Books Reviews & FAQs

Yafi Dare Duhu Hausa Novel Complete

⚫⚫⚫⚫⚫⚫An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau – kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau – manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau – Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku

This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that – we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that – pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that – our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT

*…YA FI DARE DUHU*
💋💋💋💋💋💋
( _Labari me cike da surkulle da wani irin yanayi,salonsa daban ne._ )

Wacce taji zata iya comments ta shiga. Sannan don Allah kada namiji ya shiga mata zalla.👇
https://chat.whatsapp.com/F6pkxTzby95C63uyOjV6Ys

*MALLAKAR👇*
*FATIMA SUNUSI RABI’U*
_Ummu Affan_

*GABATARWA*
_Godiya ta tabbata ga Allah ubangijina da ya bani ikon fara rubuta muku wannan labarin,wanda yar-darsa ce ta sa hakan. Tsira da aminci su k’ara tabbata ga fiyayyen halittu cikamakin annabawa,Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasalam._

*SHIMFI’DA*
_Wannan labarin k’irk’irar ran labari ne daga kwakwalwar Fatima,ban yi sa domin wani ko wata ba saboda haka duk wanda yaji yayi dai-dai da rayuwarsa to arashi ne ba da shi na ke ba da fatan za’a guji zargi._

*GARGA’DI*
_Ban aminta ba a juya min labarina ta ko wacce siga ba tare da izinina ba,da fatan za’a kiyaye._

*SADAUKARWA*
*Gaba d’aya labarin nan sadaukarwa ne ga iyayena abin alfaharina,alkhairin Allah ya kai muku har gadon barcinku ina alfahari da kasancewarku iyaye a gareni.❤️🥰💋*

*JINJINA*
_Gareki Antyna HAUWA S ZARIA(Maman Uswan)Ina alfahari da ke shugaba ta gari._

________________________________

*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_

_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_

*Page 1-2*

Babban katafaran d’akin taron cike ya ke da mutane,yayin da kowa ya ke cike da farin ciki,ko wanne tebur kujeru biyu ne miji da mata ko kuma saurayi da budurwa,an ta naji abinci kala da kala,sai abinda kake so zaka ci,ga kaji da bank’ararran rago.

Wannan babbar rana ce a gurin Abdulhamid da duk wani masoyi a garesa,Hajiya Mariya tana cikin farin ciki mara musaltuwa da ka kalleta zaka gane hakan.

A yau ne babban d’anta kuma d’a mafi soyuwa a zuciyarta ya shirya mata wannan liyafar saboda murnar cikarta shekara sittin a duniya.
( _Lallai ikon Allah ni kuwa nace”masu abu da abunsu Allah yasa mu dace Amin_ )

Gaskiya a yau tana cikin farin ciki mara misali domin taga ‘yan uwa da abokan arziki duk sun zo don tayata murna. Nan MC ya fara bayanin mak’asudun abinda ya tarasu gurin.

Daga can gefe guda kuwa,Abdulhamid na hango jin gine jikin bangon gurin waya ya ke,bayan kammaluwar wayar ya mayar da ita aljihunsa sannan ya juyo da niyyar komawa ciki. Idanuwansa ne suka sauka kan wata kyakkyawar halitta ji yayi gabansa ya fad’i,zuba mata idanuwa yayi ba wai don bai santa ba a’a sai don irin yarda idan har zai kalleta to bai gajiya da kallon nata.

Ba kowa bace face ASMA’U wacce ‘yar aiki ce a gidansu,yana matuk’ar k’aunar Asma’u sai-dai mahaifiyarsa bata maraba da hakan,tace”ba zai yuwu ya auri Asma’u ba saboda tarin banbancin da ke tsakaninsa da ita” wanda shi aganinsa wannan ba hujja ba ce.

Abdulhamid d’a ne ga Marigayi Alhaji Mani wanda a zamanin rayuwarsa ya rik’e muk’amai da dama,domin d’an siyasa ne duk da fannin kasuwancin ma ana damawa da su. Alhaji Mani mutum ne mai alkhairi da temako duk da baiyi sa’ar mata ba,matarsa d’aya ce Hajiya Mariya yaransu uku Abdulhamid ne babba sai Maryam sannan k’aramarsu Hajara,Hajiya Mariya mace mai fad’a da mai girman kai da d’agawa bata ragawa kowa hatta ma’aikatan gidanta kuwa hakuri suke da ita.

Bayan rasuwar Alhaji Mani komai na ragamar gidan ya dawo hannunta sai abinta tace akeyi,shi kuma Abdulhamid duk wani kasuwanci na mahaifinsa shine yaci gaba da gudanar dashi. Abdulhamid mutum ne mai saurin fahimta da tausayi kusan duka halin mahaifinsa shi ya gado harma ya so yafi mahaifin nasa mutumci hakuri da dattako.

Asma’u kuwa ‘yace ga Malam Haruna talakawa ne su sosai domin wata rana ma abinda zasu ci gagararsu ya ke,amma hakan bai sa sunje sunyi maula ba ko wani abu da bai dace ba,hakan ne ma yasa Asma’u yanke shawarar fara aiki domin nema musu ko da na abinci ne ita da mahaifinta domin mahaifiyarta ta rasu daga ita sai Babanta suke zama tare.
Tun lokacin da ta fara aiki a gidansu Abdulhamid sai suka sami sauk’i domin duk runtsi suna samin abinda zasu ci don daga gidan ta ke taho musu dashi kuma ga albashinta duk wata.

Abdulhamid tunda ya ganta yaji ta kwanta masa a rai,har ya nuna mata yana sonta,da farko bata amince ba domin tana ganin kamar irin abin nan ne na yaran masu kud’i dake yaudarar ‘yan aikinsu da sunan so daga k’arshe kuma su lalata musu rayuwa,da ta fahimci da gaske ya ke domin har gidansu yake biyota tad’i sai ta amince suka fara soyayya mai cike da tsafta.

Lokacin da Hajiya Mariya ta gano suna soyayya ba k’aramin tashin hankali ta shiga ba nan ta fara masifa da zage-zage sannan ta kira Asma’u taja mata kunne akan karta kuskura ta sake ganinta da Abduhamid idan kuwa tak’i zata koreta daga aiki.

To wannan dalilin ne yasa yanzu take baya-baya da Abdulhamid,domin tana san aikinta wanda dashi suka dogara don shine ke temakonta ita da mahaifinta. Wannan kenan.

Hajiya Mariya ce zaune akan d’aya daga cikin manyan kujerun da ke parlournta,tasha wani ubansun les mai tsadar gaske milk colour,k’afarta d’aya bisa d’aya,kana kallonta zaka gane akwai abinda ke damunta,abinda take tunawa kuwa jiya gurin liyafar bikin zagayonwar shekaran haihuwarta tana kallon lokacin da Abdulhamid ya nufi gurin Asma’u tana ganin haka tafi bayansa a hankali tare da samun guri inda zata jiyosu ta 6uya,gani tayi Abdulhamid ya dubi Asma’u sannan ya gyara tsuyuwarsa.
Yace”Haba Asma’u tun d’azun nake miki nuni da kizo ki ka k’i.”
Asma’u tace”Abdulhamid don Allah ka rabu da ni kaga mahaifiyarka bata son tarayyata da kai,bazata ta6a yarda ka aure ni ba,har ga Allah Abdulhamid ina k’aunarka amma dole na fidda kai a zuciyata saboda mahaifiyarka bata sona.”
“Asma’u ki dena wannan maganar Mahaifiyata bata isa ta hana abinda Allah ya tsara ba,idan Allah yayi ke matata ce sai-dai tayi hakuri.”
Asma’u tace”haka ne,amma tunda ta nuna bata so don Allah muyi hakuri da juna domin mahaifiyarka tayi min gargad’i idan ban rabu da kai ba zata koreni daga aiki,Abdulhamid sanin kanka ne da wannan aikin na dogara,kuma bana fatan abinda zai rabani dashi.”
Yace”in har kina sona Asma’u ina so ki jajirce da abinda Hajiya zata miki domin wata rana sai labari in Allah ya yarda zamuyi aure.”
Asma’u ta share hawayenta tace”to Allah ya yarda.” ya amsa da “amin”

Asma’u tana bala’in tausayin kanta tabbas tana k’aunar Abdulhamid amma tana bala’in tsoran Hajiyarsa kamar me,tasan akwai sark’ak’iya mai yawa a gabanta.

Hajiya Mariya ta mik’e tsaye bayan gama tuno wannan maganar da tayi,da k’arfi ta furta”bazai yuwu ba,Wallahi bazai yuwuba,taya ma za’ayi hakan?nabar Abdulhamid ya auri wannan da basu tara uban komai ba sai shegen talauci da yayi musu kaka gida. Hajiya Saratu ce ta shugo ita da ‘yarta tare da Sallama, a hankali Hajiya Mariya ta amsa sai wani huci ta ke kamar zakanya ,da sauri Hajiya Saratu ta k’ara so,tare da dafata tace”Hajiya Mariya lafiya kike wannan huci tare da tada jijiyoyin wuya?Safiya ‘yar Hajiya Saratu ce ita ce ta k’ara so tare da samun guri ta zauna…..

Wasa farin girki.

FREE NE😘
Rashin comments ne kawai zai sa ya koma na kudi🥴🥴🥴

Sannan wannan littafin ba sauri na ke ba,a hankali zaku biyoni domin jin inda na dosa sai-dai idan kuka faranta min ta hnyr commeents zakusha lbr duk da dai mun koma mkrnt ba zakuji ni kullum ba sai ranar da na sami lokaci.

FATIMA SUNUSI RABI’U

⚫⚫⚫⚫⚫⚫
*…YA FI DARE DUHU*
💋💋💋💋💋💋
( _Labari me cike da surkulle da wani irin yanayi na sark’ak’iya da tsantsar tausayi,salonsa daban ne._ 👌 )

*MALLAKAR👇*
*FATIMA SUNUSI RABI’U*
_Ummu Affan_

________________________________

*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_

_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_

*Page 3-4*

Suma guri suka samu suka zauna,Hajiya Mariya tace”ni da wannan yaron ne mana,yana so ya jawo min abin kunya ya rasa wacce zaice yana so sai ‘yar aikin gidan wacce sai tayi aiki ta sami kud’i take ciwa kanta da iyayenta,ki duba Hajiya ki gani me yaron nan ya rasa?meye baya dashi?amma ya rasa wadda zan aura sai ‘yar aiki wacce ba abinda suka tara sai tarin tsiya.”

Hajiya Saratu tayi ajiyar zuciya tace”gaskiya Abdulhamid bai kyauta ba,amma ni aganina Hajiya tunda yaron nan ya nuna ita yake so to kiyi masa yarda yake so”
Wani uban tsaki Hajiya Mariya ta saki kafin tace.
“Dad’ina da ke Hajiya Saratu mutum ba zai ta6a kawo kukansa ki share ba,yanzun don Allah wanne irin abin kunya ne idan har na bar Abdulhamid ya auri ‘yar aikin gidan nan?”
Hajiya Saratu tace”ba’abin kunya ba ne,tunda Allah bai hana aure tsakaninsu ba.”
Safiya ta saka kuka tace”ni daman na yarda Hajiya baki k’aunata kamar ba ke ce kika haifeni ba,kin san yarda nake son Abdulhamid bani da wani buri da ya wuce na mallakesa a matsayin mijina amma har kike cewa abarsa ya auri ‘yar aiki.”
Hajiya Mariya tace”ai kuwa naji dadi,ni ban san da wannan maganar ba amma yanzu magana ta k’are ba fashi ke zaki auri wannan yaron.”

Safiya taji dadin maganar ji tayi kamar an sata a cikin aljannah ta rungume Hajiya Mariya.
Tace”Na gode Hajiya Allah ya cika mana wannan buri namu” “amin” Hajiyar ta amasa.
Hajiya Saratu batace komai ba dpmin tasan yarda ‘yar tata ke k’aunar Abdulhamid sai-dai sam ita bata da son kai shiyasa bata fad’awa Hajiyar ba don tasan daman wannan hukuncin shi zata yanke domin tasan yarda Hajiyar ke mugun k’aunar Safiya.

Hajiya Mariya da Hajiya Saratu aminan juna ne tun suna yara tare suka taso,sai-dai ita Hajiya Saratu tafi aminiyar tata tsaurin tunani macece mai hankali da zurfin tunani tana son Abdulhamid bata son abinda zai 6ata ransa shiyasa take yawan basa shawarwari domin mahaifiyarsa tana da wuyar sha’ani. wannan kenan.
………………………
Yau Malam Haruna ya tashi jikin nasa ba dadi da rashin lafiya hakan yasa hankalin Asma’u yayi mugun tashi domin tasan idan ta rasashi bata da kowa daman shi kad’ai gareta gashi kuma bata da kudi bare ta kaisa asibiti.

Tun safe suke abu guda har yamma hankalinta ya tashi sosai ganin bata da ko sisi gashi wata yaja domin yau ashirin da hudu muke ga wata hakan yasa ta yanke hukuncin zuwa gurin Hajiya Mariya ta temaketa ta bata kudin aikinta na wannan watan tunda yayi nisa ko ta samu takaisa asibiti.

A parlour ta isketa ita da iyalanta,ta duk’a har k’asa tace”don Allah Hajia alfarma nake nema daman Babana ne bashi da lafiya kuma bani da kud’in da zai kaisa asibiti,shine nake so atemaka a bani kudin aikina a yau duk da muna ashirin da hudu ne kuma naga oga Abdulhamid da ashirin da bakwai yake bamu harda biyarma wani lokacin yana bamu”
Abdulhamid da ke zaune gefe yana jin wannan maganar aljihu yasaka hannu tare da ciro kudi masu yawan gaske ya mik’a mata,sannan ya mik’e.
Yace”tashi muje a kaisa”
Da hanzali Hajiya ta dubesa tare da dakatar dashi.
Tace”Abdulhamid lallai ka haukace,a gabana kake cewa ta tashi ka kai ubanta asibiti?to wallahi bazai yuwu ba”
Ta nuna Asma’u da hannu tace”ke munafukar banza ina so ki sani daga yau na sallameki daga gidan nan kar in sake ganinki kar in sake ganin kin zo min gida tunda ba ubanki ya gina ba”ta dawo da kallonta ga Abdulhamid.
Tace”Kai kuma idan baka rabu da wannan yarinyar ba sai kaga mummunan matakin da zan d’auka a kanka,sannan kuma na saka ranar auranka da Safiya d’iyar Aminiyata Hajiya Saratu don ka sani ba fashi.
A razane ya dubeta yace”haba dai Hajiya me zanci da wata Safiya gaskiya bana sonta tsarinta basu min ba”
Tsawa Hajiya ta daka masa”dakata Abdulhamid Umarni nake baka ba shawara ba don haka ba fashi”

Asma’u kuwa kuka take sosai tana rok’on Hajiya ta barta taci gaba da aikinta dashi ta dogara tayi alk’awari bazata sake kula Abdulhamid ba,amma k’iri-k’iri Hajiya tace”bazai yuwuba kar na sake ganinki” cikin matsanancin kuka ta duk’a tace”Hajiya na tuba don Allah kiyi hakuri” ganin zata isheta da magiya sawa tayi aka mata korar kare.

Shi kuwa Abdulhamid bedroom d’insa ya shige tare da fad’awa saman royal bed d’insa ya fashe da kuka kamar wani k’aramin yaro,tabbas yana k’aunar Asma’u yana sonta so na hak’ik’a son da bai ta6a yiwa wata d’iya mace irinsa ba.
Asma’u yarinya ce da ko wanne d’a namiji natsattse mai hankali da natsuwa zai so mallakarta a matsayin mata,tana da kyawunta ba wanda ya 6aci ba dai-dai gwargwadon misali babban abin sha’awa a gareta tarbiyyarta ga natsuwa da hankali,amma wai kawai saboda kawai basu da kud’i abin duniya shine zai sa a k’ita?yasan dai Hajiya bata da wata hujja cikakkiya da zata iya cewa shine musabbabin da zaisa tak’i amincewa da auransa da Asma’u ba bayan wannan. Haka ya dunga sak’a da walwara cikin wani irin hali da yanayi mai wuyar fassarawa.

Tunowa da yayi Asma’u tace mahaifinta na gida bashi da lafiya sai yaji hankalinsa ya sake tashi sam bashi da kwanciyar hankali,tashi yayi ya kira k’anwarsa Hajara domin yasan yarinya ce mai hankali,dubu hamsim ya bata yace taje ayi duk abinda ya dace,lokacin da taje gidan ta iske Asma’u nata kuka ta tasashi gaba,da sauri ta k’ara tace”Asma’u lafiya?me ya sami Baban?Asma’u ta dubi Hajara tasan tana da kyirki sosai domin halinsu gida da Yayanta,tace”gashi nan dai ko motsi bayayi tunda na dawo na iske shi a haka”Hajara ta fita da sauri tayi kiran wasu mutane domin su temaka musu su sakashi mota,bayan sun sakashi kai tsaye wani asibiti mai zaman kansa Hajara ta nufa dashi,yayin da Asma’u ba abinda take sai kuka da kiran”Baba don Allah karka mutu ka barni bani da kowa sai kai,Baba kai ne gatana.

Hajara ita kanta hawaye ta ke saboda tausayawa Asma’u……….

MUJE ZUWA

Sharhinku shine zai k’aramin kwarin gwiwa my fans don haka zafafan comments zakuyi domin samun lavarin cikin lokaci.

COMMENTS
SHARING
PLEASE

FATIMA SUNUSI RABI’U⚫⚫⚫⚫⚫⚫
*…YA FI DARE DUHU*
💋💋💋💋💋💋
( _Labari me cike da surkulle da wani irin yanayi na sark’ak’iya da tsantsar tausayi,salonsa daban ne._ 👌)

*MALLAKAR👇*
*FATIMA SUNUSI RABI’U*
_Ummu Affan_

*MASHA’Allah my fan’s naji dadin sharhinku kwarai da gaske kuma ina yinku fiye da yarda kuke yina,fatana dai kuci gaba da comments shine k’arfin gwiwar ko wacce marubuciya na gode sosai da soyayya WhatsApp and Facebook luv u all.🥰*

________________________________

*AREWA WRITER’S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_

_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_

*Page 5-6*

Bayan isarsu asibiti da sauri likitoci sukayi kansa domin ceto rayuwarsa,aka aka samu numfashinsa ya dawo sai-dai bai dai-daita ba ganin yanayin da mahaifinta ya ke yasa idan banda kuka babu abinda take Hajara ce ke k’ok’arin tausarta da rarrashinta. Duk wani abu da suka buk’ata Hajara ce ke biya domin kud’in da Abdulhamid ya bada sunyi ma kad’an hakan yasa dole sai da ita ma ta biya a nata aljihun.

Asma’u babu abinda take sai godiya,Hajara sai-dai tace”babu komai”

To ba laifi zuwa yanzu da suke kwana biyar a asibiti jikin Malam Haruna yayi kyau sosai ya sami lafiya,inda har likita ya sallame su tare da fad’a musu lalurar da ke damunsa ta ciwon sugar sannan ya rubuta musu list na irin abubuwan da zai iya ci da wanda ba zai ciba saboda had’arin da suke dasu ga lafiyarsa,suka basu magunguna sannan suka sallamesu Hajara ta biya komai Abdulhamid ne ya bata sannan ta kaisu gida ta wuce kasuwa sai da ta ciko but da duk wani abu da akace Baban ya dunga ci sannan ta kawo musu wanda umarni ne daga Abdulhamid godiya sosai Asma’u da Baban suka dunga mata tace”ba komai duk wani abu da nake yi Abdulhamid ne ya bani” ta zaro kud’i d’ari biyar-biyar na dubu hamsim tace”ga wannan yace in baki domin ko zaku buk’aci wani abun” nan ma godiya suka dunga yi Asma’u harda kuka.
……………………
To Abu dai ya kankama domin an saka rana ta bikin Abdulhamid da Safiya wata biyu masu zuwa,farin ciki gurin Safiya abin ba’a magana sannan baya musaltuwa domin tana ganin ta samu cikar burinta.
Zaune suke ita da k’awarta a parlour na gidansu Sadiya k’awar Safiya ce tun a secondry suke take har zuwa yanzu da suka kammala digirinsu.
Sadiya tace”gaskiya k’awata na tayaki murnar samun cikar burinki wato Abdul” Safiya ta gyara zama tare da gyara kwalar rigarta tace”ke dai bari wallahi ji nake kamar in jawo wata biyun nan su dawo gobe,don gani nake kamar lokacin baya sauri”
Sadiya tayi dariya harda shewa da tafa hannu tace”kai k’awata kar fa azo kifi ango zumud’i”
Safiya ta d’anyi wani gajeran tsaki”mtsuwww!” tace” uhmm bari kawai kewai a tunaninki Abdul ya fara sona ne?” Sadiya ta zaro ido da cewa”ban gane ba”
Safiya tace”kawai k’arfinsa aka fi shiyasa ya amince amma fa baya k’aunata hasalima akwai wacce yake so”
Sadiya tace”Amma ke me yasa zaki aure sa baya sonki?kin san kuwa had’arin da ke tattare a cikin irin wannan auran?”
“Na sani mana kawai dai ina sonsa ne,kuma zan aure sa,ni kaina na rasa gane wanne irin so ne nakewa Abdul inaji a zuciyata zan iyayin koma menene akansa,sanar dashi da nayi ina sonsa nasan bai dace ba amma bani da yarda zanyi ne,Sadiya son da nakewa Abdul ban san iyakarsa ba tun lokacin da na kammala karatuna na dawo k’asar nan naci karo dashi naji ya shiga zuciyata kuma zan iya yin komai akansa.”
Sadiya ta sauke a jiyar numfashi tace”hmmm kin san an san yaran hausawa da kunya aka sannu ke kuma kin furta kina sonsa dole ya wulak’antaki.”
Safiya tace”wallahi bani da yarda zanyi ne son nasa ya min yawa bazan iya furta miki adadin son da nakewa Abdul ba.”
“To shi kenan Allah ya sanya alkhairi nidai shawarar da zan baki shine ki dage da addu’a Allah ya za6a miki mafi alkhairi.”
Tace”ni nasan Abdul alkhairi ne agare ni.”
Murmushi sukayi duka Sadiya tace”to Allah yasa hakan.”

Tari ya ke sosai harda kakarin amai,zuwa can kuwa amai mai k’arfi ya kwace masa ya dunga yinsa kamar zai amayar da ‘yan hanjin cikinsa,da ya gama yana k’ok’arin tashi sai ya zube a gurin cikin amai yana nishi sama-sama kamar numfashinsa zai fita,sai kuma tari ya turnik’esa yayin da zuciyarsa ke bugawa da k’arfi tsananin azaba yasashi dafe saitin zuciyarsa,hawaye kuwa sai kwarara suke a gurbin idaniyarsa.
Gaba d’aya sun harlara saman dinning table domin breakfast shi kad’ai suke jira amma shuru bai fito ba,hakan yasa Hajiya duban Hajara tare da umartarta akan taje ta kira Abdulhamid.
Lokacin da ta isa d’akinsa a sank’are ta iskesa kwance cikin amai cikin matsanancin tashin hankali ta d’aga hannu aka ta kurma wani uban ihuw tana kiran sunansa jin ko amsawa ya kasa yasata fita da gudu tana kira “Hajiya!Hajiya!!Hajiya!!!wayyo Hajiya Yaya Abdul zai mutu”
Cikin hanzari Hajiya ita da Maryam suka mik’e bedroom d’insa suka nufa duka har suna bige juna. Yarda suka gansa ya tada hankalinsu musamman Hajiya,Hajiya da Maryam suka temaka masa yayi wanka Hajara ta ciro masa kaya suka saka masa me gadi da direba ne suka kinkimesa zuwa mota sai asibiti.
Likitoci sunyi iya bincikensu inda suka tabbatarwa da Hajiya yaranta ya kamu da ciwon zuciya,lokacin da Hajiya taji haka hankalinta ba k’aramin tashi yayi ba,likitan ya k’ara dacewa”Hajiya akwai wani abu da yaranki ya 6oye a zuciyarsa kuyi gaggawar samar masa shi domin samun cikakkiyar lafiyarsa idan kuwa ba haka ba zuciyarsa zata iya kumbura daga k’arshe sai-dai ki rasashi” Hajiya ta dafe k’irjinsa tace”zamu rasashi Doctor?” yace”kwarai kuwa.”
Kwanansu uku aka sallamesu Hajiya bata cewa Abdulhamid komai ba domin tasan damuwarsa sai da suka koma gida sannan ta zaunar dashi shi da sauran ‘yan uwansa harda aminiyarta Hajiya Saratu da ‘yarta Safiya kuma matar da Abdul zai aura.
Hajiya Mariya tace”Abdulhamid naga a son da kakewa wannan yarinyar Asma’u har zaka halaka kanka da rayuwarka saboda haka tunda bakajin magana to na yarda ka aureta amma dole ne ka had’asu biyu ita da Safiya.”
Abdul wani irin farin ciki ne yaji ya jiyarci zuciyarsa da gangar jikinsa amma sai ya basar da cewa”a’a Hajiya ni tuni na riga na hakura da ita” tace”k’arya kake Abdulhamid domin idan ka hakura babu yarda za’ayi ciwon zuciya ya sameka,don haka na yarda da auranku amma ina so ka sani har abada bazan ta6a son Asma’u ba ita da duk abinda zata haifa tare da kai” Hajiya Saratu tace”haba dai Mariya bai kamata kice haka ba ki cire wannan maganar”
Tace”gaskiya na fad’ar masa domin ban son nan gaba yace na tsani matarsa da ‘ya’yanta”
A 6angaran Abdul kuwa wannan bai damesa ba domin yasan dole wata rana Hajiya taso Asma’u ‘ya ta gari ce zatayiwa Hajiya biyayya iya bakin k’ok’arinta zuciya kuwa dai tana son mai kyautata bata(Ni kuwa nace kayya dai Abdulhamid).

Lokacin da yaje gidan su Asma’u ya sanar da ita Hajiya ta amince da auransu sai ta nuna rashin farin cikinta tace”Abdul wannan maganar ni a gurina tuni ta wuce a gurina yanzu ina maka kallon d’an uwane kaima ka dubeni da wannan sigar,don haka don Allah mu mance da aminda ya faru a baya domin nasan har abada Hajiya bazata k’aunace ni ba,yanzun ma nasan ta amince ne saboda wani k’udiri nata ba akaran kanta ba duk da dai RASHIN SANI YA FI DARE DUHU”
Cikin kwantar da mirya da salon dad’in baki irin na maza idan suka so abu yace”Asma’u kiyi hakuri ki amince dani nasan Hajiya tun da tace ta amince to ta amincen ne sannan nasan dole watarana ta soki musamman idan taga kin haifamin d’an saurayi ko ‘yar budurwa me kama da ke” ya k’arashe da salon zolaya,murmushi sukayi duka ya d’aura da cewa.
“Asma’u ina sonki so mai yawa,addu’a itace ta dace mu dage dayi” haka ya dunga kwantarwa da Asma’u hankali,wacce dama k’arfin hali take don son da takewa Abdul mai yawa ne hakan yasa bai sha wuya ba wajen sakko da ita har ta amince.
Lokakacin da akasa saka na Safiya ba a k’ara komai akai ba Malam Haruna yace wa Abdulhamid lokacin yayi kusa da yawa shi bashi da komai da zaiwa Asma’u kayan daki yace karya damu shi Asma’u kawai yake so ba wani abuba.
Hakan yasa lokaci nayi akasha biki na ‘ya’yan gata ko da yake ita Asma’u bata da wani gata Abdulhamid shine gatanta,an kashe dukiya wajen ku kuwa masu abu da abunsa inda Ango Abdulhamid ya zamo angon mata biyu Safiya da Asma’,domin Safiya ce aka fara kaiwa a matsayin uwargida sannan Asma’u amarya,duk anan gidan Hajiya aka ajesu inda akawa kowa part d’insa da yake gidan mai girma ne sosai kamar gidan wani gwamna. Ko waccensu babban parlour da d’akunan barci biyu sai kitchen da toilet haka ko wanne bedroom da toilet abin dai gwanin ban sha’awa da burgewa.

To my fans anyi aure dai,to koya zaman zai kasance🤔🤔 kuci gaba da biyo Ummu Affan.

Leave a Comment