Books Reviews & FAQs

Zayn Malik Hausa Novel Complete

….ZAYN MALIK….✿_

*EXQUISITE WRITERS FORUM*

NA
Mai_Dambu

*FREE PAGE♡*

CHAPTER-01
Scandal 💔

بسم الله الرحمن الرحمن
*Wannan littafin sadaukarwar ne ga , Aunty Mamie Allah ya saka da alkhairi Nagode sosai 😍🤩🥰 ina alfahari da samun ki a gefe na Allah ya barki da oga giwar Mata*

_ALHAMDULILLAHI YAU GANI NA DAWO A SABON LABARI ME TAKE A SAMA! INA MATUKAR GODIYA DA BIBIYANA DA KUKA YI A KALLABI NAGODE SOSAI LABARINA NA KUDI NE DAN HAKA MU CIGABA DA CANCAREWA POSTING BA KULLUM BA DUK BAYAN KWANA BIYU_

_____________________________________

 

“Ya Allah kamar yadda ka nisanta sharri da alkhairi Ya Allah ka nisanta Kaltumah da Alhaji Abba Yerwa! Ya Allah kamar yadda ka raba wuta da ruwa ka raba Kaltumah da Alhaji Abba Yerwa.!”

Shiru yayi na wani lokaci, yana cigaba da had’a siddabarun shi, kafin ya d’aga wani abu a cikin keji sama, bude kejin yayi tare da juyawa ya kalli inda garwashi yake, ya tako zuwa wurin sannan ya cigaba da zagaye garwashin kafin ya zuba wasu irin tarkace wanda suka had’a da barkono da wasu itacce,  sannan ya watsa su a cikin wutar kaskon. Tashi sama bayanin yayi shi kuma ya gyara rikon tsuntsuwar ya fara kiran sunan Kaltumah.

“Kaltumah! Kaltumah!! Kaltumah!!! Ki shiga duniya, a manta dake a manta da kome naki, dangin ki da Alhaji Abba Yarwa ya manta dake ta manta da kome naki, Kaltumah ki Haukace ki lalace karki mori kowa kar a more ki, Aljani zinkidu ku tafi da ita ta shiga duniya ta b’ace kamar yadda ake binne gawa. Kaltumaaaahhhhhhh! Hhhhhhh”

***
KADUNA STATE
Millionin Quarters

Zaune suke sun nutsu kana ganin su kasan ba ƙaramin abu bane ya ajiye su a wurin. musamman dan matashin cikin su da ya kwanta a restchair, yana dan jijjiga shi. Kyakyawar gaske kuma shugaba a cikin su.

Fari ne me kyau, idan ka dube shi zai iya kiran shi da Balarabe, ko irin buzayen nan, tashi yayi ya zauna yana kallon su, kafin a zare glass din idanun shi, sai da ya lumshe idanun kafin ya ware su akan dayan su, blue eyes din shi suka bayyana, har suna bada wani irin haske kamar an watsa musu oil, lashe lips din shi yayi cikin yanayin shi da yake kara tsorata abokan shi. Dan kimanin shekaru ashirin da biyar.

Saka hannun shi yayi a cikin Aljuhun wandon shi ya zaro lighter. A hankali ya zaro mandular shi, wato wiwi. Bude takardan yayi a hankali ya murzata, kafin ya nad’e ta, ya kunna ta yana me manna ta a bakin shi, zuka daya yayi mata yana kallon su baki ɗaya. Idan akwai abinda ya tsana a rayuwar shi, shine sharri.

Zuka na biyu yayi mata ya gama da wiwin hayakin na fitowa ta hanci da bakin shi.
“Easy ZM! Za a samu mafita fa” basu gama magana ba, suka ji sarin na yan sanda. Bude idanun shi yayi cikin bakin ciki da takaici, kafin ya sake murmushi yana me kallon abokan shi da suke niman hanyar arcewa.

“ZM tashi mu tafi don Allah kar ka bari su shigo” kallon abokin shi yayi sannan ya  wani dauke kai yana faɗin.
“Inji gidan uwar wa?” Dafe kai abokin yayi yana kara jin tashin hankali.
“Don Allah tashi mu tafi kaji wallahi zasu kama mu” abokin ya faɗa.

Gyara zama yayi ZM yayi yana kad’a kafar shi, bakin shi kuwa fiduwa yake.
“Don Allah kaga duk sun ware tashi mu gudu” abokin ya faɗa kamar zai yi kuka,
“Kasan dai ko cikin uwarka ka shiga ba zasu kyale ka ba, just go zan tsaya” Dabas abokin ya zauna yana kallon shi.

Abu uku yake saka shi kaunar ZM na farko bai da tsoro na biyu kome dacin gaskiya sai ya fade shi, sai dai a mutu. Na uku mutum ne da yake da wata irin zuciya ko bashi yayi laifi ba zai tsayawa abokan shi.  Bubbuga kofar da ake ya katse mishi tunanin shi,mikewa ZM yayi ya nufi kofar da zai kai shi inda ake bugawa. Rike hannun shi abokin yayi yana girgiza mishi kai.  Juyawa ZM yayi da sauri ya sungume shi, bai tsaya ko ina ba sai bakin window da sauran abokan suka dira, ganin yan sanda yayi, dan haka ya sauke shi yana kallon shi,. murmushi yayi sannan ya riko hannun shi suka nufi wata kofa, dauko kujera yayi tare da nuna mishi kofar silif din dakin ya ce mishi.
“Abul Khair bi nan zan ji da su.”

“Zayn!” Abul Khair ya fada idanun shi a waje.
“Zanci ubanka haura ka tafi.”
“Ba zan iya tafiya na bar ka ba” inji Abul Khair,
“Ko mahaifa guda muka wallahi ba zaka bi ni ba”

Ya fada yana juya mishi baya, tunda ya fadi haka yasan halin abokin shi dan haka ya haura cikin silif din ya zauna shi kuma ya fita tare da rufe kofar dakin. Yana fita falon ya samu har sun balla kofar falon zasu shigo.
Zama yayi yana kallon su, har suka shigo yana zaune.

Cirko cirko suka yi suna kallon shi kafin suka ce mishi.
“Zo mu wuce!”
“Kofar da kuka balla waye zai gyara min?”  Ya tambaye su,.kan shi yana kasa kamar ba shi yayi maganar ba, dan Allah bai daura mishi tsoro yan sanda ba.
“Zaka tashi mu tafi ko sai mun shiga jikinka”
Banza yayi da su, ya dauki kafa daya ya daura akan ɗaya. Yana kallon su kamar ba da shi suke magana ba. Sun san halin shi da Masifar taurin kai, ko kashe shi zasu yi tunda ya daura daya akan daya da zai tab’a bin su ba, dan haka suka karya murya tare da ba shi umarni cikin lallume.
“Kazo mu wuce”
“Gidan uwar wa zan tafi?”
Ya fada yana kallon kofar da suka balla mishi.
“Ok za a gyara maka amma muje”
Kallon su yayi sannan ya dauke kan shi.
“Kunsan dai ni ba barawo bane?”
“Mun sani, zamu kai ka kamar yadda ake raka gwamna ko wani me muƙamin gwamnati.”

Tashi yayi suka saka shi a matsayin su, suka fita da shi wallahi idan ka ga yadda yake tafiya da buga takama zaka rantse da Allah wani mukami ne da shi, a madadin ya shiga bayan motar su sai gashi sun bude mishi gaban motar ya shiga ya zauna, sauran yan sandan suka shiga baya, aka wuce da shi office din Yan sanda.

Da gudu Yaran Makotan su, suka nufi gidan su.

Da gudu yaran suka shiga.
“Assalamu alaikum, Hajiya Umma yan sanda sun tafi da Ya ZM yanzu nan” suka fada tare da kallon dattijuwar da ta sake kofin hannun ta. Cikin tashin hankali ta shiga kiran surukanta.
“Talatu!!”
“Ina kuke ne?” Da sauri matan gidan baki daya suka fito, suna kallon ta.
“Hajiya umma lafiya?”
Cikin tashin hankali ta zauna tare da fashe musu da kuka.
“Innalillahi wa’inna alaihil raji’un, Hajiya Umma me aka Miki?”
“Wayyo Zaynu na yan sanda suka kama Allah ya isan mishi Yaron da babu ruwan shi.”

A hankali sauran matan gidan suka fara juyawa suna watsewa a wurin.
“Talatu ki kira min Uban shi ya zo ya ciro shi” ciki matsanancin damuwa. Ta ce mata.
“Kiyi hakuri zai dawo Insha Allah, Kinsan baban su ya ce kar na kuma mishi maganar Zayn Malik, ban san ya zan yi ba” ta fada itama cikin damuwa sosai, babu uwar da zata so a ce nata ya lalace, sai dole amma ina ba dan haka ba yaushe Zayn  zai zama haka a cikin unguwa duk da bata san abinda ya faru ba, tana da yakinin yana da gaskiya baya aikata kome sai da hujjar shi.

Tun karfe biyu ake niman wanda zai amso ZM a hannun yan sanda har dare,

A bisa al’adar gidan idan mazan suka dawo kasuwa, dakin Hajiya Hajiya Umma suke fara shiga kafin su wuce na manta su, Alhaji Uwaisu shi ya fara shigowa gidan, dan haka aka gaya mishi. Be yarda ya shiga wurin Umma ba sai da ya tura Bashir kanin su, kuma babban Uban dakin ZM.

“Assalamu alaikum!!” Aka rangad’a sallama daga bakin kofar Hajiya Umma.
Sai da ta kunkure bakinta sannan ta mike a hankali tana daura zanin ta, ta bude kofar ban dakin ta watsar da ruwan bakin ta. Sannan ta amsa sallamar da kyar.
“Wa’alaikumunsalam” daga haka ta tashi ta koma saman kujeran ta zauna tana taunar goro hannunta dauke da casbil. Sake sallamar aka yi nan ma ta amsa. Sannan ta cigaba da abinda take.
“Umma kiyi hakuri gani nan sai yanzu na samu labarin abinda.” Wani lafiyayyen harara ta wurga mishi wanda ya bashi damar hàdiye sauran kalaman ta. Suna cikin haka aka sake sallama,  daure fuska tayi tam.
“Wa’alaikumunsalam”  har da sauran da suke cikin dakin kana ganin su kaga Yaran ta, watsa musu harara tayi iyaka sannan ta juya musu baya tana zumbura baki.
“Umma kiyi hakuri! Insha Allah na tura Bashir ya tawo da shi. Amma maganar gaskiya ki mishi magana ya daina abinda yake domin wallahi”
“Idan ka shirya koran mu a gidan ba sai ka rantse ba, ai na jima da tanada kudin hayan da muke a gidan ku. Kawai Yaro bai da ikon yayi dan wasa jinin shi sai a shiga tsatsagar shi me ye da ake niman kama min kurwan Yaro kawai idan ka gaji da zama damu Abdulmaliku ka kare ni da Baban Umma ka huta ganin mu kawai”

Kallon sauran Yaran tayi da suka sunkuyar da kawunan su, ta zabga musu harara kamar idanun ta zai fadi ta ce musu.
“Kun wani sunkuyar da kai kamar wasu Na Allah, nan kuwa munafukai ne baki dayan ku, sai gyada kai kuke kamar kadangare yasha hantsi. Ku tashi ku bani wuri munafukan banza munafukan wofi, ku da zaku  boye shi kune kuka mika shi ga yan sanda masu rusa-rusan kai kamar tukwanen shuka.”
“Allah ya huci zuciyar ki” inji mahaifin Zayn Alhaji Abdulmalik Yanzu haka Bashir yana can! Amma Hajiya a mishi magana abin da yake janyowa yana tab’a martabar siyasata”

“Na kwad’a siyasar na cinye aikin banza, anya AbdulMalik anya kana kaunar Malami kuwa? Yaro karami ka mishi kawon zuga!”
“Hajiya Zayn din ne karami? Shekaru talatin da shida, sau nawa ina nima mishi aure yana ki

Office din Yan sanda.

Kallon shi ispetor na yan sandan yakin yayi, sannan ya kalli wani babban mutum da yake gefen su da wata budurwar yarinya. Murmushi yayi sannan ya mai da Idanun shi kan dan sandan.
“Officer kace me dan ban fahimci abinda kake nufi ba?”

Kallon yarinyar yayi da mutumin gefen ta ya ce mishi.
“Wannan yarinyar me suna Radiyah, tace kai ne ka mata cikin jikin ta”

Dariya yayi sannan ya juya yana kallon yarinyar, kafin ya ce mata.
“Ke!” Da sauri ta d’ago kai tana kallon shi.
“Kika ce abinda yake cikin ki nawa ne?” Yadda yayi maganar yasata girgiza mishi kai.
“Magana nake dake, kuma magana zaki yi”
“Yallabai kaga yana bude mata ido”

Wata ƙatuwar harara ya wulla mata, tare da mikewa.
“Officer ka tambaye ta na tab’a had’a hanya da ita?”  Ya tambaye ispetor yana zare idanun shi.

“Mr Malik calm down! Wannan case din bana nan ne aka shigar da kara amma kasan ba zan  tab’a barin wani abin kunya ya faru da kai ba, balle Alhaji AbdulMalik Zain Malami ba, dan haka ka kwantar da hankalin, kasan case din is About money by…”

Mikewa yayi tsaye ya zuba hannu a kugun shi, ya kalli Yarinyar sannan ya cewa baban ta.
“Zan kebe da Yarka?”
“Yaro bana son abin kunya” juyawa yayi gaban ispetor din ya gyada kai, mikewa dan sanda yayi ya fitar da tsohon waje,  takowa yayi gaban Yarinyar yana kallon ta from toe to head. Cikin wani killer smile ya ce mata.
“Chilling yan mata let me serve you”
Cak ya dauke ta sama, tare da kallon yadda take kokarin magana.
“Don Allah ka rufa min asiri, wallahi biyan mu aka yi dan Majalisar dokokin na garin nan Alhaji Musa Me gari” wurga da ita yayi sannan ya gyara tsayuwar shi.
“Sanata ko?” Girgiza kai yayi sannan ya juya ya fita.

Daga shi sai gajeran wando da rika open chears, yana tafiya kawai zaka fahimci shi din kiran mutanen farko ne, ko ba a gaya maka ba, domin gefen hannun shi tattoo, tsayawa yayi a gaban Uban Yarinyar. Ya ce.
“Kaci Arzikin furfuran ka, da sai nayi ta kwallo da kai wallahi sai na kareraya kashin ka. Akan dan karamin kudi zaka bata shekarun ka!”

“Muje my Boy an gama na yau!”inji wani mutum da yake dauke da takardu da brifcase.
“Uncle bash kafin nan bari na fara zuwa gidan Sanata Musa Me Gari”
“That’s my Boy naji kome a wurin ispetor” suna fita kuwa yan jarida suka musu caaaa.
Daga can wata yar jarida ta wurgo musu tambaya.
“Brrst Bashir Zayn Malami shin dama dagaske an jima ana zargin Mr Malik da abin kunya?”

Body guard din Brrst Bashir Zayn Malami ne, suka fara kokarin kare su.
“Zayn Malik Malami dama da gaske kai dan dan daba ne? Dama an jima ana zargin ka da Safaran miyagun kwayoyi da lalata Yan mata shin da gaske ne?” Juyawa yayi sannan ya Zubawa yar jaridar idanu.
Murmushi yayi sannan ya taka har gaban ta, duk da Brrst Bashir yana jan shi bai fasa ba, sai ya ya isa gaban ta sannan ya rike abin nad’an murya ya ce mata.
“Waye ya sani tunda kina cikin su!” Yana fadar haka ya juya abin shi, har dai tafi ya koma dawowa gaban ta ya wani fisgota sai da ya haɗa da kirjin shi.
“I like your dress, you look sexy, amma idan kika sake ba iya gidan jaridar ba hatta wanda ya tsaya miki sai na saka buldoze na binne ku da ranku make my words”

Wani shegen tsoro ne ya kamata, yan jarida basu fasa saukar shi a hoto, hakan ya shiga motar yana me kwantar da kujeran shi.
“ZM”
“Kaci kutmar Ubanka sauka a motar shege” ya fada zafaffe.
“Muje Sam” inji Brrst,
“My Boy!”
“Meye?”

“Ka kwantar da hankalinka”
“Sam ka kai ku resident na Sanata Musa Me Gari!”
Babu musu sam ya bawa motar wuta. Suka nufi gidan sanata Musa Me Gari. Har cikin gidan ya shiga, ya samu sanata yana tattaunawa da wasu yan jam’iyyar shi. Cikin fushi ya bude motar sannan ya nufi inda sanata yake.
Bodyguard din sanata ne suka fara kokarin dakatar dashi, cikin fushi ya mangare daya ya kuma saka kafa ya kwashe dayan.

Yana isa gaban Sanata ya riko kwalar rigar shi.
“Zayn Malik!” brrst Bashir Zayn Malami ya daka mishi tsawa, amma ina jan Sanata yayi ya nufi wurin da aka tara ruwan da agwagi suke wasa ya tsuma kan shi.
“Ban damu ba idan ka tafi gidan Yari dan ka karya wuyar dan iska mara mutunci, ko ciwo dan Allah ya saukar be dan ya kankara zunubi amma da ina da iko ahalina ba zasu yi jinya ba, kai ne zaka kai min ahali matakin bakin ciki, toh wallhi na kuma ganin haka dai na kashe banza irin ka” sannan ya cire kan shi ya cilla gefe guda. Yana tsaki,

*Hi Habibity na fara zayn Malik sabida wasu dalilai, kuma nan da karshen wata zai zama ana azumin arfa so kwanakin Ibadat ne ba na shiririta ba! And ZM na kudi ne 300₦🔞 abu na gaba labarin zai zo yadda ba zaku yi nadamar shi ba thank you fanmily’s*

PAID BOOK

_….ZAYN MALIK….✿_

*EXQUISITE WRITERS FORUM*

Mai_Dambu

*FREE PAGE♡*

CHAPTER-02
Family Affair🎊

بسم الله الرحمن الرحمن
Kakkabe hannun shi yayi sannan ya juya yana me barin wurin, idanun shi ta sauka akan wata kyakyawar budurwa, murmushi yayi mata kamar yadda ya saba matukar zai ga yan mata toh wallahi sai yayi broke heart din yarinya, wani kallo yayi mata tare da d’age mata gira daya. Dauke kai tayi zata wuce ya tsare hanyar.

“Ke yar wancan mutumin ne?” Yadda yayi tambayar he look like innocence, cikin matukar shakkar shi tayi baya.
“Ina son nayi amfani da wannan damar na gaya miki You are so cute” Wayyo Allah, wani narkewa tayi, sannan ya juya yana kallon Alhaji Musa Me Gari, yana mishi gargadi tare da nuna mishi yar shi.” Sannan ta wuce. A hankali ta bi bayan shi da ido, ba karya he look hot and sexy. Kamar munafika ta wuce abinta.
Shiga mota yayi yana sauke ajiyar zuciya.
“Kai banza dan daudu kunna min Mandula”
“Not in my car!” Brrst Bashir Zayn Malami ya fada cikin daurawar fuska.
“Hm! Kawai ce min jobless” shiru Brrst yayi bai tanka mishi ba, dan yasan ba abu ne me wuya ba, ya yarfa shi ba, haka suka isa yana murde mandular shi, har suka shiga cikin gidan.
Tun a bakin kofar main falor ya hadu da Mahaifin shi, cikin matsanancin bacin rai ya kunna tv.
“Abin da muke fama da shi kenan, dan gidan sakataren shugaban kasa Alhaji AbdulMalik Zain Malami bamu isa muyi wani abu ba, idan yayi laifi yana da daurin gindi a gwamnati.”

“Aikin kenan!” Ya fada yana d’aga kafadar shi.
“Zayn!!”
“Yes dagus!” Wani sabon bakinciki ne ya kuma rufe Alhaji AbdulMalik.
“But you know what you”
“Abba ba laifin shi bane sanata Musa Me Gari ne fa ya haɗa kome.” Inji Abul Khair.
“Kai ma ya saye ka ne da baki?” Ya kalli dan uwan shi.
“Bashir kana ganin abinda Yaron nan yake min? Talatin da wani abu babu aure babu aiki?”

Wata dabi’a da Zayn yake da ita shine matukar Baban shi zai fusata toh, ko shine da gaskiya zai kwantar da kan shi yayi ta bada hakuri, yawan nada hakurin zai saka ka dauka ko gobe ba zai kuma ba, kuma zai kuma zai ba da hakuri,
“Allah ya huci zuciyar ka Abba” daga haka bai kuma cewa kala ba, sai shigowar Hajiya Umma.
“Towwww! AbdulMalik! Cinye shi kake da bakin ku na yan siyasa? Tun daga cikin gidan na zata a gidan rediyon ake magana ashe shalele ka saka a gaba, kai taso muje na baka laula maganin baki domin ba zan so a cinye min kai da baki ba, na shiga duniya na rasa wurin zama ba.”
Ta janyo hannun Zayn tana watsawa Abban shi kallon banza.
“Muje yau zan bar gidan AbdulMalik na huta da gorin da yake maka nq ka fita Zakka a cikin gidan nan!” Ta fada tana jan hancin ta,
“Hajiya kiyi hakuri!”
“Nice hawainiya! Ai ko A musulunce nima mahaifiyar ka ce, idan na D’aga maka nono zai bika, balle shi da na haifa. Su Yara bin su ake da addu’a ba da bakin cin goro ba, waye zai ce bai san halin dan yau ba? Koda na tsufa ai nasan me nake yi, wai ma tukun kai dan kaniyar ka baka yi amfani da kariyar nan bane ka dirke yar mutane da ciki?”
“Hajiya umma”
“Toh ai dole na tambaye ka ko Uban masu gida. Allah ya jikan malami, mutumin kirki, kai ma gadon shi kayi domin ba karamin kuzari ne da kai ba, ikon Allah toh amma an zubda cikin ko?”
“Hajajju bafa ni nayi mata cikin ba, sharri aka makala min”
“Haba dan albarka ko nace, ai nasan kaf garin Kaduna babu na Allah irin ka da ce iyaye zasu fahimci irin baiwar da Allah yayi maka na son addini da ibada ba zasu zarge ka dan ka saka gajeren wando ba”

“Hajiya!”
“Na’am Zainu!”
“Yunwa nake ji!”
“Toh dan albarka, tabawa!” Ta kwalawa me aikin gidan kira, da sauri matar ta shigo tana yarfe hannu ta, da take wanke Allahu.
“Hajiya Umma gani”
Daukar medical glass dinta tayi tana kokarin sakawa ta kalli fuskar tabawa ta ce mata.
“Malami yana son cin abinci me yau aka mana?”
“Hajiya umma ai tuwo ne miyar ganye ban kammala ba”
Cikin kwantar da murya ta ce mata.
“Haba tabawa, tun yaushe ake girki a gidan nan ba a gama ba har yau? Salon nayi magana kice nayi hakuri”
“Kiyi hakuri wallahi Muhideen ne ya mai da min aiki ba, ba dafa mishi”

“Toh Allah ya kyauta, ki cewa talatu”
“Hajjos bar shi naje da kaina kinsan na mata laifi”
“Allah sarki dan Albarka ai ni na jima da sanin Allah yayi baiwar tausayi a ranka da haka yara suke ba zan yi kaico da yaran gidan nan ba” ta fada cikin takaici.
Mikewa yayi sannan ya fita yana wani uban tsalle wanda ya zame mishi dabi’a da al’ada kamar wanda ake cilla shi da karfen mayyen karfe.

Da wani irin kaunar shi da Tausayin shi take bin shi, akwai abinda ta sani ya zame mata dole kaunar Zayn Malik, ya zame mata dole kiyayye kome, ya zame mata inuwar Gajimare, ya zama farin cikin ta a lokacin da ta rasa nata. “Zaynu” ta furta a hankali.

“Wallahi Mama ba zan iya zuba ido yana zubar da mutuncin gidan nan ba, haba don Allah akan shi aka fara samun farin ciki?”
“Kulu! Bana son haka” shiga cikin falon yayi da sallama, cikin kauna da farin cikin ganin shi ta zuba mishi ido. Tsayawa yayi ya zuba hannu a cikin Aljuhun gajeren wandon shi, mikewa tayi ya nufi hanyar kitchen, a hankali ya shiga takawa falon.
Yana zuwa wurin Yar shi ya ce mata.
“Ki gayawa mijin ki ya sauya Uban daki, idan ya cigaba da bibiyar Musa Me Gari toh wallahi sai na karya mukamikin shi” ya D’aga kafada yana wucewa kitchen.
“Banza dan jagaliya”
“Na yarda shi yasa ya boye Miki gaskiyar ya ajiye mistress a kinkinau ba” ya fada yadda ita ɗaya zata ji.
“Zaynnnnn!” Ya shige abin shi kitchen din.
A hankali ya samu tana Juye abinci a trey, tana ajiye kome a wurin shi, zuwa yayi ua daura kan shi a kafadarta.
“Mama!”
“Zayn Malik!”
Ta kira shi,
“Am sorry!”
“You didn’t right”
“But” juyawa tayi ta mika mishi trey din daidai shigowar Kulu.
“Mama!! Kice ya maimaita abinda ya fada!”
Kallon Zayn tayi sannan ta ce mata.
“Duk abinda zai fada yana kan hanyar gaskiya. Babana sake fada”
A shagwab’e ya ce mata.
“Mama mijin ta mistress ya ajiye a kinkinau, sannan babu amfanin kullum tana hanyar gida”
Ajiye trey din yai sannan ta ce mata.
“Mama me ta rasa? Degree biyu gare ta, sannan bata haihu ba tana zaune tana bautawa wani kato yana tara yan mata suna abinda suke so. Ahhh am so curious matsamin na wuce ban da uncle Bashir yana dakatar dani dan uban mutum tuni ban karya mishi kwankwaso ba.”

“Kayi magana in loyalty mana ai kaine kasa da ita” ajiye abincin yayi kafin ya Kum dauka ya fita abin shi, murmushi mama tayi sannan ta ce.
“Ya tsaya a cikin gidan ya tsaya a waje taya ba zan kauna ce shi ba?”
Yana fita side din shi ya wuce, a barandar da zai kai shi side din shi yaji muryan Ghali mijin Basmah sai D’aga murya yake, ajiye trey yayi ya nufi wurin, Mami sai hakuri take bashi. Kowa a wurin hakuri ake bashi, amma kamar wanda ake tunzura shi.
“Dan iskanci nace taje tayi family planning amma ta kuma ɗaukar wani cikin, wallahi ba zan dauki nauyin cikin ba sai dai a zubar” ita kuwa abin tausayi sai kuka take Basmah.
“Idan ta zubar ta min waya nazo mu koma”
Shiru yayi yasan qanwarsa da Mami ba jika take ba, amma ganin yadda Abba ya sunkuyar da kai ya bashi haushi.
Yana zuwa ya cakume wuyar Ghali kamar zai damfara shi da ƙasa.
“Dan Uban ka waye ya hana baka je an cire maka jijiyar ka ba? Dan akuya shi ne da mutuncin uban mu zaka zo ka yarfa shi? Waye ya mata cikin”
“Alhaji Zayn wallahi Ni ne! Alhaji Zayn duk abinda kace na rantse daga yau nabi Allah na bika”
Sauke shi yayi yana gyara kwalar rigar shi.
Jan hancin shi yayi, sannan ya juya tare da rike kugun shi.
“Ka ganta?” Cikin fusata ya wani dunkule hannayen shi, kamar dai rufe shi da duka.
“Sabida su ko kallon yaran wasu bana yi gudun kar a musu abinda nake yi! Idan kaga ba zaka iya aure ka tara iyali ba me yasa tun farko ka fara? Kannena mata jin su nake kamar na goya su ba baya, shine kazo kana mishi ihu akai, Mami na baka hakuri kana kuncewa babban abu kazan uba, wannan ya zama karo na farko da na karshe,na kuma ganin ka a kofar gidan mu wallahi sai na karya kafar ka banza.”
“Allah ya huci zuciyar ka, wallahi an gama” da gudu Basmah ta nufi Zayn tana me rungume shi.
“Nagode Yaya” idanun shi ne ya cika da kwalla. Yana nuna mishi yatsa,
“Ka tafi gobe zan kawo ta” jan hannun ta yayi zuwa barandar ya ajiye ta a restchair dake barandar ya saka mata abincin.
“Yaya!”
“Keep quiet and eat” cikin shashekar kuka take cikin Abincin tana kallon shi, kokarin danne emotions din shi yayi ya shiga dakin shi ya dauko mandular shi, ya kunna yana zukar ta, kafin ya kunna wakar sahibin shi bomm Marley.
Yana gyada kai, yana kara jin ina ma da a zamanin bomm Marley yazo wallahi sai ya tafi har Jamaica, yana sha yana kara gyada kai a wakar shi me suna. Stand up. Sai wani jinjina kai yake kamar ya samu Abin yi.

Daga can baradan Hajiya Umaima da suke kira Mami ita ce take kallon shi, duk da ta tsani Zayn amma bai hana yau wanke mata rai ba.
“Haka yake,.ba iya abokan shi yake karewa ba hatta dangi da iyaye yana karewa, dazun kana fada dan ya daki Alhaji Musa Me Gari, toh kome shi ya shirya da fari na zata kawai yana adawa da kaine dan zaka fita karar Gwamna yanzun sai na kara fahimtar ai shi ka tsare mishi wani abu ne na daban. Ka gan shi can tsuma kan shi yayi a ruwa kawai”
Alhaji Uwaisu ya ce.
“Yaya ka nima mishi aiki mana, ya daina zaman gidan anan baki daya baba jin dadin abinda yake”
Kallon shi barista Bashir yayi sannan ya ce mishi.
“Yaya Uwaisu Meye laifin shi? Yana da degree a fanin kimiyya da fasahan na’ura inda yayi karatu a jami’ar Boston na Amurka. Sai me aiki ne yaki!”
“Amma ai ga Khalid nan matar shi haihu na biyu zata yi ko Bashir? Ni da kaina na tura shi aikin soja shekara uku da suka wuce aka Kore shi, ko sai sa nayi magana da AAM akan shi ya ce takardan shi yana nan an dakatar shi ne idan har yana bukatar aikin shi zai dawo. Na nima mishi aure ya watsar me kake so nayi mishi?  Hajiya da kai da Talatu kuka lalata min Yarona wallahi”

“Shiru ma alamar magana ce Allah ya baka hakuri idan zan tafi Demark zan tafi da shi haka yayi maka?” Inji barista Bashir,
“Toh duniya ba yarda Alhaji ka mishi magana ya dawo min da Y’ata ban yarda da shi ba wallahi tsoro yake bani”
“Sai kije ki dauke ta” Alhaji AbdulMalik Zain Malami ya bata amsa,dama sun saba haka takan ce yana fifita Zayn akan Yaran ta, shi yasa take kara tsanar shi a kullum kamar ta kashe shi. Hajiya umma tana yawan gaya mata cewa.
“Ayayinda kika kare tsanarki da hassadar ki, toh anan ne Allah zai nuna miki shi yake sawa yake hanawa”

Sannan ita kanta ba zata ce ga Exactly abinda Zayn yake mata ba, amma ta tsane shi, kuma tsana me karfi.
“Ke Basmah zoki wuce, kar ganin abinda aka miki ki zata ba za a iya turmushe ki bane” lumshe idanun shi yayi yana kara jin tana burge shi, duk abinda zai mata ba zai taba burgeta ba, dan haka cikin natsuwa yake zurka mandular shi, ya dauki trey din da ta gama cin abincin ya nufi cikin gidan da shi, bayan ya kashe wiwin. A kofar kitchen din waje ya ajiye sannan ya juya zai tafi aka ce mishi.
“Huuuu!” Kallon ta yayi kafin ya rab’a gefen ta ya wuce.
” Ya Zayn sabida kai nazo”
“Dake kiran ki nayi ba?” Ya yab’a mata bakar magana.
“Hmm Ya Zayn kasan yadda na damu da kai”
Sai da yayi shiru kafin ya wuce abin shi.
“Baka san yadda na damu da kai bane?”
“Ai ni ba ciwo bane da zaki damu kanki da Ni!”

“Amma ka yi smoking?”
Shiru yayi domin ya fara gundurar da tambayar ta.
“A’a hura wuta ake a kirjina shi yasa nake kaurin hayaki”
Kallon shi tayi tare da cewa.
“Allah ya baka hakuri sai an jima”
Banza yayi da ita sannan ta wuce side din shi ya rufe kofa, ban daki ta shiga ya kwace kaya, sannan ya zauna ya cika ruwa kafin ya shiga cikin ruwan ya zauna, sai da yayi wanka sannan ta shirya ya nufi masalaci dukda ya rasa sallolin shi amma a masallaci zai yi sallah, a can yayi har sallah shafa’i da wuturi, yasan yau yayi abu mafi muni baya wasa da sallah duk inda zai shiga baya wasa da sallah lokaci biyar din nan, koda ya idar kwanciya yayi a cikin masallacin yana azkar har barci ya dauke shi. Dake masallacin a cikin gidan yake wurin sha biyu saura ya farka bayan yayi addu’ar tashi barci, sannan ya nufi side din shi yayi wanka sannan ya kuma shiryawa cikin wasu fitinannun kayan wanka, ya saka turare ya dauki key mota ya fito zai tafi, a bakin kofar gidan ya hadu da Abba.
Dauke kai yayi sannan ya shiga cikin motar ya bata wuta,  a hankali yake Bin karatun Sheikh Abdulrahman Gwangola.
Tafiyar minti talatin ya kai shi club, yana parking motar ya nufi wurin shiga yana shiga aka fara ihu.
“Zayn Malik!!!!!” D’aga hannu yayi sannan ya wuce ya nime wuri ya zauna yana me daura daya akan daya.
“Hi Baby!” Wata yar gajerar budurwa ta D’aga mishi hannu tana sanye da wata bakar short gown,  yadda take tafiya tana juyi zai tabbatar maka da babu ko dan kamfe a cikin rigar. Dauke kai yayi yana kallon Abul da yake romance da wata kirista, dauke kai yayi yana kallon wayar shi.

Zama yarinyar tayi tana son.matsawa jikin shi amma yadda fuskar shi tayi ta shanun nan ya sara kulawa ta mike tare da barin wurin, a hankali suka gama lashe juna sannan ya dawo wurin Zayn Malik suna tafa.
“Kana jin dadin kodimo?”
“Bari chilling akwai dad’i ita ta kawo min kanta, toh laifi ne idan nayi abinda take bukata….
PAID BOOK

_….ZAYN MALIK….✿_

*EXQUISITE WRITERS FORUM*

Mai_Dambu

*FREE PAGE♡*

CHAPTER-03
Kiss and Kill

بسم الله الرحمن الرحمن
Murmushi yayi tare da kallon abokan su da suke tawowa da sauran yan matan su, kafin ya kalli waiter na cikin bar din.
“European whisky”
“Ok sir Malik”
Kallon mutumin Bassam yayi, sannan ya gyada mishi kai, a hankali mutumin ya gyada kai.
Dauke wuta club ɗin yayi kome ya tsaya cak, yan mata da samari suka fara ihu,
Haske aka kunna akan Inayat Musa Me Gari, sanye take da korean sweatsuit iya gwiwar, takalmin kafar ta hill ne na gucci, a hankali ta cire scarf na wuyar ta, ta mikawa kawarta sannan ta kuma mika mata poser na takalmin,.kafin ya fara saukowa a hankali. Kallo daya yayi mata ya dauke kai.

A daidai lokacin da aka ajiye mishi whiskey din, dauka yayi a hankali ya fara sha. Kasancewar inda yake daga shi sai abokan shi yasa babu me iya hango me suke yi suma abokan harkan gaban su suke, tana zuwa ta isa gaban shi tare da cire sweatsuit din, daga ita sai wani mugun riga wanda yake da tsago har kan shafaffen cikin ta, babu abinda ya tare sai boons dinta, zama tayi akan center table din gaban shi ta daura kafarta akan lap din shi, a hankali take squeezing din lap din shi. Kallon shi tayikamar baisan me take yi ba,.asalima ko kallon inda take baya yi. Mika glass din da aka zaba mishi whiskey yayi, kafin ya riko igiyar shisa. Ya fara zuka a hankali.

Idan ka cire wiwi da yake zukarta a gida toh bayan nan baya shan kome a cikin gidan su sai mandular shi, mutum ne me iya boye shaidancin shi, ha bayyana halayyar shi na rashin mutunci. Uncle Bashir yasan yana shaye shaye,. kasancewar ya zauna da shi a Boston, ya kuma san cewa bai mai da shaye-shayen abinda zai hana shi ibada ko wani abu ba, kawai abinda yake kara burge shi da Zayn Malik shine baya niman mata, kuma bawai dan bai da desire bane a’a kawai halayyar shi ce haka mace bata gaban shi, ya karya zukatan yan matan turawa lokacin da yake nan Boston, wasu kuma sun yi kokarin ma su bashi hadin kai ya kwanta dasu kalaman shi ne.
“Duk tsiya bana fatan na haifi yar da wani zai lalata tarbiyyar ta, haka bana fatan na auri matar da wani ya gama da ita sai dai idan tazo cikin destiny dina zan karbe ta a haka, ina da kanne ina tsoron taba Kanwar wani kar a taba kanne na mata”

Wannan shine abinda ya sa sam Zayn Malik bai taba yunkurin sake layi ba, amma fa yana shawu ba balai, kawai ba kome yake tab’awa ba, a hankali ta cire takalmin kafarta, sannan ta fara goga mishi kafarta, tun daga kan kwanjin shi har zuwa laps dinta tana wani irin juya kanta, a hankali kafarta ya sauka a tsakanin cinye shi da ma sana’antar sadarwan shi, a lokacin ne ya rike kafarta, yana kallon Chain din kafar na zinari ne, sai ytsar kafarta akwai zobe siriri. A hankali ya sake tare da fisgota ta dawo jikin shi, kirjinta yana tana kirjin shi.
“Are you Lesbianess?” A hankali take shafa kirjin shi tana wani narkewa.
“Yeap amma jiya abinda kayiwa Daddy ya sani samun abokin rayuwa, please can you be my partner?”

“In capital letter no” ya hankad’ata ya mike a hankali,  mikewa tayi tare da fadawa kan shi.
“Tunda na shirya nazo nan domin ka, ka zata zan juya na koma ne, ina bukatar ka tun daga kan kyakkyawar surar jikin ka. Look at me me kake bukata?” Ta kai bakin ta wuyar shi tana sauke wani irin nishi. Kafin ta riko hannun shi ta saka akan cinyar ta.
Janye hannun yayi sosai yana me kai bakin shi kunnen ta.
“Bana harka da macen da ta kawo kan ta, domin ban san maza nawa suka saka mine din su a jikinta ba. Am always like my pleasure” daga haka ya mike da ita ya saka mata rigarta sa ta cire.
“Zayn Malik ba saka amshi tayi na ba, just 30 mins”
Dawowa yayi cikin takun kasaita, ya kalle ta.
“Ba iya computer na iya amfani da shi ba, hatta Idanuna suna yawan aiki akan wadanda nake tare da su. Keda Bassam ko? Hmm ai shi waiter din Yarona ne, look” ya nuna mata bayan ta. Hasken club ɗine ya dauke, sannan aka kunna katon tv.
“Ina son ka bani hadin kai nayi dragging din Abokan ka Zayn Malik to the hell. Zan biyaka kudi ko nawa ne, zan nuna mishi nima y’ace” juyawa aka yi kanta da hasken club ɗin.
“Oga Malik ka bamu damar koya mata hankali”
A hankali ta kalle shi sannan ta juya tana kallon mutanen da suke ihu a bar su, d’aga musu hannu yayi sannan ya kalle ta, ya mika mata kayan ta, suka fita.
“Idan nace zan yi amfani da fushina, babanki babu wanda isa ya kalle shi, kin ganni nan sai da nayi kwana uku ina tsaye a barrack sabida laifin gudu daga aikin soja, ya kike tsammanin idan na kama mutum zanci Uban shi?”
Shiru tayi domin yana kara kashe mata jiki ne, yadda yake maganar so gentle tone.
“Look kafin ka yanke hukunci ka fara duba waye mai laifi waye mara laifi” a hankali ya bude matar motar ta, ya hankad’ata ciki, zai rufe da sauri ta  rike hannun kofar. Sannan ta fito tana kallon shi.  Gaban rigar shi ta riko ya ɗan sunkuyo kafin ya kai ga nazarin me zata yi, ta shiga bashi wani passionate kiss, me matuƙar tsayar da aikin ƙwaƙwalwa, rike ta yayi gam sannan ya shiga taimaka mata akan kudirin ta na kiss ɗin, har tana jiyo tsami-tsamin whisky din da ya sha, ga kamshin mint chocolate na shishan da ya sha, .manna ta yayi da motar kafin ya cigaba da sumbatar ta. A hankali yayi breaking kiss ɗin.
“You deserve my mouth!” A hankali ya janye daga jikin ta, ya juya abin shi da uban gudu ta bishi tana me rungume shi.
“Zayn Malik! Please be My partner” juyawa yayi yana kallon ta, sannan ta goga hannun shi a bakin ta.
“Idan na zama partner ɗinki zina zan yi dake, zan iya ajiye ki inta lalata dake, the end of the na naje na nimo kamilar mace na aura kina tsammanin nayiwa rayuwarki adalci? Kin ga shi bariki iya ce, Imma kwabarka tayi kauri Imma tayi ruwa goben ka ce abin dubawa, dan haka zaki iya tafiya.”

Ya juya abin shi, ya koma cikin club ɗin, kallon Bassam yayi sannan ya ce mishi.
“Nagode”
“Kai Zayn babu godiya,  kafin yau bani da kowa sama da kai, iyayena ma sun san da haka, ka bani rayuwa me kyau,” inji Bassam.
Jan hanci Zayn yayi, kusan haka ya zame mishi dabi’a, dan haka ya juya yana niman Abul Khair.
“Gayu ina Abul?”
“Ya fita chilling da wata yarinya”
Girgiza kai yayi yana faɗin.
“Ok zan ware, bana son na kai 2am a waje. Amma maganar gaskiya shine wallahi ku guji zina masifa ce, gara irin wannan rayuwar ta zuke zuke da ace kullum kana lalata ya’yan Jama’a, ya zaka ranar da aka yiwa naka?” Ya mike yana zuba hannun shi a cikin Aljuhun.
Sannan ya mika musu hannu suka yi musabaha, kafin ya nufi wurin bar din ya mika atm card din shi, suna cire kudin suka mika mishi suna godiya.
Fita yayi idanun shi ya sauka akan motar Abul, dan uban motar motsawa take da kanta, zunzurutun yadda ake sex a cikin ta.
Tab’e baki yai sannan ya tab’a key motar shi, sannan ya bude ya shiga, tsabar haushi juyawa yayi ya daki tayar motar Abul.
Sannan ya shiga tashi ya tadda ita, a cikin motar kuwa, kwantar da sit Abul yayi, yana kwance da bayan shi yarinyar tana saman shi. Shi kuma yana rike da boons dinta yana squeezing dinsu, ita kuwa sai wani moan take.
“O baby fuck me! Please fuck me out of your mind”
Sama da kasa take mishi tana wani irin nishi, hannun shi ya mai da waisting dinta, ya shiga buga ta da karfin tsiya.
“Yes…. Yes… Oh shit haaaaa” ya sake wani irin Nishi yana ture ta a jikin shi, baki daya ruwan jikin yarinyar yana zuba a jikin shi, da sauri ya mike tare da saka tissue paper yana goge jikin shi. Hararan ta yayi sannan ta bude asusun motar ya ciwo rafa na dari biyu-biyu ya cilla mata,
“Out” ya daka mata tsawa, da sauri ta tafi ta, tana saka pant dinta a waje, shi kuwa cire condom din jikin shi yayi ya saka a cikin tissues din da ya goge jikin shi, sannan ya tadda motar shi yana jin wani iska yana yana shiga mishi.
—
_01:45am_
Ya shiga cikin gidan su a hankali yana kallon ko ina ma gidan ga security suna aikin su. Wucewa yayi part din shi, a hankali ua bude kofar ya shiga. Yana karewa falon kallo.

A hankali yake shaƙar kamshin wani turare na daban, dan girgiza kai yayi dan yasan baya cikin maye, dakin shi ya nufa, tare da kunna wutar dakin. Idanun shi ne ya sauka akan kyakyawar cinyarta farare kal-kal, a hankali ya kashe wutar falon yana mamakin me ya kawo Judaal Mustapha Umar part din shi. Juyawa yayi abin shi ya fita a gidan ya nufi part din Hajiya Umma, ya bude kofar kitchen ta baya, ya shiga bai tsaya ba ya haura sama, dakin shi da yake kallon nata ya shiga ya wuce ban daki yayi taking shower, sannan ya fito yana me daura kunce towel din shi,  ya bude closet na shi ua ciro boxes na kamfanin Puma ya saka. Sannan ya saka farin singlet na Kamfanin Vicky. Kashe wutar dakin yayi ya kwanta,  yana nazarin yanayin garin.
Kafin barci yayi gaba da shi,
**
Washi gari. Tunda ya dawo sallah asuba, ya nufi dakin gym din shi yana d’aga karfe, sosai yake d’aga karfe.

“Good morning Hero”
Bude idanun shi yayi ya zuba mata, sanye take da skinny skirt velvet, sai whiter shit haf vest, ta daura velvet jack, daga saman kirjin ta a bude yake daga kasa kuma a rufe, ajiye mishi trey din tayi, kan ta yane da whiter veil, komawa gefe tayi tana murmushi.
“Jiya kusan har 12 ina jiran ka” cigaba yayi da d’aga karfen shi.
“Hero babu wanda zai san muna wani abu da, we shall keep it for our secret”
Ta fada tana turo mishi kirji, wallahi shi kam mamakin yan matan zamani yake kowacce burin ta ya kwanta da ita. Kallon ta yayi sannan ya ce mata.
“Bani da lafiya”
“What?”
“Eh” kallon shi tayi kafin tace mishi.
“Kamar ua baka da lafiya? Bayan gaka garau”
Girgiza kai yayi sannan ya ce mata.
“I mean ni ba namiji bane!” Ya fada yana kara d’aga karfe. Sake baki tayi tana kallon shi ita tunda take a rayuwar ta, Zayn Malik kawai ta tab’a kawowa kanta, kuma ba ta’a sanin bai da mutunci ba sai yau, kamar zata yi kuka ta ce mishi.
“Let me make it, wallahi zan duba ko dq gaske ne baka da lafiya”
“You are very stupid!” Ya daka mata tsawa, yana nuna mata hanya.
“But Zayn kasan yadda nake son ka? Wallahi na san kowa yasan ina son ja but me yasa kake min haka? Please one more time” ajiye karfen yayi sannan ya mike tare da ɗaukar trey din ya taso keyar ta har kasa inda Hajiya da iyayen shi suke.
“Idan na kuma ganin ki a part dina kiyi kukan abinda zan miki wawuya kawai” yana fadar haka ya ajiye trey din ya koma sama, kuka ta fashe da shi, tana me nufar Hajiya Umma.
“Don Allah Hajiya ina son shi, wallahi ina son shi, amma ce min yayi shi ba namiji bane”
“Innalillahi wa’inna illahi raju’un! Haba shi yasa yaron nan bai damu da mace ba, ashe lalura gare shi. Innalillahi wa’inna illahi raju’un na shiga uku yaro karami da ciwon tashin hankali, Uwaisu Bashir,  AbdulMalik kaji ko? Na shiga uku ai dole na bazama niman magani, ashe lalura ne ya kama shi..”

Aikuwa ta zuba musu nueaju ganin babu wanda yayi hubbasar yin wani abu ta buga musu tsawa.
“Kun saka manyan kawuna a gaba ina magana kun bawa iska a jiyata?”

“Ayya Hajiya ya zamu yi halin Zayn yanzun zaki samu karya yake!”
“Laha’ilaha illallah lahu Muhammadu rasulillahi, yanzun Dai ga Judaal ta fada, ke me ya faru?”

Cikin shashekar kuka ta ce mata.
“Yace shi ba namiji bane bai da lafiya”
“Aha kun dai ji bai da kuzari, wato shi girman mutum a ido kawai yake amma batun lafiya kan babu ita, nayi karya ko?”
Cikin rashin ta cewa suka ce mata.
“Hajiya bafa da gaske bane”
“Uwaka Bashir nace Uwa. Aura Bashir zaka fita idona ko sai na saka kafar wando daya da kai? Duk yadda kuka Shaku da yaron nan amma da mugun abu zaka nufe shi, toh mugun abu ta bi dare, zaku kai shi asibiti ko sai na tattara na bar muku gidan ku na kama haya?”

Takaici ne ya kama Uncle bashir ya nufi hanyar dakin shi,.yana shiga ya same shi ya fito kenan daga ban daki kugun shi daure da blue towel kan shi nade da wani whiter towel din, sake yana jin ihun Hajiya tun daga sama.
“Kai wani irin mutum ne haka?”

“Ai sai dai aljani” ya fada yana kara rike towel din kan shi.
“Baka jin magana yanzu ka wuce muje zan kai ka asibiti tunda baka da kuzari”
Murmushi yayi sannan ya ce masa.
“Ka bani mace ce ta ce maka bani da kuzari?” Ya kafe shi da idanu.
“Amma me ka gayawa Jud?”
“So take na kwanta da ita nayi haka ne dan kare kaina laifi ne?”

“Ba laifi bane amma kuma Mahaifiyar mu bazata gane fun bane, Zayn Hajiya na Mugu son ka yadda ko mu Yaranta bata mana son da take maka”
“Are you feeling nervous?”
“No but am feel guilty yadda bata kaunar wani abu ya same ka?” Sake baki yayi yana kallon Uncle bashir, kafin ya tab’e baki yana cewa.
“Weldone” ya nufi closet din shi ya cire wata crazy jeans na kamfanin KG70, sai rigar kamfanin Adidas, polo, a hankali ya ajiye su sannan ya fara shafa body lotion na Jaguars yana gamawa ya ajiye sannan ya kalli Uncle bashir.
“Excuse me i need privacy zan kasa wando” ya fada a kule.
“Sakarai yaushe ka gama yawo naked”
Cikin fushi ya ce mishi.
“Are you jealous?”
“Allah ya rufa min asiri” ya fita yana mita.
Shima Zayn din mita yake yana saka kayan shi, yana gamawa ya fesa turaren BlackMan, sannan ya dauki takalmin shi canvas na saka, ya zare wayar shi a chaji, ya fara saukowa.

Cikin tsammanin tausayi take kallon shi yana saukowa a sama, abin tausayi yaro ashe boye mata yake he seriously sick. Dole ma ta kaishi asibiti da kan ta tayiwa likita bayani dalla-dalla yadda zai daura mishi maganin kuzari, sannan ta hada mishi da na hausa ai dole ma tayi kwafa….

Leave a Comment