Books Reviews & FAQs

ASP Zarah Hausa Novel Complete

*MANAZARTA WRITTERS ASSOCIATION*📚🖊️
*M*. *W*. *A*
_Putting smile on our readers faces._
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsapp
___________________________________

*ASP ZARAH*👩‍✈️

_Daga Alƙalamin_✍🏻
_Asmau Bint Abubakar_
_Jasmine_🌸🌸

*Da sunan Allah mai rahma mai jinƙai, dukkan yabo da godiya su tabbata gun Allah maɗaukakin sarki daya bani lafiya, ilimi, basira da kuma lokaci dana samu daman rubuta wannan littafin. Allah yaƙara dubun salati a gun mafificin halitta annabinmu Muhammad S. A. W da ahlinsa da sahabbansa dama dukkan masu bin tafarkinsa har zuwa ranar tashin alqiyama.*
*Ina roƙon Allah ya tsaremin alƙalamina daga rubuta duk wani abu dazai kawo ɓatanci a cikin al’umma. Allah ina roƙonka yadda nafara rubuta wannan littafi lafiya Allah kabani ikon gamashi lafiya, kurakuran dazanyi ciki Allah ka yafemin da wanda nasani da wanda bansani ba.*

*Littafin ASP ZARAH na kuɗi ne kada a ɗau haƙƙina ta hanyar karantawa batare da biya ba. Idan kinji kinason cigaba da karantawa toh ki biya kuɗi N300 kacal domin karantashi cikin kwanciyar hankali, idan kinsan zaki dinga yimin sharing ɗin littafi dan Allah kada ki biya kuɗin banaso. Duk mai buƙatar karantawa a tuntu6eni a 07048961623 domin biya da kuma shiga group*.

*Jan Hankali*: _Ƙirƙirarren labari ne. Ban yarda a canjamin littafi ta kowace siga ba batare da izinina ba. A bi doka a zauna lafiya_ .
👩‍✈️
👩‍✈️
👩‍✈️
👩‍✈️
👩‍✈️

_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_

*Free PAGE 1*

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un”.
Shine abinda matashiyar yarinya wacce ke sanye da kayan ƴan sanda take maimaitawa, alamu sun nuna cewa suma tayi aka watsa mata ruwa ta farfaɗo duba da yadda take a kwance a ƙasa idanu a rufe ga fuskarta data jiƙe da ruwan da aka watsa mata. Jin ana ƙoƙarin ɗagata a ƙasan ne yasata buɗe ido domin ganin mai taɓatan, Ammi ce wacce take matsayin ƙanwa ga mahaifinta.

Kallon fuskar Ammin tayi wacce ta kumbura tayi jazir saboda kukan da tasha domin hatta idanunta sun koma can ciki ba’a ganinsu sosai saboda kumburin da fatar idon nata tayi.

“Zarah kuka ba shine mafita ba a yanzu, kizo kiyi sallama dasu domin a samu damar kaisu makwancinsu da wuri.” Ammin ta faɗa cikin dasasshiyar muryarta.

Buɗe baki tayi domin magana amma kukan data kasayi tun farko ya riga maganartata fitowa, take kuwa ta fara rera kukan mai taɓa zuciyar duk wani mai sauraro.
Hannunta Ammi ta kama ta ɗagota tare da nufar inda gawarwakin mutane takwas dake sanye da suturarsu ta ƙarshe a cikin makara, koda ta iso da ita wajen sake hannunta tayi tare dayin baya domin kukane yakeson ƙara kece mata.

Cikin rawar hannu ta fara yaye mayafen daya lulluɓewa gawarwakin fuska tundaga kan gawa ta farko.
“Mahaifina, Mahaifiyata, Kakannina uku, ƴan biyun ƙannena sannan ƙaramar ƙanwata. Innalillahi wa inna ilaihi raji’un.” ta ƙara fashewa da wani sabon kukan mai taɓa zuciya, lokaci ɗaya kuma ta tsagaita tare da gyara rufuwar mayafan sannan ta ɗaga hannu sama ta fara addu’a.

“Ya rabbi, Ya rabbi, Ya rabbi. Ya Hayyu ya Qayyum ya Allah ina gode maka a cikin kowani yanayi dana tsinci kaina. Ya Allah kaine shaidata ban shiga aikin ƴan sanda ba saidan na taimaka gurin gyara ƙasata, Ya Allah kasani ina tsare duk wasu dokokinka bana saɓawa da gangan saidai a rashin sani. Ya ubangijina nasan ka fini son waɗannan bayi naka shiyasa ka karɓesu daga aron daka bamu, na karɓi wannan jarabawa hannu biyu sannan ina ƙara gode maka.
Ya Allah ga bayinka nan zasu iso gabanka Ya Allah kayi musu gafara ka yafemusu zunubansu wanda sukasan sun aikata dama wanda basu sani ba, Allah kayi musu rahama, Ya Allah ka tsare daga duk wata fitina dake cikin kabari Allah ka karɓi shahadarsu. Ya Allah kabasu wani ɓangare a cikin Aljannarka.
Ya rabbi baka aikata zalunci sannan baka barin masu aikawa, Ya Allah na kawo ƙarar duk wani wanda yake da hannu a cikin mutuwar bayinka muminai.”

Hatta mazan dake farfajiyar wajen saida suka zubda hawaye tare da jinjina jarumtar Zarah.
Batare da ɓata lokaci ba aka sallaci gawarwakin sannan aka tafi sadasu da gidajensu na gaskiya.

_Kafin faruwar wannan al’amarin_.

Tsantsar abota da aminci ne a tsakanin Malam Usmanu da Malam Adamu wanda ya rikiɗe ya kuma ƴan’uwantaka hakan ya samo asaline tun daga iyayensu da sukayi zaman aminci tare, hakan kuma ya ƙarayin sanadin da yaransu suka taso cikin shaƙuwa da son juna tamkar iyayen nasu sakamakon gidajensu dake maƙotaka da juna.
Asalinsu mutanen garin Deba ne a jihar Gombe kuma a nan suke da zama da iyalansu, da sana’arsu ta noma suke rufawa kansu da iyalansu asiri.
Malam Usmanu yanada mata ɗaya Faɗimatu da ɗansu Abdul_Jalal wanda shi kaɗai suka haifa. Yayinda Malam Usmanu keda yara biyu Sulaiman da Rumaisa sannan matarsa Aishatu.
Yaran sun taso cikin so da kulawar iyayensu, tare sukeyin komai tun yarinta har zuwa girmansu.

Sulaiman shine babba cikinsu wanda a yanzu haka yake zaune a cikin garin gombe tare da yaransa biyu Muhammad Jawwad da Nusaiba dakuma matarsa Safiyat wacce yaran ke kira da Momi. Inda ya kasance ɗan kasuwane a fannin ma’adanai.
Sannan Abduljalal dake zaune a garin bauchi da nashi iyalan inda yake aiki a babban asibitin tarayya dake jihar bauchi. Yanada matarshi ɗaya mai suna Zainab (Mami) sai yaransa uku Abubakar Sadiq, Rahma, sai Fatimah Zarah.

Rumaisa kuwa(Ammi) a ƙasar Cairo take zaune da mijinta wanda ya kasance ɗan kasuwa da ƴan biyun ta Muhammad Adil da Muhammad Shahid.

Duk da kasancewar ba guri ɗaya suke rayuwa ba, sukan ware lokuta domin zuwa ziyartar iyayensu a garin Deba. Hakan yasa yaran sukayi sabo da juna sosai in banda Muhammad Jawwad da tun bayan kammala karatunshi na firamari aka kaishi England domin ya cigaba da karatunshi a can.
Haka wannan familyn suke kasancewa koda yaushe cikin so da ƙaunar juna.

Mafarkin Zarah nason zama ƴar sanda ya fara tun lokuta da dama da take ganin ana zaluntar talakawa sannan ƴan sanda suƙi ɗaukan mataki, hakan yasa tasha alwashin zama ƴar sanda.
Daƙyar iyayenta suka aminci da wannan buƙatarta ta domin saida ta kaita ga kwanciya a asibiti tamkar bazata rayu ba, ganin haka ne yasa suka amince tare da kafa mata sharuɗɗan kare mutuncinta dana danginta.

Wani al’amari daya faru a rayuwarta wanda ta kasa mantawa shine.

_Garin Bauchi_
12:30nr

Gosulo ne sosai akan titin wanda ya kasance ana yawan samun cunkuson ababen hawa duk ranar juma’a saboda tare wasu hanyoyi da akeyi sakamakon sallar juma’a da ake gabatarwa. Cikin waɗanda gosulon ya tsayar harda direban daya ɗauko Zarah daga makaranta.
Saidai gabaɗaya hankalin Zarah dake cikin motar ya koma ga wata tsohuwar almajirah dake gefen hanya zaune da roba tana bara, sosai ta bata tausayi ganin babu wasu masu bata sadaka dayawa. Jakar makarantarta ta duba saidai naira ɗari biyu ne aciki..

“Baba Sule akwai kuɗi a hannunka ne”. Ta tambayi direbansu dake jan motar.

“Ehh baza’a rasa ba”.

“Zasu kai nawa ne.”

“Inajin zasu kai dubu biyar ko sufi haka”. Ya faɗa sanda yake ƙoƙarin ƙirga kuɗin daya zaro a aljihunshi.

Karɓa tayi tare da fita a motar ta nufi inda matar ke zaune.

“Sannu Baba ya zaki zauna a rana ki koma inuwa mana”. Cewar Zarah lokacin data ƙaraso gurin.

“Ƴar nan idan kayi nesa da jama’a wasu bazasu zo inda kake su taimaka ba dole sai mutum yazo inda suke.”

“Allah sarki to baki da mai taimaka miki ne.? ”

“Da inada mai taimakamin ba zaki ganni ni ɗaya ba ƴata.”

“Sunana Fatimah Zarah ne, ga wannan sadaka ce babu yawa.” ta miƙa mata kuɗin.

“Allah ya saka da alkhairi Batula, Allah ya albarkaci rayuwarki ya kareki daga sharrin maƙiya. Allah ya bani ikon taimaka miki watarana kamar yadda kika taimakamin.”
Cike da jindaɗi Zarah ke amsa addu’o’in kasancewarta mutum mai son taga babba nayi mata addu’a.

“Bari naje direba na jirana zan dinga tsayawa wani lokaci mu dinga gaisawa.”

“Toh nagode Allah ya albarkaci rayuwarki.” Almajirar ta faɗa a fili amma cikin zuciyarta cewa take “Bazaki ƙara ganina ba yau ɗinma na fito ne da niyyar taimakon mai taimako ne, kuma gashi kinyi sa’ar kasancewa wacce zan taimakawa.

Tun daga wannan lokacin sai ya kasance duk dare Zarah zatayi mafarkin wannan almajira sannan kullum zancen da take maimaita mata a cikin mafarkin shine. _Zaki haɗu da ƙalubale da dama a rayuwarki, ki zama mai hakuri da juriya tare da fauwalawa Allah lamuranki a duk lokacin da kika tsinci kanki cikin tsanani, sannan ki zama mai gaskiya a dukkan lamuranki. Kada kiyi zalunci kuma ki bari wasu su aikata, ki jajirce wajen bada gudumawar da za’a kauda zalunci a cikin al’umma._

Da farko abin baya damunta amma bayan tayi satikai tana neman wannan almajira a inda ta ganta sai abin yafara tsorata ta musamman da mutanen wajen ke faɗin basusan wata almajira ba, hatta Baba Sule data karɓi kuɗi a hannunshi wancan ranar yace bai san ina taje ba bayan ta fita a wannan rana. Lamarin na matuƙar damunta saidai ta kasa tunkarar kowa da lamarin.

A wata ranar lahadi ne tayi mafarkin ƙarshe da almajirar wacce bata kuma zuwa mata ba saidai maganganun data gayamata a wannan rana sun tsorata ta.
_Ni ba mutum bace ALJANA CE! kuma lokaci yayi dazan koma nahiyarmu, BATULA nayi miki alƙawari bazan ƙara zuwa miki a mafarki ko a zahiri ba amma kamar yadda na alƙawaranta zan taimaka miki idan lokacin taimakon yayi. Kada ki manta da nasihata a gareki domin zata taimaka miki sosai._
Tundaga wannan lokaci bata ƙara mafarkinta ba wanda ya gaskata mata cewa aljana ta taimakawa.

Lokacin data fara aikin ƴan sanda sai ya kasance ta jajirce sosai wajen ganin ta ƙwaci duk wani haƙƙin talaka da ake dannewa, hakan ya jawo mata farin jini tare da ƙarin matsayi akai-akai har zuwa yanzu da take matsayin ASP.

Alhaji Sulaiman, wato ɗan’uwan mahaifin Zarah nada tarin dukiya sosai da baisan adadinta ba. Babba kuma sanannen kamfaninshi shine _M.J JEWELS_. Kamfanin ya samu sunan ne daga Muhammad Jawwad wato ɗan shi na fari.
Ana sarrafa duk wasu nau’ika na kayan ƙaleƙale a wannan kamfani kama daga kan ƴan kunnaye, sarƙa, awarwaro, zobuna, agogo da sauransu wanda ake sarrafasu daga ma’adanai daban daban danginsu zinari, azurfa, lu’u lu’u da dai sauransu.
A shekarar data gabata ne yasamu nasarar mallakar lu’u lu’u wanda ya siya a hannun turawa da darajarshi takai dallar amurka miliyan talatin, an sakashi a wani akwatin tsaro na musamman wanda babu wani abu dazai iya fasashi koda guduma ne da bindiga dole sai mabuɗin shi wanda yake tamkar flash na jikin laptop. Kasancewar sai yayi shekaru da dama a ajiye kafin a iya sarrafashi yasa ya ɗaukeshi daga gidanshi inda yake da farko aka maida kamfaninshi saboda hare-haren ƴan fashi. Inda aka ajiyeshi a wani ɗakin sirri dake kamfaninshi, amma duk da hakan ba’a daina barazanar satar shi ba.
Ganin hakan ne yasa shida ɗan’uwan shi Alhaji Abdul_Jalal suka yanke shawarar maida shi gidansa dake bauchi bayan an damƙa tsaronshi a hannun Zarah.

Hatta iyayen basuda masaniyar a inda lu’u lu’un da akwatin tsaronsa suke tun bayan da aka damƙa mata ajiyarshi.

*ALPHA*👽

Alpha wani taƙadirin ɗan ta’adda ne dayayi ƙaurin suna a Nigeria dama maƙotanta, ya shahara sosai wajen sace-sace da fashi gami da kisan kai. Saidai abinda yake matuƙar damun al’umma shine babu wanda ya sanshi bare inda yake zaune domin yanada yara da dama masu yimasa aiki saidai hatta wasu daga cikin masu yimai aiki basu sanshi ba.
A duk lokacin da suka yi wani gagarumin laifi suna barin tambarinsu wanda yake sunan ALPHA ne haɗi da zanen bishiyar kwakwa🏝️, ta hakane ake ganewa idan sun aikata laifi saidai har yanzu ƴan sanda sun kasa kama koda ɗaya ne daga cikin masu yimasa aiki sakamakon manyan gwamnati da suke tare dashi.

Tun bayan daya samu labarin wannan lu’u lu’u daga bakin wani yaronshi na sirri wanda yake aiki a _M.J JEWELS_. Yasha alwashin sace shi saidai matakan tsaron dake jikin akwatin ne ya hanashi samun damar satarshi amma yana kan shiri wajen ganin ya mallaki wannan kadara tare da ɗaiɗaita kamfanin _M.J JEWELS_.

Bayan ya samu labarin inda aka maida lu’u lu’un sai yafara kiran Alhaji Abdul_Jalal tare da yimasa barazanar kashe wani nasa muddin bai sanya Zarah ta damƙa mishi akwatin da lu’u lu’un ke ciki ba, ganin bai samu nasara ba sai ya maida akalar barazanar shi ga Zarah ganin ita mace ce saidai yayi mamakin taurin kai irin nata domin akoda yaushe idan ya kira musayar maganganu marasa daɗi ne yake wakana a tsakaninsu duk da barazanar dayake mata na rasa wani daga cikin danginta.
Dalilin dayasa ya yanke shawarar taɓa wani a cikin danginta ko zata saduda.
_____________________________

Ciwon ciki mai tsanani ne yake damun Rahma wanda yayi sanadin harta kwanta a gadon asibiti, satinta biyu aka sallamota bayan jikinta yayi sauƙi sosai.
Kasancewar lokaci ne na hutu yasa Ammi dake ƙasar Cairo ta yanke shawarar zuwa duba jikin Rahman tare da samarin ƴan biyunta, a garin Gombe jirginsu ya sauka hakan yasa dole suka ƙarasa garin Deba domin kwana washegari sai su wuce Bauchi.
Bayan gaishe-gaishe da hirar yaushe gamo ne suma tsoffin suka yanke shawarar ayi tafiyar dasu domin suma dai basuje dubata ba tunda tayi rashin lafiyar, nan suka yanke cewa zasuyi sammako gabaɗaya suje domin a ranar tsoffin sukeson suje su dawo saidai tafiyar bazata yiwu da Baba Faɗimatu ba sakamakon ciwon ƙafa da take fama dashi.

Da daddare Momi matar Alhaji Sulaiman ta kira Ammi tayi mata ban gajiya inda ta roƙeta akan tabar tata tafiyar sai jibi domin su tafi tare saboda gobe zataje ganin likitan ido akan matsalar ido da take fama dashi. Nan Ammi ta yanke shawarar barin tafiyar sai jibi kamar yadda ta buƙata wanda hakan zai bata daman zama da Baba Faɗimatu da za’a bari a gida ita kaɗai a ranar.

Washegari kuwa kamar yadda suka tsara ƙarfe takwas suka ɗauki hanyar zuwa gari Bauchi bayan sun tsaya a cikin garin Gombe sun ɗauki Nusaiba a gidan Alhaji Sulaiman wacce itama za’ayi tafiyar tare da ita, Shahid ne ke tuƙa motar Adil na gefenshi yayinda Malam Usmanu, Malam Adamu, Baba Aisha da Nusaiba ke baya. A haka suke tafiya lokaci zuwa lokaci suna ɗan taɓa hira.

Safiyar yau bayan Zarah tayi shirinta na tafiya aiki kamar koda yaushe akan kayan aikinta ta ɗaura Abaya sannan tayi rolling da mayafinta, fara ce kuma kyakkawa ce ajin ƙarshe daga kyawun fuska har na jiki, tana da tsayi amma ba sosai ba. Kyakkyawar fuskarta na ɗauke da dara-daran idanu wanda suke cike da gashin gira dana ido, dogon kuma matsakacin hanci ta da kuma ƙaramin bakinta suke ƙara bayyana kyawun da take tattare dashi.

Kai tsaye falon Abbansu ta nufa, a zaune ta same su shida Maminsu alamun magana suke mai mahimmanci, bayan ta gaishesu ne ta sanar dasu zata wuce gurin aiki. Abban ne ya dakatar da ita daga shirin miƙewa da take sa’an nan yace “Zarah inaso na ƙara jaddada miki cewa duk rintsi kada ki maidawa Daddyn ku Sulaiman ajiyarshi kowani hali kika tsinci kanki ciki matuƙar bashi ya buƙaci ajiyarsa ba.”

“Toh Abbah insha Allahu zanyi yadda kace.” Ta faɗa cike da ladabi

“Allah ya muku albarka gabaɗayan ku ya ƙara haɗe kanku ko bayan bama nan.”

“Ameen Abbah.”

Daganan ta miƙe ta musu sallama tare da barin falon hakan takejin wani irin yanayi a tare da ita.

Bayan fitarta ne Alhaji Abdul_Jalal ya kalli matarshi yace” Ina tsoron abinda taƙadirin nan zai aikata ga yarinyar.”

“Babu abinda zai sameta da yardar Allah.”

“Ameen dai amma wannan mutumi abun tsorone.”
Haka suka cigaba da tattaunawa game da lamarin Alpha ɗin har zuwa wani lokaci.

Ƙarfe sha biyu a cikin Gombe tayi musu kai tsaye suka nufi Gwallaga Inda anan gidansu Zarah yake.
Cike da farin cikin ganin juna aka tarɓesu sannan aka cika musu gaba da abubuwan motsa baki. Hira aka cigaba dayi har zuwa lokacin sallar azahar Inda mazan suka wuce masallaci matan ma suka miƙe domin gabatar da tasu.
Bayan anyi sallah ne kuma aka zauna cin abincin gargajiyar da Mami ta shirya, cike da barkwancin da kakannin keyiwa jikokin nasu.

Haka suka kasance cikin farin ciki har zuwa lokacin da sukayi haramar tafiya.

Baba Lado mai gadi na zaune akan wani benci dake jikin gate yaji anyi horn, koda ya leƙa bai gane na cikin motar ba sai ya tsaya batare daya buɗe gate ɗin ba, wani ne ya fito daga cikin motar sanye da manyan kaya ya iso jikin ƙofar inda Baba Lado ke tsaye.

“Baba dan Allah me gidan yana ciki kuwa.? ”
Kafin ya samu damar amsawa yaji an rufe mishi fuska da wani abu, tun daga lokacin bai kuma fahimtar komai ba.
Mutumin da kanshi ya buɗe gate ɗin motar tazo ta shige sannan ya kulle.

“Bari naje bayi na dawo Inna sai na baki saƙon da zaki kaiwa kishiyar tawa.” Faɗin Rahmah dake ƙoƙarin shiga banɗakin dake can gefe a cikin falon.
Dariya sukayi gabaɗaya domin dai Rahma akwai barkwanci dason ganin duk wanda ke tare da ita cikin farin ciki.

Shigewar Rahma keda wuya aka buɗe ƙofar falon, inda wasu mutane dake sanye da baƙaƙen kaya fuska rufe suka shigo. Adadin su bakwai ne sannan kowanne a cikinsu na riƙe da bindiga.

“Kada wanda ya motsa ko ya mana hargowa.”

Babu wanda ya motsa a ciki saidai Idan mutum ya lura da bakinsu zai gane addu’o’i sukeyi.

Babbansu ne ya bada umarnin a ɗauresu gabaɗaya tare da kulle musu sannan a bincika sauran ɗakunan ko akwai wani a ciki, dukkan sashe na gidan suka duba amma ba suga kowa ba.

Kasancewar sai an ɗaga labule Kafin aga ƙofar banɗakin da Rahma ke ciki yasa sam basuyi tunanin akwai wata ƙofa a falon ba sakamakon labulayen da suke a jere har gaba da ƙofar bayin, Idan ba ɗan gidan bama babu wanda zai san akwai banɗaki a wurin.

Waya wani ya ciro tare da karawa a kunne.
“Shugaba rayuka takwas ne cikin gidan a yanzu.”

Jim akayi daga ɗaya bangaren kafin akayi magana.
“Su faɗa muku Inda akwatin yake da mabuɗinsa idan kuma sunyi taurin kai to ku tabbatar babu wanda ya rayu cikin takwas ɗin.”…..
Bayan ya kashe wayar ne ya juyo tare da maida hankalinshi inda suke, umarni ya bada aka buɗe ma Abba bakin shi dake ɗaure.

“Alhaji inaso ka faɗamin inda akwatin da lu’u lu’un ke ciki da kuma mabuɗinsa, ba tashin hankali ya kawo mu ba ku bamu abinda mukeso mu tafi batare da cutar da wani ba.” Ya ƙarasa faɗa yana mai saka bindiga a goshin Abban.

Motsa jiki da Malam Usmanu keyi ne ya hana Abba magana ganin Ogan nasu ya nufi wajenshi tare da kunce masa ɗaurin dake bakinsa.

“Abdul_Jalalu a matsayina na mahaifinka ban yarda ka faɗamusu idan ajiyar da ɗan’uwanka Sulaimanu ya baka ba, idan kayi hakan kuma bazan taɓa yafe maka ba ko bayan raina.” Faɗar Malam Usmanu bayan an kunce masa ƙullin dake bakinsa.

“Ba muzo nan domin jin musayar kalaman da zakuyi ba, zaka faɗa mana ne ko bazaka faɗa ba.?” Ya maida akalar tambayar shi ga Abba bayan ya ƙara ɗaure ma Malam Usmanu bakinsa.

“Bazan iya faɗi inda yake ba.” Abban yafaɗa

“Shikenan bazamu ɓata lokaci ba zamuyi abinda ya dace.”

Nufar inda Nusaiba take ɗaure kusada Shahid yayi tare da tsugunawa a gabanta, hannu biyu yasa tare da jan gaban rigarta da ƙarfi hakan yayi sanadiyar yagewar rigar atamfar dake jikinta tun daga sama har ƙasa wanda ya bayyana ƙirjinta da kuma fatar cikinta.
Shahid wanda ya gane abinda yakeson aikatawa ga Nusaibar ne yasa ƙafafunshi biyu dake ɗaure ya naushi fuskarsa da ƙarfin gaske, take kuwa ya kuma da baya ya faɗi. Da sauri sauran yaran suka nufi kan Shahid saidai kafin su ƙarasa inda yake Ogan ya dakatar dasu, tashi yayi tare da isa gaban Shahid ɗin batare da yayi magana ba ya zaro wuƙa a gefen cinyarshi take ya caka mishi a ciki tare da zarewa ya ƙara caka mishi. Jini ne ya ɓalle tamkar a kwata take Shahid ya sulale babu rai a jiki.

Bakinsu na kulle duka amma hawayene ke bin fuskokinsu na bakin ciki.
Sunaji kuma suna gani ya ketama Nusaiba haddi amma babu abinda zasu iya domin sosai aka ɗauresu bazasu iya taɓuka komai ba.

Da sauri Rahma ta sake labulen jikinta na karkarwa ganin babu wanda ya ganta ne yasa tayi saurin komawa cikin banɗakin tare da kullewa.
Wayarta da bata rabo da ita na hannunta, sau da dama Mami kan hanata shiga da waya banɗaki amma takasa dainawa domin wasu lokutan babu abinda zatayi a banɗaki take shiga saboda kawai kar a sakata wani aikin tana tsaka da chat.

Tunawa da wayar da tayi yasa take tafara ƙoƙarin kiran Zarah domin a kawo musu taimako, kuka sosai takeyi amma na zuciya ganin kiran nata shiga ba’a ɗagawa.

A ɓangaren Zarah kuwa tun ƙarfe 12:30nr kwamishina ya mata kiran gaggawa domin su gana, fiye da awa ɗaya yanata yi mata surutan da basu shafi gefen da take aiki ba amma a matsayinshi na shugabanta ta kasa tanka mishi duk da tanason komawa gida su gaisa da kakanninta da ƴan uwanta da sukazo.
Wayoyinta gabaɗaya suna cikin mota hakan yasa batasan irin kiran da Rahma ke mata ba.

Sai da suka tabbatar da babu wani sauran mai rai a cikinsu kafin su bar gidan.

Ganin Zarah bata ɗaga kiran ne yasa Rahma danna kiran wani abokin Yayansu Mustapha dake aikin soja, bugu biyu ya ɗaga kiran yana mamakin kiranshi da tayi domin ya daɗe yana mata magiyar soyayyarshi amma tana wulaƙantashi.

Yana ƙoƙarin magana ta riga shi.

“Ka taimakeni Mustapha zasu kashemin iyayena dan Allah kazo da sauri”. Ta faɗa da disasshiyar muryarta saboda kukan da takeyi.

Jin abinda ta faɗa ne yasa shi miƙewa daga zaunen da yake.

“Rahma su waye zasu kashe miki iyayen kuma a ina suke.?”

“Suna cikin gidanmu yanzu haka sun ɗaure kowa da kowa nima basu ganni bane, dan Allah kazo da sau….. ” kuka ne yaci ƙarfinta batare da ta ƙarasa maganarta ba.

“Subhanallahi! Ki zauna a inda kike gamu nan zuwa.”..

Bata iya amsawa saboda toshe bakinta da tayi tana kuka.

Cikin mintuna goma sha biyar taji jiniyar sojoji wanda hakan ya tabbatar mata da Mustapha ya iso da jami’ansu na soji.

A farfajiyar gidan kuwa mai gadi ne da sauran ma’aikata biyar dake musu aiki kwance basu motsi, tun daga hakan Mustapha ya gane tabbas babu lafiya hakan yasa suka tunkari ƙofar babban falon cikin shiri da ƙwarewar aiki.

Jini suka fara arba dashi bayan buɗe ƙofar har zuwa cikin falon, da basu kasance sojoji ba toh tabbas sai wasu daga cikinsu sun firgice da ganin gawarwakin mutanen dake kwance domin kuwa kisa aka musu tamkar a kwata.
Lungu da saƙo na gidan gabaɗaya sun duba amma babu kowa hakan ya tabbatar musu cewa masu laifin sun samu nasarar tserewa.
Duk da haka sai suka raba kawunan su a ɓangarorin gidan ciki da waje.

Ƙarfin hali kawai Mustapha yake yana maida hawayen dake son zubo mishi, lambar Zarah ya shiga kira saidai ba’a ɗagawa. Ganin haka ya canja akalar kiran ga wani maƙocin shi D.P.O yayi mai bayani tunda case ɗin ba wanda sojoji zasu shiga bane, taƙaitaccen bayani kawai ya iya yimishi ya kashe wayar.

Cikin mintunan da basu wuce talatin ba ƴan Sanda da sojoji suka kewaye gidan ta kowanni fanni.

Hayaniyar mutane da taji sosai ne yasata jarumtar buɗe ƙofar banɗakin, saida ta fara leƙowa taga taron masu kaki ne sannan ta fito gabaɗaya.
Abinda ta gani ne yasata sakin ihu tare da faɗowa ƙasa sumammiya.

Sai a lokacin mutanen dake falon suka ankara da ita, shikuwa Mustapha sai a lokacin ya tuna da ita tun bayan da yayi arba da mummunar ɓarnar da akayi musu.

“Ya kamata a sanar da wani a cikin danginsu domin bazamu iya yin wani abu da gawarwakin batare da izinin su ba.” cewar D. P. O. dake kusada Inda Rahma ke kwance.

Waya Mustapha ya ciro tare da danna lambar Alhaji Sulaiman sannan ya miƙama D.P.O wayar domin baisan ta ina zai fara faɗin wannan baƙin labarin ba.
Fita yayi bayan ya karɓi wayar bai jima sosai ba ya dawo sannan ya miƙawa Mustapha wayar.

Ƙarfe huɗu daidai motocin Alhaji Sulaiman da tawagar shi suka iso, motar farko mutane biyar ne a ciki. Direba dake jan motar sai Alhaji Sulaiman dake gefenshi a baya koma Baaba Faɗimatu, Ammi da Momi.
Sauran motoci biyun koma abokan kasuwancinshi ne a ciki daya sanar musu da rasuwar suka biyoshi domin yin jana’iza.

Ganin Ƴan sanda da sojoji yasa kansu ɗaurewa domin dai Alhaji Sulaiman ɗin bai sanar dasu abinda ke faruwa ba umarni kawai yabada su shirya suzo garin Bauchi.

Momi ce tayi ƙarfin halin magana lokacin da direba yayi parking.

Tace” Daddyn su meke faruwa ne haka, meya kawo jami’an tsaro haka a gidan. Kodai Zarah ta karɓi masu tsaron da aka bata ne.?”

“Tambayoyin sunyi min yawa ku sauka mu shiga ciki, tada Baaba daga baccin nan haka tunda mun iso.” Ya faɗa gamida ficewa a cikin motar

Ammi kuwa ta kasa tankawa domin zuciya da gangar jikinta sun tabbatar mata babu lafiya.

“Meke faruwa ne naga ƴan’uwansu Zara’u sun cika gidan.?” Faɗin Baaba Faɗimatu da farkawarta kenan daga baccin data fara tun a hanya.

“Mu shiga daga ciki dai Baaba sai muji abinda ke faruwa domin dai waƴannan jami’an tsaro akwai abinda ya kawosu ko kuma suke tsaro.” Momi tafaɗa tana mai buɗe ma Baba ƙofar.

Cikin rashin kuzari Ammi ta fito tabi bayansu suka nufi hanyar shiga cikin gidan.

Sam Alhaji Sulaiman baiyi tunanin irin ɓarnar dazai tarar ba kenan domin D.P.O ɗin ce mishi kawai yayi ƴan fashi sun shiga gidan ɗan’uwan shi sunyi fashi haɗe da kisa.
Kuka yake bil hakki ganin irin kisan wulaƙanci da akayi musu duk da kasancewar ƴan Sanda sun gyarasu daga asalin yadda suka samesu bayan likita ya tabbatar babu wani mai sauran numfashi a cikin su. Saidai tambarin *Alpha*🌴 da aka zana da jini na nan a tsakiyar falon.

Da sauri ya miƙe da nufin tsayar dasu daga shigowa falon kasancewar su mata yasan dole basu da juriyar da zasu iya ganin wannan aika aikar, hatta shi dayake namiji yanajin tamkar ya ciro zuciyarshi ya aje a ƙasa saboda tarin baƙin cikin daya shige shi a lokaci ɗaya.

Saidai kash!!! Kafin yakai ga ƙarasawa ƙofar fita daga falon Momi da Baba Faɗimatu sun sako kai bakinsu ɗauke da sallama, duk da haka saida ya ƙarasa inda suke cikin sassarfa ya kare fuskokinsu daga ganin cikin falon.

“Baaba da kun ɗan tsaya a waje ana gudanar da bincikene anan.”

“Sulaimanu wani irin bincikene akeyi haka daya saka zubar da hawaye, ka matsa ka bamu guri mu ƙarasa muga abinda ake ɓoye mana. Shin ina ahalin gidan ne.?” Faɗin Baaba kenan tana mai kaucewa daga hanyar daya tare.
Bayanta Su Ammi su bi domin ƙarasawa falon.

Abinda ya guda shiya faru domin a tare gabaɗaya su ukun suka zube a ƙasa sumammu, shima dai hawayen ne yake zubo mishi.

Wani daga cikin mutanen falon ne yayi dabarar watsa musu ruwa saidai Momi ce kawai ta farfaɗo itama ba’a cikin hayyacinta ba.

“Dan Allah ku tayar dani daga wannan mummunan mafarkin ba gaskiya ban..” bata ƙarasa ba ta ƙara sulale wa.

“Yallaɓai kasa hannu anan munason mu wuce da gawarwakin asibitine domin gudanar da bincike.” cewar likitan da aka damƙa case ɗin binciken gawarwakin a hannunshi yana miƙawa Alhaji Sulaiman wasu takardu.

“Babu wani binciken da za’a gudanar saboda a yau ɗinnan nakeson a sadasu da gidansu na gaskiya, ku taimakawa waɗannan dake sume kawai.” Yafaɗa cike da rauni.

Nan ya ciro waya ya fara bugawa ƴan uwa da abokan arziki, abu da zamani nan da nan anguwar ta cika maƙil da jama’a domin sallartar mamatan.
Da taimakon likitoci aka samu damar kimtsa su a cikin likkafani Saidai kafin wani lokaci gabaɗaya sun rine daga kalar fari zuwa Ja saboda jinin dake zuba da jikin gawarwakin.
Sau uku ana canjawa amma babu wani sauyi hakan yasa aka barsu a haka.

Acan falon baƙi kuwa Limamin masallacin Juma’a na gwallaga ne tare da su Momi da aka samu suka farfaɗo dakyar, saidai har zuwa wannan lokacin Rahma bata farka ba hakan yasa aka wuce da ita asibiti.

Nasiha ya musu mai ratsa jiki hakan yasa suka sassauta da koke koken da sukeyi, nan suka miƙe suka nufi falon inda baƙi suka fara cika. Nan aka fara gaisuwa da jajantawa.

Kwamishina ne ya kalli Zarah dake zaune a kujerar dake fuskantar shi yace

“Zarah ta wace hanya kike ganin zamu iya magance matsalar tsaro a ƙasar nan.?”

Zuwa yanzu Zarah ta fara zargin akwai wani abu a ƙasa domin duk lokacin da tayi nufin tafiya sai shugaban nata ya tsayar da ita ta hanyar yi mata wasu maganganun da ba ita ya dace a faɗawa, cike da ƙosawa tace ” Yallaɓai a tunani na wannan matsala ce da zamu taro mu samu mafitar ta, matsala ce data shafi jaharmu da ƙasa baki ɗaya don haka muna buƙatar mu tattauna da sauran manyan jami’ai domin samun mafita.?”

Kafin ya samu damar amsa mata wayarsa dake gefe tayi ƙara, hannu yasa ya ɗauku wayar tare da karawa a kunnenshi batare da yayi magana ba.

“Zaka iya bata damar tafiya yanzu mun gama aikinmu sannan ka duba wayarka akwai saƙon kuɗi dana turama a asusun bankin ka.”
Abinda aka faɗa kenan daga ɗaya ɓangaren sannan aka kashe wayar batare da jiran amsar da kwamishinan zai bada ba.

Kallon shi ya maida kan Zarah yace” ASP zaki iya tafiya. ”

Cike da mamaki ta miƙe tare da sara mishi sannan tafice a ofishin, jikinta taji ya mata wani iri ga zuciyarta dake bugawa da ƙarfi tamkar zata faso ƙirjinta.

Shigarta cikin mota yayi daidai da katsewar kiran wayarta dake ringing kafin shigowarta, sai da ta zauna kafin ta sa hannu ta ɗauki wayar.
Ido da zaro ganin anyi mata kira har 66, take ta duba domin ganin masu kiran, 35 missed calls daga Rahma, 6 missed calls daga Mustapha, 15 missed calls daga Daddy sai sauran kira 10 daga mutane daban daban.

Da sauri ta shiga danna kiran Rahma saidai har ta gama ringing ba’a ɗaga, haka tayi ta kira ba’a ɗagawa kafin ya danna kiran Daddy sai dai wayarsa bata shiga.
Ganin haka yasa ta canja akalar kiran ga wayar Mustapha.

Bugu biyo ya ɗaga tare da faɗin” Zarah kina inane haka ake ta kiran wayarki bakya ɗagawa.”

“Na shiga ganawar sirri ne da kwamishina kuma wayar na cikin mota, meke faruwa ne.?” tafaɗa cike da zaƙuwar son jin abinda ke faruwa domin a lokacin bugawar da zuciyarta keyi ya ƙaru.

“Babu komai ki taho gida anason ganinki.” yafaɗa gami da kashe wayar baki ɗaya.

Cikin sauri ta taɗa motar tare da harbawa kan titi bakinta ɗauke da kalmar hasbunallahu wa ni’imal wakil saboda yanayin da take jinta a ciki.
Tun daga farkon shigowar anguwansu take ganin jerin motoci har zuwa gaban gidansu data tara cike da jama’a, nan zuciyarta ta ƙara tsinkewa gami da tabbatar mata lallai wani abu ya faru, horn ta danna a ƙofar gidan saidai a maimakon taga mai gadinsu sai taga Alhaji Sulaima na buɗe mata ƙofar.
Bata ko gama parking ɗin motar ba ta fito da sauri, hannunta taji an riƙo hakan yasata tsaya wa daga tafiyar data fara tare da waigowa Daddy ta gani a tsaye.
Kallo ɗaya ta mishi taga alamun kuka a fuskarshi.

“Daddy meke faruwane dan Allah ka faɗamin.”

Batare da yayi magana ba yaja hannunta suka koma jikin motar, ƙofar baya ya buɗe mata tare da gyaɗa mata kai alamun ta shiga sannan shima ya shiga ya zauna.

“Zarah.” ya faɗa bayan ya zauna

Cike da rauni ta amsa da” Na’am Daddy”.

“Nasan kinyi karatun islamiyya har zuwa matakin da kika sauke alqur’ani koh.?”

Kai kawai ta iya gyaɗa mishi.

“Inaso ki nutsu wasu tambayoyi zan miki.”

“Toh Daddy.”

“Inaso ki gayamin abinda Allah yace a cikin suratul Baqara a ƙarshen aya ta ɗari da hamsin da biyar zuwa aya ta ɗari da hamsin da shida(2:155-156) tare da ma’anar shi.”

Kai ta jinjina sanna tace” Allah maɗaukakin Sarki yana cewa

و بشر الصبر ين(155) لَّذِينَ إِذَآ أَصَٰبَتْهُم مُّصِيبَةٌ قَالُوٓا۟ إِنَّا لِلَّهِ وَإِنَّآ إِلَيْهِ رَٰجِعُون(156)
Fassarar shine
“Kuma kayi bishara ga masu haƙuri(155) Waɗanda suka kasance idan wata masifa ta same su sai su ce _Lallai ne mu ga Allah muke, kuma lallai ne mu, zuwa gare Shi muke komawa._

A taƙaice ayar na nufin idan Allah ya jarabci bawa da wanu abu na baƙin ciki sai ya kasance mai yawan furta kalmar “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un”.

Murmushi yayi wanda iyakar shi fuska sannan yace” Masha Allah, to me Allah ya sake cewa a cikin suratul Ankabut aya ta hamsin dashi.?”

Allah yace”

كُلُّ نَفْسٍ ذَآئِقَةُ ٱلْمَوْتِۖ ثُمَّ إِلَيْنَا تُرْجَعُونَ
Fassarar ayar
“Kowani rai mai ɗanɗanar mutuwane, sa’an nan zuwa gare Mu ake mayar daku.”(Q29:57).

“Alhamdulillahi tunda kin kasance mai ilimi, kinga kenan duk abinda yasamu bawa to ƙaddararre ne sannan da mutuwa da rayuwa duk na Allah koh.?”. Daddy yafaɗa yana mai yimata kallo irin na tausayawa.

“Ehh hakane Daddy.”

“Toh Zarah inaso ki kasance mai haƙuri tare da rungumar ƙaddarar data same mu duka, kiyi haƙuri ƴan fashi sun shigo gidannan sannan sunyi kisan kai kafin su tafi.”

A ruɗe ta kalli Daddy tanason gane inda maganarshi ta dosa.
Tace” Ƴan fashi, kisan kai.? Wa suka kashe mana.?”

Ganin tana shirin ficewa a hayyacinta ne yasa ya riƙo hannayenta biyu tare da faɗin” Ki nutsu Zarah sannan ki cigaba da faɗin kalmar Innalillahi wa inna ilaihi raji’un.”

Haka yayi ta maimaita mata har zuwa lokacin da ta ɗan nutsu kafin ya fito ya zagaya ya buɗe mata ƙofar motar ta fito sannan yajata zuwa inda aka ajiye gawarwakin kafin a fita dasu a sallace su domin farfajiyar gidan bazata ɗauki mutanen da sukazo jana’izar ba.
Dangin mamatan ne a gurin kowa yana karantu musu addu’a tare da kallon ƙarshe.

Abinda ta hangone ya sata sulalewa a ƙasa batare da sun ƙarasa ba, da sauri Ammi data hango lokacin faɗowarta ta nufi inda butar Baba me gadi take ta ɗauko tare da watsa mata ruwan ciki a fuska.
Shidai Daddy yana tsaye yakasa koda motsawa domin zuwa yanzu shima ya fara rasa jarumtar shi.

Tsiyaya mata ruwan Ammi ta farayi ganin bata farfaɗo ba.

Cikin sa’a kuwa taja numfashi mai ƙarfi.

_Cigaban labari_.

Zuwa ƙarfe bakwai na dare gidan ya ƙara cika sosai saboda ƴan uwa da abokan arziki na nesa da suka ƙaraso, domin hatta dangin Babansu Shahid dake Taraba duk sunzo kasancewar dayawa daga cikinsu jirgi suka bi.
Haka akayi ta koke koke kafinan suka saurara aka cigaba da karɓan gaisuwa.

A daren ranar dai babu wani daga cikin wannan ahalin daya samu damar runtsawa, kwana sukayi suna raya wannan dare da yiwa matattun addu’o’i tare da fatan Allah ya basu juriyar rashin da sukayi.

Daddy ne ya hana a sanar da Sadiq dake ƙasar Singapore yana rubuta jarabawarshi ta ƙarshe na zama cikakken likitan zuciya wato *Cardiologist Consultant* sakamakon asarar shekaru da zaiyi inhar baici jarrabawar.

Muhammad Jawwad kuwa sai ranar da akayi sadakar uku Daddy ya sanar dashi, shima dai kuka yayi tayi saida Daddy ya rarrashe shi. Nan yace ma Daddyn zai nemi biza ya taho bayan yayi ƙorafin rashin faɗa mishi da ba’ayi da wuri ba.

Bayan kwanaki ukun ne baƙi suka rago a gida amma kullum wuni suke karɓar gaisuwa daga mutane daban daban, masu kwana ne dai babu.
A cikin kwana ukun nan duk wanda yaga halin da suke ciki saiya kuka, Baaba kawai mai ƙarfin hali a cikin su.
Ga Rahma da har yanzu bata farfaɗo ba.

Gabaɗaya suna zaune a falo a daren ranar ukun harda Daddy da Mustapha da shima kullum baya rabo da gidan.

Zarah na kwance saman dogowar kujera yayinda tayi filo da ƙafar Baaba.
Lokaci ɗaya ta miƙe a firgice.

Kallonta Daddy yayi tare da faɗin” Lafiya kuwa Zarah.?”

“Daddy CCTV , na jona CCTV a duka falon dake gidan nan.” Ta faɗa lokacin da ta miƙe sannan da gudu ta nufi hanyar ɗakinta……

Da gudu ta nufi cikin ɗakin tare da nufar inda ƙaramar na’urarta take ajiye, sashin abubuwan da suka faru a cikin satin ta shiga tare da playing daga ranar farko.

Daddy da sauran mutanen gidan ne suka shigo ɗakin, gabaɗaya suka zauna domin kallon abinda ke wakana a cikin na’urar.
Saidai gabaɗaya babu abubuwan da suka faro a kwanaki uku da suka wuce wanda hakan ya tabbatar mata da cewa akwai wani wanda ya shaidama Alpha na’urar da ta saka.
Cike da takaici ta rufe na’urar tare da kwanciya akan gadonta.

Babu wanda ya tanka duk suka fice a ɗakin.

Babu daɗewa kira ya shigo wayar Zarah, hannu ta kai ta janyo wayar tare da kallon fuskar wayar domin ganin mai kira. Ɓoyayyiyar number ce ke kira, tamkar bazata ɗaga kiran ba saida ta kusa yankewa kafin ta ɗaga tare da karawa a kunnenta batare da tayi magana ba.

“Na tabbatar yanzu kin fara gaskata abinda Alpha yake da damar yi ga duk wanda ya shiga gonarsa.” Daga ɗaya ɓangaren aka faɗa

Zaune ta miƙe batare da tayi magana domin ta gane wanda yake maganar.

Magana ya cigaba dayi ta hanyar faɗin “Kada kiyi saurin karaya ta hanyar ajiye aikinki Zarah domin kin riga kin shiga wasan da baki da damar fita, ba’ayi komai ba tukun. Kin shirya bada kadarar ko baki shirya.?”

Mamaki ne ya cikata jin abinda ya faɗa, tabbas Alpha ba ƙaramin shiri yayi akanta ba domin da Daddy kaɗai tayi maganar ajiye aiki kuma shiɗin ma bai goyi bayan hakan ba sannan tanada tabbacin cewa ba wajen Daddy yaji wannan batun ba. Ajiyar zuciya ta sauke a ɓoye kafin tace

“Bana zuwa akan lokaci amma tabbas idan na iso waje ina jan ragamar kowani wasa tare da kasancewa mai nasara, ka faɗama kowaye ya sanar dakai cewa Zarah zata ajiye aiki da yaje ofishinta a gobe ranar litinin domin ya samu maka cikakken bayani.”

Bata jira mai zaice ba ta kashe wayar gabaɗaya.
Takalmi ta zura tare da fita zuwa falo, dukkan su suna zaune kamar yadda suke da farko.

Zama tayi kusada ƙafafun Daddy tare da faɗin
“Daddy inaso gobe zan koma bakin aiki.”

“Zara’u wace irin magana kikeyi haka, kodai kema ƙwaƙwalwarki ta taɓo ne kamar yadda ƴar uwarki ta samu.?” Faɗin Baaba wacce maganar da Zarah tayi ya tadata Zaune daga kishingiɗen da take.
Sunkuyar da kai tayi batare da tayi magana ba.

Daddy ne yayi gyaran murya tare da cewa.
“Baaba ina ganin mu barta ta koma bakin aikinta ƙila akwai wani muhimmin abu da zata gudanar ne bayan haka kuma zamanta a gida bashine zai dawo mana da waƴanda muka rasa ba. Hasalima aikin nata zai taimaka wajen binciko da masu hannu akan wannan lamarin.”

Jinjina kai Baaba tayi cikin gamsuwa da maganganun Daddyn sa’an nan tace.
“Toh yaya batun Rahmatu kuma.?”

“Ehh Amminsu zata wuce da ita can Cairo a cigaba da duba lafiyarta tunda maigidan nata ya amince, Zarah kuma zata zauna anan saboda binciken da zata cigaba da gudanarw. Sannan ina neman alfarmarki Baaba da ki cigaba da zama anan tare da ita, kasancewar mace bai kamata ta zauna ita kaɗai ba saboda kare mutuncinta. Insha Allahu kuma zamuyi ƙoƙarin ziyartar ku lokaci lokaci kamar yadda muka saba.” Cewar Daddy

“Babu damuwa Sulaimanu Allah yayi albarka ya albarkaci zuri’a.”

Da Ameen sika amsa gabaɗaya kafin kowa ya miƙe domin zuwa kwanciyar bacci wanda a zahiri ba haka bane domin raba dare suke gaban mahalicci suna kai mishi kukansu.

Washegari tun ƙarfe bakwai Zarah ta fito cikin shirinta sanye da kakinsu na ƴan sanda, baƙin wando da shuɗiyar riga, inda ta ɗora baƙar Abaya mai ratsin shuɗi a saman kayan sannan tayi rolling da gelen rigar.

Ammi kaɗai ta tarar zaune a falo tana jan carbi, ƙarasawa tayi tare da zaunawa a ƙasan kujerar da Ammin ke zaune.

“Barka da safiya Ammi.”

Kanta Ammin ta kwantar akan cinyarta tare da shafawa a hankali.

“Ina fatan kintashi lafiya.?”

“Lafiya lau Ammi, zan wuce aiki ina barar addu’a.” cewar Zarah lokacin da take gyara kanta a cinyar Ammin.

“Allah ya kareki daga dukkan sharrin masu sharri, Allah ya nesanta zuciyarki da aikata abinda ba daidai ba, Ina roƙon Allah ya baki nasara ga duk abinda kikasa a gaba. Allah ya albarkaci rayuwarki.”

Cike da jindaɗin addu’o’in Ammin take amsawa da Ameen kafin ta miƙe tare da mata sallama ta nufi hanyar fita daga cikin falon.

Gurin motarta da yaran Mustapha suka wanke mata ta nufa domin masu yi musu aiki tun bayan faruwar wannan lamarin suka aje aiki saboda tsoron kada a ƙara kawo wani harin a haɗa dasu tunda na farko dai hodar saka bacci aka shaƙa musu basusanai zai iya faruwa ba nan gaba.

Cikin mintuna ƙalilan ta isa ofishin nasu, tun kafin ta ƙarasa parking sergent Bala ya iso inda motar take ya buɗe mata ƙofa bayan ta gyara tsayuwar motar.
Ƙamewa yayi har saida ta fito sannan ya kulle motar.

“Ranki ya daɗe barka da safiya. Ya ƙarin haƙurin mu.”

“Barka dai Bala, haƙuri mungode Allah.” ta faɗa tana mai fara tafiya domin isa ofishinta.

Karbar jakarta yayi bayan yace” Allah ya gafarta musu.”

“Ameen.” tace a taƙaice.

Haka ƙananun jami’an suka jigaba da mata gaisuwa harta ƙarasa cikin ofishin ta.

Tana ƙoƙarin ajiye wayarta akan tebirinta kira ya shigo, ganin mai kiran ne yasata sakin wani kyakkyawan murmushi.

“Assalamu alaiki ya habibaty.” abinda aka faɗa kenan bayan ta kara wayar a kunnenta

“Wa’alaiki salam Dr. Jiddah amaryar Bar. Saleem.” Zarah ta faɗa tanamai zama a kujerarta

”Ki faɗawa wanda bai sani ba, naga alama tsokanar da bakiyi kwana biyu ba kikeson yi kuma ba kulaki zanyi ba. Dafatan kin tashi lafiya yasu Ammi.”

“Lafiya lau suke duka.”

“Ya ƙarin haƙuri kuma.”

“Alhamdulillah.”

“Allah ya musu Rahama.”

“Ameen Ameen. Ina kika baro maƙalematan naki banji motsinsa ba.” Zarah ta faɗa cike da barkwanci.

“Ke dai bari habibaty, jiya kwana nayi ina mishi kukan nagaji da zama a cikin masu jajayen kunnuwa shine yau ba shiri ya fita domin fara haɗa tarkacensa.” Jidda kenan take maganar cikin sanyi murya.

“Babu kyau abinda kike aikatawa fa, ki dinga damun bawan Allah yana miki abinda kikeso koda shi bayaso ɗin.”

“Auren kenan ai kema kiyi kigani ko baza’a miki abinda kikeso ba.”

Kafin tayi magana aka kwankwasa ƙofar ofishin nata da haka tace.

“Zamuyi magana anjima SA.JID zan fara aiki a ofis.”

“Innalillahi! Yanzu Zarah tun ba’a sadakar bakwai bama har kin fara fita wannan ƙaddararren aikin, so kike ki jama kanki zance a gari.”

Shiru Zarah tayi na wani lokaci kafin tace” Jiddah ya zanyi to, *Alpha* kinsani Idan ban kasance a ofis ba na wani lokaci mutane da dama zasu rasa abubuwa masu mahimmanci sanadin wannan mutumin.”

“Shikenan Allah ya taimaka, nima dai Insha Allah zuwa wani watan zamu dawo.” Jiddah ta taɗa cike da tausayin Zarah.
Sallama sukayi sannan suka katse kiran lokaci guda.

Umarni ta bada a shigo lokacin da take ajiye wayar a kan teburinta.

Sergent Bala ne ya kuma shigowa hannunshi ɗauke da farar takarda, saida ya sara mata kafin ya fara magana.

“Ranki ya daɗe wannan saƙo ne daga ofishin mai girma kwamishina, jiya da yamma ya aiko tare da bada umarnin lallai akai miki saboda abune mai mahimmanci. Dama yau nakeson kawo miki idan na tashi a aiki sai kuma gaki kinzo.”

Kaɗa kai Zarah tayi kafin tace” Sau sa dama Bala ina gayamaka ka koyi saka maganganu a cikin kalma ɗaya, basai kayita dogon sharhi ba a matsayinka na ɗan sanda. Anaso maganar jami’i ta banbanta dana sauran mutane, anfiso idan kayi magana sai mutane sunyi nazari sosai kafin su gane ainahin abinda kake nufi ba kamar yadda kake magana yanzu ba.”

Ƙamewa ya kuma yi kafin yace.

“Ayimin afuwa ranki ya daɗe zan gyara.”

Bata kula da maganarshi ba tace.

“Me takardar ta ƙunsa.”

“Ranki ya daɗe bani da damar buɗewa saboda a kulle take cikin envelop.”

Hannu tasa ta karɓi takardar tare da buɗe envelop ɗin ta cirota.
Mintuna biyu ta ɓata wajen nazartar abinda ke cikinta.

Ɗagowa tayi daga kallon takardar tare da maida kallonta ga Sergent Bala sa’an nan tace.

“Taron ƙarawa juna sani a harkar aiki ne ake umartana naje wanda za’a gudanar a garin Abuja. Cikin sati ɗaya za’a gama gudanar da taron wanda zai fara ranar alhamis, sannan kaida Jennifer ne zamu kasance tare.”

Bata jira mai zaice ba ta bashi umarnin tafiya.

Jingina kanta tayi da jikin kujerar sannan ta lumshe idanuwa.

Haka ta wuni a ofishin sam takasa taɓuka komai bayan kuma da shirin yin aiki ta fito saidai ta danganta hakan da saƙon kwamishina daya risketa.

Cikin kwana ukun ta kammala duk wasu shirye shiryen ta na tafiyar.

A gefe guda kuma su Ammi na shirye shiryen tarban Muhammad Jawwad da shima zai iso ƙasar ranar Alhamis wanda rabonshi da ita tun yana ɗan shekara 14.

Jirgin ƙarfe tara Zarah zatabi zuwa garin Abuja yayinda jirginsu Muhammad Jawwad zai sauka ƙarfe takwas da rabi.

“Daddy ina jin ku wuce kawai zanbj ta ofishin kwamishina kafin mu wuce.” Zarah kenan ke faɗi bayan ta gama amsa wayar da Sergent Bala ya bugo mata.

“Babu rabon zaku haɗu da ɗan’uwan naki kenan saboda shima kwanaki biyar zaiyi ya koma saboda inaso ya dawo ƙasarshi ya cigaba da aiki.” cewar Daddy

“Banji daɗin haka ba gaskiya amma tunda zai dawo ƙasar gabaɗaya zamu ga juna.”

“Shikenan Allah ya kiyaye hanya.”

“Ameen Daddy.”

Sauran iyayenata ma addu’ar sauka lafiya suka mata kafin ta shige motarta ta fice a gidan.

Daddy, Momi da Ammi sune sukaje airport tarbar ɗan nasu domin Baaba batada damar fita saboda halin takaba da take ciki.

Basu jima da isa ba jirgin ya sauka, dubawa suke domin ganin ta inda zai ɓullo amma basu ganshi ba.
Wani kyakkyawan bature ne suka ga ya nufo inda suke tsaye, basu ankara ba suga ya rungume Daddy tare da faɗin” Nayi kewarka Daddyna.”

Salati Ammi ta shiga rafkawa tana faɗin.

“Jawwad kaine haka.? Shikenan masu jajayen kunnuwa sun canja ka, ka koma jinsinsu.”

Dariya sukayi gabaɗaya sannan suka nufi gurin da motarsu take, ita kuwa Momi kunyar fulani da kawaicin ɗan fari ne ya hanata magana.
Mota suka shiga tare da nufar gida.

 

A ɓangaren Zarah kuwa koda kwamishina ya gama zayyana mata tsarin yadda taron zai kasance saita miƙe domin tafiya, har ta kama hannun ƙofar da nufin buɗewa ta fasa tare da waiwayowa ta kalli kwamishinan da hankalin shi ya koma kan takardun dake saman teburinsa tace.

“Yallaɓai nace ba.”

Kallonta yayi batare da yace komai ba.

Murmushi tayi mai cike da ma’anoni kafin tace.

“Yallaɓai idan ba damuwa ka faɗawa wanda ya baka umarnin wakiltani a matsayin wacce zata halarci wannan taron cewa _Babu ma’ajiyar CCTV a ofishin ASP Zarah sannan baya buƙatar na’ura mai ɗaukan sauti domin sanin abubuwan da nake gudanarwa a cikin ofishina._

Bata jira mai zaice ba ta buɗe ƙofar tare da ficewa a ofishin…….. ✍🏼

*Jasmine*🌸🌸

Leave a Comment