Books Reviews & FAQs

Zaman Iddah Hausa Novel Complete

/16, 8:42 PM] Zahrabukar: *ZAMAN IDDAH*
_(A gidan miji nah)_

*True life story*
_labari ne mai taba zuciya labarine akan zamantakewar aure tsakanin kishiyoyi hakuri juriya tuggu makirci tsantsar nadama halayyar wasu mazajen da ba duka mata Suka sani ba_

_Na_
_Zahrabukar_

_writer of_
Nuwairah
Arwanatu
Karshen duniya
Haihuwar fari
Daga tsintuwa….loarding
And now
Zaman iddah

*EXQUISITE WRITERS FORUM*

*Dedicated to Siddikatulkayr yahya faru farar fuska farar aniya farar zuciya ALLAH ya kare min Ke siddiey beauty kece karfin guiwa ta ko ina kokarin sarewa Kina Karfa fa min guiwa zuciyarki Mai kyauce bakin ciki bai samu muhalli acikinta ba alkairin ALLAH ya baibaye rayuwarki yakawo mana santalelen miji mu hau jirgi muzo Saudi musha biki*

Http://wa.me/+23408038541511

*003*

Akan shi idanunta ya sauka ta ganshi ba yau ta fara gani ba ta sani duk wasu abubuwa da take nema ta rasa ɓatansu na da alaƙa da mijin nata,
sai dai ta share tana kuma mishi kyakkyawar fatan canja hali ko ba daɗe ko ba jima,
diriri cewa yayi ya fara sosa ƙeya to sai ta basar dashi ta jefa mishi sassanyan murmushi sai yaji guiwar shi ta sace
wace iriyar mace ce ita? anya yana yi wa kanshi da ita adalci?
ta katse mishi tunanin da cewa
Ango kasha ƙamshi wannan wanka haka kamar yau ne ?”
Yaɗan ɓata rai ya langaɓe kai yana cewa
“kin ganki? zaki fara ko? ni ba wani ango anan wallahi wankan nan duk naki ne gimbiyar mata”
Tasan ya faɗa ne kawai amma duk da haka kalaman shi sun faranta mata rai matuƙa ta ƙarasa gaban miror tajawo stool ta xauna tana murmushi ta fuskance shi tace “Dan ALLAH fa Hayateehyh kace yau duka rana tace to ina godiya amma nima na barwa ƙanwata ga saƙon ka kai mata in ka fita ina gaisheta” ta miƙa mishi box ɗin nan wani sashi na zuciyarta na gargaɗinta wani kuma na ingiza ta
yasaka hannu ya karɓa yana janyota jikinshi ya fara sakar mata hot kises ta ko’ina haɗe da sakin wani marayan kuka mai nuna tsantsar farinciki
ita ya dace ace tayi kukan na rabata da abu mafi muhimmanci da ya rage mata a rayuwa amma ita murmushi take tana tapping bayanshi alamun rarrashi
yace “wace irin mutum ce ke? kullum zuciyarki daɗa sabunta ta ake da abubuwa masu yawa karamcinki kulum ƙaruwa yake dame xan sa ka miki ne nikam NOORY?
ta ɗago shi ta saka idanunta cikin nashi rauninta ya bayyana ta share wasu siraran hawaye da suka saci hanya suka fito mata tace “Abu biyu Hayatieyh ka min su a duniyar nan ka tabbatar min dabaka cikin butulan maza”
da sauri yace “meye?ki gaggauta faɗa insha ALLAHU zaki sameni cikin maza adilai”
ta janye jikinta daga nashi tace “kaje idan kadawo zamu yi magana”
ta faɗa hakan ne dan ta samu ya fice ko zata samu bugun dz zuciyar ta keyi ya daidaita
zai kuma magana ta langaɓe kai ta nuna mishi ƙofa bai musa ba ua cusa box ɗin aljihu ya manna mata kiss ya fice da sauri
binshi tayi ta datse ɗakin tun anan ta sulale bakin ƙofar ta fashe dz wani irin kuka mai cin rai
lokuta da dama takan rasa wai shin ita kam wace irin cusashhiyar ƙwanya gareta? meyasa har yanzun ta kasa daidaita rayuwarta tasan me ke mata ciwo a rayuwa?
Naseer dai Naseer dai ko da yaushe shine raunin ta? again dai yau ya ƙarasa rabata da sauran abinda ya rage mata mai muhimmaci a rayuwarta!

cike da farinciki ranshi fess ya fito harabar gidan ua jujjuya ya kalli ko’ina na gidan ya jinjina kai haɗe da salute wa kanshi yake cewa “next target ɗina gidan nan ne duk da dama nasan tuni ya riga ya zama mallaki na takardun kaɗai suka rage da sign su shigo hannuna ,ki shirya Niriiyyah watan kukan ki ya kusa tsayawa bazan huta ba sai naga kin ta gayyara a rayuwa sai na ganki akan bola kina tsince tsince suturar sakawa ta gagareki abinci da wajen kwana sun gagareki a sannan zan fara sabuwar rayuwa cike da farinciki da annashuwa nida galleliyar amarya ta Bintuuuuu”ya ƙarasa faɗar sunan cike da shauƙi bege da tsananin ƙauna ya faɗa motar da ita kanta mallakin Nuriyya ce,
yaja ya fice daga gidan bayan mai gadi ya buɗe mishi get ɗin,

**********************
ta daɗe agun gurfane tana dukan cikin matuƙar galabaita ga ciwo ga yunwa ta mance when last da tasaka wani abu cikinta sabida izayar wannan matar
ita kam hakima hamshaƙiya tana ciki tana ji ta kuma san ko waye ke bugun ƙofar shiyasa tai shiru wannan ma salo ne na azabtarwa so take sai tazo akan guiwar ta tana tuma a ƙasa tana roƙonta akan ta taimaka ta kaita acire cikin tasani yunwa ma kaɗai ta isa ta saka ta miƙa wuya,
ta riga ta toshe duk wata kafa da wani xai san meke faruwa a gidan duk da ma ba wai tana tsoron wani ko wata bane a a tafiso case ɗin wannan ya zama silent case daga ita sai ita ta kashe ta ta binne a gidan babu wanda yasani,
ko zata samu cikar burinta da gaggawa na mallakar gidan da dukiyar gidan da maigidan
[4/16, 8:42 PM] Zahrabukar: *ZAMAN IDDAH*
_(A gidan miji nah)_

*True life story*
_labari ne mai taba zuciya labarine akan zamantakewar aure tsakanin kishiyoyi hakuri juriya tuggu makirci tsantsar nadama halayyar wasu mazajen da ba duka mata Suka sani ba_

_Na_
_Zahrabukar_

_writer of_
Nuwairah
Arwanatu
Karshen duniya
Haihuwar fari
Daga tsintuwa….loarding
And now
Zaman iddah

*EXQUISITE WRITERS FORUM*

*Dedicated to Siddikatulkayr yahya faru farar fuska farar aniya farar zuciya ALLAH ya kare min Ke siddiey beauty kece karfin guiwa ta ko ina kokarin sarewa Kina Karfa fa min guiwa zuciyarki Mai kyauce bakin ciki bai samu muhalli acikinta ba alkairin ALLAH ya baibaye rayuwarki yakawo mana santalelen miji mu hau jirgi muzo Saudi musha biki*

Http://wa.me/+23408038541511

 

*001* _Raunin zuciya_

A kasalance take dubañ shi cike da matuk’ar raunin zuciya bakin ciki da kallon tsantsar butulci irin na wasu mazan da ba duk lokaci take kallonshi dashi ba take duban shi ta share hawayen da ke ta fitar burgu daga idanunta
Ta janye raunannun
idanunta ta mik’e da niyyar ficewa daga dakin yayi saurin rikota,
Ya langabe Kai ya Zuba Maya fitinannun idanunshi a hankali ya lumshe su ya dora kanshi a kafadar ta yafara sakar mata numfashi Mai dumi wanda ya tilasta mata sakin ajiyar zuciya yana d’an yawo da hannunshi a sassan jikinta yace “haba mana qurratul ayn wannan ba halinki bane zuciyar ki mai kyauce ce uhmhm? Dan kwarin guiwata na tunkare ki da tabbacin samun goyon bayanki karki bani kunya mana”
Ya dan saurara yana kuma kashe mata jiki ya kara rungumo ta jikinshi sai sakin ajiyar zuciya take ba ta dai ce komai ba
Ya dan girgiza ta kadan yaana cewa “talk mana sweet heart kice min wani abu bana son shirun nan naki ke ko zagina ne kiyi sai inji sanyi a raina ko love Of ma life”
Dagaske ne bazata iya magana ba haka take ta gwammaci ta dauke duk nauyin wata jarabta da ta bude baki tace wani Abu wata irin strong heart gare ta abubuwa da yawa bata iya tankawa sai dai ta danne abin a zuciyar ta
Shi kanshi ya sani bazata ce komin ba
Wani salo ne dai na daban
Daga cikin ire iren salon da ya saba amfani dasu ya cimma burin shi a kanta’
Kirrr karar kiran waya ya shigo wayar shi ya D’an basar aka kuma kira ya share wani kiran na kuma shigowa a hankali ta zame jikinta daga nashi ta nufi kofa ta fice hannunta dafe da saitin zuciyar ta,
Tasani ko bai fada ba *BINTU* ce yarinyar da yake kan neman auren ta
Tana ficewa yayi saurin tashi ya rufe kofar yana d’an tattaka rawa ya d’aga kiran fuska cike da farin ciki da nishadi
Suka ci gaba da sheka soyayyah, yana kuma bata tabbacin a yau din nan zai cika mata burin ta yasan Nuriyyah yasan Wacece baya jin ko ita tasan kanta kamar yanda ya Santa

Kai tsaye dakin ta ta nufa hawaye wasu na korar wasu zuciyar ta na wani irin ciwo ta bude safe din ta ta dauko wani hadadden box mai kyalkyali ta rungume shi a kirjinta so take taji ta yi kuka mai sauti amma sautin kukan yaki fitowa so take ta samu abokin shawara abokin fadawa kuka damuwa da farin ciki bata da ko daya duk Naśeer ya rabata dasu akan wani dalili nashi
A hankali ta bude akwatin wani irin haske mai kashe idanu ya bayyana ta saka hannu ta fiddo wata kwankwatsetsiyar sark’a dakekiya ta ajje ta dauko yan kunnen da abin hannun da yan kunnen tana kallon su
Shawara take nema bata da abokin shawara sai zuciyar ta idan zata nemi shawaran zuciyarta kuma tasan amsar itace YES
Kullum zuciyar ta bata bata amsar NO dangane da lamarin Naseer
Tsawon shekaru goma kullum tana karfafa wa kanta guiwa akan komae ta sadaukarwa Naseer ya cancanta ne!
Ta tattara su ta rungume tana tuno asalin ma mallakin sarkar da muhimmancin ta a rayuwar ta amma sanda ya dace ta tallafa mata Naseer ya katantane ya Hana,
Da sauri ta kawar da tunanin ta Mai da sarkar da sauran abubuwan cikin akwatin ta ajje kan mirror idan ya shigo zata bashi tasan ba karamin farinciki zaiyi ba ita kuma farincikin shi yafiye mata komai a duniyar nan

 

**********************
Da karfi ta fizgota cike da masifa ta wurgar da ita kasa kanta ya bugu da tiles din kitchen take ta fasa wani marayan kuka tana girgiza mata Kai jikinta sai kyarma yake
Tsabar tsoron wannan matar da take bakinta har kumfa yake tsabar bala’i take cewa” ke din me? Banza a banza har kin isa ? Wallahi ko ubanki dake kabari ya fasa kasa yafito yayi kad’an ubanwa yace kika yarda kika dauki ciki? A gidana? Hmm babu tsarin yarana zasuyi yan ubanci da wasu a gidan ubansu wallahi ke ga kafaffiya ki zubar kin ki zanga ta gidan uwar wa zaki haife shi ‘
Cike da rashin imani take saka k’afa ta dirka mata akan cikin
Ta fasa wata gigitacciyar Kara ta fara mulmula a kasa tana wata irin gumza ita kam sai wani huci take kamar wata kububuwa,
Ta saka hannu ta matse cikin tana zazzaro idanu cike da mugunta 😰😥😰😥

*Ki Fara bi tun yanzun in zaki bi IN baki da raayin karantawa yanzun ki tara kada kice zaki bini PC inbaki daga farko tom*

_littafin karshen duniya complete doc ya kammala Mai bukata ki tuntube ni ta number na #500 kacal insha Allah bazaki nadamar siya ba_

Zahratieyh kawar oum nurain taku🤣😂🤣😅🤣
[4/16, 8:42 PM] Zahrabukar: *ZAMAN IDDAH*
_(A gidan miji nah)_

*True life story*
_labari ne mai taba zuciya labarine akan zamantakewar aure tsakanin kishiyoyi hakuri juriya tuggu makirci tsantsar nadama halayyar wasu mazajen da ba duka mata Suka sani ba_

_Na_
_Zahrabukar_

_writer of_
Nuwairah
Arwanatu
Karshen duniya
Haihuwar fari
Daga tsintuwa….loarding
And now
Zaman iddah

*EXQUISITE WRITERS FORUM*

*Dedicated to Siddikatulkayr yahya faru farar fuska farar aniya farar zuciya ALLAH ya kare min Ke siddiey beauty kece karfin guiwa ta ko ina kokarin sarewa Kina Karfa fa min guiwa zuciyarki Mai kyauce bakin ciki bai samu muhalli acikinta ba alkairin ALLAH ya baibaye rayuwarki yakawo mana santalelen miji mu hau jirgi muzo Saudi musha biki*

Http://wa.me/+23408038541511

*004*

Sai da ta bushi iska ta mula tasha Ac sannan tazo ta buɗe ƙofar zuwa lokacin Hunaifa ta sare ko hannun bata iya ɗaga wa ta riga ta sare da rayuwar tasan ƙila kam ita ta ta taƙare ga azabar ciwon mara ga yunwa sannan taji ƙaran buɗe ƙofa
cike da isa ta xuro kanta tana tattaɓe baki ita Hunaifa ko idon ta kasa buɗewa tsabar galabaita cije baki Haj Kareema tayi a ganin ta har ta samu damar yin bacci a guje ta koma cikin falon fridge ta buɗe ta ɗauko ruwa mai sanyi ta dawo batayi wata wata ba ta buɗe robar ruwan ta sheƙa mata tana ta girgiza jiki shiru Hunaifa bata motsa ba ba dan sanyin ruwan bai ratsa ta ba a a sai dan rashin kuzari ta ciji yatsa tana girgiza kai tace “ke ƙarya kike wallahi na haɗu da waɗanda suka fiki taurin rai ma kuma naci galaba a kasan su ke ɗin nan wallahi ƙarya kike”
Hunaifa nason yin magana amma maganar bata fita
ciki Karima ta koma da sauri ta ɗauko wayarta ta dawo inda hunaifar ke kwance tayi dialing wasu numbers ta kara a kunne wayar bata daɗe tana ring ba aka ɗaga daga can ɓangaren,
kuka ta fashe dashi mai ƙarfi tana magana tana kukan har shaƙewa take tsabar iya makirci cewa take “ta gudu Alh wallahi yarinyar nan ta gudu kawai dan na hanata zubar da cikin jikinta tana ƙoƙarin shan maganin na rutsa ta wallahi sai da ta yanke ni a hannu da na matsa mata cewa tayi idan na kuma yunƙurin hanata sai ta cinna wa gidan wuta dama ta tsaneka haka nan aka aura mata kai kuma itace ajalinmu harsu Nadra” taja majina ta ɗan saurara jin me yake cewa a tsawace yace “what? hunaifar ? to ya akai ta fice? ko ta zubar da cikin?”
tace “wallahi alh a guje na rufeta a kitchen ɗin amma yarinyar nan ta fice ta ƙofar baya bayan tabar min saƙon mu jira muga me zai faru nikam am scared alh kadawo dan ALLAH kada yarinyar nan tayi nasarar xubar da cikin nan a nemo ta aji me takeson a mata?”
a hasale ya katse ta da cewa “ƙarya ne wallahi taje duk inda zata nafi ƙarfin ta min barazana yau ɗin nan zan tura mata saƙon saki da gargaɗin duk ta saki wani abu ya samu cikina wallahi sai na gigita kaf familynsu”ƙit ya kashe wayar wani wawan tsalle Karima ta daka ta fara rawa jikin Hunaifa tuni ya fara rawa duk abinda suka tattauna komai ya shiga kunnenta tunda a handsfree ta saka wayar wasu zafafan hawaye suka xubo mata ƙiri ƙiri tana ji an ƙulle ta da muguwar sarƙa ita kam ta sadakar ta barwa ALLAH komai tasan yana ji kuma yana gani
Karima irin mazga mazgan matan nan ne ga tsawo ga ƙwari ɗaf ta saka hannu ta ɗauki Hunaifat da ta kasance siririya jiki ba wani auki ga ciwo ya galabaitar da ita tana ji bata da ikon hanawa
Direct lambun gidan ta nufa inda a ido lambu ne amma agun Karima ɓoyayyiyar maƙabarta ce wacce ita kaɗai tasan da zamanta a gidan a ƙalla akwai gawarwaki kusan shida na jarirai da take binnewa da an haifesu har yau kuma babu wanda yasani a wannan fagen bata gayyar kowa sabida sirri wannan sirrin tane acewarta
Akwai inda take ɓoye kayan aikin ta
ta riga ta gama da hunaifa tasan tunda tace ta gudu hankula duk zasu koma ne akan nemanta neman da har ƙasa ta naɗe baza a ganta ba’
A tsayen ta sako ta ƙasa sai da bayan ta ya amsa ta ƙarasa wani guri ƙasar gun a daddale babu mai cewa in an tona za a samu wani abu ta duƙa ta fara haƙa ƙasar haƙa tayi mai zurfi ta fiddo kayan aikinta’
hada wata siririyar wuƙa da aka lulluɓe da jan ƙyalle, da sauri ta kwashi kayan ta nufi inda ta yada hunaifa idanunta nata zubar hawayen nadamar auren alh ma’aruf kwaɗayin iyayenta ya kawota mahalaka bata ankare ba taji an caka mata wani abu gefen ciki jini yayi tsartuwa Karima kamar ba mace ba babu imani ko rauni a zuciyarta ta fara magana tana lasar jinin jikin wuƙar tace “kinga kuskurenki na biyu na farko kinyi kuskuren auren miji na na biyun shine yaja miki tafiya barzahu bana barin bashi a nan ɗin nan akwai gawarwakin jinjirai shida dasuka rantse sai sunxo duniya to sun zo ɗin amma basu mori shigowa cikin ta ba tunda a ranar suka koma naso ki bari a zubar da cikin jikin ki kinƙi da kin bari an zubar da kin rayu to kinsa taurin kai zan aika ki lahira bayan nagama ɓata miki suna abu ɗaya da nakeso ki sani har yau alh bai da ɗa ko ɗaya a duniya ni bana haihuwa amma su nadra ƴaƴa na ne kuma dole su amsa sunan ƴaƴan alh duk da ba ƴaƴan shi bane ke ni kaina banda tabbacin ina iyayensu suke ta saka wuƙar ta laso jinin ta lashe tace wannan sirri ne sai mun haɗu a ƙiyama”
bata jira komai ba ta caka wuƙar a ƙirjin hunaifa bayan ta danne mata baki,

*ki fara bi in zaki fara ko ki tara karmu nisa kicemin daga farko tom*
[4/16, 8:42 PM] Zahrabukar: *ZAMAN IDDAH*
_(A gidan miji nah)_

*True life story*
_labari ne mai taba zuciya labarine akan zamantakewar aure tsakanin kishiyoyi hakuri juriya tuggu makirci tsantsar nadama halayyar wasu mazajen da ba duka mata Suka sani ba_

_Na_
_Zahrabukar_

_writer of_
Nuwairah
Arwanatu
Karshen duniya
Haihuwar fari
Daga tsintuwa….loarding
And now
Zaman iddah

*EXQUISITE WRITERS FORUM*

*Dedicated to Siddikatulkayr yahya faru farar fuska farar aniya farar zuciya ALLAH ya kare min Ke siddiey beauty kece karfin guiwa ta ko ina kokarin sarewa Kina Karfa fa min guiwa zuciyarki Mai kyauce bakin ciki bai samu muhalli acikinta ba alkairin ALLAH ya baibaye rayuwarki yakawo mana santalelen miji mu hau jirgi muzo Saudi musha biki*

Http://wa.me/+23408038541511

*002*

Bata ƙyale yarinyar nan ba sai da taga bata numfashi ta tashi tsaye tana ƙyaƙyata dariya cike da mugunta ranta fess ta nufi fridge ta buɗe ta dauko robar ruwa har sun fara dutsi ta bude ta kwar a mata wata iriyar ajiyar zuciya ta sauke mai haɗe da sheshsheka idanunta a rufe ta kasa buɗe su sabida nauyin da suka mata wata iriyar azaba take ji a dukkan sassan jikinta nadama take danasani take na kuskuren shigowa gidan wannan ƙeƙasashshiyar matar marar imani, ba tun yau ba ta mata kashedi yafi dubu akan kuskuren da zatayi idan ta aurar mata miji tana ganin wasa take ashe ita ke wasa da rayuwar ta tsawon wata uku da tayi agidan me ta ƙaras?
tunaninta ne ya katse sanda taji an jata ƙiiiii kamar wasu kayan wanki
Bata tsaya ko’ina da ita ba sai da ta kaita bakin ƙofar shigowa falon ta wurgar bayan ta ya bugu da ƙasan wurin ta rintse ido tana kiran sunan ALLAH
sai huci take tana haki tana maseefa
tace ” ki kwana anan ki wuni anan daga yau wallahi kinji na rantse na haramta miki shigon min falo bare kice zaki shiga wani so called ɗakin ki ai wanda baiji bari ba zai ji hoho zan ga uban da ya ɗaure miki ƙugu tsaye nake ƙyam a gida na ke ɗin nan baki isa ki rushe min record ba wallahi kiyi shawara da zuciyarki kwanaki uku ya rage Alh ya dawo kina da damar zubda cikin kafin ya shigo ƙasar nan ki samu ƴenci kema in ba haka ba wallahi sai kin gwammaci mutuwar ki akan rayuwar da zakiyi”
Fuu ta kwashi ƙafafun ta tayi ciki ta bugo ƙofar hada saka key,
sai kokawa take da numfashin ta da kuma zuciyarta anya? anya ba zata xubar ba? bala’in yayi yawa duk ixayar da matar nan ke mata bata iya ɗaga ido ta kalleta ko ta buɗi baki ta faɗa wa wani halin da take ciki ta saka hannu ta shafo cikinta wasu hawaye masu ɗumi na zubo mata wani irin so ƙauna da begen abinda ke cikinta ya mamaye xuciyarta anya idan ta zubar dashi ta mishi adalci? wata zuciyar ta kawar mata da wannan tunanin ta jefo mata na ƙunci da bala’in da xata shiga a hannun kishiyarta ,
a hankali ta tashi zaune tana dafe bayanta
zuciyarta na rarrabuwa da neman mafita da maslaha ta fara buga ƙofar falon

 

*************************
Kusan awa ɗaya ya kwashe suna xubar da ruwan luv shi da Bintu ranshi fess yarinyar tayi ne ba ya jin ko ranshi ta nema zai hana ta tasan sirrin maza ƙwarai ta iya tafiya da xuciyar wanda ya faɗa tarkon ta
jin yarinyar yake ta cika ko’ina a zuciyar shi cike da farinciki bayan sunyi sallama kamar kar su rabu a wayar ya nufi toilet ya ɗan watsa ruwa
Shaf shaf yafito da sauri sauri ya kintsa kasancewar shi mutum mai sassanyan kyau tsaf ya fitoo cikin dark blue ɗin shaddar data amsa kyakkyawar fatar jikin shi da bata cika haske ba ya kafa hula data dace da zaren da aka ƙawata ɗinkin shaddar dashi haka ma takalmin yabi jikinshi da turaruka masu sanyin ƙamshi ya dubi kanshi a madubi cike da ƙaunar kai da alfahri yana ta sakin murmushi
ya fito ya nufi ɗakin Nuriyyah yana sauya yanayin fuskar shi zuwa tausayi da neman agaji! a hankali ya tura ƙofar ya shiga ɗakin
bata ciki da alamu tana banɗaki ya fara wurwurga idanu idanunshi ya sauka akan miror ya hango wannan akwatin da sauri ya haɗe wani daddaɗan miyau wani sanyi na kwaranya a zuciyar shi
ya hango jakarta saman bedside drower da sauri ya ƙarasa ya zuge ziff ɗin ƴen canji yake so da zai zuba mai a mota bai ko tsaya ƙirgawa ba ya ɗebo kuɗin ya cusa aljihu daidai ta fito banɗakin ,

*ki fara bi tun yanzun in zaki fara ƙawata idan baki da raayin karantawa yanzun ki tara abinki kada muyi nisa kice kina nema daga farko*

_ƘARSHEN DUNIYA YA KAMMALA IN KINA BUƘATAR COMPLETE DOC #500 KACAL NA TABBATA BAXAKI NADAMAR SIYA BA_
[4/16, 8:42 PM] Zahrabukar: *ZAMAN IDDAH*
_(A gidan miji nah)_

*True life story*
_labari ne mai taba zuciya labarine akan zamantakewar aure tsakanin kishiyoyi hakuri juriya tuggu makirci tsantsar nadama halayyar wasu mazajen da ba duka mata Suka sani ba_

Leave a Comment