Books Reviews & FAQs

Wanda Baiji Bari Ba Hausa Novel

Copied By
YAYA HAYAT
(admin
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
Cool novel, makeup and kitchen1⃣
Cool novel, makeup and kitchen2⃣
AND
Cool novel, makeup and kitchen3⃣)

WHATSAPP NO:+2349030159301
☄
☄☄
☄☄☄
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*WANDA BAIJI BARI BA*
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
☄
☄☄
☄☄☄

*AMEENCI WRITER’S ASSOCIATION* 📚✍🏻

*MEELAT MUSA* 🌹

*PAGE* 1

***
*Rayuwar ƙarya ce tasa ma kanta, sannan kuma bata ɗauki duniya da sauƙi ba, iyayenta basu da hali amma ita ala doƙe sai tayi rayuwa irin ta masu kuɗi, iyayenta basu da hali amma dole sai tayi makarantar kuɗi, ganin rayuwar data ɗauka yasa mahaifiyarta take mata nasiha, amma wanda yayi nisa baya jin kira*

*Ba anan ta tsaya ba, zuwanta makarantar kuɗi yasa taga yanda “ya”yan masu kuɗi suke rayuwa hakan ya ƙara hura mata wutar halin data sa kanta, ta raina cimar gidansu, sannan duk inda taji mai kuɗi ko wani fitattace wanda duniya tasan dashi yanxun nan zatace ɗan uwanta ne,*

*tayi ma duniya babbar iba, saboda haka duk inda ake biki na masu kuɗi ko suna, kana buɗe idonka saika ganta, ba,a nan ta tsaya ba, wannan rayuwar tasa ta cin bashi idan taci bata biya, sannan kuma ta ƙware wajen 4 1 9*

*Ko hutu akayi idan kuɗin makaranta sukai mata tsaye , ko ƙawayenta sunce kwana biyu bata zo ba, sai tace tayi tafiya ƙasashen waje, idan kuma taga mahaifiyarta da abu ta zura mashi ƙahon zuƙa bawai tayi sata ba, ah ah da ƙarfin tsiya zai zama nata*

*Idan kuma taji biki duk inda zataje ta samo kuɗin anko sai tayi, kai wannan wace irin rayuwa ce?”””” hmmm muje dai muji*

****
*W*ani ƙayataccen wurin cin abinci ne, kana ganin wurin cin abincin kasan bana yara bane, wuri ne da aka tanada dan masu kuɗi suxo su more kuɗin su , dan mai waƙa yace kuɗi da maciji maganin su kashewa,

Jawwahir a gefe zaune tare da wata tsohuwar fitilar kwai kusa da ita, a gabanta kuma ga lafiyayen abinci da lemu, wayarta a hannunta a kunnenta kuma ta saka earpies, glass ɗin idonta ta cire ta ajiye a gefe sannan ta fara cin abinci,

Tana ci tana latsa wayarta, saida ta gama cin abincin tsaff sannan tasha lemon ta, jakarta ta jawo taga duka naira 100 ne a ciki, murmushi tayi sannan ta tattara kayanta ta tashi a wurin,

Saida ta miƙe tsaye har ta fara tafiya sannan tasa glas ɗinta a fuskarta, inda ake biyan kuɗi taje, ta tambaya nawane kuɗinta?”” dubu biyu, tace okey,

To yanxun gaskiya banda kuɗi a hannuna dan shigowata gari kenan tana magana tana taɓe baki, taci gaba da cewa kaga abinda ya bani wahala nan, ta ɗaga fitiƙar kwan hannunta, tace ka taɓa ganin ta ne?”””

Yace Eh, tace ko kana da irinta ne?”” tana magana tana ɗan buɗe idanuwanta yanda take maganar ta nuna abun yana da mahimmanci, yace banda irin ta, jawwahir tace ashsha, ai yanxun nemanta ake, idan ka kawo ta miliyan ɗaya cass za”a baka, dan akwai wani abu da turawa suke nema a cikinta,

Nan nigeria ne ake bamu ita mu bayar da miliyan ɗaya mu kuma idan muka kaita ƙasashen waje muna samu miliyoyin kuɗi, ɗan tsaki tayi sannan tace riƙe fitilar inje in ciro kuɗi a banki in dawo,

Yace to ya karɓi fitilar ita kuma fita tayi, tana fita shi kuma yaji ance miliyoyin kuɗi ake siyen fitila kuma tace daƙel ta samo ta, saboda haka sai ya ɗauke fitila yaje ya ɓoye,

Jawwahir tana fita ita kuma, bata sharce ko ina ba, napep tahau, ta faɗa mashi inda zai kaita, ya ɗauketa suka tafi, bayan sunje ta sauka wata super market ta shiga, tana shiga wurin wani taje ta bashi wayarta tace ya riƙeta ya bata dubu ukki yanxun nan zata dawo,

Yace to, karɓar wayar yayi sannan ya bata kuɗin, ta dawo ta hau napep tace ya mayar da ita inda ya ɗauko ta, yace to, suuuuuuuuu har suka iso wurin,

Bayan ya ajiyeta, ta sallameshi , da sauri ta shiga wurin, inda ake biyan kuɗin taje cikin sauri tace yawwa malam ga kuɗink bani fitalar sai waya ake yo man, ana jirana, ɗan dube dube ya shiga yi wai baiganta ba,

Idanuwa jawwahir ta zaro tace lallai babu zaman lafiya, domin anan waa yanxun nan ance man an ƙara man dubu ɗari biyu akai saboda haka ko fitilata ko kuma insa a kulle man kai,

Yace haba hajiya ai duk abun baikai haka ba, yanxun tunda ta ɓata sai mu raba asara, idanuwa jawwahir ta zaro tace asa me?”” aini bansan asara ba haka kuma bansan ƙaddara ba,

Kawai fitila na zaka bani, yace hajiya kiyi haƙuri bara in baki dubu ɗari takwas kiyi haƙuri da hakan tunda ƙaddara ta faɗa mata don Allah, tsaki jawwahir tayi sanna tace nidai kawai kaja man asara, amma banda yanda zanyi bani, amma bana karɓar ceak zunzurutun kuɗi nake so, yace kada ki damu, ina zuwa,

Tafiya yayi ya shiga wani wuri, bayan wani lokaci yazo da kuɗin ya bata, ta karɓa, ta irga, sannan tayi tafiyarta daga wurin, tana fita ya ɗauko fitalar yace banza, sai inkai in samu kuɗina, niko nace ba jawwahir bace banza kaine banza,

Jawwahir tana fitowa ta hau abin hawa, inda ta bada wayarta taje, ta bashi dubu ukkun data karɓa, shi kuma a bata wayarta, sannan tayo gida da kuɗin ta jimmm a jaka,

Tana dawa gida, ko sallama babu haka ta shige ciki, inna tace jawwahir ki dawo ?”” tace umm, ɗaki ta shiga ko takalmin ƙafarta bata cire ba, ta haye saman gado, kuɗin ta fiddo ta sake irgawa, sannan ta kece da dariya tace jakki dan uwarka idan miliyan ɗayan gaskiya ne, zan barka haka ne ka bani dubu ɗari takwas?”” uhm Allah yasa kaje da fitilar wani wuri a zaneka , daria tayi sannan ta haɗa kan kuɗinta ta ajiye, wayarta ta jawo ta fara kiran wata ƙawarta,

Bayan sun gaisa tace mata gobe insha Allah zan shigo sch kinsan bana nan naje *solvenia* jiya na dawo, tace Allah ya kaimu lafiya, tace ameen,

 

Kam lallai wannan wace irin rayuwa ce? 🤔uhum muje sannu a hankali,
☄
☄☄
☄☄☄
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*WANDA BAIJI BARI BA*
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
☄
☄☄
☄☄☄

*AMEENCI WRITER’S ASSOCIATION* 📚✍🏻

*MEELAT MUSA* 🌹

*PAGE* 2

*Allah ya baki lafiya halima yahya ubangiji yasa zakkar jiki ne, Allah ya baki ladar jinya*

*****
*J*awwahir saida ta gama latse latsen wayarta tana kiran ƙawayen ta cewa ta dawo daga *solvenia* sannan ta cire kayan jikin ta, towel ta ɗauro ta fito tsakar gida,

Saboda gayunta da iskancin ta, inna haka ne sunan da suke kiran mahaifiyarsu dashi, amma ita haushin yayyen take ji da basu kiran ta da irin *momsy* irin su *momy* ko *mama* ko *ammi* ko *mami* ko *mamma* ita wannan abun baƙin ciki yake mata, saboda haka ita idan zata kira *inna* saidai tace mata *innasco* ko kuma tace *innas* ita ala dole sai tayi gayu, a cikin ƙawayenta kuma idan tana bada labarin gidansu zata *mom* ɗin da *dad* haka take cewa,

Jawwahir tana fitowa ta kalli inda inna take zaune tace innas lafiya naga kinyi jugum?”” sai kace an aiko maki da saƙon mutuwa, inna tace ai da saƙon mutuwa aka turo man zaifi man sauƙi akan turbar da kika ɗora rayuwarki, tsaki awwahir tayi tace ai ku matsalar ku kenan baku ma mutum fatan alkairi kullum sai addu”ar ƙaryarshi ta ƙare,

Kujera ta samu tayani gulma ta zauna tana kallon inna tace innasco lura da wani abu ɗaya a rayuwa ita fa dama kika ganta so ɗaya take zuwa a rayuwa,

Yanxun dana biye maku haka zan zauna babu ilimi, tunda shi wancan tsoho Allah yasa matatciyar zuciya ne dashi baya iya nema ya wani ɓige da kasa icce a bakin titi, sai inje in nemo,

Bakinta ta taɓe sannan tayi ƙasa da maganarta cikin yanayin kuka tace ni wallahi kunya ma nake ji ace shine babana,

Idanuwa inna ta zaro tace iskancin naki har yakai nan kuma?”” jawwahir tace ai tuni na wuce nan, ke innas ashe baki karatun jawwahir daidai,

Inna tace idan kina
rufa ma kanki asiri ki daina wannan rayuwar ki bari, ita rayuwa duk abinda Allah ya nufa zaka samu saika sameshi, idan kikai haƙuri kika zauna a gida Allah zai kawo maki,

Jawwahir tace wallahi babu abinda zan samu idan na zauna shin yauma nake zaune gidan ne?”” ai kinga ban samu ba, amma idan mutum ya miƙe zaiga samu idan kuma ya zauna zaiga zama,

Miƙewa tayi tsaye ta ɗauki kwandon wanka, tace wallahi innas wancan awakin naki idan basu daina man kuka idan ina waya ba Allah duk sai na tattara “yan iska na siyar, danni yanxun ina gama makarantar nan zanje inje in samu aiki , kuma mota zan siya,

Inna tace aikin uwarki, wane sakarai zai ɗauke ki aiki da takardun ƙaramar makaranta, { secondry sch } jawwahir tace innasco baki san ɗiyar taki takai ba, ai wani babban comparny ne, za”a ɗauke ni aiki na baban abokina ne,

Inna tace baban abokin ki kuma?”” tsaki jawwahir tayi tace ai wanda baije makaranta ba baya ganewa shi yasa nace ki koma ko yaƙi da jahilci kiyi dan idan na faɗi magana ki riƙa gane inda tayi………””” daga nan bata sake magana ba ta shige bayi,

Ajiyar zuciya inna tayi tace Allah ubangiji ya shirya ki, ina dabbonta suke ta kalla wasu hawayen baƙin ciki ya zubo mata dan tasan rabuwarta dasu yaxo, tunda har jawwahir tace suna mata kuka idan tana waya,

Inna tace to nidai ai ba bakinsu zan ɗaure ba, amma dole inma Sadiq waya yaxo yaci uban yarinyar nan,

Da “yar waƙa ta fito daga cikin kewayen , haka ta taho tana raira waƙarta har ta shige ɗaki, inna ta bita da kallo tana mata addu”ar shiriya, inna tace Allah sai ya baka “ya”ya amma kowa da irin halinshi, Allah ubangiji ka shirya mana zuri”a, lokacin da inna ta jiyo jawwahir ta kunne waƙa da sifiku ta ƙure volume, tashi tayi daga wurin ta nufi wurin bisashen ta dan basu abinci,

Jawwahir tana gama shirinta, gado ta haye, dan ita ko sallah bata tsayawa yi bare ma tayi ma kanta addu”a,

Inna kuma tana fitiwa daga garken awakinta, waya tayi ma sadiq yaxo tana neman shi, yace to amma baya gari idan ya shigo insha Allah zaizo saboda yanxun dare yayi inna tayi amshi addu”a da fatan dawowa lafiya,,,

*******
*T*unda safe jawwahir tana tashi wanka tayi ta fara shirin tafiya makaranta, dan suna shire shiren fara s s c e, sabida haka kuma ta samo kuɗin da zata biya na jarabawa, inna ce ta shigo ɗakin da rubar tuwo a hannunta,

Gaban jawwahir ta ajiye tace kici tunda ban dama koko ba, wata “yar munafikar dariya jawwahir tayi daidai lokacin da take ɗaure zariyar wandon ta, tace hajiya innasco kenan, waye zaici wannan ?”” inna tace ke,

Idanuwa jawwahir ta zaro tace Allah ya sawaƙe inci tuwo ke yanxun don Allah innas baki man faɗa inci tuwo in tafi abun tsotsayi inyi amai ai kin gama ja man raini wallahi , dan gajeren tsaki tayi daidaii lokacin data ɗauki jakar makarantar ta tayi gaba,

Tana fitowa baba ta gani ba tare da ta kalli inda yake ba tace barka da aafe *babasco* tsaki baba yayi sannan yace zo nan dan uwaki , ɗaure fuska jawwahir tayi sannan tazo gaban baba tayi mashi tsaye, yace haka zan gaya maki magana tsawonki ya kere nawa?””” sauri nake na makara makaranta idan na dawo na biyo ta kasuwar, bai sake magana ba, ita kuma ta fice daga gidan………………

 

Inna ce ta fito daga ɗaki tace kayi haƙuri yau zansa sadiq yayi mata shegen duka dan mu huta kwana biyu, baba yace Allah dai shirya ubangiji ka shirya mana zuri”a, ameen,

 

 

Fatan alkairi gareku masoyana, 💋 kune alfaharina farin cikinku shine nawa, 💋
☄
☄☄
☄☄☄
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*WANDA BAIJI BARI BA*
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
☄
☄☄
☄☄☄

*AMEENCI WRITER’S ASSOCIATION* 📚✍🏻

*MEEELAT MUSA* 🌹

*PAGE* 3

*****

*J*awwahir tana fita ƙofar wani gida ta tsaya, tana daɗe tana tsaye sannan wata ƙatuwar mota ta fito, da sauri ta matsa kusa da motar glass ɗin motar ya sauƙe, tace haba don Allah kayi sauri wallahi ina ganin kamar na makara yau,

Murmushi yayi sannan yace to shigo muje, da sauri ta zagaya ta buɗe gaban motar ta shige shi kuma ya figi motar a 360, ƙura kuma tayi masu rakiya,

Wannan daya ɗauki jawwahiri maƙotansu ne, iyayenshi basa zama a gari sosai shi kuma yana zaune sabida karatu yake, kuɗi garesu sosai a gidansu, jawwahir taxo ta nemi alfarma ya taimaka ya rufa nata asiri ya riƙa kaita makaranta,

Dan bata shiga makarantar ba sai da tayi j,s,c,e sannan ta shiga makarantar kuɗi, to shine yake taimakawa yakai ta, idan bai samu lokaci ba ko yana rashin lafiya idan taje makaranta zata ce yayanta baya lafiya, sunan sa *ja”afar* saboda tsabar yaudara take kiranshi da *honey j* dan tace ɗan yayan dad ne, kuma dad ɗinsu yake riƙonshi, tace ya mutu kanta ita kuma bata aurenshi gaskiya,

Lokacin da suka isa makaranta ya ajiyeta ,godiya tayi mashi sannan ta fita, tana fita ya tafi, ita kuma ta nufi gungun ƙawayenta, sai sannun da zuwa ake mata tare da fatan ta dawo daga *solvenia* lafiya,

Wasu kuma suna cewa ina tsaraba, jawwahir tace tsaraba su bari sai an tashi sch kowa ya faɗi abinda yake so sai ta siya masu, haka dai ta tusa su gaba taci gaba da zungura masu ƙarya, wai su dad da mom sun tafi *australia* da tare zasu amma saboda exam da zasu fara ne ba”a tafi da ita,

Amma tana gamawa zata bisu dad yace su haɗu a *edmonton canada* haka dai taci gaba da zazzaga masu ƙarya, daga baya kuma tace wata ƙawarta hafsat babu biki ne?”””

Hafsat tace akwai biki mana amma ankon yayi tsada da yawa jawwahir tace ba damuwarta bane, nawa ne kuɗin ankon shin inane ma ake bikin inji idan yaman?”” hafsat tace gidan tsohon gomma ne, jawwahir tace haba zamu fasa ,

Nawane kuɗin?”” hafsat tace gaskiya idan dai zakije kawai hajiyata ware ma bikin nan dubu ɗari ukku in haɗo maki ankon farty da deaner, murmushi jawwahir tayi sannan tace idan mun tashi sch zan baki, ƙawayen su dake wurin suka ɗauki shewa yayi masu mura ai suke da majina, taken da suke wa jawwahir kenan, dariya tayi sannan suka wuce class,

Lokacin da, aka tashi break taje ta biya kuɗin jarabawa , ta dawo class,

Ana tashi makaranta kuma ta tattara ƙawayenta suka tafi wata super market tace kowa ya ɗauki abinda yake so, haka kowa ya zaɓi abinda yake so, su dama “yan gayu anci komai a gida an ƙoshi saboda haka choculets suka ɗauka da ɗan abinda dai mutum yayi ra”ayi,

Haka akai mata bill kuɗi masu yawan gaske ta biya, tunda tana da kuɗin da tayo danfara jiya, bayan sun gama ta bada dubu ɗari ukku kamar yanda hafsat tace, haka sukai ban kwana kowa ya kama gabanshi,

Napep ta hau tayo gida, tunda ga nesa ta hango ƙofar gidansu da mutane, tsaki tayi sannan tace shege idan dai kaine ko uwarka ta dawo duniya bazan bayar da kuɗin nan ba,

Tana isowa, taga malam sani , yace yawwa ga “yar banzar nan ta dawo, jawwahir tace kaine ɗan banza, ni ba ɗiyar banza bace da sadaki aka auro uwata ta haifi ɗiyar sunna, malam sani yace bani kuɗina, jakarta ta buɗe tace kaga ina da kuɗi?”” yace Eh tace to na ƙarfin babbar bala”i ne idannkana da wanda ya tsya maka yazo ya karɓa,

Babanta yace ke jawwahir basu kuɗinsu kinsa an tara man mutane a ƙofar gida cikin unguwa duk inda na wuce ana zagina, dariya jawwahir tayi sannan tace kaine kaci bashin?””” yace ah aha, dafa ƙirjinta tayi sannan tace nice naci bashi kuma bazan biya ba,

Malam sani yace ai shi yasa na taho maki da hukuma, dariya jawwahir tayi sannan ta kalli inda “yan sanda suke tsaye tace da wa”an nan “yan iskan kuratan ka ɗauko man wanda idan na hunce duk saina masu jegen duka, baba yace jawwahir basu kuɗin su, yace dubu goma ne, jawwahir tace 10k ne kuma wallahi idan dai wanda ya mutu zai dawo to zan bayar da kuɗin nan,

Inda “yan sanda suke taje jakarta ta buɗe ta basu 5k tace suje susha ruwan sanyi, ana basu kuɗi suka wuce daga wirin, inda malam sani yake ta kalla sannan tace ɗan tsoho ka bani kunya saboda dubu goma kake ta wani tada jijiyar wuya,

Idan ka bayar da zakka ya kake ji?”” malam sani yace ai wannan haƙƙin Allah ne na fitar jawwahir tace nima shine ka bani, na gode, tana faɗin haka tayi cikin gida, malam sani yayi ta Allah ya isa, sannan ya tafi,

Lokacin da jawwahir ta shigo gida sadiq ta gani zaune da wasu irin dorinai a gabanshi , gabanta ya faɗi amma ta basar ta wuce, zata shiga ɗaki yace ke zonan dan uban da ya haifeki, dariya tayi sannan tace nifa nace ka fita a harkata idan ba haka ba wallahi zansa a ɗaure man kai,

Yace bazan fita harkar ba dan ubanki, tace kada ka sake zagina, yace zaki rama ne?””” tace ɓacin rana ake gudu, yace to nace ubanki, tace kaima ubanka tunda uba baifi uba ba, tana magana tana burguɗa baki, lokacin data zage shi, wani ɓacin rai ya baibaye mashi zuciya, dorinar ya ɗauka yaci gaba da zabzabga mata babu ji babu gani, tun jawwahir tana iya rama wa har tayi laushi sannan yace kuna dan ubanki kin daɗe baki kwashe awakin kika siyar ba,

Murmushi tayi cikin yanayi wahala tace wato saboda wa”ancan mayunwatan tumaki aka dake ni?”” yanxun na gane dalili, girgiza kanta tayi sannan tace da kyau, har yanxun tana wurin ta kasa tashi, sadiq shi kuma fita yayi yabar gidan,

Yana fita jawwahir cikin wahala da nishi tace wallahi tunda kika sa aka dakeni saina siyar dasu kisa a kasheni don Allah, kuma daga yau kada ki kuskura ki sake man magana tunda baki kauna ta, inna bin jawwahir tayi da kallo, ta tashi a gajiye tayi ɗaki,

Tana zuwa kayanta ta cire sannan taje tayi wanka, bayan ta shirya waje ta fita ta kira almajiri ya wanke mata kayan makarantar ta, tana bashi tayi waje………………………

 

 

 

Ku kasance tare dani💋
☄
☄☄
☄☄☄
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*WANDA BAIJI BARI BA*
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
☄
☄☄
☄☄☄

*AMEENCI WRITER’S ASSOCIATION* 📚✍🏻

*MEELAT MUSA* 🌹

*PAGE* 4

****

*T*a daɗe da fita sannna ta dawo da wasu mutane guda biyu , inna ta fito daga ɗaki tace wa”an nan fa?”” mutane da jawwahir ta shigo dasu tace kada wanda yayi mata magana, nuna masu wuri ta fara yi, wai nan zasu gina mafa ɗakinta,

Inna tanajin anyi maganar gina ɗaki, ta tsaya tana kallon jawwahir, inna ta kasa haƙuri tace jawwahir wane irin gink zaki kuma?”””” ɗaure fuska tayi sosai sannan tace ba nace kada ki sake man magana ba?””” tana maganar tana zaro ido sai kace itace uwar inna ce ɗiya,

Inna tace ai ba gidanki bane bare kice zaki gina ɗaki, sai ki bari sai kinyi naki sannan kiyi yanda kika dama,

Baba ne yayi sallama ya shigo gidan, ganin mutane tsaye a gidanshi abin ya bashi mamaki, kallon inna yayi yace mata lafiya?””” inna tace wai jawwahir ce zata gina ɗaki, baba ya kalli jawwahir yace ɗakin uwarki zaki gina?”””

Nan gidana ne, nine na siyi abuna ba wani ya siya man ba, yana magana yana ɗaga hannunshi alamar nuna faɗin gidan shi da kuma jaddada ma jawwahir gidan gashin kansa ne ba na wani ba,

Jawwahir tace to ai kasan ina da gadonka ka ko?””” baba yace ai sai ki bari saina mutu sannan, jawwahir tace abinda nake jira amma naga har yanxun nesa bata zo kusa ba,

Baba kallon jawwahiri yayi sannan ya nuna kanshi yace ni kike ma fatan mutu?”” jawwahir tace idan baka san mutu sai a raba gadon gidan a bani kaso na, baba yace aiko na mutu baki gado na, dariya jawwahir tayi sannan tace hmmm dama wanda ya mutu zai dawo, daka ga yanda zan mayar da gidan nan idan ka mutu,

Ta ɗaga hannun ta alamar nunawa zansa a ruguje gidan nan kaff, ayi man ginin zamani sannan kuma duk bangon ko wane ɗaki zansa a ɓarke manshi a maƙala man *AC* insa ƙaton get da arna masu gadi, sannan kuma ina karnuka su riƙa gadi na,

Baba yace kinyi asara tunda kare zaiyi gadin ki , murmushi jawwahir tayi sannan tace ba asara bace jin daɗi ne, kai kuma sannan kana can ciki kabari an danne mana kanka da ƙasa, ni kuma in haye saman kujeru na alfarma in riƙa asawaki da naman kaji,

Baba yaji anbun yafi ƙarfinshi saboda haka yace gida dai tunda gidanshi ne babau ubanda ya isa yayi mashi gini, itama ba ta sake ma baba magana ba, ta juya taci gaba da magana da masu aikin gina mata ɗaki,

Saida suka gama sannan ta sallamesu gobe suxo su fara mata aiki,

Yinin ranar haka jawwahir ta yini tana ta “yan maganganunta, saida taje wajen garke tumakin inna ta tsine masu albarka , inna dai batayi mata magana ba,

Da daddare inna garin kwaki ta jika da ƙulli, duk kashedin da jawwahir tayi ma inna bata jiba saboda haka garin ta zuba tace mata gashi taci, jawwahir ta ɓata fuska kamar zatai kuka tace lallai innas yau na tabbatar baki kauna ta, ni zaki jiƙa gari ki bani?”””””

Tun ina karama banci abu mai gina jiki ba, yanxun na samu na ɗan fara cin kaji da lemo da yought mai kyau ni zaki kawo ma gari inci ya shanye man jinin jiki?”” hmmm aiko awakinki kika bawa wannan garin kin ɗauki alhakinsu bare ni da kike taƙamar kin haifa, inna dai batayi magana ba haka jawwahir ta ƙare iskancinta inna bata sake magana ba,

Har 10:02pm jawwahir na tsakar gida, inna tace taxo ta kwanta tace bata ƙara shifa ɗakinta sai an gina mata nata, inna tace ga tabarma ki kwanta, jawwahir tace barta yau a tsaye zan kwana, inna ta shige ɗaki tabar jawwahir tsakar gida, haka ta gaji da tsayuwa ta kwanta ƙasa,

Da safe kuma a ƙofar ɗakin inna taje tace ta miƙo mata kayan makarantar ta, dan baza ta sake shigowa ɗakin ba, inna ta tattaro kayan ta watso mata, dan ta gaji da iskancin jawwahir,

Jawwahir dariya tayi sannan ta tattara kayan tace oh O Oho a haka dai za”abarmu wallahi, inna dai batayi magana ba,

Data gama shirin sannan masu gini sunxo, ta basu kuɗin bulo da yashi da suminti, sannan ta tafi makaranta,

Yau ko honey j bata tsaya jira ba, dan abin mai zafine, napep tahau tayi tafiyarta,

Lokacin da aka tashi makaranta, ba gida ta nufo ba, wata ƙatuwar ma”aikata ta nufa, tana zuwa wani Office ta shiga, kallo ɗaya zakai ma mutumin kasan hutu ya gama zaunawa a jikinshi suka gaisa,

Bayan gaisuwa jawwahir tace ranka ya daɗe wata ƙaruwa ce na kawo maka, yace ina jinki, jawwahir tace kasan wata tsohuwar tv da,akayi da mai kwaure?”” yace Eh yasanta, jawwahir ta gyara zama tace kana da irin ta ne?”” yace ah ah wani abu ne?”” tace ni na samo ɗaya dakel , yace mi ake da ita, tace neman ta ake sosai wanda ya kawota miliyan biyar za”a bashi,

Alhaji ya gyara zama yace da gaske?””” jawwahir tace gaskiyar magana kenan, nima lokacin da naje *venezuela* naga ana kaita su kuma can suna bada kuɗi sosai, to nazo na sameta dakel nama ɗauka kana da irin ta da siye zanyi,

Yace nawa zaki siya ne?”” jawwahir tace to tunda kaine ai sai in siya miliyan shidda tunda kana da mutumci, Alhaji yace Allah sarki shi yasa nake sanki wallahi kina kawo man ƙaruwa jawwahir tace ai babu wani damuwa, yanxun ma, idan kana da miliyan ɗaya ka bani don Allah sai in kawo maka tv ɗin ka ajiye idan na kawi maka sai ka bani,

Alhaji yaji kuɗi saboda haka yace babu damuwa, yaushe kike san kuɗin ne?”” tace idan da hali yau, alhaji yace to babu damuwa, ki kawo tvn tace ni yanxun abubuwa sun man yawa amma zan dawo anjima ma kawai in kawo maka,

Alhaji yace to, jawwahir tayi godiya sannan ta baro office ɗin,

Kai tsaye gida ta nufo, tana zuwa abinda idon ta ya gane mata shine ɗakin da aka fara gina mata ake rushewa , ga kuma sadiq zaune a gefe, da gudun bala”i ta isa wurin ta fara cewa kai malam lafiya?”” baku san kuɗi aka sa aka gina ba?””

Sadiq yace tunda kina da kuɗi gobe ma sai kisa a sake gina maki wani, inda sadiq yace zaune ta kalla murmushi tayi da gefen bakinta , tace hassada ta ƙarasa maganar tana ɗaga girarenta, sadiq yace anyi hassadar ko zakiyi maganain abun ne?”” jawwahir tace yanxun nan kuwa basai anjima ba,

Schbag inta kawai ta yadar a tsakar gida ta fita da gudun bala”i, gudu take sosai kamar wanda taɓin hankali ya sama, tana isowa bakin titi, napep tahau, bata zame ko ina ba, sai police station, tana zuwa ta fara rattafa masu masu bayani, tana kuka yanda take maganar dole ta baka tausayi, wani ɗan sanda ya bada hilux ɗaya yace aje a taho da sadiq, saboda jawwahir tace basu haɗa komai ba haka nan yaxo gidansu yake tayi mata asara idan tayi gini ya rusa shi, ta ƙara da cewa ita marainiya ce da tayi mashi magana kuma yace duk ubanda ya tsaya mata ya ganshi, ranka ya daɗe shi yasa nazo wurinku kubi man haƙƙina dan ku masu adalci ne,

Ɗan sanda yace haƙiƙa kuwa kinzo inda za”a share maki hawayenki, yace ma “yan sanda maza kuje ku kamo mana shi, da sauri suka fito su dukansu suka shiga mota hada jawwahir,

Jawwahir tayi bake bake a cikin mota tana gaba sai nuna masu hanya take har suka tun karo cikin unguwarsu,,,,,

Suna zuwa tace to su jira ta shiga ta kirawo shi, suka ce mata to, tace idan ba haka ba yaji na ɗauko ku guduwa zaiyi, suka ce to, haka jawwahir ta shiga cikin gida tace ma sadiq idan ka isa biyoni waje,

Shi kuma cikin rashin sanin abinda take magana yace miyasa dole sai waje?””” jawwahir tace idan har kai ka cika mai ƙarfi kazo waje mu raba fili, sadiq bai sake magana ba, sabida haka wani ƙaton dutse a gabanta ta ɗauka ta jefa mashi, shi kuna da gudu ya taso ya biyo ta,

Tana ganin ya biyota ita kuma tayo waje da gudu, suna fitowa tace yawwa kunga banzan nan kuka ma man sakarai , haka suka danƙe sadiq suka jefa mota, itana jawwahit motar ta hau suka nufi station,

Suna isa sadiq yana san yayi magana amma jawwahir tace kada su barshi yayi magana dan yace ya raina “yan sanda, hannu tasa cikin brezer ta ta fiddo kuɗi ta basu tace tana so a lilƙisa mata shi yanda idan ance yayi mata sikanci gobe zai kiyaye ta, tun tana nan akafara cima sadiq uwa , ita kua ta juyo tayo tafiyarta gida,

 

 

Kam lallai wannan wace irin rayuwa ce? Muje sannu muga irin iskancin jawwahir, dan hausawa sunce wanda baiji bari ba?”” lallai bazai ƙijin hoho ba,💋
☄
☄☄
☄☄☄
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*WANDA BAIJI BARI BA*
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
☄
☄☄
☄☄☄

*AMEENCI WRITER’S ASSOCIATION* 📚✍🏻

*MEELAT MUSA*

*PAGE* 5

****
*J*awwahir tana zuwa gida ko sallama babu haka ta shiga ban kaɗai ban kaɗai, inna tace mata ina sadiq daya biki?””” dariya jawwahir tayi sannan tace hajiya innasco kenan, ai babu wanda zai taɓa jawwahir ya zauna lafiya, yanda nayi asara yau sai sadiq yayi asarar jinin jikinshi gaba ɗaya, dan naje na bawa “yan iskan kuɗi suyi mashi shegen duka dan idan ya dawo zai gane cewa jawwahir *fitilar sharri ko ba mai ina kai safe*

Tana faɗin haka ta faɗa ɗakin inna ta kinkimo tv ta fito, wani tsunma taje ta ɗauko ta fara kakkaɓewa, inna tace ita kuma ina zakije da ita ne?””” jawwahir tace gadona nake fiddawa kinga lokacin da zaki wuce lahira kila lokacin ina ƙasashen waje kila ina irin su , *England* ko *serbia* ko *texas u s a* ko *mexico* ko *california u s a* ko *japan*haka dai tayi ta lissafo ƙasashe, har ta gaji sannan tace kinga ai gara inci rabo na in tada molaƙa,

Inna tace to tunda ba ubanki ne ya siya man talabijin in nan ba, baza ki ɗaukar min kayana ba, wannan tv tun ta aure na ce, har kin iya lokaci ɗaya kixo ki rabank da abuna?””””

Jawwahir tace ai shi yasa nace da sauranki, lumfasawa tayi sannan ta dafe ƙirjinta, bayan wani lokaci ta ɗago fuskarta ta kalli inda inna take tsaye sannan tace innasco?””” inna ta kalleta, jawwahir tace kinsan abinda ake cewa plasmer?”” inna tace gulasmer?””” dariya jawwahir tayi sannan tace talabijin bango, ita wannan yanxun an daina yayinta, zanje in siyar da wannan in siyo wanda ake yayi kinji innas, ta ƙarashe maganar tana buɗe idanuwanta cikin sigar iskanci da rashin kunya,

Inna tace nida bansan ta bango nafi san ta girke, jawwahir tace to bari inje in siyo maki, daidai lokacin da ta kinkimi tv zata fita, inna ta riƙeta, tace ajiye man kayana, ɗaure fuska jawwahir tayi sannan tace ke bari ganin ina lallaɓa ki amma kina wani haye man, zaro idanuwanta tayi sannan tace sakeni kafin tumbinki yasha iska, da sauri inna ta saki jawwahir, tana sakin ta jawwahir tayi dariya tace ashe baki san mutuwa,

Tsaki tayi sannan tace malama bani wuri, inna ta matsa ta kinkimi tv tayi waje, tana fita ƙofar gida tasa almajirai suka ɗaukar mata ita suka kaima mata bakin titi, napep ta hau ta nufi office ɗin alhaji,

Mai napep in tasa ya ɗaukar mata tvn har cikin office, bayan ya ajiye ta sallameshi , bayan ya tafi tace ma alhaji ranka ya daɗe gata, amma don Allah ina ƙara ja maka kunne kada kayi man sakaci da dukaya, alhaji yace kada ki samu damuwa, jawwahir tace bani kuɗin to,

Wata jaka ya jawo ya bata , ta riƙe a hannunta, sannan tace ni alhaji da mota zan siya, miye shawarar ka?”” tayi maganar cikin yanayi tausayi tace abubuwa sunman yawa saboda dad har yanxun yana *london* kuma wani lokaci driver baya zuwa da wuri yana kaini sch, so ina so in siyi motar,

Alhaji yace gaskiya ki siya yafi kyau a haka, jawwahir tace ni nextweek ma *india* zanje dan muna da biki gidan tsohon gwamma, alhaji yace ashe kinsan shi?”””

Murmushi jawwahir tayi sanann tace ai dashi da dad inmu mamansu ɗaya babansu ɗaya, alhaji yace ki taimaka man ki bani number shi don Allah, gaban jawwahir ya faɗi , amma ta dake ta basar, tace swry nabar ɗaya wayana a gida, amma insha Allah zan turo maka, yace babu damuwa,

alhaji yace jawwahir jawwahir gaskiya familynku babban family ne, jawwahir tace sosai, alhaji yace to cikin yayun gwamna waye babanki a ciki?””” nan ma dakewa tayi sannan tace dawa dawaye ka sani ne?”””

alhaji ya fara yo mata lissafi , saboda ita dai bata san kowa ba, dan haka tace lallai to cikinsu da waye nayi maka kama?””” alhaji kawai canka yayi ya faɗi sunan wani, jawwahir dariya tayi sannan tace ai daɗina dakai kana ganewa, a daidai lokacin da ta miƙe tsaye,

Alhaji yace to maganar motar fa?”” jawwahir tace ina so, munyi waya da dad yace inje wurin wani yayanshi ya siya man motar ni kuma muna da arziƙinmu bana so ina dogara da kuɗin gidan wani saina dad, amma nace kawai zan samu rance idan ya dawo sai ya bani in biya,

Amma idan aka siya man motar miliyan 2, idan dad ya dawo zai bayar da 3milion, alhaji najin haka yace to aini zan siyo motar nan, jawwahir tace to babu damuwa ka siyo kuɗinka zasu zo hannunka,

Jawwahir tace bara in wuce gida, Alhaji yace to, yana ƙara jaddada mata maganar number tsohon gwamna, tacd kada ya samu damuwa,

tana fitowa abin hawa ta tare , tana shiga, gabanta ya fara faɗuwa lallai wannan alhajin ɗan iskane a gidan uwar waye zan samo number gwamna”””???””

tsaki tayi tace ɗan iskan wato shi yama fink ƙusa kai kenan lallai,

har ta iso gida tsine ma alhaji take dan bata san ta ina zata fara nemo number ba,

tana shiga gida da “yar jakar kuɗinta matse, ta tadda sadiq zaune a tsakar gida, wata “yar munafikar waƙa ta fara, har zata wuce yace ke zo nan, tsaywa tayi ba tare data juyo ba, miƙewa tsaye yayi ya matsa kusa da ita, yana fuskantar ta,

yace jawwahir wannan wace irin rayuwace kika zaɓar ma kanki?””” tayi shiru, yace idan kina rufa ma kanki asiri ki rufa ma kanki asiri ki tsaya inda Allah ya ajiye ki, wannan rayuwar da kika ɗauka ba hanya bace mai bullewa, kinje kinsa an dakeni,?”” har abadan duniya baki da kamata mune zamu faɗa maki gaskiya, mutanen duniya saidai su tsine maki albarka,

jawwahir tace yawwa anzo wurin kawai dai kace kana so ka tsine man albarka ne , kuma sai ka tsaya kana ta laɓe laɓe?”” kawai kace jawwahir Allah ya tsine maki albarka shikenan, dan ka tsine man sai akace maka zan lalace ne?”” hmm kacu gaba da shiga harkata, idan har baka kiyayeni ba saina sa an tsiyaye maka idanuwa kama rasa wanda zaiyi maka jagora, tsaki tayi sannan tack gaba da tafiya, tana cewa kuma gobe zansa aci man gaba da gini idan lafiyar jikinka ta isheka sai kasa a sake rusawa,

sadiq tsaki yayi saboda a gajiye yake idan yace ma zai daketa shine zai wahalar da kanshi, dan haka fita yayi yabar gidan,

ita kuma tana shiga ɗaki kayanta ta cire, sannan ta zaro wata katuwar wuƙa daga ƙugunta, ƙofar ɗaki tazo ta zauna saman kudinka ta fara wasa ta, tana cewa udan ba”a daina sa mana ido ba, haka zamu shige cikin maƙoshin mutum, takai wuƙar wurin bakinta tana ma kiss tana kallonta kamar wata ɗiyarta, taci gaba da cewa nasan kina nan kinajin ƙishirwar jini, kiyi haƙuri nayi kashedi dan *duk wanda baiji bari ba tofa lallai bazai ƙijin hoho ba, haka bahaushe yace*

Dariya tayi sannan ta miƙe tace bara muje muyi wanka saboda ɓacin rana, kwando ta ɗauka ta nufi bayi,

ita kuma inna tana gefe taji kashedin jawwahir gabanta sai faɗuwa yake Allah dai yasa ba ita da zata yanke ba,

Jawwahir na fitowa daga wanka, ta kalli inda inna take taga duk ta takure wuri ɗaya, abin ya bata dariya ta fara kwalkwala dariya har abin ya bawa inna tsoro, inna ta kasa kallonta sai kallon ƙasa take jawwahir tace hajiya innasco halan yauma tuwo kikai mana ko?””

inna tace ban sani ba, dariya jawwahiɗ tayi sannan tace ai duk laifinki ne, ga awaki kin wani kama kin ɓoye sai kace rayuwarki , hajiyata ki fito dasu kawai kice daɗi ki tada molaƙa ko kin zama rayayya, inna tace dan ubanki yanxun mutuwa nayi?”” jawwahir ta ɗaure fuska sannan tace ai banbancinki da matacce idanuwanki kawai da suke lufashi,

inna bata sake magana ba jawwahir ta shige ɗaki tana shiga ɗaki ta sake sheƙewa da dariya , tace muguwa ashe bata san mutuwa, ji yanda idanuwanta suke wani far far, tana nuna yanda idon inna yakeyi cikin madubin da take kallon kanta tana kwaikwayon maganar inna, haka tayi ta iskanci daga baya tayi shirin kwanciya bacci ta haye gado,

inna tananan zaune har baba ya dawo , yana dawowa inna cikin tsoro ta fara gaya mashi jawwahir zata kashe ta, baba yace ƙarya take dan ubanta , inna tace hada ceman *wanda baiji bari ba, wai bazai ƙijin hoho ba*

Baba yace barta dan ubanta da kanta take, kuma kada ki kuskura ki nuna mata kinajin tsoronta idan ba haka ba zata hana maki zaman lafiya, inna tace to, haka baba yayi ta rarrashin inna da kalamai masu daɗi, daga baya suka tafi ɗaki dan kwanciya bacci,

*na gode ku kasance tare dani*
☄
☄☄
☄☄☄
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*WANDA BAIJI BARI BA*
🔥🔥🔥🔥🔥🔥��🔥
☄
☄☄
☄☄☄

*AMEENCI WRITER’S ASSOCIATION* 📚✍🏻

*MEELAT MUSA* 🌹

*PAGE* 6

*****

*T*unda safe jawwahir ta tashi tayi wanka, mai ta shafa da “yar powder tana zaune tana duba agogon hannunta saboda yau basu da makaranta,

Wayarta ta ɗauko ta kira ƙawarta hafsat wanda itace ta gayyace ta bikin gidan tsohon gwamna, ta kirata bayan sun gaisa tace mata hafsat wai bikin da zamuje don Allah ya kuke dasu?””” hafsat tace mata wani abu ne?”” jawwahir tace inaso kawai in sani ne, hafsat tace matarshi ce yayar mamana uwa ɗaya uba ɗaya, jawwahir tace to kina da ƙawa a cikin yaran gidan?”” hafsat tace mata Eh, jawwahir tace to babu damuwa,

Bayan sun gama wayar jawwahir tayi ajiyar zuciya, ita kaɗai tasan dalilinta na yin haka, inna ce ta shigo ɗakin da kofi a hannunta, miƙawa jawwahir tayi ita kuma ta miƙa hannun ta karɓa , tana dubawa taga koko ne, tsaki tayi ta taɓe fuskar ta tace haba innasco tsakanin da Allah kamarni a gidan nan za”abani tsari inyi kalaci dashi don Allah?””” tana maganar tana nuna kanta, inna tace shinwai da kike man wannan zaɓin kece kika kawo ayi maki abinda kike so?”””

Jawwahir tace ai baki gaya man kina so ba, idan kikai haƙuri ai na kusa fara aiki, inna ta zuba ma jawwahir ido tana kallonta, ɗago kai tayi ta kalli inna sannan tace kin wani zuba man ido kina kallona kamar kinga wata sabuwar halitta, inna tace ai sabuwar halittar na gani tunda kin zama mai baƙin hali,

jawwahir tace tou pha yau kuma wannan sunan na samu?”” inna tace kullu addu”ar shiriya nake maki saboda wannan ba turba mai kyau bace kika ɗora ma rayuwarki wallahi, idan baki hankali ba zaki fuskanci matsala a rayuwarki,

Jawwahir tace matsala kuma ta nawa??”” ai na gama zama cikin matsala tunda dai nazo cikin talauci,

Inna tace kidai ɗauki duniya da sauƙi idan har kina so rayuwa tazo maki da daɗi, yawwa yawwa tou fa ci gaba Allahu akabar jawwahir duk itace take faɗin haka, tace ikon Allah idan muna biki zamu ɗauke ki kije ki riƙa wa”azi, dan na lura kina san jaddada gaskiya, tsaki inna tayi sannan ta ɗauki kofin kokon da jawwahir ta ajiye saman gado ta fita,

Kallon inda wayarta take dan kira ne ya shigo, tana ɗauka taga alhaji ne, tsaki tayi sannan tace shege uban cusa kai bari kuma inji da wace yaxo, wayar ta ɗauka sannan ta fara magana cikin yanayin bacci, alhaji yace ranki ya daɗe ashe ma baki tashi bacci ba?”””

tace ummm, yace dama maganar number ne, jawwahir tace haba ina sane ban manta ba, amma ka bari kawai insha Allah zan turo maka bara in gama bacci yace tom, da haka sukai bankwana ta kashe wayarta,

tsaki tayi sannan tace wannan ɗan iskan wato so yake ya ƙure ƙarya mai haɗama, tsaki tayi sannan tace idan yasan wata baisan wata ba,

wayarta ta ɗauko ta shiga neman number hafsat bayan wani lokaci ta ɗauka, jawwahir tace mata ƙawata zan shigo idan Allah ya kaimu don Allah ki kaini gidan yayan mamanki, hafsat tayi dariya sannan tace baki bari sai biki?”” jawwahir tace nidai inaso inje dan ki gabatar dani bana so ranar biki inje inyi ta raɓe raɓe gara ki gabatar dani kowa yasanni, tace kada ki samu damuwa Allah ya kaimu da rayuwa muje, jawwahir tace amin sannan ta kashe wayarta,

jakar kuɗin data dan faro wurin alhaji ta ɗauko, kuɗin ta shashshafa sannan tayi masu kiss tace da sannu zakuyi rayuwar jin daɗi zan kashe ku ta hanyar da kukafi buƙata, murmushi tayi sannan ta rufe jakar kuɗin ta ajiye,

agogo ta duba taga 9:22am ɗan gajeren tsaki tayi sannan ta fito tsakar gida, ta yage baki tana hamma gami da miƙa, da sauri ta sauke hannuwanta ƙasa dan ganin sadiq, tsaki tayi sannan tace gafa aljarabatu tsutsar zaure bari inji yau kuma da wace yaxo ,

Inda take tsaye ya nufo, kallonshi take har yanxun shima ita yake kallo baiyi magana ba, saida ya matso dab da ita, sannan ya shaƙo wuyanta ya jijjiga ta ya buga mata kai da bango, ta tafi ɗimuwa ta wani lokaci , idanuwanta suka kawo hawaye , cikin yanayin wahala tayi magana da disashshiyar murya kamar wanda take shirin tafifa lahira tace sadiq mi nayi maka?”” baiyi magana ba ya zare belt in jikinshi yaci gaba da dukanta, yana dukanta yana cewa da maganar gini da maganar soka ma inna wuƙa shine laifinki, kafin ki kashe ta gara ke in aika ki lahira kowa ya huta, dukanta yake babu ji babu gani, dakel tayi magana cikin kuka tace ke innas ni nace zan soka maki wuƙa?”” inna tace Eh ai da kanki kikace tayi haƙuri wuƙar ta kusa shan jini, cikin kuka jawwahir tayi murmushin ƙarfin hali sannan ta riƙe belt in ta kalli sadiq tace kada ka sake dukana,

yace idan na sake mi zakiyi?”” tace hukunci zan ɗauka da hannuna dan idan wuƙar bata sha jinin innas ba zata sha naka, wannan shine karo na ƙarshe da zan sake faɗa maka ka fita harkar jawwahir idan ba haka ba wallahi nice *ajalinka* jin wannan kalma yasa sadiq ya haɗiya miyau dakel lokaci ɗaya kuma zuba ta keto mashi, belt inshi ya fara maida a jikinshi dan duk abinda jawwahir tace zatayi aikatawa take, dan haka ya yanke ma kanshi hukuncin ya fita harkar ta,

Yana gama sa belt inshi ya fita daga gidan, yana fita tayi tsaki ta kalli inda inna take zaune, da runanin idanuwanta da suka sha kuka suka gaji, ta ƙura ma inna ido, kallon ya ishi inna ta miƙe ta sake wuri, inda ta koma taci gaba da kallonta, inna taga bata daina kallonta ba, don haka ta ɗauke fuskarta daga saitin jawwahir tana kallon wani wuri daban, tsaki jawwahir tayi sannan ta ɗaga ɗan yatsanta ma nuni tace idan har baki kiyayeni ba ta girgiza kanta sannan tace jini zaiyi ambaliya a gidan nan,

Shin wai da wane ɗaukar alhaki zakiji?”” ku baku bani ba, na tashi ina neman na kaina kunsa man ido, kuma dan na wasa “yar wuƙata sai ciki ya ɗuri ruwa?”” to kici gaba da haɗani da sadiq kinsan Allah hmmm kinma dai san sauran,

Inna tace duk abinda kike man sai Allah ya saka man, Lbanza wadda bata sallah duk ranar da kika mutu Allah maƙabartar anna zansa a rufe ki,

Duk duniya jawwahir ta tsani ayi mata gorin sallah , dan haka abin yayi mata ciwo , tsaki tayi sannan tace shin sai ina ruwanki da sallah ta?”” aikinki haihuwa tunda kuma kin kawoni duniya ai kinyi ƙoƙari daga nan kuma mun raba jaha, idan ma banyi sallah ba ina ruwanki da sallahta kabarinki daban nawa daban,

inna bata sake magana ba, jawwahir taci gaba da cewa ai sallah nasan ko guda nawa akeyi a rana kuma nasan ko raka”a nawa ake yi a kowace, inna dai tayi banza da ita,

Nan ta yini zaune ƙofar ɗaki abun yana mata baƙin ciki, saida aka kira sallahr la”asar sannan ta tashi tayi wanka akayo alwallah akai sallah ta shirya sannan ta fita dan samun abinda zata ciwo ma cikinta,

tana fita daga gida inna tu ƙokacin da take sallah abun ya bata dariya, dan duk sanda tayi mata gorin rashin sallah sai tayi sallah, idan tayi a ranar washe gari batayi sai kuma lokacin da aka sake mata gori,

ita kuma tana fita, ƙofar gidan su *honey j* ta tsaya , ta kirashi a waya yaxo, tace don Allah ya bata aron motar shi, zataje wuri cin abinci, yace mata saidai suje tare dan yasan halinta yanxun nan tana iya dawowa tace ɓarayi sun tareta sun kwace motar, ɓata fuska jawwahir tayi sannan tace to muje babj damuwa, cikin gidansu ya koma ya ɗauko motar ya fito, yana fitowa yace ta shigo su tafi, ta shiga suka ɓace daga wurin kamar walƙiya,

abinci mai rai da lafiya suka ci , suna gama cin abincin yace suje yawon miƙe ƙafa, haka suka tafi sukayi ta shawagi a cikin gari, har aka kira sallah isha”i, sannan suka nufo gida, a ƙofar gidansu ya kaita, sannan ta mashi saida safe, shima yayi mata fatan alkairi ta fita ta shige gida shima ya nufi gidanshi,

Inna da bacci ya fara ɗauka taji shigowar jawwahir da sauri ta miƙe tsaye, ta fara murtsike idanuwa, jawwahir tace innasco ya dai?”” inna tace lafiya qalau, murmushi jawwahir tayi da gefen bakinta sannan tace kwanta kiyi baccinki wuƙar nan na mayar da ita wa wanda ya ara man, a daidai lokacin data haye saman gado, inna kuma ta koma saman “yar katifarta tayi kwanciyarta,

*****

Da safe, jawwahir na zaune tsakar gida tana waya da hafsat dan tafiyarsu gidan tsohon gwamna , suna cikin waya awakin inna su kuma sai meyyy meyyyy mayyyyy meyyy, hafsat tace kina ina haka ne?”” dan ita jawwahir babu ƙawarta data taɓa zuwa gidansu idan kace zaka zo yanxun ta fara cewa zasuje *egypt* ko sunje abuja, tun ana kwakwar zuwa gidansu har aka gaji aka barta,

jawwahir tace naɗan fito ne ina cikin anguwa dad ne ya fitar da zakka nake rabawa talakawa, hafsat tace okey, to bara na bari ki gama sai kinzo anjima jawwahir tace to , sallama sukai ta ajiye wayarta,

Tana miƙewa tsaye ƙofar gida ta nufa, tana mita lallai nine za,a tona man asiri, kam ina waya anajin kukan tumaki ta girgiza kanta sannan tace lallai wata rana nima akuyar za,a ɗaukeni, daidai lokacin da ta iso ƙofar gidan wani maƙocinsu,

bayan sun gaisa tace mashi yaxo ya sayi tumakan gidansu, yace to, suje yayi masu kuɗi, yace to haka jawwahir ta tuso ƙeyarshi gaba har suka iso gida, haka suka kutsatso har cikin gidan suka shiga cikin garke, ya faɗa mata ko nawa ya siya, tace kawai ya bayar ya bata kuɗin dan shi dama sana”arsa kenan, haka ya tusa ƙeyar dabbibin ya tafi, inna bata nan bare tayi magana,

yana tafiya taje ɗaki ta ajiye kuɗin, sannan ta fito taje tayi wanka, tayi shiri mai kyau , ɗan ƙarya ya samu dama jawwahir ta wanku, wanka tayi ba na wasa ba kuma shigar da tayi ta dace da jikinta, wanka tayi na, na wuce raini, tunda dama ƙarya ce aikinta, bare tasan babban gida zasu, haka ta buɗe jakarta ta cika ta da kuɗi,

Tana fitowa daga ɗaki wayarta ta fara ƙara tana dubawa hafsat ce, murmushi tayi sannan tace yawwa kawai ku jirani a bakin hanya ina zuwa, taci gaba da cewa kema nace ku jirani miye kuma sai kin biyo man , tom kada ki damu gani nan gab da bakin titin,

Tsaki tayi sannan ta kashe wayar tace shegiya uwar kwakwa ke dole sai kinxo nan , kin gaji ki gama kwakwar taki, haka tayi ta mita da tsegumi har ta iso bakin titi, tun daga nesa ta hango motar su sunyi parking daidai inda babanta yake kasa icce,

kam lallai ɗaure fuskarta tayi gam kamar ta hango ajalinta, tana isowa bakin titin baba ya fara cewa ke jawwahir ina kuma zakije?”””””””””””””
Copied By
YAYA HAYAT
(admin
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
Cool novel, makeup and kitchen1⃣
Cool novel, makeup and kitchen2⃣
AND
Cool novel, makeup and kitchen3⃣)

 

Leave a Comment