aisha ummi at 01:52
WANI HASKE..1-70
Ummi A’isha🏻: *WANI HASKE*
_*NA*_
_*UMMI A’ISHA*_
_*1-7*_
*JAN KUNNE*- Ban yarda wani ko wata su juya
min wannan labarin ba, duk wanda ya sauya
labarin ko ya cire sunan marubuciyar yasa
nasa,ko kuma ya kwafi wani abu daga cikin
labarin Allah ya isa ban yafeba.
~~~Cikin nutsuwa matashiyar budurwar wadda
bata wuce shekaru 23 a duniya ba take harhada
takardun ta wanda ke baje a saman teburin da
take zaune, tako ina hayaniya ce take tashi ga
kida ya cika ko wanne lungu da sakon dake
cikin makekiyar babbar chochin _*(church)*_
wadda kallo daya zaka yi mata ka gane cewar
masu halatarta da yawa, ciki harda wannan
budurwa mai suna *GOODNESS*.
Tattara takardunta taci gaba dayi har ta
kammala zuba su cikin wata madaidaiciyar jaka
baka ta dauki jakar ta rataya ta nufi hanyar kofa
domin fita daga cikin church din, tana sanye
cikin bakar body hug matsatsiya wadda ta
kamata sosai, da wando jeans kanta daure da
gashin kanti wanda aka yiwa kananan kitso
fiyeda kimanin dari biyu, hannunta da kafarta
kuwa sunsha blue farce akan zako zako din
faratanta, lokacin da take fitowa tayi kicibus da
saurayinta promise yana kokarin shigowa,
Hannunta ya kama suka koma waje ya dan
dubeta yana murmushi “dear ba dai har kin
tashi ba?”
Kai ta daga masa kafin ta iya bude bakinta “eh
nagaji ne ina son zanje gida amma nasan ma
bazata tafi yanzu ba sai anjima saboda yau da
akwai night service”
Kamar zai yi kuka yace”pls dear ki dan jira
zuwa anjima sai mu tafi tare, kinga akwai inda
nake son ki rakani”
Kanta ta girgiza “am sorry promise, yanzu inada
aiki agida, baba yana azumi yau, kasan yau
Thursday so ina son naje na shirya masa kayan
shan ruwa tunda ma bata nan” ta kare maganar
tana duba agogon hannunta.
Sakin hannunta promise yayi yace “babu
damuwa agaida baba pls,sai mun dawo”
“Ok bye bye” tafada tareda juyawa tafara tafiya
da sauri domin tana son ta isa gida da wuri ta
shiryawa mahaifinta kayan shan ruwa.
Misalin karfe _5:30_ ta isa gidansu dake
unguwar state low cost, gidan babu kowa
lokacin data shiga, tana ajiye jakarta ta fito
tareda shiga kitchen bayan ta kunna wakar
_there is no one like you_ a wayar selularta,doya
ta dauko tafara ferewa tanayi tana bin wakar.
Kamar daga sama taji sallamar nura makocinsu,
_”yes come in”_ tafada tana dariya domin tayi
murna da ganinshi, ciki ya shigo ya janyo wata
farar kujerar roba ya zauna yana cewa,
“Ina ma take?”
“Ma bata dawo daga church ba, nima dan baba
yana azumine da bazan dawo yanzu ba wlhi”
Tunda tafara maganar nura yake kallonta acikin
ranshi yana mai jinjina kokarin mahaifinta wurin
rikon addini ga taqwa da iya zama da mutane
da yake shi Allah ya soshi da rahama sai ya
bashi *WANI HASKE* acikin rayuwarsa su kuma
iyalin nasa aka barsu haka,
Dan murmushi yayi sannan yace “to albishirinki,
yau nazo miki da babban labari yar gidana”
“Hmm nura you done start ba? Ehem kazo yau
ma zaka fara tsokanata ko?”
Murmushi ya saki yace “yau babu maganar
tsokana tsakaninmu, yau nazo ne na karbi
credentials dinki zan kaiwa wani babban mutum
wanda yake neman mai irin qualification dinki
zai daukeshi aiki a office dinsa”
_wooh, thank you God, am very grateful with this
suitable job, eheeee”_ tafada tareda daka wani
uban tsalle tayi watsi da doyar da take yankawa
ta nufi cikin daki.
Duk sai da ta hargitse dakin kafin ta iya tattaro
takardun nata gaba daya ta kawowa nura tana
fadin _make I go and photocopy this”_
Karba nura yayi yace bari yaje yayi mata
photocopy din ita taci gaba da aikin da take, duk
ta diririce haka taci gaba da aikin tana yi tana
rawa tana waka har nura ya dawo ya isketa
ahaka,ya bata original din takardun nata yayi
mata sallama ya tafi da zummar zai kirata a
waya ya sanar da ita duk halin da ake ciki.
“Idan nasamu aikin nan zan tara kudi na kai
baba can mecca yaje yayi aikin hajji, zan kai ma
Jerusalem taje itama tayi aikin hajji, nima zanje
Jerusalem, zan kai anty Bilkisu mecca” tafada
tana fara’a, sai murna take alla alla take ma ta
dawo ko babanta ta basu labarin abinda ya faru.
Tana cikin yin aikin mahaifinta ya dawo lokacin
ta kammala harhada masa abincinsa kunune
kawai ya rage bata dama ba,
“Sannu da zuwa baba” tafada tana fara’a, masu
karatu nidai _*ummi A’isha*_ sai da na cika da
mamaki ganin irin kamalar baban goodness
domin mutum ne mai tsananin riko da addininsa
yana rike da casbaha goshinsa manne da *wani
haske* wato tambarin salla.
“Yau dai da alama kina cikin farin ciki, kodai
wani abun ya farune bayan fita ta?” Mahaifin
nata ya fada shima fuskarsa dauke da fara’a
“Baba nakusa fara aiki, dazu nura yazo ya karbi
credentials dina” tafada cikeda murna,
“Ato Alhamdulillah,Allah ya bada sa’a, ina
maman naku?”
“Baba, ma bata dawo daga church ba, yau akwai
night service, may be ma su kwana acan” ta
bashi amsa,
“To shikenan” yafada tareda shigewa cikin dan
madaidaicin falon da yake gidan, bai jima da
zama ba aka kira sallar magrib yafito yayi
alwala ya tafi masallaci kafin ya dawo goodness
ta jere masa kayan shan ruwansa ta kule acikin
daki tana sauraron irin wakokinsu wanda suka
saba yi a church gefe kuma wani jibgegen Bible
dinta ne take karantawa.
* * * * * * * * *
Washe gari tun gari bai gama budewa ba
goodness ta tashi tayi wanka ta dauki Bible
dinta ta nufi church, can ta tarar da
mamanta,church din cikeda Jama,a masu tarin
yawan gaske nanfa aka shiga bauta cikin kida
da raye raye, mata da maza, manya da yara
kowa ya dage sai tikar rawa yake, rawar ta
dauke su fiyeda awa uku kafin aka dakata
pastor ya fito yayi addu,o’i aka rufe,
Saurayinta promise yana rikeda ita suka fito ma
tana binsu a baya, agaban church din suka ja
suka tsaya tafara bawa promise labarin ta kusa
fara aiki,
“Wow ashe mun kusa yin aure, tunda gashi zaki
fara aiki”
“By the grace of God hakane dear dan ina fara
aikin nan babu kuma abinda zamu jira”
“Gaskiya am very happy dear, babu damuwa
Zan zo gidanku letter,ga ma can naga tana
jiranki”
“Thank you dear” tafada tareda juyawa ta nufi
inda ma ke jiranta,
“Ma nura yazo jiya fa ya amshi credentials dina”
tafada lokacin da suka fara tafiya,
Bata rai ma tayi ta tamke fuska tace, “Goodness
bakya jin magana ko? Nace kidaina kula
musulmi, babu ruwanki da muaulmi saboda
addininku ba daya ba amma bakya ji”
“Sorry ma,wallahi ba nice na kulashi ba shine
yazo har gida yace akwai wani vacancy awani
company ana neman wanda yayi irin karatuna”
“Ehem, yayi kyau to amma ko kin samu aikin
nan indai wurin musulmi ne ba zakiyi ba, nafi
son kiyi aiki awurin Christian inda zaki kara
samun training akan addininmu domin my
ambition is u to become a pastor”
Wata dariya goodness ta saki tace “that’s my
sweet ma, nima mama burina shine nazama
hakan sannan ina son idan nafara aikin nan
natara kudi na kaiki Jerusalem”
Sai a lokacin maman tayi murmushi tace
“yawwa my daughter haka nake sonki”
Suna hira suna shirya yanda abubuwansu zasu
kasance har suka karasa gida, goodness ce
rikeda manya manyan Bible guda biyu daya nata
daya na ma, lokacin da suka shiga baban
goodness yana kitchen yana dafa ruwan wanka,
cikin kitchen din ma tabishi ita kuma goodness
ta nufi cikin daki.
Haka suka ci gaba da gudanar da rayuwarsu,
ranar Sunday da safe nura yazo gidan amma bai
samu goodness ba saboda ta tafi church da
yamma ya sake dawowa, a kofar gida suka yi
clashes ita da ma suna dawowa daga church
sunsha kwalliya sosai tamkar masu shirin zuwa
gidan biki, ma wani dandakeken leshi tasa
golden colour, tasha gwaggoro shima golden sai
takalmi da jaka,
Ita kuma goodness tana sanye cikin english
wears masu kyau riga da skirt dukkaninsu black
colour skirt din iya gwiwarta,
“Welcome ma” nura ya fada yana rissinawa
mama,
Fuskarta babu fara’a tace “yawwa thank you” ta
wuce cikin gida,
Kallonsa goodness tayi duk sai taji babu dadi
tarasa dalilin da yasa ma bata son mu’amula da
musulmai alhalin kuma ita bata ga illar hakan ba
saboda tasha zama da musulmai kuma
dukkaninsu masu hali na kwarai ne, babu
mugunta, babu cutarwa babu cin amana,kai to
ita taya ma zata ki musulmi alhalin mahaifinta
shima musulmin ne?
“Nura kayi hakuri dan Allah, ma yau ranta a
bace yake”
Girgiza kai nura yayi yana murmushi yace “karki
damu babu komai, dama zuwa nayi nasanar
dake ranar monday ki shirya kije ABU AL’AMIN
Company ltd,zaki karbi upper dinki sannan zaki
fara aiki”
Wani uban tsalle ta daka ta kaiwa nura runguma
ya goce yana dariya
“Nagode nura, nagode, kayi min komai, amma
ranar tare dakai zamuje, kaine zaka rakani”
“Kin san nima ina zuwa office fa, amma dai zan
duba idan da hali zan rakaki”
“Thank you nura, God bless”
Cikin ihu ta shige gida tana cewa “thank you
God, thank you, thank you”
Kan cinyar mama taje ta fada tana murna,
babanta yana zaune kan kujerar dake
fuskantarsu yana sauraren su,
“Ma i am a worker now, i done get a job in one
comp called abu… Abu something, i have forget
the remaining name but i get it, nura said i
should go and collect my upper of appointment,
mama pls join me to celebrate this wonderful
issue”
Shafa kumatunta ma tayi tana dan murmushi
“my daughter i don’t want to make u upset, but
for frank speaking am not happy with this job”
Cikin kidimewa goodness ta kalli ma tace “ma
why, why”
“My daughter u are the only one i have, kinga
sister dinki musulma ce, and your dad is
muslim, ke kadai ce kike tare dani shiyasa
sometimes am fell so afraid about your
relationship with Muslim, kar kema su rinjayeki
kibi addininsu, if this occur i will not happy
goodness”
Hannunta goodness ta kama tana murmushi
“ma indai akan wannan ne karki damu, bazan
musulunta ba, i promised you this, kuma ai ma
ko a secondary sch da musulmai na zauna
harna gama sch nawa, amma babu ruwana da
addininsu suma babu ruwansu da nawa, akoda
yaushe suna fada min cewa addininsu ya basu
dama suyi mu’amala da Christian babu haramci
aciki, and when i was in the polytechnic duk
course mate nawa Muslim ne suma basu da
problem, kuma ma ga baba shima musulmi ne”
Tsaki ma ta danyi tace “am not asking u about
this rubbish, kawai ina fada miki ban yarda kiyi
tarayya ko wani mu’amula da musulmi ba,
sannan kiyi min alqawari cewar ba zaki
musulunta ba, duk lokacin da kika zama
musulma to bani ba ke, kuma sai na yanka ki,
you heard?”
“Am agreed ma,and i promised you i will not
become a muslim, i wish my self to die under
this religion (Christianity)”
Shafa kanta mom tayi tace “thank you my
daughter, am very proud of u” sannan ta juya ga
mahaifin goodness wanda ke zaune yana
sauraronsu bai ce komai ba tace,
“Papa goodness kaji your daughter done get a
job, so ka saka mata albarka, pls bless your
daughter”
“Allah sanya alkairi kinji goodness, Allah yasa
wannan aikin ya zamo _*WANI HASKE*_ acikin
rayuwarki, Allah ya baki nasara….”
Da sauri ma ta katseshi “ah papa goodness i
don’t like this thing fa, nace kasawa yarinya
albarka an you have started your muslim prayer,
ah”
“Ah ma leave him to finish pls” goodness ta
fada fuskarta cikeda damuwa
Tashi ma tayi ta dauki Bible dinta ta wuce
dakinta ta kyalesu a falon.
*Ummi A’isha*
[11/6, 10:31 AM] Ummi A’ish🏻: *WANI HASKE*
_*NA*_
_*UMMI A’ISHA*_
_*8-10*_
~~~Juyowa goodness tayi ta kalli mahaifinta
wanda fuskarsa ke dauke da alamun damuwa a
tattare da ita,
_”am sorry baba”_ tafada idonta taf da kwalla,
“Kar kiyi kuka babu komai, abinda nake so dake
shine kiyi hakuri da rayuwa aduk yanayin da
tazo miki, duk da cewa nasan yanzu banida
kalmar da zan iya fada miki tayi tasiri acikin
zuciyarki saboda mahaifiyarki tasa kin taso da
tsanar addinin musulunci acikin zuciyarki alhalin
kuma musuluncin shine addini na gaskiya, ina yi
miki addu,a kamar yadda Yar uwarki ta gane
kema Allah yasa ki gane gaskiyar, Allah ya
hadaki da *wani haske* acikin rayuwarki”
Yana kaiwa nan ya tashi ya fita daga cikin falon
yabarta zaune,
Sam maganar da mahaifinta yayi bata wani
tsaya mata arai ba saboda bata fahimci
maganganun nasa ba kwata kwata,
Channel ta canza ta kamo wata channel inda
ake nuna wani Nigerian film mai suna _bad
romance_ ,film din taci gaba da kallo har ma
tafito ta sameta tace ta shiga kitchen tayi girki
ita zata koma church yanzu,
Tashi tayi tashiga kitchen din ta dora tuwon
amala da miyar ogu tana yi tana yan wake
wakenta _”there is no one like you, ehhh there is
no one like you, ohhh there is no one like you”_
Muryar promise saurayinta ta jiyo atsakar
gidan yana kwalla mata kira domin shi bashida
katanga da gidan duk lokacin da ya ga dama
zuwa yake,
Lekowa tayi ta hango shi wuyansa dauke da
wani siririyar chain mai tambarin cross ajiki, ga
suma da ya tara tuli guda, faratan sa kuwa
tamkar na mage saboda tsayinsu,
“Welcome dear, ka shiga ciki ina zuwa” ta fada
tareda sake komawa cikin kitchen din, amalar da
miya ta zubo masa tazo ta sameshi a falo yana
kallon film din da ta tashi tabari,
Abincin ta ajiye masa ta zauna kusa dashi, “dear
ranar monday zanje na karbo upper dina”
Kamo hannunta promise yayi fuskarsa dauke da
fara,a “congratulations my dear, nayi murna
saboda nasan bikinmu ya kusa”
Kafadarsa ta dan kaiwa duka “see you, kaci
tuwo gashi”
Hannun yasa yafara cin amalar yana dariya
“dama nadade da yin mafarkin wannan lokaci,
nayi mafarki zaki samu wani abu ashe wannan
aikin zaki samu”
“Nima fa sai da nayi mafarkin dear, kabari kawai
ma taci burin wannan auren namu tayi shiri
sosai don tunkararsa”
“Yes oh,i like this” yafada yana kai loma, dariya
goodness tayi takai masa kiss a kumatu.
*
Ranar monday kamar yadda nura yace haka
goodness ta tashi cikeda murna,doki, da kuma
farin ciki ta shirya cikin riga da wando na jeans
da t shirt tasamo hill shoe mai mutukar tsini
tasa tayiwa ma da babanta sallama nufi Abu
Al’amin company ltd, lokacin karfe _8:30_ na
safe.
Lokacin da taje company din bata wani sha
wahala ba aka nuna mata office din da zataje ta
karbi offer dinta bayan anyi mata verification,
zama tayi tana jiran mutumin da zai bata offer
din domin har lokacin bai zo ba.
Tana nan zaune tana ta kallon ma’aikatan
kamfanin yanda kowa yake zuwa yake bude
office dinsa ya shiga gashi company din kato ne
yanada tsananin girma, gefe ga kuma wani dan
madaidaicin masallaci, bin offices din da ido tayi
ta yi tana jinjina tsaruwarsu,hawa hawa
kowanne department da side dinsu, tana ta
wadannan kalle kalle har wanda take yazo, ya
bude kofar office dinsa ya shiga, mikewa tsaye
tayi tana cewa “welcome Sir” gamida binsa cikin
office din,
“Are you goodness jacob?” Mutumin ya
tambayeta,
“Yes sir, nice” tafada tana dan rissinawa, wurin
zama ya bata sannan ya karbi original din
credentials dinta ya dudduba, bayan yagama
gani ya dauko wata zungureriyar wasika ya
bata, a lokacin ta rubuta acceptance letter ta
bashi ta tafi bayan ya sanar da ita cewar next
week zata fara halartar office, cikeda farin ciki ta
koma gida tana zuwa ta rungume ma wadda
take cikin kitchen tana harhadawa papa
goodness kayan shan ruwa, nan ma ta shiga yi
mata hudubar babu ita babu musulmi, kar ta
yarda tayi wata mu’amula ta arziki dasu.
Cikin wadannan kwanakin goodness duk tayi
sune kan shirye shiryen yadda zata fara zuwa
office, tayi wanki ta goge kayanta kaf, ko ranar
lahadi da taje church cikeda murna take, suna
tashi daga church tabi promise ta rakashi wani
club inda ake wani party, sai wurin _9_ ta dawo
gida ta bar promise acan yana cashewa yana
kora giya.
Washe gari ranar monday _9_ dai dai a office
tayi mata nan aka nuna mata office dinta ta
shiga a matsayinta na secretary din Genera
manager wanda za arinka bata albashi akan
naira _25,000_ banda wasu allowances da zata
rinka samu, office din GM din ya hadu iya
haduwa sanyin AC sai tashi yake tako ina, a falo
office din nata yake wanda aka zuba mata kujeru
da tebur ga kuma drawers na ajiye files,shi
kuma ogan office dinshi na ciki.
Wani dan ihu ta saka “yeeehhh” lokacin da ta
zauna akan luntsumemiyar kujerarta ta aiki
amma da alamar yau GM din bai zo ba saboda
taji office din nashi arufe, wayarta ta zaro daga
jaka tafara kiran promise, yana dauka ta sanar
dashi yau gata a office kuma ga yanayin office
din, kashe wayar tayi tana kallon wasu baki
wanda suka shigo da alama wurin ogan suka zo
nan tayi musu bayanin ance baya nan yayi
tafiya zuwa abuja amma acikin satin nan zai
dawo.
Kwana uku da fara zuwanta office din har ta
dan fara sabawa da mutanen wurin, ranar
Thursday lokacin da taje Massinger yake sanar
da ita oga yazo, ahankali ta bude kofar office din
ogan ta shiga tana sanye da skirt baka na jeans
da t shirt light blue tasa takalmi cover shoe
baki, kanta daure da bakin dan kwali,
“Excuse me sir” tafada lokacin ta takai tsakiyar
office din,
“Yes” yafada ba tareda ya dago kanshi daga file
din da yake dubawa ba, hakan ya bata damar
kare masa kallo, black beauty ne sosai dogo
marar jiki mai dogon hanci, akwai saje agefen
fuskarsa ga dan karamin gemu da ya tara,
bakinshi kamar na mace domin wani dan tsut ne
sai dai lips dinsa jajaye ne jur, yana sanye cikin
milk colour din shadda da hula kalar kayan
amma duk da yasa hular hakan bai hanata ganin
tabon sallar dake manne agaban goshinsa ba
saboda ya dan tura hular tasa zuwa keya,
ayanda ta kwatanta shekarunsa ba zasu wuce
_35_ ba a duniya, gaba daya office din ya cika
da kamshin turarensa na _explorer_.
Tsayawa tayi kyam agaban teburinsa tana
kallonsa ko kiftawa ba tayi,shi kuwa bai dago ya
kalleta ba har sai da ya kammala abinda yake
yi, ahankali ya dago manyan fararen idanuwansa
ya zubasu akanta,
_”good morning sir”_ tafada cikin rawar murya
saboda ganin baiwar surar da Allah ya hore
masa,
_”morning”_ yafada atakaice cikin sanyayyiyar
muryarsa, juyawa tayi zata tafi har taje bakin
kofa taji yace,
“Aturo min director admin and finance” cikin
maganarsa d’ai d’ai, domin kalma kalma yake
maganar ahankali, gashi muryar sa ta cika sanyi
sai kace cool water.
_*Ummi Shatu*_🏻
[11/6, 10:31 AM] Ummi A’isha: [8/20, 9:27 PM]
Ummi A’isha🏻: *WANI HASKE*
_*NA*_
_*UMMI A’ISHA*_
_11-15_
~~~ “Ok sir” tafada cikin in ina tareda bude
kofar office din tafita tanata ayyana maganar
wannan bawan Allah acikin ranta gashi wani dan
gayu dashi, massinger ta aika ya kirawo masa
daf din kamar yadda yace.
Tana nan zaune akan kujerarta tana yan dube
duben files din da aka fito dasu daga office
dinshi,
Karshen wata wasika ta duba wadda ya rubuta
hatta wasikar kamshin turarensa take yi, sai
alokacin idonta yakai kan sunansa JABIR.M.
AHMAD, jabir ta maimaita sunan tana mai shafa
sunan nasa da hannunta, director ne yafito yace
da ita ki shiga GM yana kiranki,
Tsam ta mike ta shiga office din yanzu kuma
jarida yake dubawa ta daily trust ya dorata akan
table din gabansa, duk da yaji maganarta amma
bai dago ba har sai da yakai aya lokacin tafi
minti 2 a tsaye,
Dagowa yayi ya kalleta ahankali ya fara magana,
“staff officer ya sanar dake dukkan ayyukanki?”
Tabbas staff officer ya sanar da ita amma
saboda tana bukatar taci gaba da sauraron
maganarsa wacce yake yi dalla dalla yasa tace,
“No sir”
Dan lasar lebensa nakasa yayi ya mayar da
idanuwansa kan jaridar da yake karantawa,
“Ok, to aikinki ne kula da duk wani shige da fice
na files din da akayi amfani dashi anan office
din, sannan zaki rinka rubuta duk wata wasika
wadda zata fita daga nan office din”
Tunda ya fara bayanin take binsa da kallo
musammam ma dan karamin bakinsa mai dauke
da jajayen lips,
“Kin gane” yafada a hankali,
“Yes sir”
“Kina iya tafiya”
“Ok sir” tafada tareda juyawa tafita daga cikin
office din.
Kujerarta ta koma ta zauna tana jinjina isa da
takama irin na wannan mutumin kodai dan yaga
yana da kudine, ko dan yana da kyau? Tana nan
zaune yafito daga office dinshi yana gyaggyara
hannuwan rigarshi da alama alwala yayi zai tafi
salla,
“Adawo lafiya sir” tafada bayan ta mike tsaye
“Yawwa” yafada a takaice, yafice,komawa tayi ta
zauna jagwaf tana cewa “ohh wannan mutum da
rashin kulawa da mutane yake”.
Mintuna kadan wadanda ba zasu wuce 20 ba ya
dawo ya wuce cikin office din shi. Kallo ta bishi
dashi har ya shige office din shi ta jiyo tana
jijjiga kai.
Lokacin tashi yana yi ta tattara kayanta ta nufi
gida lokacin karfe _5:00_ dai dai, tana zuwa ta
tarar da ma bata nan har ta tafi church sai iya
babanta ne agidan, wanka kawai tayi taci teba
miyar kuka wadda ta tarar an dafa agidan ta
dauki Bible dinta ta nufi church.
Washe gari ya kama friday kamar yadda ta saba
haka ta shirya ta tafi office, lokacin da taje GM
din bai zo ba dan haka ta zauna tafara karanta
jaridar sa da aka kawo masa, tana cikin
karantawar ne ta jiyo kamshin turare mai
mutukar dadi hakan ya sata tsaida idanuwanta
akan hanyar shigowa, minti kadan ya bullo yana
sanye da farar shadda sai kyalli take dinkin
tazarce, kansa dauke da hula ja yana amsa call,
cikin sauri ta mike tsaye tana yi masa sannu da
zuwa, hannu kawai ya daga mata ya wuce cikin
office dinsa.
Mintuna biyu da shigarsa ta dauki jaridunsa
guda biyu ta shiga office din,
Good morning sir”
“Morning” yafada ba tare da ya dago ya kalleta
ba, jaridun ta ajiye ta juya ta fita, zama tayi
tana tunanin to shi wannan wanne irin mutum
ne ? Sai dai kuma fa yanayinsa da wannan
dabi’un nasa sun burgeta saboda ita mutum
marar hayaniya yana mutukar burgeta maganar
Massinger ne ya katseta,
“Oga yana kiranki”
Cikin sauri ta mike ta shiga ciki, ta tsaya “gani
sir”
Rubutun da yake yi yaci gaba dayi, “yau ba
aturo min wani mail daga office din governor
ba?”
“Eh ba aturo ba sir”
“To zasu turo,idan an kawo ko bana nan ki
turawa director personnel, meeting za muyi da
governor zasu bayar da kwangilar gina gidajen
ma’aikata guda dari biyar”
Idonta kyam akan bakinsa yanda yake mul mul
da baki yana yi mata bayani ita dai wannan
bakin nasa yana burgeta, jin shiru bata amsa ba
yasa shi dagowa ya kalleta kur yaga ta kura
masa idanuwa ko kiftawa ba tayi,
“Kina jina?”, yafada tareda dan buga teburin
gabansa, firgigit tayi ta fara yan kame kame,
“Yes sir, zasu kawo, eh zan kawo maka”
Girgiza kai yayi yace “you can go” acikin ransa
kuma yana cewa “anya kuwa wannan yarinyar
kanta daya? Sai ayita yimata magana amma ba
zata amsaba sai dai ta zubawa mutum ido”
Tana fita taga wasu baki sunzo su biyu mata
nan tafara binsu da kallo daya bayan daya,
“Ya akayi?” Tafada lokacin da take zama akan
kujerarta,
“Sannu sakatariya munzo ganin malam jabir ne”
daya daga cikin bakin tafada,
“Yasan da zuwanku? Shi ya baku appointment?”
Tafada tana yatsina fuska
“Eh shine yace muzo office mu sameshi”
“To yanzu dai bazai samu damar ganinku ba
saboda aiki yake yi” tafada tana janyo drawer
zata dauko wani file,
“Haba ranki ya dade ki shiga ki sanar masa
mana idan yaga zai ganmu sai mu shiga idan
kuma bazai ganmu ba ahikenan”
“Bazai ganku ba”
Mikewa sukayi suka fita zukatansu babu dadi,
kallo ta bisu dashi “an fada muku ina haukane
da zan barku ku shiga wurin wannan
zankadeden? Ai wannan nawane” tafada tana
murmushi.
Tun daga wannan rana goodness ta bullo da
sabon salo domin duk bakuwar da tazo ganin
GM bata barinta ta shiga mazan ma sai tayi
niyya, yauma tana zaune akan kujerar ta ta
hada tea saboda lokacin da ta fito daga gida
bata yi breakfast ba, wata mata ta shigo yar
madaidaiciya da ita tasha les mai tsada tana ta
kamshi tace tazo ganin GM nan goodness tace
baya nan, matar tace “munyi waya fa dashi
shine yace nazo yau”
Karkacewa goodness tayi tace “to sai ki kirashi
ki fada masa ai”
Juyawa matar tayi tafita tana zaro wayarta
daga cikin jakarta, ko minti biyar ba ayiba sai
gashi ya fito da kansa, kanshi ko hula babu
hakan ya kara masa kyau,
“Meyasa idan nayi baki bakya zuwa ki fada min
sai dai kice musu bana nan? Wannan aikin
nasaki?
“Sorry sir” tafada tana kallon fuskarsa,
“Yanzu kinga meeting zamu yi da S. A ta
commerce and industry amma tazo kince mata
bana nan alhalin kuma abinda zamu tattauna da
ita abune mai muhimmanci”
“Sorry Sir” tafada tana zare ido,
“Bani mail din da aka kawo min daga code of
conduct bureau”
Hannu ta mika ta zaro takakardar cikin rashin
sa’a kofin shayin data hada ya tuntsire akan
takardar tare da sauran files din dake kan tebur
din.
_*Ummi Shatu*_🏻
[11/6, 10:31 AM] Ummi A’isha🏻: [8/21, 2:52 PM]
Ummi A’isha🏻: *WANI HASKE*
_*NA*_
_*UMMI A’ISHA*_
_16-20_
~~~Kallonta yayi da manyan dara daran fararen
idanuwansa ya juya ya koma office ba tare da
yace da ita komai ba, hakan ya sake rudata,
_”ohh God help me pls, pls God”_ tafada arude
lokacin da tafara diri diri acikin office din,
“Allah yasa kar oga ya bani query yau”
Hankalinta atashe ta dauki mail din ta bashi
cikin office dinshi, lokacin da ta shiga baya kan
kujerarsa, yana can kan wata doguwar kujera ta
zaman baki, ya dora kafafuwansa akan dan
glass table din dake gaban kujerar, yana kallon
wata tasha a satellite wacce aka saka karatun
alwur’ani mai girma, indai bata manta ba tun
lokacin data fara shigowa office dinshi wannan
channel din taga yana kunnuwa koda yaushe,
“Am sorry sir” tafada tana rikeda takardar,
“Je ki dorata akan table dina” yafada ba tare da
ya kalleta ba domin idonshi yana kan TV,
“Thank you sir” tafada tareda juyawa ta nufi kan
table dinshi ta dora mail din ta juya ta fita daga
cikin office din zuciyarta cikeda murna.
Karfe biyar ta tashi ta tafi gida tana zuwa ta
tarar da sister dinta tazo anty bilkisu sai dai ita
musulma ce, suna zaune itada mahaifinsu suna
hira goodness ta shiga kunnenta sakale da
earphone tana sauraren d banj cikin wakarsa ta
_a new day has come_ tana bin wakar ta shiga
falon, ganin anty bilkisu yasata dariya, “hey
when did you come?”
“Tun safe nazo ashe kin fara zuwa office?”
“Inata so ai nazo gidanki na fada miki ban samu
time ba”
“Ayya babu komai Allah ya sanya alkairi” yayar
tata tafada tana kare mata kallo yadda ta dame
cikin wasu riga da wando,
“Amin, ma taje church ko?”
“Tun dazu ta tafi” inji mahaifinta,
“Oh make i quick because we have weekly prayer
today” tana gama fadin haka tayi wurgi da
jakarta ta shige daki ta dauko bible dinta ta
ajiye akan kujera, ta shiga kitchen ta zubo
abinci, sakwara miyar agushi, kusa da anty bilki
tazo ta zauna tafara cin abincinta tana cewa
“anty ya mijinki? Ranan mun dawo daga church
nida promise da ma mun ganshi amma shi bai
ganmu ba”
Murmushi anty bilki tayi “ya fada min shima ya
ganku” amma acan kasan ranta wani bacin rai
takeji marar kwatantuwa, ace mahaifiyarta da
yar uwarta basu bawa annabi Muhammad
(S.A.W) gaskiya ba,
Mintuna kadan ta cinye abincin ta dauki Bible
dinta tafita tana cewa “anty idan nadawo na
sameki to, idan kuma kin tafi kigaida mijinki”
Tana fita anty bilki ta dubi mahaifinsu, “yanzu
baba haka zamu ci gaba da ganin mama da
goodness suna zuwa church? Addininsu daban
namu daban yanzu hakan yayi daidai?”
Girgiza kai yayi “Bilkisu halin mahaifiyarku sai
ita, da ace tanada rabon musulunta da tuni ta
musulunta to bata da rabo, tun kuna yara
kanana ni na musulunta amma ita taki saboda
macece mai taurin kai da kafiya, ke kuwa
lokacin da ta fahimci kina sha’awar musulunci
tun daga nan ta tsaneki tamkar ba itace ta
haifeki ba, da salla babu abinda take miki haka
zata barki kaca kaca dake amma idan Christmas
tazo kar kiso kiga irin kwalliyar da take yiwa
goodness, nidai ina nan ina yi musu addu’a akan
Allah ya shiryar dasu, kema kici gaba da addu’a
kinji?”
Kwallar idonta ta share saboda tabbas tasan
tasha wahala a hannun mama dalilin bin
mahaifinta da tayi ta taso a musulma dama yar
gata sai goodness itace shalele saboda halinsu
daya da mama wurin kyamar addinin musulunci,
su a kafiran ma yan akida ne,
“Babu komai baba, zanje nakoma” tashi tayi
tareda ajiye masa wasu yan kudi wanda ba zasu
haura dariya shida ba domin yanzu baya aiki ya
jima da yin retire.
Lokacin da goodness ta taso daga church tare
suka taho da saurayinta promise, wata yar
karamar robar giya ya dauko daga cikin
aljihunsa ya fara kurba,
Bata rai tayi ta dauke kanta, “promise am tired
with your habit, baka da aiki sai shan giya?
Gaskiya yana da kyau ka daina shan giya,
kazama dan gayu kadaina wadannan halayen”
Kallonta promise yayi da kyau “goodness har
lokaci yayi da zaki fara cewa kin gaji halayena?
Goodness kece kuwa, nine fa promise dinki
masoyinki, ko har kin fara mantawa dani ne?”
“Ni ba wannan maganar nake maka ba kawai
dai ina son kadaina wannan shan giyar ne”
Jijjiga kai yayi yace “good kije gida zanzo
nasameki agida”
Batare da tace masa komai ba ta wuce tabarshi
awurin tana tunanin ita yanzu koda zata auri
promise to sai ya koma irin oganta na office
wato GM, kai bama ta tunanin zata iya auran
promise din.
Lokacin data koma gida kwanciyarta tayi ta
kunna irin wake wakensu tana saurara domin
akwaita da son kida kullum bata da wani aiki sai
sauraren wakoki kusan duk sabuwar wakar data
fito tana da ita, shigowar ma da promise ne ya
katseta ta tashi zaune, ma tazo kusa da ita ta
zauna tana cewa,
“Wake up, meya hadaki da promise?”
Kallonsa tayi sannan ta kalli ma “ma cewa nayi
ya daina shan giya”
Wata tsawa ma ta daka mata “shut up, naughty
girl,idan baisha giya ba me kike so yasha? Baki
san nida har burkutu nake dafawa nake sayarwa
ba? Babanki ne da ya musulunta yazama
musulmi ya hanani sayar da burkutu, kuma bari
kiji tunda yanzu kin samu aiki to bikinku keda
promise ya kusa,kin jini?”
Daga kai tayi, tashi ma tayi ta wuce daki, tana
ganin haka itama tawuce dakinta ba tareda ta
kalli promise ba, tun daga lokacin taji ta tsani
promise ta tsani halinsa ko church taje bata
kulashi church dinma abinda yasa take zuwa
saboda ma na daya daga cikin manya manyan
church dinne da daina zuwa zatayi takoma
wata.
Yau tunda tazo office take baza idanun ganin
GM amma shiru yau bai zo ba, wani file director
planning yaturo ta bayar kuma file din yana
office din GM shine last wanda tayima sending
din file din dan haka ta tashi ta shiga office
dinshi,
Office din sai kamshin turarensa na explorer
yake yi tamkar yana ciki, kan table dinsa taje ta
fara duddubawa amma yawancin abubuwan
dake kan table din littattafai ne da suka shafi
addini, drawer tafara jawowa tana dubawa nan
dinma duk littattafan sane na addini, jijjiga kai
tayi ganin yanda har a office ma koman shi na
addini ne, dakyar ta iya gano file din karkashin
wata drawer dauka tayi ta fita.
Yinin ranar tayi shine cikin rashin jin dadi wanda
ita kanta ta kasa gane dalili amma tafi alakanta
hakan da rashin ganin GM, nan kuma zuciyarta
ta shiga gargadinta gamida tunasar da ita,
“Ke goodness karfa ki jawowa kanki abinda zai
dameki saboda mutumin nan tsarinsa da naki ba
daya bane, addininsa da naki ba daya bane,
al’adarshi da taki akwai banbanci kuma koda
ace yana sonki to ba lallaine ma ta yarda kuyi
aure ba saboda ita tafi sonki da promise bata
son ki auri bahaushe” zuciyarta ta lissafo mata
wadannan bayanai alokaci guda,
Tabbas hakane to amma ai shi so babu ruwansa
da addini ko al’ada farat daya yake shiga koda
ba a shirya masa ba, kasa hakuri tayi ta koma
cikin office dinshi anan ta samu visitors cards
dinshi birjik, guda daya ta dauka ta koma falo ta
kwafi phone number dinshi ajiki tafara kiranshi
ba tareda tasan abinda zata fada masa ba gashi
gabanta sai faman faduwa yake dum dum,
Kamar baza adauka ba sai kuma taji ya dauka
cikin sanyayyiyar muryarsa mai haifar da kasala
yace “Assalamu Alaikum
warahmatullah,wabrakatuhu”
“Hello sir” tafada a diririce,
“Yes” yafada ahankali,
“Ina yini sir? Yau baka shigo office ba gashi
kanata samun visitors sir” ta shararo karya
saboda bata da abunda zata fada masa,
“Lfy, ki basu hakuri su dawo next time, nayi
tafiyane amma yau zan dawo, gobe zan shigo
office”
“Ok sir adawo lafiya” bai bata amsa ba ya yanke
kiran, duk da haka taji dadin jin muryarsa sosai,
murmushi ta dan saki sai kuma ta bata rai
saboda tuno promise da tayi, ita yanzu a duniya
babbar matsalarta bata wuce promise ba, bayan
shi bata da wata damuwa domin tasan auren
Malam jabir kamar tayi ta gama ne.
Washe gari da safe 8:30 ta shiga office lokacin
duk sauran ma’aikatan basu zazzo ba hatta shi
kanshi ogan bai iso ba hakan yasata shiga office
dinshi ta dane kujerarshi tana juyi tana cewa
“lallai oga yana shan laushi, ashe ni akan kashi
nake zama ga inda laushi yake”
Juyin da zatayi taga ya bude kofa ya shigo,
zumbur ta mike jikinta yana rawa,
“Welcome Sir, sorry sir” tafada atare,
Kujerar baki ya nufa yaje ya zauna ita kuma
tamkar wata munafuka ta fara takowa tana
kallon kasa, daidai lokacin driver dinshi ya turo
kofa ya shigo hannunsa rikeda wani kyakkyawan
yaro wanda da gani babu tambaya tasan dan
oga ne, jarida driver ya ajiye agabanshi ya juya
ya fita, kusa dashi yaron yaje yazauna tareda
kwanciya ajikinshi,
“Good morning sir? Dama ina duba letter headed
ne zan tura mail shine kazo ka sameni” tafada
idonta akasa,
“Kin ganta?” Ya tambayeta yana kallon jaridar
da yake dubawa,
“No sir ban gani ba”
Tashi yayi hannunsa rike dana yaronshi ya nufi
kan kujerarshi,
“Abbu kekena ya karye” yaron ya fada tareda
dalewa jikin kujerar dake gaban teburin baban
nashi,
“Kabari kar kaji ciwo” yafada ahankali,
“Abbu cikina yana fashewa kaji”
“Menene fashewa” yafada yana jawo drawer din
table dinshi,
“Abbu abinci da yawa ne yasa cikina yake
fashewa”
Dan murmushi goodness tayi ta karbi letter
headed din ta juya zata fita,
“Abu zanje gurin baba idi driver” bai jira amsar
uban ba ya ruga da gudu har yana bige
goodness, tana fitowa ta ganshi a kasa yana
kuka,
“Sorry big boy stop crying” tafada tareda
dagashi, daukarshi tayi taje ta zauna akan
kujerar ta,
“Kadaina kuka kaji”
Kai ya daga mata yace “dama bana yin kuka,
abbu yace ni namijine na rinka abu irin na maza,
kuka ba na maza bane na matane”,
Fashewa da dariya tayi ta shafa kansa, “ya
sunanka?”
“Al’amin jabir m Ahmad” yafada yana goge
idonsa da bayan hannunshi,
“Muje na siyo maka chocolate ko?” Girgiza mata
kai yayi,
“No thank you, abbu yana siyo min da yawa”
“To muje ka rakani ni in siyo nawa”
Kudi ta Zara a jakarta ta kama hannunshi suka
fita aikin da zatayi ma bata bi ta kanshi ba haka
ta tafi ta barshi, can bakin titi sukaje ta siyo
chocolate packets biyu ta siyo biscuits manya
manya guda biyu,acan kuwa sai nemansu ake yi
basa nan gashi GM yana son tafiya dama ba
zama yazo yi ba unguwa zaije shiyasa ya taho
da al’amin din, lokacin da su goodness suka zo
yana cikin mota yana jiran al’amin da ma’aikata
suka bazu nemanshi office office, sai zubawa
goodness labari yake kamar dama can ya santa,
Kayan ta danka masa a hannunsa “ungo
kayanka kaji idan kaje gida kasha kai kadai kar
kabawa brother dinka”
“Banida brother ni kadai ne” yafada yana dariya
irinta ta yara,tareda shigewa cikin mota yana
tsalle ajikin abbunshi,
“Abbu kaga chocolate dina”
GM baice komai ba sai kallonshi da yayi yakuma
maida kallonshi jikin window nan ya hango
goodness tana dagawa al’amin hannu.
Tun daga wannan rana bai dawo office ba saima
tafiya da yayi zuwa jihar katsina nan goodness
ta shiga cikin damuwa amma kullum cikin yi
masa waya take tana fadar karya da gaskiya
dan kawai taji muryarsa shi kuwa baima san
tana yi ba, ganin irin mutanen da suke zuwa
wurinshi yasata tambayar massinger dinshi
kodai GM yanada traditional tittle ne? Murmushi
yayi yace da ita kawai dai malamin addini ne
shiyasa mutane suke zuwa sosai hakan ba
karamin dadi yayi mata kuma dama taga
alamun hakan sai dai ita ahalin yanzu tana cikin
matsala domin ma tafara tasowa da maganar
bikinsu da promise wanda ita kuma yanzu bashi
take so ba.
_*Ummi Shatu*_🏻
[8/22, 9:02 AM] Ummi A’isha🏻: *WANI HASKE*
_*NA*_
_*UMMI A’ISHA*_
_21-25_
~~~Bayan ta tashi daga aiki tana komawa gida
ta samu ma zaune tsakar gida tana tace gasarar
koko yau da alama ba taje church ba ko kuma
taje da wuri ta dawo,
Agajiye ta zauna tana kallon ma “ma sannu da
aiki”
“Yawwa my daughter, daga gani kin gaji”
“Ma nagaji sosai wlhi, ina baba?”
“Bai jima da fita ba, sannan gobe ne birthday din
promise dan haka gobe ba zakije office ba
church za muje, gobe zaki sawa promise zoben
alqawari (promise ring) shima zai sa miki, daga
nan kuma sai maganar biki”
Wata uwar faduwar gaba goodness taji saboda
jin maganar da ma tafada nan ta bata rai ta
kalli ma,
“Ma nifa yanzu bana son promise, akwai wanda
nake so, shi promise kwata kwata bai dace dani
ba ni bana son mai shan giya”
Ido cikin ido ma take kallonta “waye wanda kike
so?”
Cikin faduwar gaba tace “ma oganmu ne a
office”
“Musulmi ko? Bahaushe? Kina so ya aureki ya
sakeki ko? Hausawa saki suke yi gashi suna yin
kishiya saboda su basa yin auren zobe”
Daga kai tayi “ma nayarda indai zai aureni”
Matacin gasarar ma ta saki yafadi a kasa tana
tafa hannu “oh chineke, goodness you want to
marry hausa man? You want to marry a person
that your religion and his religion are not the
same, the man that your tribe and his tribe are
not the same even your culture are not the same
with his own culture, hmmm any where, tunda
haka kin zaba, Allah yabaki sa’a amma idan kika
auri hausa man duk abinda yayi miki babu
ruwana, kar ki zo wurina and lastly koda kin auri
hausa ba zakibi addininsu ba, idan kikace zaki bi
addininsu sai na kasheki goodness”
Ajiyar zuciya goodness ta saki “ma kin san dai
nima ina son wannan addinin namu bazan iya
rabuwa dashi ba dan haka ki daina doubting
akaina”
“Goodness in kin bar addininmu kin karbi nasu
sai na tsine miki albarka, sai nasa Allahnmu yayi
fushi dake”
“Ma bazan karbi addininsu ba kidaina fadin
haka”
Tashi ma tayi ta kinkimu bokitin gasarar ta tayi
kitchen dashi tabar goodness da tagumi tana
tunanin yanzu ta ina ya dace tafara tunkarar
auren GM? Tambayar da tayita nanatawa
zuciyarta kenan.
Daren ranar ba tayi bacci ba, asussubar fari ta
dauki bible ta tafi church lokacin ma ta dade
acan tana zuwa ta shiga sahun masu bauta ta
zuba gwiwoyinta a kasa ta rufe ido ta fara
addu’ar samun nasara awurin Malam jabir, sai
da rana ta fito sannan ta dauko jakarta ta dawo
gida tana kiran _”fire, fire”_ domin su a church
dinsu wuta suke bautawa (Allah yayi mana tsari
da ita)
Tana zuwa gida wanka tayi ta shirya cikin riga
da wando matsattsu ko tea bata sha ba ta nufi
office, karfe _9:00_ ta isa lokacin har GM ya
dade a office dan haka jakarta kawai ta ajiye ta
nufi cikin office dinshi domin ta kagu taga
kyakkyawar fuskarshi gashi zuciyarta sai
harbawa take yi fat fat,
Kwankwasawa ta danyi kafin ta bude kofar ta
shiga, can ta hangoshi zaune kan kujerarsa
hannunsa rikeda wani littafi wanda ba zata iya
tantancewa ba yana dubawa sannan ya kunna
karatun alqur’ani kasa kasa yana saurare, yana
sanye cikin farar shadda mai kyau sai kyalli
take, kusan duk kayansa farare ne a yanda ta
fuskanta domin bata taba ganinshi da wasu
kalar ba daga fari sai milk colour,
“Good morning sir” tafada tare da dan
durkusawa,
“Morning” yafada a hankali, sanin bazai kara
magana ba ya sata juyawa zata fita,
“Am kinga” yafada ahankali, hakan yasa ta dawo
tace “na’am sir”
“Kidaina irin wannan shigar idan zaki fito office,
ki rinka sako normal kaya saboda nan kinga
cikin mazane kuma mu a addininmu hakan bai
dace ba, kamar yadda kuma a addininku hakan
laifi ne, dan Allah akiyaye”
Kur tayiwa dan karamin bakinsa da idonta
lokacin da yake mata magana, dagowa yayi ya
kalleta yaga itama shi ta kurawa ido,
“Kinji abinda na fada”
Sai alokacin ta dawo hayyacinta “yes sir, nagode
sir”
“Ok kina iya tafiya” yafada tareda mayar da
idonsa kan littafin da yake karantawa,
Office dinta ta koma ta zauna tana murmushi
amma kuma zuciyarta har yanzu bata daina
bugawa ba, tunani tafara yi itafa duk kayanta
totally babu atamfa domin bata dinkasu kuma
ko ta dinka ba dinkine na cin mutunci domin sai
anyiwa atamfar kaca kaca kafin a dinkata, sai
anyi mata gutsi gutsi, dan haka kayanta daga
riga da skirt sai riga da wando amma duk da
haka zata daure ta zabo masu dan dama dan
ganin tabi maganar da ya fada mata kuma
hakan da yayi ba karamin sake burgeta yayi ba.
Da yamma ta tashi daga aiki ta koma gida, a
kofar gida ta hadu da nura cikin murna ta jashi
cikin gidan domin dama tana son ganinshi,
“Yanzu kin zama worker kinyi wuyar gani ko?”
Nura ya fada ya dariya,
“Sorry nura dama inata son nayi maka waya,
nura dan Allah ka taimakeni ka sanar dani wani
abu dangane da GM dinmu domin zuciyata ta
kasa kyaleni in huta”
Kallonta nura yayi “ban fahimceki ba, wai malam
jabir kike nufi? Me ya faru?”
“Nura nothing, i beg ka fada min pls nura, am in
bad condition, ina bukatar jin wani abu game
dashi domin ina son na aure shi”
Zaro ido nura yayi “aure? Aure fa kikace
goodness, taya kike tunanin wannan auren naku
zai yiyu kina Christian kina ikirararin Allah
ukune, kina mai yarda da cewa Annabi Isah
Allah ne, kina cewa Maryam Allah ce, kina cewa
Isah dan Allah ne, shikuma mal jabir yaki yake
da wannan kalmar, kiran mutane yake akan su
daina furta wadannan kalmomin, kira yake abi
Allah shi kadai,tayaya wannan hadin naku zai
yiyu? Da ace shi ba malami bane mai wa’azi
tabbas may be zai iya aurenki, to amma shi mai
wa’azi ne malamine wanda yayi suna ba a iya
kasar nan ba har da sauran wasu kasashe na
musulmai ai kinga abun kunyane agareshi aji
yana auren wacce ba musulma ba”
Ajiyar zuciya goodness ta sauke mai nauyi
“gaskiya ka fada nura amma kuma ni rashin
aurenshi agareni wlhi tamkar rasa rayuwata ne
dan Allah nura ka taimakeni” ta fadi hakan
lokacin da kwalla tafara bin kumatunta,
“Shikenan goodness babu komai zan taimaka
miki domin nasan haduwarki da malam jabir
_*Wani Haske*_ ne acikin rayuwarki, zan
taimaka miki har kikai ga samun wannan
hasken, yanzu kin san ya za ayi? Zanje gidansa
anjima da daddare zan halarci majalissinsa inda
yake karantarwa bayan sallar magrib anan zan
nemi fatawa cewar wata wacce ba musulma ba
ta ganni tana sona shin zan iya aurenta? Kinga
anan zan gane ko zai yarda ya aureki ba tare da
kin musulunta ba”
“Good nura nagode sosai, ina jiranka idan ka
dawo”
Tashi nura yayi ya fita a lokacin ma ta shigo
tana rikeda bible dinta “hey goodness, meya
hanaki zuwa church? Am asking you meyasa ba
kije church ba? Kin fara wasa da addinmu ko
goodness? Idan kinci gaba da haka pastor will
punishe you nikuma ba ruwana ehem”
“Sorry ma dawowana kenan daga office, gashi
nagaji shine nabari sai da daddare zanje church
din night service”
Fara,a ma tayi cikeda murna tace “i like you my
daughter, God bless you, ina babanki fa?”
“Ma babu kowa agidan lokacin da na dawo ina
jin ya fita”
Kada kai ma tayi ta wuce cikin daki tabar
goodness zaune anan zuciyarta tanata harbawa
domin rashin sanin abinda nura zaizo mata
dashi.
Kamar yadda nura yace haka yayi bayan an
tashi daga karatu ya dubi malam jabir yace
“malam ina da tambaya, wata yarinya ce ta
yaba da nagarta ta kuma ta yaba da rikon
addinina da halayyata tace tana son na aureta
to amma fa ita ba musulma bace, mahaifiyarta
ma ba musulma bace mahaifinta kuma musulmi
ne, to malam ya halarta na aure ta?”
Kallonsa malam jabir yayi yana murmushi “ya
halarta ka aureta,addini ya baka dama amma
sai ta kasance wacce ba mazinaciya ba, sai ta
kasance ya ba baiwa ba wannan shine sharadin,
addinin Allah mai saukine, babu haramci a auren
ma’abota littafi kwata kwata sai dai idan mutum
bashida ra’ayi ne domin ba kowanne mutum ne
zai auri wacce ba musulma ba, kaga kamar ni
idan ka bani wacce ba musulma ba bazan
aureta ba saboda wasu dalilai amma nasan
aurenta ba haram bane”.
Daga kai nura yayi dama tun farko abinda ya
zarga kenan, “to malam amma misali idan kaga
yarinyar zata fada cikin wani hali marar kyau ai
zaka aureta ko?”
Murmushi malam yayi har sai da hakoransa
suka fito “kune yara ku ya kamata kuyi irin
wadannan taimakon”
Yana kaiwa nan ya tashi ya shiga gida, tahowa
nura yayi jikinsa a sanyaye, a farkon layinsu ya
hango goodness tsaye tana jiran dawowarshi.
Tana hangoshi zuciyarta taci gaba da dukan uku
uku har ya karaso suka samu wuri suka zauna,
“Goodness gandoki kin kasa zama agida kin
biyoni nan”
Murmushin karfin hali tayi “ya akayi”
“Komai mai yiyuwane da yardar Allah amma shi
dai a ra’ayinshi bashida sha’awar auren wacce
ba musulma ba sai dai wannan ba shine yake
nuna cewar bazai aureki ba, kinga na farko shi
mutumne wanda ya karanci addini tsantsa
saboda asalima baifi shekara 5 da dawowa
_Nigeria_ ba daga _madina_ acan yayi karatunsa
na addini wanda ya shafe fiyeda shekaru _20_
acan, bayan dawowarshi ne yayi aure yanzu
yana da yaro guda daya, amma goodness mezai
hana ki yarda ki karbi musulunci idan kikayi sa’a
ta sanadiyyar karbar musuluncin ya aureki”
Da sauri ta girgiza kanta hawaye na bin
kumatunta “no, nura ba zan iya musulunta ba
nidai ya aureni a haka nayi addini na yayi nashi,
idan nace zan musulunta ma bazata yarda ba”
“To shikenan yanzu kin san ya za ayi?
Mahaifinsa za muje mu samu kiyi masa bayani,
shi mal jabir mutum ne mai tsananin biyayya
wa mahaifinsa, baya ketare umarninsa, nasan
indai mahaifinsa ya yarda shima zai yarda”
Dan murmushi tayi “Allah yasa ya yarda, nura
nagode, yaushe zamuje?”
“Gobe za muje da safe sai ayi masa bayani”
Cikeda murna sukayi sallama ta tafi church,
acan ta kwana sai da asuba ta dawo, yanzu
promise ya gama gane cewar ta daina sonshi
dan haka shima ya fita a harkarta.
Karfe 10 nasafe suka hadu da nura suka tafi
unguwar masanawa inda acan mahaifin mal
jabir yake, gidane babba kato da masallaci a
kofar gidan, acikin masallacin suka sameshi
yana lazimi, tsoho ne dan kimanin shekaru 70
aduniya fuskarshi duk farin gashi amma jikinsa
ras yake,
Ita goodness bata shiga ciki ba awaje ta tsaya
tasa doguwar riga yar kanti ta daura bakin dan
kwali, nurane ya shiga ciki suka gaisa da tsohon
yayi masa bayanin komai wanda yasani babu
abinda ya boye tun daga farko har karshe
sannan ya kara da cewa “mahaifinta da
mahaifiyarta dukkaninsu yan okene ne amma
suna zaune anan jalingo, sannan mahaifinta ya
dade da musulunta tun shekaru masu yawa da
suka wuce ta sanadiyyar wani makocinsa da
suka zauna tare agarin jos, amma ita mahaifiyar
har yanzu tana nan akan addinin yahudu da
nasara”
Dan murmushi tsohon yayi yace “yaro wannan
mutumin da kace ya musulunta nine nabashi
kalmar musulunci lokacin ina zaune agarin jos
ina koyarwa a jami’ar addinin musulunci dake
garin, shekarune masu yawa bana mantawa aka
kawo min shi akace zai musulunta, nine nan
nabashi kalmar shahada, babu komai insha
Allahu jabir zai aureta kamar yadda take son ya
auretan, amma ka sanar da ita idan tasan zata
aureshi ne da niyyar ta cutar dashi to gara ta
fasa idan kuma tsakani da Allah take sonsa to
falillahil hamdu insha Allahu sai jabir ya zama
_*WANI HASKE*_ acikin rayuwarta”
“Mun gode malam, Allah ya kara girma da nisan
kwana” nura ya fada tareda tashi ya fito inda
goodness ke tsaye tana sauraronsu, duk
wadannan maganganun da akayi acikin
kunnenta akayi su shiyasa farin ciki ya mamaye
zuciyarta marar misaltuwa, machine din nura
suka hau suka bar wurin ya tafi kaita office duk
da cewa yau tasan ta makara sosai amma haka
zata daure taje dan ta ganshi,
Murna fal acikin zuciyarta nura yana ta kara yi
mata karin bayani har suka je office din ta
sauka tana yiwa nura godiya ta shiga ciki,
Massinger dinsu ta samu zaune shi kadai
ganinta ya fara yi mata sannu da zuwa, anan
yake sanar da ita oga yana conference room
yana meeting da directors dinshi, wannan rana
ta yau goodness na cikeda farin ciki.
Sai da lokacin salla yayi sannan masu meeting
din suka firfito domin zuwa salla, office dinsa ya
nufa domin yin alwala, yana shigowa sukayi ido
hudu da goodness, dauke idonsa daga kanta
yayi yashiga office dinsa bayan massinger ya
bude masa kofa, binsa ciki tayi lokacin ya cire
hular kansa yana saka silifas zai shiga toilet,
“Sannu sir” tafada cikin farin ciki
“Yawwa” yafada yana balle clips din hannun
rigarshi,
“Sir yau naje unguwane shiyasa ban zo da wuri
ba”
“Babu damuwa amma ki kiyaye next time”
“Yes sir” bai sake magana ba ya nufi toilet.
***
Bayan ya tashi daga office around _5_ ya nufi
gidan mahaifinshi, a babban falon shi ya tarar
dashi zaune ya bude katon alqur’aninshi yana
karantawa, jin sallamar malam jabir yasashi rufe
alqur’anin ya juyo ya dubeshi da fara’a a
fuskarshi,
Zama yayi kusa dashi ya russuna ya
gaisheshi,bayan ya amsa ne yace
“Jabir dalilin kiran da nayi maka ayau shine
kaga dai nafarko kana daya daga cikin mutanen
da ake girmama su acikin garin nan ake koyi
dasu, kuma kallum aikin samun lada kake yi,
wannan dalilin ne yasa yau na sake kawo maka
kokon barar wani aikin samun ladan, nasan
Allah ya hore maka arziki, da kuma zuciyar da
zaka iya rike mata biyu, wannan dalilin ne yasa
na umarceka da kayi hakuri ka daure ka auri
wata yarinya ma’abociyar littafi wanda nake
kyautata zaton cewa idan Allah ya yarda _*wani
haske*_ ce agareka kamar yadda kaima zaka
kasance _*wani haske*_ agareta, ba musulma
bace amma ta kamu da tsananin sonka saboda
nagartarka da kyawawan dabi’unka gamida
kyawawan halayenka da ta duba,ni kuma nasha
mata alwashin insha Allahu zaka aure ta zaka
zame mata _*wani haske*_acikin rayuwarta”
Tun farko tun asali ko acikin mafarki bai taba
tsammanin zai iya aurar wacce ba musulma ba
saboda basa burgeshi amma yanzu bazai iya
yiwa mahaifinshi gardama ko musu ba dan haka
ya aminta “shikenan malam insha Allahu zan
aureta kuma zan zauna da ita”
“Allah yayi maka albarka jabir, amma kayi min
alqawari zaka riketa bisa amana”
“Malam insha Allahu zaka sameni mai rikon
amana akanta tareda yin adalci”
Albarka mahaifin nasa ya shiga saka masa
tareda yi masa fatan alkairi acikin rayuwarsa,
sallama yayi masa ya tashi ya tafi yana jimamin
wannan al’amari acikin ranshi, wai a matsayinsa
na mai wa’azi shine zai auri wacce ba musulma

Leave a Comment