✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨
(𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)
𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (001)
……..A matuƙar razane Iffah ta shiga girgiza Tajwar Eshaan jikinta na rawa, gaba ɗaya ta daburce jin jikinsa ya saki ma gaba ɗaya a kanta, hannu ta kai saitin hancinsa, ƙirjinta ya sake girgiza tamkar zuciyarta zata ɓallo daga cikinsa ta faɗi. Cikin fita hayyaci ta cigaba da ɗan girgiza kafaɗunsa dake jikinta da faɗin, “Karka min haka, dan ALLAH ka tashi, ka tashi ka faɗamin, ka faɗamin wanene kai, wanene Ajmaal? Minene alaƙarka da shi? Idan ka mutu nima wlhy mutuwa zanyi… wayyo Ummu wayyo Babiy na shiga ukuna….” kuka ta fashe da shi mai tsuma rai tana mai ɗaura goshinta kan nasa da cigaba da ambaton “Innalillahi wa’inna ilaihiraji’un! Shike nan ni Fhareedah, shike nan na kasheshi Ummu, Ummu na kashshi na shiga ukunaaaaa!!”.
A tare Miran Jasim da Miran Arshaan dake shigowa suka ɗauki salati, yayinda Malikat Bushirat da kalaman Iffah sukai matuƙar cakar ƙirjinta tamkar saukar mashi juwa ke neman zubar da ita a ƙasa, cikin sauri Daneen Ammarah dake bayanta ta riƙota itama jikinta na rawar. Jasrah dake bayansu kam tuni tayi kukan kura akan Iffah da ruɗani ya hanata sanin shigowarsu duk da salatin da su Miran Jasim ke faman jerawa har yanzu. A birkice ta janyo Iffah baya ta shaƙeta, faɗi take itama sai ta kasheta, sai ta rabata da numfashinta. Ganin Jasrah na neman yin kisa da gaske Daneen Ammarah tai saurin zaunar da Malikat Bushirat a kujera ta nufesu. Da ƙyar ta iya ɓangare Iffah da taimakon Miran Arshaan da sai da yaga Daneen Ammarah ta zaburo sannan shima ya zabura. Yaraf Iffah ta zube ƙasa tana jan numfashi da ƙyar, yayinda Jasrah ke cigaba da zabura cikin kuka akan ita sai fa ta kashe Iffah. Ƙoƙarin tanƙwarata Miran Arshaan yake yi amma sai ta sake kufce masa. A wannan karon kam da ƙyar Daneen Ammarah ta ɓanɓare Jasrah ta hanyar sauke mata mari itama.
Ɗifff kowa ya ɗauke wuta a ɗakin sai kakarin wahalar da Iffah keyi, dai-dai nan kuma Sayeed Aashiq Ali ya iso da likitoci, kasanwarsa uba a gare su a tsawace ya basu umarnin duk su fice. A kaikaice Miran Jasim da Miran Arshaan suka dalla masa harara kafin su fice, Daneen Ammarah ta taimakawa Malikat Bushirat da bata tofa ko kanzil ba har yanzu, Miran Arshaan kuma ya kama Jasrah. Iffah kasa tashi tayi dan da gaske ta shaƙu, dole sai da aka taimaka mata itama. Da ƙyar aka iya ɓanɓare hannun dake cikin na Tajwar Eshaan har yanzu tana kuka kamar ranta zai fita. Sashenta aka maidata, tare da sake zagaye sashen Shahan-shan ɗin da tsaro na musamman. Likitansa da wasu ƙwararrun likitoci biyu dake a kansa domin ceto rayuwarsa tuni bincikensu ya gano musu dafin macizai da guba da ya sha. Sun sami nasarar kashe kaifin dafin macizan, sai dai sun tabbatar da gubar ta fara ma jikinsa illa, idan kuma ba’a gaggauta yin wani abu ba zai iya rasa ransa duk da a yanzu ma dai sai abinda ALLAH yayi.
Hankalin su Malikat Bushirat da gaba ɗaya ta gama fita a hayyacinta ya sake tashi, dan gani suke ma Tajwar Eshaan ya rasu ne likitocin na ɓoyewa ne kawai. Saboda duk wanda ya ga a halin da aka samesa bazai taba sakankancewa zai rayu ba. Malikat Haseena tsohuwa mai ƙarfin hali da jarumta, duk da yanayin da nata jikin yake bata gaza nuna ƙoƙarin ta ba.
Da taimakon Daneen Ammarah aka maida Iffah dake matsanancin kuka tamkar wadda ta zautu sashenta, suna shiga ta riƙo kafaɗunta cikin tashin hankali tana mai girgiza ta, “Ibnati kice min ba haka bane kar zuciyata ta buga, dan ALLAH ki faɗa mana gaskiya miya samesa, minene ya faru?”.
Babu alamar Iffah zata kare kanta, sai ma wani irin karkarwa da jikinta ya farayi hawaye na rige-rigen sakkowa a kumatunta. Sai ma kawai ta tafi luuu ta zube ƙasa….
★A firgice Iffah ta farka daga barcin da likita ya sakata na dole. Dan tun bayan shafa mata ruwa ta farfaɗo yanda take kuka da surutai sai tai kamar wadda ta zautu. Daneen Ammarah da ke kallon al’amarin nata matsayin ruɗani ne suka saka doctor danƙara mata allurar barci gudun kar wani abu ya samu brain ɗin ta. Saurin riƙota tai cikin muryarta data sha kuka ta shaƙe take faɗin, “Ibnati kwantar da hankalinki…”
“Mamy hankalina bazai taɓa kwanciya ba. Dan ALLAH a wane hali yake? Ya rasa ransa ko? Ku kaini na sake ganinsa karki ce a’a dan ALLAH Mamy”. Duk wanda ya ga yanda Iffah ke jero waɗan nan tambayoyi yasan har yanzu a birkice take, dan tuni hawaye sun sake ma fuskarta kaca-kaca. Riƙota Daneen Ammarah tai ta rungume itama tana nata hawayen…
A tsawace Jasrah data faɗo musu babu zato ta bama jami’an dake a bakin ƙofar izinin shigowa ɗakin. Daneen Ammarah tai saurin dakatar da ita itama a ɗan zafafe.
“Jasrah!! Ki dawo cikin hankalinki, idan kin manta bara na tuna miki. Ita ɗin Zawjata-almilk ce, ba hadimar daular ruman ba, ba ɗakin barcinta ba koda falonta haramunne shigarsu…..”
Itama Jasrah cikin rufewar idon ta tari numfashin Daneen Ammarah “Nima idan kin manta bara na tunatar dake Daneen Ammarah. Ada wannan abar ke amsa sunan da kike tunanin zai bata waccan darajar da kariya, a yanzu ko sunanta ƴar ta’adda, mai kisan kai, kisan kan ma na Shahan-shan…..”
“Kin tabbatar da ita ta aikata?”.
Ta katseta itama a fusace.. “Mikike buƙatar ji bayan wanda kunnuwanmu sukaji? Da wanda idanunmu suka gani?”.
Rikici ne yake neman ɓarkewa a tsakaninsu, kowanne na ƙoƙarin ganin ya tabbatar da gaskiyarsa akan Iffah. Abune da bai taɓa faruwa ba, dan akwai girmamawa tsakaninsu musamman kasancewar shekarun Daneen Ammarah sama dana Jasrah. A yanda suke a fusace su duka ya sake hargitsa kan Iffah da gaba ɗaya ta daina gane komai, sai ma hajijiya da ke neman son sake zubar da ita a ƙasa tai nasarar jingina da bango…..
★….
A ɓangaren al’ummar ƙasar ruman kam dake faman zanga-zanga jin abinda ke faruwa hankali ya rabu gida biyu, wasu sun yarda harda shiga jimami. Wasu ko na kallon abin ta fiskar yaudara ne kawai Tajwar Eshaan ɗin na son ƙetare ƙasar ne saboda baya son yin murabus. Wasu kuma sun kasance ƴan babu manufa ne kawai. Ƙasa ta ɗauki ka-ce-na-ce tako’ina har wani bayajin zancen wani, haka ma kafofin yaɗa labarai da social media.
Duk yanda suka so jin bakin likitocin da suka dubashin hakan bai yiwu ba, sai dai an sami hatsabibin da ya haɗa guntun bidiyon cewar Shahan-shan babu lafiya kai babu ma alamar yana raye. Wannan video shi yay rugugin amsa kuwa cikin ƙankanin lokaci a kowace kafar ƴaɗa labarai na ƙasar. Duk da ɗan jaridan abinda yay kuskure ne sai wannan bidiyo ya zama tamkar alkairi, dan kuwa ya sauya labarin Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed daga azzalumin da bai son yayi murabus zuwa abin tausayi da fara tunanin anya kuwa babu wani abu a ƙasa da mutane ya kamata su sani?. Cikin ƙankanin lokaci bakin ƴan jarida da masu rajin faɗa aji suka fara fashin baƙi akan al’amarin, daga sauran talakawan ƙasa ma kowa nata faɗin al’barkacin bakinsa, wasu ɓangarori na mutane kuma suka fara binsa da addu’ar fatan alkairi da samun lafiya..
★★…..
Al’amarin fa tamkar wasa ƙaramar magana ta zama babba. Tabbas a yanda su Miran Jasim sukai shiri na gaske akan Iffah bata da wata mafita ta kowanne mahanga, sun kuma tsaya tsayin daka wajen nuna ƙarfin iko da tabbatar da Miran Jasim matsayin magajin kujerar Tajwar Eshaan har lokacin da ALLAH zai bashi lafiya shine zai cigaba da jan ragamar mulkin sarautar Shahan-shan. Wannan damar dake a hanunsu sukai amfani wajen damawa aka miƙa Iffah zuwa cikin kurkukun masarauta. A gefe kuma masarautar ta ɗauki ɗumi fiye da na sanda ake zanga-zanga kan murabus ɗin Tajwar Eshaan. Kowa faɗin albarkacin bakinsa yake, masu goyon bayan Iffah da ganin ta ƙarasa musu abinda suke burin gani, da masu zaginta da ganin gangancinta, da masu yima su Malikat Haseena ALLAH ya ƙara a cewarsu sun fifita lamarin Iffah fiye da Zawjata-almilk na baya da suka rasa ransu. Surutai dai kala-kala sai wanda kunnenka yaso ji. Dan har zuwa dare babu alamar masarautar zata lafa sai ma fita gari da maganar ta farayi har wasu kafafen yaɗa labarai sun fara tsegunta zancen a kaikaice…..
★………..★
Zuwa safiya daular ruman ta gama cika tako ina da sarakuna na jihohi dan labari ya gama karaɗe ko’ina. Dole amintaccen likitan Tajwar Eshaan da suka kwana kansa ya tattauna da manema labarai dan kwantar da hankalin mutane bisa umarnin Malikat Haseenat. Ya tabbatar da Tajwar Eshaan ɗin na raye, an kuma sami nasarar daƙile dafin macizan da aka shayar da shi a cikin madarar da bincikensu ya tabbatar musu. Sai dai zai cigaba da karɓar magani zuwa wasu ƴan kwanakin da zasu iya ji daga garesa. Hankali ya ɗan kwanta kaɗan, nanfa aka shiga jera masa addu’oin samun lafiya tamkar ba suke zanga-zanga yay murabus ba.
Sai dai kuma ga wasu hankalinsu ya sake tashi ne. Dan Wannan sauyi da aka samu saɓanin abinda sukai hasashen faruwa ya matuƙar tada hankalinsu. Saboda tun da Malikat Haseena ta bada umarnin sanar da ƴan ƙasa halin da Tajwar Eshaan ɗin ke ciki Miran Jasim da Miran Arshaan suka kasa zaune suka kasa tsaye. Sunbi wasu hanyoyi ta ƙarƙashin ƙasa domin daƙile fitar zancen ga al’ummar ƙasar ta ruman sai dai hakan ya gagara, dan Malikat Haseenat ta tsaya tsayin daka tare da rufe idonta wajen ƙin ganin komai sai ƙoƙarin wanke Shahan-shan ɗin ga talakawansa…
★★……
“Dole ne mu gaggauta sake salo muma, dan a wannan gaɓar idan har muka bar shaiɗanin yaron nan ya tsallake to mufa bazamu tsallake ba”.
Miran Jasim ne mai maganar hankali tashe yana faman kai kawo. Cikin gamsuwa Miran Arshaan ya amsashi da faɗin, “Kafin hakan dole ne mu fara kauda yarinyar nan. Dan barinta itama tamkar kashe maciji ne bamu sare kansa ba. Dan na tabbata zuwa yanzu ta dawo hankalinta kamar yanda Barbushi ya tabbatar mana abinda yay mata bazai jima a jikinta ba. Kaga kuwa a ƙalla yanzu muna da kusan awanni takwas da faruwar komai, na kula kuma tsohuwar can son dawo da martabar jikanta take yi kawai ta amfani da wannan ciwon”.
“Haka ne, kaima kayi magana mai ƙyau. Amma kasheta a wannan gaɓar bazai yiwu ba, dan in har muka aikata hakan zai ƙara tabbatar ma mutane abinda tsohuwar ke son a duba, kuma zai sake ɗaukaka darajar jikan nata dan na kula hankulansu ya fara dawowa kansa duk da ƙoƙarin da mukai na munana shi a zukatansu. Na rasa mi wannan matsiyacin yaron ya taka haka? Haka shima fa ubansa ya dinga wajiga rayukanmu”.
Ƙwafa Miran Arshaan yayi mai haɗe da cije lips. Cikin takaici da nuna jin zafi yace, “Lokaci yayi da zamuyi yaƙi na gaske wajen shafe babin duk wanda yay ƙoƙarin cigaba da kasancewa a gaban nasarar mu. Ba Eshaan kawai ba, hatta tsohuwar can da uwarsa lokacin kasancewar su larihi yayi”.
Wani banzan murmushi Miran Jasim ya saki yana mai kallon Miran Arshaan ɗin, a zuciyarsa kam faɗi yake (Har da kai a cikin wannan lissafin Akhi. Dan bazan taɓa hawa karagar mulki da wani maƙiyi shaƙiƙi ba) a zahiri kam sai ya ɗan bubbuga kafaɗar ɗan uwan nasa murmushi kwance a fuskarsa. “Shiyyasa bazan taɓa daina alfahari da kai ba”.
Murmushi shima Miran Arshaan ɗin yayi, a tashi zuciyar yana ayyana (Kwanaki kawai zakai na ɗan-ɗanar mulkin da ka kwashe tsahon rayuwarka kanayi, dan bazan taɓa bari ka wuce kwanan wata ɗaya ba. Ni kaɗai na dace da cancantar zama magajin daular ruman) a zahiri kam kaɗa kansa yayi har da ɗan risinar da kai alamar girmamawa yana murmushi………✍️
Hummmm. barkanmu da sake dawowa filin daga ƴan uwa. Barkanmu da salla kuma. Ya ibada? ALLAH ya sa muna cikin bayin da aka ƴanta, ya yafe mana kurakuranmu. Ya biya mana buƙatunmu na alkairi. UBANGIJI ka sadamu da rahamominka marasa yankewa. Fatan alkairi a gareku baki ɗaya🥰😍😘🙏.
*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*
*DAUDAR GORA Billyn abdul*
*KI KULANI hafsat xoxo*
*A RUBUCE TAKE Huguma*
*RUMBUN K’AYA Hafsat rano*
*IDON NERA Mamuh ghee*
_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_
_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_
_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_
_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_
_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_
_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_
_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_
ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN
MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171
SAI A TURA SHAIDAR BIYAN
09033181070
IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA
09166221261
*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*
+227 96 09 67 63
Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA
KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.
MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨
(𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)
𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (002)
……..Murmushi ta saki mai sanyi bayan gama sauraren dogon bayanin nasu, ta ɗan muskuta zamanta na ƙasaita cike da ƙarfin hali da sake bayyanar rauninta na tsufa da halin rashin ƙarfin jiki da jiyyar kwana biyu ta haddasa mata. Malikat Haseenat kenan tare da manyan masu faɗa ajin masarauta da suka buƙaci zama da ita akan lamarin Iffah da suke buƙatar shiga kotu domin yanke mata hukunci dai-dai da abinda ta aikata bisa tunzurawar Miran Arshaan da Miran Jasim. Cikin dattakonta da ƙasaita ta sake jan numfashi a karo na biyu idanunta akan su Miran Jasim, sai kuma ta ɗan kaudasu tana jinjina kai.
“Bazan hana ko dakatarwa ba akan gurfanar da mai laifi irin Zawjata-almilk. Sai dai a nawa adalcin ina bada ƙwarin gwiwa da shawara ga masu zaman shari’ar bin komai a sannu da yin ƙwaƙwƙwaran bincike. Sashen Shahan-shan dai zagaye yake da ƙyamarori, hakama madarar da aka tabbatar ya sha tana buƙatar musan daga ina ta fito, shi kansa dafin data zuba waya samar mata da shi har ya shigo cikin masarautar nan?. Abu na ƙarshe shine bata tsaro na musamman da saka idanu a dukkan abinda zata ci. Dan in har wani abu ya sami yarinyar nan batare da gaskiya ta fito ba a tabbata hukunci zai koma hannuna, kuma zan iya zartar da shi akan kowa. Idan nace kowa ina nufin kowa ma koda nice a karan kaina”.
Babu wanda ya iya tari a falon sai jinjina kawuna kawai suke. Yayinda Malikat Haseenat bata sake tofa komai ba sai ma ƙoƙarin barin falon da tai ta hanyar gara wheelchair ɗinta da remote ɗin jikinta (nace kaga ƴan gatan duniya lols😉). Da kallo suma kawai suka bita babu alamar wani zai ce har lokacin. Sai dai zukatan wasu tamkar zasu kama da wuta dan baƙin cikinta, ji suke kamar subi dare wajen mata yankan rago su zubar da jinin banza. Wasu ko gamsuwa sukai da bayanin nata, dan dama sunbi wannan ayarin ne kawai saboda rashin ƙarfin cewarsu, amma da za’a basu zaɓi sunfi buƙatar ayi haƙuri ma har Shahan-shan ya ƙarasa samun lafiyar da kowa ke fata…..
★★★…..
Kusan a tare suka iso falon kowa ransa a dagule. Sai faman huci suke kamar wasu zakuna. Tamkar basuga juna ba suka fara kaikawo kamar masu safa da marwa. Sunyi haka ya kai sau hur-huɗu kafin Miran Arshaan ya dakata cikin ƙunar zuciya ya furta, “A wannan gaɓar maciji muka kashe bamu sare kansa ba. Kauda wannan yaron a bayan rayuwar wannan tsohuwar sunansa BAYA DA ƘURA….”
“…Idan har barin wadda rayuwa ta zame mata saura ƙiris a zahirance zai amsa suna baya da ƙura to cigaba da numfashin waccan yarinyar sunansa BAYA DA TARNAƘI”. Miran Jasim ya katsesa a zafafe shima. Tsaye sukai sunama juna kallon kallo. Kafin Miran Arshaan ya katse shirun ta hanyar faɗin, “Tsuntsayen biyu jifa iri ɗaya suke buƙata. Inba haka ba a cikin ƙarfin iko za’a tabbatar da ƙarfafa mai rauni”.
“Na tabbatar da hakan ta hanyar gani da ido, kunnena kuma sun jiye min tabbacin AKWAI WATA A ƘASA bayan tatsuniyar gizo da ƙoƙi”.
“Miye mafita?!”.
Cewar Miran Arshaan cikin tarar numfashin Miran Jasim. Miran Jasim ɗin ya kafesa da idanu yana sakin wani murmushi. “A wannan gaɓar jifar tsuntsu huɗu da dutsi ɗaya ne ba biyu ba”.
Jimmm Miran Arshaan yay yana kallonsa, dan a saninsa da hasashensa tsuntsayen da ya kamata su jefa uku ne kawai ba huɗun ba. Sai dai kafin yace komai Miran Jasim ɗin ya katsesa da sake faɗin, “Tabbas huɗu ne, sai dai zamu fara kauda ukun kafin cikon na huɗun, dan haka dole ne a gobe mu ziyarci Barbushi”.
Miran Arshaan zai yi magana sai kuma ya haɗiye, batare da ya ƙara tofa komai ba ya nufi hanyar fita yana faɗin, “Asuba ta gari”.
Da wani mugun kallo Miran Jasim ya bisa, yayinda shima Miran Arshaan ɗin ya fice yana taunar lips tabbacin da nasa ƙudirin shima.
(Nace “Hummm”).
★★…..
Yau kwanakinta uku cif a cikin ɗakin da aka garkameta mai tsananin duhu da bata iya banbance dare da rana, sai ɗan hasken da kan leko ta window dake can sama karami na hasken rana ko wutar lantarki. Ta matuƙar zama wujiga-wujiga da fita a hayyacinta dalilin ƙin cin abincin da ake kawo mata sau ɗaya a kowane yini, sai madara. Tun a ranar farko ta gama fahimtar akwai babban ƙuli da ya kamata ta fara fahimta kafin zuwan wannan lokacin. Zuwa yanzu ta gama fahimtar su Miran Jasim sunyi amfani da ita ne, sunyi amfani da ita duk da itama da wannan ƙudirin a ranta. Sai dai kuma cika baki ne kawai, ta fahimci a hakanne a randa ƙaddarar dake tafiya da rayuwarta ta yanzu ta tabbata. Dole ta kira hakan da ƙaddara, dan inba ƙaddara ba babu ta yanda zata iya cutar da waninta mai bautar ALLAH da hanunta. Ƙwarai da gaske tanajin zafi, matuƙar zafi na rasa ƴan uwanta guda biyu a dalilin auren Shahan-shan. Hakan kuma shine ya zama sanadin komai na jin kangarewar zuciya da ƙudirin da babu tabbacin iya aiwatar da shi. Komai ya nema canja mata a lokacin da tai tozali da fuskarsa, bata san dalili ba ta dingajin kamar shi bazai iya kasancewa mai cutarwa ba, ta dinga jin dole akwai abinda yake ɓoye da ya kamata ta sani, sai dai a lokacin data gama shirinta tsaf akan hakan ƙaddara ta sake sauyata, komai ya nema rushewa a zuciyarta batare da riƙe wata makama mai ƙwaƙwarar hujja ba ta yanke hukunci ga wanda bata da wata hujja ko shaida akansa, wanda maimakon ya bada umarnin ɗaukar mataki a kanta ya nuna mata hanyar kuɓuta ta hanyar bata umarnin zubar da madarar da bata san yanda akai takaita gareshi ba. Amma kash, da alama ƙoƙarinsa na kubtar da ita bai tabbata ba. Dan gashi maƙiyansu da alamu suka nuna shirinsu bana yau bane sun gama cin nasara, nasara biyu a lokaci ɗaya, kaudashi da kaudata itama batare da ta san mi taci burin son sani ba. Sai ma sake tsunduma a duhuwa tayi. Dole ta kira gaɓar da suna duhuwa, dan tanada tambayoyi masu ɗunbin yawa akan kanta ma. Mafi girma a ciki sune taya Ajmaal ya zama Shahan-shan? Wake halaka matansa idan har ya kasance ba shi bane? Miyasa bai iya cewa komai bayan shine keda hakkin cewar? Da gaske ta rasa iyayensu suma da ɗan uwanta tilo daya rage kokuwa duk cikin shirin su Miran Arshaan ne?…. Shi kansa Sir Fawzan tana da bukatar sanin wani abu a kansa. Sai dai ta yaya? Ta wace hanya? Duk yanzu bata sani ba. Zafafan hawayen da a kwana ukun nan bata taɓa gwada sharewa ba suka sake zubowa masu zafi. Ta lumshe raunanan idanunta murmushi mai ciwo na suɓuce mata. Fuskarsa take kallo a kan allon zuciyarta a lokacin da yake sakar mata murmushin da har abada bazai taɓa zama mai gogewa ba a tarihinta. Siririyar dariya da tafin dake shiga kunnenta a bazata ya saka ɓacewar murmushin kan fuskar tata da buɗe lumsassun idanun nata lokaci guda..
Kanta ne ya sara da ƙarfi, da sauri ta maida su ta rumtse sakamakon hasken daya ratsasu mai kaifi, yau kwananta uku tana a cikin duhu, dolene karfin idanunta ya samu rauni a lokacin da aka samar da haske cikinsu. Duk yanda taso sake buɗewa ta kasa, dan har cikin kwakwalwarta taji shigar kaifin hasken na bazata. Ta cije lips a hankali tana mai ƙoƙarin ganin ta riƙe hawayenta da son danne tasirin raɗaɗin dariyar izgilancin da bata san daga wanda take fita ba. Sai dai zuciyarta na bata Miran Jasim ko Miran Arshaan ne. Bata da ƙarfin tashi daga kwancen da take, dan haka tai jarumtar sake buɗe idanun nata sannu a hankali a karo na biyu, zuciyarta na ambaton (Hasbinallahu wani’imal wakil). Da ƙyar ta iya tsaidasu akan Miran Jasim dake zaune ƙafa ɗaya kan ɗaya bisa kujerar da basai tayi wani tunani ba da ita aka shigo masa. Raɗaɗi idanun ke mata, gasu a kumbure jajur amma haka tai jarumtar cigaba da tsaidasu a kansa harya gaji dan kansa daga dariyar yay shiru..
_“Zawgatu al-ibn! (Daughter in-law) proud of you. Kin zama ta daban a cikin dubun da bazan so na manta ba. Duk da nima dai nasan ban cancanci ki manta ni ba ta sauƙi, na san na cancanci zama abin alfaharinki a yanzu. Cikin sauƙi na cika miki burinki, gaskiya na cancanci karɓar tukuyci na musamman. Koda yake kwantar da hankalinki bama sai kin bani komai ba, zamanki anan ma babban tukuyci ne. Zan sake faɗa “Ina al’fahari da ke”. Yay wata ƴar dariya mai ƙona zuciya dake shiga har ƙarƙashin zuciyar Iffah, amma kasancewar ta jarumar gaske mai ƙarfin zuciya sai batako motsa ba, raunanan idanunta kuma har lokacin suna a kansa duk da raɗaɗin azabar shigar haske dake ratsasu har yanzu. Dan kansa ya tsagaita da dariyar tare da gyara zamansa yana binta da wani shegen kallon ƙurulla har yana lasar lips ɗinsa kaɗan.
“Bana son ki kalleni da irin kallon da nake da yaƙinin shine a allon zuciyarki Zawgatu al-ibn!. Ina son ki dai fahimci ni ɗin mutum ne mai son kansa, zan kuma iya kauda koda yatsan hannuna ne in har zai iya zame min cikas domin samun cikar burina”. Yay wata ƴar dariya a zahiri, a can ƙasan ransa kam kallon da Iffahr ke masa ko ƙiftawa babu yay masa tsaye a kan allon zuciya, amma kasancewar sa gwani sai ya shanye babu alamun hakan a kan fuskarsa. Sai ma miƙewa yay cike da kasaita, a gabanta yaje ya tsugunna tare da kai hannunsa fari sol zai shafa fuskarta. Cikin wata irin zabura da ƙarfin da Iffah bata san yay ragowa a jikinta ba taja da baya tana watsa masa wani mummunan kallo har hucinta na bayyana akan hancinta. Murmushin gefen baki yay da lumshe idanu, sai kuma ya janye hannun nasa cikin ɗage kafaɗa da son basarwa. Idanun ya sake lumshewa da buɗewa a kanta yana shu’umin murmushin dake sukar zuciyar Iffah matuƙa. “Hakan ma ya burgeni Zawgatu al-ibn”.
Harara ta watsa masa kai kace idanun zasu faɗo, cikin kaushin muryar da ke fita da ƙyar ta fara magana a karo na farko cike da gargaɗi. “Kai fagalalle ka rubuta ka ajiye, a duk ranar da koda ɗan yatsan ka yay kuskuran taɓa jikina ni Fhareedah bint Zayyan na maka alƙawarin karyasa, karaya irin wadda har kabar duniya tabonta bazai goge a idanunka da zuciyarka ba. Iffah babban goro ce sai magogin ƙarfe”.
Tabbas maganarta ta matuƙar sukarsa, ta kuma zauna daram bisa zuciyarsa tamkar rubutu akan dutse, amma a zahiri sai ya murmusa harda lasar lips a karo na biyu. “Immm bazance kinyi ƙarya ba kam, nima shaida ne ke ɗin babban goro ce, kuma tabbas sai ni magogin ƙarfe. Ina miki albishir daga yau ki fara takaba da irga kwanakin zamowarki babban goro ta magogin ƙarfe ni Shahan-shan na ƙasar ruman Tajwar Jasim ibn Abdul-majeed Aliy! Nayi alkawarin sai na maidake karuwar da zata zama a ƙololuwar abin kwatance a duniya duka bama ƙasar ruman kawai ba. Daga yanzu kisa a ranki ƙaddararki ta fara a hannuna hhhh!!!”.
“hhahhaha!!!”.
Itama Iffah ta fara dariyar kamar yanda yake yi, sai dai tata cike da ƙarfin haline kawai. Tsagaitawa yayi da tasa yana kallonta cike da mamakin da yake ƙoƙarin dannewa, sai dai kuma fuskarsa na ƙoƙarin fallasa shi. Ganin bata da alamar tsagaita dariyar tata ya miƙe cikin zafin rai….
“Alfahari da ƙaddara akan Fareedah rauni ne ai Aam! Dan ƙaddarar itace hasken fitilar nasarar Iffah. Ƙyaƙyƙyawan mafarki Uncle”. Ta ƙare maganar da cigaba da dariyar da tafi ta farko saka ƙuna a zuciya.
Miran Jasim dake tsaye cak shi bai fitaba shi bai dawo ba yay wani irin cizar lips, sai kuma ya fice cikin zafin nama dan har ƙarƙashin ruhinsa dariyar Iffah ke shigarsa.. Sai da ta daina jin takun sawunsa gaba ɗaya da kulleta da aka sakeyi sannan ta tsagaita itama, a maimakon dariyar sai ta fashe da kuka mai tsuma zuciya. Ta tabbatar duk abinda Miran Jasim ya faɗa zai aikata mafiyinsa, sai dai ba tana kuka bane akan kanta, tana kuka ne a maimakon talakawan ƙasarta da Tajwar Eshaan bin Haysam Abdul-majeed. Tana kuka ne akan tsananin buƙatar son sanin zahirinsa da baɗininsa da su Miran Jasim suka zaburar da ita. Sai dai tasan guri ya ƙure, ƙurewa irin ta numfashi da ƙarewar rayuwa. Koda ace shi ya rayu ita bazata rayu ba, koda ace wasun sa na buƙatar ta rayu ita bata buƙatar rayuwar a halin yanzu………✍️
(ALLAH sarki Iffah 😭🙏).
*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*
*DAUDAR GORA Billyn abdul*
*KI KULANI hafsat xoxo*
*A RUBUCE TAKE Huguma*
*RUMBUN K’AYA Hafsat rano*
*IDON NERA Mamuh ghee*
_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_
_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_
_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_
_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_
_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_
_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_
_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_
ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN
MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171
SAI A TURA SHAIDAR BIYAN
09033181070
IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA
09166221261
*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*
+227 96 09 67 63
Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA
KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.
MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*
𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨
(𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)
𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (03)
……Kamar yanada Malikat Haseenat ta faɗa an sake tsaurara tsaro a ɗakin da Iffah take, bana dakaru kawai ba harda tarin jami’an tsaron da Shahan-shan kawai suke bama tsaro tako ina yayinda ta kasance cikin masu iya bibiyar komai kai tsaye. Shi kansa abincin da ake kai mata a yanzu ya kasance na musamman dake samun saka ido, dan a rana ta biyar da yunwa ta nema mata illa sai dai likita ya shiga ya dubata. Dan dole ta koma cin abincin sai dai bata wuce lauma uku ko kurɓa uku na madara take ta ajiyewa..
….A ɓangaren masu faɗa ajin masarauta ana ta cigaba da tattara bayanan da suka kamata ta hanyar bincike. Sai dai tsaiko na farko da aka fara samu shine rasa cctv footage na sashen Tajwar Eshaan da ga asubahin randa al’amarin zai faru har zuwa lokacin isar su Daneen Ammarah da su Miran Jasim sashen. Sai wayar Iffah da itama aka nema ƙasa da sama aka rasa da lap-top ɗinta. Wannan al’amari ma ya kawo ka-ce-na-ce bana wasa ba har takai jami’an tsaro cafke mai kula da ɗakin tsaron aka garƙame. Amma kuma juyin duniya yace bai san yanda akai ba. Hakama hadiman sashen Iffah kaf ɗinsu an tattare, suma kuma sun rantse sun kuma basu san yanda akai wayar Iffah da lap-top ɗin sukai ɓatan dabo ba. Ba kuma suga wani ya shigo sashen ba. Waɗan nan abubuwa na rashin makamar tabbatar da Iffah akan laifin da kowa keda yaƙinin ta aikata ya kawo rabuwar kai da rikici babban akan mata hukunci. Yayinda su Miran Jasim suka sha jinin jikinsu, dan haka suka zama ɓangaren masu nuna kawai a kashe Iffahn. Ɗayan sashen kuma da suka haɗa da zuri’ar Sayeed Khairul-Bashar suka bore akan bincike na har sai an tabbatar a kuma ji dalilinta dan in ma har ta aikata to dole akwai saka hannun wasu a masarautar.
Rikici ne bana wasa ba, dan har takai anyi wani zaman a karo na biyu amma sam babu masalaha daga kowane ɓangare. Ɓangaren kuma dake ganin kashe Iffahn shi yafi sauƙi sune ɓangare mafi ƙarfi dan da yawansu na jikin Tajwar Eshaan ɗin ne. Malikat Haseenat ce kawai ke nuna a dai cigaba da bincike kar a aikata aikin dana sani. Hakama Daneen Ammarah sam zuciyarta taƙi aminta Iffah zata aikata bisa raɗin kanta, idan ma har ita ta aikata ɗin kenan tunda har yanzu babu wata shaida dake nuna itace ɗin ta bashi madarar dan bayan ita suma masu dafa masa abinci da amintacen hadiminsa duk suna a rufe. Ƙulle-ƙullen su Miran Arshaan ne yasa dukan zargin yafi ƙarfi akan Iffah. A yanzu haka kuma sunyi kane-kane wajen sake rura al’amarin da nuna ɗaukar zafi fiye da kowa musamman Miran Jasim daya kasance mai riƙe da masarautar har zuwa samun lafiyar Tajwar Eshaan da ake fata…
★★…. ★…..
Har cikar kwanakin mako babu wani cikakken masalaha akan al’amarin, sai ma ɗaukar zafi da kowane ɓangare suka sake yi. Iffah kuma taƙi taɓuwa bisa jajircewar Malikat Haseenat na sai fa anyi bincike. Wannan kafiya ta saka Miran Jasim da Miran Arshaan kasa zaune da tsaye. Barbushi kuma ya tabbatar musu in har fa Malikat Haseenat na numfashi bazasu taɓa samun yanda suke so cikin sauƙi ba. Dan haka ya basu zaɓi biyu. Kodai su gaggauta kasheta da hanunsu, ko kuma suyi ƙoƙarin tunzura Malikat Bushirat dayin amfani da ita kamar yanda sukayi da Iffah ta kawar musu da ita. Hankalinsu ya tashi, dan kashe Malikat Haseenat abu ne ba ƙarami ba musamman a wannan gaɓar da take taka wata rawa mai banbanci da tasu duk da tafisu kusanci da Tajwar Eshaan. Duk yanda suka tattauna da aunawa sun gafa wannan hanyar mai wahala ce a gare su, dan haka suka zaɓi nufar sashen Malikat Bushirat ɗin domin fuskantar ta kai tsaye. Fatansu zaman ya zame musu jifan tsuntsu biyu da dutsi ɗaya, dan tunda aka fara rikicin nan Malikat Bushirat taƙi tofa komai ma, ta tattare hankalinta kacokan akan ganin lafiyar Tajwar Eshaan da aka hana kowa gani a masarautar sai ita da Malikat Haseenat har zuwa yau da ake cika kwanaki tara da faruwar komai…….
★… MALIKAT BUSHIRAT ★…
Yanda take magana cikin fitar ɗacin sauti tana kaikawo a fusace zai tabbatar maka ranta a ɓace yake ƙololuwa. Malikat Bushirat kenan da tun faruwar al’amarin nan babu wanda zaice yaji bakinta duk wannan sa toka sa ƙatsin da akeyi. A yanzu babban burinta bai wuce samun lafiyar tilon ɗan nata ba, batun hukunta wadda ta zama sanadin komai wato Iffah kuwa duk faɗi tashin da ake komai tana sane, sai dai bata shirya saka baki ba a yanzu acewarta akwai lokaci. A tsahon kwanakin nan dukkan wani motsin masarautar ruman a cikin kunenta yake fiye da masu kai kawon. Hauhawa da bunƙasar ɓacin ranta na yanzu kam yana da alaƙa ne da tattaunawar ta da su Miran Jasim, zaman nasu kuma kacokan ya alaƙantu ne ga hana hukunta Iffah da Malikat Haseenat tayi kai tsaye har sai anyi binciken da ta sharɗanta.
Irin wannan fusatar ga Malikat Bushirat shine fatansu, dan haka suka dubi juna cikin son danne murmushin kan fuskokinsu. Zama suka gyara tare da sake buɗe sabon shafin abinda suka faro. Miran Arshaan ya sake marairaice fuska mai cike da tsantsar damuwa yana mai duban Malikat Bushirat..
“… Ni a ganina ɓacin rai ko damuwa bashi ne zai zame mana mafita ba. Mu zauna mu tattauna yanda abinda ya dace kafin lokaci ya ƙure. Ban san miyasa Mammah ta ɗauka al’amarin nan da rashin muhimmanci ba. A yanda nake ji a zuciyata da tuni labarin wata akeyi ba yarinyar nan ba. Dan banga dalilin da zaisa ace wai sai anyi bincike za’ai mata hukunci bayan komai data aikata a bayyane yake, wannan tamkar muna nuna rashin muhimmancin ran yaronmu ne ma ai…..”
“Gaskiya kam Arshaan Akhi”. Miran Jasim ya tari numfashinsa da sauri, cikin nuna ɓacin rai shima ya cigaba da faɗin, “Ni kaina komai na kasa fahimta musamman akan ra’ayin Mammah. Sai nake ganin bata damu bane? Ko kuwa tafi son yarinyar sama da gudan jininta? Inba hakaba minene na waɗan nan sharaɗin marasa tushe? Bayan komai a bayyane yake. To gashi tace sai anyi bincike, amma dai-dai da cctv footage an nema an rasa tabbacin komai shiri ne. Inada yaƙinin komai sai dai yarinyar nan ta shirya kafin ta shigo masarautar nan. Dan binciken mu ya nuna ta aurensa ne dama domin ɗaukar fansar ƴan uwanta guda biyu, shiyyasa ta kwantar da kai ta shiga jikinsu musamman Mammah da Akia Ammarah da a yanzu suke nuna goyon bayansu kan cigaba da rayuwarta sai kace sun manta matsayin wanda taso halakawa a gare su…”
Maganganunsu sake hargitsa Malikat Bushirat suke da tunzurata. Tuni jin zafin Malikat Haseenat da tsanar Daneen Ammarah ya sake bunƙasa a ranta. Dama kullum Jasrah cikin munana Daneen Ammarah ɗin take a wajenta yanzu bisa huɗubar Miran Arshaan, dan tafi kawo mata zancen duk motsinsu a masarautar fiye da kowa, musamman daya kasance ra’ayinsu ya babanta da nasu akan hukunta Iffah. Yanda take sake kumbura jira suke kawai suji tace wani abu, amma kasancewar ta mace mai bahagon hali dama fahimta ko uffan da suke so bata tofa ba, sai cika take dai tana batsewarta ita ɗaya. Duk yanda suka cigaba da fanfatan kuma batace ɗin ba har lokacin samun damar ganin Tajwar Eshaan yay a gareta, dan tunda abin ya faru suma ɗin basu samu ganinsa ba kasancewar akwai doka mai haɗe da babban tsaro akan ganin nasa ga duk wanda ya kwana ya tashi a daular ta ruman, su kansu bisa tsayawar Malikat Bushirat ɗinne da itama sau ɗaya take da hurumin ganinsa a rana zasu ganshi yau ɗin.
Duk wani motsi da shiga da fitar jama’a a ƙarƙashin saka idon masu tsaron sashen yake a yanzun. Tako ina ka waiga cctv camaras ne. Su kansu ma’aikatan cikin sanya ido suke a kowane motsin tsakaninsu dan a yanzu kowa bai yarda da kowa ba ake. Sun sami tarba daga ƙwararren likitansa daya kasa ya tsare, yana hakane kuma bisa umarnin Malikat Bushirat ɗin. Cikin girmamawa ya gaidasu, batare da damuwa da yanda suka amsa masa cike da isa da ƙasaita ba ya jagorancesu zuwa ɗakin da aka warewa Tajwar Eshaan ɗin domin jiyya. Ɗakine tamkar asibiti, dan komai zaka samesa na aiki ingantattu da kowace ƙasa zata iya alfahari da shi. Dan ƙasar ruman na ɗaya daga cikin ƙasashe masu ƙwararrun likitoci da duniya ke alfahari da su tako wane fanni. Hakan yasa hatta shi kansa Shahan-shan dan yana ciwo bai ƙetare ƙasar haihuwarsa, kai sai ma dai su azo tasu ƙasar neman lafiyar saboda ingancin su….
Zaune yake a gadon marasa lafiyar bayansa jingine da tausasan filo da jikin gado da aka ɗago, duk da ya ɗanyi rama ƙyawun haibarsa da kwarjini na manne da cikar kamalar fuskarsa. Yayi fayau da shi da ƙara hasken daya bayyana bakin kwantacciyar sumar kansa data kumatunsa zuwa haɓa, light blue ɗin kayan jiyyar da suma suka ƙara fitar hasken fatar tasa tar-tar ga mai kallo sun masa ƙyau kamar ya saka ne domin ado. Sai manyan idanunsa da har yanzu fatarsu ke a ɗan kumbure alamar dai yana cikin halin jinya. Duk da jin an shigo bai motsa ba idanunsa nakan lap-top ɗin da yake sarrafawa cike da nutsuwa da ƙasaita.
Daga Miran Arshaan har Miran Jasim sukai turus alamar mamaki, dan sam zukatansu basu ayyana musu samunsa a haka ba musamman yanda likitansa yaƙi cewa komai game da zungurar da ƴan jarida ke masa akan son sanin halin da Tajwar Eshaan ɗin yake a yanzu. Saboda tun washe garin da suka tattauna da ƴan jarida basu sake cewa komai ba akan yanayin jikin nasa. Malikat Bushirat da hankalinta gaba ɗaya ke akan gudan jinin nata ta ƙarasa garesa fuskarta ƙawace da murmushi. Sai da taja kujera ta zauna a gefensa kaɗan ya ɗan ɗago saboda shigar ƙamshin turarenta cikin hancinsa…..✍️
*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*
*DAUDAR GORA Billyn abdul*
*KI KULANI hafsat xoxo*
*A RUBUCE TAKE Huguma*
*RUMBUN K’AYA Hafsat rano*
*IDON NERA Mamuh ghee*
_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_
_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_
_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_
_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_
_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_
_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_
_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_
ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

Leave a Comment