*💖ABNUR💖*
By maimoon🤓
Elegent Online writers
*Free book* page 1
Bismillahi ar-rahmani ar-raheem_______
Hasken farin watan daya haske illarin garin shiyake bata daman ganin inda take sanya ƙafafuwanta gabaɗaya she is not in her right senses tafiya kawai takeyi ba tare da tasan inda ta nufaba
Tafin hannunta ta sanya ta share hawayen da ya zubo mata a karo na ba adadi she really wish all dis was a dream cigaba da tafiyan kawai takeyi a ƙauyen da ko sunansa ma bata saniba Ita dai kawai burinta tayi nesa da inda ta fito
A daidai kofar wani gida ta ja ta tsaya saboda batajin xata iya cigaba da tafiyan saboda galabaitan da take sake yi rabonta da abinci tun breakfast shima ba wani sosai taci ba gashi a yanda xata ƙiyasta saboda yanayin shirun garin da kuma duhun dare aƙalla ƙarfe 11:00 zai iyayi
Guri ta samu ta zauna a ɗan dakalin dayake ƙofar gidan tare da kifa kanta tana cigaba da kukan da har takejin zuciyarta kamar ba’a jikinta yakeba batasan iya lokacin data share a zaune a wajen ba kawai dai taji idanunta na lumshewa alamar bacci takeji
Muƙewa tayi a hankali akan dakalin tana jin zuciyarta na mata zafi batason tuno abinda ya rabo ta da gida a cikin wannan tunanin bacci ɓarawo yy nasaran fizgarta duk da ba ɗaɗin baccin takejiba sam
Sanyin asuba tare da kiraye kirayen sallah a masallatan da suke ƙauyen yasata ɓuɗe idanunta a hankali waɗanɗa suka kumbura Sukayi jajir saboda tsananin kukan ta sha zaunawa tayi akan dakalin tana jin duk jikinta na mata wani irin ciwo ta shiga ƙare ma ƙauyen kallo tanason tuno inda take dafe kanta da ke tsananin ciwo tayi tana jingina da bango wasu hawaye Masu ɗumi suka sake gangaro mata
Hannunta tasa da sauri da kare fuskarta saboda hasken fitilar daya haske mata fuska
“Subhanallahi mutum ko aljan” mutumin ya tambaya da alamar tsoro a tare dashi yana tsaye daga ƙofar gidan da take zaune kasa cewa komai tayi sai hawayenta da ya ƙara ƙarfin gudu juyawa mutumin yy da sauri ya koma cikin gidan sai gashi ya ƙara fitowa tare da wani ɗan saurayi da alama shima alwala yayi na tafiya Masallacin
“Kaganta nan wlhy nidai har na tsorata” tsohon ya faɗa yana nunama saurayin ita da alama ɗansa ne ƙarasowa kusa da ita yy ya tsaya ɗan nesa kaɗan da ita yana faɗin ” baiwar Allah ” ɗago kanta tayi a hankali tana kallonsa hawayen idanunta na cigaba da kwarara tsura mata ido kawai yy sai kuma ya juya ya kalli babannasa yace “baba ko xata shiga ciki kafin mu dawo daga masallaci lokaci na ƙurewa “wani kallo babannasa yy masa yana nuna ta yace “ta shiga ina wai, kasan wacece ita xakace ta shiga ciki “miƙewa yy yana sake kallonta sai kuma kawai yy wucewarsa baban ma ya bisa a baya suka nufi masallaci
Har aka idar da Sallah gari ya soma haske tukun suka nufo gida tun daga nesa suka hangota still tananan zaune inda suka barta baba ya kalli kamal yace “anya wannan yarinyar mutum ce kuwa “murmushi kamal yy yace muƙarasa mugani “daidai kusa da ita ya durƙusa ya sake cewa “baiwar Allah” a karo na uku sannan ta ɗago kai ta kallesa murmushi yy mata yace “me ya sameki haka kike zaune anan da alama ma anan kika kwana ki faɗa min ko akwai taimakon da xan iya baki “nan ma shiru tayi ta sake miyar da kanta shiru yy kamar mai tunani sai kuma yace to ki tashi mu shiga ciki kiyi sallah nasan bakiyi ba ko kallonsa kawai takeyi kamar statue sai da ya sake maimaita abinda ya faɗa tukun ta miƙe a hankali jiri na ɗibarta saboda gaskiya tana buƙatar tayi sallolin da ake binta
Kallonta yy tayi saboda baiga alaman yar ƙauyen bace ko duba da irin suturar da ke jikinta kaɗai to itakuwa me ya kawota ƙauyennan haka har suka shiga ciki ta tsaya a zaure tana raba ido baba da tunda yaga kamal ya tsaya wajenta ya shige cikin gida ya samu a tsakar gida zauren ya nuna masa yace “wannan yarinyar baba nace ta shigo ko xatayi sallah “saída baba yy shiru sai kuma yace “kamal mutum fah yanxu abin tsorone kuma kwata kwata batayi kamar yar nan ba bawai bana son taimaka mata bane” kamal yy murmushi yana komawa zauren tare da faɗin “karka damu baba banji ajikina mai cutarwa ce kuma mu ai dan Allah mukayi da kyakkyawar nufi idan ma ta cucemu Allah baxai barta ba
A zauren ya sameta a rakuɓe yace baiwar Allah shigo yayi gaba tana binsa a baya har ƙofar ɗakin mahaifiyarsa sallama yy ta amsa sannan ya shiga itama ta bishi a zaune suka tarar da ita har lokacin akan abin sallan ta gaisheta yy ta amsa da fara’a tana kallon baƙuwar sai kuma tace ” kamal wannan Fah a Ina ka samo ta” murmushi yy yana miƙewa yace” to muma dai a ƙofar gida muka ganta da alama ma anan ta kwana kuma taƙi magana shine nace mata ta shigo ko xatayi sallah” kallonta kawai umma takeyi sai kuma tace “to badamuwa bari tayi sallan idan mun karya sai muji daga ina take haka dan sam batayi kalar yan ƙauyennan ba” yauwa umma kamal ya faɗa yana ficewa daga ɗakin dan tafiya gona tare da baba dake jiransa a waje
Abuja nigeria_
A haukace yake sauƙowa daga matakalan da yake haɗesu uku uku hurhuɗu hankalinsa a matuƙar tashe ƙofa ya nufa da azama yana sake dialling din number a wayarsa ɗaya daga cikin securities ɗinsa ne ya ƙaraso da sauri yana faɗin “morning sir” wani kallo da yy masa ya sashi shiga hankalinsa ya sake faɗin “sorry sir” juyowa yy gabaki ɗaya yana kallonsa yace “ina take” a tsorace guard ɗin yace “sorry sir we have tried our level best but still we are not able to reach to her” cakumo wuyansa yy a zafafe Yana faɗin “what the heck do you mean baku ganta ba wata sani ,ina xata je she has no one but me so na baku nan da awa ɗaya ku nemo min *NOOR* duk inda ta shiga a garin Abuja” hankaɗasa yy baya tare da sake faɗin “sorry sir” sake kallonsa yy sannan yace “don’t u dare ,keep ur fucking sorry to yourself , just make sure lokacin da na baku kundawo min da noor gidannan “sai kuma ya juya a fusace ya nufi motarsa ya fice a gidan a guje
To ABNUR has just started the story is yet to begin 🤓😇
*💖ABNUR💖*
*By maimoon*🤓
*Elegant online writers*
*Freebook*
*page* 2
Tunda ya fito gidan yake yawo a cikin gari yama rasa ta ina zai fara neman NOOR ,ina zata je ,wata sani bayan shi, ya tabbata bata da inda zata je da ya wuce gidansa ,har yamma yana gararamba.
Gefen titi ya samu yayi parking ya jingina kansa da steeryn motan, ya rasa ina zai nufa don neman ta, ɗago kanshi yayi da idanuwansa da suka gama rinewa sukayi jajir ya jingina kansa da seat ɗin motar .
Why Noor? ,am I really that bad to you da kika zaɓi ki barni? ,do you have any idea halin da nake ciki yanxu ?please Noor ki dawo gareni i promise I will mend my ways ,na miki alƙawari zan gyara please Noor.
Da ƙyar ya samu ya kai kanshi gida, har jiri yake ji dan rabonsa da abinci tunda ya fahimci Noor bata gidan .
Baibi takan kowa ba har bodyguards ɗin da suke gaishesa, ko takalmansa bai cire ba ya faɗa kan gadon katafaren ɗakinnasa yana kallon saman ɗakin, yana sake zurfi a tunanin ina zata shiga a garin Abuja .
Kamal ne ya fito daga ɗakin ,mahaifiyarsa na biye dashi ,zama tayi a tsakar gidan shima yaja ƙaramar kujera ya zauna yana fuskantar ta yace ,”umma da muka fita dama bata ce miki komai bane? “.
Ďan shiru umma tayi kamar baxatayi magana ba sai kuma tace,” wlhy kamal nayi iya tambaya amma batace min komai ba, banda kuka babu abinda takeyi, yarinyar tana da babbar damuwa sosai ,amma rashin sanin daga ina ta fito shine babbar damuwar “.
Kamal yace ,”hakane amma gaskiya tana buƙatar taimako sosai ,kawai mu bari muga kwana biyu ko xata ji sauƙin abinda yake damunta, sai tayi mana bayani” .
Shiru umma tayi sai kuma tace “toh Allah dai ya kyauta gata kyakkyawa wlhy kuma daga dukkan alamu yar gidan masu kuɗi ce ,”kamal ya miƙe yana faɗin,” wlhy nima haka na gani”.
Fita yayi daga gidan dan yanaso ya je gidansu Abdul, dan yanaso ya amso kuɗin sa dake wajensa dan komai na gidannasu ya ƙare kuma gashi amfanin gona bai nuna ba bare ,
har ƙofar gidan yaje ya aika yaro ya kira masa shi, a ƙasan wani bishiya suka zauna Abdul ya kallesa yace “kuɗinka ko kamal” .
Kamal yayi murmushi yace “saboda bana zuwa wajen ka sai idan inason kuɗi koh “,Abdul yayi dariya yace “wlhy ba haka bane kawai dai nasan halin garin ne yadda babu kuɗi”, shiru kamal yayi sai kuma yace “wlhy Abdul banso na tambayeka ba amma wlhy ina matuƙar buƙatarsu “.
Duk sukayi shiru kafin Abdul ya nisa yace” wlhy kamal bandashi nima “,shiru yayi sai kuma yace, “babu damuwa karka damu wlhy”, daga haka ya miƙe yana faɗin “to sai mun haɗu anjima da daddare”, Abdul ma ya miƙe yace “ba damuwa nagode kamal “.
Daga haka ya juya yana ta tunane tunane har ya iso a tsakar gidan ya samu umma tana ƙoƙarin shiga kitchen kusa da ita yaje yace,” umma dama naje wajen Abdul ne ko zan samu kuɗin wajensa amma bansamu ba “,umma ta nisa tace ,” to Allah ya kyauta amma dai yau yaza ayi kenan, yanzu babanka ma ya dawo bai samuba ,wlhy gashi muna da baƙuwa ” .
D’an murmushi yayi yace “yanzu dai akwai wani ɗan canji a jikina idan na fita zan nemo mana abinda zamuci yau, amma dai gobe sai yadda Allah yayi da mu”, duk juyawa sukayin jin motsin mutum a tsaye suka ganta tana kallonsu umma tace “ah ah Noor Kin fito “.
Girgiza mata kai tayi tace ,”umma inaso zan shiga bayi ne,” da sauri umma tace “ayya gashi can bari na saka miki ruwa a buta “,da sauri ta karɓi butan hannun umma tana faɗin “laa umma karki damu dan Allah”.
Ta wuce wajen randar ta ɗebi ruwan umma tace .”ga ruwan zafi idan zaki surka ,tace “toh” cup ta ɗauka ta ɗebi ruwan ta wuce bayi ,
Umma da kamal na nan zaune ta fito ta ajiye butan sannan ta nufi wajen tabarmar da taga sun shimfiɗa sun zauna.
Itama zama tayi sai kuma tace “umma dan Allah kuyi haƙuri da shiga rayuwarku da nayi, amma ina neman alfarma a wajenku dan Allah ina so in zauna da ku na wasu kwanaki, nasan ya dace na faɗamuku abinda ya raboni da gida , amma na muku alƙwari zan fada muku insha Allahu “.
Aai da ta ɗan yi shiru sai kuma ta sanya hannuta ta ciro ɗan kunnen gold ɗin dake kunnenta ta miƙama kamal tace “yaya kamal gashi ina so dan Allah ka siyarmin da wannan ɗan kunnen “.
Sai da ya kalleta ya kalli ɗan kunnen sai kuma yasa hannu ya karɓa yana kallo yace,” tabb Gwal ne fa”.
Tayi shiru tana kallonsa yace,” sai dai bazan iya sayarwa a garinnan ba , sai dai gobe insha Allahu , tunda ranar kasuwan cikin garin kusa damu ne , su suna siya sai inje can na sayar miki ,” ahankali tace “nagode sosai Allah ya saka muku da alkhairinsa “, duk suka amsa da ameen .
Washe gari kamar yadda sukayi haka ya shiga cikin gari ya sayar , duk da dai an masa an siya ba yadda kuɗin sa ya keba ganin cewa ɗan ƙauye ne, haka ya ɗaure kuɗin a mayafi ya dawo gida, a tsakar gida ya samesu suna hira da umma ya zauna shima yana warware wa ya miƙa mata.
“Yace gashi Noor “,ta karɓa tana murmushi ta ƙirga kuɗin sai kawai ta girgiza kai sannan ta kama hannun umma ta danƙa mata kuɗin.
Dubu biyar kaɗai ta ɗauka a kuɗin umma ta zare ido tana kallonta girgiza kai tayi tana kallon umma tace “umma dan Allah karkice komai kiyi haƙuri jiya naji hirarku da kamal dan Allah ku karɓi kuɗinnan ,na baku ne a matsayin yan uwana saboda kunyi min taimakon da bazan taɓa mancewa daku ba, kunyi min taimako alokacin da nake tsananin buƙatarsa”.
Umma rungumeta kawai tayi tana sake jin son yarinyar har ranta, tana sake kwaɗaituwa da son jin dalilin ta na barin gida , a hankali ta share hawayen ta tace.
” Ni ban san me ya raboki da gida ba Noor, amma ke ɗin alkhairi ce a wajenmu, kuma mungode Allah ya saka miki da alkhairi kuma ya fitar da ke a cikin duk matsalolin da rayuwarki ke ciki”.
Shidai Kamal kallonta kawai yakeyi sai kuma yace “Noor kuɗinnan”, shhhh tace masa “yaya kamal pleaaaaase karkace komai”.
Nurmushi kawai yayi yace “to shikenan nayi shiru Allah ya saka”, daga haka suka ci gaba da hirarsu tana samusu baki jefi jefi, but hankalinta da tunaninta gabaɗaya suna wani wajen daban.
Wasu sabbin hawayene suka cika idanunta, she is sure baida buƙatarta a rayuwarsa, kuma bayida asara idan har bata tare dashi , he never loved her but tayima kanta alƙawari koda mai kama da ita bazai sake gani ba.
zatayi nisa dashi irin nisan da bazai taɓa cinmata ba, a hankali ta sanya hannu ta share hawayen tana ƙaƙalo murmushi, ganin umma tana kallonta sai kuma ta miƙe ta nufi ɗaki duk suka bita da kallo .
🥱🥱🥱🥱🥱🥱
#maimoon
💖 **ABNUR**💖
*By* *maimoon* 🤓
*Elegant* *online* *writers*
**Freebook**
*Page* *3*
Kwanci tashi asarar mai rai,yau kwanan Noor goma kenan a ƙauyen Marke dake jihar Kano.
duk da cewa har yau ba tayi musu cikakken bayanin abinda ya rabota da gida ba,amma sun fahimci ita ɗin mutum ce mai matuƙar daɗin zama, sannan bata da son magana sosai.
Hakan yasa suke zaune tare da ita, har zuwa sanda zata yanke shawarar sanar dasu ainihin abinda ya rabota da iyayenta ,
Umma tana matuƙar ji da ita, kuma hakan yasa basa ma ɗago maganar, saboda yadda daga an tambayeta, sai dai ta fara kuka, Sannan akoda yaushe maganar ta baya wuce”Umma kuyi haƙuri insha Allahu zan sanar daku ,har ma abinda baku tambaya ba”.
A bangaren ZANNUR kam babu sauƙi, yayi iya ƙoƙarin sa ,ya haukace da neman ta har gidajen Radio,but har yau shiru ,ga baki ɗaya ya fita hayyacinsa ,bai taɓa tunanin za tayi koda tunanin hakan a zuciyar ta ba, talkless of aikata shi a aikace
Yau ma a gajiye ya dawo,bayan ya gama yawan nemanta kamar yadda ya saba ,duk da ya baza mutane sunfi a ƙirga da hotunanta ana nemanta, but shikanshi ya kasa daina wa.
kullum gani yake idan ya fita yau zai ci karo da ita ,bazai taɓa manta yadda abubuwa suka kasance ba shekaru biyu da suka wuce,ɗakinsa ya wuce ya zauna akan kujeran dake ɗakin yana jingina da kujeran “i can never give up on you, har sai na ganki sannan kin tabbatar min da bakinki zaki dawo gida na, idan ba haka ba, ban san tayaya zan yafe ma kaina ba ,I know I will never be able to
forgive my self idan har wani abu ya sameki”.
Da ƙyar ya miƙe daga kan kujeran ya zare rigar jikinsa,ƙirarsa na ƙarfafa ya bayyana, duk da yanzu rabonsa da workout ɗinma tun ranar da Noor ta bar gidan, wanda a da yake cikin morning schedules ɗinsa da baya iya tsallakewa,
bayi ya wuce yayi wanka, yana fitowa kayansa kawai ya zura, yana jin yanda cikinsa ke kukan yunwa.
A hankali yake sauƙowa stairs ɗin, gaba ɗaya ya canza kamar ba Zannur ba, ‘the master of all’ harta masu aikin gidan sun san baya cikin kwanciyar hankali, duk wanda yake tareshi yasan yana cikin matuƙar damuwa.
Falon ya ƙaraso ya zauna yana rage ƙarfin ac, dan kamar sanyin zazzaɓi ma ya keji a jikinsa, Yasira ta ƙara so wajensa da sauri tana faɗin “Sir Should I serve your dinner?” Kallonta kawai yayi ,sai Kuma ya mayar da kansa ya jinginar, yama rasa me zai ce mata, bakinsa ya masa nauyi,sai da ta sake tambayan tukun ya ɗaga idanunsa,masu rikitarwa ya zuba mata su, sai kuma yayi gyaran murya yace “miss You Are fired!”
Zaro ido tayi tana kallonsa, nan take tafara hawaye tana faɗin “Sir I am very sorry Dan Allah Kar ka koreni” “why shouldn’t i?” ya katse ta a tsawace , “sanda ta tafi ta barni why don’t you stop her ?”
Ta buɗe baki zatayi magana, yayi saurin sanya yatsansa a baki , yace “shhhhh not another word, abinda nakeso dake yanzu shine,U Should get out of my sight immediately,before I lose my temper completely”.
Da sauri ta miƙe daga tsugunan da tayi, takoma kitchen da sauri! ,Ƴan matan da ke cikin kitchen ɗin suka kece da dariya ,Amina tace “sai da nace miki kar kije! ,kwanakin nan Sir neman inda zai huce haushinsa yake”.
Asabe da ke goge goge, tayi ƙwafa tana faɗin “sai kace sanda Madam ɗin takenan ya damu da ita” ,Ameena tace “Wallahi fah nima abin mamaki yakeban” ,Yasira dai bata bi ta kansu ba, ta wuce ta ƙofar baya dake kitchen ɗin, ta nufi shashen ma’aikatan gidan, a zuciyarta tana sake dana sanin zuwa tambayarsa da tayi.
Shi kuwa ko a jikinsa, kawai burinsa ta inda Noor zata ɓullo ,wayarsa ce tafara ringing,a hankali ya ɗaga wayan yana kallon mai kiran “Maami” da ya gani ya shashi shafa yalwataccen sumarsa, he has been avoiding her since, dan baisan me zai ce mata ba sam, shahada yayi ya ɗau wayan “sallama yayi daga ɗayan ɓangaren ammi ta amsa tana faɗin
“Habibi ina ka ajiye wayarka, I have been trying to reach you but baka picking calls ɗinka, I hope everything is fine there? ” shiru yayi kafin ya samu ƙarfin halin haɗa kalmomin bakinsa “maami ya Dubai?” “lfy ƙalau habibi ina Noor” shiru yayi ya kasa cewa komai ,shirun da taji yayi yawa ya sata sake faɗin “Habibi are you there? “Umm…Maami” “are you okay my boy? mai yake faruwa me kake ɓoyemin? I hope you are not trying to hide anything!”
“maami babu komai fah don’t you believe me”
“na yadda da kai mana my boy, to yanzu ina Noor? it has been long tunda mukayi magana da ita, kai mata wayan ”
A ɗan daburce yace “umm wai Noor ..in kai mata wayan? to ai tayi bacci,batajin daɗine shine sai ta kwanta”
“ok shikenan maybe next time Allah ya sauwaƙe ka kira abbun ka, yace yakiraka baka picking ” “a hankali yace “insha Allah Maami” daga haka yayi hanging Kiran yana sauƙe ajiyar zuciya.
Da sauri kamal ya shigo gidan, hannunsa riƙeda jarida wanda hotonta ke jiki ɓaro ɓaro ,ita kaɗai ya samu a tsakar gidan tana wanke kwanukan da suka ɓata da safe ,yanayin da taga ya shigo ya sata saurin ɗauraye hannunta,
tana ƙarasowa tsakar gidan dai dai umma ma ta fito daga ɗakin ta, tana faɗin “Noor Nikam Ina kikaga na ajiye goron da ke cikin ledannan ne?
tsayawa tayi tana kallonsu yadda sukayi cirko cirko a tsakar gidan. “Lafiya?” Ta tambaya tana kallon Noor “umma nima wallahi bansani ba, haka naga ya shigo kamar ba lafiya ,umma ta karkata akalar tambayan nata ga kamal da ke tsaye yana kallonsu,
miƙa mata jaridar yayi yana faɗin, Abdul ne ya shiga cikin gari ɗazu, shine nace masa ya siyomin jarida dan na karanta, shine fah kawai naga hoton Noor ajiki ,Umma ta karɓa tana dubawa, sai kuma tace to me aka rubuta ajiki? ko yan uwanta suke nemanta? ai dama dole su nemeta!! ”
Kamal kallonta kawai yake ganin tana ƙoƙarin wucewa ɗaki ya sa yace”Noor!” Ta juyo Amma Bata dawo ba, a hankali yace “bakya tunanin ‘yan uwanki suna cikin wani hali na rashin ganinki? kuma haryanzu baki ga buƙatar ki sanar damu komai ba!?”
shiru tayi ba tare da tace komai ba, a hankali umma ta ƙaraso inda take ta dafata tace”Noor bana miki kallon ƙasa da abinda na haifa, bakya tunanin idan ke ‘ya tace kika bar gida irin haka, hankalin dole ya tashi to bare mahaifiyar ki, Yakamata ki faɗa mana abinda ya rabo ki da gida Noor, ko kina tunanin bamu kai musan damuwarki bane ?
da sauri ta girgiza mata kai tana faɗin”umma dan Allah karkice haka, wallahi kun kai kuma har kunfi haka a gurina”ta share hawayen da ya zubo mata tace “insha Allah na muku alƙawari yau zaku san komai game dani, amma ina neman alfarmarku, ku bari zuwa baba ya dawo zuwa dare, ina so na baku labarina a gaban sa “umma ta yi murmushi tana faɗin Allah ya kaimu Allah ya muku albarka “suka amsa da ameen
Maimoon#
*💖*ABNUR**💖
*By* *maimoon* 🤓
*Elegant* *online* *writers* 📚📖
*Free* *book*
*Page* *4*
Kamar yadda ta faɗa kuwa, hakan ce ta kasance, bayan sallar isha duk suka taru a ɗakin Baba ,kasancewar Umma ta sanar masa komai ,
Kamal na shigowa ,Umma ta aikasa ya kira Noor,tunda ya zo ya kirata take jin faɗuwar gaba,shi kuwa dama bai tsayaba, yana kiranta yayi juyawarsa ya koma ɗakin,but zuciyarsa na cike da ɗokin jin labarin nata.
Hijab ta sanya, tana karanto addu’a a ƙasan ranta ,tasan yanayin da take ciki yana da nasaba da tuno labarinta da zatayi.
a hankali ta ƙarasa ɗakin kanta a ƙasa ,sallama tayi duk suka amsa suna kallon ƙofar ,a hankali ta ɗaga labulen ɗakin ta shiga ,can nesa kaɗan da su ta zauna tana fuskantarsu gabaki ɗaya, a hankali ta gaishe da Baba,ya amsa da fara’a yana tambayar lafiyanta ,ta amsa da ladabi ,kana Baba ya ƙara da cewa
“Noor naji komai a bakin Aisha, tacemin yau Zaki faɗamana daga inda kika fito, da kuma dalilin fitowar taki ,naji daɗi matuƙa da kikayi wannan tunanin dan yana da kyau musan hakan ,saboda haka muna sauraranki kuma inaso ki faɗamana iya gaskiyarki”.
A hankali Kamal ya gyara zamansa yana kallonta ,Umma ma kallonta kawai takeyi,sai da ta share guntun hawayen idanunta, kafin ta fara da faɗin……
WAIWAYE (mafarin labarin)
_Garin_ _BAULAWA_ _dake_ _ƙarƙashin_ _jihar_ __Kaduna_Nigeria_
Yarinya ce yar kimanin Shekaru 16 ,doguwa ce sosai ,fara tass kamar balarabiya, fararen ƙafafuwan ta da babu takalmi take tsalle dasu, tana caɓalasu a cikin ruwan daya kwanta a ƙasan saboda ruwan saman da ake kan yi a garin,
Gaba ɗaya ta gama jiƙa jikinta,har gashin kanta da yake tare waje guda ta cureshi ,wani irin farin ciki take wanda fuskarta ya kasa ɓoyewa ,
Yara ne sun kai su shida a zagaye da ita,suna jiƙa jikinsu suna wasa ,ta biye musu kamar wata sa’ar su ,
duk wanda yake garin ya kwana da sanin wannan hali nata,tana matuƙar son ruwan sama, hakan yasa ko a ina take idan har ana ruwa to akanta yake ƙarewa, kuma abin mamakin shine ko irin zazzaɓin nan na mura batayi idan ta shiga ruwan.
Malaman makarantarsu kuwa sunsha dukanta, akan ana aji tana shiga ruwa, amma inaaa gobe ma zata koma har sun haƙora sun ƙyaleta .
Ɗaga kanta tayi sama ganin ruwan na shirin ɗaukewa ,ta ɓata fuska sauran yayyafin da ke sauƙa yana sauƙa mata a samar kyakkyawar fuskarta ,a hankali ta kama ƙasan rigarta tana matse ruwan, sannan ta nufi ƙasan bishiyan neem ɗin dake kusa da su ta zaro takalmanta ,ta sanya su ba tare da ta kula yaran da suke cigaba da wasansu,da ruwan caɓalin da ya kwanta ba kawai tayi hanyar gida.
A daidai zauren ɗan ƙaramin gidan ta tsaya tana sake matse kayan jikinta ,sai kuma tayi sallama tana ƙarasawa tsakar gidan ,babu kowa hakan ya bata daman saurin faɗawa ɗakinta ta kwaɓe jiƙaƙƙun kayanta,ta canza wasu ,ta buɗe jakarta ta ciro littafan makarantarta ta zauna ta naɗe ƙafafu ta ajiyeshi a gefe,
Jin alamar mutum na zuwa kusa da ɗakinnata ya sata saurin buɗewa ta fara karantawa ,ɗaga labulen Nenne tayi tana kallonta,sai kawai tayi murmushi tana faɗin
“Noor!”
Da sauri ta amsa “na’am Nenne” Nenne ta ƙaraso cikin ɗakin tace “ina jiƙaƙƙun kayan da kika jiƙa” shiru tayi tana kallon Nenne ta ƙasan ido ,a ranta tana addu’ar Allah yasa kar tayi mata faɗa,
Ai kuwa kamar Nenne tasan miye a ranta ta soma faɗin “wai Noor meyasa baki san ciwon kanki bane sam,mutum bayi da aiki sai shiga ruwan sama, bakya tsoron sanyi ya kamaki?”
Ita dai bata ce komai ba, sai ma wasa da ta shiga yi da takaddar hannunta ,idanunta na cika da hawaye ,dan Allah na gani batason faɗa sam ,tsorata ta yakeyi ,
Tsagaita wa Nenne tayi da faɗan,sanin halin ƴartata ta ƙarasa kusa da ida tana jawota jikinta,ai kuwa kamar jira take ta rungume ta ta soma kuka, shiru Nenne tayi sai kuma tace “Noor,bawai Ina miki faɗa bane dan bana sonki Ah ah ina miki faɗane saboda babu wanda ya kaini sonki, a yanzu ina tare dake ,watarana ba na nan Noor,banaso ki sha wahalan rayuwa ko bayan raina ,shiyasa nakeso ki san ciwon kanki tun yanzu,Noor ko babu komai watarana aure zakiyi ki tafi gidanki ,koh haka zaki je ki masa idan kunyi auren ?” ta tambaya tana murmushi jin bata amsa ba sai ajiyar zuciya da take sauƙewa ,yasa Nenne cigaba da magananta dan tasan ba amsawar zatayi ba ,
“Kina jina Noor”Nenne ta faɗa tana shafa kanta ,girgiza mata kai tayi ,Nenne tace”Noor ko babu aure Akwai mutuwa ,banaso na rigaki mutuwa ki shiga wani haali,da sauri ta ɗago tana rufe mata baki take wasu hawayen suka sauko mata ,ta sake rungume Nenne tana faɗin “Nenne bazaki barni ba, idan har kika mutu nidai binki zanyi,kuma Ni bazan yi aureba har abada”.
Murmushi kawai Nenne tayi tace “to shikenan naji ,yanzu ki cigaba da karatunki bari naje wani unguwa yanzu na dawo” ,da sauri tace Nenne zan biki ,nan take Nenne ta haɗe rai tace bazaki bini ba kuma idan kika kuskura kika fita a gidannan kafin na dawo zan saɓa miki” ,a hankali ta gyaɗa kai tana faɗin “insha Allahu Nenne ”
Nenne ta fice a ɗakin ,ita kuma ta cigaba da karatun ta tana tunanin,” ina Nenne take zuwa kwana biyunnan da bataso ta sani?”
Sai da ta tabbatar Nenne ta bar gidan sannan ta rufe littafin, ta mayar jakanta, ta ɗauko jiƙaƙƙen kayan taje ta shanya ,sannan ta dawo tayi kwanciyar ta a ɗan ƙaramin gadonta ,tana sake tunanin maganganun Nenne,
Ita bazata yi aureba har abada, saboda bazata taɓa yadda ,wani yayi mata abinda mahaifinta yayi ma Nenne ba,kowa yasan mahaifinsa amma banda ita,ko kamanninsa bata saniba, sai sunansa da take anfani dashi ,alhalin yana raye ,yana birni yana cigaba da rayuwarsa ,kamar bai san da su ba.
_ABUJA_ _NIGERIA_
Murza steery kawai yake, hankalinsa gabaki ɗaya yana kan tuƙin da yakeyi ,a hankali yayi horn a gaban wani babban Duplex house,mai gadi ya wangale masa gate ɗin yana ɗaga masa hannu,bai bi ta kanshi ba, sai ma cusa motar da yayi cikin gidan Yana driving a hankali ,fuskarsa ɗauke da wata ƙasaitacciyar murmushi,tafiya kamar na minti takwas a cikin gidan, ya kaisa parking space ɗin da aka adana dan motocinsa .
A hankali ya ƙarasa ciki yayi parking, sannan ta fito daga motar, wani remote ya danna, nan take motar ta ɗagu sama ta jeru a cikin ƴan uwanta da suke hawa hawa ,anan take wata motar daban tayi replacing ɗin waccar,
body guards ɗinsa su shida ya kalla yadda suka tsaya suna jiran umurni,bai ce musu komai ba, ya nufi main entrance ɗin gidan, yana taɓa bluetooth ɗin kunnensa ,a hankali cikin murya mai amo ya fara faɗin “then they are all fired” ɗan shiru yayi yana cigaba da tafiyarsa, alamar yana sauraron mai maganan sai kuma yayi ɗan murmushi yana faɗin,”then I will meet you in 3 hours time”
daga nan ya kashe wayarsa ,daidai ya iso ƙofar da zai sada shi da main hall na gidan ,security ɗin ƙofar ya sanya sannan ya ƙara sa cikin parlorn yana zama a kan kujera , turarensa na _SHUMUKH_ shi ya kaima su Amina da ke kitchen saƙon dawowarsa, dan tuni ya karaɗe ko ina ,
da sauri Yasira ta fice daga kitchen ɗin ,kasancewar ita ce in charge na kitchen ɗin ,ɗan nesa dashi ta tsuguna tace ” Sir lunch is ready , should I serve you!?” bai ɗago daga danna wayar da yakeyi ba, ya miƙe ya nufi bedroom ɗinsa Yana faɗin “maybe later” da kallo kawai ta bisa .
wani ɗaki ya shiga ya jingina da bangon ɗakin yana bin ɗakin da kallo ,cameras ne kala kala ,da kuma hotuna iri iri na nature da na mutane iri iri ,murmushi kawai yayi ya nufi Camera ɗaya ya ɗauka, sannan ya ƙarasa balcony ɗin ya kai Camera ɗin idonsa, sannan ya ɗauki entire area ɗin a hoto ,yana jin matuƙar farinciki,
ɗaukan hoto is his passion,he is very proud to be an explorer ,tunanin inda zai je next domin ɗaukan hotunansa yakeyi ,yana buƙatar zuwa guri that is full of nature, but still local,
Yana son capturing al’adu da kuma sabbin abubuwa that’s why yake neman inda zaije a cikin Nigeria ya gaji da capturing ƙasashe ,so yake ya fito da beauty na ƙasarsa ,ya kamata yayi research yaga ina zaije tourism this time a cikin Nigeria,
fita yayi a ɗakin ya nufi ɗakinsa, ya zauna gefen gado yana dialling Numbern Maami, ringing biyu taɗaga tana faɗin “Habibi” a hankali kuma a shagwaɓe yace “Maaami ” yadda yayi maganar yasa ta faɗin “and now ,me kake so kuma this time!?”,wani murmushi yayi dan yasan Maami ta gama ganesa ,ya shafa yalwataccen sumarsa, da bayida maraba da ta asalin larabawan Dubai, a hankali yace”not much Maami ,kawai suggestion ɗinki nake nema akan wani abu”
tace “ok am all ears Habibi, hope dai bawani abu bane ya dameka ko” murmushin ya kuma yi yana lumshe idanunsa sannan yace “not at all ,kawai dai so nake nayi exploring a ƙasata ,Ina so naje tourism somewhere very local but full of nature ,shine nace bana tambayi suggestion ɗin ki ,i know, no one will know better than you do”
wani murmushi Maami tayi da har yana iya jiwowa tace ” ok then why not Kaduna state well the state is full of nature just the way you like it” shiru yayi sai kuma yace ” amma kin manta nace miki local ,Kaduna ai is too polished for what I want”
dariya Maami tayi tana faɗin “and what about villages ɗin dake under Kaduna” ɗan shiru yayi sai kuma yace “kamar wanne kenan?”
“Wannan kuma you have to research to find out ” “okay Maami ,Abbu fah ?” “Abbu yaje finalizing deals da wasu companies a ukraine ” “okay then I guess we will talk later” “okay Habibi take care” a hankali yace “sure” sannan ya katse wayar ,ajiyeta yayi ya jawo laptop ɗinsa ya shiga yin research akan Kaduna state ,
_BAULAWA_ ya sake maimaita sunan ,a hankali yayi murmushi yace “i guess I already got it!”
Wayansa ya ɗauka yayi dialing Numbern personal assistant ɗinsa , Yana ɗagawa yace masa “we are going to Kaduna by Wednesday ,so prepare the needful ” “yes Sir ” taufeeƙ ya amsa ,kashe wayar yayi yana faɗawa kan gadon a hankali ya furta”its going to explore, Allah yasa na samu abinda nakeso a wannan ƙauyen” ,sai kuma ya ƙara murmushi yanajin kamar wani al’amari mai girma na tunkarosa
Is it really going to explore!?me zai faru a ƙauyen BAULAWA ,zai samu abinda yake so kuwa !?🤓the story has just begun🤝
*ABNUR*
*By* *maimoon* 🤓
*Elegant* *online* *writers* 📚📖
*Free* *book*
*Page* *5*
*Wednesday*
*Abuja Nigeria*
Ƙarfe 7:30 dai dai, ya fito daga Gym ɗin dake cikin gidan ,gaba ɗaya ya gama haɗa zufa,Gym wears ne a jikinsa na kamfanin Nike,Wanda ya karɓesa matuƙa kamar dan kwalliya ya sanyasu, a tsanake yake haura steps ɗin duk da kuwa sauri ya keyi ,dan yau zai wuce Kaduna,
Amina,Asabe,da kuma,Yasira da suka ɗan buɗe ƙofar kitchen ɗin ,suka bisa da kallon, ajiyar zuciya suka sauƙe a tare,ganin ya gama haurawa,
Amina tace”wato kuɗi yayi ne Wallahi, shidai Sir a rayuwar sa ba shida matsalar komai,na farko ga kyau,ga kuɗi, ga iya shiga mai kyau,ke Ni komai yasa gani nake kawai dan kwalliya ya sa su” Asabe ta karɓe tana faɗin “hmm! kawai mata ta rage masa Wallahi shi ke nan ya cika cif-cif” Yasira tace”taɓ Sir kam ko zaiyi aure ba yanzu ba wallahi” Amina ta amshe “to sannu Maami!, kika sani?,wataƙila ma munkusa shan biki ko ba haka ba Asabe?” ta faɗa tana tafawa da Asabe , “aikuwa wallahi idan zaiyi ma ba sani zamuyi ba sai dai muji guɗar ƴan kawo amarya” Asabe ta faɗa tana ƙarasa wanke kwanukan dake cikin sink ɗin ,
Yasira dai bata sake cewa komai ba ta fice a kitchen ɗin tana wani ɓata rai ,Asabe ta sake tuntsirewa da dariya tana faɗin”kai kaji wahalalliya,wallahi wahala ce Bata isheta ba” Amina tayi ƙwafa tana faɗin “atoh ai ita taga zata iya” suka cigaba da wanke wanke suna taɓa hira.
Wanka ya fito ,a gaggauce ya shirya cikin riga da wando na kamfanin _LOUIS_ _VUITTON_ sai da ya gyara sumarsa yanda ya keso,sannan ya gyara gemu da sajensa wanda duk wanda yasan larabawan Dubai yasan yadda Gemu da sajansu yake,sai da ya gama ɓata lokaci a gyaran sannan ya ɗau perfume ɗinsa na _SHUMUKH_ ya feshe jikinsa da shi ,wani button ya danna ,wani drawer ya buɗe wanda takalmansa suke jere ,na different companies _,WHITE ADRIAN ITALIAN SHOES_ ya zaro ya sanya a ƙafafunsa ,ya ƙara danna wani button ɗin wani mini drawer ya buɗe ,Agogo ya cire guda ɗaya ya sanya sannan ya kwashi wayoyinsa da jakan laptop ɗinsa ya fice a ɗakin,
Da sauri bodyguard ɗinsa guda ɗaya ya ƙaraso ya karɓi kayan hannunsa yana gaishesa, Taufeeƙ dake tsaye ya ƙaraso shima tare da faɗin”morning Sir”. “morning “ya amsa a taƙaice ,buɗe masa mota yayi ya shiga baya ,shikuma ya shiga gaba,ɗaya daga cikin bodyguard ɗin ya shiga mazaunin driver ,sauran kuma suka shiga wata mota daban ,suka fice a gidan,
Amina,da Asabe dake leƙen window suka sauƙe Amina tana faɗin ,”to sai kuma sanda muka ganshi, Aljanun sun motsa ” Asabe ta ce”kee bari a jiki babu ruwana wallahi” Amina tace “ke ma ai kinsani irin wannan fitar da yayi tunda kika ga Sir Taufeeƙ ,to zasu je yawon ɗauke ɗauke ne ,ai dama tunda naga Sir Taufeeƙ ya zo jiya ya haɗa abubuwan ɗaukan hoto da akwati da komai Na Sir ,nasan to sai kuma mun gansu”
Asabe tace “to ai hutareren mu ” Amina tace “wallahi Fah ” suka koma kitchen, dan dama tun sauƙowar sa sukaji shine yana fita suka fito su leƙa .
Kasancewar tsakanin Abuja da Kaduna ,ba wani nisa bane ya sa su tafiyan da mota, ƙarfe biyu saura suna cikin Kaduna, hotel suka wuce, wanda dama Taufeeƙ ya gama shirya komai ,sai da suka tsaya sukayi sallah ,sannan suka ƙarasa , a hankali ya juyo ya kalli Taufeeƙ yace”tomorrow by 8 “zamu tafi ,make sure by 7 waɗancan sun koma Abuja ,”
a ladabce Taufeeƙ yace “Sir your security matters, da dai anje da su for security purposes”.
“just do as are told mr” ya faɗa ba tare da ya juyoba ,
“pardon Sir ,your wish is always my command , za’a yi kamar yadda kace”
bai sake cewa komai ba har suka iso ƙofar ɗakin nasa ,da sauri Taufeeƙ ya sa katin ,ƙofan ta buɗe ,sai da ya tabbatar ya gama masa duk wani abun da zai buƙata ,kafin ya bar ɗakin ,ya nufi nashi ɗakin dan shima yana buƙatar hutu.
Washe gari tun bakwai ya sallami bodyguards ɗin suka koma Abuja, kamar yadda Zannur ya buƙata ,
ƙarfe takwas dai-dai ya fito daga ɗakin, ya shirya tsaf cikin ƙananan kaya, kansa sanye da facing cap sai shade a idanunsa , Snickers ne a ƙafansa na kanfanin Adidas ,a hankali yake tafiya Taufeeƙ na biye dashi bayan yaje ya yi checking out daga hotel ɗin ,har packing space ɗin, “pass the key” ya faɗa a taƙaice”
Taufeeƙ ya miƙa masa key ɗin a zuciyarsa yana faɗin “shi zaiyi driving kenan” mazaunin driver ya shiga ,sai da Taufeeƙ ya gama saka jakansu da kuma jakan kayan cameras da zasu buƙata, a motan,sannan ya buɗe mazaunin mai zaman banza ya zauna ,
warming motar yayi sannan ya tada ya fice a hotel ɗin, map Taufeeƙ ya buɗe ya ajiye a gaban motan ,yana ganin directions ɗin daya kamata subi,
suna fara shiga garin yayi parking motar ya sauƙa , Taufeeƙ ma ya sauƙa , makullin ya wurga masa ya caɓe ,shikuma ya buɗe bayan motan Camera ya ɗauka ya haɗa komai nata sannan ya koma wajen mai zaman banza , Taufeeƙ yayi murmushi yana shiga mazaunin driver ,a zuciyarsa yana tunanin da alama za’a samu abinda a ke so a wannan garin.
Basu wani ƙara tafiya mai yawa ba sukaga hanya ta ƙare mota bazata iya bi ta shiga ba ,sauƙa Taufeeƙ yayi ya dudduba sai kuma ya dawo yana faɗin “Sir i don’t think akwai hanya fah da mota zai ƙarasa, sauƙe Camera dake idonsa yayi yace “so!?”
Taufeeƙ ya sosa ƙeya ,yace “I guess da ƙafa zamu ƙara sa ,ina ganin ƙauyen is just a little bit ahead,
murmushi Zannur yayi ganin yayi capturing butterfly ɗin da yake ɗauka ,ba tare da yace komai ba ya sauƙa a motar da sauri Taufeeƙ yace “Sir zan kira faruƙ yana cikin Kaduna sai ya zo ya juya da motar ,gyaɗa masa kai kawai yayi yayi gaba yana sake kallon ɗan hanyan da zasu wuce ɗin.
A firgice ta farka daga baccin daya kwashe ta a zaune ,ta miƙe da sauri tana leƙa tsakar gida ,hasken data gani tarr ne ya sata komawa ɗakin da sauri ta ɗauki jakan makarantar ta ,da roban abincinta tasa goran ruwanta a jaka ,sauri sauri ta fito dan tasan yauma tayi latti,tun asuba ta shirya dan kartayi latti amma gashi sai da tayi latti ,ɗakin Nenne ta leƙa ,taga bata ciki,”to ina Nenne taje da sassafe nan” ganin batada amsa gashi tana sake ɓata lokaci ya saka tai saurin fita a gidan ,
sauri sauri take tafiya ,dan dai makarantar da ɗan tazara,ganin saurin bazai mata ba yasata kwasa da gudu , Allah Allah take ta isa ,saboda yau ne za’a faɗi mutum ɗaya a duk cikin makarantar da ya samu scholarship ɗin zuwa cikin Kaduna karatu , gwamnati zata ɗauki nauyinsa saboda hazaƙarsa ,
Tun da ta shigo taga kowa na aji ,aji ta wuce tana sanɗa a ƙofar ajin ta tsaya ganin akwai Malama a ciki ,sai da taga Malamar ta fara rubutu tukun tayi sauri ta shigo , ta zauna a baya ,sannan ta miƙa ma na kusa da ita jakarta ,a haka sukayi ta passing passing ɗin jakar har kujeran gaba ,wanda shine wajen zamanta ,da dabara ta dinga canza wajen zama har ta iso gaba,tana shirin zama kawai Malaman ta jiyo ,
“Noor!” Malaman ta Kira sunan ta ,da sauri ta juyo ” Malaman tace “You Are late again ,right!?” da sauri acikin harshen turanci ,dan kar ta ƙara ma kanta laifi idan tayi venacular tace, “dan Allah Malama kiyi haƙuri ,wallahi makara nayi” ,juyawa Malaman tayi ta cigaba da rubutu tana faɗin “zo ki tsaya a gaban Allo har sai na gama in faɗa miki hukuncinki” tsaya wa tayi tana marairaicewa ,Malama ta sake cewa ” kafin na ƙirga uku na ganki a gaban Allo Noor,ɗaya.. ,biyu..” kafin tace uku tayi saurin ƙarasawa gaban Allon ta tsaya, tana kallon duka ƴan ajin,
sai da Malama ta ƙara sa rubutun tukun tace “toh yanzu kafin a fara darasi, ina so in sanar da ku ,mutum ɗaya a cikin makarantar nan da Gwamnati ta ɗauki Nauyin karatunta ,bakowa bace face…….”
Duk ɗalibai suka zuba mata ido ,sai da ta ɗan yi murmushi kafin tace ” _NA’IMA_ _RAZAƘ_ _ABDULKARIM_ wacce kuka fi sani da _NOOR_ ” .
Duk student ɗin suka hau murna dan dai sun san ,she deserve it ,itakam ta kasa ƙarasawa ma ,sai da Malamar tace mata “congratulations” tukun ta ƙarasa da sauri ta rungume ta kawai ta fashe da kuka,
Malamar ta shafa kanta tace “karki damu You deserve it Noor,ni dama nayi tunanin haka”
a hankali ta ɗago tace” Malama dan Allah ina so zan tafi gida” , “kije badamuwa gobe sai ki dawo congratulations once again” da sauri ta juya ƴan aji na ta mata murna ,tana binsu da murmushi ,
sai da ta fita daga makarantar tukun tayi wani tsalle tana faɗin “Nenne na samo scholarship zan tafi birni ,ita kaɗai take surutunta tana Allah,Allah ta isa wajen Nenne,
“Baiwar Allah” taji an mata magana da sauri ta juya tana kallon wanda yake mata maganan ,saida ta runtse idanunta ta buɗe ganin ɗan birni ,a zuciyarta tana faɗin ,kar dai tun yanzu ne za’a tafi da ita karatun ,ah ah gaskiya ita fah idan ba da Nenne zasu tafi tare ba ,bazata je ba,
“Baiwar Allah” Taufeeƙ ya sake faɗa yana kallonta yadda yaga ta wani rufe idanunta da sauri ta buɗe idanunta ta kallesa ,ta marairaice tafara faɗin ,”dan Allah ba yanzu ba ,ai Ni bansan yau za’a tafi ba ,na ɗauka sai na shirya dan Allah ku bari na fara ɗauko Nenne sai mu tafi tare,
kallonta kawai yakeyi har ta gama tukun yace ” baiwar Allah tambaya nakeyi, a garinnan ko akwai wani waje da za’a iya biya a kwana ”
shiru tayi sai kuma ta watsa hannunta tace “oho” “kina nufin baki sani ba”
“Eh” ta faɗa tana juyawa ta cigaba da tafiya “keeeee” taji an faɗa da wata Muryar da ta tilasta mata juyowa tagako waye dan ta tabbata ba shi ne wanda ya tambayeta ba.
#maimoon
*ABNUR*
*By* *maimoon* 🤓
*Elegant* *online* *writers* 📚📖
*Free* *book*
*Page* *6*
A hankali ta juyo, tana sauƙe idanunta a kansa,yana tsaye ,tun daga ƙafafuwan sa, take kallonsa, har takai kan fuskarsa,kallonsa kawai takeyi babu kiftawa, bata san yaushe ya ƙaraso kusa da ita ba,sai dai kawai ji tayi yace,”to ko zaki nuna mana gidan mai garin,garinnan?”
Sai da ta saita kanta sannan tace “to nidai yanzu wallahi sauri nakeyi,saboda haka ku nemi wani ya rakaku, inada wani abu mai matuƙar muhimmanci a gaba na yanzu haka”
bata jira abinda zai ce ba, tayi saurin juyawa tana cigaba da tafiya,
Taufeeƙ ya sake baki, yana kallonta,lallai sai yau ya yarda, rashin sani yafi dare duhu,idan ba haka ba,the whole Sir Abubakar shuraim (Zannur)banda,sa kai wanda hausawa suke cewa ,yafi bauta ai ko ganinsa ma wannan bata isa tayi ba wallahi,
Shidai ya na tsaye a wajen kamar wani statue, sai da ya kalli ko ina yaga babu alamar mutum sannan ya juya ya kalli Taufeeƙ,da sauri Taufeeƙ ya ce
“Sir You don’t have to worry, I will manage everything” daga haka ya yi saurin juyawa ganin wani matashi ya tsayar da shi, sai da ya tambaye sa ko akwai gurin kwana na kuɗi, matashin yace babu,kafin yace masa ko zai rakasu gidan mai gari, matashin yace babu damuwa,
Sai da saurayin ya rakasu har gidan mai gari, Taufeeƙ ya ce “ɗan saurayi to ko zaka mana sallama da shi mai garin,kafin ya rufe bakinsa mai gari ya fito, yana gyara rawaninsa, matashin yace”gashi nan ma maigarin,
Taufeeƙ ya masa godiya shikuma ya juya ya bar wajen,mai gari ya washe baki ganin Larabawa a ƙofar gidansa yana faɗin “ah ah baƙi mukayi,to to to sannunku da zuwa”,cikin gidan ya koma ya fito da tabarma,ya shinfiɗa musu,sai da suka zauna sannan Taufeeƙ ya fara masa bayanin dalilin zuwan nasu.
Mai gari yayi gyaran murya yana faɗin”dan dai wannan babu wata matsala,dan gurin da zaku zauna kam,amma sai dai fa zaku biya haya”.
Taufeeƙ yace babu “damuwa,zamu biya ko nawane”, mai gari yace “to madalla sai ku tashi in nuna muku wajen”.
Sai da ya nuna musu inda zasu zauna, Taufeeƙ ya biya,sannan mai gari ya koma gida yana ta murna, ya samu kuɗi.
Sai da Taufeeƙ ya gyara yadda zaima Sir Zannur daɗi sannan ya shigo musu da kayayyakin su, shidai bai ce komai ba, dan dai ya je wuraren da suka fi wannan complications, idan dai har zai samu abinda ya ke so, bare nan.
A gajiye yake, hakan yasa wanka kawai yayi, ya kwanta, yanajin nishaɗi, daga gobe yakeso ya zaga garin ya gani idan har zai samu abinda yakeso duk da yaga alamar hakan tun daga shigowar sa garin.
A take bacci ya ɗauke shi, Taufeeƙ da ya shigo ɗakin bayan shima yaje nasa ɗakin ya shirya, ya buɗe jakan kayansu ya ɗauko bargo,mai matuƙar kyau da taushi, ya lulluɓa masa, ya tsaya ya na kallonsa,
“Sir is such a rare gem, samun kamarsa sai an tona gaskiya,yana fata da kuma addu’ar Allah ya bashi mata, wacce zata bashi farin ciki, wacce zata kula da shi,dan he really deserve that, Amma bai san meyasa sam batun aure baya cikin ajenda ɗin rayuwarsa.
Fita yayi daga ɗakin, ya ja masa ƙofa ya fito waje, tafiya kawai yakeyi yana kallon garin mai cike da ni’imomi iri-iri,sai yamma ya dawo,a shirye ya gansa tsaf da alama fita zaiyi yace
“Sir zakaga garin ne” “eh” kawai yace ya sa kai ya fice, shima ya bisa a baya, sai da suka zaga garin sosai, sai da sukayi sallar isha, sannan suka dawo gida,a gaskiya garin yayi masa ba kaɗan ba,yasan zai samu abinda yakeso a nan.
Daga gidan mai gari aka kawo musu lafiyayyen abinci,har da su kaza, Taufeeƙ ne kaɗai yaci, shi kam kwanciya kawai yayi, daga haka bacci ya ɗauke shi
Ita kam Noor tunda ta koma gida,tundaga tsakar gida take ƙwala kiran “Nenne,Nenne,burina ya cika,rayuwarmu ta kusa canzawa Nenne,ganin Nenne bata fito ba ya sata ƙarasawa ɗakin,da sauri Nenne dake kwance tana fitar da numfashi da ƙyar, ta juya mata baya,dan bataso ta fahimci halin datake ciki,amma inaa ta makara,
Da sauri ta ƙara so ta tsuguna tana kallon Nenne,hankali tashe ta soma faɗin “Nenne baki da lafiya ne, me ya sameki Nenne na”, cikin ƙarfin hali Nenne ta riƙe hannunta sannan ta shafa kanta tana faɗin,ki kwantar da hankalinki,babu komai fah kawai zazzaɓi ne yake damuna tun safe,kuma naji sauƙi sosai”,Noor ta sauƙe ajiyar zuciya,tana faɗin Alhamdulillah, ai nazata ciwonki ya tashi”,
Gyara zama tayi ta riƙe hannuwan Nenne duka biyu tana faɗin “Nenne na samu scholarship,gwamnati zata ɗau nauyin karatuna a cikin gari”,
Nenne ta faɗaɗa
murmushinta tana faɗin “masha Allah, Allah yayi miki albarka Noor,ya haɗaki da alkhairi ko bayan raina”, Noor bata wani kula da batun Nenne ba ta miƙe tana faɗin,
“Gobe ranar bikin shekara,dole ma na je na binciko abinda zan ci ado gobe dashi”, ta faɗa tana miƙewa tabar ɗakin,
Ai kuwa ranar batayi bacci da wuri ba,sai kai komo take tsakanin dakinta,da ɗakin Nenne, sai wajen ƙarfe sha biyu tukun tasamu bacci ya ɗauke ta a ɗakin Nenne,
kallonta kawai Nenne takeyi yadda take baccinta,a nutse,tana fata da addu’ar Allah ya bawa ƴar ta kyakkyawar rayuwa,mai ƴanci ba irin nasu ba,shafa kanta tayi,sannan ta mata addu’ar bacci ta shafa mata,itama ta lumshe ido,take bacci ya ɗauke ta.
Washegari tun safe ta shirya acikin uniform ɗin ta na boko,sai lokacin waɗannan mutanen jiyan suka faɗo mata,to me ya kawosu ƙauyen su,more especially ɗayan ma,yayi mata kwarjini da yawa,ko me zasu je yi a gidan mai gari,
da wannan tunane tunanen ta gama shirinta tsaf ta yi ma Nenne sallama, ta fice a gidan,dan dai yau batayi latti ba,
Tun safe Sir Zannur yake zaga garin, Taufeeƙ dai binsa kawai yakeyi,idan yaga abinda ya birgesa sai ya ɗauka a hoto,mutanen ƙauyen sai kallonsa sukeyi,
wasu samari yaga sun zuba masa ido,ganin irin kallon da suke masa ya sa shi ƙara sa wa inda suke yace
“sannunku”
, da sauri ɗaya yace sannu bawan Allah,kafinma ya sake magana duk suka taso suka zo kusa dashi,suna masa sannu,
murmushi yayi yace “in ɗauke ku hoto!? Ya tambaya yana ƙoƙarin sakewa da su,da sauri suka ce “eh” ai kuwa suka hau jeruwa, ya ɗauke su yana nuna musu,
ai kuwa sai yaga mutane sunata ƙaruwa, wai suma a ɗauke su.
abin har ya bashi dariya, harda tsofaffi gyarawa yayi yana ta ɗaukansu a hoto,yana ɗan yin baya,don ya samu capturing abinda yake so,
buge mutum ɗin dayayi garin komawa bayanne ya sashi saurin juyowa yaga waya buge, bai sani ba, ita kam da har ta kai ƙasa, kasa ɗagowa tayi,
a hankali ya ƙarasa wajenta ya miƙa mata hannu,ɗaga kai tayi ta kalleshi,tabi hannunsa da yake miƙa mata da kallo,
miƙewa tayi ba tare da ta kama hannun nasa ba, tana karkaɗe jikinta,
A hankali yace “meyasa kina tafiya bakya kallon gaban ki”
Da batayi niyyan kulasaba, amma jin abinda yace ya saka juyowa ta kallesa da kyau sannan ta maimaita abinda ya faɗa sai kuma tace”malam sai kuma aka ce maka, kai ka dinga tafiya da baya da baya akan layin da ba siya kayi ba ko”
Kallonta ya tsaya yi,sai yanzu ma ya gane ta da sauri Taufeeƙ ya ƙaraso,yana kallonsu,
Bata sake cewa komai ba, kawai ta juya tayi wucewarta,baki sake suka bita da kallo, kafin yayi ƙwafa yana juyawa ya bar wajen,
Tun da aka tashi school ta dawo gida take shirin bikin shekara da ƙyar ta samu ta gama shirya wa, duk da bata yi kwalliya irin na yan ƙauye ba, sai dai ɗigon kwalli da ta yi guda uku a ƙasan haɓarta,sai fararen lumsassun idanunta da ta sanya wa kwalli,
ta fito rass da ita,sai da ta shiga tayi ma Nenne sallama, sannan ta fita a gidan ta nufi wajen bikin shekara wanda ake yinsa duk shekara a ƙauyen,duk wani al’adu nasu za’a yi a wajen.
Tana isa wajen ta tarar har an fara, can nesa ta samu ta tsaya tana kalle kalle,
Tun shigowar ta wajen ya lura da ita, ya tsaya da ɗaukan hoton da yakeyi yana kallonta,shi kansa bai san dalilin da yasa yake kallonta ba,samun kansa yayi da ɗaukan ta hoto ba tare da ta sani ba,
yayi mata yakai kala uku, kafin ta juyo, karaf idanunta ya shiga nashi,kallonsa tayi taga yana ɗaukan ta hoto ai kuwa ta wani murguɗa baki ya ɗauka a haka,
sai da ya kalli cikin
camera ɗin sai ya samu kansa da yin murmushi kawai,bai sake kallonta ba ya cigaba da ɗaukan abinda ake yi,
A ƙarshe aka kira ƴanmata,aikuwa ita da ƙawayenta suka shiga,waƙa aka saka musu na mutan ƙauye,suka hau yin rawar a nutse, a hankali, baya ya koma yana kallonsu, yadda suke rawar a tare suna juyawa, ba ƙaramin burgesa abin yayi ba, hoto ya shiga ɗaukan su,wanda duk nata ya fi yawa a ciki,
Ba a tashi taron ba har kusan magrib, duk aka fara watsewa, Taufeeƙ ya ƙara so inda yake a tsaye ya jingina da wata bishiya, yana kallon hotunan, a kan nata ya tsaya yana kallo, yanda ta murguɗa baki da taga yana ɗaukan ta murmushi yasake yi, a zuciyarsa yana faɗin”she is just Soo naive”.
Taufeeƙ yace “Sir Are we leaving now,Yakamata ka huta fah,”. Ɗagowa yayi yakallesa yana jin nishaɗi wanda ya daɗe baiji irinsa ba,ko dan bai taɓa ganin al’adu namu na ƙasar Hausa bane,shi kansa bai sani ba,
Batare da ya kalle shi ba yace “kaje zan dawo anjima, ina son na yi wani abu first”.
Taufeeƙ ya buɗe baki zai yi magana ya ɗaga masa hannu kawai, bai sake cewa komai ba ya juya ya bar wajen.
Tsayawa yayi yana tunanin to me ya hanashi komawa gida,what is he waiting for,shi kansa bai sani ba,
kamar ance ya ɗaga kansa ya hangeta tana nufo inda yake,ita kaɗaice sai ɗan ƙaramin sanda,da ta riƙe a hannunta tana wasa da shi,
tsayawa tayi tana magana da su lantana, sai dariya takeyi, Camera ya ɗauka ya cigaba da ɗaukan ta hoto, yadda take dariyan ya sa ya kasa ɗauke idanunsa a kanta,
kamar ance ta juyo kuwa taga, yana ɗaukan ta, a fusace ta taho inda yake, tana kallonsa ta fara faɗin,
“malam wai lafiya”, sai da ya kalleta kamar bazai yi magana ba sai kuma ya gyara tsayuwa yace, “me kika gani,na Sanki ne da zaki tambayeni lafiya”.
Da mamaki take kallonsa sai kuma tace “baka Sanni ba, Ni ma ai ba saninka nayi ba, to meyasa kake ɗaukana hoto?,
Wani kallo yayi mata sannan yace”sai kuma wa ya ce miki ke nake ɗauka?, saboda ke kaɗai ce, sai ke zan ɗauka?,ga kyawawan ƴanmata nan in rasa wa zan ɗauka sai ke”.
Sake baki tayi tana kallonsa sai kuma ta juya a fusace zata bar wajen ba tare da ta ce masa komai ba,
riƙe hannunta taji anyi, da sauri ta juyo tana kallonsa da mamaki, da sauri ya sake hannun nata yana kallonta da idanunsa da suke sakata jin ta kasa nutsuwa,
A hankali cikin lallaɓi yace, “ƙanwata me yake haɗa mu ne kam naga tunda nazo garinnan muke samun matsala da ke”, jin a yadda yayi maganan ya sata faɗin”to waya sanine,”
murmushi yayi sai kuma yace to shikenan tunda baki sani ba, can we be friends? Da sauri ta kallesa sannan ta ce ƙasa ƙasa”Ni bana abota da maza”
Kallonta ya ƙarayi,shi dariya ma take basa wallahi, sai kuma yace “kinga Ni baƙo ne a garinnan, ko a garinku bakwa son baƙi ne?
Girgiza kai kawai tayi, yace yauwa ƙawata, to yanzu miye sunan ƙawar tawa a hankali ta ce “Noor”
“Ni kuma Zannur” ya faɗa yana kallonta,murmushi kawai tayi,sai kuma yace to,yanzu kinga tunda mun zama friends shikenan nima sai ki nuna min garinku koh!?, Gobe insha Allahu zan jira ki sai ki zaga dani in ga garinku, ko bazaki nuna min ba? Ya tambaya yana kallonta,
“Zan nuna maka ” tafaɗa tana kallonsa, kawai mamaki takeyi daman ashe yana da sauƙin kai?,ai ita gani takeyi, yadda yake da kyau ɗinnan bazai ma kulata ba,
A hankali tace “sai da safe dare nayi zan tafi gida,
“To ƙawata sai goben zan jira ki anan”
Bata sake cewa komai ba ta juya ta wuce abinta,tsayawa yayi yana kallonta, shi mamakin kansa ma yakeji, sai kuma yayi murmushi, yana shafa kansa ya juya ya bar wajen,
a zuciyarsa yana tunanin maybe it’s because the girl is too naive and tana da innocent face,bai taɓa tafiya da yayi masa daɗi irin wannan ba,yaje ƙasashe da yawa Amma the happiness daya samu a nan is something else,
ɗakin Taufeeƙ ya buɗe yaga har yayi bacci, kawai ya ja masa ƙofan ya koma nasa ɗakin
sai da wanka, yayi Sallah, sannan ya shirya acikin kayan bacci masu matuƙar taushi, ya kwanta bai daɗe ba bacci yayi awon gaba dashi.
Itama hakan ce ta ɓangaren ta tunani tayi tayi dama haka ƴan birni suke da sauƙin kai, ko dai wannan ɗinne ya fita daban,sake shigewa jikin Nenne dake bacci tayi, itama bacci yayi awon gaba da ita.
What will happen next is the unthinkable,ƙaddara a ko da yaushe dama akace ta riga fata🤗🤓

Leave a Comment