HAYATU BABA ZUBAIRU
(admin
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
Cool novel, makeup and kitchen1β£
AND
Cool novel, makeup and kitchen2β£)
WHATSAPP NO:
+2347039625239
SURBAJO
[3/18, 09:42] Zahra muhd mahmudπ: ππππ
πππππ
*SURBAJO*
πππππππππ
Zahra Muhammad mahmud
Bismillahi rahmanir raheem
Allah yanufa nagama Allah gatan bawa Lfy
Seku sake sabon zama domin ga sabon darasi nakawomuku
Innayi kuskure pls kutunasar dani
*page 1*
Sauri yake ya isa gida sabida yaga bakwai na safiya tayi.
Tunda yaje sallar asuba bedawoba yana masallaci seyanzu
Addua yake Yi azuciyarshi Allah de yasa Aisha taga dama ta
tashi daga baccinnata na qaddara
Tundaga shigarshi falo yafahimci adduarshi bata amsuba
duba da ganin falon dayayi ahargitse kamar filin dambe duk
da de dama sabon falonne zama acikin wannan yanayin
Jikinshi asanyaye yahaura sama inda dakinta yake
Ilai kuwa Tana kwance akan gado tana sharar bacci
Binta yayi da kallo zuciyarshi nakuna sabida tun jiya yashaida
mata zekoma bakin ayki yau jirgin karfe takwas zehau zuwa
phortercot amma shine ko tashi a bacci batayi ba
Inda sabo yasaba da halinta
Juyawa yayi yakoma dakinshi domin yayi wanka sabida yasan
ko toilet dinta yace zeshiga yayi wanka seyakusa amai sabida
karni da zarnin da toilet din yakeyi
Cikin Rabin awa har yagama shiryawa cikin kakinshi na soja
yayi kyau sosai sabida dama kyakkyawanne
Jakarshi yadauko sannan yadauko key din motarshi dakinta
yanufa
haryanzu Tana bacci
Tashinta yayi
Koda tabude ido taganshi tsaki tayi sannan tace Amman
wallahi al-ameen kaidan rainin wayone yanzu fisabilillahi ina
bacci zakazo katasheni
Beyi mamakiba Dan yasaba dajin abinda yafi haka daga
gareta
Nizan wuce yabata amsa
Kudi yaajiyemata kimanin dubu Dari uku a kan bedside drower
kallon kudin tayi awulakance sannan tace namenene wannan
Nacefanene kiyi amfani dashi kafin nadawo sabida inna tafi
wata uku zanyi kafin nadawo
kan ubance inji Aisha tafadi tana sakkowa daga kan gadon
sannan tace wallahi kayi kadan zakayi wata ukunne zaka
mikomin 300k wallahi baze yiwuba tafada yayinda ta zubar da
miyaun daya taru abakinta ajikin bangon dakin
Al-ameen bameson hayaniya bane Dan haka yace se nawa
kike so
500k tabashi amsa bemusaba yadauko yakara mata sannan
yace senadawo pls kiyimin addua
Agayas tabashi amsa gamida komawa takwanta
Fita yayi wani kurtun sojane yazo dasauri yaamshi kayansa
yasa aboot sannan yabudemasa bayan motor yashiga sannan
Shima yazaga mazaunin direba yatada motor sukafita yayinda
motoci biyu na sojoji sukasa motor atsakiya suka nufi Airport
suna zuwa kai tsaye jirgi yashiga Dantuni aka gama shirya
komai
jirginsu yadaga zuwa rivers state
Safe trip alameen
Love you all Maman Yusuf
[3/18, 09:43] Zahra muhd mahmudπ: ππππ
πππππ
*SURBAJO*
πππππππππ
Zahra Muhammad mahmud
*page 2*
Tunda alameen yafita taci gaba da baccinta bata tashiba se
Tara sannan tamike tashiga π½ tayo alwala tayi sallar asuba
π³
Tana idarwa kitchen tanufa madara ta kwaba akofi da Milo
tazuba ruwan sanyi tajuya yayi kauri kamar chocolate
Tadauko gorar faro tadawo falo tafarasha
Aduniya babu abinda Aisha ta tsana irin girki Sam batason
yinshi shiyasama bata iyaba
Zamanta keda wuya taji ana ringing bell dasauri taje bakin
kofar taleka Dan ganin waye
Ihu tasa tun kafin ta bude kofar
Tana budewa suka rungume juna ita da bakinnata
kawayentane su biyu
Kai tsaye dakin Al ameen tamusu masauki dan batason su
rainata insukaje nata dakin
Afalonshi suka zauna hira suka shigayi dawadda tadace
dawadda bata daceba suyi gulmar wannan suyi ta waccan
Can kuma tafara basu labarin yadda suke kwanciyar aure da
mijinta kamar yadda suka saba (waiyyazu billah)
Shewa suke kawai suna kara zugata suna fadin eshat baby
baki da wasa
Dariya tayi tabasu labarin yadda suka rabu yau da alameen
Daya daga cikin kawayennatane mesuna Ruky tace wo
mutuniyar kina wuta muna binki da petur ina namu salary din
tunda kin tatsa muma seki sammana koya kikace zuly baby
A wannan gaskiyane wacce aka Kira da zuly tabada amsa
eshat ce tafara mgn haba sisters harse kun roka ay kunwuce
hakan agurina danhaka ku kwantar da hankalinku nifa wlh
kunfiyeminshi so dubu agurina Danni Al ameen dashi da
banza duka daya Suke. Kuma sabida nasan zanbaku naku
kasonne yasa nace seyakaramin kudin Dankaka zanbaku 200k
kuraba
Ihu sukayi suka rungumeta suka hada baki gurin fadin heyyy se
madam Allah de yabiya Hajiya.
*ASALIN LABARIN*
al-ameen jibrin sulaiman shine cikakken sunanshi matashine
Dan shekaru 35 da haihuwa. dane ga rt major general jibril
sulaiman
Mahaifinshi Dan asalin garin kanone awata anguwa daake Kira
lungun gabari canne asalin tushensu amma sanadin aykin soja
yasa yadawo kaduna da zama a malali yake da zama alayin
sultan road
Hamshakin mekudine ajihar kaduna domin ajerin masu kudi
nagarin in akace daya to tabbas shine nabiyu
Matarshi daya mesuna Hajiya binta suna kiranta da umma
yaransu hudu. Kabeer shine nafari sannan alameen se
munawwara da autarsu amal
gidan alhaji jibrin gidane gidan tarbiyya Dan yaransu gaba
daya babu mehalin banza
Mahaifiyarsu nabasu tarbiyya Dede gwargwado kudi besa tayi
watsi da tarbiyyar yarantaba
tunbayan da mahaifinsu yayi rt yakoma fannin business
nakasa da kasa yanada kamfanoni a fadin jahohin nigeria
mutumne shi metsoron Allah bashida buri dawuce a yaransa
yasamu megadonsa a gidan soja kullum adduarshi kenan inda
Allah yataimakeshi ya bashi alameen
tunda alameen yafara mallakar hankalin kanshi yaji yana
shaawar zuwa aykin soja
Koda yatuntubi mahaifinsa da batun bakaramin farinciki yayiba
baayi satiba yasamomishi aykin dayake akwai hanya
shiko kabeer accounting yakaranta yanzu haka yana ayki a
cbn yanada mata daya Da yaronshi guda daya mesuna
Waleed kasancewar sunan abbansu yaci
munauwara kuwa yanzu Tana js3 yayinda auta amal ke
primary 4
tunda alameen yafara aykin soja gabadaya hankalinshi
yamaidashi abangaren aykinshi kullum burinshi yataimaki
kasarsa
lokacin a kaduna yafara aykin kamin ayi posting dinshi zuwa
Abuja
kamar kullum yauma yataso daga ayki da misalin karfe
shadaya nadare a nda yake aykin dan haka ta Badarawa
yabiyo dan zefi mishi saukin isa gida
yawuto bustop kadan Dede galadima road jikin katangar
gidan Baba boss yaganta tsugune Tana kuka ga gurin yayi
shuru babu mutane har yawuce seyaji yanason sanin meyasa
ta kuka kuma take zaune abakin titi
ribas yayi yadawo gurinta layin galadima road din yashiiga
Dede gidan kallon kwallo yayi parking sannan yafito yatako da
kafarsa zuwa inda take
sallama yamata agigice tadago kanta tana kallonshi kara
matsawa kusada ita yayi yace yanmata meyafaru ne kika
zauna anan kina kuka
ganin uniform din soja ajikinshi ne yasa tace aranta bari
infada masa maybe yataimakamin
cikin kuka tace wlh mamanace tawuni yau Tana wankau har
zuwa dare sannan tasamu kudin dazamuci abinci dashi
tunsafen bamuci abinciba shine yanzu ta aykoni insiyo garin
rogon dazamu sha bansan yaakayiba kudin suka fadi shine
nake kuka dannasan yau seta kasheni tafadi Tana sake
rushewa da kuka
yaisa haka alameen yafadi yana kallonta balaifi tanada kyau
dede gwargwado kuma yarinyace dabazata wuce 18years ba
yasunanki yatambayeta
sunana AISHA tabashi amsa
inane gidannaku nunamasa gidan tayi da hannunta danba nisa
taso muje yace da ita
zaromishi ido tayi tace wlh najemata ba sakonnan yankani
zatayi Dan Allah kawuce ka kyaleni anan
bazata yankakiba nizan biyata kudin
Amman Anshi Wannan Kijewancan shagon kisiyomuku kayan
tea 2k yabata godiya tashiga yimasa kamar zatayi sujada
dagudu ta tsallaka titin tasiyo kayan tean dawowa tayi tace
nasiyo
gaba tayi yana binta abaya harsuka isa kofar gidan yace shiga
kiyimin Sallama da mamannaki wucewa tayi tana murmushi
Dan ita yau jitake kamar sallah saboda zasu sha tea Wanda
rabonta datashashi tun kafin babanta yarasu yanzu ko kimanin
shekararsa hudu da rasuwa π
mamanta Data fito taga sojane ke sallama da ita cikintane ya
murda dakyar suka gaisa sannan yamata bayanin abinda
Aisha tafadamasa
yakara dabata hakuri sannan yadauko kudi a aljihunsa
kimanin50k yabata yace tayi hkr duk sanda yasamu lokaci
zedunga lekosu godiya Mama takeyi harda hawaye
sallama yamata yakarasa gurin motarshi yashiga yanufi gida
*wacece Aisha*
love you all Maman Yusuf
[3/18, 09:47] Zahra muhd mahmudπ: ππππ
πππππ
*SURBAJO*
πππππππππ
Zahra Muhammad mahmud
*Page 3*
Aisha Bello Musa shine asalin sunanta haifaffiyar garin
kadunace acikin anguwar Badarawa
Sunan mahaifinta malam Bello mahaifiyarta kuma sunanta
maimuna suna kiranta da inna
Su ukune agurin iyayensu Aisha itace tafarko se kannanta
guda biyu zaituna da Umar
Shekarar Aisha 18 mahaifinsu yarasu tun Tana js1
Mahaifiyar itace taci gaba da kulawa dasu har zuwa yanzu da
Aisha ke ss2 awata makarantar gwamnati dake anguwarsu
Kannanta ma duk government schools sukeyi
Rayuwace suke mecike da kunci Dan abunda zasuci yafi
karfinsu se inna tayi wankau suke samu suci abinci so daya
arana
Aisha yarinyace me dogon buri arayuwarta kuma bata da
godiyar Allah ko kadan
Tahadu dasu Ruky da zuly ne amakarantarsu inda halinsu
yazo daya suka kulla kawance
Basuda ayki dayawuce suyi gulmar kawayensu har gida ansha
biyo Aisha akan tayi gulmar wata akureta
Mahaifiyarta macece me sakaci da tarbiyar yaranta tun bayan
mutuwar mijinta Wanda hakan yasamu asaline asanadin zafin
talaucin dasuke fama dashi
kwasam segashi Allah yaturomusu alameen
Tunda alameen yatafi besake zuwa gidanba hasalima baya
biyowa ta unguwarsu
Aisha tafi inna Damuwa darashin zuwannashi sabida tunda
tadora ido akanshi taji takamu dasonshi
Har bakin titin anguwarsu take zuwa tatsaya kozata ganshi
babban abinda yasa takesonshi mijine na nunawa kawa itako
bata da buri dayawuce ace taburge kawayenta
Yau jummaa dawuri alameen yataso daga ayki ta Badarawa
yabiyo har yawuce layin Su Aisha se yatuno da ita danshi
harga Allah yamanta dasu tun bayan barinshi gidansu kwana
yayi yashiga layin Dede kofar gidan yatsaya
Aisha ce atsaye azauren gidan Kai ba dankwali takira me
agwaliba Tana siya tun agurin tafarasha fadi take Kai malam
wannan da tsami
Mamakine yacika alameen ganinta dayayi ahaka gashi tasa
wata π Data bayyana halittar kirjinta Dan har ta saman rigar
ana ganinsu
Hon yamata dasauri takai dubanta inda taji hon din dagudu
takarasa fitowa tanufeshi dasauri alameen yadauke idonshi
daga kallonta sabida yadda take gudun yasa halittar kirjinta
yin wani juyi na musamnam sabida Allah yawadata ta dasu
Karasowa tayi jikin motor Tana dariya
Sannu dazuwa soja sunan data kirashi dashi kenan
daurewa yayi yayi murmushi yace yauwa kanwata
Kashigo mana daga ciki tabashi amsa
Fitowa yayi suka shiga zauren gidan gaisheshi tayi
Yaamsa sannan yace
lalle bakyason shiri Dani tunda bakya muamala da dankwali
kunyace takamata dagudu tajuya Tashiga gida tasako hijab
sannan tafadawa inna sojan rannan yazo murnace takama
inna dasauri tace uwaki Aisha shine kika barshi awaje yisauri
kije ki kirashi yashigo dasauri tadawo gurinshi tamishi iso
zuwa cikin gidan
Kan tabarmar da inna tashimfidamasa yazauna gaisheta yayi
cike da girmamawa sannan yasanar dasu sunanshi dana
mahaifinshi
Inna da Aisha ne suka hada baki gurin cewa Alhaji jibrin
sulaiman de Wanda mukasani
mamaki tambayar tabashi sabida arude suka masa ita
eh shi yabasu amsa
Ajiyar zuciya sukayi dukansu daganan inna tabashi tarihinsu
yatausayamusu sosai inda daga karshe yayi musu alkawarin
kulawa dasu
tundaga wannan lokaci alameen yamaida gidan inna kamar
gidansu inyazo sallama kawai yake yashiga sosai yake musu
hidima dantuni yasauyawa su Aisha makaranta ita da
kannenta
Yayinda ita kuma Aisha kullum sonshi Karuwa yake azuciyarta
zuwa yanzu har waya yasemata iPhone6+ burin aisha yafara
cika dantuni tasauya tayi kyau namusammam ga sutura Tana
shiga ta alfarma bata da wata damuwa data wuce ta auri
alameen
insuna waya so tari tasha yunkurin sanardashi halin datake
ciki seta kasa
yau alameen ne yakawomusu ziyara bayan sungaisa da Inna ta
tashi tafice dama zata barkane Aisha dawowa tayi kusa dashi
tazauna tace Yaya alameen kamar yadda take kiranshi juyowa
yayi Yana kallonta ganin yadda tanatsune yasa yagane mgnr
dazatayi me muhimmaci ce sabida kwatakwata Aisha bata da
natsuwa
yaakayine kanwata yatambaya
kunyace tarufeta amna bata dazabi dayawuce tasanar dashi
yaya Don Allah zaka iya aurena? Jin tambayar yayi kamar
saukar aradu danshi Sam bayason Aisha amatsayin wacce ze
Aura danyafison mace me natsuwa
AA yabata amsa
kuka tasamishi tana Don Allah kataimaka kaaureni wlh tunda
nafara ganinka naji inasonka katausayamin sonka zeiya
kasheni wlh tafadi Tana ruko kafarshi
dasauri yamike yace amma Aisha bakida hankaliko taya zan
iya auranki Bari kiji infadamiki bakya cikin jerin macen
danakeson in Aura Danhaka bazan boyemikiba wlh banasonki
kiyi hkr kinemi wani yana gama fadin hakan yajuya yafice daga
gidan ranshi abace
innace tashigo taga Aisha kwance akasa dasauri takarasa
kusa da ita ga mamakinta farin kumfa tagani yana fitowa
daga bakinta agigice tadagota ina babu numfashi ajiyeta tayi
tafita tsakar layin Tana neman taimako napep akasamo akasa
Aishan aciki inna Tashiga suka nufi asibiti
πππ

Leave a Comment