Books Reviews & FAQs

Yarena Addini Na Hausa Novel Complete

+++++++ YARENA ADDININA +++++++
An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau – kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau – manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau – Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku

This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that – we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that – pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that – our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT

FARKON LABARI

Garin Doko gari ne mai yalwar jama’a masu sana’u daban-daban wasu Manoma, wasu *yan kasuwa suna yawan zuwa cin kasuwanni a garuruwa daban-daban. *Yan garin yaren Hausa suke yi saboda haka Hausawa ne yawancinsu, sai wasu kadan Fulani a garin. Garin yana karkashin karamar hukumar Garki dake Jihar Jigawa.
Yau daren goma sha hudu don haka garin ya gauraye da hasken farin wata, ko kwandalarka ce ta fadi a kasa zaka iya ganinta saboda hasken farin wata. Matasan Samari da *yan mata wadanda shekarunsu basu wuce goma zuwa goma sha biyar ba sune suke shawagi suna tsalle-tsalle suna wasanni kala-kala da alama suna jin dadin yanayin garin a yau. Ga hasken wata tar ga wata iska mai sanyi na kadawa.
Suhaif saurayin da babu mai iliminsa, kyau, nutsuwa, hankali da tsantsar iya kwalliya da gayu, yana fitowa daga gidan Kakarsa sai ya tsinci kansa da samun wani dan dakali a kofar gidan ya zauna yana kallon yaran da suke wasanni kala-kala yana murmushi shi kadai. Yana tuna baya lokacin da suke kamar haka suma sunyi duk irin wannan. *Yan maza suna wasan langa, wasu na wasan *yar buya. *Yan mata kuma gada suke yi. Wata zabiyar yarinya ce mai zazzakar murya ta ware murya ta fara rero waken gada ta ce.
“Uwar miji ta zagen na durkusa ina ta neman gafara.
Uban miji ya zagen na durkusa ina ta neman gafara.
Da kishiya ta zagen na lillisata na kaita Ofishin *yan sanda sun lillisata sun juyata sun kaita lahira sai gata a duniya.
Iyaraye nanaye aiye raye iye nanaye *yan mata.

Dariya ta kubcewa Suhaif ya fada a bayyane ya ce “Kai mata, mace bata son kishiya. Sai ga dandazon mata *yan kai amarya sunzo wucewa za’a kai amarya gidan mijinta. Mata dauke da kwallayen alkaki da nakiya na gara. Wata guda daya daga cikinsu ta goya amarya a baya, sai rera waka kawayen amarya suke yi. Suhaif ya bisu da kallo har suka wuce. Gefensa kuma wata kanwarsa ce (cousin) dinsa mai suna *Yar Hajja tana zaune da fitila a gabanta tana sayar da kwai ana *yar fashe, duk wanda aka fasa nasa an cinye shi sai ya bawa wanda ya fasa kwan ya cinye. *Yar Hajja ta ware murya ta rada tallar gyada da karfi ta ce
“Ta soyu da manda rangadau.
Tayi arewa da filin dakata amaro,
Sai ta sake rerowa,
“Goro goriye goro daushe, goro dan Kano dan Kaduna wanda bai ci ba yaci sabo.

Cikin tsokana Suhaif ya ce da ita “Ke zabiya rufe bakin kar sauro ya fada miki. *Yar Hajja uwar son kudi bayan tallar Koko da kike da safe, kiyi ta dan wake da rana da daddare ma sai kin sayar da goro da Kwai da gyada amaro. Bari inzo inci alakoro. Ya taso ya zo gaban farantin *Yar Hajja ya tsaya. “Yar Hajja ta ce “A’a bana bayar da alakoro sai dai ka saya, wallahi Babangida ka cika son kudi duk kudin da kake jidowa idan kaje Kano kace baza ka saya ba sai dai alakoro kai ko tausayina baka ji. Suhaif ya kyalkyale da dariya ya ce “Kaji ta wai kudin da nake jidowa a Kano kamar wani barawo, kudin ma jido shi ake yi a Kano? Ai kin fini son kudi, lashe money sunanki fa. Ya kai hannu zai dauki kwai daya sai *Yar Hajja ta janye farantin ta ce “Wannan Kwan nawa ne na kashin kaina amma gyada da goro na Hajja ne kakata kuma kakarka ce babu abin da zata ce maka. Ya ce “Ni ai ba tsoho bane bana cin goro. Bana cin gyada kuma tunda ni ba mayunwaci ba ne kwai ni zanci. *Yar Hajja ta dauko kwai daya ta mika masa, ya karba ya mikawa wani yaro a kusa dashi. Sai ya fisgo kwan gaba daya farantin ya ce da yaran dake wajen “Ku shirya yanzu zan rarraba muku kwai ku ci kyauta sai kuyi mata wakar yayi kwantai. *Yar Hajja ta fashe da kuka ta tashi da gudu zata shiga gida taje ta fadawa kakarsu cewar ga Suhaif nan zai rabar mata da kwanta. Suhaif ya kwalla mata kira ya ce tazo ta karbi kudin kwanta zai siye ya bata kudinta. Ta dawo tasha kunu ta rike kugu. Ya zaro *yan dari-dari guda uku sababbi fil ya mika mata ya ce “Kudin kwan nawa ne? Nasan baifi dari biyu ba ga dari uku nan ki rike, uwar son kudi. Ta kyalkyale da dariya ta rafsa buda tana murna ya saye kwan duka harma ya kara mata kudin. Suhaif ya dinga rabawa *yan mata da yaran dake zazzaune a zagaye da fitilar *Yar Hajja kowacce ya mika mata sai farinciki ya rufeta daya bayan daya yake binsu. Daga karshe sai ya hango wata budurwar yarinya a can gefe a zaune da jakar kayanta a gabanta. Ya ce “Waccan kuma wacece ta tafi gefe ta zauna ita kadai? *Yar Hajja ta ce “Mu ma bamu santa ba, bamu taba ganinta a garin nan ba, tun dazu tazo ta sauna tana kallon mu. Munyi mata magana tayi shiru. Suhaif ya karasa gareta, ya mika mata sauran kwan dake hannunsa guda biyu. Tasa hannu ta karba. *Yar Hajja ta dauko fitila da sauri ta zo tana haska wannan baiwar Allah, sai taja mayafinta ta rufe fuskarta, Suhaif ya yiwa *Yar Hajja tsawa ya ce ta daina haskata sannan ta tafi da fitilar. Suhaif ya durkusa a gabanta ya ce “Yan mata ya sunanki ne? Ta yi shiru bata amsa ba. Ya sake cewa bamu sanki a garin nan ba, haka baki yi kama da *yan garin nan ba. Daga wanne gari kika zo? Tayi shiru bata amsa ba. Yana shirin jeho mata tambaya ta uku sai yaji ta rushe da kuka mai tsanani. Yaji hankalinsa ya tashi ya hau lallashinta yana cewa “Daina kuka Allah Ya baki hakuri na daina tambayar ki. Can da kukan ya tsagaita sai ta dago da wasu dara-daran idanuwanta farare sol ta dube shi cikin wata sanyayyiyar murya ta ce “Ina so insha ruwa ko zaka taimake ni da ruwa? Ya ce “Zan taimake ki da ruwan sha *yar uwata. Ya tsura mata ido yana kallonta yana mata murmushi, sai ta sunkuyar da kai kasa. Ya kwallawa *Yar Hajja kira ya ce taje cikin gida ta dauko kwanan shan ruwan Hajja Kakarsu sabo, ta kawo masa ruwan sha mai sanyi na tulu. *Yar Hajja ta tashi ta nufi gida don dauko ruwan sha.
Suhaif ya sake duban Yarinyar ya ce “Idan na taimake ki da ruwan sha, zaki taimakeni ki fada mun sunanki da kuma inda kika fito? Ta gyada kai kai tana jujjuya kwai biyun dake hannunta. Ya nisa ya ce “Kawo kwayayen in bare miki. Ta mika masa ba tare da ta kalleshi ba. Kafin ya gama barewa *Yar Hajja ta kawo ruwa a cikin kwanan sha, mai sanyi kuwa tamkar daga firij ya karba ya mika mata. Lallai ta kwaso kishirwa kusan kwanan shan duka ta shanye, kadan ta rage. Ya mika mata kwan sai yaga ta karba tana ci bayan kishirwar data kwaso da alama akwai jin yunwa ma a tare da ita. Suhaif ya ce “Gashi kuwa kwan ya kare dana suyo miki wani sai dai gyada da goro. Ta girgiza kai ta ce “Ya isa na gode. Har yanzu a durkushe yake a gabanta. Ya nisa ya ce “Ina jiran amsar tambayata. Tayi narai-narai da ido ta ce “Sunana Fatima ana cemin Iman. Daga tashar *Yankaba na hau motar Gumel, kudin motata bai cika ba shine masu motar suka saukeni anan garin suka ce anan kudina ya kare. Ya ce “Ke kuma Gumel kike so kije suka sauke ki anan Doko? Yanzu idan aka baki kudin motar zuwa Gumel shi kenan matsalarki? Iman ta rushe da kuka ta ce “Gumel din ma idan naje bansan inda zani ba, bansan kowa ba kuma. Suhaif ya gyara tsugunansa ya ce “Iman ban gane ba, baki san inda zaki ba kenan? Ta kara rushewa da kuka mai tsanani tana cewa “Ban san in da zani ba, ban san kowa ba a duniyar nan. Ya bude baki yana mamaki can ya ce “Iman yi shiru ki daina kuka in tambayeki. Ina Iyayenki? Cikin kuka ta ce “Ni a Makka a ka haife ni, uwata ta rasu kwanannan, ubana kuwa tun ana goyo na ya rasu. A Makka muke zaune, sune kadai suka rage min bansan danginsu ba. Shine askarawa masu kame a Makka suka kamoni. Suhaif ya girgiza kai cike da tausayi ya ce “Oh my God! Yi shiru Iman insha Allah zan taimakeki. To amma abunda ya daure mun kai shine daga jin Hausarki kun dade a Makka baku da takardar shaidar zama (igama)? Iman ta sharbe hawaye ta ce “Wahala da wulakanci nake sha tunda iyayena ba su bar min wata dukiya ba, aikin gidan larabawa suke yi kuma daman bamu da takardar zama, ina yawo askarawa suka kamani suka kawo mu kasar, bansan kowa ba a Nigeria. Kukan ya sake kece mata. Ya girgiza kai yayin da tausayinta ta sashi kwalla.
Ya nisa ya ce “Iyayenki *yan asalin wanne gari ne? Iman cikin shesshekar kuka ta ce “Sun ce su Fulanin Sokoto ne, Suhaif ya ce “Allah Sarki *yan Sokoto kuwa suna da kirki, zo in kaiki cikin gida wajen Kakata in shaida mata. Ya rike mata jakar kayanta tana biye dashi suka nufi cikin gidan. *Yar Hajja da kawayenta suka bi su Suhaif da kallo suna *yan gulmammakinsu. *Yar Hajja ta ce da kwayenta “Babangida zai kai mana wannan bakuwar gida karfa aljana ce ko mayya ta cinye mu cikin dare. Kwayenta suka ce “Wallahi, dan kuwa lokacin da kika haskata da fitila mun ganta kyakkyawa ce, kamar aljana don kyau. *Yar Hajja ta ce “Dalla, waye ya ce muku aljanu kyawawa ne? An ce har kaho garesu da kofato a kafarsu.
Suhaif na shiga suka iske Hajja Kakarsa a tsakar gida yayi sallama ya shiga. *Yar tsohuwa ta amsa ta ce “Wa nake ji kamar Babangida, dawowa kayi, tsokanar da kayi mun dazu bata isheka ba? Ya yi dan murmushi ya ce “Daman ban tafi ba ina kofar gida, Hajja ga wata marainiya na tsinto a kofar gidanki tana zaune tana kuka bata san kowa ba bata san inda zata ba. Iman shigo ki zauna akan tabarma. Hajja ta ce “Marainiya ka tsinta a kofar gidana? Suhaif ya ce “Gata kuwa kina ganin mu tare. Iman ta zo ta zauna a gefen Hajja ta duka ta gaisheta. Hajja ta amsa gami da sa hannu ta shafa kan Iman ta ce “In shafa kan marainiya in samu lada. Allah Sarki daga ina kike? Iman ta rushe da kuka mai cike da tausayi. Sai Suhaif ya fara bawa Kakarsa labarin Iman kamar yadda ta fada masa. Hajja ta ce “Sokoto, wai akwai nisa da sai kaje ka nemo *yan uwanta su taimaka su rike yarinyar nan, tunda babu iyayen a raye marainiya ce, su riketa tunda sune jininta. Suhaif ya ce “Ai Hajja babu zancen akaita a roke su tunda bata taba zuwa Nigeria ba a can aka haifeta bata san su ba. Kuma ko da ace tasan inda suke, yanzu duniyar nan mutane basa abu sabi Allah komai na ganin ido suke yi, sunga babu ran iyayenta wulakantata za su yi, yanzu idan muka ki riketa yaya za’ayi taje garin? Allah Ya kiyaye ai barin yarinya budurwa kamar wannan hatsari ne sai ta fada hanyar banza a garin ta sami abunda zata dinga cin abinci. Kawai ta zauna anan garin Allah Ya rayata, mu bama wulakanta *yan uwanmu Musulmai, muna son Musulmi kuma ko yaya yake. Hajja ta yi murmushi ta ce “Babangida sarkin zuciya har ranka ya baci yanzu ka farajin haushin danginta kenan? Bi a hankali Babangida kasan yaran yanzu wai so nake a bincika ko auren dole aka yi mata ta gudo kasan yaran nan basa so su fadi gaskiya. Iman ta rushe da kuka ta hau rantse-rantse ita ba auren dole za’ayi mata ba. Ta sake shaida musu bata san *yan uwanta ba, da taje wajensu. Da man kuma ita kadai iyayenta suka haifa don haka yanzu da ta taho ma babu mai nemanta. Suhaif ya ce “Hajja kinji ko, kinji wannan abun tausayi to yanzu tayaya zamu dauki yarinyar nan mu kaita inda bata san kowa ba? Ga Hausarta nan ma bata fita, babu alamar karya a labarin Iman. Iman ki kwantar da hankalinki kinzo gida, kinzo wajen mutanen da suke sonki. Mune danginki, zamu taimake ki insha Allah. Ta dago ta dubi Suhaif ta ce “Nagode madalla. Suhaif ya nisa ya ce “Babu komai Iman yanzu zan tafi in barki anan gidan zaki kwanta, gobe da safe zan dawo, Hajja ki bata tuwo taci don ta kwaso yunwa. Hajja ta ce “Ai dole ne yanzu zan zuba mata tuwo. Iman ta ce “Na gode madalla, sai dai kafin in ci abincin ina son inyi salloli tukunna. Suhaif ya nuna mata buta da bandaki, yayi musu sallama ya tafi.

Reedwan Suraj Isma’il

YARENA ADDININA
CI GABAN LABARIN

Suhaif na isa gida ya iske mahaifinsa Alh. Hayatu suna kofar gida a zaune shida wani bako yazo neman na cefane. Bayan ya gaishe su sai ya sami waje ya zauna a gefensu. Baba yace da Suhaif ya shiga ya aunowa wannan bawan Allah gero kwano uku Suhaif ya je ya auno ya kawo. Mahaifinsa ya hadawa mutumin da kudi dari biyu ya bashi, Mutumin yana ta godiya ya dauka ya tafi. Alh. Hayatu ya dubi Suhaif ya ce “Yaya na ganka duk kayi sanyi kalau kamar marar lafiya? Suhaif yayi murmushi ya ce “Lafiyata kalau Baba, sai dai ina tausayin yadda nan gaba talakawa zasu ci gaba da rayuwa a kasar nan. Yanzu Allah ne kadai Yasan yawan magidantan da suke cikin halin rashi ga iyali da yawa haka suke kwana da yunwa sabo da babu, sun buga ko ina basu samowa iyali komai ba, su kuma ba musakai ba ballantana suyi bara. Taimakon irin wadannan yana lada tunda baza su iya yawon bara ba, su kuwa musakai zasu iya bara a basu.
Alh. Hayat ya girgiza kai don tausayi ya ce “Hakane Suhaif, kasar nan sai addu’a, talaka yana wahala Allah Ya canja mana wannan rayuwa. Suhaif ya ce “Amin Baba, amma kaga da za’a sami iri-irinka, masu hali su dinga taimakawa marasa hali da kan musulmai ya hadu, sun so junansu musulmai, da masu yin bara sun rage bara. Abu ne mai wahala kaga wanda wanda ba Musulmi ba yana bara duk yawancin masu bara Hausawa ne kuma Musulmi kaga bama kishin YARENMU DA ADDINIMU. Amma sai kaga mai kudi ya tara abincin da zai iya ciyar da iyalinsa har tsawon shekaru, makwabcinsa kuwa bashi da ko kwayar shinkafa. Alh. Hayat ya yi murmushi ya ce rufin asiri dai Alhamdulillahi tunda duk shekara ina samun amfanin gona wanda zai isheni in ciyar da iyalina har wata shekarar, amma nima wataran na cefane sai mun harhada da mahaifiyarka da kai kanka dan abinda ka samo a Kano. Daman mutum ba zai ga Allah yayi masa wata baiwa ba sai ya dubi wanda yafi, amma muddin yana duban na sama dashi wanda suka fishi ba zai godewa Allah ba. Yanzu me yasa na dage na hakikance na ce sai kayi digiri? Duk garin nan waye ya taba wani karatu me zurfi kamarka? Ai dan a sami ilimi a garin wanda wataran in Allah Yasa ka zama wani kusa a gwamnati ka tuna da *yan garinku ka zo ka taimakemu. Dan haka abunda nake so da kai shine kaga ka gama karatunka na digiri kuma ka fito da sakamako mai kyau (First class). Bautar kasa ya rage muku kuje kuyi shikenan ka samu aiki ka fara. Duk garin da aka kai ka bautar kasa kaje babu komai dan ina jiyo ka rannan kana hira da dan uwanka Najib kana cewa idan ba Kaduna ba ko Kano aka kai ka babu in da zaka je kai baza kaje Kudu ba. Suhaif yayi murmushi ya ce “Baba ba kudun ne bana so ba, saboda bana so in shiga cikin mutanen da Yarena, addinina ya bambanta da nasu, kaga ko a B.U.K bana zama dasu a daki daya saboda bana sonsu suma basa son Bahaushe Musulmi. Baba kawai ka taya ni da addu’a Allah Yasa a kaini arewa. Alh. Hayatu ya ce “Zan taya ka da addu’a amma fa kai ka fada mun cewar *yan Kudu arewa ake turosu, *yan arewa kuma a kai su kudu sai dai idan mutum yayi sa’a. Ni dai ina baka shawara karka dauki wannan sanadiyyar raunana karatunka kace baza ka je bautar kasa ba dan an tura ka kudu. Ina da kyakkyawan zato a kanka Suhaif ka rike karatunka ka nemi aiki ka taimaki al’ummar garin nan, naga kana son taimako kana kishin Yarenka da Addininka.
Suhaif ya gyara zama ya ce “Baba ai barewa ba zata yi gudu danta yayi rarrafe ba, abunda duk kaga ina yi a wajenka nake koyi kamar son taimakawa mabukata da kishin YARE da ADDINI. Alh, Hayat yayi dariya ya ce “Ai shi yasa ake son iyaye su zamana masu kyakkyawar dabi’a don duk abinda suke yi shi *ya*yansu suke kwaikwaya, Allah yayi maka albarka ya taimakemu baki daya. Suhaif ya ce “Amin Baba, yanzu ma daga gidan Hajja nake naje gaisheta. To ina fitowa kofar gidan sai naga *yar Hajja da kwayenta a kofar gida suna sayar da goro da kwai. Suka nuna min wata yarinya bakuwa ce bata san kowa a garin nan ba tana kuka tana neman taimako bata san inda zata je bama. Da nayi mata tambayoyi sai ta ce ita marainiya ce bata da uwa bata da uba ita kadai kuma suka haifa. Danginta kakaf bata sansu ba Nigeria ma bata taba zuwa ba, a Makka aka haifeta shine aka kamota don bata da takardar zaman kasar ba tare da tasan inda zata je ba. Baba idan kaga yarinyar sai kayi mata kuka abun tausayi, shine na kaita gidan Hajja na ce su bata abinci ta kwana gobe inji shawarar da zaku yanke. Alh. Hayat yai shiru can ya ce “Suhaif waye ya ce maka ana irin wannan gangancin? Da daddaren nan ka tsinci yarinya ka dauke ta ka kaita gidan tsohuwa kace ta kwana, ba ka kaita gidan me gari ba shima idan yaga bazai iya riketa ba a kaita wajen hukuma su riketa. Bakasan duniya ta lalace ba, ka taimaki mutum shi kuma ya cuceka. Yanzu idan ka bibiya ma yarinyar karya take yi. Ko aure aka yi mata bata san mijin ta gudo. Suhaif ya ce “Baba ba haka bane duk wannan tambayoyin Hajja tayi mata nima nayi mata ta rantse ba auren dole aka yi mata ba. Kuma yarinyar kintsattsiyar yarinya ce Baba, ko daga maganarta zaka san yaran Hausa bai ishetaba, Baba Musulma ce tana neman taimako mu taimaketa mana. Yanzu idan muka kyaleta tayi gaba zata iya fadawa wani hannu a cuceta a matsayinta na mace budurwa akwai hatsari. Daga jin Hausarta zaka san ba girman nan ba ce. Alh. Hayat yayi shiru can ya nisa ya ce “Suhaif tunda kace haka na amince kaje ka taho da yarinyar nan gidan yanzu, don ba za’a bar tsohuwa ta kwana da wacce ba’a san asalinta ba, duniyar nan a bar tsoro ce. Ni kuma zan shiga gida in sanarwa Mahaifiyarka da kannanka kafin ku karaso.
Suhaif har zaiyi magana ya ce a bari sai gobe, sai yayi shiru ya amsawa mahaifinsa da “To madalla Allah Ya kara arziki da wadata. Ya tashi ya nufi gidan kakarsa, Babansa kuma ya shiga cikin gida.
Suhaif yayi sallama a gidan Hajja ya tarar da Iman ta gama cin tuwo tana wanke hannu, Hajja kuwa tana kishingide akan shinfidarta. Tana jin muryar Suhaif sai tayi zunbur ta tashi zaune ta ce “Muryar wa nake ji kamar Babangida, daman baka tafi ba ko dawowa kayi baka gama tsokanar daka saba bane? Suhaif yayi dariya yazo ya zauna a kusa da ita ya fara koro mata bayanai kamar yadda suka yi da Babansa a hankali suke maganar ba tare da sun bari Iman taji ba. “Zancen banza yarinya mai hankali da nutsuwa har na fara jin dadin zama da ita shine kake so ka dauke mun ita? Gata wayayyiya tafi *yar Hajja wayo ko talla suka je ba zata ajiye kayan tallar ba ta hau wasa da kawaye kamar yadda *yar Hajja take yimin. Suhaif ya kwashe da dariya ya ce “Ai ba’a yayin dorawa *yan mata talla yanzu Hajja, yayin karatun boko ake yi. Kinga Iman bata yi kama da *yan talla ba da mai ilimi take kama. Anyi-anyi kibar dorawa *yar hajja talla kinki, taci makarantar kwana anan Garki babu nisa kinki yarda a kaita ai lokaci zan samu inzo in sace ta in kaita makarantar dole ta zauna tayi karatu. Takaici ya hana Hajja yin magana saita gyara filo ta kwanta. Suhaif ya juya dubi ya dubi Iman wacce ta takure a gefe kan tabarmar da tayi sallah tana jan carbinta yayi murmushi ya ce “Iman ki dauko kayanki kizo mu tafi can giddanmu su Baba suna so su ganki ku gaisa. “Bata kara ko sakon daya ba ta tashi cikin ladabi gami da amsa masa ta nufi dakin da ta ajiye jakar kayanta ta fito. Suhaif ya mike tsaye yana yiwa Kakarsa sallama, kamar yadda ya sani daman baza ta amsa ba saboda tana jin haushin dauke Iman kuma yayi mata maganar makarantar *yar Hajja wacce da zarar yayi mata in ranta yayi dubu sai ya baci. Iman ma tazo ta durkusa a gaban Hajja tayi mata sallama gami da yin godiya, Hajja ta amsa dakyar. Suhaif fuskarsa cike da murmushi ya shige gaba Iman na biye da shi suka fice. Sun danyi nisa Suhaif ya juya ya kalli Iman ya ce “Af kawo jakar kayan in taya ki rikewa. Ta sunkuyar da kai kasa ta ce “Ka barshi nagode zan rike babu komai. Suhaif ya sake mika hannu ya ce ta bashi ya rike mata. Sannan ta mika masa jakar suka ci gaba da tafiya.
Suna isa gidan a tsakar gida suka iske Baban Suhaif da Babarsa. Bayan sunyi sallama sun amsa musu sai suka shigo Suhaif ya dubi Babansa ya ce “Ga Iman din na taho da ita. Iman tazo ta durkusa a gabansu ta gaishesu suka amsa dukkansu. Mahaifiyar Suhaif ta ce da Iman ta dawo gefen tabarma tazo ta zauna. Iman tayi godiya cikin ladabi ta zo ta zauna a kusa da mahaifiyar Suhaif. Suhaif ma ya sami waje ya zauna. Alh. Hayat yayi gyaran murya ya dubi Iman ya ce “Yarinta ki fada mana gaskiyar dalilin da yasa kika bar garinku, karki boye mana idan kina so ki zauna damu anan baza mu kore ki ba sai mu zauna tare. Kuka ne amsar tambayar da yayi mata, tayi kuka har ta godewa Allah, su duka lallashinta suke yi, dakyar ta tsagaita da kukan. Cikin shesshekar kuka ta ce “Duk abunda na fadawa Suhaif shine gaskiyata ban boye muku ba, ina neman alfarma ku yi min sutura ku taimake ni in zauna daku babu inda na sani, babu wanda na sani. Tausayinta ya rufe su Goggo mahaifiyar Suhaif har hawaye take yi ta ce “Iman yi shiru daina kuka zamu rike ki tamkar *yarmu ta cikinmu. Goggo ta kwallawa Naja’atu da Zubaida kira suka fito daga dakinsu suka zo suka sami waje suka zauna. Alh. Hayat ya shaida musu ga *yar uwa kuma kawa tazo zata zauna dasu, ya shaida musu marainiya ce tana neman taimako don haka kada su wareta su riketa tamkar *yar uwarsu jinin su domin haramun ne cusgunawa maraya. Sun dauki alkawarin cewa zasu zauna da Iman lafiya tamkar *yar uwarsu. Daga karshe Goggo ta ce su dauki jakar kayanta su tafi da ita dakinsu suyi mata shimfida kusa da shimfidarsu. Farin ciki mara misaltuwa ya rufe Iman ta sake durkusawa ta yiwa su Alh. Hayat godiya. Naja’atu ce ta dauki jakar kayan Iman na biye dasu har cikin daki suka yi mata shimfida ta kwanta. Daga karshe Suhaif ya yiwa Mahaifansa sai da safe ya tashi ya nufi shagonsa dake zauren kofar gidan. Bayan Alh. Hayat da Goggo sun taba hira suma suka shiga dakinsu suka kwana.

Mahaifin Suhaif Alh. Hayat dan garin Doko ne haka ma Mahaifiyarsa Raliya. Raliya ita ce matar Alh. Hayat ta farko kuma tun daga kanta bai sake aure ba. Hayatu yana son Raliya sosai don sunyi soyayya mai wahala dakyar iyayensu suka yarda suka daura musu aure, kasancewar Raliya kyakkyawa ce duk garin babu mai kyanta a waccan zamanin, samari da dattijan garin masu kudi da masu sarauta sun fito neman aurenta. Ita kuwa ta ji bata son kowa sai saurayinta Hayatu shi kuma a lokacin maraya ne ba uwa ba uba sai kakansa ne yake rike dashi amma yana da sana’ar yi, da gonar gadonsa makekiya yana nomawa kuma yana da tumakan da yake kiwatawa. Yana da ilimin boko daidai Junior secondry school ya kuma sauke kur’ani yafi a kirga. Ba karamar gwagwarmaya aka sha ba wajen neman auren nan. Kakar Suhaif Hajja ita ta haifi Raliya Mahaifiyarsa. Ta kekashe idanuwanta ta ce ita fa *yar ta ba zata auri dan yaku bayi ba sai mai kudi. Mahaifin Raliya lokacin bai rasu ba shine ya takura Hajja ya canja mata wannan tsattsuaran ra’ayi nata ya ce dole a aurawa Raliya saurayin da take so tunda bai sabawa shari’a ba. Shi musulmi ne kuma yana da sana’ar yi. Dole bada son ran mahaifiyar Raliya ba aka daura musu aure da Hayatu.
Allah Ya albarkace su da *ya*ya mata har uku sai dai kash, da sun fara dan wayo sai su rasu, daga baya ne suka haifi Suhaif. Raliya tayi ta addu’a tayi kuka, tayi fargaba akan tana tsoron ko shima Suhaif mutuwa zaiyi kafin ya girma amma Allah mai komai mai kowa sai Ya raya musu shi har sai da ya shekara shida, sannan akayi masa kanwa mai suna Nadiya ana yaye Nadiya itama ta rasu. Bayan nan ta kara haifar *yan biyu suna rarrafe suka rasu. Hakika wannan rasuwar yara guda shida ba karamin tayar da hankalin Raliya da Hayatu yayi ba suka dukufa da yin addu’a suka rungumi dansu kwaya daya Suhaif, tamkar su hadiyeshi don kauna.
Alh. Hayatu su uku ne a wajen iyayensu akwai Furera itace Babba tana Garki tana aure. Sai Alh. Hayatu sannan kaninsa Usman. Allah ya yiwa Usman arziki don haka yana da katafaren gida a Kano a Unguwar *Yankaba da matarsa Usaina ana kiranta Usai ita *yar Gumel ce suna da *ya*ya uku. Babban dansu sunansa Najib, sai na biyun Sagir sai *yar autarsu Zubaida. Don haka Alh. Hayatu yayi shawarar gara ya dauki dansa kwaya daya jal ya kaishi Kano wajen kaninsa Usman ya hadasu da Najib dansa a saka si a makarantar boko me kyau yadda zaiyi ilimi sosai. Haka kuwa akayi tun daga Nursiry har suka shiga primary tare ajinsu daya Suhaif da Najib kuma daman kamarsu daya tunda iyayensu kamarsu daya kamar an tsaga kara suma kuma kowa da mahaifinsa yayi kama sai dai Suhayf ya dauko farar fatar Mahaifiyarsa da gwarzagwarzan idanuwanta. Suhaif yana firamare aka yi masa kanwa Naja’atu Raliya bata ma dora rai akan Naja’atu ba don taji a jikinta ba rayuwa zata yi ba ita ma. Amma babu wanda yasan gaibu sai Allah Ya raya Naja’atu har ta girma.
Naja’atu Hayatu da Zubaida Usman suma sa’anni ne duk da Naja’atu a garin su Doko tayi karatun firamare sai daga baya ta koma Kano aka hadata da Zubaida a makarantar Sakandire daya wato F.G.C Kano nan suka gama shima Suhaif da Najib F.G.C Azare suka gama suna fita daga sakandire suka wuce Bayero University Kano inda Suhaif ya karanci Enginearing, Najib kuma ya karanci Physic. Sun gama cikin wannan shekarar sakamakonsu ya fito, bautar kasa zasu wuce.
Raliya kuwa su biyu mahaifinsu suka haifa ita da kaninta Nasiru shima ya haifi *ya*yansa da yawa duk suna mutuwa sai Rabi ce kawai tayi saura wato *yar Hajja tana karama mahaifinta ya rasu Hajja ta dauketa shine yanzu take rike da ita.
Naja’at Hayat da Zubaida Usman sun shaku bayan *yan uwantaka ta jini ga kawance, don ko a makaranta ba sa rabuwa har *yan biyu ake kiransu daman kuma kamarsu daya suma sai dai Zubaida ita kuma ta danfi Naja’atu haske. Yanzu ma haka basu fi watanni biyu da kammala karatun sakandiren su ba shine kuma suka dungumo Doko suka zauna har suka shiga makarantar Islamiyya. Kullum da safe daga karfe tara zuwa sha biyun rana, ranar alhamis da juma’a ne kawai basa zuwa makaranta. Sai su zauna a gida suyi ta hira da mahaifiyarsu Raliya wacce suke kira da Goggo tamkar wasu kawayenta. Suyi labari suyi dariya su tafa haka suhaif ma yake zama da mahaifiyarsa yayi ta hira, wasa da dariya, sai dai son girmansa yayi yawa bai cika zama da kannensa Naja’at da Zubaida yayi hira dasu ba. Wani lokaci idan *yan fara’ar basa kusa ko kallansu yayi sai su hau makyarkyata suyi wuf su shige daki. Amma wasu lokutan yakan yi hira dasu, amma yana taka musu birki idan yaji hirar tasu ta fara shiga raini. Yafi yin wasa da *yar Hajja saboda dariya take bashi, bayan kauyancin daya addabi halinta gata rikon Kaka ce, saboda haka tabargazarta tayi yawa.
Fargabar Suhaif da Mahaifansa daya, ita ce a zaman Iman da su Naja’at sun san dole sai Iman ta fuskanci wariyar launin fata don sai sun hade mata kai su biyu sun wareta duk da sa’anni ne su duka ukun. Ba sau daya ba, ba biyu ba Naja’at da Zubaida sun sha yiwa kawayensu halin ko in kula baku damemu ba, kanmu kawai muka sani, bamu san ku ba. Duk kawar data rabesu sukan shareta har ta gaji ta kama gabanta kansu a hade yake su biyu basa son su sami ta uku. Haka kuwa aka yi suka ware Iman suna wani kaf-kaf da junansu ita kuma tana binsu, idan suna hirarsu tazo ta zauna ta tsoma musu baki. Idan aiki suke yi tazo ta sa hannu suyi tare. Suhaif yasa ido sosai yana kula da yanayin zamansu, ya gane abinda ke faruwa. Bai wata-wata ba ya kira Naja’atu da Zubaida dakinsa ya ja musu kunne sosai yayi musu fada, yaci layar muddin basu canja halinsu ba, sunja Iman jikinsu tamkar *yar uwarsu, kawarsu to lallai su guji hukuncin da zai yanke a kansu. Ko tantama basu yi a zuciyarsu ba sunsan zai aikata abunda yace zaiyi musu in har suka kuskure gargadinsa. Suna daurewa suna jan Iman a jikinsu badan sun saba da ita ba, sai don dolen da Yaya Suhaif yayi musu. Ko da suka fara zama da Iman sai suka ji sun fara sonta har cikin zuciyarsu, saboda Iman mutum ce mai tsananin dadin zama. Mai hakuri, mai fara’a tasan me take fada, mai son aiki ga tsananin ladabi da biyayya bayan tsantsar ibada ta rike addininta.

Gason Reedwan da ta ke …..lolx =))
*yaudara* ni na ma mance ko wacece Matawata,,,, na daina sonta ga daidai dani Iman……………reed1
Ehem to gwauraye a huta anan sai kuma gobe da yardar Allah.

Reedwan Suraj Isma’il

INA KWANAN KU?

_____________________ YARENA ADDININA
CI GABAN LABARIN

Ba su Naja’at kadai ba har su Goggo da Babansu nan da nan suka ji Iman ta shiga ransu saboda wadannan kyawawan dabi’unta. Inda tafi burge Babansu shine tunda Iman tazo gidan nan ya huta da bugun kofar dakin su Naja’at da asuba, kafin yazo ya tashesu sai ya tarar Iman ta tashesu tuntuni har sunyi sallah. Haka kuma take zama ta bude alkur’ani tayi ta kwarara karatun alkur’ani da kira’arta da muryarta mai dadi har garin Allah Ya waye. Dole su Naja’at suka fara koyi da ita. Goggo kuwa Iman ta kara shiga ranta saboda rashin son jikinta akwai aiki ko an hanata bata hanuwa. Kafin su ankara ta gama aikin gidan kakaf, har aikin da basa yi kullum Iman ta kirkiro shi kamar cire yana, da wankin bandaki kullum. Su Naja’at masu son jiki sunyi farin ciki da zuwan Iman gidan nan saboda hutawarsu kawai suke yi. Ko Goggo ta korosu ta ce su zo su taya Iman aiki sai ita Iman ta hana su ta ce su bari kawai zata yi. Ko kuma idan tana gudun kada Goggo tayi musu fada sai ta ce su sami waje su zauna su dinga yi mata hira tana aikin. Nan da nan suka ji sun shaku da Iman. Matsalar daya ce wacce take kawo musu illa wajen kara shakuwa da juna ita ce Hausa bata ishi Iman ba. Tana so ta fadi wani abu da yawa da yaren Hausa bata sanshi ba, haka idan suka fada bata cika ganewa ba. Harshenta yafi kama da na Fulani, wani lokacin kaji kamar Larabci ne yafi yawa a bakinta, Hausa dai kadan-kadan take yi. To inda Allah Ya tarfawa wannan matsalar tasu ta bambamcin yare ruwan sanyi shine da ga baya sai Iman ta fuskanci Goggo tanajin fulatanci, itama ashe fulatanci ne yarenta sai suka fara yarawa. Sannan sai suke turanci tsakaninta da Zubaida da Naja’atu da Suhaif. Babansu kuma daya fuskanci tana jin larabci sai shima suke yarawa, duk da bazai iya doguwar hira da ita ba sosai da Larabci bai kware ba. To fa yare ake zubawa a gidan nan kala-kala.
Suhaif yayi-yayi Iman ta saki jiki dashi su saba su dinga hira abu ya faskara taki yarda su saba. Kunya ce da ita sosai, daga gaisuwa babu abinda take kara ce masa sai dai idan yayi mata tambaya ta amsa, ta mike ta shige daki. Saboda ita nema ya fara zama da kannensa yana hira idan yazo ya same su suna hira, amma dif zaiji Iman ta dauke wuta ta daina zuba labari ta hau gyara nayafi tana tura gashi cikin dankwali. Idan ta sunkuyar da kai kasa ba zata kara dagowa ta kalleshi ba, balle suyi hira.
Bayan zuwan Iman da wata guda ta nuna sha’awarta ta shiga makarantar Islamiyyar su Naja’at da Zubaida. Bayan sun shaidawa shugaban makarantar cewa zasu kawo sabuwar daliba ya ce su biya mata kudin wata sai ta fara zuwa. Iman da Zubaida da Naja’at suna tashi da sassafe suyi aikin gida suyi wanka duk da ba kayan makaranta (uniform) suke sawa ba sai su saka manyan hijabansu wani lokacin Iman takan saka katuwar (nikaf) ta rufe fuskarta, su dauki jakar littattafansu su tafi. Ajinsu daya kasancewar nan ne ajin manya wadanda suka yi nisa, sun sauke alkur’ani tuntuni hadda ake koya musu. Da aka gwada Iman don asan wanne aji za’a saka ta sai suka ga Iman harta wuce *yan manyan ajin saboda tayi nisa sosai a hadda. Haka a fannin hadisai da zauransu. Tunda babu aji na sama dana su Naja’at sai suka sakata a ajinsu. Iman bata wasa da karatunta akwai hazaka a gida da makaranta koda yaushe ka ganta da littafinta a hannu tana karantawa idan bata da aiki. Haka take kara koyowa Zubaida da Naja’at inda suka kakare. Goggo ma ba’a barta a baya ba, ta yarda da hankali da nutsuwar Iman don haka take zama da Iman tana koya mata karatun kur’ani.
Yau Alhamis babu makaranta bayan duk sun tashi da asuba sunyi salla, kamar yadda *yan makaranta suka saba sai kowacce ta zauna akan abin sallarta ta bude kur’aninta tana karantawa har saida gari ya washe. Naja’at da Zubaida suka gyara shinfida suka sake kwantawa suka bude wani sabon barcin da basa samu suyi saboda makaranta. Iman ta mike ta fito tsakar gida don ta gaishe da Baba da Goggo sai taji tsit babu kowa da alama dai sun koma barci. Ta juya zata koma dakinta sai taji karar bude kofa. Tana jiyowa sai taga Baba ne ya fito daga daki dauke da wata bakar leda a hannunsa. Ya yi wanka ya yi kwalliya yana ta kamshin turare. Tayi sauri ta durkusa har kasa ta gaisheshi cikin harshen larabci. Ya amsa mata cike da fara’a ya shaida mata yau Kano zaije sai gobe zai dawo idan su Naja’at sun tashi ta fada musu ya wuce. Ta amsa masa da to, sannan tayi mas fatan Allah Ya kiyaye hanya. Ya fita ita kuma ta koma daki ta cire hijab da doguwar riga baka dake jikinta ta daura wani tsohon zaninta wanda ta mayar da shi na aikin gida ta sanya wata yaloluwar riga fara (tea shirt) ta daura dankwali ta fito tsakar gida don fara aikin gida. Tsakar gida kaca-kaca saboda sunsha hirar dare anci gyada ansha rake duk an zubar a tsakar gida. Kwanukan da aka cicci tuwo ne a watse a tsakar gida. Wasu a kicin, wasu kuma an kaisu wajen wanke-wanke kusa da rijiya. Iman sarki tsafta, ta tsaya kawai tana kallon tsakar gidan saboda mamaki da takaicin daya dameta a zuciya tana fadin “Daman haka muka yi da tsakar gidan nan jiya da daddare a duhu ban share ba, yanzu a dattin nan muka kwana? Ga babban abun kunya a haka Baba ya fito yaga tsakar gidan nan, zaice bamu da amfani a gidan. Tama rasa ta ina zata fara, wanke-wanken zata fara ko shara? Sai ta tsayar da shawarar ta hada kayan wanke-wanke ta fara share tsakar gida da kicin. Haka kuwa tayi ta share gidan ral a binka da Siminti ya fita yayi tas ko tsinke bata bari ba ta tattara ta kwashe. Sannan ta dauko kujera da omo bayan ta jawo ruwa a rijiya ta zauna ta fara wanke kwanukan da suka bushe da tuwo miyar kuka.
Suhaif ne ya dawo daga rakiyar mahaifinsa, ya rakashi har bakin titi ya hau mota sannan ya dawo gida. Yana sako kai cikkin gidan saiya ga Iman a zaune tana wanke-wanke kanta a sunkuye a kasa bata ganshi ba, kuma karan kwanukan da take wankewa basu barta taji motsin shigowarsa ba. Ya tabbata Iman bata zaci zai shigo a dai-dai wannan lokacin ba kuma bata zaci yana kallonta ba data ruga daki ta saki hijabinta. Ba zata zauna da damammiyar rigar nan a gabansa ba, saboda bata bude ko wutsiyar gashinta a gaban wani namiji. Iman ta san addininta, tasan darajar ta *ya mace gata da kunya.
Daya tabbatar bata ganshi ba sai bai bari ta ganshi ba yaja da baya a hankali ya koma. Wani dan karamin wundo ya tsaya yana lekenta domin yana kokonto ko ba ita ba ce bama. Saboda shi har yanzu baima kare mata kallo ba balle ya santa sosai, tsakaninsa da ita ya ganta a lullube cikin hijabi ta durkusar da kai ta gaishe shi, wani lokaci ma fuskarta a rufe da nikaf kafarta da safa. Yasan fara ce amma bai dauka tas-tas kamar haka ba. Ya kurawa fuskarta ido yana kallon hancin dodar, ga wani lumshasshen ido mai dauke da far tas da bakar kwayar ido dara-dara. Gashin girarta mau taushi a kwance dodar bakinkirin. Bakinta karami dai dai ita ga lobawar kumatu ko magana take balle tayi murmushi ko dariya. Ga wata *yar siriritar wushirya a tsakiyar fararen hakoranta. Fatar jikinta abar kallo ce farinta mai kyau tas da ita kama daga fuskarta har tafin kafarta jawur da ita. Suhaif ya shiga tunani a zuciyarsa “Anya kuwa wannan ba *yar Larabawa ba ce? Kai dole ruwa biyu ce ko uwarta ko ubanta a sami balarabe. Tana da tsananin kyau wadda ko a mata sai sun tsaya sun kalleta sun kara kallonta balle namiji. Suhaif ya nisa ya ce a zuciyarsa “Lallai dole ki boye wannan kyawun naki saboda mu anan kasar bakake zaki zame mana tamkar wata zinariya abar kallo abar sha’awa wanda kowa yake fafutukar tara kudi ya mallaka domin zinare abun ado ne ga mata, kadara ce ga da namiji shiyasa kowa yake son ya mallakeshi. Allah Ka bani Iman, Allah Ka sani inason Iman tun ranar dana fara ganinta har cikin raina.
Dankwalin kanta ne ya sulmiye zai fadi duk da hannunta da bakin tukunya tayi kokarin sa bayan hannu ta dafe dankwalin don kada ya fadi abun ya ci tura, kasancewar yana da santsi sai ya sulale yayi kasa yayin da idanuwan Suhaif ya dira akan wani lallausan gashi dogo baki wulik. Ya sake murtsike idanuwansa yana kallo. Gashi ne dai Suhaif ba karya idanuwanka suke nuna maka ba. Ta lunkube gashin ta tufke bai san iyakar sa ba amma ko ba’a fada masa ba yasan zai tabo gadon bayanta. Gashin kanta bashi da alaka dana bakar fata daga gani wannan tsatson jajaye ce. Suhaif ya fada a ransa “Dolo Iman ta hada jini da farar fata ko Uwa ko Uba, amma bari mu saba zan binciketa a hankali.
Ko da ta mike tsaye ta dauki kayan data wanke tana mikawa kicin sai Suhaif ya bi kira da dirin jikinta da kallo. Wai!! Allah Yayi halittarsa ance mutum tara yake bai cika goma ba ko ta ina aka ragu wannan? Mai madaidaicin tsawo ce. Ta fi kiba daga kugu daga sama siririya. Kafarta abar kallo ce saboda anyi mata shape mai kyau wanda shi ya taimaka wajen kara dirar jikinta. Tea shirt din dake jikinta bata da kauri don haka ta sake fito da cikar kirjinta. Ya ja dogon numfashi ya shafa kirjinsa ya fada a bayyane “Allah Ka bani wacce nake gani yanzu, kasa ta soni kamar yadda nake sonta. Bayan ta gama kwashe kayan wanke-wanken sai ta zo ta wanke bakin dake hannunta da ruwan kyau da omo. Sannan ta dauki dankwalinta dake kasa a cikin ruwa ta kade ta daure kanta, ta dauko tsintsiya da ruwa da omo ta fara wanke wajen.
Yaji zuciyarsa ta hau dukan uku-uku saboda ya sake sarkewa da son abunda ba lallai bane ya samu sai ya shiga tausayin kansa kamar ya rushe da kuka. Yasa hannayensa biyu a aljihu ya jingina goshinsa a jikin bango ya runtse idanuwansa yana zulumi da takaicin ta yaya ma zai saba da Iman balle ya sami soyayyarta? Yarinyar da ko hada ido sau daya bata yarda su yi, zaman minti uku bata yarda suyi, magana jimla biyar basu taba yi ba. To yaya zaiyi? Yana tambayar zuciyarsa yana tambayar kansa. Motsi ya ji a bayansa ya juyo da sauri, sai yaga Iman ce dauke da tsintsiya a hannunta daya hannun kuma dauke da abun kwashe shara da kanzo a ciki tazo zata zuba a abun zuba sharar dake ajiye a zauren. Saboda tsananin firgita Iman ta zubar da abubuwan dake hannunta. Ya sake zare wadannan manyan idanuwansa ya kalleta sai taji wani abu yarr a cikin jikinta, taji kamar a tsirara take, hankalinta ya tashi yau wanda take tsananin kunya da jin nauyinsa ya ganta a haka. Ta fisgo dankwalin kan ta tana so ta rufe jikinta sai taji ta tuje gashinta ya zubo a fuskarta da bayanta yaraf, ta fara ja da baya. Yana kallonta ya durkusa a hankali ya dauki tsintsiyar da abun kwasar sharar ya fara tattara kanzon data zubar a gabansa. Sai gabanta ya fadi tana gudun ko tayi laifi ta zubar da kanzo yana kwashewa ta hau in ina ta ce “I’m sorry. Ya sakar mata wani lallausan murmushi ya girgiza kai ya ce “ba mishkila, tafi kawai. Abunda ya bashi mamaki sai yaga tayi masa murmushi ta duka ta ce “Thank you ta sunkuyar da kai kasa ta juya ta tafi. Ya ajiye tsintsiya da abun kwasar shara yazo ya jingina ajikin kofa yana kallon yalo-yalon gashin nan nata har sai da ta shige daki sannan ya dawo ya kwashe kanzon daya zube ya shiga dakinsa ya kwanta tamkar bashi da sauran laka a jikinsa. Babu abinda yake hangowa a idanuwansa da zuciyarsa sai Iman.
Tun daga wannan rana Iman ta sake kara jin kunyar Suhaif sai kara gudunsa take, haduwa tayi musu wuya sai wasan *yar buya in dai ba kure musu tayi ba bata yarda ta tsaya su gaisa. Abun yana damun Suhaif babu yadda zaiyi ya hanata wannan hali, kuma duk gidan shi kadai take yiwa haka duk sauran ta saki jiki dasu rai-rai yake jiyo hirarta amma a gabansa sai tayi shiru, a hankali sai ta zame ta gudu daki shi kuwa a zuciyarsa ya saba da ita don tunaninta da sonta ya zame masa abokinsa na yau da kullum, tana zuciyarsa koda yaushe yana tunaninta, son kuma karuwa yake yi.

A yau da yamma Najib ne ya dira a garin Doko daga Kano, ya iske Suhaif a dakinsa yana zaune kan katifarsa ya jingina a jikin filon daya jingina a jikin bango. Tunanin Iman ne yake damunsa ya saka wannan ya cire, ya saka wancan. Sallamar Najib ce ta katse masa tunani ya amsa a sanyaye yayin da hankalinsa gaba daya ya tattara ga kallon mai shigowa. Kasancewar yamma tayi ga babu wuta, dakin ya fara duhu. Suhaif bai gane fuskar mai shigowa ba duk da yaso ya dauki muryar amma yana kokonto anya kuwa Najib ne zai zo da yammar nan. Kuma a yadda suka yi da Najib ba zaizo yau ba, ya ce zai je Bauchi ya dawo tukunna. Najib ya karaso kan katifar da Suhaif ke zaune ya kama masa hannu suka gaisa sannan Suhaif ya gane ko wanene. Cikin mamaki Suhaif ya ce “Malam Najib kaine, kasan kuwa ban ganeka ba? Gaskiya mutumin nan kayi min zuwan bazata. Najib yayi dariya ya sami waje ya zauna a kusa da Suhaif ya ce “Haba dai, ba dai tun shigowata baka gane ni ba. Na dauka zaka gane muryar? Suhaif ya ce “Naso in dau muryar saina ce kai ba kai bane yaushe ka dawo daga Bauchi? Ko dai *yar Bauchin za’a samo mana ne? Ka cika yawan zuwa Bauchi. Su duka suka tuntsire da dariya. Naji ya ce “Kai wallahi ka cika rudu, bana gaya maka bikin Aliyu Bauchi course mate dina muke ba? Kasan ni ai sai Samira Tukur, bayan har yanzu yarinyar nan garani take ban samu shiga ba ina ni ina jijjibo wata kuma? Samira ta cika yanga da yawa. Suhaif ya fada yayin da yake tabe baki.. Najib ya kwashe da dariya ya ce “To meye kake tabe baki? Suhaif ya ce “Ai haka take idan zata yi magana a wani tabe baki a yatsune fuska kafin ta gaishe da mutum shi yasa ban cika rakaka ba wajenta.
Yanzu a label nawa take ne? Najib ya ce “Lebel two ta shiga tana Micro-biology anan B.U.K Old Side.
Najib ya gyara zama ya ce “Daman labari na kawo maka da dimi-dimi, da sai gobe zanzo naga kai gara in zo yau in fesa maka wannan abun farin cikin. Kasan kamar akan kaya nake Allah-Allah nake su turamu bautar kasa nan muje muyi mu dawo mu sami aiki mu ma a dama damu a gwamnati, Babana yana da abokai a kusoshin gwamnati. Last week ma ya kirani falonsa ya dubeni ya ce, “Wai kai da dan uwanka Suhaif yaushe zaku je bautar kasa ku fara aiki har na yiwa abokaina maganarku fa. Na ce “Mun kusa tafiya Baba. Suhaif ya harareshi ya ce “Kai mayen kudi ne wallahi baza ka iya aikin banki ba. Ni har yanzu baka fada mun labarin da ka kawo min da dimi-diminsa ba. Najib ya ce “Ina dawowa daga Bauchi na shiga School na tarar an kafe sunayenmu kowa da garin da zaije bautar kasa. Suhaif ya zabura ya dafe kirji ya ce “Kaga nawa? Najib ya ce “Ba dole ba ai kafin in tsaya in duba nawa naka na fara dubawa an turani Kaduna kai kuma Ogun.
Suhaif ya daka tsalle ya mike tsaye ya ce “Bazai yuwu ba, danme za’a turani kasar inyamurai? Ai nafadawa Baba, indai kudu ne ba inda zani don haka kayi shiru karma ka bari su Baba su sani dan ba zanje ba. Najib ya mike ya nufi kofar fita yana cewa “Kai wallahi dan yawa ne, bari in fadawa Baban da kaina dole ma kaje. Suhaif ya damko Najib ya rike shi, Najib kuma na kokarin fisgewa. Baba ya zo wucewa ya gansu suna kiciniya. Ya daka tsawa ya ce “Meye hakan, kamar wasu *yan yara kuke wasan kunce? Najib ya kyalkyale da dariya ya durkusa ya gaishe da Baba sannan ya gaya masa abunda yake faruwa. Suhaif kuwa sai bata rai yake yana tsaye yana hararar Najib. Baba ya fusata ya sharba masa Carbin dake hannunsa ya rufe shi da fada fafafafa “Sai kaje wallahi. Ko na mutu na bar wasiyya a tura ka. Yaro ka gama karatu bautar kasa ta gagareka wai kai sai arewa, kudun zaka je dole ne ai. Najib ya yiwa Baba sallama ya ce ba kwana zai yi ba.

Leave a Comment