyau, Ahmad addu’a ya dinga yi safiya ta waye ya koma dakin Hafizan sa domin kuwa ya san ita ko da sau goma zai yi baza ta taba hana shi ba.

 

 

 

Gari na waye ya duba gefensa bai ga Hadiza ba, murmushin gefen bakin ya yi domin kuwa ya san ta shiga kitchen ne, wanka ya shiga ya yyi shirin zuwa office, shigowa ta yi dakin ta ajiye masa abincinsa da gefe, “ina kwana my sweet, da fatan ka tashi lafiya” cewar Hadiza ta na durkusa har kasa, “lafiya lau alhmdllh, my sweet wifiy da fatan kema haka” cewar Ahmad “ni ma alhamdulillahi” Hadiza ta fada ya yin da ta shiga zuba masa breakfast dinsa, domin kuwa duk ranan da ya kwana a dakinta to fa baya barin dakin har sai ya yi break dinsa a dakinta kafin ya fitowa dining.

 

 

 

Ya na gama breakfast ya fito daga cikin dakin, da ya ke yau Hafiza ce ta ke da girki bata wani dafa musu komai ba, ruwan tea kawai ta iya hada musu sai bread da butter, nan dai Ahmad ya dan ci bread din ba sosai ba ya kora da ruwan tea sannan ya tashi ya fice daga gidan.

 

To fan’s yau fa ranan Hafiza ce😂 ku dai kawai mu je zuwa💃

 

*Don Allah sis ki daure ki yi Comment ki kuma tayani sharing, masu share Allah ya saka da alkhairi👏🥰*

 

 

Ta ku a koda yaushe Mom Juwairiyyah😍 Sahibar👸Royal Star🪄
*🤍🤍WACE CE YAFI SO🤍🤍*
(Gajeran labari ne)

 

TSARAWA DA RUBUTAWA

_Maryam Yusuf Ummu Juwairiyyah {Sahibar👸Royal Star🪄}_

~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
*🌟ROYAL STAR WRITER’S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~

Ban yi alkawarin posting a koda yaushe ba🧏‍♀️

wannan book kirkirarren labari ne idan hali ya zo daya katari ne aka yi.

Dedicated to UMMUSALMA SANI SALMAN (Yar lelen royal star🪄)

 

Special gift to (NANA SMILE) ina yinki sosai Aunty Nana a duk in da ki ke, miss you so much

 

Da sunan Allah mai rahama mai jin k’ai amincin Allah su kara tabbata ga fiyyayen hallita Annabi Muhammad (S.A.W) Allah ina rokon ka yanda ka bani ikon farawa lafiya Allah ka bani ikon gamawa lafiya, Ameen

Wannan page naki ne, ke ka dai my lovely sis Fatima Sani🥰ta cikin group din *Doctor Rumaysa fan’s club* Ina matukar jin dadin sharhin ki, Allah ya faranta miki yanda ki ke faranta min😇

*DON ALLAH IDAN KIN GANI KI TAYANI SHARING*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

Shafi na 4

___________________Hafiza ko gyara dining din ba ta yi ba, ta tashi ta shigewarta daki nan ta hau online cikin wani group nasu ta shiga mai suna *DOMIN JIN DADIN MA’AURATA* group din su Ummu Juwairiyyah ke nan, group din matan aure ne zallah in da ake tattaunawa game da batutuwan da ya shafe zamantakewan aure, da kuma kayan gyaran jiki namu na mata.

 

 

“Aslm” ta tura nan take mutane suka fara mata reply da “wslm” gaisawa ta shiga yi da matan group din, nan kuma ta ce dasu “to yau wane kalar topic ne damu?, don Allah manyan mata ku fito mu tattauna wallahi yau miji a dakina ya ke” nan fa mutane suka fara mata reply, wanna ta ce “ai shirin tsaftace muhhalin mu ne, za’a gabatar wata ta ce a’a shirin dai zamantakewar aure” nan dai suka shiga bata amsar tambayarta, sai ga admin ta fito ta yi musu sallama, ta shiga gabatar musu da lecture’n da suke gabatarwa a ranar, wanda ya tafi kamar haka.

 

“Kamar yanda ku ka sani ce wa lecture’n mu na yau mai taken yanda zaki tarairayar Oga a bedroom, nan dai ta shiga basu lectures masu matukar zafi, sosai Hafiza ta ji dadin lectures din ko ba komai ta karu sosai, nan ta tashi ta jika ruwan kanumfarin da ya zame mata ruwan sha a koda yaushe ta shiga toilet ta yi shelving gashin gabanta da hammata ta shafa turaren miski, uhmm nan da nan ko ina na jikinta ya dau kamshi.

 

 

 

Kitchen ta shiga ta ɗauko katon bowl dinta ta shiga yin wani had’adden hadi na ayaba da gyada da madara peck, hadasu ta yi waje daya ta shanye abunta tass, nan ta shirya cikin wasu kananan kaya, ba kadan ta yi matukar kyau ba, sanin mijin nasu ya kusan dawowa ya sa ta saka kayan don ba ta yi niyan saka komai ba, ta fison ta d’aura towel, to shi kuma Ahmad ba ya so.

 

 

Zaune take saman gado ta yi wani irin wawan zaman ko pant bata da, Ahmad shigowa ya yi parlourn dauke da sallama a bakinsa, ba kowa a parlourn bare a amsa masa, direct dakin Aunty kamshi😂ya fara shiga waton Harira.

 

 

Kamar ko da yaushe yau ma hakan ce ta kasance ba abunda dakin ke yi face wani irin ƙamshi mai matukar dadin gaske, Ahmad lumshe idanunsa ya yi a lokacin da kamshin turaren ya ziyarce hancinsa, nan dai ya yi yanda ya saba yi musu, domin kuwa shi haka nashi dokar take, in dai ba’a dakin ki yake ba, to idan ya dawo daga office dole ne zai shigo dakin ki domin ganin lafiyar ki, bai fi minti biyar ba ya bar dakin ya shiga dakin Aunty dandanos😂waton Hadiza, ita ma bai fi minti biyar ba ya bar dakinta, ya shiga dakin Hafiza sallama dauke a bakinsa.

 

 

Ko amsa masa sallama ba ta yi ba, bare ma ya samu gaisuwa daga gareta, ganin HQ na masa oyoyo yasa ya shiga sakan mata dariya ko ba komai yau akwai kwasan dadi, “Babyna sannu da gida, fatan ki na cikin koshin lafiya?” Sama-sama ta amsa masa ta na cicci mishi magani, dan tea ta hada masa ya dan sha ta kawo masa tuwon semo da miyar danyen kubewa, bai wani iya ci ba sosai, don abincin ba wani dadi ya masa ba.

 

 

Wanka ya shiga, still ta na nan a gun da ya barta, ta na ta faman dannan wayan hannunta, wani irin kallon I’m ready ya gefe ta dashi, ita ma nan da nan ta sakan masa murmushi an tsosa mata gun da ke mata kaikaiyi, Ahmad haye gadon ya yi, tun kafin ya nemeta ta haye shi, ta shiga wasa da gemen shi ta na shafa wuyan shi har zuwa ruwan cikin shi……..

 

 

Mu je zuwa💃

*Ku yi comment ku yi Share don Allah👏🥰*

 

Ta ku a koda yaushe Mom Juwairiyyah Sahibar👸Royal Star🪄
*🤍🤍WACE CE YAFI SO🤍🤍*
(Gajeran labari ne)

 

TSARAWA DA RUBUTAWA

_Maryam Yusuf Ummu Juwairiyyah {Sahibar👸Royal Star🪄}_

~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
*🌟ROYAL STAR WRITER’S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~

Ban yi alkawarin posting a koda yaushe ba🧏‍♀️

wannan book kirkirarren labari ne idan hali ya zo daya katari ne aka yi.

Dedicated to UMMUSALMA SANI SALMAN (Yar lelen royal star🪄)

 

Special gift to (NANA SMILE) ina yinki sosai Aunty Nana a duk in da ki ke, miss you so much

 

Da sunan Allah mai rahama mai jin k’ai amincin Allah su kara tabbata ga fiyyayen hallita Annabi Muhammad (S.A.W) Allah ina rokon ka yanda ka bani ikon farawa lafiya Allah ka bani ikon gamawa lafiya, Ameen

Wannan page naki ne, ke ka dai my lovely sis Fatima Sani🥰ta cikin group din *Doctor Rumaysa fan’s club* Ina matukar jin dadin sharhin ki, Allah ya faranta miki yanda ki ke faranta min😇

*DON ALLAH IDAN KIN GANI KI TAYANI SHARING*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

Shafi na 5

_________________A daren ranar sosai Hafiza ta tafi dashi duniyar dadi, sai da ta tafi dashi Makka da Madina suka dawo sabbatu kala-kala ba irin wanda Ahmad bai yi mata ba, sa bo da tsanin dadinta da yaji, sai da ya yi kusan sau uku ya na neman ta kara masa, ai kuwa ba gardama ta gyara kwanciyarta styles iri daban-daban ba wanda ba ta mishi ba, koda safiya ta waye Ahmad ya kusan makara zuwa office.

 

 

“Wayyo Yaya Ahmad wallahi ban koshi ba, kawai zan kyale ka ne sa bo da karka makara zuwa office” Hafiza ta fada ta na kashe Masa ido daya, Ahmad nan da nan ya ji Ahmad dinsa ta mike ta na neman abincin ta, “wallahi Hafiza shi ya sa nake matukar kaunarki sam ke bakya gajiya dani, Allah nima zanyi kewarki sosai my sweet wife” Ahmad ya fada.

 

 

Hafiza shagwabe fuska ta yi tare da ce wa, “ga shi kuma kai da dawo daki na sai kuma nan da kwana biyu, Allah ni ban koshi ba, gwanda ma mu koma ka kara min” Hafiza ta sake fada ashagwabe. Ahmad suman tsaye ya yi ganin yanda ko ina na jikinta ke rawa, gata nan dai daman yar duma-duma.

 

 

 

Hafiza irin matan nan ne yan duma-duma fara sol masu matukar kyan gaske, gashi kuma ita din Coca-Cola shape ne da ita ko ina na jikinta cif cif cif, to Harira ma ta fita jikin kyau, amma fa ita bata cika son abun ba, ita dai ma Hafiza ba daga baya ba, ta na da jikin kyau sosai sai kuma gata da matukar son abun idan ana yi sam bata gaji, gashi ta san wajeje da dama da zata taba a jikin Ahmad ya ji nan da nan ta gama dashi.

 

 

 

Ahmad sosai yake alfahari da Hafiza sam baya son abunda zai taba ta, kwata-kwata bqya kaunar bacin ranta, idan ta na ciwo kuwa ya rasa natsuwarsa ke nan, baya taba samun sukuni har sai ta samu lafiya duk da wani Abu idan ta yi masa ba kadan yake jin haushi ba, domin mutumiyar fa ba abunda aka iya sai…..😂wannan ke nan.

 

 

Da kyar Ahmad ya iya b’anb’areta daga jikinsa ya mata wayau ya fice daga gidan, ita kuwa Hafiza dakinta ta shiga ta yo wanka, amma sa bo da rainin wayo irin nata sai ta fito parlourn gidan ta na fadin “washhhhh bayanaa wallahi jiya dai na murzu ba kadan ba, Ya Ahmad ya iya jiyarda mace dadi” Harira da wani irin bakin kishi ya tokare mata zuciya ta ja tsaki, tare da ce wa “aikin banza, bakar mayya kawai, zata gama tsose masa ruwan jiki, sai wani washhh din munafuci kike ta yi wa mutane Mtwssssssss” cewar Harira ya yin da ta sake jan wani irin dogon tsaki ta bar parlorn.

 

 

Idan gina ya tanka mata to Hafiza ta tanka, sha’anin gabanta ta cigaba da yi, “yauwa Hadiza don Allah dan taimaka ki tace mun gashin nan nawa, Allah Yaya Ahmad ne ya sa ni wanka har sau biyu,” Hafiza ta fada ta na marairaice fuska, Hadiza harara ta maka mata ita ma ta bar parlorn.

 

 

 

Hafiza wani irin dariyar mugunta ta yi tare da ce wa “Yan bakin ciki kawai, wallahi Yaya Ahmad ya fi so na daku” kara sakin dariya ta yi, tana tuna moment din su na jiya ita da Yaya Ahmad dinta, wani irin latsar baki ta yi, tana tuna lokacin da ta ke masa sucking ya na sabbatu.

 

 

Ahmad ne zaune cikin office dinsa, ya kammala ayyukansa na yau, ya lula duniyar tunani, waton yanzu dai rayuwan gidan sa ya fara damunsa al’amarin matan nasa ya fara ishe shi, dukkansu yana matukar sonsu amma kuma ko wacen su bata cika quality’s din da yake so ba, to a gaskiya yakamata ace ya fara nuna musu gazawarsu game da abunbuwan da suke yi don shi kadai ne zai sa su gyara.

 

 

 

Musmman ma ita Hafiza, shi mai matukar son ado ne sosai ya na matukar son kamshi amma ita Hafiza ko kamshin ma bai dame ta ba, ba ruwanta da turare bare ita Hadiza bai ma taba gani ta da turare ba, yana tsaka da tunani sai ga kiran Hadizan ta shigo wayansa, kada ku manta Hadiza ita ce mai tarairayar miji.

 

 

 

“Hello Hubbyna fatan ka wuni lafiya, ina rokon Allah ya cigaba da tsare mun kai my Habiby, na ji ka shiru ne har yanzu shi ya sa, na ce bara na kiraka ko lafiya, don Allah kayi ka dawo, Allah ina matukar kewanka sosai duk da na san ba’a dakina ka ke ba, amma na san kam zaka shigo dakina ina matukar bukatar ganin ka my zaujil khairi” Hadiza ta fada ta na wani irin yauki tamkar ya na ganinta.

Leave a Comment