πππππ
AUREN SIRRI
πππ
πππππ
Bismillahirahmanurrahim
Aysha A bagudo
Page 1-2
Lekki Unguwace mai dauke da karancin mutane da suke rayuwa acikinta ,a silent place, saboda bata cika hayaniya mutane ba , dauke da tarin sanyin ni’ima mai dadi sakamakon kusancinsu da ruwan teku” unguwace da tattara kan manya ma’aikata da kusoshin gwanati, hade da manyan masu kudi ,ga tarin yan yahoo boy’z domin mafi yawancisu sunfi sha’awar zama acikinta. rayuwar mutane unguwar abin sha’awa bbu ruwan wani da wani domin suna rayuwasu ne tamkar a kasar waje .
PLASNUW ROWS FAMILY ESTATE
Estate ne mai dauke da tarin dangi acikinta , hadin kai tattare da zaman lfy, Sam bbu hayaniya acikin wannan family kowa kagani cikin nishadi da farinciki zaka gansa ,ga tsantsar fahimtar juna dake tsakanin wannan family. kwakkywan family ne masu matukar kaunar junansu .
Let alh Muhammed bello khaliyal ,haifafen garin Lagos ne ,Amman asalinsa fulanin khaliyal ne dake jahar kebbi. sananne mai kudi ne yayi tashe tun alokacin da duniya ke kwance. sannan kuma take zaman lfy, marigayi Muhammed bello soldier ne daya taka rawar Gani a kasar nan .
ya rike mukamai da dama a wancan lokacin. ya rasu yabar tarin dukiya da da ya’ya da jikoki bila adade.
gabadaya family Muhammed bello bbu talaka aciki domin sun gaji dukiya mai tarin yawa daga mahaifinsu .
kafin rasuwarsa dake shine babba a dakinsu kuma Allah yabashi tarin dukiya da en’uwan , dan ganin ya inganta rayuwar kannensa kafin daga baya ya Gina wannan katanfarin estate din mai mazan kanta.
ya tattara kan yan’uwasa suna zaune a ciki ,yana da mata hudu hjy shema’u wacce aka musu aure tun saurayi da budurwa tana da ya’ya goma Sha biyu, mata takwas maza hudu sai hjy hauwa mai dauke da ya’ya goma maza biyar mata biyar ,sai hajiya rabi mai ya’ya takwas maza biyar mata uku sai hajiya Fatima wacce suke kira da hjy shuwa itama tana da yaya takwas mata bakwai namiji daya .
bbu abinda bbu acikin wannan estate din kama daga makarantar islamiyya wajen wasa buga kwallo wajajen exercise wajen swimming pool library Sannan ga wani katanfarin Holl dake gefe wanda aka shiryashi da kayan kyale kyale zagaye da kujerun zama . an ginashine saboda taron sada zumunci , wanda zasu dinga yi a duk karshen wata .
haka suka taso har zuwa girmansu cike da son junansu .
anan cikin dangi mazan suka zabi matan suma matan suka zaba akayi bikinsu anan cikin estate din suka zauna tare da iyalinsu har zuwa sanda tsufa yacima marigayi Muhammed bello yayi retire.
yayinda ya’yansa da ya’yan en uwa suka cigaba da kula da estate din .
a lokacin aliyu da habib ne kadai suka rage da basuyi aure ba saboda karatu .
Byn rasuwar marigayi bello ne aka raba gado aliyu ya dukufa gurin juya dukiyarsa ,ba abinda yasaka a gaba sai neman kudi wanda acikin kankani lokaci ya gawurta yayi fice yayi suna a duniya, yayiwa sauran yan’uwansa zarra aliyu ya mallaki tarin dukiya da shi kansa bai san iyakarta ba. hade da tarin compenis a Lagos da kudancin Nigeria yana da gidajen saida man petir Bila adadi shine mallakin aliyu airlines yana da hannu jari da dama a compenis na kasashen duniya yana da gidaje a abuja da sauran garuruwa .
tsananin neman kudinsa ne yasa bai ajiye iyali da wuri ba ,burinsa bai wuce ya auri mace mai matukar kyau da tarin illimi ba .
Garin neman kudinsa ne ya hadu da fadila a india tun daga lokacin da aliyu ya daura idanunshi akanta “ya dauki son duniya ya daura mata kasancewarta kyakkywa gaske ga tarin illimi . fadila itace Diya ta biyu a gurin iyayenta su uku ne , ahmed ne babba sai ita sai farida , kin amincewa iyayenta sukayi da auren shi a cewarsu bako ne sannan kuma bakin fata. sai da aka kai ruwa rana dasu sannan suka amince da auren .
koda yazo daita Nigeria ma bata wani sha wuyan zama cikin family dinsa ba .
kasancewarta mace mai tsananin son jama’a da son yara cikin lokaci kadan tashaku da sulaiman da mahamud ya’ya ne ga yayyen aliyu sun shaku matuka da yaran ta daukesu tamkar ya’yan data haifa acikinta .
suma kuma suna maseefar kaunarta dan haka suke kiranta da ummi ,duk abinda suke so itace take musu bata ragesu da komai ba saboda bata da rowa hakan ne yasa ta sake janyo mata soyayya ta daban a gurin iyayensu.
shekarata biyar da aure mutuwar mahaifiyar ta risketa ,zuwan datayi indiya ne dazata dawo tazo da kanwarta fadila ta hada dasu Mahmoud tacigaba da rikonsu .
sai da fadila ta dauki sama da shekara takwas da aure sannan tasamu cikin murna a wajen wannan family bai faduwa .
cikinta na da wata tara cif ta haifi NASURUDEEN daga ita har aliyu suna matukar son DEENI tamkar numfashinsu DEENI yataso cikin gata da kulawar iyayensa, da dangi gabadaya suna nuna masa tsansar gata da soyayya fiyye da tunanin mai karatu .
shiyasa yataso a shagwabe a sangartacce saboda kaf estate din kowa yasan da zaman DEENI babbar matsalar da suka fara fuskanta da deeni , shine rashin magana da bai yi ,da farko fadila ta dauka ko kurma ne sai daga baya tagane tsabar miskilanci ne kawai yayi masa yawa .
duk tarin ya’yan dake cikin wannan estate din DEENI yafita dabam acikinsu, bashida aboki ,.
gabadaya baya yarda da kowa koda yaushe yana tare da umminsa ko farida ko su Mahmoud tun tasowarsa yake da burin son zama soldier yayinda ummi take bashi goyon baya wajen kiransa soja .
Domin wani lokacin zai je yatasa hotonta marigayi kakansa dake manne a falonsu gaba yayi ta kallo yana shafa fuskar tsohon yana murmushin ,Sam shi bashi da fara’a ballanantana sakin fuska koda yaushe fuska nan tashi a hade take tamkar hadari , .DEENI Nada shekara takwas byn yakare primary school aka sai mishi form din shiga makarantar sojoji ba’awani samu wata matsala ba yasamu sakamakon matsayin mahaifinsa da kakansa. sabanin wayanda basu da gata.
domin a wanan lokacin idan dai kai bawani bane ko dan wani ba ko bakada hanya a military school ,sunanka sorry.
Domin kuwa kana ji kana Gani military school zai gareka shiga .
byn wani lokacin farida ta samu miji anan cikin estate din wanda shima yakasance “Da”ne ga marigayi Muhammad bello wato habibu ubansu daya da aliyu mahaifin ga DEENI .
duk da fadila ta nuna rashin amincewarta matuka , da nuna wa er’uwartata illar aurenta da Habib Amman sai taga yarinya ta nuna tana so abunta ,dan haka ta kyaleta kuma da kunya dai ta fito fili tace batason jinin aliyu ,wanda itama kanta tasan hakan ba mai yiwu bane . itama ba wai shi din ne bataso ba ,halinsa ta tsana ,
Amman shi babban ma’aikace gwanati ne, director of land and housing & same na Lagos state gabadaya. yana da mata biyu da yaya bakwai farida ce ta uku .
Ko alokaci daya auri farida takasance mace ce mai tsananin hakuri .
duk da mijin nata Vai kasance mutun mai adalci ga iyalansa ba. Amman bata taba kawo kararshi ga ummi ba domin tasan halin ummi Sam bata son raini .
Shekarar da aka yiwa sulaiman da mahamud aure shekarace Allah yayiwa mijin ummi rasuwa wato alh aliyu Muhammad bello sunji matuwar farar daya , mutuwar tayi matukar gigita ummi dan byn ya dawo daga sallah asuba ne yayi irin kishingide nan yana lazimi koda ummi taji shiru shiru bai sake fitowa ba Sannan bai nemeta ba kmr yadda ya saba , wanda aldarsa ce da zarar gari yayi sha …yake fitowa ko yakirata a waya Amman taji shr .
tashiga dakin nasa ta tarar dashi kishingide da carbi a hannunsa .
da fari ta dauka ko bacci yakeyi sai tayi nufin ta tasheshi yakoma kan gado.
Ammai sai taga alamun rashin motse atare dashi takai hannuta wajen hancinsa da karjinsa a lokacin daya taji baya numfashi.
take ta zube anan ta sume.
har a kashare zaman makoki ummi batasan a wani hali take ba ,dan bata cikin haiyacinta’ koda ta farfado ma sai da akayi ta hadawa da addu’a Sannan aka samu kanta ta dawo daidai , dan mutuwar ta girgiza har ta kusan zarar daita .
Byn wani lokacin su sulaiman suka cigaba da tallafawa ummi da DEENI a lokacin farida na dauke da tsohon ciki duk da itama ta dan jima bata haihuwa ba, kuma har lokacin ummi bata san er’uwarta tana cikin matsala ba ,sai byn data haihu” lokacin ne ummi taga komai bbu alhalin ga tarin dukiya kmr zai kashe habibu , gashi yasake kara wani sabon auren matansa sun cike hudu cif .
ummi tayi kuka kmr may gashi tana cikin danginsu da suke tamkar tsiya madauri daya.
ba daman tace zata dauki wani mataki akan haka .
dan tasan yadda kansu yake a hade .
dan haka taci kukanta takoshi ita da er uwarta ahankali take furta kalmar shiyasa tun farko naki amincewa da auren nan naki da habibu ,ba dan komai ba sai dan irin haka Amman kika nace ,ga irin abinda nake gudar miki kennan Amman kika kiji , sai kuma ta tsagaita da kukanta ahankali tace ba yadda zamuyi da ikon Allah ,sannan ga rabo a tsakani.
Amman duk da haka sai da ummi tayi masa tatas saboda daman ita bawani sakar masa fuska take ba kuma yana shakkata.
kullum ummi acan take wuni har ranar suna yarinya tace sunan mahaifiyarsu ummi wato muzeenat , shima habibu yayi hakan ne saboda ya wanke kansa a wajen ummi,kuma yayi nasara domin hakan da yayi yasa ummi taji dadi Sosai aranta har ta dan rage jin zafinsa .
sannan bakaramin kudi ummi takashewa bby ba. haka ma ranar suna ummi Tayi rawar Gani sosai .
byn anyi suna ne ummi tasamu habibu akan dan Allah ya dinga kula da farida dan ita kadai gareta bata da kowa duk fadin Nigeria sai ita, idan ma bazai damu ba, zata bashi Rabin dukiyarta yakara akan nashi da duk wani abinda yake so, ita dai burinta kawai ya kular mata da er,uwa ,yayi murmushi kawai hade da ce mata yaji .
Byn wani lokacin farida ta kuma samun wani ciki wanda tun yana karami take fama da laulayi tun lokacin ummi tadawo da zeenat wajenta ,
a kwana a tashi bbu wuya a gurin Allah har cikin farida ya isa haihuwa gurin haihuwar ne taji jiki sosai .
koda ta haifi yaron ma bbu rai sannan itama tace ga garinku .
mutuwar ta shigi habibu matuka yayi kuka tamkar ransa zai fita ,dan shi kansa yasan yayi babbar rashin da ba zai taba maida irinsa ba.
yayi rashin mata mai tsananin kirki da hakuri da sanin darajar miji . Allah sarki ummi kusan har tafi habibu jin mutuwar tilon er’uwarta ta ,.
a wannan Lokacin ne rikon zeenat ya dawo dindindin gurin ummi ta dauki soyayyar duniya ta daurawa zeenat tana mugun ji da Yarinyar tamkar ranta kwata kwata bata son abinda zai rabata da zeenat Sannan kuma tana debe mata kewar er’uwarta .
lokacin shi DEENI na ss1 a NMS, Nigeria military school dake zariya.
yayinda DEENI Sam ba halinsu daya da ummi ba koda yaushe kagansa fuskar nan tasa a daure a cunkushi bbu wani fara’a ga shegen miskilanci tsiya sai dai mugun kyakkyawa ne na karshe . ajin farko, wato first class ,gashi da maseefar iya sa kaya kallo daya zaka masa ya gigitaka kaji yashiga ranka farar daya saboda tsabar kyawunsa sai shegen shiga ran mutane domin kusan yan’mata cikin estate din suna maseefar son sa yayinda yake girma kyawunsa na sake bayyana hade da miskilancinsa .
Tunda zeenat ta dawo gidan magana bata taba hadasu ba ko gaisheshi Tayi baya amsawa in dai bayaga idanun ummi ba yana da matsanancin tsafta wanda kusan a wajen ummi yagada .
Cikin haka ya kammala karatunsa na secondary school ya wuce NDA burinsa kennan nason zama cikakken soja itama ummi kuwa nasake karfafamasa gwiwa da bashi goyon baya yana karantar science ne ,wato likitan soja .
bansan yadda zan kwatanta muka halinsa ba Amman yakasance mutun ne shi mai bambanci ra,ayi.
byn yakare karatunsa ya fito da mukami second lieutenant star biyu kennan .
Zaune zeenat take a falo tana kallon wani serisfilm a zeeword my let home Tayi zurfi cikin kallon film din gabadaya attention dinta naga kallon ita kadai ce ummi tashiga cikin estate din yin barka taji karar Bell wanda shine kusan karo na hudu da taji ana dannawa. cikin jin haushi ta mike dan bata son abinda zai dagata daga kallon datakeyi , tana bude door din bata tsaya ganin kowaye ba ta juya abinta takoma mazauninta sallama taji hade da shigowa ta dago kanta kennan da niyar amsa sallama sai taga mutun tsaye kikam sanye da sabon kayansu na sojoji gabadaya zeenat ta gigice hade da rikicewa tsabar tsoro dan ita Allah yayita da maseefar jin tsoron soja take cikinta ya dauki kugi Amman still idanunta na kansa ta tsaresa da kallo .
in ina tasoma yi wa..wa.. waalai….ya dakatar daita da hannushi, yana zabga mata wata uwar harara muryasa a kwasashe yace yau ne kika fara ganina da har zaki wani tsareni da idanu Kona canza miki ne ?da sauri tasoma girgiza masa kai. Kai tsaye dakin ummi ya nufa tunda bai ganta a parlour ba yasan tana dakinta tana kallonsa ta kasa dauke idanunta daga garesa har sanda ya dawo fuskar nan tasa a hade yace ke…..dan iskanci kina kallon mutune bazaki iya cewa ummi bata nan ba kin wani tsare mutun da idanuwa tamkar na maciji ,dayake bawani manyan idanu gareta , da sauri bakinta na rawa tace dan Allah kayi hakuri mantawa nayi ko kallonta bai sake yi ba yaja tsarki yayi hanyar dakinsa ta tabe baki hade dacewa jarababbe kawai ai yadawo kennan, itama taja tsaki ta juya tacigaba da kallonta ..
MMN SUDAIS CE
πππππ
AUREN SIRRI
πππ
πππππ
Aysha A bagudo
Page 3-4
Sai da tagama kallonta tsab Sannan ta canza Chennal hade da tashige kitchen dan daura abinci abincin dare
bakin kofar kitchen din ta dawo Tayi tsaye abunta tana cigaba da kallonta Chennal data canza, ajima ajima tana zuwa tana duba abinda ta daura.
Karar bell taji ba kaukautawa shiyasa da sauri taje ta bude gudun maseefar DEENi dan tasan muddin yana gida baya son yawan hayaniya , yanzu ne zai gama daita, Maryam tagani tsaye da wasu en school dinsu su biyu tuni murna yakama zeenat ,ta rungume su daya bayan daya tana musu sannu da zuwa hade da basu hanya “suka shigo har cikin main parlour din hade da Sallamar su .
waje ta nuna musu da hunnu kuzauna mana suka zauna ita kuma takoma kitchen ta duba abinda ta daura taga yayi ta kashe gas din sannan ta dawo inda tabarsu hade da kawo musu drunks mai tsanyi da snacks ta ajiye agabasun .
gabadaya hayaniyya ce ta barke a atsakaninsu da murna ganin juna ,zeenat ta kalli su Sumy hade dayin kasa kasa da muryata tace kuyi magana ahankali fa sannan tace kun kyauta sai yau kuka ga damar zuwar mana , Sumy tace ba gara mu ba muna zuwa time to time.
kufa sai aikin sa rana kullum, hira suka shiga .
a inda Maryam ta dube zeenat tace wai nan fa IV suka kawo mana na birth din rukky, zeenat ta zaro idanu waje I ….me Maryam tace IV .
zeenat Tayi dariya hade da cewa uhmm badani ba” kema kinsa sarai baza’a taba barinmu zuwa wani birthday party ba ” Sumy Tayi murmushi sannan tace ai sai da nagaya rukky Amman tace ga zance ga magana ” gashi nan, ni ai nasan bazakuyi attending birthday party dinta ba ,da day itace sarkin shishigi da neman suna , zeenat tace kmr kinsani ,duk abinda ya wuce cikin gidan nan namu “ta girgiza kanta baza’a taba barinmu ba ,ki bata hakuri kawai Amman wlh har ga Allah naso zuwa ko dan rukky Sumy tace to why nut ku sace hanya kuje a boye batare da kowa yasani ba … zeenat ta kalli Sumy fuskarta a hade tace kefa kin cika matsala fa wlh.
kmr bada hausa nake miki magana ba.
ta bude bakinta kennan da niyar sake balbale summy.
sai ga DEENi ya sake fitowa parlour jikinsa sanye da jallabiya marun colour may maseefar kyau sai kyalli take zuwa ga kamshin turarensa mai mugun sanyi dadi wanda tun tasowar zeenat ta sanshi da auren Hamilton har yanzu fuskarsa a daure take tam .. kmr koda yaushe ” take ta hadiye maganarta batare da tasan Tayi hakan ba ,ta zuba masa idanu tana kallon kwayar idanunshi, sai data ya hararata, sannan ta dauke idanunta ,ta maida kallonta da hankalinta kacukam a kansu Sumy dake zaune surusuru. Yayinda gabadaya Maryam duk ta fisu tsurewa ko dan ita Yar gidan ce oho..
cikin wata irin murya mai sanyi dadi tamkar ba soja ba yace ke……ta juyo ta ahankali ta sake zuba masa idanunta dan tasan dai daita yake dan haka tabada duk attention dinta garesa.
bakisan kibawa mutun abinci bane ? Dan iskanci sai an roka ,zatayi magana ya katseta a fusace , ai ba tun yanzu nasan ke muguwar rowa ce dake ba Tayi surusuru da idanu ,da sauri tace kayi hakuri dan Allah nayi zaton ko kana azumi ne “naga kullum kana yi ”
yace “oh “dama kinsa min ido ne har kinsa cewa azumi nake kullum ?
Jikin Maryam har rawa yake ,a hankali tace wayoo Allah ashe ya dawo ,bari in gudu tun bai gama daita ya da kanmu ba , zeenat tayi shr har sanda ya sake maimaita tambayarsa hade da cewa dan ubanki bada ke nake ba kike bina da idanu kmr zaki cinyeni” ta sake girgiza masa kai,. Tana bashi hakuri
marowaciyace banza kawai mai mugun gado. shiru yayi na dan wani lokaci hade da sauke numfashi .
Sannan can kuma yace ai idan bakiyi rowa ba sai Allah ya tambayeki” km baza’asan ke…Yar uncle Habib bace .
kin taba ganin barewa Tayi gudu danta yakasa rarrafe” zeenat ta sake girgiza kai da sauri ,yace OK ashe dai kema kinsa gaskiya dole kiyi gadon rowa.
Ganin haka yasa su sumy suka nemi sulalewa duk yana kallonsu sai daya ga Maryam na shirin gudu itama dan har summy ta daura hannuta kan handle din kofar ,ya dakatar dasu da hannusa , sannan yacigaba duban zeenat yace barikiji da kyau yana mai nuna da yatsansa” nan ba gidan marowata bane gidan masu bayarwa ne aci . yace menace ? Da sauri tace gidan masu bayarwa ne.
yace gud daga yau bama ni ba ,ko wani ki kaga yazo gidan nan ki bashi ruwa da abinci yaci dan ba naki bane.
ya sake jiho mata wata tambayar yace ko abincin naki ne?, da sauri ta girgiza masa kai dan gabadaya ta sure ta kasa kwakwaran motsi sai ajiye zuciya kawai take yi , yace” baki da baki ne kike kadawa mutane kai , tace naji kayi hakuri dan Allah. Sannan ya juya kan Maryam da kadan ya rage ta fashe da kuka , ya zuba musu ritattun idanunsa da suka fi kama da mage masu saurin raunana mutun kai tsaye , yace ku kuma en iskanci banza kun wani cikawa mutane kunne da hayaniya tamkar kuna club ,kallo daya yayi musu kowace tabawa kafarta iska yaja tsaki ya juya ya nufi dakinsa.
ahankali zeenat take sauke ajiyar zuciya hade da dafe kirjinta , batasan meyasa ba ,idan har Yaya DEENI yana guri Sam bata samun cikakkiyar natsuwa “sai tarinka ganin duk yacika guri ga tsananin tsoransa da take ji yana mamaye zuciyarta . Maryam har da kuka tayi byn sun fita dan daman can ita haka take ,shegen tsoro gareta aiko, su sumy suka ce mezasu ba dariya ba dariya suka dinga yi har da rike ciki suna nuna ta aiko tace yau sai da suyi ta zama a estate din dan bazata rakasu gun securities ba sai da sukayi ta bata hakuri sannan suka jera suna hirar abunda ya faru.
Ko lokacin da ummi tadawo tuni murna da farinciki Ganin tilon “dan ” nata yamamayeta zuciyarta nan suka zauna a parlour suna hira cikin hirar ne ummi take masa maganar aure in da tace masa yakamata yanemi mata yayi aure kasan shekararka nawa kuwa yanzu ?yayi murmushi ai dole nasan shekaruna ,muke nan kullum cikin rubuta date of birth ,talatin da biyu ne kawai fa ummi Tayi dariya 32 din ne kawai kusan duk sa’annin haihuwar ka duk sunyi aure acikin estate din nan gasu yasir nan ma duk ansa musu rana dan haka kaima ka fidda mata kafin azumi DEENI yazaro idannu yana bin ummi da kallo a shagwabe yace haba first love dan sunan da yake kiranta dashi kennan tun tasowarsa …. ni din guda nawa nake da zakice inyi wani aure yanzu. Dan Allah kiyi hakuri my first lov zuwa wani lokaci ,duk hirar da suke zeenat na zaune tana jinsu haka kawai taji gabanta na faduwa lokacin da taji abinda ummi tace ,Amma jin amsar da yaya DEENI yabata yasa taji wani irin sanyi na ratsa zuciyarta .
kmr ance ya dago idanunsa suka sauka cikin nata harararta yayi yace kallon fa kin wani tsare mutun da idanu, ummi tace uhmm kafa dawo kennan karka takuramin yarinya ,
ya langwabar da kansa yana maida idanunsa kan ummi cikin sanyi murya yace haba first lov baki ga irin kallon da take bin mutune dashi bane, kmr bata san mutun ba , ummi tace kai da wani idanu ka kalleta har kasan tana kallonka. kuma ma ni banga komai ba kai dai ta kurace kawai dakai indai kana gida baka barin yarinya nan ta huta ta sarara , ya dubi ummi ya tabe baki , Sannan yace ke….kawo min coffee ,ta mike taje ta hado coffee din takawo masa gabanta na wani irin faduwa ta durkusa har kasa ta ajiye masa .
Adaidai wannan lokacin ne zeenat ta kammala karatunta na secondary school , ta fito da sakamakon mai kyau domin tasamu almost 7 credit masu kyau .
shi kansa DEENI yaji dadi Sosai sanda ummi ta nuna masa Amman dayake miskili ne, sai cewa yayi Sam shi bai ga wani kokari da Tayi ba tunda bata cinye duka ba .
ummi Tayi murmushin tace kai ne dai bakaga kokarin ta ba. Amman ni nagani km nasan Tayi kokarin Sosai .
Ina laifi duk cikin wayanda suka rubuta jarabawa tare bbu wanda yakaita marks ,.
yace ok inda ta cinye duka ne zan iya cewa Tayi kokarin ai wayanda suke cinye 9 credit ba finta brain sukayi ba.
Ita dai wasa da kallace kallacen banza tasa a gaba.
ummi ta hade fuska tana harararsa yacigaba da zagin zeenat ganin yadda ummi Ta canza fuska ne ,yasa yabar maganar , ummi ta sake duba result din tana shafawa hade da kwallawa zeenat data tashi tun sanda taji DEENi yasoma zaginta kira ,takaraso tazo ta tsaya kusa da ummi DEENi ya dauki wayarsa yana daddannawa ba ko kalli inda take ba ummi ta mika mata slip din tana murmushin tace kinyi kokari sosai , zeenat ta karba ta juya ta bar gurin dan bazata iya zama a duk inda yake ba .
ummi ta dubi DEENI tace yanzu kuma sai aure zanwa zanwa yarinyata .
DEENI ya juyo a sukwane yace wani irin aure kuma first lov da rana tsaka , kudai Bari yarinya tacigaba da karatu kawai” dan yanzu kai yawaye , an daina irin wannan auren, ballanantana mata marasa illimi “ummi ta dubesa da kyau ta numfasa Sannan tace ni tawa iya secondary zan aurar daita dan ma taki sauraran masu sonta . itama shegen iyayi ne daita kuma dai kasan matan wannan family din basa wuce secondary ake musu aure .
kuma kasan baza’a fara karatun jami’a daga kanta ba, uhm nima nafi son na aurar da abita. DEENI ya tabe baki Sannan yace Allah ya kyauta ni ko zanyi aure bazan auren Yar secondary ba wlh sai wacce tagama jami’a mai tarin illimi ,kuma ba auren family zanyi ba dan baya birgeni. yakarasa maganar yana dan murmushi ,ummi tace to Allah yabaka sa’a. amman ni tawa aure zan mata da wuri .
kai kasan halin big dady bazai taba barinka kayi aure a waje ba .
Wlh nasoma a hada aurenka dana su yasir yace uhmmmm su dai yi nasu ni sai nan gaba .
A wata yammacin DEENI zaune akan dadduma awajen shakatawa shi da abokansa wayanda duk kusan , family ne zagaye dashi gefe guda kuma flasks ne cike da ruwan zafi da kananan cups , hira suke sosai atsakaninsu Amman banda DEENI dan gabadaya daukar hirar tasu yake shirme dan duk zance nasu akan maganar aurene wanda shi kuma Sam baya kaunar ji , dan haka ya sharesu yacigaba da lasalasar wayarsa ya yinda ya kai hannunsa daya ya dauki cup din coffee wanda orready fk ya tsiyaya masa ya kai bakinsa yasha hade da rufe rikitattun idanunshi wanda yazame masa jiki fk ya kalli yasir da faysal dake tawowa inda suke, ya kwashe da dariya har suka karaso bai bar musu dariya ba fk yace sannuku da karasowa Mayan angwane kunsha kamshin kunsha kamshin ,faysal yace kai dai anyi dan iskan yaro , kai baka tsaya ruwan ido ba kana biyewa wannan ya nuna DEENI da yatsa fk yayi murmushi yace yayi an gwanen bana wannan karon gabadaya suka dara hannu suka bawa juna suka gaigaisa har DEENI.
yasir ya dube fk yace ai gara muyi aurenmu tunda muna son juna kai ka zauna kar kayi har mahdi ya bayyana ,fk yace A’a nifa bance saboda me zakuyi aurenku ba . Amman gaskiya zaku takura kanku ne kawai yanzu da wani aure wayannan kananan bbys din.
DEENI ya tabe baki Sannan ya dube fk yace shiyasa rawar kan yaran ke kara yawa ba . dukkansu suka sa dariya suna cikin dariyar ne fk har da rike ciki sai gasu zeenat da suka taso daga islamiyya su biyar suka jero kowace sanye da hijab dinta raudat da shemah da samiha da Maryam sai zeenat dake tsakiyar su dukkansu kyawawane .
da hannut fk yake nuna musu inda suke Sannan ya dakata dariyarsa ya kalli inda DEENi ke zaune tamkar bai san abinda ake ciki ba , ko kallon inda suke bai yi ba, yacigaba daddannawa da sarrafa wayarsa .
fk yace kai gaskiya bbys din nan fa su hadu dayawa fa , nima ko zan dan shiga daga ciki ne.
yasir yace dako ka huta , kabar wannan ya nuna DEENi fk ya cigaba A’a ina ai bazan barsa ba tare zamuyi namu auren , ko yakace mutumina kaga Shikenan mun huta da surutu jama’a DEENi ya kallesa a kaikaice yace A’a ku dai da kuka ji zaku iya kuje kuyi Tayi .
Amman ni ya nuna kansa da yatsansa hade da tabe baki, ba yanzu ba” har sanda su zeenat suka zo suka wuce . Suna hirarsu suna dariya Maryam ce ke basu labarin abinda ya faru jiya bbu wanda bai dara ba har ita zeenat din raudat tacewa zeenat ai ke kika daukar masa wlh kuma yarinka yi miki kennan ina ma nice daya gane kuresan suka sake yin dariya .
Tun lokacin daya dawo zance sa da ummi bai wuce DEENI kayi aure fito da mata cikin yan,uwanka kayi aure hirar kennan sai dai idan basu zauna ba .
Yau takama walimarsu zeenat ta saukar alqur’ani mai girma wanda aka shirya musu anan islamiyyarsu dake cikin estate din ,su kusan goma anyi taro walima lfy yayinda zeenat ta karbi kyaututtuka da dama saboda kokarinta har kuka ummi Tayi sakamakon tunowa datayi da er’uwarta taro ya watse lfy kowa yakama gabansa ,byn sun gama hirarsu da ya zame musu jiki suka fara hada kujerun da akayi walimar dasu . sun fito kennan suka ga Yaya DEENI da wani abokinsa zaune akan kujera biyu suna hira ,take suka ja birki samiha tacewa zeenat jeki amso wadan can kujerun, cikin zolaya tayi mata maganar dan tasan yadda take jin tsoronsa zeenat tace uhmmmm ku dai kuje “suka sa mata dariya ke wlh muguwar matsoraciyace wlh ki rage tsoransa shiyasa yabi duk ya renaki ,Tayi sororo tana kallonsu , Sannan tace to bari naje amso Tayi tafiya kmr zata isa gurinsa sai kuna ta juyo da sauri” aiko suka sake kwashe mata da dariya .
muryashi ce ta katse musu dariyar tasu lokacin daya suke kallonsa a frigice” yayinda gaban zeenat yasoma faduwa yace ke….da hannu ya nuna musu alamun suzo ‘s suka nufo inda
Yake cike da tsoro ya zuba musu rikitattun idanunsa yana kallonsu daya byn daya yana nazarinsu Sannan yace da ganinku akwai alamun rashin gaskiya atare daku ? ya nuna su da dan yatsansa zeenat Tayi saurin cewa A’a cikin inda inda uhm bbu komai fa Tayi gudun Kar wata cikinsu tafada masa shiyasa Tayi saurin yin magana ,to menene na inda inda wama ya tambayeki ?Tayi shiru tamkar ruwa yacinyeta. Sannan ya juya ya kalli abokin nasa da ya zubawa zeenat idanu yana kallonta kafarsa yasa ya take kafar manir dashi ,sannan ya dawo natsuwarsa ya mai da hankalinsa kan DEENi , DEENi ya nuna su zeenat da samiha hade da shemah da Maryam yace gasu nan bansa inda sauran suka nufa ba, manir yace ina tayaku murna walima saukar alqur’ani mai girma, Allah yasa na tsoron Allah ne ,suka hada baki wajen cewa Ameen , kallonsu kawai DEENi yayi jikinsu har rawa yake suka bar wajen.
manir yabi bayansu da kallo yace kai sisters din nan naka fa akwai kyau DEENi ya kallesa yana watsa masa harara ok iskancin naka kuma yau agidanmu zai Kare.
manir yayi murmushi yace Allah barin ma wace ta tsakiyarsu gaskiya duk tafiso haduwa DEENi ya kalli inda ya nuna sai yaga zeenat yake nufi take yaja tsaki manir yace dama ita ka zaba wlh dan nasan karshe ma auren zumunci za’a maka DEENi ya sake jan tsaki dan Allah malam karka dameni da wannan shirme bazan ,manir bai daddara ba ya sake cewa Allah dama tsayawa kayi akayi Yar gida tunda duk tarin matan dake sonka baka kallonsu , a fusace DEENi yayi magana dan me zan kallesu alhalin banda abinyi dasu.
manir yayi murmushi ina ma ni ne kai wlh tsayawa zanyi na kwashi gara son raina har sai nagaji in more kuriciyata , DEENi yace ai kai dan iskanci ne lamba daya , wlh ka guji abinda kakewa ya’yan mutane “ko dan gaba .
ka dauki neman mata tamkar wani abinci, manir ya dan daki kafadar DEENi yace ai sun fi abinci dadi ,.
Amman Allah koni ina son na daina bin matan bazan ,wlh abun ne da kmr wuya Amma kacigaba da yimin addu’a . DEENi ya nuna sa kai zanwa addu’a saboda banda abinda zan roka Allah , manir ya dage masa gira daya yes meye dan kamin addu’a kaga idan Allah ya shiryani sai kabani wacce Yar dimadimar sister din taka na aura , bai kulasa ba sai canza zance da yayi nan dai suka cigaba da hirarsu har zuwa sanda sukayi sallama da juna .
Abinda zai daure maka kai bai wuce yadda ummi ke sake bawa zeenat kulawa ta musamman ba ,ta kowani part tana iya kokarin ganin ta fito da diyarta ta tsab, zeenat bata rasa komai ba tun daga dangin sutura da mayuka shafe masu tsada zuwa kayan kwalliya ana cikin haka tafiya takama ummi zuwa India dan haka ta tasa diyarta gaba suka tafi zeenat taji dadin zuwansu India tamkar karta dawo ,watan su daya suka tattaro suka diro Nigeria saboda bikin family dinsu yakusa koda ta dawo ma su Maryam sun dinka mata duk anco din da aka fidda tunda damar suna da telarsu ce da yake zuwa har gida ya karba dinki,.
biki akayi sosai bakama hannu yaro an kashe kudi tamkar ba’asan ciwonsu ba bidia iri kuma a duk anan cikin estate din akayi komai, daga karshe akayi walima washegari ranar Sunday aka daura auren en mata biyar haka ma samarin aka dan kowace gidan mijinta, ya saura mutun uku ne cal suka rage da basu aure ba, Maryam da shemah sai zeena amaza kuma fk da DEENi sai kamil .

Leave a Comment