๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ
*ZANBA CIKIN AMINCI*
๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ
ECRITE:
_PAR_
*QUEEN ZEEFAT*
Yar
Mutan
Niger
Wattpad@nazhabibou
๐ซโจ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*๐
_(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)_๐ค
โ *[ T.M.N.A]* โ ๐๐๏ธ
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_BISMILAHIR RAHAMANIR
Page 1
Dandanzon matasa ne maza da mata ke fitowa daga cikin wata babba kofa wada a samata aka rubuta *LYCEE TECHNIQUE DAN KASAWA DE MARADI* hakan ya nuna cewa makarantar boko ce gashi kuma kowane matashi da jakar makarantar sa a baya wasu kuma a hannu kowa sai kama gaban shi yake sanadi tashi da akayi daga makarantar, wata yarinya ce ke tafowa tana nufo kofar makarantar hannun rike da wata farar takarda da jikar makarantar a dayan hannu sanye take cikin dongon hijabin ta har kasa da nikaf a fuskar wada ko eyes inta ba’a gani don fuska rufe take gaba daya ga safa da take sanye da ita ta hannu da ta kafa duka ilahirin jikinta rufe yake babu abinda ake gani, tana tafiyar ta mai kama da hawainiya cikin kwonciyar hakali da nutsuwa kamar mejin tausayin kasa a haka har ta kawo baki kofar makarantar tayi wajan wani shago dake gefan makarantar mai shagon dake zaune daga daya bangaren shagon yana ganin ta ya taso yace malama mikike bukata banji mitace ba sai gani nayi ta mika masa takarda hanuta ya karba yayi cikin shagon da takadar a hannu sa ba’a fi minti biyu ba sai gashi ya fito daga shagon ya mika mata takarda biyu a maimakon guda da tabasa karba tayi ta bude jakar makarantar ta fido kudi ta mika masa ta juya takoma cikin makarantar da takardun a hannu ta daidai wani office ta tsaya ta kwonkwasa sai ga wani datijo ya fito wanda baza ya fuce 50 years tadan rusuna ta mika masa daya takardar ta juya da dayar wajan parking space dake cikin makarantar ta nufa tsayawa tayi daidai wata hadadiyar benz kirar mercendy ta bude jakar ta makaranta ta fito da makulin mota budewa tayi tashiga ta tayar da motar tare da barin cikin makarantar a lokacin da daliban dake cikin makarantar basu huce mutun shida sabida kowa ya kama gabansa.
Driving tayi natsawon minti 20 kamin take kawowa wata kayataciyar anguwa daga ganin anguwa ba me yawon mutane bace sabida yanayin ta ya nuna hakan ga wani hadadan kuma babban filin ball daya ya karama anguwar kyau macha allah
Wajan wasu mayan tsararu kuma kayatacin gidaje guda biyu dake irin daya naga ta nufa komin su gidajan irin dayane sedai guda yafi guda girma shima ba sosai ba wanda ya fi girma a cikin gidajen ta nufa tana dana hon mai gadi ya wangale mata tagamemiyar porte (get) in gidan ta tura hancin motar ta a ciki, tsaruwa haduwa kayatuwa kai yayine gidan karsha ne wajan haduwa babu abinda ba na rayuwa a gidan parking space kadai ma na gidan abin kalon to baran tanama farfajiyar gidan
Parking in motar tayi a parking space dake cike da motoci sun kai kala 10 ta fito daga cikin motar ta kule tareda fitowa daga parking space in tayi hanyar shiga gidan, gidan dauke yake da sashe guda uku daya a gefen hagon gudan a kefan dama se dayan natsakiya kuma shine bangare mafi girma da ke cikin gidan hanyar babban bangaren tanufa tare da murda wata daleliyar kofar da zata sadaka da falon gidan shiga tayi hade da salama a bakin ta wada in ba kusa kake da itaba ba zaka taba jin abinda ta fada wooow nace tare da furta allah sarkin dadi inji barawon takanda lokacin dana tsintsi kaina a wani katarfaran falon da ya tsaru iya tsaruwa komi na falon brown and milk color ne, falon dauke yake da bedroom guda biyar da cuisine (kitchen) guda se set uku na kayatatun kujeru sabida girman falon da dan madaidaicin table central (center table)milk color shi ba babba ba shiba karami ba wanda ya kawata tsakiyar kujerun se TV stone dake jikin bangon falon akasa tare da wata tangamemiyar TV dake manne a bango babu ce kadai ha babu a ciki ga wani kayatacen kamshi dake tashi a falon mara misali
sabida shagalta danayi wajan kalon tsaruwar falon har na manta da rahoto nake dauko maku falon ne ya tsaru irin tsaruwar da ban taba gani irinta ba sai a TV
Babu kowa a falon hakan yasa ta nufi kofar daya daga cikin bedroom din dake falon ta mudar kofar tashiga da kafar dama hade da yar siririyar salama a bakinta wani ni’imtacan kamshi mara misiltuwa ya daki hancina nace macha allah, babu wani tarkace a ciki amma ya hadu daga bed da wardrobe sai dressing miror da kujera babba guda dake gefe sai douche interne (bathroom) da abin ajiyar jaka kusa da armoir (wardrobe ) da abin rataye kaya da ke manne da bangon dakin sai agogo itama manne a can saman bango babu abinda babu a cikin na more rayuwa kana ganin yanayi dakin zaka gane na yan mata ne daki dai macha allah
Tana karasa shiga dakin taje dan gaba da kofar dakin tacire takalmin dake kafarta ta juya tayi bakin gadon dake cikin dakin ta zauna ta cire nikaf da hijabin da ke jikin tare da cire safar hannu ta da ta kafa ta mike tare da nufar wardrobe ta bude ta ciro serviette (tawel) juyowa tayi da niyar nufar hayar toillet take nan takardata da biro dake hannu na suka subice min la’illaha illa anta subhanaka inni kuntum bina zalim ku kuke ganimu bamu muke ganin kuba na furta tare dajan baya da karfi sanadiyar tozalin da nayi da kyakyawar fuskarta juyawa tayi tare da shigewarta toillet da sauri nayi wajan peper da biro na dan na dan labarta ma masu karatu haduwar yarinyar da kyau dinta bai musultuwa banta ganin kyau irin nataba ko acikin larabawa da turawa
Yarinya yace da bazata fuce 18 years ba dogowa amma ba can ba tsayin ta daidai da ita siririya ce amma ba sosai ba ita ba fara ba kuma ba za’a sanyata a layin bakake ba yarinyar cafรฉ au lait ce (shacolate in milk color) irin black americain din nan ce idan kanganta a kusa da wani black americain din ita zaka iya cewa tanada haske amma ba sosai ba da kaire mutun zai tantance kalar fatar ta ma saidai a kimanta gashi girar ta ya kwanta luf luf sai sheki yake da daradaran idanun ta farare tas dasu se bakin da ke cikin idanu ita nata brown ne mai kamar baki da zarazaran gashi idanuta tsaf dasu sai dogon hancin ta har baka da dan karamin bakinta da ya karama fusakar kyau da sheki allah ya mata kyau na gasken gaske baza taba iya musulta kyau irin nata sedai a kiman tashi shima sabida du yanda zaku misilta ta tafi da hakanan
Turo kofar toillet din tayi ta fito daure da tawel da ya sauko mata har ga gwiwa sanan da daya kuma a saman kanta ga ma zauna da allah ya azirtata dasu kamar ba na karamar yarinyar yar shekara 18 ba wajan dressing mirror tanufa ta ja dan taburan ta zauna mika hannu tayi saman dressing mirror din ta dauko wasu hadadun turare guda uku irin na shafawa ajiki ta shafe jikinta gaba daya dake da damshin ruwa kafin ruwan su tsane a jikin ta janye tawel din dake saman kanta saiga gashi ta ya bayana wanda yake dogon baki kirin dashi daga zaune da take gashi yakai har kusa da ma zaunanta da kadan bai ida tabo suba ta dauki abin busar da gashi tana busar dashi da ya bushe ta dauki man kai mai kyau ta shafa masa tare da daukar mashaci ta shace gashin take gashi ya gara kyau da sheki ta dauki shoushou (ribon) zatasa saka ta kasa sabida yawa da tsayin gashi baza iya daure shiba tayi tayi ta kasa a haka ta hakura ta barshi zube a bayan ta tashi tayi ta nufi wardrobe ta fido wata hadadiyar doguwa riga mara nauhi baka mai ratsin ja tasaka tare da dauko hijab da darduma ta rufe wardrobe komawa tayi wajan dressing mirror din ta feshe jikinta da dadadan turare na fesawa mai kamshin gaske tsakiya dakin ta dawo tashinfida darduma tasaka hijab tare da tayar da salllah.
Tana idar da sallah tayi adu’o inta ta mike ta linke dardumar da hijab sanan ta mayar dasu inda suke komin ta cikin tsari nutsawa da kwonciyar hankali take yinshi ta dauko dan kwalin rigar dake saman gado ta aza a saman kanta daya rufe duka ilahirin kanta sai dan jelar gashi daya fito a bayan ta da ya kusa tabo mazaunan ta komawa tayi wajan dressing mirror din ta dauko ribon din ta fita daga cikin bazata
Commentรฉ
Et
partager
Comments
And
share
๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ
*ZANBA CIKIN AMINCI*
๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ
ECRITE:
_PAR_
*QUEEN
ZEEFAT*
Yar
Mutan
Niger
Wattpad@nazhabibou
๐ซโจ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*๐
_(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)_๐ค
โ *[ T.M.N.A]* โ ๐๐๏ธ
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_ BISMILAHIR RAHAMANIR RAHIM
Page 2
tana fita daga dakin ta nufi stairs dake dauke da bedroom uku dakin dake gefen dama ta murda ta shiga da salama, wata mata ce da ba zata fuce 45 ans (years) ba fara tass da ita kamar ka kwontala jini ya fito matar tayi masifar haduwa kana kalon fuskar ta zaka hango muguwar kamar da suke sosai da yarinyar sedai sosai tafi yarinyar haske amma yarinyar ta fita kyau nesa ba kusa amma kana ganin ta zakasan cewa mahaifiyar tace sabida kamar da suke dakin mahaifiyar tata shima yayi matukar haduwa masha Allah
Murmushi ne dauke ga fuskar mahaifiyar tata ta lokacin da ta dago tana mai amsa mata salama oyoyo AFREEN dina diyar albarka karaso ki zauna wada aka kira da AFREEN ta karaso ta zauna kusa da mahaifiyar ta da murmushi a fuskar tace Maman sannu da gida yawa AFREEN ya akayi yau kuka jima baku taso daga makaranta tunda zu nike falon kasa inajiran zuwan ki har nagaji da zama na taso na tafowa ta daki dan nayi sallah danaga lokaci yayi, AFREEN tace wly Maman wani exercise ne mukayi na mass mai wahalar gaske duk ya caza mana kwakwalwa sai fah 12:30 muka fito daga aji kuma sai na karbi peper excercise din ga malamin mu nayi copin ta a wani shago da ke jikin ecole (school)din tamu sabida inaso nasake yinta a gida sanan na mayar masa da tasa tarkardar sanan natafo gida da copie din danayi, kamin na nufo gida 12:50 tayi shiyasa gashi har lokacin komawar mu da yamma ya kusa tayi maganar cikin wata irin murya me nuna nutsasiyace yarinyar ce, mahaifiyar tata tace gaskiya kam yanzu karatu se kun kara bada hima sabida kuna shekarar ku ta karshe kinga ga exam din ku na karshan shekara sai kun shirya masa tun yanzu fa ba se lokaci ya kure maka kinga kuma in mutun na son samin cikar burin shi dole sai ya wahala kamin ya ke cin ma nasara dan haka AFREEN a dage da karatu nasan bakida wasa amma akara saman wanda akeyi Allah dai ya taimaka kuma yamaki albarka tace ameen Maman bari naje na kwanta koda na minti 30 kamin lokaci ya karasa yi ta na fadar haka tare da mikewa tsaye maman tace to jeki amma kitabatar da kinyi Sallah kamin ki kwonta tace maman ai har nayi sallah da wanka kamin na shigo nan to madala kinci abinci ma kuwa a’a maman ban jin yunwa AFREEN ta fada a takaice, maman tace ko alama, yama zaki cemin bakin jin yunwa alhalin daga makaranta kike nasa da har kikaje kika dawo baki ci komi ba muje nazu ba miki abinci kici ina aka taba yin karatu ba cin abinci sai mutun ma yakasa gane abinda ake koya masa maman ta fada tana mikewa daga zaman da take ta nufi kofa kamin takai ga fita dakin AFREEN tace to Maman ga ribon ku daure min gashi na ni nakasa amsa ribon din Maman tayi ta daure mata gashi tareda juyawa ta bar daki ba musu AFREEN tabi bayan ta suna sabka down stairs din suka nufi dinning table taja kujera ta zauna maman zata zuba mata abincin tayi maza ta karba tace Maman bari dan Allah zan zuba ma maman ta barmata ta zuba tare da komawa cikin falon ta zauna daya daga cikin kujerun dake falon tana ganin maman tabar dinning ta fara cin abinci, ba dayawa taci ta tashi ta nufi cikin falon tace maman na koshi fah maman tace kedai AFREEN bakya son cin abinci ko??? to tashi ki tafi ki kwanta ki futa amma da dadare sai kinci da yawa to maman insha Allah
Tashi tayi ta nufi dakin ta tana shiga tayi kan gado ta kwanta tare dayin bismillah hade da karanta adu’o in da ake karan tawa idan za’ayi bacci, bata jima da kwanciya ba barci yayi awon gaba da ita.
Maman na zaune a falo tana kalon TV aka bude kofar wani daki wada ke daya daga cikin bedroom din dake falon wata farar mata doguwa mai matsakaicin jiki tafito daga dakin ta karaso cikin falon ta zauna tace Maman fauzia barka da warhaka barka dai umman Zeinab har kin fito tace eh a takaice daganan ba wanda yasake cewa komi falon yayi shiru baka jin motsin Komi tv sunfi minti 10 a wajan kamin ake kara bude wata kofar nan ma dai wata matar ce ta fito ita ba doguwa ba kuma ba gajeriya amma wanan baka ce kuma macha Allah tana na dan jikin amma ba irin mai yawan nan ba, murmushi dauke a fuskar ta karaso falon ta nemi guri ta zauna tare da furta sanun ku da futawa a tare suka juyo suka amsa wada aka kira da Maman fauzia tace Tanti yara yau najiki shuru tun dazu baki fito ba injin dai lafiya tanti yara tace wly Maman fauzia kaina ne naji ya na min ciwo shiyasa amma koda nayi sallah nasha magani wanzu kam da sauki cikin nuna kulawa Maman fauzia tace Allah Sarki da bacci ma kikayi da shikenan da kin tashi sai kiji kin warware tanti yara tace a’a bama sai na kwanta ba yayi sauki ina yata sabida itama nafito Maman fauzia tace Allah kara sauki tana ciki dakin ta tana bacci kin san yau sai kusan 1:00 tazo gida tace wani exercise aka basu mai zafi shiyasa suka jima a makaranta Allah sarki diyata ta kwaso gajiya kenan gashi kuma lokacin komawa na yama yayi Tanti yara tafada hade da daga kanta a saman bangon falon tare da kalon agogon dake manne da bango tace kinga ma har 2:20 tayi bari naje na tasheta kada ta makara Tanti yara tafada tare da mikewa tana mai nufar dakin AFREEN murmushi kawai Maman su fauzia tayi tareda maida hankalin ta ga TV umman Zeinab dake wajan batasa masu baki a maganar suba tabi bayan Tanti yara da harara tace wajan neman a sanka har a manta dakai Allah rabamu da shishigi da cusa kai taja wani dogon tsaki hade da mikewa ta nufi dakin abinta binta da kalo Maman fauzia tayi har ta shige dakin ta banko kofar Maman fauzia ta girgiza kanta tace Allah ya shirya sabida ita yanzu abin umman Zeinab ya daina bata mamaki
Tanti yara nashiga dakin AFREEN bata sameta a ciki ba amma taji kara ruwa a toillet alamun tana ciki hakan yasa ta nemi gefan gado ta zauna tana jiran fitowarta bayan kamar minti 5 da zaman ta aka turo kofar bayin AFREEN dake ciki ta fito daure da da tawel da alma wanka tayi, bata lura da tanti yara dake cikin dakin ba kawai ta nufi wajan dressing mirror ta zauna tana mai tsane jikinta kamar daga sama taji murya Tanti nacewa AFREEN diyata har kin fito da sauri ta juyo ta sauke mayan idanun akan Tanti ta saki wani kayatacan murmushi tare da tasowa ta nufo wajan tanti da sauri tare da rungume ta tace tanti na yanzu nake cewa idan na shirya sai naje wajanki kamin na fuce makaranta sai gashima Allah ya kawomin ke Tanti tayi dariya tare raba jikin da na AFREEN tace kai AFREEN kedai kinki girma dubi fa yanzu da a tsaye nake da kin kayar dani wai yaushe zaki girma ki daina shirme cike da shagaba AFREEN tace wlh tanti nidai bason na wani girma nayi zamana a haka ya fimin tanti ta dafe kanta tace kinji shirmen ko bafa kiyi kiba nake cewa ba a’a nufi na yaushe zakiyi hankali tanti ina fa da hankali kinga fa shekara ta har 18 fah AFREEN ta fada tana mai turo dan karamin bakinta cike da shagwaba to shikenan naji jeki ki shirya ki karasa shiryawa kada kiyin lati AFREEN tace to tashi tayi daga gaban Tantin ta koma ta zauna gaban dressing mirror tafara shafa mai da turare cikin nutsuwa take komi ha ta gama shirya wa cikin wata hadiya doguwa riga ta Atanfa da ta karbi jikin tayi matukar yi mata kyau saka safarta ta hannu da ta kafa tayi tare da dauko dogon hijabin ta tasaka har ya najan kasa taje ta sake bude wardrobe ta ciro nikaf ta ruke a hannu ta juyo wajan tanti da tunda tafara shiryawa take kalonta tace tanti na kamala ajiyar zuciya tanti ta sauke tace waike AFREEN yaushe zaki daina irin wanan shigar haka an ce mutun ko fuskar sa ba ya bari a gani to koni dai ni dake da aure a kaina bana irin wanan shigar taki to wai tayaya wani zai ganki yaji yana sonki har ayi wata maganar aure a cikin wanan shigar du wanda ya ganki zaiyi zaton matar wani baban malami ce ke
AFREEN ta waro idanu ta tareda turo dan garamin bakin ta tace tanti ni ina ruwana da wani kuma nida ke harakar karatu na nidai nafison nayi shigana a haka kofa cikin class bana cire nikaf dina tanti kinga fa shekarana biyu yanzu ina cikin ta uku a school din mu amma bu wanda ya taba ganin fuska na kwanaki da aka kawo mamu wani sabon malami yace dole sai na bude fuska na ko na fitar masa daga aji ni kuma nafita bayan fitana wai yake tambayar yan ajimu wai miyasa bana bude fuskana sukace ce masa suma basu sani ba suma tunda suke basu taba gani fuska na ba ko ance na bude bana budewa sai kawai yace aje acemin na dawo nazo na zauna haka na dawo ajin na zauna ba tareda na fida nikaf din ba amma ana ganin eye dina.
AFREEN tace tanti bari naje kada nayi lati tare da saka takamin a kafarta Tanti tace yi maza ki fuce naga har 2:50 tayi amma yau AFREEN ki ban mamaki yada kika yi magana da yawa haka AFREEN tasaki murmushi tare da bari cikin dakin tanti na biye da ita a baya tace tanti wai ina anti khairat tunda nazo ban ganta ba Maman ki ta aiketa gidan yayar ku amma yanzu ta dawo nasan dai sai kin dawo zaku hadu tanti ta fada AFREEN tace to Tanti dan Allah ki fada ma maman cewa nafuce sabida nayi lati kamin na je saman stairs nayi mata salama lokaci zai kure ta fada tana me murda kofar falon tafita Tanti na mata Allah kiyaye hanya ta amsa da ameen tare da ficewa daga falon gaba daya
Wajen parking space ta nufa tac ciro makulin motar tareda nufar motar da tashigo da ita dazu ta bude ta tashiga ta tada motar tare da barin cikin parking space din ta nufi kofa mai gadi na ganin haka ya wankale mata kofar ta fita a guje sabida latin da tayi tafiyar minti 10 yakai ta makarantar parking space taje ta paka motar ta fito ta kule ta yin hanyar ajin nasu da aka riga aka shiga tsaya wa tayi bakin kofar ajin ta taba hannu daga ciki aka amsa da oui rentre(yes enter) tashiga da salama tare da gaida malamin ta nemi waje ta zauna malamin binta yayi da kalo har ta zauna kamin yaci gaba da explaind din lesson daya ke.
Karfe shida daidai suka fito daga ajin nasu ita da wata farar yarinya da bazata wuce shekarun AFREEN ba tsayisu yaso ya zo daya sai dai AFREEN ta fita da kadan itama kyaukyauwace yarinyar ba lafi sanye take da riga da sket na Atanfa sunyi matukar yi mata kyau sanye take da dan karamin hijab da baikama ta gwiwa ba, yarinyar tace AFREEN wai yaushe zanga fuskar ki dubi fah tun lokacin da muke dake, har gidan ku nasha zuwa baki taba bari naga fuskar ki ba basan ko sabida miyasa kike boyemin fuskar ki ne wai idan ma kin boyema kuwa ai ni bai kamata ki boyemin ba duba fa kiga yanda yanzu ko a hanya nagaki bazan sheda kiba inba tafiyar ki nagani ba AFREEN tace hasina kenan wlh ba abinda yasa ni ke boye wanan fuskar ta waba saida dalili babu wani dalili AFREEN idan dai kin dauke ni a matsayi kawa to ki nuna min fuskar ki yanzu ba se anjima ba gaskiya yanzu ai zanji kunya idan aka tambaye kamanin kawata nace ban saniba ai za’amin dariya ace du kawancan dake tsaka nin muma basanki ba AFREEN tace kiyi hakuri dan Allah kawata wlh watarana zan nuna maki fuska ta amma yanzu rishin ganin fuskata a gareki shine mafi alkairi a’a ni wlh bazan taba yarda ba gaskiya wata muguwar kama ce gareki daza kice wai rishin ganin fuskar ki shine mafi alkairi ka mardai wata aljanah
AFREEN tace wlh hakan da fada maki gaskiya ne hasina a’a kedai ki nunamin don wly idan baki nuna min yau ba kuma yanzu wlh bana shiga motar kiba kuma kawancan mu daga yau ya kare haba hasina meyasa zakice haka nan hasina tace kindai ji abinda nace ai ko to kinga ma tafiya ta da sauri AFREEN ta riko hannuta tace yi hakuri kawata muji mota sai na bude fuskar ki gani haka hasina ta bita suka nufi idan motar take tabude motar ta shiga hasina ta bude wajen me zaman banza ta shiga ta rufo kofar AFREEN nagani tashiga tayi saurin wiwa motar key tare da barin cikin makarantar hasina na mata masifa amma ko kulata ba tayi ba, bata tsaya ko’inaba sai kofar gidan su hasina, hasina na ganin ta tsaya takai hannun jikin kofar zata bude ta fita taji ta a kule fuska a matukar daure ta juyo daniyar masifan ce AFREEN lokaci guda tasaki wata irin kara hade da furta wa innahu suleymanu wa innahu bismilahir rahamin rahim, inna lillahi wa inna illaihi raji’un la’illaha illah anta subhanaka inni kuntum mina zalumin a tatare ta jero wa yanan adu’o in gaba daya a lokaci guda sanadiyar arba da tayi da kyaukyauwa fuskar AFREEN.
Ganin yanda ta firgice tana kokarin bude motar ta fita yasa AFREEN sauri bude mata motar da sauri ta fice daga motar ta shige gidan su kamar wada tayi wani mugun gamo da abin tsoro mafi tsoratawa a fadin duniya.
Commentรฉ
Et
Partager
Comment
And
Share
๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ
*ZANBA CIKIN AMINCI*
๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ๐ธ
ECRITE:
_PAR_
*QUEEN
ZEEFAT*
Yar
Mutan
Niger
Wattpad@nazhabibou
๐ซโจ *TAURARIN MARUBUTAN NIGER (ASSO.)*๐
_(Tsintsiya mad’aurinki d’aya)_๐ค
โ *[ T.M.N.A]* โ ๐๐๏ธ
https://www.facebook.com/Taurari-marubutan-niger-111773560677003/
_BISMILAHIR RAHAMANIR RAHIM
Page 3
AFREEN ta aza kanta saman steering din motar ta ce ga abinda nake gudu ya faru yanzu bansan yaza ta doki abin
ba da ban bude mata fuskan ba kuma tace ban doketa a matsiyin kawata ba dana bude mata fuskar kuma nasan yanzu ma gudu na zatayi wai wane irin kyau ne dani wanda mutane basu iya jure ganisa kodai wata kama gareni mai ban tsoro wada ni ban ganin ta sai na tare dani tare ta jero ma kanta wa’inan tambayoyin da taga batada mai amsa mata su yasa ta mayarda nikaf inta ta tayar da motar ta nufi gida,tana zuwa gida bayan mai gadi ya bude mata get ta shiga tayin parking motar a parking space tafito ta nufi cikin gidan ta na shiga falo da salama ta tarar da mahaifiyar ta dake zaune tana kalo gaida ta tayi sanan ta karasa kusa da ita ta zauna a saman carpet mahaifiyar ta ta amsa tace AFREEN yanzu dinma kin jima a makarantar injin dai lafiya
Lafiya lau Maman AFREEN ta fada a takaice tana mai cire nikaf din fuskar ta maido da kalon ta tayi wajan mahaifiyar tata cike da damuwa kamin takai ga magana Maman tace lafiya ki AFREEN naga kama akwai abinda ke damunki dubi fuska na Maman wai ni kyau gareni ko muni wace irin munmuna kama ce dani da duk wanda ya kaleni ya ke firgita alhali ni banga abin firgita a cikin tsarin halita na taba ko kama nike da mutanan boye ban saniba kodai da gangan mutane kemin hakane tunda ni ban ga abin tsoro a tatare dani ba AFREEN ta tambayi mahaifiyar ta ta da hawaye kwance cikin idon ta da alamun damuwa a tatare da ita Maman tace ko alama ba ko daya daga cikin abinda kika zayana a tare dake AFREEN maza mayar da hawayen ki kada kiyar da su zubo dole ne mutune su ringa firgita da irin kyau da Allah ya maki ba wani ba ma ko ni dake mahaifiyar ki mamakin wanan baiwar kyau da Allah ya maki nake AFREEN.
Yan magana nace wada yayi fari ya gama kyau amma ni tuni na karyata wanan magana tunda Allah ya azurta ni dake tunda kinga kedai ba za’a saki a layin farare ba haka ma ana bakake babu ke a ciki sedai asaka ki a tsakatsakiya amma kinga duda haka Allah ya miki kyau irin wanda baza’a iya musilta shi ba dan haka godiya ya kamata kiyi wa ubangiji da yabaki baiwa kala kala ba wai butulce mashi ba.
Kuma ina me gargadin ki da kada kiyi anfani da kyau da Allah ya maki wajan saba masa ki zamana me kyautatama sa komi rantsi duda banda shaku a kanki amma yanzu zamani ya canza kawaye ma na iya sauya ma mutun tarbiyar da iyayensa suka mashi dan haka ki kula AFREEN kisan irin kawayen da zakiyi mu’amala dasu ba kowa ake kawance da shiba.
Dan haka ki fida damuwa a ranki sabida kyau ki ba me tsoratarwa bane kawai dai dole ne ya firgita mutane bama karma a bazata mutun ya ganki, tunda wasu za su ringa tunanin cewa kedin munmuna ce shiyasa baki yarda aga fuskar ki wasu kuma suce kyau ne dake shiyasa amma baza su taba tunanin kyau naki ya kai haka ba wasu zasu ce ra’ayi ne da ganin dama ko suce da gangan ne yasa kike saka nikaf ba mai taba zaton dalili ki nayi haka kinga Maman ni yanzu harma na saba ban iya fita babu nikaf sabida dana fita mutane sai su dinga min kalon kurila wasu ma har guduwa suke wasu kuma mamaki nake basu kamar dai babu wanda ya fini kyau a duniya Maman kinsan a kawai masu kyau sosai wanda suka fini nesa ba kusa ba amma kuma nawa kyau se yadinga firgita mutane ga laraba wa da indiyawa nasan da cikin su a kwai wanda suka fini kyau nesa ba kusa ba amma su ba’ayi mamakin nasu ba sai nawa, hum AFREEN kenan bazaki ganeba ne kefa naki kyaun na daban ne indiyawa ko larabawa suma nasu kyau daban yake bama yanayin ki guda dasu kinga su a cikin suma za’a iya samun wanda kyau su zai iya firgita mutane fiye da naki to kinga ke yanayi kyau naki ne yake firgita mutane da basu mamaki badan wai ba za’a iya sami me kyau fiye danaki ba ne a’a ke hada baiwa da Allah ya baki me sa du wanda ya ganki yake ganin annuri da kyau suna karuwa a fuskar ki fiye da yada ke kike gani
Dan haka ki kula kiji tsoron Allah ki guji sabama ubangijin ki dan bai cancanci haka daga garemu ba Allah abin bauta ne dan haka mu bauta masa fiye da yanda ya umurce mu idan har za muyi ma kan mu adalci ma halicin ya cancanci mu kadaitashi ko dan rayuwa da ya bamu sadakar yi aiko ubangiji mu ya gama mana komi Allah dai ya kara mana imani da tsoron sa a ciki zukatan mu ya bamu lafiya da kwonciyar hankali mai daurewa ya tsare mu kuma ya kare mu daga duk wani iftala’i da sharin duk wani mai shari Allah yamana kyaukyauwan karshe yasa mugama da duniya lafiya.
AFREEN ta amsa da ameen Maman zata sake magana Maman ta katseta da cewa kada kikara ce wa komi AFREEN.
Tashi kije daki kiyi wanka ki futa kinga magariba ta gabato ba musu ta mike tace Maman wai ina anti khairat tace tana dakinta to Maman bari naje na shirya sai naje wajan ta
Tana juyawa idanun suka sauka cikin na tanti da take tsaye tun dazu tana sauraran su amma su ba su san tana wajan ba take ta sakar mata da murmushi tace tanti barka da wara haka tanti ta amsa tana mai mayar mata da murmushi tace tanti zanje inyi wanka ne zan fito idan nayi sallah tace to sai kin fito AFREEN ta nufi dakinta ita ko tanti ta karasa cikin falon.
******
Hasina a guje ta shiga falo gidan su tana wage wage da sauri mahaifiyar ta dake cikin falon ta mike tace subhanalahi ke lafiya kika shigo min falo a guje hasina data durkushe kasa saman carpet tana sauke ajiyar zuciya ta dago ta kali mahaifiyar ta tace ummi gamo nayi koko miye ni ban saniba gamo kuma hasina a ina .
wlh ummi nidai nasan mun fito daga aji tare da AFREEN wanan kawarta wa danake baki labarin nace mata yau ita zata kaini gida tunda direba daya kaini makaranta yake ce min da ya sauke ni zaiyi tafiya idan mun tashi na shiga napep to sai na matsama AFREEN kan cewa doli sai ta nuna min fuskar ta a yau inba haka ba zamu daina kawancan to sai tayar da zata nuna min tace muje mota muna shiga sai taja motar bamu tsaya ko’ina ba sai kofar gidan nan na juyo gunta daniyar balbaleta da masifa kawai mizan gani,
Hanisa ta dan nisa kanan taci gaba ummi kinsan mi nagani ummi ta girgiza mata kai hasina tace wata daleliyar yarinya mai masifar kyau nagani du yanda zan kwatanta kyauta ba zaki gane ba ummi wlh ba AFREEN nagani ba aljana ce sabida babu mai irin wanan kyaun nan acikin mutane to wani ummi ina ma tayi da AFREEN din da muka tafo tare nashiga uku ummi kawata naci kin hadari abinda yakara firgita ni ummi tunda muka biyo hanya nakema AFREEN masifa ta min shiru hakan na nufin cewa dama tun bisa hanya bada AFREEN nike magana ba oh Allah ka tsare AFREEN ka kareta daga sharin wanan aljana wlh ummi kyau din ta ya yuce musali hasina ta fada a firgice tana mai sake waigen kofar falon wai kar ace aljanar ta biyota
Komawa ummi tayi ta zauna tace haba hasina ya zaki ma kawarki haka yanzu ya kike su taji tunda kike ban labarin ta kina cewa ko a aji bata fida nikaf nasan da akwai abin take boyewa kuma tanada dalilin yin hakan ta yiyuwa sabida kyau inta yasa bata bude fuskar gudun faruwar abinda kika mata yanzu kewace irin birkitata ce da bazaki iya aje hankali ki tantance ba ka kikace ta nuna maki fuskar ta amma kuma sai ki saka mata da haka haba hasina baki kyauta kawai baki taba tunanin kyaun ta yake haka bane kuma gani fuskar ta ya zo maki a bazata shiyasa amma ba wata aljana dakika gani kawarki din daice AFREEN
Wata irin nauyayar ajiyar zuciya hasina ta sauke tare da kura ma mahaifiyar ta ido na wajan sakan 5 kamin ta nisa tace hakane fah zancan ki ummi sabida kamin ta yarda zata nuna min fuskar ta seda tace min nuna min din ba alkairi bane ba amma na matsama ta nayi wawanci sosai miyasa nayi mata haka oh ni hasina Allah shirya min halina ya fitar min da tsoro. Amma fah ummi ba laifina bane wlh kyau AFREEN ne ya wuce tunanin mai tunani kuma hakan yazo min a bazata ummi tace hakane yanzu tashi kishiga ciki ki futa sai ki kirata ki bata hakuri
Haka hasina ta tashi ta shiga dakin ta da tunani iri iri a zuciyar ta
******
AFREEN nashiga daki ta cire kayan jikin ta ta fada toillet wanka tayi tare da dauro alwala ta fito tayi wajen dressing mirror ta gama abinda take sanan ta nufi wardrobe ta sake ciro wata doguwa rigar tasaka tare da hijab ta nufi gun da take ajiye darmuma ta dauko ta shinfida tare hawa ta kabarta sallah.
Tana idar da sallah da adu’o inta ta nufi ma’ajiyar kur’anai da litatafan adini ta dauko kur’ani Ta koma saman darduma ta fara karantawa tana nan zaune a haka har aka kira sallar isha ta tashi ta mayar da kur’anin ta dawo saman darduma ta tayar da sallah tana idawa ta nike darduma da hijab ta maidasu ma’ajiyar su ta koma inda gadon ta yake ta doki dan kwalin rigar da ta ajiye a saman gadon tare da ribon ta daura dankwalin rigar da ribon a hannu ta ta nufi kofa tana bude kofar dakin suka ci karo da wata farar yarinya a bakin kofar kyaukyauwa ce itama bazata fuce 21 years suna da kamar jini a tsakanin su sai dai ita fara ceda sauri AFREEN ta saki kofar tana murmushi wanda har saida fossette (dimple) dinta suka bayana tayi tsale ta rugumeta tace wayo anti khairat nayi kawarki duk yau tunda safe da na ganki bansake ganin ki ba tunda zu nake tambayar Maman ke khairat tace to kuma shine in kinyi kewata shine bakije waje naba ai gashi nida nadamu dake nazo na ganki, AFREEN tace dagaske Anti khairat yanzu ma da kika ganin na bude kofar nan zan fita wajan kine zanje bakiga yanda na kagu naje na ganki ba dan Allah Anti khairat shigo mana tace a’a dama ai yurina kikayi niyar tafiya ko AFREEN ta daka kai alarma eh sai Anti khairat tace to muje daki na AFREEN tace to Anti karbi ribon din nan ki daure min sai mu fuce.
Karba ribon din Anti khairat tayi tace to juya AFREEN ta juya tare da since dan kwalin dake kanta khairat tace ni ban san ranar da zaki iya daura ribon a kanki ba tace wlh anti nima ban san ranar ba baki ga gashi nane yayi yawa ba gashi kuma da tsayi sosai ni ha tsoro ma yake ban Anti khairat tace to idan ya baki tsoro ki daina karba mana murmushi kawai AFREEN tayi batace komi sabida tagane mitake nufi tana gama daure mata gashi ta kama hannuta suka bar kofar dakin ta ce mu fara zuwa mu gaida papa kamin nan cike da zumudi AFREEN tace papa ya shigo ne khairat ta amsa da eh.

Leave a Comment