Books Reviews & FAQs • Kalaman Soyayya

“Yar Barrack Hausa Novel Complete

7/10/2022, 8:59 PM] Maman Nur: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
_*YAR BARRACK*_
(The barrack girl)
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman noorul hudah

Wanan labarin kirkiraren labarine banyi shi dan cin zarafin kowa ba,in ya Zo dai’dai da rayuwarki akasi aka samu

Ban yarda wani ko wata ta juyamin labari ta ko wata tsiga ba,yin haka’ babban laifine a kiyaye please

Ina wa masoyana Barka da sallah Allah ya maimaita mana,ko wacce ta kullo min naman sallah🀣
Godiya ga masoyana Wanda a kullum suna tare Dani,Ina godiya and for those da sukayi min text ban samu na muzu reply ba. kuyi hakuri kunsan inda babban sallah Ke kasancewa akwai aiki sosai but Ina mugun yinku and hail to those da suka bani barka da sallah Ina godiya so Nike in natsu in muku godiya,Ina godiya ga dukkan fans dina na groups dina,Ina su anty nafee nijar,anty baida’u,anty haddy,karimatu,Ina su hawwah,anty jammy,mummy Ina Miki barka da sallah,maman assadiq,maman Naseem,Kai yawa ne da ku duk Ina gaisuwa…..da wata Kuma matar baban mu🀣itama Ina mata barka da sallah…Ina customer na,to those who patronize my saloonπŸ€ͺIna godiya a huta gajiya,dukda wasu nayi dissapointing dinsu nasa sunyi sallah ba kitso…my best friend Rabi nasan ni Mai laifi ayi min afuwa kitso dai sai …..🀭ba rana

πŸ…Ώ1️⃣&2️⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Police barrack block 11room 13

Tsaye take da sauranyita Peter Wanda shima d’an sanda ne but kurtu ne a bachelor blocks yake Wanda yake d’auke da d’aki daya sai toleit da kicin

Cikin so da kauna ta kalleshi tace”eyyah Peter why are you like this?kullum Ina nuna maka soyyaya da kauna but Kai baka da buri sai kuntata min ta hanya niman Mata haba ”

Yace”ke da anyi magana ki ce kin bani komai but yet har yanzu ban Shiga ciki ba”

Tace” cikin Ina?in gidan mu ne muje ciki Mana me ke ciki, daddy baya Nan kuma Samuel baya gida muje ka gan gidanmu”

Yace”don’t play dump with me Gladys kin San irin cikin da Nike nufi ”

Tayi kicin kicin da fuska tace”Ban gane ba wani irin cikine wanan”

Hannun ya Kai kirjinta ya shafo ai buge hanun tayi tace”useless boy you think iam stupid da Zan Bari ka tab’ani toh ka je yau ko kaine autar maza iam done with you useless boy look at him like you want to shiga ciki,oyah Shiga ciki nahhh let see ”

Ganin zata Tara me jama’a yabar wurin da sauri Yana mamakinta ta bishi da zagi

Matsifa take dama ya lafiyar Kura balle tayi hauka ita dama abin fad’a baya Mata kad’an shiyasa kowa a barrack ke kudun shiga harkarta in Banda kawarta hafsat Dake jure matsifarta ko da yake kusan halinsu d’aya ai”

Hafsat ce ta fito ta backyard tace”you and who again?”

Cikin matsifa tace”isn’t that useless fellow Peter Wai in Bari ya shiga daga ciki ni na ma d’au wani d’aki zai shiga ashe Wai gindos yake nufi zaici”
Hafsat ta kyalkyale da dariya tace”tell me something ba kunya ya fad’a Miki zai shiga ciki sai ka ce wani shagon wanki da guga”

Cikin matsifa tace”he better not let us meet ko a hanya if not I will give him the disgrace of his life useless boy just because na bashi fuska he has the audacity to tell me nonesense”

Hafsat tasan mitar kawarta ta katse maganar da cewa mu bar maganar in mun dawo we are getting late for the birthday party wohhh and kisan irin sha’anin da za ayi ”

Cike da matsifa tace” ai uwarsa zanci shege kawai atsararre,Dan Gani karuwa yace”zai shiga ciki”

Hafsat tace”hurry nah go and get ready,nifa matsalar dake mita”

Shigewa tayi ciki tana wakanta na choir,Jesus na you be oga,Jesus na you be oga every other God na so so yeye,Every other God na so so yay…….”

Karasawa tayi ta bude gana most go dinta ta ciro kayan Christmas dinta,tace”God no go shame us,God don’t let us die in poverty please God of mercy,kayan Nan kullum sai ka ce dashi aka haiho Ni kullum fa shine a ko wani hoton sha’ani karfa a zo a Samin suna ”

Mikewa tayi ta koma falo hango kayan blessing tayi a shanye kofar room dinsu ta karasa da sauri tana kalle kalle kayan Basu Gama bushewa ba suna da sanyi ta ja skirt din sanan ta ja top da gudu ta shige dakinsu ta kulle tana cewa’god no go shame us”

D’aki ta Shiga ta kunna fan tasa kayan a saman fan ta Shiga wanka wanka ta fito sai warin sabulun s t take ta karasa saman kujeransu ta zauna tana shafa Vaseline bayan ta Gama ta shafa Jan Hoda da man Baki tayi kyau ba laifi ta shiga tasa under wears bra dinta ma an gyara shi da zare wajen hannu Saida ta tsaya tana kallo sai Kuma ta Fara sawa tace”God no go shame us,if not because of that useless fellow Peter na Gama sa raina na kusan aure ya kawo zancen Shiga ciki useless fellow but in my heart I know God no go shame me”

Shiryawa tayi cikin kayan da Suka Mata yawa ta nade hanun rigar a ka’ida siket din iya guiwa ya kamata ya tsaya mata amma da yike blessing ta fita tsayi sai ga skirt ya Zama 3qter sai beyi Mata kyau ba ga shi Suna warin sanyi ta zuba turare splash sai ya bada wani kamshin daban tana gyara wajen kugun da yayi Mata yawa ta kalli kanta a madubi ta girgiza Kai tace”God no go shame us we trust him”

Shiryawa tayi tasa lofers ta fito tana tafiya da k’yar gudun Kar siket din ya
Zame

Tunda ta fito hafsat data fito daga kofar gidansu ta zuba Mata idk

Tace”ah’ah Gladys what happened

Ajiyar zuciya ta sauke tace”hafsa God no go shame us wohhh e no go shame us”

Hafsat ta fashe da dariya tace

Maman Nur
[7/10/2022, 8:59 PM] Maman Nur: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
*_YAR BARRACK_*
(Barrack girl)
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹
By maman nurul
Hudah

πŸ…Ώ3️⃣&4️⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Hafsat ta fashe da dariya tace”Kinga ki kuwa Kamar zombie kayan waye wanan duk sun Miki yawa Kamar zombie ga warin sanyi da sukeyi gaskiya kije ki canza Kaya Gladys

Gladys tace”my sister I have checked all my clothe wallahi bani da Kaya sai na Christmas shima sabar sawa kullum wallahi ya kide Kuma ko Ina za aje shi Nike sawa,hafsat Ina cikin situation wallahi bani da Kaya fa a whole me gladys but bazan ce komai ba I know God no go shame me,we they here now, I have faith God will never shame me,he will 1day send me a rich guy that zai biya min bukatu he will not shame me iam giving you my world”

Hafsat tace”in Kika je gidan da kayan nan bazan b’oye Miki ba you have shame yourself Gladys gomma ki je kisa Wanda Kika Saba sawa zaifi Miki wanan”

Gladys tace”no is better in ji kunya yanzu than a Samin suna for the rest of my life,haba hafsa duk inda muka je sai anyi hoto Koda a wayane Baki San mutane da ajiye history ba,yanzu karkiyi mamaki hotunan har jikoki kila ma an samun suna ban sani ba”

Hafsat tace”ki hakura da zuwa mama toh’

Tace”in Bana zuwa irin wanan birthday din Taya zan had’u da zazzafan gayu azima tana da connection she is dame rich nasan Manya samari zasu je gun shiyasa,you know she own a saloon na kanta niko gashi na koya aiki na iya ko kudin dryer bani dashi ”

Hafsat tace”Gladys Babu Wanda zai so ki a Haka da wanan oversize kayan”

A fusace tace”ah’ah why are you like this? haba ba komai Ido ke gani Baki ya fad’a b except you want God to shame you’

Sanin halinta yasa hafsat batayi magana ba tayi gaba cike da haushi ta bi bayanta tana ta mita tace”you are downgrading me if not for that stupid and useless boy that broke my heart this evening if not,I have plans of getting married this year but Wai zai shiga ciki useless and stupid boy ”

Hafsat tasan mitar ta Bata ce komai ba har Suka fita titi,hafsat ta tare adaidaita tace”army barrack zaka kaimu”

Yace”saba’in saba’in”

Gladys da karasowarta kenan tace”oga hamsin ne meyasa kuke Haka?shiyasa Allah ke kunyata ku a tsakiyar titi keken ke lalacewa”

Yace”shiga muje

Shiga Sukayi,Gladys tace”Peter really broke my heart today after giving him my love Ashe dai nayi waisting time Dina ne ”

Hafsat tace”kema gaki da masu sonki ki nace sai shi ki duba fa harun inda yake tsananin kaunarki Kuma aurenki zaiyi ga kudi ga kyau he is 1 in a million but you refuse ni da zaice Yana so na i will not hesitate to accept his proposal”

Gladys ta Mata wani kallo tace”that is why you are in shame if you like go and meet him and confess your love for him I swear I will never date a muslim guy duk rintsi,inyi aure ko kwana biyu banyi ba ya sake aure from there ya Fara wulakantani bayan ya kwashi albarkatun jikina da nayi complain ya danna min saki that how they are”

Hafsat tace”wallahi karyane ba duka musulmai ke Haka ba in kin gan Haka ta faru aurene ya mutu ai Kuma akwai kaddara”

Tace”ji wata magana kuyi ta fakewa da kaddara mu Christian in muyi auren ai till death do us part ne toh Babu kaddarane me I will never in my life get married to muslim ”

Hafsat tace”is useless talking to you shiyasa kike ta wahala ba saurayin kirki Suma musulman masu nace miki sune da laifi ga matar musulma birjik sun nace Miki

Fuska d’aure tace”you are downgrading me because of Peter broke my heart today ko ba komai muna Nan ai dake you will witness my church wedding I have faith God no go shame usby god grace my dream will come true Bani da buri kamar in gan nayi church wedding ”

Hafsat da ta tsuke fuska saboda ta lura Gladys Bata da aiki saina kushe musulunci

Me adaidaita yace”mun Kai”

Ita ta Fara fitowa ta bashi 200 sai ta gan ya ja Keke

Binshi tayi Yana barin gaban barrack din ya paka ta karasa tace” meyasa kuke hakane?”

Yace”bafa guduwa nayi ba,na hango sojane na karasowa kin San ba a parking a wajen

Ya Kare Yana duba Mata canji da alamun beda caji sai dubawa yake

Wani mota ne ya fito daga barrack din baka wulik duk tintec sai kyalli take

Horn ya Danna Mata Amma taki barin inda take gashi wurin Babu wadatacen girma ga katon Culvet Kuma me keken yaci Rabin titi

Kara dannawa horn yayi Taki tashi,Hafsat dake inda ya Fara saukesu ta zaro Ido sai Kuma taje kusa da Gladys din ta Kama hanunta fisgewa tayi tace”live me alone mutane Basu da hakuri haba minti nawa ne Zan ansa canji na in bar nan Amma saboda rashin hakuri Yana niman maidani kurma da horn ”

Gyara Zama yayi Yana kallon ikon Allah yau ga iskanci

Tsoro ya Kama me napep kudin dake hanunshi ya watsa Mata ya ja keken da gudu

Sake Danna horn din yayi Amma haushin me Keke daya wuce Mata da arbain yasa ta gyara tsayuwa a saman titi

Hafsat tace”kila fa soja ne zane ki zaiyi ”

Tsaki tayi ta gyara tsayuwarta again,Hafsat da tsoro ya kamata tayi saurin barin wurin

Shi daman Yana da bad temper balle an rainasa ji yayi ranshi ya mugun b’aci,Yana kokarin kunna motar sai Kuma yayi tsaki ya fito sanye da wando sojoji da farar Riga me kyau me v shape kyakyawa ne sosai fari Sol sab’anin Gladys dake chocolate colour,fuskar nan a murtuke

Daga Kai tayi ta kalleshi sai ta ji fadiwar gaba tsoro na taso Mata Amma tana kokarin dannewa dan ta Zama jaruma tunda ta rigada ta Fara dole ta gama

Tun Kan ya karaso kamshi shi ya Isa gareta ta lumshe Ido ta sake budewa

Saida ya Kai kusa da ita ta kasa daurewa ta Fara ja baya

Da hanzari ya kamota ya wanka Mata wani Mari daya d’auke Mata ji da ganinta,sit kake ji kamar anyi ruwan sama an d’auke sai bΓ yan wasu mintina ta saki wani ihuuuuu ta rungumeshi ba tare da tasan tayi haka ba

Ture ta yayi ba tare da yace”komai ba ya Kara Mata wani Marin ta Fadi a culvet Hafsat dake gefe ta saki fitsari a jiki dan fuskarshi kadai ya isa ya tsorataka

Komawa yayi motarsa ya kunna ya jata a guje

Hafsat ta tsallako da gudu tana kuka tace”God no shame Gladys wohhhh…”

Kasa fiddata tayi Saida ta nimi taimako Gladys aiko Bata numfashi

Bayan awa hud’u

General hospital

My fans muje zuwa god no go shame us🀣wanan littafin sadaukarwa ne ga kawayena na police barrack,hafsat an co….I miss barrack life🀣

Maman Nur
[7/13/2022, 10:45 PM] Maman Nur: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
*_YAR BARRACK_*
(Barrack girl)
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹

Paid book

πŸ…Ώ9️⃣&1️⃣0️⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Karasawa tayi lokacin har sophy ta fito daga mota itama cikin wando uniform take sai farar Riga a baya an rubuta Nigeria army

Ko kad’an glad batayi la’akari da dressing dinta ba fuskarta take kallo

Shi ko be kalleta ba dan harga Allah ya mance ta wallahi shi dama bawai ya gan fuskarta bane ko a wancan ranan be damu da yasan fuskarta ba

Dukawa tayi cikin ladabi tace”Ina kwana mama”

Sophy ta had’e Rai dama in akwai abinda ta tsana a duniya shine a kirata mama”

Gla batayi la’akari da fuskar da ta hade ba ta mike tace”now I see whree this useless man got his stobbornness in gaishe ki ki’ amsawa anyway ni ba Ina son gaisuwarki bane Daman na so warning d’anki ne kafin in Rama abinda yayi min dukda ko na fad’a Miki bazai Hana in Rama ba wallahi zuwa nayi in Rama abinda ka min ran Nan”

Kallon mahaukaciya yayi Mata yace”are you ok”

Girgiza me Kai tayi tace”urmm urmmmm nida ok bamu sake had’uwa ba tun Randa ka dakeni malam”

Kama hanun sophy yayi suka ratsata ta Kama me hanun d’aya tace”iam not done with you”

Tun farkon Fara maganarta dama ran sophy ya b’ace mussaman kiranta da tayi mama

Sophy tace”muje kawai glad Bata ce komai ba ta bisu da kallo ai dama Basu Kai da shiga hotel din ba Suka ji tasss tasss”

Da sauri suka juya glad CE tsaye da wata katuwar tsanda ta rusa me glass

Rungume hanun yayi Yana kallon ikon Allah toh wai me yarinyar Nan ke nufi ne kodai akwai abinda take sha,tsabar b’acin rai ajiyar zuciya kawai yake saukewa

Karar fasa glass yasa su anty da customer fitowa anty na ganin gla na b’arna ta tsallako da gudu ta riketa tace”Gladys miye Haka wanan fa customomina ne kikewa b’arna

Gladys na nishi tana fidda wani hucin takaici tace”anty I don’t care if they are your customer,do you know what this useless man did to me shine fa yayi min Wanan dukan har asibiti na kwanta yanzu Kuma as a good Samaritan that iam na ganshi da mamanshi na fad’a Mata abinda yayi min I was expecting zatayi me fad’a but no sai magana banza ta Gaya min sai na me kwatankwacin abinda yayi min,useless man…Daman nasan God will never shame me sai gashi mun sake had’uwa”

Anty taji ba dadi Jin glad tsakaninta da Allah ta dau sophy maman oga Umar ne saboda hakan a gunta cin fuska ne

Cikin kwatar da murya inda su sophy dake gefe bazasu ji ba tace”budurwasa ce gla ba maman sa ba”

Goge fuska gla tayi ta d’aga murya tace”you mean he is dating this old woman?anyway that is none of my business anty yanzu burina in Rama abinda yayi min”

Mutane sai mamakin tsaurin idonta suke suna hango matsifar data jawowa kanta

Itako matsifa take yace”now I see the reason why you are in shame,and by God grace you will forever be in shame,in Banda abin kunya why will you date a woman that is old enough to be your mum ai kunyar kenan you think zaka wuce free ne wallahi bazaka tab’a wuce free ba”

Shi kallonta ma kawai yake trying hard to control himself,kallonshi sophy tayi tace”ita din wacece”

Ya Buda Mata hanun yace”oho”

Hawa saman motar tayi tana mitarta sai ga hafsat ta sauka a adaidaita da kula a hanunta

Hankalinta tashi yayi ganin gla a saman mota ta tattare rigarta kallon gefenshi tayi ta ganshi tsaye Yana tunanin dukar da zaiyi Mata ganin ya Fara zuwa gun motar da hanzari jiki na rawa hafsat dake tsaye ta Sha gabanshi tace”kayi hakuri sir wallahi Bata da hankali

Hankad’a hafsat yayi gefe ta Fadi jikin wani karfe kanta ya fashe ta saki wani Kara

Be bi ta kan hafsat ba,anty da ta tsorata tayi gefe

Karasowar shi tayi dai’dai da dirowar Gladys daga saman mota Daman jira take ta karaso kafin ma ya Kai Mata duka ta Kai me bugu a jiki

Wanka Mata Mari yayi sai ga Gladys tana juyi can ta fad’a jikin mota

Ya shako ta ya sake sauke Mata wani mari,wani ihu tayi tana Kiran anty

Idanun ya Umar ya rufe shiyasa beyi la’akari da mace bace Kuma karamar yariya yayi ta dukan ta

Sake matseta yayi kamar ya samu sa’an shi a jikin mota glass din data fasa duk ya ji Mata ciwo a kafafuwa saboda ita ba takalmi a kafafuwarta,sinin wata fashashen glass Dake jikin mota ya manneta sai abin ya tsoketa a baya sai ga jini na sauka tuni ta sume

Belt sophy ta bashi ai Aiko yayi ta lafta mata,kowa na tsoron zuwan kwatar Gladys dayawa na ganin ita ta jawa kanta miye na Shiga harka soja

Anty tun tana rokarsa daga nisa har ta fashe da kuka sophy ce zata taimaka Kuma ko a jikinta

Habib daya dade tsaye ya Zo wucewa ne ya gan motar Yayar nasa a fashe ga Gladys a sama ya paka nasa Yana kallon ikon Allah

Hafsat da ke zaune ta kasa tashi tun ture ta da yayi da k’yar tayi karfin Hali tashi ganin kashe Gladys zaiyi tana rike waist ta karasa ta duka tana rokon shi tana kuka

Da wanan Daman Habib ya

Maman Nur
[7/13/2022, 10:45 PM] Maman Nur: πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„
*_YAR BARRACK_*
(Barrack girl)
πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹

Paid book

πŸ…Ώ1️⃣1️⃣-1️⃣2️⃣

Bismillahir Rahmanir Rahim

Habib ganin hankalinshi na Kan hafsat data Kama me wando Habib ya d’auki gla ya Kai mota shi Habib mutum ne me tausayi balle in aka ce ya’ mace Yana da raunin akan mata

Bude bΓ yan mota yayi ya sakata a mota shiko ya Umar bema lura da Habib

Tashi Hafsat tayi ganin Habib zai tada mota ta bishi da gudu,shiko ya Umar ya karasa gun sophy ya kamata yace”are you ok?”

Tace”yes muje toh”

Binsu anty tayi shago ta cigaba da aikinta saidai hankalinta na Kan Gladys but gaskiya bazata iya rufe shagonta ba da wanan customers data samu, she can’t compromise Kuma ai Gladys ta had’u da match dinta ne

Habib dake tuki ya kalli bayan mota yace”Wai me tayi Masa ne!”
Cikin kuka hafsat tace”Ni ban San meyasa ko Ina ya ganta sai ya duke ta ba,dan kawai sun gan bamu da kowa shine za ayi ta zalinta mu,ranan ma fa Haka yayi Mata wanan duka watan ta biyu tana jiyan wallahi da nasan gidansu da sai naje gun magabatansa su Mana iyaka dashi

Habib ya dan juyo ya kalleta yace”in na kaiku gun magabantansa Zaki iya magana?”
Tace”kasan shi ne?”

Yace”eh yayana ne in Kuna so ai sai in Kai gun mahaifinmu zai dau mataki”

Hafsat tace”ai yanzu ma nan zaka kaimu wallahi ya ganta kafin ma a kaita asibiti ”

Murmushi yayi dan shima zaiyi amfani da wanan damar ya d’au fansa abinda ya Umar yayi Masa last week da ya Kai kararsa gun Abba akan wai dan yaje club

A fili ko cewa yayi kin San waye mahaifinmu”

Ta girgiza kai,yace”malam jabir ne mahaifin mu ai”

Tace”kana nufin malam jabir dai gidan yawa”

Yace”yes shi Wanda ya daketa Yaya na ne ai,in munje so nike ki dage ki masa bayani karki kalli fuskarshi dan zai iya Miki kwarjini ki daburce ”

Tace”toh ”

Kofar gidan ya paka ya Shiga ciki almajira ne ke Kai kawo a zauren,cikin gida ko matan gidan na harkokin gabansu daga Mai yin lalli sai kitso duk kowa na gida anyi busy

Shiga yayi shiyan malam ya ganshi kwance a falo Yana hutawa da yike Yana azumin na kwanaki goma da akeyi kafin sallah

Zama yayi a kasar carpet yace”Abba Sannu da hutawa”

Gyrawa Abba yayi daga kishigid’e da yake yace”yauwa habibullah ya ayyuka toh Allah yayi maka albarka”

Yace”Amin”

Dan shiru yayi Yana tunanin ta inda zai Fara,Lura da magana a bakinshi yasa Abba cewa”Yaya dai habibullah akwai magana”

Habib ya daure yace”Daman Abba Dana fita ne zani aiki sai na hango motar Yaya Umar pake glass duk a fashe shine na faka in gan meke faruwa kawai sai na gan ya rufe wata Yar yariya da duka Kamar sa’an sa Dana nimi Jin ba’asin maganar Wai Ashe ganinsu tayi da wanan matar da kuka rabasu Wai ta duka tana gaisheta tace”Ina yini umma”shine yaji haushi Wai ta Kira budurwarsa umma wallahi Abba baka gan dukan da yayi Mata ba,abinda ya bani haushi inda jama’ar wurin suke ta cewa”Wai Dan alhaji jabir ne gidan yawa yake wanan zalunci Dan ya gan mahaifinsa Mai kudine shima sojane yake take Wanda ya ga dama sai ka ji surutu wallahi da k’yar na jata tana mota yanzu ”
Gyara Zama Abba yayi yace”daman be rabu da matan ba?”

Girgiza me Kai habibullah yayi yace”suna tare ”

Yace”toh Ina yariyar take?”

Habibulah yace”tana motata a sume”

Mikewa yayi dama da kayan jikinshi Suka fita gun mota

Hafsat na ganinshi ta fito a mota ta fashe da kuka tace”shikenan dan bamu da kowa ya nimi kashe yariya Nima gashi ya b’alla min kugu ka taimaka baba kayi mana adalci

Bude motar yayi Yana ganin gla ya rintse Ido duk jikinta bruises ne

Yace”Ina zuwa ”

Ciki ya shiga fuska ba walwala ya tarar da su ummi zaune suna Hira

Yace”hauwa'”

Ummi ta d’ago ta kalleshi yace”Aisha,hafsat,Khadija ku saka mayafinku ku biyo ni kofar gida”

Yana fadin Haka ya fita,jikin kowa a sanyaye Dan sunSan ranshi a b’ace yake hijabi Suka sa har nikab Suka fito

Ya Bude musu bayan motar,yace”kun gani toh faruku ne yayi wanan aikin akan ta gaida wanan matan da Muka rabasu ta kirata umma,Ashe Daman ban Isa da farouk ba?”

Ummi ta kurawa Gladys Ido cike da tausayi

Mama tace”watoh dai watsar da maganar mu yayi ya nimi nakasa ta akan wanan fitsararriya matar

Hafsat ta fashe da kuka tace”wanan ba shine farko ba kwanaki ma Haka yayi Mata duka kwanarta 20 a asibiti Wai haushi take bashi ita kafura ce ”

Abba yace”ku koma ciki dama nuna muku zanyi domin hukuncina bazaiyi mishi dadi ba wallahi,kafin ya sani a bakin duniya Ni Zan sashi Kai habibu muje asibiti

Shiga motar yayi su ummi Suka Koma ciki mama ce ta Shiga baya ta zauna sai hafsat itama ta shiga suka tafi asibiti

Yanayin inda aka dade kan Gladys ya Kara b’ata ran Abba domin ba karamin rauni taji ba a baya

Suna tsaye daddy da hafsat ta Kira ya zo asibiti

Gaisawa sukayi da baba a mutunce yanayin daddy yasa Abba gane akwai matsala domin dukda ba giya ya Sha ba a wanan lokacin warin giya yake ya ja hafsat waje da sunan zasu siyo Abu

Saida suka fita yace”labarin yarinyar Nan Nike son ki bani ”

Kuka ta fashe dashi ta kwashe komai ta fad’a me ba abinda ta b’oye me sai yaji tausayin Gladys din Jin Wai marainiya ce ita din ”

Komawa ciki sukayi rike da kayan tea fuskarshi a murtuke yace”Mr Philip I want you to give my son your daughter hands in marriage I mean Ina nemawa d’ana auren Gladys ”

B’am hafsat taji kirjinta ya huga sai ga abban hafsat da mummy sun iso

Daddy yace”iam sorry na gan kokarinka akan daughter na but bazata auri musulmi ba

Abba hafsat daya ji dadin lamarin dan a waya hafsat ta Basu labarin abinda ya faru ya washe Baki yace”malam karka damu Zan mishi bayani

Gefe Suka Koma da abban hafsat malam yayi mishi bayani yace”ai shi wanan birkicece ana bashi kudin zai aminci naji dadin wanan abin Ina kaunar Gladys dan burina ta auri D’ana Ahmad but na rasa ta Ina Zan b’ullowa al’amarin saboda Sha shidda ce yariya wani lokaci Amma akwai kamun Kai yariya

Hafsat ta karaso tace”wallahi Kar a d’aura wanan auren infa Gladys taji wanan labarin da matsala”

Malam yace”inko ba a d’aura auren nan yau ba toh mutuwa nayi ko Kuma Umar din ne ya mutu ”

Mama itama ta bada goyon baya hakan

Niko nace chabbb akwai show

God no go shame us

Leave a Comment