Books Reviews & FAQs

‘Yancin Mata Hausa Novel Complete

🔘° *Y’ANCIN MATA* °🔘°
_(Barrister Hazifa)_
*1441H/2019M.*

 

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍️*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

“`🎐G•W•A🎐“`
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*

 

*NA MARUBUCIYA:-*
*NEAT LADY✍🏼•*

 

*SADAUKARWA GA:-*
*GASKIYA WRITER’S ASSOCIATION.*

 

~Wattpad @GaskiyaWritersAsso.~

 

“`BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM“`

_Alhamdulilah yau gashi Allah ya dad’a had’a mu a cikin sabon littafi na Wanda nake fatan zaku bani hadin kai wajan ganin mun kai karshen sa cikin kwanciyar hankali, Wannan littafi bana siyarwa bane kuma banyi shi Dan cin zarafin wata ko wani ba,_

 

_ban yarda a canja min labari ba_.

 

*SHAFI NA 1📑*

*__________📖* Tafiya take tana cikin sauri tana duba agogon dake d’aure a tsintsiyar hannun ta , yarinya ce y’ar kimanin shekara goma sha biyar tana sanye da dogon hijjabi da alama daga islamiyya ta dawo , titin tas babu kowa gashi magariba ta gabato hakan yasa take ta sauri dan tasan halin unguwar tasu yanzu sai a sace mutum .

Wata mota ce bak’a k’ira Benz tazo ta gifta yarinyar a guje , cike da tsoro yarinyar ta cigaba da sauri kamar zata tashi sama , cak motar ta tsaya tare dayin reverse har ta dawo inda yarinyar take

 

Wasu maza ne suka fito daga motar basu tsaya wani tunani ba suka fesawa yarinyar wata hoda a fuska , nan dake tayi baya zata fad’i suka taro ta suka saka ta a mota suka cigaba da gudu.

 

Sabon sirinji suka d’auko suku dibi jinin yarinyar sannan suka rife sirinjin , basu tsaya a ko ina ba sai a bakin wani asibiti d’aya daga cikin mazan ya d’auki wannan jinin ya shiga cikin asibitin .

 

Direct lab ya nufa yana zuwa ya mik’a musu kamar yadda suka saba , gwajin cutar k’anjamau akayi akaga babu , sannan akayi na ciwon hanta shima akaga babu , result din ya karb’a ya juyo a guje ya koma cikin motar suka cigaba da tafiya.

Basu tsaya a ko ina ba sai a bakin wani k’aton gida mai bala’in kyau ,horn suka danna mai gadi ya bud’e suka shiga cikin gidan , parking suka yi cikin sauri suka d’auko yarinyar suka shiga da ita parlourn gidan.

 

Bedroom suka shiga da yarinyar suka kwantar da ita suka fito suka tsaya suna jiran ogan nasu yazo .

 

Basu wani dade ba ya fito daga d’aya d’akin ya tafiya dak’yar kamar Wanda baya San taka k’asa , zama yayi a kan d’aya daga cikin yace “Aikin Ku yayi kyau zaku iya tafiya”

Cikin rawar jiki suka amsa da “An gama ranka ya dad’e a ji dad’i lafiya” suna gama fad’ar hakan suka juya suka fita daga parlourn.

 

Mik’ewa yayi ya shiga d’akin da yarinyar take , murmushi yayi yace “Babu laifi tayi” k’arasawa kan bed d’in yayi tare da kwanciya kusa da yarinyar, a hankali ya zame mata hijjabin daga jikin ta ya Zuba mata ido yana kallon ta , tab’e baki yayi kamar yaga kashi haka ya zuge zip d’in rigar ta ya fara sha’anin sa .

Bai bar yarinyar nan ba sai ya tabbatar yayi mata kaca-kaca sannan ya kyale ta , wani bakin Abu ya d’auko ya kama hannun yarinyar ya rubuta _BAD MAN_ da manyan bak’i tare da yin singing a gaba , kayan ta ya d’auko ya saka mata sannan ya fito daga d’akin.

 

Kallon agogo yayi a yaga har sha d’ayan dare tayi tsaki yayi ya dau waya ya kira yaran sa yace ” Dalla malamai kuzo Ku d’auke min wannan bazawarar a gida na”

Jin ya ambaci bazawara yasa suka gane ya yiwa yarinyar fyade ,cikin rawar jiki suka dawo gidan suka d’auke ta suka shiga mota suka jefar da ita a inda suka d’auke ta.

 

Bad man kuwa shiryawa yayi cikin k’ananan kaya ya shiga mota ya nufi club.

 

Washe gari

 

*****

 

“Umme na shirya zan tafi wajan aiki” wata kyakykyawar budurwa ta fad’a tana rataya jaka

Wacce aka kira da Ummen tace “To Hazifa Allah ya kikaye hanya Allah ya bada sa’a”

Hafiza tace “Ameen Ummee na , ina Hanifa?”

Ummee tace “kema kinsan tunda suka samu hutun makaranta bata da aiki sai bacci”

Hafiza tayi dariya tace “To in ta tashi ki gashe ta na tafi ” ta fad’a tana fita daga gidan.

 

Sauri take ta Dan ta isa titi sabida ta kusa makara a wajan aiki, mutane ta gani a kan titi an cika a waje d’aya da alama akwai abinda ya faru a wajan , da sauri ta k’arasa wajan tana fad’in “lafiya jama’a meya faru?”

Wani mutumi yace “wani Mara imanin aka samu yayiwa k’aramar yarinya fyad’e kalli kiga halin da take ciki” ya fad’a yana nuna inda yarinyar take

 

Cikin tashin hankali Hafiza ta k’arasa wajan ta durk’usa a gaban yarinyar , ganin halin da take ciki yasa Hafiza ta fara hawaye tana fad’in ” wannan ai Iman ce y’ar mak’otan mu , Dan Allah Ku samo mota mu kaita asibiti ”

 

Adaidaita sahu aka tsayar aka saka yarinyar da take sume bata numfashi ,

Suna zuwa aka shiga da yarinyar d’akin taimakon gaggawa likitoci suka rufu akan ta Dan ganin Dan ceto rayuwar ta ,

 

Zama Hafiza tayi tana tunanin halin da yarinyar take ciki , wajan minti talatin wani likita ya fito ya kalli Hafiza yace “muje office”

 

Bin bayan sa tayi suka shiga ta zauna yace “Fyad’e aka yiwa yarinyar nan na rashin imani dan Yanzu haka sai da aka yi mata dinki kuma itama akwai wannan tambarin a hannun ta”

Dukan table Hafiza tayi tace “Bad man again”

Dr Amin yace “Eh tabbas abinda yake jikin hannun ta kenan”

Cikin b’acin rai Hafiza tace “Wai waye wannan Bad man din ?”

Dr Amin yace “Allah ne ya sani Dan har yanzu ko full name dinsa ba’a sani ba balle kuma a san fuskar sa , kuma duk wacce yayiwa fyad’e sai yayi mata wannan tambarin a hannu, lauyoyi , y’an sanda har yanzu basu gano waye wannan mutumin ba”

 

Hafiza ta mik’e tace “Ni BARRIER HAFIZA nayi alk’awarin ganin bayan wannan mutumin , nayi alk’awari sai na gurfanar dashi a gaban kotu”.

 

 

 

 

*TO YA KUKA JI A CIGABA KO A TSAYA?*😉

 

 

 

 

*Comment & Share*

 

 

*© NEAT LADY*
°🔘° *Y’ANCIN MATA* °🔘°
_(BARRISTER HAFIZA)_
*1441H/2019M.*

 

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍️*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

“`🎐G•W•A🎐“`
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*

 

*NA MARUBUCIYA:-*
*NEAT LADY✍🏼•*

 

*SADAUKARWA GA:-*
*GAKIYA WRITER’S ASSOCAITION*

 

~Wattpad @GaskiyaWritersAsso.~

 

*SHAFI NA 2📑*

*__________📖* mik’ewa Dr Amin yayi yace “Ina bayan ki Barrister nima zanyi k’ok’ari wajan ganin an kamo wannan Bad man din”

Juyowa Hafiza tayi tace “Nagode sosai , dani da kai zamu had’a k’arfi da k’arfe wajan ganin bayan wannan mutumin, yanzu mu koma wajan Iman d’in”

Fita suka yi daga office d’in suka koma d’akin da aka kwantar da Iman , basu dad’e da shiga ba ta farka tana bud’e ido a hankali , nan take abinda ya faru ya shiga yi mata yawo a kwakwalwar ta ,

Juyowa tayi ta kalli Hafiza da ta Zuba mata ido tana kallon ta, cikin kuka Iman tace “Aunty Hafiza meye ya faru dani bayan wannan mutanen sun zuba min Abu a fuska?”

 

Cikin Tausayi Hafiza tace “ki kwantar da hankalin ki Iman ki daina kuka kinji”

 

Bud’e k’ofa akayi aka shigo ko ba’a fad’a ba ansan dangin Iman ne suka k’araso , Maman ta ta k’arasa wajan tana goge hawaye ta zauna kusa da Iman d’in tace “kiyi Hak’uri Allah yana bayan mai gaskiya, Allah ya tona asirin nan mutumin” ta fad’a cikin dashewar murya

 

Mik’ewa Hafiza tayi ta isa kusa da Iman ta dafa ta tace ” Iman a cikin Wanda suka Zuba miki Abu a fuska babu Wanda zaka iya ganewa?”

Iman tace “bazan iya gane su ba tunda ta baya na suka biyo daga nan kuma ban kuma sanin inda kaina yake ba sai yanzu”

Numfashi Hafiza ta sauke tace “Mama zan tafi wajan aiki amma insha Allah zan iya bakin k’ok’ari na wajan ganin na binciko wannan mutumin”

 

Mama tace “Allah ya baki sa’a Hafiza , Nagode sosai Allah yasa kiyi nasara akan sa”

Murmushi Hafiza tayi tace “Ameen Mama daman addu’ar Ku make nema , ni na tafi Allah ya k’ara lafiya” ta fad’a tana fita daga d’akin.

Sallama tayiwa Dr Amin ta fita daga asibitin.

Da kallo Dr ya bita yana wani irin murmushi dashi kad’ai yasan ma’anar sa .

 

Hafiza kuwa bata wuce ko ina ba sai cikin babbar kotun dake garin Kaduna , bayan an gama shari’ar y’an uwanta lauyoyi ta kira maza da mata ta had’a meeting bayan su zauna Hafiza ta kalle su tace ,

“Na had’a wannan meeting ne badan komai ba sai dan mu had’a kai mu kama wannan Bad man d’in da yake cutar y’ay’a mata a banza , yanzu maganar da nake muku y’ar mak’otan mu Iman tana can a asibiti a kwance , meye amfanin mu in banu binkico wannan azzamulin ba , sabida na taimakawa mata nayi karatun lauya kuma har yanzu ina kan baka ta , ya kuke ganin za’a b’ollowa abin?”

Mik’ewa barrister Hidaya tayi tace “Sam bada ni za’ayi wannan aikin ba haka kawai ina zaune lafiya , ai nasan kin San Barrister Hadiza itama irin halin kine da ita ta nace sai ta gano wannan mutumin in takaice miki labari karshe sawa yayi aka d’auko ta yayi mata fyad’e na rashin mutunci kuma d’auki hotunan ta tsirara ya watsa su a social media, tsabar bakin ciki sai da ta kusa mutuwa wallahi, Dan haka Hafizatu Allah ya baki sa’a nayi nan” ta fad’a tana fita daga wajan.

 

Jin haka yasa sauran matan suka tsorata suka dinga barin wajan sai da ya zama daga Hafiza sai maza guda biyu a zaune , Hafiza tace ” to ko kuma zaku gudun ne?”

D’aya daga ciki ya mik’e yace “wacce Hidaya ta baki labari tare suka had’a kai da Barrister Buhari shima bai kyale shi ba sai da yayiwa matar sa da k’anwar sa fyad’e kuma ya turo masa hotunnan yace masa in bar aiki a kansa ba wallahi sai ya yad’a su a media, nima bazan iya ba Allah ya baki sa’a”

D’ayan yace “A’a nima tsaya ni mu tafi bazan iya ba wallahi inason matata da y’an uwana ” ya fad’a suna fita tare daga wajan.

 

Dukan table tayi tace “wai waye wannan Bad man d’in? Su kuma matsorata kowa ya gudu sun barni ni kad’ai , to ni da Allah na dogara babu abinda ya isa yayi min indai Allah bai tsara hakan ba, ” mik’ewa tayi ta rataya jaka tace “ina nan akan baka ta na ganin bayan mutumin nan” ta fad’a tana fita daga wajan.

******

 

Sauke wayar yayi daga kunne yayi murmushi mai baiyanar da sirrin kyaun sa yace “Barrister Hafiza sabuwar customer ta kenan , ina yi miki barka da shigowa rayuwar Bad man , da kinsan waye ni da bakiyi gangancin k’ok’arin shiga rayuwa ta ba amma babu komai nasan ta yarda zan b’ullo miki sai kinyi Dana sananin sanin sunana a rayuwar ki”

Waya ya d’auka ya kira yaran sa suna d’auka yace “another baby” kawai ya kashewar wayar ya cigaba da murmushi.

 

*Tofa ya akayi yasan shirin Hafiza a kansa*🤔

 

*Comment & Share*

 

© *NEAT LADY.*
°🔘° *Y’ANCIN MATA* °🔘°
_(BARRISTER HAFIZA)_
*1441H/2019M.*

 

®☄
*GASKIYA WRITERS ASSOCIATION✍️*
_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

“`🎐G•W•A🎐“`
*_GASKIYA DOKIN ƘARFE•_*

 

*NA MARUBUCIYA:-*
*NEAT LADY✍🏼•*

 

*SADAUKARWA GA:-*
*GASKIYA WRITER’S ASSOCIATION*

 

*TUKWICI GA:-*
*MAMA NA BINTA WRITER OF _CIN AMANAR KAUNA_*😘😘

 

~Wattpad @GaskiyaWritersAsso.~

 

 

_Oh ni Haleematu 🙄fan’s fa kun fara rikiciwa harda masu biyo ni prvt wai Dan Allah Dr Amin shine Bad man, me kuke ci na baka na Zuba bafa a fara labarin ba , kudai Ku kasance dani a koda yaushe danjin yadda zata kasance._😉

Ina yinku masoyana🥰

 

*SHAFI NA 3📑*

*__________📖* Basu d’auki wani lokaci ba suka kawo masa yarinyar da ya bukata , kamar yadda suka saba sai da suka biya asibiti akayi gwaje-gwaje sannan suka kawo ta .

Bai d’auki wani lokaci mai yawa ba ya fito yana tab’e baki yana tsaki kamar Wanda akayiwa dole , zama yayi a kan kujera sannan ya d’auki waya ya kira su yace suzo su Fitar masa da yarinyar daga gida , da rawar jiki suka iso suka d’auko ta kamar jaririya suka fito

Har zasu fita ya dakatar dasu da fad’in “duk Wanda zakuyi Ku tabbatar wannan yarinyar asibitin cikin gari aka kaita, bance Ku kaita ba amma kusan inda zaku ajjiye ta ” ya fad’a yana danna waya kamar bashi yake magana ba

Ciki da bin umarni suka amsa da “an gama oga” suka juya suka fita.

 

*****

 

Hafiza kuwa koda ta fito daga wajan meeting d’in gida ta wuce , koda ta k’arasa gida a zaune ta tarar da Ummee da Hanifa a zaune suna cin Abinci , sallama tayi ta zauna ba tare da tace komai baba
Cike da mamaki suke kallon ta , Hanifa tace “Aunty Hafiza lafiya kuwa?”

Tsaki Hafiza tayi ta bawa su Ummee labarin duk abinda ya faru har had’a meeting d’in da tayi sai da ta basu labari , Salati Ummee tayi tace “kai amma wannan yaro baya kyautawa , to ai ni banga ta zama ba tashi zanyi naje asibitin na dubo Iman d’in Ku zauna a gidan bara naje na dawo” har zata mik’e sai kuma ta koma ta zauna tace “yauwa Hafiza d’azu Abbie dinku yace na fad’a miki kinyi karatu kin gama kin fara aiki to dole ki fito da miji ayi miki aure , yace ya Zuba miki ido ne yaga iya gudun ruwan ki to yaga baki da alamar yin aure yanzu to baki isa ba cikin wanda suke zuwa Neman auren ki ki Fitar da d’aya , na Isar da sak’o” tana gama fad’a mata haka ta Mike ta shiga d’aki ta tayiwa Abbie waya ta tambaye shi zuwa asibiti ya barta sannan ta fito ta tafi.

 

Tunda Ummee tayiwa Hafiza wannan maganar tayi shiru bata yi magana ba , Hanifa tace “wai tunanin ne kike yi ne?”

Hafiza tace “ba tunani nake ba kawai dai ina tunanin Wanda zan aura zai bar ni na cigaba da aikina kuwa?”

Hanifa tace “wannan ai ba matsala bace tun kafin ayi auren zakuyi da wajewa in ya aure ki zai barki ki cigaba da aikin ki , indai yasan mahimmancin alk’awari zai barki kiyi wallahi”

 

Hafiza tace “hakan kuwa za’a yi Nagode y’ar uwata”

 

*WACECE HAFIZA?*

 

Alhaji Kabir Fulani shine sunan mahaifin ta haifaffen garin Kaduna amma asalin su fulanin Gombe ne, shi kadai iyayen sa suka Haifa tun yana yaro mahaifin sa wato Isma’il Fulani da mahaifiyar sa wato Ladi tun yana yaro Allah yayi masu rasuwa ya taso a hannun kanin mahaifinsa wati Jamilu wanda ake kira da Kawu Jamilu , Ummee wato Batulu itama y’ar garin ce ita kad’ai ce matar Alhaji Kabir Fulani , Alhaji Kabir Mai arzuki ne dai-dai gwargwado ci da sha da sutura , kudin makaranta babu abinda ya gagare shi Dan har Makkah ya biya yaje shida Kawu da kuma Ummee ,

Y’ay’an su biyu duka mata babbar itace Hafiza , ta biyu kuma Hanifa su kad’ai Allah ya basu hakan yasa suke mutukar kaunar yaran , duk da son da suke musu basu bari tarbiyyar su ta lalace ba sunyi k’ok’ari wajan ganin su bawa yaran tarbiyya ,

Hafiza y’ar shekara ashirin a duniya kyakykyawa ce sosai sai dai ba fara bace sosai Dan Hanifa ta fita haske , tun Hafiza na yarinya in taji labari an yiwa yarinya fyad’e kuka take yi sosai wani lokacin ma ta saka cin Abinci sabida kuka , hakan yasa ta lashi takobin yin karatun lauya kodan ta tsayawa yara mata ta karb’ar musu *Y’ANCIN SU* idan irin hakan ta taso,

 

Mahaifan ta sun bata kwarin guiwa sosai wajan ganin ta cimma burin ta a rayuwa , a haka har ta kammala digree dinta tayi dautar kasa ta fara aiki ,duk wani case na fyad’e indai yazo hannun ta sai ta San yadda tayi taga karshen sa, B’angaren islamiyya kuma tayi sauka tun tuni harda haddar alkur’ani izu sittin akan ta itada Hanifa.

 

Wannan kenan

Suna zaune Hafiza tana cin Abinci yaro yayi sallama yace ana sallama da Hafiza a waje , kafin tayi magana Hanifa tayi saurin cewa “jeka kace tana zuwa ”

Hafiza ta kalle tace “meye haka?” Hanifa tace “eh ina sane nayi hakan nasan in ba haka nayi miki ba ba zuwa zakiyi ba”

Tsaki tayi ta Wanke hannu ta ta saka hijjabi ta fita .

 

A tsaye ta mutumin yake ya juya baya , sallama tayi masa tare da sunkuyar da kanta sabida yadda kirjin ta yake bugawa da k’arfi , cike da fara’a saurayin ya amsa yana murmushi yace “malama Hafiza an wuni lafiya?”

Hafiza tace “Lafiya lau ” Saurayin yace “To nidai sunana Hafiz haifaffan garin Kano amma ina zuwa nan nake da zama sabida anan nake aiki , wato Hafiza tunda na dora idona akanki naji duk duniya babu wacce nake so kamar ki , wallahi kuma da gaske nake ba karya nake ba kuma ni da shirin aure naza ba yaudara ba , shin zaki iya karb’a ta a matsayin masoyin ki?”

Tunda ya fara magana ta sunkuyar da kai tana sauraran abinda yake fad’a a hankali tace “hakika ina godiya sosai da har kazo ka furta ni Kalmar kana sona , duk Wanda yace yana sonka a duniya ya gama yi maka komai amma ka bani lokaci zanyi tunani”

Murmushi yayi yana k’ara jin sonta har cikin zuciyar yace “haka ne malama Hafiza zan baki lokaci kiyi tunani kiji in na kwanta miki a rai to Masha Allah haka ake in kuma akasin haka ne kaii bama a fatan hakan”

Yadda yayi ne ya bata dariya hakan yasa tayi murmushi

Yace “ko zan iya samu number wayar ki domin mu dinga gaisawa ?”

Hafiza tace “babu komai kowa na saka maka ” yace “kai amma Nagode”

Ya ciro wayar sa ta saka masa number sannan sukayi sallama ya tafi.

 

Da murmushi akan fuskar ta ta shiga gida , Hanifa na ganin yanayin fuskar ta kwashe da dariya tana fad’in “da alama angon yazo yau kenan , tb gaskiya Aunty Hafiza kin fad’a da yawa wannan Zuba murmushi haka”

Itadai Hafiza d’aki ta koma bata kula ba , har zata zauna wayar ta tayi k’ara tana dubawa taga Dr Amin cikin sauri ta d’auka yace “Hafiza kiyi kizo asibiti yanzu an kuma kawo case d’in Bad man”

Hafiza tace “ya salam wai wannan wane irin mutum ne haka , shikenan nan dai gani nan zuwa insha Allah” ta fad’a tana kashe wayar tana fatan Allah yasa wannan taga wata shaida da zata iya gane shi ko yaran sa ko gidan sa

 

Fitowa tayi ta fad’awa Hanifa sannan ta bar gidan cikin sauri.

 

*****

 

Zaune yake akan kujera yana danna laptop , wata yarinya ce ta sakko da sauri ta bud’e k’ofa zata fita ya Daka mata tsawa da fad’in “ke!! Dawo?”

Cike da shagwaba ta dawo ta zauna tana fad’in “haba Yaya Dan Allah wai kama ta sai ka dinga hana ni fita na fad’a maka babu abinda zai same ni”

Tsaki yayi yace “ke wai kunnen k’ashi ne dake? sau nawa zance miki ki daina fita kedai sai dai driver amma bakya ji ko?”

Tace “Haba Yaya Dan Allah nifa na rasa meyasa baka sin ina fita ni kad’ai bayan babu abinda zai same ni”

Cikin tsawa yace “Tashi ki bani waje!”

Cikin rawar jiki ta mik’e ta koma d’aki tana kuka.

 

Bad man kuwa ko a jikin sa Dan ko zata yi kukan jini baza ta fita ita kad’ai ba sabida yasan akwai mutane da yawa irin sa , haka kawai tsautsayi ya fad’a kan kanwar sa shiyasa yake killace ta sabida baya son duk abinda zai b’ata mata rayuwa.

Leave a Comment