Books Reviews & FAQs

Wuka A Zuciya Hausa Novel Complete

7/18, 9:22 PM] F A T E E🤎:             *_Wu’ka a zuciya❤🔪*_
(_Bleeding heart💔_)

~Love❤️,Touching Story💔~

_Story and written_
_by Bintou_

__Marubuciyar__
*_hawan jinina_*
*_Maqaryaci (fake life)_*

*001*

”_Bismillahir Ramanirrahim
Da sunan Allah Mai rahama mai jin kai_
_Ya Allah ka ban ikon kammala wannan littafin  Nan sannan kasa in isar Da sakon Da nake San isarwa Ameen,_”’

*_Wannan littafin badan cin zarafiN wani ko wata zanyiba*_

*80% True Life Story Ne*

_*The Beginning *_

*Kaduna-Kabalan doki*

3:35Am

Dare Ne Sosai,ko ina yayi tsit, Baka jin sautin komai Sai Na tsuntaye, The sky was aglow with bright city lights, wata da Taurari Sai Walqiya Suke Kaman azurfa a sararin samaniya Jefi  Jefi haushin  karnuka  Na cigaba da Ratsa  Ni’imtaccen Shurun Daren  Hasken street light ne Mamaye da ko Ina na fadin Anguwar, a daidai  lokacin da kowanne halitta ke ganiyar hutawansa,  yayin da wasun mu suka duqufa kan darduma SuNa kai kukansu ga Mahalicci .

Kofofi  Uku Ne Ajere Masu dauke da launi   Milk color ne wato mai ruwan Madara , dan madaidaicin gini ne Mai dauke da matsakaitan dakuna guda uku ma tsakaita.  .  *da kaga ginin zaka gane gidan tazurai ne*

A bakin qofar tsakiya Na hango wata budurwa wacce bazata haura Shekaru Ashirin da ‘daya ba , tsugunne take ta takure waje Guda sai Faman makyarkyata takeyi Kamar Mai jin Sanyi  Fuskarta a 6ace da Jirwayen hawaye kallo daya zaka mata ta Baka tausayi .

kofar farko da ta ji an bude ya sa ta kamewa daga inda take durkushe lkci daya ta xaro ido gabanta ya fadi don ita dai a iya saninta babu kowa a dakin farkon .

“Subhanallah  Aeesh me kike yi anan Cikin daren Nan to 4aM fa.”

Cewar gayen da ya fito hannunsa Riqeda buta A tsorace.

Miqewa tayi Cikin azama ta  nufoshi Sai a yanzu wasu zafafan hawaye suka Samu daman 6ullowa suka wanke Mata fuska

“Uncle Kamal please Tell him ya fito Muyi magana bazan iya Komawa Gida yayinda yake fushi dani ba ”

Ta qarashe cikin  matsanancin kuka.

Sosai Aeesh xata baka tausayi  Sbd ynd take kukan takanin  ta da Allah.

sakin baki Kamal yayi cikin  Mamakin Da ya kasa 6oyuwa a Allon fuskarsa, Taya zai yarda ita dince Ma?, an ya ba Aljannu Ne suke Neman Suyi masa Siddabaru ba?, kalloN qafafunta yayi don ya tabbatar da ita din ce, tabbas itace,  Cikin Mugun Mamaki yace

“Karkice Min tun bayan Esha’i Dana jiki dashi baki koma gida ba”

Kasa ce wa komai tayi sai hawaye da sukafi ‘karfiN ta.

Kamal  jiyakeyi tamkar yamata kuka, tausayi take bashi ainun, wannan wace irin Masiface? Akan soyayyar ‘da Namiji Mace ta kasance a waje a daidai wannan lkcn sbd ‘dan sa6anin da suka Samu da shi a cewarta Idan Bai yafe Mata ba Bazata iya Barin Motsawa daga wajen ba.

Tabbas Aareef yana bata wahala sosai akan soyayyar Shi, gashi anzo ga6ar tashin hankalin da bazata iya sarrafa kanta akan shi ba , duk Aeesha tagama canja kamanni, tarame sosai, Ga uban haske datayi sai kace Ba Aeesh Muneer ba, a halin yanzu  ko mak’iyinta dolene ya tausaya mata

Kauda kansa yayi cikin yanayi Na qoqarin dakatar da hawayen sa Zubowa yace

“A haka Arrow ya shige ciki Ya bar ki a waje?,  Anya yasan kina Nan kuwa? ”

“Yasani ba”

Haushi  yakamashi, wai wannan, abokin Nashi Anya zuciyar Mutane gareshi kuwa ❓, Abubuwan da yakeyi Sam basu dace ba,Wlh Idan Allah ya tashi kamashi akan haqqinta bazai ga dakyau  ba.

Huci Mai zafi ya furzar kana yace

“Mey ya hada ku? ”

“Dama Akan Abin da ya faru jiya Ne,  yau Reey ta tareshi a Hanya ta ci mutuncinsa, Tho yaji Zafi Sosai  shine  ya kira Ni  Bai daice Min komai ba amma Na fahimci yana Cikin Fushi daqyar Na samo kan sa yayi Magana ….. yace In zo, Ban Samu daman zuwa Ba Sai bayan Isha’i lattin a Nayi Ne yasa Ya qara Jin Ciwo sosai ya qara daukan Zafi akan nada babu irin Roqon da ban Mishi ba Amma Bai kula Ni ba Ina ji Ina gani yashige ya kulle ‘kofar, Don Allah Uncle Kamal ka taimaka wa Rayuwata Ka Bashi tayani haquri … Wlh bazan iya daga ‘kafata daga Nan ba Alhalin fushin bearr Na kaina ba…. ”

Bai katseta ba har ta Kai aya  kalloN ta yakeyi yayinda wani Mugun tausayinta ke cigaba da ratsa duk wata kafa ta jikin sa

Ahalin yanzu ba qaramin tausayi take bashi don abun duk ya hargitse mata Akan Aareef ta Zama kamar zautacciya , tsawon lokacin dasuke tare be ta6a ganinta acikin irin wannan yanayin ba, Duk da tashayin Abubuwan al’ajabi da dama akan shi, Amma Na yau yafi Na Kullum ta6a Masa zuciya,  _Akan laifin da ba ita tayi ba ya za6i ya Azabtar da ita ta irin wannan sigar?_  .

“Wlh arrow bashi Da digon imani ”

Kamal ya fa’da a Zafafe tareda qarasawa Kofar Aareef ya shiga Bubbugawa da iya qarfin sa amma kamar babu wani mahaluki dake rayuwa a dakin .

Roqon sa ta shiga yi akan ya Daina  buguN ‘kofar da qarfi bazai ji dadin haka ba in  ya farkq.

Duk bubbugar kofar din da’ake yanaji amma beda kuzarin motsawa, he’s so weak har cikin zuciya, jinshi yake kamar marar lakka ga barcin dake jan shi, Don saida yayi Nisa da barci sannan aka fara buga ‘kofar.

“Aaroe…Arrow open up”

inji Kamal yana sake bubbugawa yana leqenshi at the same time ta Small Opening Din Door lock .

Shiru Aareef yayi don be iyawa, da yana iyawa da be dauki tsawon lokaciba, Ban da tsaki babu Abin da yake ja babu Abin da ya tsana kamar Un Necessary things that interrupt his Sleep .

Ganin beda niyyar budewa ya ‘Kara tun zura Kamal

“Aareef Pls bu’de ‘kofar Mana kayi baqi  ”

A fusace ya miqe yana jan tsaki tareda duba agogo qarfe 3:52am.
A ransa Maimaita kalmar baqi yake.

Kamal  Najin Alamar An fara bu’de ‘kofar yayi azAmar Shigewa Dakinsa da ‘yar Butarsa Gudun Abinda zaikai ya kawo daga 6angaren Arrow.

Yana hada ido da ita yaji Gabansa ya fa’di, Shi fa har ya mance da ita fa.

Girar sama da ta qasa ya hade ya Kauda fuska rai 6ac3 yace

“Mey wai”

Ya fada fuska a yamutse.

“Al bearr Please…………. ”

“What…!, Me ya kawoki Cikin Daren Nan?, wae ke wace irin Mayya ce? ”

Aareef ya dakatar da ita a tsawace.

“Beer har yanzu Baka haquraba? ”

Wani kallo ya watsamata sannan yaja dogon tsaki yana cewa

“Mey kikeyi a Nan at this time of night?, Wai ke wace irin Mahaukaciya ce?, a haka kike so Na Aureki?, in Na Aureki me Na Aura kenan?  rashin Aji?, ko Rashin Kamun kai ko Kuma Yawon dare? ”

Dago jajayen idanunta tayi  Duk ilahirin jikinta rawa yake zuciyarta Na bada wani irin sauti Na bugawa. Ga hawayen dasukaqi Tsayawa.

“Albeer Ni kk kira Mahaukaciya…?, Ni kake Alaqantawa da irin munanan maganganu irin wannan, Ni zaka tozarta Aarrow?,  I have been waiting for u Since 8:30 just to hear the word of forgiveness from u, pease please Don Allah… Please forgive me on Reeyyer’s Behalf 🙏… I payed for happiness please Don’t break our promise ”

Ta qarashe Cikin Rarraunar Murya Mai ban tausayi.

KO kadan bai ji digon tausayinta ya dirsu a ransa ba illa ma ‘kara tunzurashi da tayi.

“Awww Gori zaki Min akan  kin bani wasu ‘yan chanji for us to be happy❓,  wait lemme Tell you Something Yes na kar6i kudiN ki don maganar peace or whatever, Amma Right now Subscription Din ki ya qare and again ki sani  bakikai standard din zaki Siya haappiness Dina ba koda daidai da second dayane.
Bakida wannan quality din, and also kudinki basu isa susani yafe Miki ba saboda I don’t fucking care about your goddamn money! Ke suka Dama ni ko ajikina, lastly kisan wanda zaki dinga bibiya dadaddare domin yayinda kike bin wasu kamar kadduwa kike ikirarin kin zo bada haquri wasu a lokacin Suke sanin kin wanzu a duniyarnan , koda Wasa karki Sake Nuna kin Sanni Ni Albeer din ki na tafi Love Strike  If Not a bakin Soyayyar ki, Eh na fada, Wannan Karon ba yayanki zaki hada Ni dashi ba,  Ki hada Ni da uwarki ko ubanki da yake ‘kar’kashin ‘kasa.. F… U.. C… K….. Uh, f*ck Dem”

Aeesha datayi mutuwar tsaye bata ko motsi takasa cewa komai don she never expect this 4rm Him da Ace wani ne ya gaya mata Aareef zai iya mata haka da nan take ta qaryatashi   .
Dakyar ta iya bude baki ta nuna kanta da yatsa duk ilahirin jikin ta rawa yake

“… Ni… A”

“Go to hell!.,.. To hell with you and ur fucking act , if u wish Ki kwana a nan don’t go home I don’t fucking care! BASTARD! ”

ya ‘karashe maganar da banging kofar da karfi yayi Shigewarsa.

Har tsakar kanta taji zagin dakuma bugawar kofar ako da yaushe bata Ganin laifin sa koda Me yayi Mata Amma ayau ta6o marigayin mahaifinta da yayi yasa taji zafin maganganun Sa.

Bin inda yake da kallo kamar zai dawo wajen, zuciyarta  inbanda bugawa babu abinda take ga wani suya na musanmman da take.

Kalaman sa sai faman yawo suke Mata a qwaqwalwarta.

ji tayi Kafafunta Na neman kasa ‘daukarta,  Wani irin yam, yam takeji yana yawo a jikin ta Cikin takaitaccen lokaci Duhu ya Mamaye Mata ganin ta tayi baya ta fa’di a sume .

Daidai lokacin kamal ya idar da Sallah yafito Daga dakin Shi……. 🔏

_*Asalin labarin *_

Zaune yake a tamfatsetsen office ɗinsa, dagashi sai dogon wandon suit da kuma rigan shan iska (open  shirt)  dake sanye ajikinsa, laptop ɗinsa ne agabansa yana shigar da wasu bayanai gaba ɗaya hankalinsa nakan laptop ɗin.

turo ƙofar office ɗin akayi tare da shigowa, yaji motsin buɗe ƙofar amma sam baiɗago kansa ya kalli wanene ya shigo cikin office ɗin ba,duk da Qamshin turaren Su Na Black Lady ya bayyana Masa ko su waye,   yau sosai ƴan miskilancin nasa suke kusa.

Jingina bayanta tayi da jikin ƙofar tana kallonsa yayinda Juwayriyyah ta qarasa da Sallamarta, wani irin murmushine ya bayyana akan fuskarta, 6acin ran da ta shigo dashi ya ware.

Bata san meyasa ba kallonsa kaɗai idan tayi yakan sanya mata nutsuwa, sosai take,  komai nasa yana burgeta tana son duk wani abu nasa, musamman yanayin yanda yakeyin adonsa da miskilancin sa Wanda dama zamu iya cewa Gado sukayi Gabaki ‘dayansu ita dashi.

cikin takunta Na qasaita tasoma takowa zuwa cikin office ɗin,    Ƙaran takalman dake ƙafanta shiya fara sanar dashi ta Shigo .

jiyayi  ya rasa duk wani Nutsuwa tasa Harta ƙaraso gaf da inda yake bai ɗago dakansa ya kalleta ba,  cikin muryar shagwaɓa tace.

“Kai yaya kafa saN Na Shigo ”

Kamar ma baisan da mutum a wajenba haka yayi banza da ita,

Turo baki tayi kamar zatayi kuka tace

“Yaya Ashman Dakai fa Nake ”

Batareda ya ‘dago ba yace ta fita tayi sallama sannan in ya amsa ya bata umurni sai ta shigo.

Ranta baiso ba haka ta fice Juwayriyyah Nata Faman yi mata Dariyaa.

A bakin qofa ta tsaya tayi Sallama sai a lokacin ya ‘dago, ya Amsa Sannan ya bata umurnin ta Shigo.

Ta Shigo tana kumbura Fuska, ko kallon su baiyi ba yace

“Kuje parlor ku jira Ni ”

Tun daga yanayin Maganar sa suka fahimci yau kam hali ya Motsa, Basu Musa ba Suka Shiga ciki.

Saida ya Gama Abin da yakeyi Sannan ya iskosu zuwa lokacin Aeesh ta cika tayi Fam.

Dariya taso ta bashi Amma ya basar ya dubi Reey daketa Faman gaidashi yace

“Qanwata Me Zan kawo Miki?, liquid ko Solid Ko kuma swallow kike So Na saN kina sonshi Sosai”

Magana yakeyi Ahankali Cikin Nutsuwa Fuskarsa Na kalloN Side Din Reey.

Dariya Aeesha tayi don ta fahimce Shi da ita yake, Hakan wai duk Salon kaucewa A rarrasheta ta saki fuska Ne.

Cikin dariya takai mishi jifa da Pillow CusSion ya  kar6e Shima dariya.

“Nasa P. A mutuniyarki ta kawo muku Abinci kafin Nan meke tafe da ku?,  Naga Alama kamar an 6atawa Qanwata rai 2n a waje shiyasa ko arzikin Gaisuwa ban Samu ba ”

Guntun tsaki taji
“Mtsww…. Wlh wani Gayene yake ta Faman Bibiyar Rayuwata, yau harda Zuwa gida yana gayawa Umma wai Aurena yakeso ”

“This is Serious ”

Ya fada yana gyara Zaman shi sannan ya cigaba da cewa.

“You mean kin Samu life partner Right…. …? ”

Sai ya kwashe da dariya, Irin dariyar da bata ta6a Ganin yayi irin shi ba tunda suke.

Murmushi mai ciwo tayi ganin yadda yake dariya harda tafa Hannu.

Wato ga mahaukaciya , kodayake duk wanda yasan yanayin Alaqarta da Samari yakuma ji abinda takecewa yanzu saiya yimata daukan mahaukaciya.

“Is it funny?” Ta tambaya tana kallon yadda fuskarsa ke qara annuri.

“Very funny” yafada cikin dariya.

Murmushi  tasakeyi

“It may sound funny but amma am not joking..am serious 😒, I need ur help”

“Yes, it’s a joke, a creepy joke Abege”

Yafada murmushi akan fuskarta

“Bro Saidai yanzu ba lokacin barkwanci bane, we’re discussing a serious issue, magana ta hankali”

tafada tana ha’de fuskarta .

Ajiyar zuciya ya sauke,

“Ok Mrs yace yana Son ki Me kikeso Nayi? ”

“Haba yaya Ashman Yanda kayiwa fatahi haka zaka Masa please kace an badani wa kai”

“No I can’t…..”

Ya fa’da Calmly yana runtse idanu.

 

Alhmdlillah
Ya Allah yanda Na fara da Sunanka kasa Na qare Da Sunan ka  🙏🙏🙏🙏🙏🙏

Ina jiran ra’ayoyin ku Akan wannan page din…..

4th March

Bintou ❤
[7/18, 9:22 PM] F A T E E🤎:                 💔 *WUƘA A ZUCIYA* ❤️🗡️
_(Bleeding hearts)_

*002*

*Let me decorate each and every ray of the sun before it shines bright on Eid….With happiness and success, prosperity and glory ,Ya ALLAH kasa Azumin da muka yi  karɓaɓɓu ne ,ka biya mana Buƙatun mu,YA Allah🙌👐🤲 EIDBARAK 💙💙💙*

*002*
*Still the beginning*

…ki bashi Dama”

Kusan a tare Reey da Eesh suka dago Suna dubansa a mamakince

“In bashi Dama Kuma”

Cewar Aeesha Cikin tsananin mamaki.

“Eh…..Ya nemi soyayyarki ne, Yana neman ki bashi Daman da bakibawa sauran samarin bane, At least give him a chance”

Ya qarashe Maganar da Zuba mata idanu , itama Zuba masa Idanun tayi tana turo baki  ,saiya sakar mta harara dawani munafikin murmushi, saika rantse da ALLAH kallon soyayya yamata.

Ita kam sunkuyar da kanta tayi Saboda wani irin Abu da taji ya ratsa Duk  ilahurin jikinta.

duk da kwarjinin dayamata saida ta sake turo baki gaba da hararsa a kaikaice, ALLAH ma yasota baiga hararba.

“Nifa Zuciyata nada Wanda take so”

Kallon mamaki ya mata, ya zuba mata idanu, Murya Chan qasa Cikin sigar ra’da yace

” Wa …kenan…..?, Ke har kinsan Menene so?, Kinsan yanda ake fa’dawa a so?, me kika sani akan so”

“Yaya bansan So ba, Amma masana so sun fasalta yanda so yake, ko ban kamu duka ba nasan na kamu ta wani 6angaren bugun Zuciya ta ‘karu daga lokacin da na kalli qwayar idonsa ,dogo ne sosai kyakkyawar fuskarsa a Koda yaushe Dauke take da wani irin shauqi ta musammman ,Salon sa daban yake a Cikin Al’umma, Shikadansa ke Maye gurbin Aboki da na ‘yan uwantaka ya mamaye gabaki Daya Cardiac Region Dina 💘, Bai barma wani Koda mashaqar iska a Zuciyata bah, jarumi yake, Sadauki na Bai Chantanci na ha’da Alaqarshi da wani ba Koda bana sonsa hakan kamar cin Amana ne”

Hararara juwayriyyyah ta Wurga mata hadi da jan tsaki wlh da tasan Maganar da ta kawo su kenan bazata yarda ta rakota ba ,Wannan ai cin fuska ne🤕.

Ashman kam idanunsa ya lumshe yana sakin wani k’asaitaccen murmushi daba koyaushe yake irinsaba.

“….okay if I may ask who is he?, how can I get to know him?”
Ya fada a hankali

“Me zai hana”

Tayi maganar tana kallon Reey , Nan ma hararar ta sake Wurga mata tana  dogon tsaki”

Dariya tayi don tasan dalilinta nayin haka.

K’asaitaccen murmushinsa yayi yana gyara zamansa

“Lallai koma waye na tabbata yayi babbar Sa’a  kamar yanda qanwata take mai Babbar Sa’a itama, Waye Wannan luckiest guy din…tell me”

“Wani Handsome ne a  kamala yk, I think bayada nisa da Asibitin ka You might know him sef, yanada good Qualities da ake buqata ya zama Abokin rayuwata but dukda haka i don’t know why Besty hates him”

Ta ƙarashe maganar cikin marairaicewa tana duban Reeyah.

“If he makes you happy he doesn’t have to make sense to Her, ke zaki zauna dashi ba ita bah”

Da mamaki Reeyah ta kallesa saiya d’agamata gira Sai kuma yad’an ta6e baki .

“Yaya na tabbata da ka taɓa ganinshi bazaka Goyi bayan soyayyar su ba, He’s Rough bashida nagarta ko kaɗan”

Cewar Reey

“What ever….bake Zaki zauna dashi Ba”

Dariya Esherh tayi mata mai haɗe da fakaitaccen gwalo.

Shima Mmurmushi yayi yadan ja hancin ta ,saitin kunne ya ya ra’da Mata.

“Your courage was ur crown and u wore it like a queen I like ur smile”

Kallonsa tayi sannan ta kalli juwayriyyyah wacce ta basar tunda ya kafa mata ƙusa, ya d’aga mata gira da cije lips sannan ya mik’e.

Tamkar sokuwa haka ta bisa da kallo Wasu abubuwa na cigaba da yawo Cikin jininta.

gaban filing cabinet dake office d’in ya nufa, ya dauko wani key ya dawo inda ya barta tamkar wata gunki, hannunta ya kamo ya damqa mata key ɗin.

“Key din office ɗina ne ,In kinje asibiti Gobe, ki ba Hisham akwai surgeries 2 da ya kamata muyi gobe…. Dr Naseer ne zai wakilce Ni , cus Bazan samu zuwa gobe bah ,Zan je Kano…”

“What…! kano kuma?….”

Ƙasa ƙarasawa tayi sakamakon wani mugun kallon daya watsa mata wanda ya hargitsa y’an cikinta da tunaninta, Tunda take bai taɓayi mata irin kallon nan ba hakan yasa ta tsorata Sosai.

A ransa kou cewa yayi ~Anzo wurin~

Ta6e baki yayi yaɗan janye idonsa daga gare ta, Shiru yayi na ɗan Wani lokaci kafin yace

“Wani abu ne ya taso na Gaggawa,So I have to go”

“Ayyah Yaya we gonna miss u”

Reey ta fada cikin sanyin murya.

“I feel like crying …”

Aeesh ta faɗa cikin rawar Murya Kamar mai Shirin kuka.

Saurin ɗagowa yayi ya dubeta, ta Sunne kai tana Matse Ƙwalla.

~Yasan za’a Rina ko ɗazu da zai taho office daga Asibiti saida yasha faama da ita dan cewa tayi binshi zata yi,Alhalin lokacin barin aikinta baiyi ba~

Haka kawai yaji jikinsa yayi sanyi, yasani yanzu nan sai tayi masa kuka, Wani irin Shaƙuwa ce ta musamman a tsakanin su da Basua iya rabuwa koda na wasu awannin ne .

Haɗe fuska yayi ya kauda kai daga kallon ta gudun kar Kukanta yayi tasiri wajen karyar masa da zuciya.

“Kar ki Mn kuka anan”

Daidai lokacin Door Bell yayi ƙara ya bada izinin a shigo.

P.A ɗinsa ce ɗauke da Tray ,Shigowa tayi tana wani irin karaikaya As usual, cusa kai babu kwarjini .

Wani Irin harara AEESH ta danna mata, Bata san meyasa ba she just hate her , ji take kamar ta maƙuro wuyarta ta aikata chan inda in an tafi ba’a  dawowa, Tunda take a duniya bata taɓa tsanar wani Abu kamar yanda ta tsani Meenal (P.A) ba.

Ƙarasowa tayi Cikin ƙasaitaccen takunta mai jan hankali Tana ƙoƙarin Ajiye Tray ɗin ya miƙe tare da ɗaukar Keys da phones ɗinsa Batareda ya kalleta ba yace

“Amina…. ki ba ma Gateman Abincin , am off for today”

Diff komai nata ya tsaya She can’t believe What he just said!, Ya ko san Wahalar da tasha Wajen Girka shayin kuwa not Even what she went through When Oning gas!, Saura ƙiris ta ƙona ƴar yatsar ta Don ita tunda take Bata taɓa kusantar Kitchen da Sunan yin Girki ba.

“But sir……”

Kasa ƙarasawa tayi sakamakon dakatar da ita da yayi ta hanyar daga mata hannu.

“Ihkty Ku tashi mu tafi”

Wani irin sanyi ne ya ziyarci zuciyar Esherh A lokaci guda , bata san lokaci da ta Saki wani ƙayataccen murmushi ba , kusan a tare suka Miƙe ita da Reey Yayi gaba suna binsa a baya,Babu yanda Meenal ta iya dole ta fita Zuciyarta na ƙuna kamar Garwashi, ta kudurta a ranta saita ɗauki fansar wulaƙancin da Yayi mata a gabar mara kunyar ƙanwarsa.

Kai tsaye Gidan Su Esherh ya sauke su Batareda ya shiga ciki ba ya juya ya koma nasa Gidan inda yake ɗan hutawa.

Itama Juwayriyyyah bata Wani Jima ba Esherh ta rakota Ta koma gida.

Tunda Ashman ya Gaya mata zai tafi Gida kano take jin Wani iri,Taji Gabaki ɗaya tafiyar tasa bata Kwanta mata ba, Jikinta yayi sanyi Sosai, Har Umma ta fahimci Akwai Abinda ke damunta , aranar jiki a sanyaye ta wuni har dare.

Yau kam kamar yanda yasaba Zuwa a ko wane lokaci Suna cin Abincin Dare tare yaɗanso ya makara.

Bayan An idar da sallar Isha’i suna Zaune itada Habeeb ƙaninta tana masa  Assignment ,Umma ta shigo parlorn tana cewa

“Har tara saura Sufyanu Baizo ba, kije ki ɗau Abincinki kici kuje ku Kwanta kunsan Gobe Akwai Aiki”

“Zaizo ƙila yana hanya ne”

Ta faɗa Cikin turo baki.

“Tho Anty ki kirashi Mana”

Cewar Habeeb

“Banida numbern shi”

Wannan Furucin da tayine ya fallasa dalilin rashin Walwalarta Tunda ta dawo _(Ƙila saɓani Suka Samu a tsakanin su)_
_cewar Umma Cikin Ranta_

A fili kuma Taɓe baki tayi ta ce

“Kunfi kusa…”

Sallamarshi Ce ta dakatar da ita duk suka ɗago suna Amsa Sallamar.

“Kaga Ɗan Halak kaƙi ambato, Yanzu muke Zancen ka da ita”

“Umma hala Gulmana ta kawo mk?”

“A’a Gani nayi yau ka jima baka shigo ba shi yasa nace taci nata abincin karta kwana da yunwa”

“Ayyah aiko ban kyauta ba na bar ƙanwata da yunwa, Amin Afuwa na Samu Emergency call ne a asibiti and you know I can’t Ignore it ,…..Ina wuni umma”

Ya ƙarashe maganar da durƙusa har ƙasa tareda Duban Aeesh Wacce ta kafe shi da ido.

“Lfy lau, ya gajiya? Shine yau ko kashigo? , infact dazu Ina Ganin Shigowar Motarka Amma Ka kasa Shigowa kayi Wucewarka”

“Wlh Umma ɗazu agajiye nadawo ne kuma nayi tunanin baki nan, yanzui ma ttunanina kunriga kunyi barci ne”

“Ayyah, to ya Aikin ya tafi?”

Ta tambaya tana Kallon Aeesh da har yanzu idanunta ke kansa Ta kasa Janyewa daga kallon sa.

Ƙarasowa yayi ya Zauna kusa da Aeesh, hakan Yasa Ta dawo daga duniyar tunanin da ta shiga .

Miƙewa Habeeb yayi yanufi hanyar Kitchen Yana faɗin

“Aunty wannan irin kallo haka?”

Murmushi duk sukayi

“Yaya, anyi Aikin lfy ?”

Murmushi kawai yayi Batareda ya bata Amsa ba

“Yayi kyau, Sufii shine kuma mu Saidai muji a salensa? Ashe Gobe zaka gida ko a gaya mana? ,Ai ko ƴar daddawar Nan na baka Ka ba Uwata Goggo”

Shiru yayi yana Murmushi don dama yasan arina Aeesh ta riga ta gaya mata komai.

“Umma kiyi haƙuri tafiyar Gaggawa ce ta zo Mn nima ban shirya Masa ba,Kuma ae ko yanzu bata ɓaci ba In Akwai daddawar Sai ki bani na bata”

Murmushi sosai tayi

“Aikam akwai Daddawanni ma kala kala In zaka Tafi kamin magana in haɗa maka da Citta harda Kanumfari nasan tana so ”

“To umma”

“Yaya tare zaku da Anty?”

Inji Habeeb ya faɗa lkcn da jera msu Abincin su saman carpet

“Nope”

Ya bashi Amsa a Takaice

Wasu zafafan hawaye ne suka gangaro Mata tay saurin taresu da bayan hannunta gudun karsu gani ,Amma inaa ta makaro tuni Duk suka Ganota.

Miƙewa Umma tayi Tayi ɗakinta tana musu sai da safe.

“Yaya Na lura kaida Aunty ɗayanku bazai iya Rayuwa Batareda ɗayan Ba”

Habeeb ya faɗa yana maida hankali kan Assignment ɗinsa.

“Me yasa kace haka?”

“Yaya Aash kaida ita Tare kuke komai tun tasowar ku,Alaƙar dake tsakanin ku zaku fi dacewa da juna a matsayin MATA DA MIJI ,Bazan manta ranar da ta dawo Gidan nan Ba Ummu Da yaya Saleem Sunyi Sunyi taci abinci Taƙi ci wae Sai kazo, kamar da wasa ranar kwana tayi taƙi cin komai sai kuka ,Kai kuma kamar kasan komai Da sanyin sassafe kayi Mana dirar Mikiya, Ranar Naga Abin Mamaki Naga tsantsar Shaƙuw…….”

“Ma frnd Shut up….”

Aeesh tayi Saurin Dakatar dashi

“Yen yen yen yen ,Surutu babu Comma babu Full Stop …..!, Abege carry ur books and Go to bed”

“Ikhty …”

Ashman ya kirata Cikin Sanyin Murya.

“Na’am yaya na”
Itama ta amsa Cikin Sanyin Murya.

“ZAKI AURENI….?”

“In Aureka inyi ya da Sadauki Na?”

Ta faɗa innocently…

Bude idanunshi yayi ya kalleta Batareda ya iya cewa komai ba, chanza maganar yayi da Cewa

“Am hungry let’s eat”

Miƙewa Habeeb yayi  yay msu Saida safe.

Babu ɓata lokaci ta zame ta zauna Bisa carpet Shima ya Samu Guri ya zauna, As usual da kanshi yayi serving dinsu sannan ya Saka Two Spoons a ciki.

Ba musu tashiga ci Saidai Duk yadda yaso su hada ido taƙi yarda, Yayi Expecting Fiye da haka daga Gare ta, Wannan Shine karo na Farko a rayuwarta da zaiyi tafiya har na Tsawon kwanaki Biyar Batareda ta bishi ba , Dole taji wani iri , ya saban mata da Hakan Basua iya Kwanaki biyu basuga juna ba duk uzurin da wanin su keda shi , Tare Suke Abubuwa da dama tare suke Cin Abinci a kwano ɗaya, idan ta kama ba yadda zasu yi Sai dai Su ci tare ta Video Call,suna ci suna kallon juna Shaƙuwar dake tsakanin su ya Samo asali ne tun Sanda Mahaifinta ya Rasu ta dawo Hannun Mahaifinsa da zama lokacin da Gabaki ɗaya ahalin Gidan Suka tsaneta Basu ƙaunar Ganinta a lokacin ya ɗauketa ya maidata tamkar ɗiyarsa wacce ya haifa ta cikinsa babu Abinda ya isa ya taɓa ta babu Abinda ya isa ya Rabata dashi, shi yake mata komai kama daga Wanka wanki shike Kaita makaranta ya dawo da ita yay mata girki Suci tare , har lkcn da takai matakin SS2 a Secondary School ya koya mata Yin Wasu Abubuwa Dakanta Irinsu Wanki da Shara,Amma bai koya mata girki ba Gudun kar Tayi kasada ta Ƙone ko don wata rana,Tana kammala karatun ta Secondary dakansa ya samar mata da Gurbin karatu A KASU inda take Karantar BNSC NURSING a lokacin yana Shekararsa ta Ƙarshe na masters ɗinsa a Jami’ar Bayero Ta Kano inda shima yake karantar MS(master of surgery) dinshi bayan ya kammala MD (Doctor of medicine) ,Yanzu yana aiki a asibitin da Mahaifinsa ya bar masa inda yake aiki a matsayin MSSDoctor , a halin yanzu Aeesh tana Shekarta Na ƙarshe a jami’ar strike ɗinda ASSU Suka je ne yasa take Zuwa Asibitin yayan nata dan Ƙarin Experience ,Dama chan tana zuwa Voluntary in ta samu Time.

Tuttura Abincin taitayi har saida taci rabi sannan ta ture plate din tana goge bakinta da tissue.

Kamo hannunta guda yayi ganin tana niyyar tashi hakan yasa ta fasa tashin Saidai ko dagowa batayiba.

“Ikhty Fushi kikeyi da Yayanki?”

Shiru tayi kanta Kasa

“Am so sorry , banyi hakan don na ɓata miki Rai ba ,nima banida choice I have to go Alone….”

Har yanzu shiru tayi batace komai ba kuma bata dagoba.

“Ikhty idan da inada yadda zanyi nima Tun farko da Ban shirya tafiyar nan ba Amma a halin yanzu tafiyar was my last hope”

Ɗagowa tayi idanunta na tara ruwa ,Murya na rawa tace

“Kasan I couldn’t stay back without you for 5hrs, And u want to Go for 5days”

Matsowa Yayi gab da ita ya matse Hannunta  cikin nasa, cikin Wani irin Muryar da shi kansa baisan Yanada itaba yace

“Na daɗe banje Gida ba Tun sanda Kuka Samu saɓani da Su Hajjo ,And….Akwai Abubuwa masu muhimmanci da zanyi a Chan I missed home, didn’t u care about my feelings  More than 7Mounths Without Setting my Eyes On my fam Just because of u?”

Yafada Cikin wani irin ɓoyayyen lamarin dayake dannewa yaqi dannuwa.

Kallonshi take idanunta na cigaba da kawo ruwa don tunda take beta6a yimata maganaba cikin wannan yanayin ba ,Tausayinsu ne ya kamata ~Masana Sunce Idan Mutun na Shaye Shaye yakan Sha matukar wahala kafin ya rabu dashi, ita nata ƙaddarar ba ta Shaye Shaye bace, Shaƙuwar Da tayi da yayan nata ne yasa take Ganin kaman Rabuwa dashi na ɗan wani lkc zai Iya Zama Barazana Ga rayuwarta~

Hannayen ta dake cikin nasa ya Matse a hankali wanda hakan yaba hawayen da suka taru a idanunta daman Digiwa Saman Hannunsa.

“You care about them but they hate u, Basua ƙaunarka ko kaɗan”

“I know but what about my siblings”

Shuru tayi ta sadda kai Hawaye na cigaba da ɓulɓulowa daga Kwarmin idanunta .

“Ammma In ka tafi we need to be in touch”

Tafada cikin cracking voice

Ajiyar zuciya ya sauke yana kallon yadda take ƙoƙarin taro hawayen dasuka cika idanunta ta Dakatar dasu daga zubowa.

Yasan yadda takeji, she’s in pain, kallo daya zaka mata kagane ,Kukan da take Daga Zuciyarta take tahowa direct.

Cikin kwantar da murya wanda yafi kama da rad’a yace

“Sure Girly”

Hawayen datake dannewa ne suka kufcemata suka gangaro kan kumatunta.

Ji take kamar idan Ya tafi bazai dawo ba, ji take kamar tafiyar da zaiyi itace silar da zata Rabata dashi har Abadah.

Dagowa tayi ahankali ta kalleshi da rinnanun idanunta dake sheƙin hawaye, zuciyarta na zafi.

Shima kallonta yake yanajin kowanne digar hawayenta har cikin zuciyarshi, idanunshi suka fara chanza kala yanajin kamar shima yafara zubda nashi hawayen, Ko kuma ya fasa tafiyar Gabaki ɗaya.

“Ƙarfe nawa zaka tafi Goben”

“May be 9:00 na safiya”

Lumshe idanu tayi taba hawayen dasuka cika idanunta damar gangarowa sannan tabude ta kalli Agogon dake manne a parlon 9:25.

“Kenan Saura  12hrs ka tafi Please Stay with me All these while”

Murza hannunta yayi ahankali yana jin shesheqanta harcikin ranshi,  yasa hannu yashafo kumatunta da ya gama Jiƙewa da leman hawaye, Ya share mata Sannan yaja hancinta cikin  wani Irin murmushin sa Na musamman yace

“Sure Baby”

“Idan Zan dawo zan taho mki da jirgi da Mota da komai dakomai ,Zakiyi ta wasa dasu har sai kin gaji, ….kuma daga wannan lokacin bazan ƙara barinki ba, Zan dawo na zauna ko yaushe muna tare dake har Randa kika Zama cikakkiyar matar aure gun  Sadauki a ranar kinci ado Sai Ƙamshi na Musamman kike Zubawa Hannayenki Sunsha Zanen lalle Fuskar nan taki na Fidda Annuri da haske na musamman A ranar Darajarki ta Ninku Akan nada,Ranar da Zan damƙawa sadauki Amanarki in zaunar dake in Miki nasihar zaman Haƙuri a Gidan Aure daga Ƙarshe in ɗora da Addu’ar Allah ya dawwamar daku Cikin Inuwa ɗaya Har Abada ……”

Kanta ta ɗora bisa kafaɗarsa kawai tayi tana Murmushi.

Sosai take jin daɗin kalamansa Hakan yasa taita kaɗa kai tana murmushi .

Ahaka ya cigaba da Kwantar mata da hankali da daɗaɗan kalamansa had barci  ya dauketa, Bata farkaba sai four shima Umma ce ta tadata tayi Sallah,lokacin ya tafi masallaci.

Ƙarfe Shida saura ya dawo ,Watsa ruwa yayi a bandakin daki Yaa Saleem sannan yafito.

Lkcn har Umma ta shirya masu Abin karyawa, Sama sama Suka tsakura don Gabaki ɗaya su yau a Sanyaye suka farka.

Saida Ya kimtsa Sannan ya bar Gidan tareda Rakiyar Ƙanwar tasa da ƙaninta Habeeb Bayan Umma ta bada saƙo a ba Goggo.

Ranar Da ƙyar ta iya Shiryawa taje Asibiti , a Ranar kuwa Ba iya na kusa da ita ba Hatta majinyatan da take kula dasu Suma sun fahimci Akwai damuwa a tattare da ita .

Ƙarfe Goma sha biyu na Rana Ashman ya sauka Garin Kano, kai tsaye bai nufi nasu gidan ba ,Zarce wa Gidan Abokinsa Bilaal yayi kusan nace nan ya wuni suna tattaunawa Don rabon da su haɗu kusan 7 months kenan, ko kaɗan Bari kewan Aeesh Ya hana shi walwala ba ,Hasali ma tattara Duk wani abin da ya shafe ta yayi ya ajiye a gefe ,Tsakanin Tahowansa izuwa yanzu sunyi Waya ya kai sau Goma.

Sai Dare ya baro Gidan Ya nufi Gidan Gonar Abbban sa nan ya kwana, Sosai yake tsoron tunkarar Gidan Mahaifin nasa Bai san me zai taras a chan ba ,idan ya tuna yanda Suka Rabu lokacin Zuwansa na ƙarshe sai yaji kamar ya kama hanya ya koma inda ya fito(kd) ,Amma duk da haka babu yanda ya iya dole ya daure ya shiga Gidan Gobe ,ya jure Duk Abinda zai faru dashi.

*kaduna*

Washe Gari bata wani damun kanta wajen shirin Asibiti ba, don bazata jeba, wanka kawai tayi ta kimtsa kanta sannan tahau danne danne a wayanta.

Haryanzu fuskarta a cunkushe yake don haryanzu bata bar kewan yayan nata ba.

data ta kunna tahau WhatsApp

Kamar jira ake saiga message din Reey na “Kehh…..!”.

‘Mayyar chatting’ tafada cikin zuciyarta sannan itama ta tura mata

” hyy”

“Ke banza Gani Hanyar Gidan ku Ki shirya Mu tafi Asibiti, Akwai drama”

“Manafuka A hanyar Gidan namu Kike Chat?”

“Ke banza Faɗa ake yi Tsakanin Dr Dan da Sister Ushey”

Dirowa tayi daga kan Gadon da take zaune ta waro manyan Idanunta kamar tana Gabanta hannunta har Ɓari yake wajen typa

“Da gaske?”

Aikam kaman Jira Take tayi mata Reply

“Wlh serious, Nima ban Riga naje ba Hajara ce ta Kirani ta koramin”

“Okay Gani nan ….Gani nan ”

“Be fast Please”

“Babe Uniform ne jikinki ko Scrub?”

Sticker din dariya Reey ta turamata sannan ta rubuta

“Pink Scrub na Saka, Hala Ko wanka bakiyi ba”

Sticker din kallon kin ma rainani ta turamata sannan ta tura

“Ke nake jira kizo ki wanke Ni”

Sauka tayi ta kashe datarta sannan ta miƙe da azama ta shige banɗaki Wanka tayi sharp Sharp ta fito, ta sanya  Pink Scrub ɗin ta wanda yasha Guga, Ƙaramar farar Hijab ɗinta ta Saka ta ɗauko Baƙar After Dress ɗinta ta ɗora akan Scrub ɗin ,baƙar Canvas ɗinta Mara nauyi .

Masha Allah tayi kyau sosai musanmman data Saka farar Medicated shade a idanu mai taken High Index Lenses.

saukowa tayi ahankali, a Store ta ga Umma tana Jera Kayan Abincin da Zubairu Ya Kawo msu, kallo ɗaya tayi mata ya dauke kai.

Murmushi tayi taqaraso wajenta tana cire glass din idonta.

“Umma na , Na samu Emergency Call a Asibiti na tafi”

Harararta Umma Tayi

“Tunda ga Likita ba”

“Oho dai ni Na tafi ”

Tana Fadar haka Ta maida farar tabarau ɗinta,Sannan tayi waje da sauri.

Binta da kallo Umma tayi  ta Girgiza kai .  _Aisha Kenan Sarkin Shirme_

Fitowar ta yayi daidai da isowar Reey a Napep.

Leƙowa tayi Tana harararta bayan Napep din ya Tsaya , Murmushi Aeesh tayi Ta ƙarasa Ta hau, me adaidaita Ya jasu suka wuce.

Suna hanya saiga kiran Ashman ya shigo ta whatsapp video call dannawa tayi tare da d’auka Tana Sakin Wani ƙayataccen Murmushi.

Daga shi sai jallabiya yana Zaune a Cikin Motar sa ,Ya Gama shiryawan sa na zuwa Gida amma ya kasa tada Motar yanzu haka ma kiranta yayi Don tayi Motivating ɗinshi , ko zai Samu Ƙwarin Gwiwa daga Gare ta.

Aash yana ganin fuskanta ya saki murmushi tare da fad’in

“Inye Sister Nurse kin Sauya Ra’ayine?”

Itama murmushin ta saki tare da fad’in

“Tausayin Patients Ɗinka naji,Nasan they can’t do without Me”

Murmushi kawai yayi, sannan yace

“Kicewa Juwairiyyah in ba hello Akwai Hi ”

Dariya ta saki tare da Kara wayar saitin Fuskar Reey da ta kauda Kai tana haɗe rai

“Ka ganta She doesn’t miss u”

“Ayyah har Yanzu Bata huce ba?, Give the phone to her”

“No Ahky,We doesn’t Deserve people Who care less about us, Forget her Abege We can still Do without her”

Yanda tayi maganan cikin shagwaba yasa shi yin murmushi Sosai, Daidai lokacin Mai adaidaita ta iso ƙofar Asibiti.

Saukowa Reey tayi ta Sallame shi,Itama Cikin sauri ta fara yunkurin Fita,Cikin rashin Sa’a Ta taka Kimonon Jikinta,Wayarta ta Suɓuce zata Faɗi, ƙara ta saki da ƙarfi wanda Yasa Ashman dake kallonta Ya toshe Kunnensa da ƙarfi.

Kamar daga Sama ta ga an taro wayar kafin ta kaiga faɗuwa Ƙasa.

Wani irin Relaxation breath ta Saki Tareda faɗin Alhamdulillah.

Hannu takai Zata karɓi wayar tareda faɗin

“Thank y….” cak maganarta ta tsaya da wani Ƙamshin Turarensa ya bugi hancinta.

Saurin dagowa ta yi cikin rashin gasgata da mammaki bayyananne.

yankewa gabanta yayi yafadi ganin shi dinne tsaye a Gabanta Riƙeda Wayarta a hannunshi ya zubamata piercing eyes ɗin shi.

Mutuwar tsaye tayi tana kallonshi idanunta adan ware alamun mammaki qarara a fuskarta.

Meyasa Take yawan Ganinshi a Inda bata zata ba?, meyasa Zuciyarta take yawan bugawa a duk Lokacin da Ta Gansa?, meyasa Take kasa Janye idanunta daga Kallonsa a duk lokacin da ta Gansa?, Meyasa take jinta a cikin wani irin Yanayi mara misaltuwa a duk Lokacin da ta Ganshi?,Gashi Ita ko ko sunansa Bata Sani ba, A duk lokacin da suka haɗu Kalaman Soyayya yake zuba mata yay tafiyarsa, ita kuma a duk lkcn da taji yana Wa’ennan zantuttukan Kasa yunƙurin komai yake,Shiyasa bata taɓa furta masa wata kalma ba,All she knows is SHE LOVES HIM.

Binshi tayi da kallo daga sama har qasa Zuciyar ta na Tsere.

Sanye yake cikin qananun kaya, tsadadden jeans trouser da top NAVY blue mai Gajeren hannu, kansa babu hula Sai sheƙi yakeyi,Yar sumar kanshi a kwance luff sai qyalli take, kullum qara mata kyau kwarjini da haiba yakeyi.

kallonshi take tana jin wani irin shauqin da bata ta6a jiba na dibarta yayinda qaunarsa ke qara hauhawa acikin birnin zuciyarta.

Jitake kamar ya ta Goyashi tayta zagaye Duniya dashi tana Shaida msu Irin Tsananin ƙaunar da takeyi masa.

Shi yafara janye idanunsa akanta yana Smiling sanadin Ganin Dr Ashman da Yayi a fuskar Wayarta .

“Sorry..”

Ya furta Cikin Sanyin Murya tare da Mika mata wayar.

Karɓa tayi Cikin mutuwan Jiki, Cikin ƙanƙanin lokaci Ganinsa yasa ta mance da wayar da suke yi Yaya Ashman, In har Zata dinga Ganinshi a ko wane lokaci tho babu Shakka zata iya Manta da kowa ya zamana Sai an Tuna Mata Kowa Zata gane kowa…

Shi kansa Ashman Zuba ido Yayi yana jiran Abinda zai faru Next,Don Shi kansa Ya Shiga Tunani Ganin irin Yanayin da Ƙanwar tasa ta shiga daga bayyanar Bawan Allahn Nan……….

 

 

*NIMA JIRA NAKE NAJI ME ZAI FARU?*

*WANE NE SHI?*

*MEKE TSAKANIN AASH DA AEESH?*
_*SHAKUWA CE?*_
KO
*SOYAYYA CE?*

DROP UR COMMENTS 😉

THANKS 💙💙💙

MAY 2ND💙💙

EID MUBARAK 💙

NAYI GABAS🚶🏾‍♀️🚶🏽‍♀️
[7/18, 9:22 PM] F A T E E🤎:
🔪*WUƘA A ZUCIYA*🔪
💔( *_Bleeding hearts_* )💔

*004*
_The Engagement_

*KANO*
Yana shiga Part ɗinsa ya Cire kayan Jikinsa ya dora Towel Ya Shige Bathroom.

Tara ruwan dumi yayi a jacuzzi sannan ya hada mayyukan wanka Masu Ƙamshi,Yana Yamutsa Fuska Sosai yakejin Kyamar Jikinsa A Rayuwar sa ya tsani wani abu Ya taɓa masa Fatar Jikinsa koda Turare wani ya Fesa masa bazai ji Ƙamshin ba Illa ma Kyamar Da Zai haddasa masa .

ruwan  yashiga yayi shuru Zuciyarsa na zafi, Lallai yaran Nan Sun manta koshi waye.

Lumshe idanunsa yayi Dumin Ruwan na Ratsashi ,a hankali Brain ɗinsa yay Masa Recapping Abinda ya faru Recently.

WHAT! ….

Ya furta awkwardly yana ware lumsassun Idanunsa, Lallaima raini ya shiga tsakaninsa da wann yaran, a yau sai yaga Wanda ya tsaya Msu Sai ya ladabtar dasu ta yanda Ko a hanya Suka Gansa Bazasuyi gangancin Hada hanya dashi ba.

Ya Dade cikin ruwan saboda dadinsu don harya fara gyangyadi sannan ya Cuccuɗa Fatarsa ,Gashinsa kuwa yasha dirza Kamar zai Fiddasu ,Ya daɗe yana wanke ko’ina na Jikinsa Kaikace Wani Mugun Abu aka watsa masa, Saida ya gaji don kanshi sannan yafito ya jawo wani Milk din towel dake gefe hange.

Yadaura sannan ya fasa sabon brush ya matsa toothpaste yayi brush daganan yayi alwala yafito.

Wata doguwar jallabiya yasaka ya haye sallaya Wanda dama already a shimfide yake a kusurwar dakin yayi sallar Azahar da ta Riga ta wuceshi Tun A hanya.

Ya Dade zaune tana kwararo addu’o’i sannan ya shafa yamike horn Ɗin Motocin da Yaji ne yasashi leƙawa ta Window.

Taɓe baki yayi Ya Sako takalmansa ya shiga Kitchen ya haɗa coffee.

Yau ran Ashman yafi Garwashi Zafi jira yake a taɓa ta ya ƙona Koma waye  .

Kwance yake Amma hankalinsa na wajen daddynsa Wanda ya hango ɗazu sun dawo.

Tun dazu yake ganin kiranshi Amma ya kasa Ɗagawa Gudun kar Ɓacin ran nasa Ya shafi Abbansa, Su Baffa kuwa da tuni sukaji Labarin Ya Shigo Gidan Allah Allah yake ya sauko Ya Fesa masa Labarin da suka taho masa Dashi wanda yana Kyautata zaton Sai ya ɓata Ran Ashman Fiye da Tunani shi ,Shi kuma a duniya babu abinda yake kauna Irin ganin Ɓacin ran Ashman.

Bari Mu leƙa Kaduna ,Mu taɓo masoya❤️

*Kaduna*

Fuskar ta ɗauke da Wani irin Ƙayataccen Murmushi ta Isa Gidan Su Juwairiyyah.

Tun a Bakin Kofa ta fara Ƙwalla Uban Sallama Reey na zaune a Dinnin tana Cin Abinci , tana Jinta Tayi Saurin ‘daukar Plate ɗinta Tayi ɗaki.

Burki taja a parlon tana Binsu da Kallo Suma  ƙannen Reey da kallo Suka Bita Ganin yanda Ta faɗo Musu a Guje, Kwatancen Kurame tayi Musu tana Tambayansu Reey?

Suma da Kwatancen Kurame suka Bata Amsa suna Nuna Mata ɗakin Reey.

Aikam Da gudu ta Ƙarasa Ɗakin, Ta Banko ƙofar babu ko sallama.

Reey na Ganinta ta haɗe Rai ta Sake Tankwashe Ƙafarta ta Cigaba Da Abinda takeyi.

“Ke wai Aljanna ce?, yaushe kika dawo?, har kin cire Uniform Kin fara Cin Abinci?”

Aeesh ta faɗa tana Cire Kimonon da takalmanta haɗe da Ajiye jakar Hannunta.

Ko ɗagowa batayi ba,Bare tasawa Ranta Zata tanka ta.

Aikou Batai Wata wata ba Ta haye Gadon ta Jawo Plate ɗin Shinkafar da takeci Wacce tasha Barbaɗen Cowslow.

Kafin Reey tayi wani yunƙuri har ta Arce a Guje ,A Dinnin ɗin parlor taja Burki Ta zauna Tasa Cokali ta fara ci ,Tana Ganin Reey ta kusa Iskota ta Cire Cokalin tasa Hannu bibbiyu ta Wawuri Abincin takai bakinta.

Fuska Reey Ta yatsine tace

“Yama Yama Dirty Nurse…..”

Shaƙewa Sosai Aeesh tayi ,Abincin ya tsaya mata a Maƙoshi yaƙi wucewa , Kofin Ruwa Reey ta Miƙa mata ta Zauna Kusa da ita Tana Mata sannu.

Saida ya lafa mata Sannan tace

“Har Kun Gama Hirar Kenan?”

Murmushi Aeesh tayi Ganin Bestyn nata Ta sauko daga Fushin  nata ,Gyara zama tayi ta ture Plate Ɗin Gabanta.

“Hmmm….In Gaya Miki Saura Kaɗan in Furta Masa yasan Komai,Amma ikon Allah Sai na Tsinci Kaina d Fadar akaso haka!,Amma fa Na bashi Assignment ne, Shine zai zama nawa inshaAllahu”

Tsaki Reey taja

“Allah ya Raka Taki Gona”

“Ameen ”

Aeesh ta faɗa tana jawo Plate ɗin Shinkafarta, tasa Spoon ta Cigaba da Ci.

“Besty Pls Meyasa Kika Tsane Sadauki Na?”

”Ba Tsanar sa Nayi ba”

“I see it in You, Idanunki Sun kasa Ɓoye zazzafar Ƙiyayyar da kike masa Besty why?”

komawa tayi tayi balancing akan kujerar tareda lumshe idanu, zuciyarta kamar ana hura wuta, ya zatayi Aeesh Ta Fahimce Irin Haɗarin dake Cikin Soyayya da Ɗan Titi?, ya za’ayi ta fahimtar da ita Illar Soyayya da Gogaggen ɗan Majalisa Mai Yawo da Gangband?.

“Please Besty Tell me…?”

Muryar Aeesh Ta katseta.

“Saboda Shi kyakkyawa ne ,I hate Handsome men, Mayaudara Ne”

Murmushi Aeesh tayi harda Tafa hannu.

“Hhhhhh  Bravo….kinyi Tunani mai Kyau, Shirmammiyar Besty tah, shikenan saboda Shi kyakkyawa ne Sai akace Miki an Rubuta cikin Ƙaddarar sa Dole sai ya Yaudare mace?”

“What Ever …. it’s your life, I hated him Koda Ya Aureki bazan Ta6a Kaunarsa ba Koda na Second ɗaya ne….Aeesh i hate Your Sadauki”

Jikin Aeesh Ne Yayi Sanyi ƙalau, Ji tayi kamar Reey ta Chaccaka Mata *Wuƙa ne a Zuciya*

Ahankali ta Ture Plate ɗin gabanta idanunta na kawo ruwa, Ta Miƙe Haka taita takawa ahankali har takai sama  dakyar tashige wani dakin da babu kowa ciki (dakin kannen Reey ne) ta fada kan gado tana lumshe idanu Wanda hakan yaba hawayen idanunta damar gangarowa.

Bin Sahunta Reey tayi Ta Shiga Rarrashi,ita kanta bata taɓa Zaton Soyayyar da Aeesh kema Sadauki yakai ga haka ba,Da ƙyar ta Samu tayi shiru ta daina kukan Amma , Sosai Walwalarta ta ragu.

Dakin Reey ta koma ta sauya kayan Jikinta zuwa Wata baƙar jallabiya , Lokacin Reey na zaune kan Gado tana daddana wayar Aeesh.

Text message ne Ya shigo Ai batayi wata Wata ba Ta buɗe,Ganin Sabuwar Number ce yasata fara karantawa a fili.

*Tsakanin Aiki me Kyau da wanin sa Akwai wani Gurbi….”*

“Thofa Aeesh Dama kinyi Applying Aiki ne?”

“A’a Amma cigaba”

Farowa tayi daga Farko

_*Tsakanin Aiki Mai Kyau da wanin sa ,Akwai wani Gurbi, kuma zan Nemeki a wajen*_

*_Kinsan Ko wacece ke?_*
*_ke ɗin Wata Rubutacciyar Al’amari ce Mai Girma Daga Allah_*

_*Ke wata Madubi ce wacce Kika haska Wata fuska mai daraja*_
*_Wannan Duniyar Ba a wajen ki take ba, Ki kalli chan Cikin kanki_* *KECE DUNIYAR*

_*Duk Abinda kike burin Zama Kin Riga da kin samu*_
_*Kece Makullin Tawa rayuwar, Don Allah Ki bani Dama Ko sau ɗaya ne in Nuna Miki Tsantsar Soyayyar Da nake Miiki*_

Leave a Comment