A MAFARKI NASANTA 💫
In my dream I know her
By
Pha’eezah almustapha
Daga alkalamin✍️✍️Fa’eeh Bungudu
BISIMILLAH RAHAMANI RAHIM
Wanan shine litafina nafarko Dana fara wallafawa Allah Ina rukonka daka bani damar kamalashi lafiya kamar yanda nafarashi lafiya👏
*PERFECT ESSENTIAL WRITER’S ASSOCIATION
💫P.E.W.A💫
Home of Perfect Writer’s together we stand🤝
ESSENTIAL WRITER’S 📚🖊️*
Pen 🖊️is mightier than the sword🗡️*
Dedicated to my lovely sis Laila Almustapha Murai💔
Yaa Allah ina rokon ka kabani damar rubuta abunda Al umma zasu yi aiki dashi kuma su Amfana, kabani ikon rubuta shi cikin koshin lafiya na kammala shi lafiya👏👏👏
Warning!!!Banyarda wani ko wata su juyamin labarina ba ta kowace siga batare batare da an nemi izini na ba wannan dokace kuma duk wanda yayi ban yafe ba wannan labari kirkira ne bada gaske bane duk wanda yayi dai dai da labarinsa to yayi hakuri akasine. Daga cikin abunda littafi na ya kunsa
*Tausayi*
*zumunci* *zazzafar soyayya* *sarauta* *cin amana* *ta,addanci*
DASUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJINKAI
EPISODE 1️⃣
FREE PAGE1️⃣
Natsatssiyar budurwa ce ke tafiya anatse bata kallon komai face inda take sanya kafafunta, tayi nisa acikin tafiyarta kenan ta tsinkayi muryar wata budurwa na kwala kiran Halee! Halee! da jin wannan murya ta budurwar dake kwala kiran Sunan halee ko ba,a fada mata ba tasan khady ce tsayuwar ta da minti biyu sai ga khady ta iso inda take atsaye.
Isowar khady keda wuya ta furta haba Halee kinsan bakya da issashiyar lafiya ya za,ayi kije Aiken baba ta ta maimakon ki fada mata gaskiyar cewa baki da lafiya nasan zata k’yaleki ni sai intafi kinga ko yanzu gudo wa nayi bayan bayan tashiga bandaki,nasan da kin sanar mata da ni sai intafi koh haka ke da dadi ga uwar rana gashi bakya da lafiya,har taga ma mitar ta kyakkyawar budurwar nan da aka kira da halee bata tanka mata ba.. Daga ni dai yarinyar miskila ce😄 chan bayan kamar minti biyu haka ta cigaba da tafiyar ta kamar bataji abunda khady ke fada ba duk da kuwa tana jinta rass kuma tasan tabbas ko ba,a fada ba khady gudowa tayi tabiyo ta.
Da khady taga alamar ba tsayawa zatayi tabata kudin aikar ba na baaba tsaibe,kuma taga alamar yan miskillancin sun motsa dole haka tabita suka cigaba da tafiya atare har suka iso kantin da zasu yi siyayyar ta kayan miya
Sallama sukayi atare amsa musu sallamar tsohon dake tsaye akan tebir na kayan miyan yayi cikin sakin fuska Dan dama baba tsohon yasan su musamman halee ya saba da ita sosai tunda kusan kullum sai an aike ta yin cefane da sauran aikace aikacen akasuwa.
Washe baki tsohon yayi yana furta a,ah Haleematu sadiya ce kayataccen murmushinta tasaki jin ya ambaci cikakken sunanta Wanda mutun daya ne ke kiranta da wannan Sunan sai kuma mutun daya Wanda bata San ko wanene shi agareta ba Amma tabbas aka ambaci cikakken sunanta tana jin wani iri ajikinta
Muryar baba tsohon ce tadawo da hankalinta agaresa yana furta na nawa za,a bada cikin Dan murmushi ta furta baba tsohon ina wuni lafiya,ita ma halee haka amsa musu yayi duka yana dariyar halee aransa najin ga tambayar da yayi mata ga abunda ta furta masa shiyasa yarinyar tashiga ransa Dan akwai tarbiya gata kamila anatse kara mai maitawa yayi” na nawa za,a bada”cikin Dan yin kasa da kai ta furta acikin zazzakar muryar kamar ana busa sarewa ko algaitu gata da sanyi Wanda intana magana zakaji har tsikar jikin ka natashi na Dari uku da ta furta ne yasanya ni dawo wa daga sumar tsayen danayi tun lokacin da ta buda baki ta gaisar da tsohon.
Toh baba tsohon ya furta aleda ya saka musu baka ya mika musu sallama sukayi masa sukayi wucewar su, suna tafiya khady na zuba uban surutu alokacin da ita kuma Halee take ta zullumin komawar ta gida Dan tasan gamuwar su da Babah Asabe bamai kyau bace dan tasan sai ta mata fadan dadewar ta duk da dama ta saba,Amma yau da yakasance batajin dadin jikinta tana fama da matsanancin ciwon kai sai take jin shakkun yadda zata iske gidan,tana cikin wannan tunani sai ga hawaye shar😢 a idanunta gwanin tausayi Khady data lura da yanayin da take ciki ne duk da ba bakonta ganinta hakan Dan danan hankalinta yatashi Dan tana mugun son halee kamar jinin jikinta,da tausayinta cikin tausayinta ta furta haba Halee meyafu kuma, dan Allah kitsaida hawayen nan suna Sosa mun rai kuma kinga kan hanya muke kiyi hakuri nasan damuwar da kike ciki bata wuce sanin ko ke wacece bah da damuwar baabah ta ‘baaba Asabe’ kiyi hakuri in sha Allah komai zai zamo tarihi Halee nah hawayenta ta share mata wayenda ke tsiyaya a I danunta tana girgiza mata kai alamar ta tsayar dasu da kyar ta tsayar da hawayen ta ganin damuwa kwance akan fuskar Yar uwarta!tafiya suka cigaba da yi kowa da abun da yake sakawa aransa,babu Wanda yakara furta uffan har suka iso gidan,
Dan madaidaicin gidane suka tsaya kafin su shiga cikin dar dar musamman Halee gidane dai dai na talaka mai rufin asiri ginin bulo da filista zauren gidan suka tsaya suna shawarar Wanda zai fara shiga domin gudun abunda zasu tarar dakyar dai dukansu sukayi shahadar shiga da sallama abakunan su
Sallamar su ta ta katse ganin Baba Asabe na mitar rashin dawowar Halee akan lokaci da kuma fitar Khady bada saninta ba,
A hankali halee take ta durkusa gurin Yar matashiyar matar da bazata wuce shekara talatin da uku ba a duniya!Baba Asabe kenan wadda Sunan ta yake Lauratu amma mafi yawan mutane suna kiranta da Asabe saboda masifarta da ankira Baba Asabe za,a San itace Dan Sunan ta kaf ya bace.
Cikin sanyin muryarta da yazame mata jiki tace baaba ga kayan miyar kinga na dad’e koh wallahi Baba tsohon ne mun tarar da layi agurin sh…uwar hararar da baba Asabe ke sakar mata ce tasan ya ta yin shiru badan ta shiryawa hakan ba,dama kanta adone yake dan bata son kallon cikin idanun manyanta musamman ma na Baba Asabe ….taci karo da hararar da take sakar mata,bata ida ganin tsawon hararar ba ta kara done kanta kasa cikin tsoron abun da zai biyo baya..
Kiran Sunan Allah take yi a zuciyarta Dan tasan yau tata takare sai ta sha rankwashi akai da gori kala kala da zagin da bata so zuciyarta ce taji tsinke tausayin kanta da kanta yakamata.
Bata ida gama tunaninta ba ta tsinkayi muryar Baba Asabe nama khady fadan binta da takeyi abaya inta aiketa duk da kullum haka suke muddin Baba asabe ta aiki Halee to tabbas in Khady tadawo sai ta bita sundawo tare koda kuwa dawowar su daga makaranta ne aka tura Haleen sai ta yi sand’a ta bita…
Baba asabe ce take furta wallahi Hadiza ki shiga taitayinki Dan ubanki na fahimci bakya game zancen da nake maki ace ke kullin sai kinsaka ni yakar baki ehh~bakinta har kunfa yakeyi saboda masifar da ke cinta dama Baba Aabe masifaffiya ce ta bugawa ajarida.
Wai nikam nace dama haka masu suna Lauratu suke ne??😂
Hankalin khady (Hadiza) yayi dubun tashi bata kanta takeyi ba Dan tasan karshen masifar kan halee zai kare. Ahankali ta furta innata kiyi hakuri ke dallah rufe mun baki sha shar banza kawai ana miki gata kina botsarewa,inji cewar Baba Asabe , aikullun haka kike cewa ayi hakuri tau Dan ubanki ki kara kiga yadda yadda zanyi da suyar namanki agidan nan takai karshen maganar tana ban kamata harara
Kiwuce ki cire uniform dinki kizo ki Debi ruwan zafi gasu chan nadora miki amadafa.
Toh Khady ta furta cikin tutse bakinta mai makon ta wuce sai ta tsaya taga yadda za,a kwashe da Halee tana jin tsoron tashin ciwon Yar uwarta Wanda take ganin hard a damuwa kesanya tashin sa,tana mugun son ta da tausayinta, gashi yanzu haka tana fama da kan daya zame mata al ada dan duk yatashi tana wahala sosai wasu lokuttan har suma takeyi inyatashi saboda yadda take samun high temperature.
Bayan Baba Asabe tajuyo kan Halee wadda ke durkushe har yanzu bata daga duk da yadda rana ke gasata ga sumintin yadau zafi hawaye take zubarwa na tsoron masifar ta Baba Asabe Dan tasan kanta abun zai dawo ya kare ga ciwon kanta da ke ta kara hawa jikinta sai kara dumewa yake yi da zafi..hawayene shar suka zubo a I don ta suna sauka abisa kyakkyawar fuskarta.
Mu hadu a next page domin jinya zata kaya tsakanin Halee da Baba Asabe
Me kuke tunani akan Halee??
Kucigaba da bibiyata domin warware muku duk wani tunanin ku.✌✌
Yawan like dinku da comment shi zai tabbatar mun da kuna bibiyata,in har naga comments da like da yawa zan kara muku yawan pages.
Nasan zaku ga chanji na sunan Baba tsaibe da yakoma Asabe ga wadanda suka fara karantawa babu editing
💫A MAFARKI NASANTA💫
in my dream I know her
By
Pha’eezah Almustapha
Daga alkalamin✍️✍️fa’eeh Bungudu
*PERFECT ESSENTIAL
WRITER’S ASSOCIATION
💫P.E.W.A💫
home of perfect writer’s together we stand 🤝
ESSENTIAL WRITER’S 📚🖊️*
Pen🖊️is mightier than the sword 🗡️*
EPISODE1️⃣
FREE PAGE2️⃣&3️⃣
Typing📲📲📲
Gefen hijab dinta tasanya ta share hawayenta muryar Baba Asabe ce tadawo da ita daga maganar zucin da takeyi
Da masifa take furta munafuka algunguma wallahi bari kiji duk ranar da kika kara bari Hadiza tabiki in na aike ki wallahi ko na lahira sai yafi ki jin dadi sha sha marar asali kawai tsintacciya yar gaba da fatiha wadannan kalmomi da Baba Asabe take yawan furta mata suna daga mata hankali sosai fiye da zaton mai tunani duk ranar da Baba Asabe ta furta su agareta sai tasha kukan ta ita kadai alokacin kuwa Khady ce kawai ke iya lallashinta.
Har tunani take yi anya kuwa ita badaga sama tafado ba,wasu lokuttan kuma takanyi tunani kodai ita din yar gaba da fatiha ce kamar yadda Baba Asabe ke yawan furta mata,tunani barkatai dai ke shiga akanta aduk lokacin da ta tunano da kalmomin masu muni agareta sai dai kawai takori shaidan da Addu,ar neman tsari daga sharrin zuciya.
Dan tun Tashinta gidan wayennan kalmomin su suka bayyanar mata da ita din wacece agidan Baba Adee tun alokacin da ta fara mallakar hankalinta ta fahimci cewa ita din ba jinin Baba Adee bace da Baba Asabe sai dai duk da cewa ta fahimci komai akai bata taba gigin tambayar dayan su asalinta ba dan gudun maganar da zataji wadda zata iya saka ta rasa rayuwar ta wadda ayanzu take maleji da ita,Barema koda zata tambayi Baba Asabe baza ta iya sanar mata da komai ba domin koda Baba Adee ya kawo Halee gidan bai sanar da ita komai akanta ba,yadai sanar mata ya tsinceta ne akan hanyar shi takomawa gida tsakin gusau da furfuri dake jihar zamfara wannan kenan.
Cigaba….
Maganar da Baba Asabe ce keyi tadawo da ita daga dogon tunanin da tashiga na munanan kalmomin da Baba Asabe ta furta agareta Baba Asabe ce ke furta sakarya munafuka ana magana kina sunne kai kamar takwarai sha sha sha ballagaza kuma wallahi kinji narantse na kara aikarki kika dade sai kinci ubanki, mtssw taja uban tsaki tawuce warta fuuuu.
Kamar ance tajuya tahango Khady tsaye itama tana tsiya yar da hawaye kamar yadda itama Halee take zubar da nata hawayen
Yau nina naga ikon Allah inji cewar Baba Asabe wai ke Hadiza Uban me kika hada da yarinyar nan ne ehhh sha sha wuce kiban guri ko in tattakaki anan mtsww tana sanya hannu ta warci ledan kayan miyar ta shigewar ta madafa tana mitar ita kadai,Ta dora sanwar rana dan dama duka aikin gidan Halee ce keyi toh yau ma anyi lattin dora girkin ne kuma tasan Baba Adee yana nan dawowa bada jimawa ba shiyasanya ta kyaleta bata tilas ta mata yin girkin ba.
Alkalamin✍️✍️
💫💫fa’eeh bungudu💫
💫A MAFARKI NASANTA💫
Bayan shigewar Baba Asabe a kitchen Khady tayi sauri ta matso inda Halee ke durkushe tayi zukunnin rakumi cikin uwar ranar da ta bude tana ta faman zubda hawaye ga hannunta dafe da kanta dan tun lokacinda Baba Asabe ta zage ta da kalmar dan ubanta kanta yakara sarawa bayan jin wadanchan kalmomin na farkon Baba Asabe take yawan furta mata na marar asali tsintacciya bayansu babu abunda ke kona mata rai kamar azagi mahaifinta da mahaifiyar wanda ko da za,a yankata bazata iya cewa ga yadda kamanninsu yake ba ko tana da iyayen oho?Amma duk aka zagesu tana jin bakin ciki marar misaltuwa wanda bazai fadu ba,tana sonsu duk da bata taba ganinsu ba ko jin labarinsu.
Dafa kafadanta da Khady tayi ne yadawo da ita daga dogon tunaninta dakuma kara gudun ruwan hawayenta wanda zuwa yanzu kukanta yafara karfi har da shessheka dago lulu eyes din ta tayi wayenda suke dauke da zara zaran eyelashes masu tsarin kyau masu dauke da kwarjini farare tass dasu kwayar idonta har wani walkiya take yi na farin cikin idanun nata,A yanzu kuwa sunkoma jajaye saboda damuwa da ciwon kan datakefama dashi ga kuma kukan da tafara yi.
Zararan eye lashes nata sunkara curewa guri daya saboda ruwan hawen da suka jika su,Khady kuwa tunda suka hada idanu da Halee taji guiwoyin ta sun sage dan kuzarin datake dashi taji ya gushe,tausayi Babbar kawar tata kuma wadda tazame mata yar uwa wadda takejinta kamar tsoka da jininta.
Ahankali ta furta Halee! kanta ta kara dagowa akaro na biyu bayan mayar dashi kasa da tayi tana tsiyayar hawaye da idanu Khady tama alamar ta tashi suje daki tunda tasan yanzu bata bukatar wani dogon zance saboda ciwon kanta gashi taji jikinta yakara daukar zafi sannan in Baba Asabe ta iskosu wata masifar ce sabuwa wadda kuma take tunani ayanzu kwakwalwar Halee bazata iya dauka ba,Hannunta ta mikamata Halee bata ce komai ba takama hannun Khady ga gamn ta rike.
Ahankalin suke takawa kowa da tunanin da yake yi azuciyarsa harsuka isa dakin da yake chan gefe mallakinsu su biyu
Baba Asabe da duk taga komai …..✍️✍️✍️
💫A MAFARKI NASANTA💫
daga Alkalamin✍️✍️
💫fa’eeh bungudu💫
please like share & comment
💫 A MAFARKI NASANTA💫
in my dream i know her
By
Pha’eezah almustapha
Daga Alkalamin ✍️✍️
💫fa’eeh bungudu💫
Dedicated to my lovely sis laila Almustapha murai💔
*PERFECT ESSENTIAL WRITER’S ASSOCIATION
💫P.E.W.A💫
Home of perfect Writer’s together we stand🤝
ESSENTIAL WRITER’S📚 🖊️*
pen 🖊️ is migthier than the sword🗡️*
EPISODE 1️⃣
FREE PAGE4️⃣
Typing📲📲📲
Bata ce musu kala ba har suka shige dakin tsaki taja mtssw tana furta yarinya sai kace mayya da shegen taurin ran tsiya ace duk wahalar da nake gana mata bata sanya ta guduwa daga gidan nan ba mtssw takara jan wani tsakin tana furta mayya kawai tun randa tazo gidan nan Baban Hadiza samun shi ya ragu gashi komai shi shalelensa dan naman miyar ma da muke samu da yawa ya ragu ada daga ni sai hadizata yanzu kuwa takai karshen maganar cikin jan dogon tsaki wanda Yafi nadazu tayi shigewar ta daki tana cigaba da masifarta ita kadai
Nikam nace Baba Asabe shi naman miyar halan dai bakisan sauyin ubangiji ba 😇
💫fa’eeh bungudu💫
Halee da Khady shigar su daki keda wuya dukkaninsu suka samu guri suka zauna kowa rai ba dadi musamman khady wadda take jin haushin abun da mahaifiyarta keyiwa Haleen.
Matsowa Khady tayi inda Halee ke shingide gefen katifarsu data sha gyara kamar gadon Amare🤩
Zama kusa da ita tayi tare da kamo Hannunta daya ta furta cikin tausayin Haleen kiyi hakuri kibarwa Allah komai ninasan Babata bata taba kin kiba har cikin ranta kawai dai shaidan ne ke zugata da kuma sharrin wani yanki na zuciyarta dan yin shiru tayi kafin tacigaba da magana Halee! dago kyakkyawar fuskarta tayi ta kalli Khady ….banason Son ina ganin damuwa abisa kyakkaywar fuskar nan taki,Mai sanya samarin zamfara hadarin titi😉
Tunda Khady tafara magana bata tanka mata ba amma maganar ta takarshe sai da tasaka ta yin wani kayataccen murmushi wanda har sai da two side dimple dinta dana kasan gemun ta suka lob’a gwanin burgewa.
Itama Khady Murmushinta tasaki mai kyau wanda har cikin ranta yake nuna tsantsar farin cikinta naganin murmushin yar uwar tata Halee wanda yake ba kullum take yinsa ba duk da fuskarta irin ma,abociyar yalwar murmushi ce kamar ta junaid Abban sojoji😄Amma damuwa ta hana ta bayyanar da asalin annurin Fuskarta.
💫Fa’eeh Bungudu💫
Dama Khady tasan tabbas ta furta mata irin wannan kalmar sai ta yi murmushi,ita abunda ke sakata yin murmushin gani take bawani kyau ne da ita ba kamar yadda Khady ke yawan fada mata da kuma classmate nasu,saboda ba kullum take samun damar duba fuskar ta ta ba Amadubi dan cewa take bashine agabanta ba,ita gani take kyawon da duk ake fada tana dashi nabanza ne saboda kyawu ba asali baida amafani acewarta,ita yanzu sanin asalinta ya fiye mata kyawun komai agareta a cikin duniyar nan.
So dayawa in Khady ta matsamata da cewar tana da kyau na fitar hankali takan cemata “kyawu ba asali babu amfani” kuma da ta fadi wannan kalmar sai ta fashe da kuka Khady tayi ta aikin lallashinta Yanzu ma khady bata matsa mata da wata maganar ba dan gudun karamata damuwa…..
Wash hannu nah wallahi typing wahala 🥹
kuyi manage da wannan ba yawa
Mu hadu a next page domin kara warware muku matsayin Halee agidan Baba Adee
Kuyi hakuri da sauyin dakuka gani🙏
Masu comment da like ina godiya🙏🥰
khadseen🥰
Halimatu B Auki🥰
💫fa’eeh bungudu💫
Pls like share & comment
💫A MAFARKI NASANTA💫
in my dream i know her
By
Pha’eezah almustapha
Daga Alkalamin✍️✍️
💫fa’eeh bungudu💫
Dedicated to my lovely sis laila Almustapha murai💔
*PERFECT ESSENTIAL WRITER’S ASSOCIATION
💫P.E.W.A💫
Home of perfect Writer’s together we stand 🤝
ESSENTIAL WRITER’S
📚🖊️*
Pen🖊️is mightier than the sword 🗡️*
Proud of my first my novel👌
*JIN JINA TA💪💪 MUSAMMAN ZUWA GA BABBAR KUNGIYAR MU*
💫P.E.W.A💫
Ina alfahari daku musamman uwayen gidana🏢
*MHIZ BAREEMAH* (marubuciyar yan biyu macizai ne) the twins snake🐍🐍
*OUM AMJAD* (marubuciyar yan biyu)the twins👭
EPISODE1️⃣
FREE PAGE5️⃣
TYPING📲📲📲
Kawar da shirun nasu tayi ta hangar ta hanyar furtawa Halee kitashi ki watsa ruwa bari indebo muna ruwan zafi tana gama fadar haka ta cire hijabin uniform dinta tayi waje.
Bayan fitar ta daga dakin Halee ta tashi daga kishingid’en datake tacire hijabinta ta nad’esa Sa tasanya acikin acikin sip dinsu wadda Khady bata ya mutsa ba,sannan ta jawo zanen da take wanka dashi tayi tadaura bayan ta cire kayan jikinta tasanya acikin basket na Tara datti Dan karamin hijabinta Wanda take wanka dashi tasanya ta cigaba da gyara kayan da duk suke ahargitse acikin sip dintasu Wanda Khady ce ta ya mutsa su dazu da zataje makaranta..
Tana cikin gyaran sip d’in ne sai ga khady tadawo da ruwan acikin small bucket bayan ta amsa mata sallama ne
Ta Tsinkayi Muryar Khady Tana Furta nidai Halee kibar gyara kayan nan kinga baki da lafiya duk da naga yau jikin naki da sauk’i nazata sai munje asibiti ~takai karshen maganar fuskarta da alamar damuwa
Hararar wasa wasa Halee tasakar mata tana idasa lankafe hijab daya daya rage saura ta gama,Ahankali ta juyo ta dauki ruwan zafin da Khady ta ajiye mata tare da furtawa Khady karki damu Sisi nah nafara zama strong women tayi maganar ne cikin sanyin muryarta da yazame mata jiki takai karshen maganar tana sakar mata kayataccen murmushinta mai Sa maza👨 had’ari atiti😎
—————————– 💫fa’eeh bungudu💫
Itama Khady murmushin ta mayar mata dashi bata k’ara cewa komai ba ta kama hangar da zata sadata da d’an madaidaicin toilet dinsu dake cikin dakin har ta kusa isa ta tsinkayi muryar Khady na furta “Halee kibari inzo in had’a miki ruwan tunda naga baki da karfin jiki tafiyar taki takara. Zama slowly”
Ko ayanzun ma murmushin Halee tasakar mata Wanda har kyawawan hakora ranta farare Tass suka bayyana gwanin burgewa,itama Khady Murmushin tayi tana furta ohh! Yau su Anty Halee yan sarautar sun motsa kenan girgiza kanta tayi tana kara sakin murmushi na mamakin halin Yar uwarta na rashin son yin magana.
Itama cire uniform din nata tayi tadaura zanen da wankanta tayafa katon mayafi tana ficewa daga dakin
————-
Tun akofar dakin nasu tafara magana cikin farin ciki take furtawa Baba Adee sannu da zuwa saboda tajiyo muryar shi lokacin suna magana da Khady.
A bangaren Halee kuwa tana shiga toilet din ta fara gudanar da wankanta cikin natsuwarta da tazame mata jiki duk da yadda ranta yake ba dadi….
“Dady sannu da zuwa” ya hanya?Muryar Khady ce ta ratsa tsakar gidan nasu har zuwa barandar da wannan dattijo yake azaune.
Murmushi wannan dattijon yi har takara so inda yake dattijon kirki Wanda sunan shi yake Abdul rashid Amma anfi saninsa da Baba Adee Wanda akalla zai kai shekara hamsin aduniya.
(wannan suna Khady ce tafara sanya masa shi alokacin tana karama bata iya fadin Dady kamar yadda Halee ke fadi sai ta mayar dashi Adee Wanda ganin haka yasa itama Halee ta mayar dashi Adee jin Yar uwar ta na kiransa haka)
Sai kuma sunan yabisa har na waje suka kara masa da Baba wannan kenan..
Har ta durkusa agabansa Murmushi ne kwance akan fuskar Sa ganin yadda ta turo baki gaba nak’in amsa mata sannu da zuwan da ta masa,Baba Asabe ce dake tahowa da amadaidaicin kofin silver domin kawo masa yasha ta furta kekam dai Hadiza meyake damunki ehhh!daga dawowar Sa sai fara turar masa baki kamar wadda aka daka tana magana tana tsiyaya masa ruwa akaramin cup shima na silver mai kyau
Kurb’a ruwan da Baba Asabe ta mikamasa kurba guda yace rabu da ita kinji dije,aiko ida rufe bakinsa baiyi ba Khady takara turekke bakin nan gaba….
Dariya yayi wadda take fitar da suffar shi ta magidantan kirki yace ke koh:khadija Dan Ankiraki da dije ai bawani abu bane suna ne mai dadi koh! yakai karshen maganar yana Dan yin murmushi,ganin tayi shiru batace komai ba,yace nasan fushin da like yi nafarko ban karba miki sannu da zuwan ki ba na biyu na kiraki da sunan tsofaffi yakai karshen maganar yasa cikin yin Yar karamar dariya wadda har far in hakorinsa na Makkah ya bayyana sannan yacigaba da magana kin san Khadija nace kibar yimin sannu da zuwa tundaga nesa shiyasa na kyaleki na biyu kuma ayi hakuri laifi nane shalelen Laure….yana murmushi
Baba Asabe dake gefe itama murmushinta yi,Itama Khady murmushin ta saki jin ankira ta da shalelen Babarta cikin dariya ta furta hard a ta dadynta dukan su dariya suka sanya.
Maganar Baba Adee ce ta dakatar da da riyar su Wanda maganar bata yima Baba Asabe dadi har fuskanta ya nuna,inda yake furta “yake cewa ina Shalele “……………..
Yawan likes dinku da comment shahizai Sa Ku samu page biyu arana
*A mafarki nasanta *📒
Daga Alkalamin
💫fa’eeh bungudu💫
Mu hadu next page✌✌
Dan jin cigaban maganar ta Baba Adee
Dakuma jin Amsar da Khady zata bashi, nasan kun matsu kuji asalin Halee
——————
Kucigaba da bibiyata ahankali zan warware muku duk wani sashe na littafina….
WASAN YANZU AKA FARA👏
Kuyi hakuri ba editing domin dazu sai da nagama wahalar typing gaba daya ya goge.
Pls like share and comment.
💫A MAFARKI
NASANTA💫
In my dream I know her
By
Pha’eezah Almustapha
Daga Alkalamin✍️✍
💫Fa’eeh Bg 💫
Dedicated to my lovely sis Laila Almustapha
Murai💔
*PERFECT ESSENTIAL WRITER’S ASSOCIATION
💫P.E.W.A💫
Home of perfect essential writer’s together we stand🤝
ESSENTIAL WRITER’S📚🖊️*
Pen 🖊️is mightier than the sword🗡️*
EPISODE1️⃣
FREE PAGE6️⃣
dama na fada muku page dinku na friday sai yau to ga alkawarinku nan na cika✌️✌️
TYPING📲📲📲
Khady cikin murmushi ta furta tana daki na barota ta shiga wanka kai yad’a ga mata alamar gamsuwa,firarsa ya cigaba da yi da yarsa cikin lumana yana tambayar ta ya karatunsu na islamiyya da na boko tana bashi amsa da alhamdullillah, masha Allah sai akara dagewa kinji Ya furta cikin jin dadi,kai Khady ta d’aga masa tana furta in sha Allah Anan take sanar masa da Halee bata je ba yau,Assha!Assha! meya hanata zuwa injin dai ba ciwon kanne nata yatashi ba…Yakai karshen maganar cikin nuna tausayinta kara furta wa Khady yayi tun yaushe yatashi ?tun dazu da asuba,tashi ki kira mun ita in ta fito tau tace sannan ta tashi ta wuce dakin nasu domin kiran Halee.
💫Fa’eeh Bg💫
Kanshi ya juyo dashi gefen da Baba Asabe take Yana furta Laure shine baki gayamun ba tunda nashigo,Baba Asabe da tun da tun dazu take cike da jin haushin shi nakiran Halee da yayi da shalelensa duk da bayanzu ne tafara jin yana kiranta haka ba tun tana karama,Dan bata son yana nuna wa Halee soyayya fiye da Khady duk da yana kamantawa Acewar ta yar tsintuwa ba “ya bace,dakyar ta bud’a bakinta tabashi amsa saboda haushi ga tsoron ta nuna mishi taji zafin maganar da yayi mata dakuma Kiran Halee Shalelensa,Haba Baban Hadiza yanzu fa ka dawo,ruwa kadai kasha ni dama yanzu nake niyyar sanar maka takai karshen maganar cikin danne wani kololon bakin ciki da yataso mata,niyya ya maimata abayyane yana gyad’a kansa cikin alhini ya nagayamiki duk randa ciwon shalelena yatashi ki rika kirana awaya in ba nanan sai inturo nurse kamal ya duba ta Amma da yake ita ba Khadija bace sai kike yin biriss da lafiyarta,ace kullum sai na maimaita miki maganar cewa ita din amana ce ta Allah agare mu,Amma na fahimci bakya ganewa kuma na fahimci har yanzu na baki dauke ta amatsayin yarki ba dan ina da tabbacin da Khadija ce keda wannan lalura haka da kin kasance mai kulawa nasan da gudu zaki sanar mini in ya tashi amma dan rashin Amma ni kike shaida ma wai yanzu kike da niyyar sanar mini,nasan kuma da khadijan ce da tun da asuban nan kinkira kinsanar mini,nasan kin sani keda kanki kika karbi amanar yainyar nan ba wani ba dan haka kiji tsoron Allah ki kara riketa da Amana.
Duk wannan maganar dayake kanta nakasa dan tasan yau ta dan ballo wani yanki na fad’ansa,ita inbanda tasan duk randa Halee bataje makaranta ba ciwon ta yatashi da bazata san bata da lafiya ba,tunda kosu yaran sun sani ko sungayamata babu abunda take iya yi face ma tabi Haleen da zagi ko gwacine,batun yau ba Halee na rashin lafiya Amma Baba Asabe bata kiransa tasanar masa in baya gida da yake ba,a garin yake aiki ba in yatafi yana kwana biyar ko sati kafin yadawo shiyasa wasu lokuttan har ta gama jinyarta bai sani ba.
Maganar shi tadawo da ita daga maganar zucin da takeyi….Yana furta wallahi Laure ki guji b’acin raina izuwa wannan lokaci ransa yakara baci ya hasala jin saoboda shirun da tamasa,Cikin danyin kasa da kai Baba Asabe ta furta Baban Hadiza Allah yabaka Hakuri,bai tanka mata ba sai ma cigaba da maganar sa da yayi yana furta baki san girman Amana ba Laure ba shiyasa Amma zanyi maganinkin dan bana son kikawo mini shirme cikin gidana dan haka kikiyayi b’acin raina karki kai ni baango ………..
Sallamar su Halee ce ta dakarar shi daga sake yin magana,Assalamu alaikun dady nah
Halee ce ke ke maganar da murmushi kwance abisa kyakkyawar fuskarta kyau da annuri wanda ke nuna farin cikinta na dawowarsa gidan,cikin shigarta ta wata doguwar riga yadi pink mai taushi da d’an madaidaicin hijab dinta fari wanda yakara haska farar fatar ta wanda har kashe ido take yi kamar zinari acikin azurfa,inka kalle ta kyakkyawar fuskarnan sai sheki take yi kamar wankakken gold gwanin burgewa kai bazaka ce tana da daamuwa….
💫Fa’eeh Bg💫
Wslm Halimatu Sadiya mai tagwayen suna kuma shalelena inji cewar Baba Adee cikin farincikin ganin ta yake furucin murmushi kwance afuskar shi shima.
“sannu da dawowa ya hanya” ? inji Halee tana kara sakin kayataccen murmushinta jin yakira cikakken sunanta wanda kamar ga bakinsa aka rada sa,kuma tana jin dadi yakira ta da hakan,Alhmdllh lafiya qlau hanya yakarfin jikin ki ance baki ji dad’i ba, cewar Baba Adee,ehhh naji sauki alhmdllh ai har nasha magani na yanzu kafin in fito,d’anyin shiru tayi tuna yadda tasha maganin wanda sai da Khady tace zata hada ta da dady ne sannan tasha shi dakyar kamar tayi kuka dan ta tsani magani ko allura,Dan kallon khady tayi wadda itama ita take kallo jin yadda take bayani kamar ba sai da ta tilasta mata ba,kawar dakanta tayi daga kallon Khady tana maida hankalinta ga Baba Adee wanda ke furta masha Allah haka ake so ai har ina maganar akira likita ko muje asibiti
Murmushi tayi tana yin kasa da kanta wanda har kyawawan hakoranta farare tass suka bayyana gwanin burgewa tace Naji sauki dady kuma sosai,murmushi ya karayi yana furta to madalla Allah yakara Afuwa,Ameen Halee da Khady suka amsa, yakaratun su da makaranta ya tambayeta kaamar yadda yatambayi Khady,Alhmdllh ta furta,kara furta mata yayi ya gidan kuma dan shiru tayi sai kuma cikin yanayin sanyinta ta furta lafiya lau kai yajinjina kawai batare da yakara furta komai,Baba Asabe ce da tagama girkinta na jallof din taliya da taji alayyahu,Ahankali tasauke wanda ta zubowa Baba Adee agaban sa cikin wani filet na tangaram irin na da mai kyau tana furta Baba Hadiza ga abincinka nan tayi maganar fuskar ta sai sa sai sa ba fushi ba murmushi dan bataso tana wani abu yakara hawa,wadda tun lokacin da ta samu su Khady sukazo gurin ta bar wurin tare da kayansa ta kai masa daki sannan ta wuce kitchen.
Bayan ta aje abincin ne ta koma ta debo masa ruwa na randa masu sanyi acikin jug mai kyau na kofin silver sannann tazauna,bai cemata komai ba yajawo filet din da ta aje agabansa yadora gabansu Halee yana furta kuje ku wanko hannayenku kuyi bisimllah muci abinci koh cikin farin ciki suka amsa masa da tau,Baba Asabe ce tayi karaf tana da niyar da katar dasu tana furta gana su chan akitchen na zuba musu suje su dauka,hannu kawai yadaga mata yana kara mata maimaita musu da suje su wanke hannayensu,wanke hannayen su keda wuya suka fara cin abincin tare dashi bayan duk sunyi bisimillah abayyane yaji su suna ci da hannu shi da spoon,cikin natsuwa suke cin abincin su tare dashi gwanin burgewa wanda dagani sun saba ne,Baba Asabe bata kara furta komai ba harsuka gama cin abincin su suka sha ruwan randa masu sanyi wayenda takawo masa,bayan sun wanke hannayensu suka furta alhmdllh atare wanda dama dab’i ar da ya sabar musu da itace,zasu yi basmala atare hamdala atare komai suna yinsa atare ne sun tashi da soyayyar junansu tun suna kana na.
💫Fa’eeh Bg💫
Masha Allah ya furta to tunda duk kun koshi sai aje afara shirin zuwa makarantar islamiyya koh,ehh suka amsa suna mikewa suka wuce dakin su cikin natsuwa ..
Shima tashi yayi ya wucewarsa nasa dakin domin watsa ruwa,Baba Asabe bata iya cemasa komai ba har ya yi shigewar sa dan tasan ta ba’llo ruwa,tasan bazai jirata ta hada masa ruwan wankan ba duk da shi ba mutum ne mai riko ba.
Abunda yafaru kafin fitar Khady gidan shine bayan tadawo makaanta
Cikin sallama ta shiga madai daicin gidan dai dai rufin asiri gida ne mai dauke da daki uku biyu suna kallon juna sai daya achan gefe wanda yake shine nasu halee biyun kuma nasu Baba Adee da Baba Asabe,sai toilet daya natsakar gida, da kichen shima chan gefe farkon shigowa gidan ga tsakar gidan ma da wali gidan masha Allah ko ina ka duba kwal kwal yaji suminti,inda ta iske Baba Asabe tsakar gidan tana fifita da yake lokacin zafi ne,Sallamar ta Baba Asabe ta amsa mata da murmushi ta na furta tagaban goshina kindawo itama khady cikin mayar mata da murmushin ta furta ehh Babata nasame ki lafiya,lfyalau Hadizata
Babata yau Dady zai dawo koh!inji Khady,ashe kina lissafi yar nan yaufa ne zai dawo murmushi mai hade da murna khady tayi tana furta yo ba dole ba Babata, Munyi missing nasa ne tana maganar tana dosar dakinsu da gudu tana kwalawa Halee kira,Halee! Halee!
Tana yaye labulen taga wayam katifarsu bakowa adakin, katifarsu kadai ce da tasha lailaya sai kayan sip dinsu wanda Khadyn ta ya mutsa kafin taje makaranta,wanda Halee ce take aikin bayan tadan ji dama damar jikinta,tana cikin aikin ne Baba Asabe ta kirata ta Aiketa kasuwa kutsa kanta tayi cikin tare da kara lelleka ko ina dan tabbatar wa indagaske Haleen bata ciki ne har toilet dinsu ta leka bayan ta kwankwasa taji shiru tambayar kanta tayi toh ina Halee taje ita da bata lafiya kuma?ganin bata da mai bata amsa yasanyata fita daga dakin bayan ta sargafe jakkarta ama ‘ajiyarsu,fitowar ta keda wuya ta yo tsinke gurin Baba Asabe tana mai furta Babata ina Halee taje ne,fuska adaure Baba Asabe ta furta na aiketa kasuwa,tun yaushe Khady ta kara furtawa cikin jin haushin Babar ta ta,shiru Baba Asabe tamata wanda dama tasan tunda taji tana kwala kiran sunan Halee tasan cewa sai tazo ta tsureta da tambayoyi kamar yar jarida ,kuma ta san tana iya bin bayanta yanzu dan haka kuwa bazata bartata fita ba komai kafuwarta
Khady ganin bata bata amsa ba yasa ta furta babata kinfa san bata da lafiya kika aike cikin wannan uwar ranar tana maganar kamar zatayi kuka shine kuma kika ta har kasuwa duk wayennan kantin basu isaba sai kasuwa…..
Baba Asabe ce ta furta an aiketa din wani ta fadawa bata lafiya ne eh dazaki zo ki tsare ni da surutun banza…

Leave a Comment