*Shimfiɗa…*
Akwai wasu ƙaddarorin da kan zo da wani irin duhu, wanda zai mamaye rayuwar ɗan adam, ta yanda ko da tafin hannunsa ba zai iya gani a cikin wannan duhun ba.
Kuma an ce HASKE ne kaɗai ke maganin duhu.
Ɗan adam kan shiga halin neman HASKEn da zai yi amfani da shi wurin gusar da wannan duhun dake bibiyar rayuwarsa.
Shin menene duhun?
Wasu tarin ƙaddarori ne waɗannan da ke tafe da matsanancin duhu?.
Shin a ina wannan HASKEn yake?
Sannan kuma menene wannan HASKEn?
*💡HASKE…💡*
_(Maganin duhu!)_
*©SALMA AHMAD ISAH*
TAURARI WRITER’S ASSOCIATION.
بسم الله الر حمن الر حيم*
*Page 01*
__(★★)__
*Shekara ta 2000.*
*Makoko, Lagos State, Nigeria.*
*01:40 Na dare.*
Wata matace ke tafe cikin sassarfa, sanye take da atamafa kalar ruwan goro, wanda akewa laƙabi da me dalma. Hannunta riƙe da wani abu, wanda ke duƙunƙune cikin zani.
Kanta ta ɗan ɗaga ta kalli sararin samaniya, ta ga yanda hadari yake gangamuwa, ga kuma iska me ƙarfi da aka fara, sai cida da tsawa da ake har da walƙiya.
Ƙafafuwanta ne suka taka birki, a lokacin da ta kawo gaɓar ruwan shiga yankin Makoko. Tarin kwale-kwalen dake bakin ruwan ta kalla, sannan ta kalli abun da ke hannunta. Hawaye na bin fuskarta ta girgiza kai tana faɗin.
“Ba zan iya aikata haka ba!”
Sai kuma ta shiga juyawa tana kallon kewayen wurin da take, babu kowa sai gilmawar karnuka. haka ta nufi wani kwale-kwale dake cikin tarin kwale-kwalen dake wurin, ta shiga cikin kwale-kwalen ba tare da tsoro ba, ta tsuganna tana aje abinda ke hannunta.
Kafin a hankali ta kai hannunta kan zanin, ta buɗe shi, nan take fuskar jaririya sabuwar haihuwa ta bayyana, don da alama yanzu ta zo duniya, saboda ko jinin haihuwarta bai bushe daga jikinta ba. Fuskar yarinyar ta ƙara rufewa da zanin, ta ɗora wata sarƙar ƙafa a kan zanin. Sannan ta miƙe ta fita daga cikin kwale-kwalen. Ta dawo ta bayansa, ta shiga turashi cikin ruwan, har ta samu nasarar turashi gaba ɗaya. A kan idonta kwale-kwalen ya shiga yawo a kan ruwan. Ya na nufar gidajen katakwayen dake saman ruwan. Sai da ta share ƙwallar idonta tukkuna, sannan ta juya da gudu ta bar wurin.
Ma somin ƙaddarar kenan, a ganinta ta kawo ƙarshen matsalolin, tun da har bata kashe jaririyar ba kamar yanda aka umarceta. Tun da har yarinyar ta yi nesa da gidan, wata ƙila komai zai ƙare.
Tana wannan tunanin ne ba tare da sanin cewa yanzu ne komai zai fara ba, dan kuwa barin yarinyar da ta yi a raye, shi ne musabbabbin buɗewar ƙofofinsu wasu tarin ƙaddararo da ko ita kanta bata san da aukuwarsu ba. Saboda ta kashe maciji ne batare da ta sare kansa ba. A yanzu ne komai zai fara!.
*Present day…*
*Shekara ta 2024.*
*Makoko, Lagos State, Nigeria.*
*06:30 na Safe.*
“Wai Shola ba za ki fito ki tafi wurin aiki ba?… Kin kusa makara fa!”
Cewar wata baƙar mata cikin harshen yarbanci, yayin da take zaune a kan dandaryar katakon da aka kafa ginin gidanta da shi. Daga can cikin ƙaramin ɗakin gidan, muryar wata matashiya ta bata amsa cikin faɗin.
“Takalmi nake sakawa Gigi!”
Matar ta girgiza kanta tana dawo da dubanta kan mijinta dake kwance a gefenta. Fuskarsa ta ɗan leƙa ganin idonsa a rufe, zatonta bacci yake. Amma a zahirin gaskiya ba baccin yake ba, idonsa biyu, tunanin rayuwa ne yasa shi a gaba.
Damuwar halin da gidansa ke ciki ita ce ta sako shi a gaba, ba dan ‘yarsa ɗaya Shola ta duƙufa wurin nemo kuɗin da zasu ci abinci ba, da tuni gidan nasu ya jima da durƙushewa. A da shi ne yake kula da gidan, amma tun bayan iftila’in hatsari da ya afka masa riƙon gidan nasa ya koma hannun ‘yarsa DIYA, wanda sukewa inkiya da SHOLA.
“Ga ni na fito”
Cewar Shola, bayan da ta fito daga tilon ɗakin gidan nasu, a tare suka dubeta, daga Gigin har mijinta da ya buɗe idonsa.
Sanye take cikin wani baƙin wando me faɗi, sai wata farar oxford shirt. Kanta yafe da baƙin gyale. Ƙafafunta sanye da fararen canvas da suka fara jin jiki. Wannan shi ne kayan da ta saba sakawa idan zata je wurin aiki. Fara ce sosai, tana da matsakaicin jiki, idan za ka mata adalci, a kallon farki idan ja mata za ka kirata da bafulatana.
Gigi ta yi murmushi.
“Ga guntuwar shinkafar jiya, ki ɗan taɓa kafin ki tafi”
Shola ta girgiza kanta tana sauƙowa daga kan mattattakalan katakon gidan nasu.
“A’a Gigi, ni idan na ci ku me za ku ci?, kawai ku ci, idan na je wurin aiki zan samu abun da zan ci”
Gigi ta miƙe tana fitowa daga gidan katakon nasu, ta tsaya kusa da Sholan dake kiran sunan Ekene, wanda yake zaune a gidan dake gaban nasu, dan ya zo ya fitar da ita bakin gaɓar ruwan unguwar tasu, dan ba’a zirga-zirga a unguwar sai da kwale-kwale.
“Ya kamata ki taɓa wani abun Shola”
Diya ta juyo ta kalleta.
“Karki damu da ni Gigi, ko biredi ne zan siya na ci, ke de ki kula, na bar miki ɗari biyar a ɗaki, wata ƙila za ku buƙace ta”
Gigi ta yi murmushi tana shafa kanta, tare da saka mata albarka.
“Shola ga ni”
Cewar Ekenen da take kira, bayan da ya fito daga ɗakinsu na katako.
“Na kusa makara Ekene! Ka zo ka fitar da ni”
Ta faɗi tana dubansa. Saida ya ɗaga busassun hannayensa ya yi miƙa, kafin ya sauƙe yana jan wata baƙar tsohuwar singlet da ke rataye a jikin wata gwafa ta gidansu. Sannan ya zagaya ta inda kwale-kwalensa yake, ya cinto shi daga jikin wani ƙarfe da ya ɗaureshi, sannan ya shiga yana ɗaukan marar kwale-kwalen, ya zagayo da shi har zuwa ƙofar gidansu Shola.
Shola ta yi wa Gigi sallama, sannan ta hau kwale-kwalen. Ekene ya fara tuƙasu. Diya ta ci gaba da kallon irin wahalar rayuwar da ake a yankin nasu. Kaf gidajen yankin na katako ne, kuma a saman ruwa suke, dan gaba ɗayan unguwar ma kanta malale take da ruwa, shi yasa ko ina zaka sai ka hau kwale-kwale.
Sosai ake shan wahalar rayuwa a yankin, yawancin mazaunan yankin masu zuwa cirani ne, sai ‘yan gudun hijara, da kuma wanda ƙaddara ta zama silar zuwansu wurin. Yankin nasu ya haɗa tarin ƙabulu, da kuma mutane masu mabanbanta halaye. Kowa ta kansa yake a wurin, babu ruwan wani da rayuwar gidan wani.
“Mun iso!”
Cewar Ekene, sanda suka iso bakin ruwan. A hankali ta miƙe, hannunta riƙe da jakarta. Godiya ta masa tana fita daga kwale-kwalen. Hanya ta yanka ta so ma tafiya. Kafin ta samu isowa tashar bus ɗin da ta saba hawa.
Tafiyar munti 55 ce ta kaita cikin Victoria Island. A wani bus stop suka tsaya, ta fito daga motar bus ɗin, tare da sauran mutanen da suka shiga motar. A ƙafa ta fara takawa, har ta iso Cactus restaurant. Wurin da take aikin raba abinci kenan.
Memakon ta shiga ta ƙofar gaba kamar yanda kowa ke shiga, sai ta zagaya zuwa backyard ɗin ginin restaurant ɗin, ta shiga ta ƙofar kitchen ɗin restaurant ɗin dake baya.
“Shola sai yanzu kika iso?”
Ɗaya daga cikin masu girkin wurin ta tambayeta, yayin da take ƙoƙarin saka apron ɗinta dake rataye a jikin wani hook. Zaren apron ɗin ta gama ɗaurawa tana faɗin.
“Eh Wallahi, sai yanzu na samu isowa”
“Diya! Diya!”
Tun daga nesa suke jiyowa muryar Orisa cikin ƙwalla kiran sunan Diya. Kafin Diyan ta amsa, Orisa ta bayyana a cikin kitchen ɗin.
“Wai ya aka yi kika makara?…. MD ya zo yana ta faɗa!”
Orisa ta faɗa mata cikin harshen yarbanci, Diyah ta saka jakarta cikin wata loka tana amsa mata da.
“Yau ban farka da wuri ba ne!”
“Lalle kam, ke har wani lokacin miƙe ƙafa ki yi bacci kika samu?”
Orisa ta tambaya. Diya ta miƙe tana kallonta.
“Orisa mutum idan be huta ba ai sai ya samu matsala, mu yini muna aiki mu koma gida kuma a ce ba za mu yi bacci ba?”
Orisa ta gyaɗa kanta.
“To yanzu dai ba zan ce za ku tsaya kuna yi ba. Ga wani plate ɗin brown spaghetti can, ki ɗauka ki kai teburi na sha takwas”
Cewar Ifunaya, shugabar sashensu na masu kaiwa abinci.
“Ok”
Diya ta amsa tana raɓa Orisa, plate ɗin brown spaghettin ta ɗauka ta ɗora a kan wani tray me kyau, ta nufi ƙofar shiga cikin restaurant ɗin.
Da misalin ƙarfe tara na dare ta kamo hanyar dawowa gida, bayan da ta tashi daga aiki, hannunta na dama riƙe da wata farar leda. Kafaɗarta kuma saƙale da jakarta. Kasancewar a yankin nasu ba ko ina ne me wutar nepa ba, yasa take amfani da hasken wayarta, wurin haska hanya.
Kuma har zuwa lokacin akwai sawun mutane a waje. Ranta ne ya ɓaci asanda ta iso bakin ruwan yankin nasu, ta iske babu masu yin fito, sai de tarin kwale-kwale a bakin wurin. Ga shi Ekene tsabar talauci da ya masa kanta ko waya ba shi da ita, bare ta kirashi dan ya zo ya fitar da ita.
Haka ta duba ɗaya daga cikin kwale-kwalen da ta san me shi, ta fara tura shi zuwa cikin ruwan, kafin ta ɗale ciki tana ɗaukan marar fiton sa, ta fara tuƙa kwale-kwalen.
Ganin hasken fitila kunne a tsohon gidansu da ya kusa durƙushewa ya sa ta fahimci cewar har yanzu basu kwanta ba. A kan matakalar katakon ƙofar gidan nasu na ƙarshe ta dire,sannan ta ɗaure kwale-kwalen a jikin wani ɗan katako dake jikin gidan nasu.
Sannan ta ɗebi kayanta da ta aje su a cikin jirgin, ta fara taku a hankali, saboda yanayin jimawar da katakon ginin gidan ya yi, ya sa ba sa taku da ƙarfi, dan abu kaɗan ne zai iya sawa ya karye, saboda wasu wuraren ma sun karye ɗin.
A tilon ɗakin nasu ta tarar da su, Gigi na zaune tana wa Papi firfita, sun kunna mosquito coil, sai wata dundurusun fitilarsu mara haske sosai dake ci. Ɗakin babu komai sai wasu lamitssatssun katifu guda biyu, dake yashe a ƙasan ɗakin, sai ‘yan wasu jakkukkunansu na kaya. Dan basu cika tara tarkace a ɗakin ba, gudun kada katakon gidan ya ɓalgace.
“Ba ku yi bacci ba?”
Ta tambaya tana cire viel ɗin jikinta, Gigi ta kalleta tana faɗin.
“Tukunna dai, zafi ne ya hana mu kwanciya”
Diya ta dawo bakin ƙofar ɗakin nasu, ta ɗauke labulen ɗakin, saboda iska ta ɗan samu ta shigo ciki. Ta dawo ta ɗauki kwandon soso da sabulunta, ta fita waje.
Ɗan siririn banɗakin gidan ta shiga, da wani ruwa rabin bokiti ta samu ta ɗan yi wanka, sannan ta fito, jikinta ɗaure da zani, ta dawo ɗakin ta saka wata doguwar rigarta. Sannan ta zauna kusa da Gigi, tana jan ledar da ta shigo da ita.
“Papi na samu kuɗin siyan maganinka, amma ɗaya aka samu, sai a yi maneji”
Papi ya kalli tilon ‘yar tasa, ƙwalla na shirin taruwa a idonsa, a shekarun da suka wuce ya tsinceta, shi ya kula da ita har girmanta, sai ga shi a yau ita ce take kula da shi, rayuwa kenan.
“Allah ya miki albarka Shola”
Ta sunkuyar da kanta tana amsa masa da amin.
“Yau me kuka ci da rana?”
Ta faɗi tana fitar da sauran kayan da ke cikin ledar, Gigi ta aje muficin hannunta tana faɗin.
“Taliya muka ci”
Robar da ta zubo sauran abincin da ya yi saura a restaurant ɗinsu ta fitar, dan idan abinci ya yi saura su ake rabawa.
“Ga abinci na zo da shi, Papi ka tashi sai ka ci”
Kansa ya girgiza mata.
“A’a Shola, ke da Giginki dai ku ci… Amma ni na ƙoshi”
Shola ta ɓata fuska.
“Idan baka ci ba ni ma ba zan ci ba”
Da sauri ya yunƙura ya zauna.
“Yi haƙuri to, zan ci”
Ta ɗan yi dariya tana kallon Gigi, Gigi ta yi murmushi tana shafa kanta.
Haka suka gama cin abincin tana basu labarin abubuwan da suka faru da ita yau a waje, wani abu da tun tana yarinya take yi, duk inda zata je ta dawo, sai ta basu labarin abun da ya faru da ita a wurin.
Ko da suka gama cin abincin sai ta ɗauki katafarta ta fita da ita rumfar ƙofar gidan nasu, ta shimfiɗata, ta kawo wani jemammen bedsheet ta shimfiɗa. Kafin ta kawo wani fatattakkakken net ta ɗaura. Ta shiga cikin shimfiɗar tata ta kwanta.
Tana hasashen yanda ranar gobe zata kasance, wannan ita ce rayuwar da take gudanarwa tare da iyayenta, rayuwar tasu me wahala ce, amma kuma suna cikin farinciki. Shekaru uku kenan da fara aikinta, kuma a shekaru ukun da suka wuce ne, Papi ya samu hatsarin mota, sannan tun lokacin ƙafarsa ta samu matsala. Har aka buƙaci wasu maƙudan kuɗe wurin mata aiki, Kasancewar basu da su, ya sa suka dawo gida suka zubawa saratar Allah ido.
Ganin zaman ba zai kaisu ba ya sa ita Diyan shiga cikin gari neman aiki, kuma cikin nasara ta samu, da shi ne suke iya rayuwa a yanzu.
A. ISAH CE✍️.
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*💡HASKE…💡️*
*©SALMA AHMAD ISAH*
TAURARI WRITER’S ASSOCIATION.
°°°
Akwai ɗaya daga cikin members ɗin gidan nan, da Allah ya yi wa mijinta rasuwa, ina so ku saka shi a addu’a, Allah ya ji ƙansa ya gafarta masa.
°°°
*Page 02*
~~~
*Coca-Cola Arena, Abu Dhabi, Dubai…*
_🎶When I look at you, I see a star, Shining bright, no matter where you are._
_My heart is full of love, it overflows,With you by my side, my joy it grows._
_Your beauty is like a work of art, My love for you comes straight from the heart._
_You’re my one and only, it’s plain to see, Forever yours, that’s how it will be.🎶_
Maƙaƙaren hall ɗin cike yake da mutane. Babu abinda ke tashi a wurin, sai sautin mutanen wurin, suna rera waƙar dake tashi a hall ɗin. Daga can kan stage kuma wani kyakkyawan matashi ne tsaye, sanye cikin baƙar T-shirt, da baƙin khaki trouser. A saman T-shirt ɗin kuma ya ɗora red bomber jacket. Hannunsa na dama riƙe da microphone, sassanyar muryarsa ce ke rera waƙar dake tashi cikin sifikun wurin.
A dai-dai lokacin da kiɗan waƙar ya sauya, a lokacin masoyansa dake wurin suka sa ihu, har da masu tsalle, wasu na ɗaukarsa a hoto, wasu video wasu na ɗaga takardu masu ɗauke da sunansa.
Yayin da shi kuma ya dage wajen ganin ya farantawa masoyansa ransu. Su ma kuma suna jin daɗin show ɗin na yau, dan burin ransu ne ya cika, yau gasu ga babban masoyinsu, yana rero musu daɗaɗan waƙoƙinsa, cikin nutsatsiya kuma sassanyar muryarsa.
Daga baya kuma sai sautin koran sunansa ya cika wurin. Cike da jin daɗi da kuma farin ciki ya tsaya yana kallon masoyan nasa.
“TAUQEER AGHA!”
*
Tsaye yake a gaban katangar glass ɗin dake a ɗakin hotel ɗin da ya sauƙa, idonsa manne kan kyawawan gine-ginen dake garin na Abu Dabhi, shi kansa garin yana masa kyau, musamman da daddare. Duk da ya je ya yi rawa a kan stage, ya yi waƙa, ya yi ihu, amma baya jin gajiya a jikinsa, dan zuwa gobe zai koma ƙasarsa ta gado, wato Nigeria.
Ƙaran wayarsa dake kan gado da ya ji ne ya sa shi waigawa. Sannan a hankali ya soma taku zuwa jikin gadon, ya kai hannunsa ya ɗauki wayar. ‘Umma’ shi ne sunan dake yawo a kan screen ɗin. Da wani ɗan guntun murmushi a kan fuskarsa ya ɗaga wayar. Sallama ya fara yi cikin daddaɗar muryarsa. Bayana an amsa masa sallamar ta cikin wayar kuma ya gaida matar cikin girmamawa.
“TAUQEER zuwa goben za ka dawo?”
Kansa ya gyaɗa a hankali yana juyawa.
“Insha-Allah Umma!”
“To Allah ya dawo da kai lafiya, Allah ya temaka”
“Amin”
Ya amsa yana sauƙe wayar daga kunnensa, dan wayar ta yanke, sumar kansa ya shafa daga gaba zuwa baya, yana fitar da wani hucin iska daga bakinsa.
A hankali ya zauna a bakin gadon yana jujjiya kansa, kafin a hankali ya kwanta a kan gadon, bacci yake san yi, amma kuma baccin ya ƙauracewa idonsa.
*Agha Mansion, No.854, Lekki pahse 1, Lagos State, Nigeria.*
Wani katafaren gida ne, wanda za’a iya kiransa da fada me zaman kanta, dan ko ginin gidan ya amsa sunan gida. Daga waje ma kawai gidan abun kallo ne, bare kuma ka saka ƙafarka a gate ɗin farko na gidan.
Tun daga kan maƙareren gate ɗin gidan, za ka fara cin karo da wata shimfiɗeɗiyyar kwalta, wadda zata sada ka da cikin gidan. Kyakkyawan garden ɗin gidan, shi ne a farkon gidan, kafin ka iske ainahin ƙofar shiga cikin gidan. Gidan ginin bene ne me hawa ɗaya.
Kai da ganin gidan ka san cewa wannan ya fi ƙarfin zaman mutum ɗaya, duk da ginin ba na yau ba ne, amma kayan da aka zube a cikinsa sabbbi ne, ‘yan ya yi, hakan ke nuna cewar mammallakan gidan na kula da shi yadda ya kamata.
Agha Mansion kenan. Gida ne na iyalin mutum ɗaya. Agha Muhammad shi ne ainahin tushen kafuwar ahalin. Shi da matarsa Fariya. Daga Agha har matarsa Fariya dukansu fulanin Yola ne.
Allah ya albarkacesu da yara shida: Faruq Agha, shi ne babba cikin ‘ya’yan nasu, shi ne mamallakim A. FOODS NIG LTD. Babban kamfanin da ya shahara a faɗin Nigeria, wurin sarrafawa da kuma shige da ficen kayan abinci.
Me bi masa kuma shi ne Mas’ud Agha, soja ne, me riƙe da muƙamin General.
Sai Tayyab Agha, shi kuma ya kasance likitan ƙashi, sannan ya mallaki asibiti tasa ta kansa.
Me bi masa shi ne Muzamil Agha, shi kuma ya bi sahun yayansa Faruq, dan tare suke kasuwancinsu.
Sai autarsu, kuma mace ɗaya tilo a cikinsu Abida, wadda ta yi aure, tun da jimawa. Kuma tana zaune a garin Abuja ita da mijinta da kuma yaranta.
Kuma duka waɗanan ahalin na zaune ne a cikin Agha Mansion. Domin kaf cikinsu babu wanda bai tara iyali ba.
Matar Faruq ɗaya, sunanta Maryam, yaran gidan kuma na kiranta da Umma, mace me kirki da sanin ya kamata, ga hange nesa, da jin ƙan talaka. Yaransa huɗu da ita, TAUQEER shi ne babba, suna masa inkiya da Junior, kasancewar ya ci sunan mahaifin Maryam ɗin ne. Sai Jamal. Me bi masa kuma ita ce Iqra, sai kuma autansu Aabis.
Mas’ud na da mata ɗaya shi ma, Hafiza shi ne sunanta, yaran na kiranta da Amma. ‘Yar halin ko in kula kenan, dan ita babu ruwanta da sabgar gidan, ko me za’a yi tana gefe, dan bata damu da kowa ba. Yaranta huɗu cas, haihuwarta ta farko ‘yan biyu ta haifa, Tajuddin da Saifuddin, sai kuma Muhammad, wanda sukewa inkiya da Hammad, sai auta Khabir.
Sau kuma Tayyab, matarsa ta farko sunanta Zayya, yaran gidan kuma na kiranta da mommy, Babban burin Zayya a duniya shi ne ta ga ta fi kowa, sam bata son a fita, shi ya sa komai nata da ban ne da na gidan, ta tsani ta ji an ce yau ga wani wanda ya ɗarata, kullum so take ta ji an ce ita ce on top. Haihuwarta ɗaya, ita ma bayan shafe shekaru masu yawa, Allah ya basu ita, sai matarsa ta biyu Rahila, wadda rana ɗaya aka wayi gari aka rasata ko sama ko ƙasa, ta yi ɓatan dawo, shi ya sa yanzu ‘ya ɗaya gareshi, DEENA.
Muzamil ma na da mata ɗaya, Rahama yaran gidan na kiranta da Mama, komai da ruwanka kenan, duk wata kurɗa-kurɗa ta gidan babu wadda Mama bata sani ba, ko labarin abun da ya faru a gidan kake nema idan ka tambayi Mama ka samu. Ko zance ake ba da ita ba za ka ji ta saka baki, duk dan de ta samu labarin bayarwa, babu zancen da ba zaka ji a bakinta ba, ita fa tsabar gulmarta, har dustbin ɗin gidan take zuwa ta duba, ko an ci wani abun a gidan bata sani ba.
Tana da yara uku, Nasir shi ne babba, sai Abdullahi da suke wa inkiya da Bobo, autar cikinsu kuma ita ce Nimra. Ba ma a cikin ‘ya’yan muzamil ɗin kawai ba, duka gidan ma Nimra ta fi kowa ƙananun shekaru.
Kaf cikin yaran gidan su goma sha biyu, huɗu daga cikinsu sojoji ne. Sojojin sun haɗa da; Saifuddin Mas’ud Agha, Tajuddin Mas’ud Agha, Jamal Faruq Agha, da Nasir Muzamil Agha.
Tauqeer kuma mawaƙi ne, wanda ya shahara a duniyar waƙa. Cikin gida da waje babu inda baya leƙawa dan harkar waƙarsa. Deena kuma actress ce, tana ɗaya daga cikin jaruman da ake ji da su a Nollywood.
Iqra da Hammad kuma suna University ne. Bobo da Khabir na secondary school. Yayin da Nimra da Aabis suke junior secondary school.
*
“Halima dan Allah ki gaggauta ku gama girkin nan, na san duk inda suke zuwa yanzu sun kusa ƙarasowa!”
Cewar Umma, yayin da take tsaye daga bakin ƙofar kitchen, tana duban masu aikin dafa abincin gidan. Halima shugabar madafan abincin ta risinar da kai tana amsa umarnin uwar gijiyar tasu.
Daga haka Umma ta baro kitchen ɗin ta nufo cikin falon gidan. Kai tsaye ɗakinta ta wuce.
“Wai ni me yake faruwa a gidan nan ne?”
Hammad da ya dawo daga makaranta ya tambaya yana zama a kan ɗaya daga cikin kujerun falon. Mama dake zaune tana sakatar haƙori ta gyara zama tana faɗin.
“Junior ne zai dawo yau”
Sai ya gyaɗa kansa yana buɗe wayarsa. Daga gefen Mama kuwa, Amma ce zaune tana latsa wayarta.
Daga can ɗayan ɓangaren na falon kuma Nimra, Aabis da Khabir ne ke home work. Yayin da Bobo ke zaune a kan kujera yana shirgawa cikinsa abinci, dan shi haka rayuwarsa take, shi da abinci five and six ne, rayuwarsa gaba ɗayanta ta tafi a kan cin abinci, shi ya sa ya haɗa wata uwar ƙiba. Tsabar ƙibar da ya yi cikinsa har zama yake a kan cinyarsa, ga luɓu-luɓu kumatu kamar yalo.
“Bobo! Kai ba za ka yi home work ɗin ba?”
Bobo ya sauƙe meat pie ɗin da yake shirin kaiwa bakinsa ya kalli setin inda Hammad ke tsaye. Kuma kafin ya amsa shi, Nimra ta yi caraf tace.
“Cewa ya yi ba zai yi ba, kuma yau ma sai da uncle math ya masa horo!”
Bobo ya juyo da kansa ya kalli Nimra cikin harar. Ba tare da ya ankara ba, Hammad ya warce plate ɗin meat pie ɗin dake hannunsa yana faɗin.
“Gara uwar ci, ka tashi ka je ka ɗauko jakarka ka yi home work ɗin ko sai na mammake ka?!”
Miƙewa ya yi yana cillawa Nimra kallon za mu haɗu ɗin nan. Tiɓi-tiɓi ya nufi tagwayen stairs ɗin dake falon, har wani nishi yake idan yana tafiya, tsabar yawan da ƙibar tasa ta masa.
Kakarsu da suke kira da Hajiya ce zaune a kan wata kujera, Iqra kuma na mata tausa.
“Kakus ki na da goro ne?”
Saif da ya fito daga kitchen, hannunsa riƙe da mug ya tambaya yana kallon kakarsu. Hajiya ta wurga masa harara.
“Da za ka zo kana tambayata ka siyo ka kawo min ne?”
Ta tambaya tana wurga masa wata harar.
“Ka ji ni da tsohuwa, daga tambaya?, sai cibo ya zama ƙari? Ƙari kuma ya zama ƙababa?. Inde maganar goro ce Allah ya baki haƙuri”
Ya faɗa yana shirin wucewa, sai kuma ta fito da goron daga cikin aljihun doguwar rigar jikinta tana faɗin.
“Zo ka karɓa ba dan halinka ba!”
“Bana ci!”
Ya faɗa ba tare da ya ko waigo ya kalleta ba. Hajiya ta taɓe bakinta tana maida goronta aljihu. Iqra ta musu dariya. Kusan kullum sun saba irin wannan faɗan, ita Hajiya saurin faɗa, shi kuma Saif zuciya.
“Bar ni haka ‘yar albarka”
Cewar Hajiyan tana janye ƙafarta daga hannun Iqran.
“Hajiya ai ni yau gani na yi ma ƙafar taki kamarta ƙara jagulewa”
Hajiya ta dudduba ƙafar tata tana faɗin.
“Ke de bari, wannan ja’irin yaron ne yake ƙara rikita min ita, sai ya zo ya yi ta jagula min ƙafa, wai a dole shi likitan ƙashi”
Iqra ta yi dariya tana miƙa mata kwajirinta, ganin tana shirin miƙewa.
“Dan girman Allah Taj ka dena taremana! Haba! Ka barmu mu yi kallon nan a tsinake mana!”
Cewar Nasir, ganin Taj ya hanasu su kalli film ɗin da suke kallo a tsinake, sai tare musu yake, wai film ɗin be yi kyau ba.
“Da waya zaunar da kai yace dole sai ka kalla? Idan ba ka so za ka iya tashi ka barmu mu kalla a tsinake!”
Nasir ya faɗi yana juyo da kan system ɗin gareshi.
Mommy da Deena ne suke sauƙowa daga kan stairs. Deena sai fara’a take, saboda dawowar masoyinta, farin cikinta, abun alfaharinta, wato Tauqeer, Mommyn ma sai kallonta take cike da alfahari kasancewarta ‘yarta.
Saif dake ƙoƙarin hawa stairs ɗin ya tsaya yana kallon irin shigar dake jikin Deena. Wata mini dolman dress ce a jikin nata. Tsala-tsalan singalilanta masu kama da tsinken kwakwa bayyane a waje. Ƙafarta sanye da wedge booties me ɗan karan tudu. Kanta kuwa ya ji kitson attachment ya ƙoshi, baƙar fuskarta ta sha make-up. Ita gata wayyayye.
Ya ja tsaki a ƙasan numfashinsa yana kallon gefe, dan tsabar takaici. Haka kowa ya bisu da kallo ita da Uwar tata har suka fita daga falon, dan ita Deena tace zata je ta ɗauko Tauqeer daga airport.
Hajiya da ta taso dan shiga ɗakinta ta tsaya a setin Saif tana dafa kafaɗarsa.
“Sai haƙuri Saifu”
Ta bashi haƙurin dan ta san abun da Deena ke yi na ɓata masa rai. Ba ma shi kaɗai ba, kowa dake gidan ba ya jin daɗin shigar da take.
“Hajiya abun nata ya yi hawa Wallahi. Kar ki ga hoton da ta yi posting a shafinta na Instagram last week. Hoton ya jawo cecekuce a social media. Babban abun da yake ɓata min rai shi ne kasancewarta a cikin ahalinmu!”
“To yaya za ayi Saifu? Dole a yi haƙuri, tun da ka ga ita ma jinin gidan nan ce, kuma da ma irin haka na faruwa, duk inda aka samu yawan ahali ana samun gurɓattattu kamar haka, ku de kawai ku tayata da addu’a”
Kasa cewa komai ya yi saboda takaici, ya wuce sama, sai da ya yi nadamar sauƙowa ƙasan, dan da ace be sauƙo ba, da ba zai zo ya ga wannan abun takaicin ba.
*Murtala Mohammed International airport, Lagos.*
TAUQEER FARUQ AGHA POV.
Cike da mutsuwa ya fito daga terminal. Sanye yake da wata farar long sleeve tees, sai farin wandon rigar, ƙafafunsa sanye da fararen sneakers. Kansa sanye da p-cap. Fuskarsa kuma rufe da mask, ya rufe fuskar tasa ne, saboda ba ya son takurawar jama’a, duk da kasancewarsa me nuna so da ƙauna ga masoyansa, amma yau a gajiye yake, ba ya son kowa ya gane shi. Kansa a ƙasa yake tafe. Yayinda duffle bag ɗinsa ke riƙe a hannunsa na dama.
Daga can nesa ya hangi Deena ita da securities ɗinta biyu, sai wani yauƙi take kamar kuɓewa. Ita ga celebrity. Kuma tun daga nesan ya iya gano kalar shigar dake jikinta, hakan ya sa ya ja tsaki yana kawar da kansa.
Yau shi banda ƙaddara ma me zai yi da wannan abar, dan ba dan an cusa masa ita ba, babu yanda za ayi mutum kamar shi ya yarda da aurenta. Tsabar rashin kunya irin ta Deena ita da kanta ta kaiwa iyayensu maganar tana sonsa, hakan yasa iyayensu maza suka tambaye shi; shin ya na sonta?, be san ya aka yi ba, amma haka ya ji bakinsa ya masa nauyi a lokacin, ya kasa amsa musu da a’a, dan ko da ace zai amsa to amsarsa za ta kasane a’a ce. A rayuwarsa ya tsani mace mara kamun kai, ita kuma Deena rashin kamun kai shi ne adonta.
“Laaa! Momy! Deena Agha!”
Cewar wata yarinya cike da ɗaukin ganin jarumar dake burgeta. Mahaifiyar yarinyar da suke tafe tare ta kalli wurin da Deenan ke tsaye, sannan tace.
“Mu je ku ɗuki hoto mana”
“Ki na ga za ta yarda?”
“Me zai hana? Je ki gwada”
Cike da ɗoki yarinyar ta isa wurin. Bakinta har bayan kunne. Securities ɗin ne suka fara dakatar da ita.
“Ke! Ina za ki?”
Ɗaya daga cikinsu ne ya daka mata tsawa cikin garjejeyar muryarsa. Hakan yasa yarinyar tsorata, har wayarta na faɗuwa ƙasa.
“Ku… Ku yi haƙuri… Hoto nake so na ɗauka da… Da Deena!”
A tare securities ɗin suka juya suka kalli Deena. Wadda ta sauƙe sun glasses ɗin idonta, tana watsawa matashiyar kallon banza.
“Na miki kama da wadda za ta yi hoto da ƙazama irin ki? Dallah malama ja ƙazamin jikinki ki bar nan wurin!”
Nan take ƙwalla ta sauƙo daga idon matashiyar, dan duk sai ta ji ra muzanta, shin lefi ne dan ta nunawa wanda take so soyyaya?.
Deena ta ci gaba da taunar chewing gum, rashin mutunci da kuma muzanta ɗan adam hallayarta ce tun tana yarinya, bata ganin kowa da gashi, in dai kai ba wani ba ne, to baka isheta kallo ba, ta tsani wanda bai isa ba, musamman ‘ya’yan talakawa, dan cewa take sun fiya tsiwa da iyawa, su ba ‘ya’yan uban kowa ba, sai shegen ji da kai.
Matashiyar ta share ƙwalla tana tsugunnawa dan ɗaukan wayarta. Ta kai hannun za ta ɗauki wayar, ta ga wani farin hannu ya rigata ɗaukan wayar. Hakan ya sa ta miƙe tana kallon mamallakim hannun.
Ko kafin zuciyarta ta faɗa mata cewar bata san shi ba, mutumin ya kai hannunsa ya cire mask ɗin fuskarsa. Idanuwanta ta zaro waje tana kallonsa, nan take ta nemi ƙwallar tata ta rasa, dan ganin babban masoyinta, wanda ya fi Deena matsayi a zuciyarta.
“Password?”
Wannan sassanyar muryaryar tasa ta tambaya yana buɗe wayarta.
“Ummm?”
Ta tambaya idonta a kansa, dan ta kasa gane ma’anar password ɗin.
“Ina nufin password ɗin wayarki”
Bakinta na rawa ta ƙifta idonta.
“4457”
Password ɗin ya buɗe, ya lalubo camerar cikin wayar, kafin ya shiga, ya matsa kusa da ita yana ɗaga wayar sama. Tsabar mamaki da farin cikin da take ciki, sai ta kasa kallon cameran, ta ci gaba da kallon fuskarsa, kuma a haka ya ɗauki hoton.
Ya sauƙe wayar yana miƙa mata, kamar wata doluwa haka ta ɗago da hannuta ta karɓi wayar. Ido ɗaya ya ƙifta mata yana murmushi, sannan ya barta tsaye da baki a sake.
Mask ɗinsa ya mayar yana murtike fuska, bayan da idonsa ya sauƙa a kan Deena, wadda ita kuma take masa nata murmushin, kansa ta iyo zata rungumeshi ya yi saurin dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu. Ba ta ji daɗin hakan ba kamar kullum, ita har yanzu gani take wayewar Tauqeer ta banza ce, tun da har ba ya irin halayenta. Duk wanda baya hallaya irin tata ganinsa take wawa.
Ya raɓata ya wuce ya nufi motar da ta zo da ita, ɗaya daga cikin securities ɗin ne ya buɗe masa motar, ya shiga ba tare da ya jirata ba. Haka ta zagayo ita ma ta shiga ta ɗayan ɓangaren. Kuma har suka kai gida bai ko ƙara kallonta ba, dan daga zarar ya kalleta sai ya ji kamar zunubi yake aikatawa.
A. ISAH CE✍️.
°°°°°°°°°°°°°°°°°
*💡HASKE…💡*
*©SALMA AHMAD ISAH*
TAURARI WRITER’S ASSOCIATION.
*Page 03*
~~~
*GrowTech. AI centre, No. 10, 23rd street, Astoria, NewYork, USA.*
Cikin sassarfa wani farin dattijon bature ke tafe, sanye yake cikin baƙar suit, bayan sa kuma biye da wasu matasa wanda yanayin biyyayar da suke masa ko a tafiyarsu ke nuna cewa shi ne gaba da su. Ganin kamar inda suke san nufa ya yi masa nisa ya sa dattijon fara gudu, hankali a tashe ya kutsa kai cikin babban ɗakin kula da computers na tsaron ma’aikatar.
“Sir! Sir!, All of our computers have been hacked by an unknown hacker!”
Cewar wata matashiya tana miƙewa tsaye daga kan kujrar da take. Cikin halin ruɗu, baturen ya kalli babban allon glass dake manne a jikin wata katanga dake ɗakin, wanda yake ƙunshe da hoton gaba ɗaya fuskokin computers ɗin ma’aikatar.
Kamar wanda be yarda da abun da idonsa ke gane masa ba, ya rarumi keyboard ɗin wata desktop dake wurin, ya shiga dannawa a kiɗime, idonsa manne da babban allon glass ɗin. Sai de kuma duk dannawar da yake a banza, don kuwa dannawar tasa bata hana madatsin na’urar kwasar bayanan da ya fara ba.
Ɗagowa ya yi daga kallon desktop ɗin, gumi na tsatssafo masa, hannu ya sa a aljihun suit ɗin jikinsa ya ɗauko hanki, sannan ya shiga goge gumin.
“Did ram RAM arrive today?”
Ya tambaya, idonsa na hango masa mafita a tare da bayyanar RAM ɗin ɓaro-ɓaro.
“No sir, he didn’t appear today” wannan macen ta amsa masa.
“Get in touch with him, now!”
*No.675, 361 Stagg Street, Brooklyn, New York, USA.*
Abu na farko da za ka farra kalla a ɗakin shi ne, computers, domin kuwa kusan computers biyar ne ke kunne a cikin ɗakin, haka zalika ɗakin babu haske sosai, sai na wata shuɗiyar fitila dake ci daga can wani ɓangare na ɗakin, idan kuma ka ci gaba da wilƙita idonka a ɗakin za ka iya hangowa ƙarafunan robot da ake haɗawa, wasu an haɗasu, wasu kuma ana kan haɗasu.
Daga can jikin wata babbar desktop kuma, wani matashi ne zaune kan kujera, ya jingina bayansa da kujerar, yayin da hannyensa biyu duka ke kan keyboard, kuma cikin sauri-sauri yake daddadanawa, sannan idonsa manne kan screen ɗin desktop ɗin, kai ka ce bai ma san madannan da yake dannawa ba. Hannyensa duka biyu na sanye da agogo. Sanye yake cikin wando jeans, da Oxford casual shirt a sama, kasancewar maɓallayen casual shirt ɗin ba a ɓalle suke ba, ya sa za ka iya ganin ash T-shirt ɗin dake ƙasanta. Sumar kansa na da tsayi sosai, don daga baya ta sauƙo har zuwa wuyansa, yayin da daga gaba kuma ta sauƙo kan goshinsa. Sumar kan nasa na da kyau da kuma santsi, don tsabar santsinta har wani kannaneɗewa take. Dogon gemun da ya tara a fuskarsa ne ya ɓoye fiye da rabin kammaninsa, idonsa sanye da farin glashi, yayin da gefen wuyansa ta ɓangaren dama, ke ɗauke da wani zanen baƙin tatto, wanda aka rubuta ‘RAM’.
“Feeq! Feeq!…”
Tun daga waje yake jin muryar sanyin idaniyarsa na kiran sunan, amma sai ya ƙi amsawa, dan gani yake kamar idan ya kauda idonsa daga kan screen ɗin na sakan ɗaya duk tarin tilin aikin da ya yi a ranar zai ruguje.
“Feeq!”
Ta kuma kira tana buɗo ƙofar ɗakin. Matar ta kalleshi tana girgiza kai.
“Wai ba ka ji ina ta kiranka?”
Ta faɗi tana duban bayansa. Ba tare da ya juyo ya kalleta ba, salihar muryarsa ta furta.
“Na ji Maa, wani abu nake son ƙarasawa”
“Ka aje abun da kake ka fito ko sai na ɓata maka rai?”
Ta tambaya ranta na shirin ɓaci. Kamar wanda aka cewa tana ganinsa, ya shagwaɓe fuska yana faɗin.
“Maa tun safe nake tsara sashen magana na AI humanoid robot ɗina, amma ban gama ba, Wallahi daga na gama zan fito”
“Kada Allah ya sa ka fito ka ci abincin, ai cikinka ne ba nawa ba!”
Ta ƙarashe tana rufowa ƙofar ɗakin. Ba dan ya so ba, haka ya dakatar da komai, sannan ya ɗaga hannyensa sama yana miƙa. A hankali cikin natsuwarsa ya miƙe tsaye, sannan ya nufi ƙofar balcony yana gyara rigarsa da ta tattare daga baya saboda zaman da ya sha.
A hankali ya buɗe ƙofar, sannan ya kutsa kai. Tsayawa ya yi a jikin ƙarfen balconyn, ya kafe windown ɗakinta da ido. Don ya san za ta iya fitowa a lokaci irin wannan. Kuma kamar da ya auna. A dai-dai lokacin, aka buɗe tagar gidan dake facing nasu. Sannan fuskar wata matashiya ta bayyana. Kallo ɗaya ya mata,zuciyarsa ta buga, kamar wadda take shirin fitowa daga allon ƙirjinsa.
Yawu ya haɗiya yana gyara tsayuwarsa, tare da duba agogon hannunsa na hagu, ganin bugun zuciyarsa ya ƙaru da kashi 5 ne ya sa ya sauƙe hannun ya ƙara maida dubansa kan tagar gidan. Zuwa lokacin ita ma ta fito zuwa nata balconyn. Kallonta ya ci gaba da yi, zuciyarsa na rawa.
Wata biyar da suka wuce ya fara ganinta, lokacin da ta kama wannan gidan dake kusa da nasu gidan, kuma tun a ganinsa na farko da ita zuciyarsa ta faɗa cikin wani irin yanayi mara fasaltuwa, shi kansa ba zai iya cewa ga abun da yake ji a kanta ba, amma de ya san a duk sanda zai ganta sai bugun zuciyarsa ya ƙaru…
Tunaninsa ya katse a sanda ta ɗago masa hannu tana murmushi, hannayensa ya sauƙe, waɗanda ke harɗe a ƙirjinsa ya ci gaba da kallonta yana murmushi.
“How is your day going?”
Ta tambaya cikin ɗaga murya, dan akwai ‘yar tazara a tsakanin gidajen nasu.
“Good, Alhamdulillah”
Sai ta gyaɗa kanta tana ƙare masa kallo. Ita dai kam yana burgeta, duk da ba ta taɓa ganin fuskarsa duka ba, saboda gemun da ya rufe masa rabin fuska, amma a haka kawai idan ka kalleshi za ka san cewa yana da kyau. Ita ba ta san ɗan wani ƙabila ba ne, amma yana mata kama da baƙaƙen indians, yanayin fatar jikinsa da take Chocolat color, da kuma sunar kansa da take da laushi ko a ido, shi ne yake sawa a kallon farko da mutum zai masa ya ɗauka cewar ba’indiye ne, duk da shi ba fari ba ne.
Jin ƙarar wani abu na tashi a ɗakinsa ya sa shi juyawa ya kalli ƙofar balconyn. Sai kuma ya juyo ya kalleta.
“Bye!”
Ya faɗi yana ɗaga mata hannu. Ita ma hannun ta ɗaga masa tana murmushi.
Ɗakin binciken nasa ya koma ya shiga duba computers ɗin nasa da yake da tabbacin sautin daga su yake fita. Daga cikin system ɗinsa sautin kiran ke tashi, dan haka ya zauna kan kujerar dake gabanta yana duba kiran. Duk da ya san babu me iya masa kutse kamar haka idan ba daga CrowTech ba, wato ma’aikatar da yake aiki, ya san cewa wata ƙila kiran wayarsa suka yi ba su samu ba, shi ya sa suka datsi na’urarsa don su aiko masa da kiran.
“Ram, ana buƙatarka a center, yanzu-yanzu!”
Abun da wani matashin bature ya faɗi kenan, bayan da Ram ɗin ya ɗaga kiran. Sai da ya ɗan juya kansa, sannan yace.
“Ok, on my way”
Ya faɗi yana katse kiran. Miƙewa ya yi, ya nufi inda backpack ɗinsa take, ya ɗauka, sannan ya saka laptop ɗinsa a ciki, ya goya a bayansa ya fita daga ɗakin. Ƙasa ya sauƙa, inda yake da tabbacin Maansa na can.
Ilai kuwa, Zaune ya sameta a kan kujerar danning tana cin abinci. Harara ta maka masa tana kawar da kai. Shi kuma sai ya mata murmushi yana takawa zuwa gareta. Peck ya mata akai yana zama kusa da ita.
“Ga ni na fito fa”
“Ina za ka je?”
Ta tanbaya ganinsa da jaka, ya ɗan yi shiru yana kallon abar son nasa. A kallo ɗaya idon ka musu za ka shaida wannan kalmar ta ‘dangantaka’ ita ce ke a tsakaninsu, duk da tarin gemun da ya rufe masa fuska bai hana kammaninsa da nata fitowa ba, banbancinsu ɗaya ne, kalar fatarsu, ita ta kasance fara ce sosai, yayin da shi kuma tasa take brown colour,kamar ta baƙaƙen indiyawa.
“Daga wurin aiki ne aka kirani, suna buƙatata”
Ya amsa mata yana ci gaba da kallon kyakkyawar fuskarta.
“Lami! Lami!”
Ta shiga ƙwala kiran Lami tana kallon ƙofar kitchen. Ram ya dafe kansa yana girgiza shi, be san yaushe Maan nasa za ta iya faɗin sunan robot ɗin dake girka musu abinci a gidan ba.
“Maa Kiyara,! Kiyara ne sunanta ba Lami ba”
Ya faɗa mata abun da ya saba faɗi a duk lokacin da ta yi rafkanuwa wurin kiran sun robot ɗin. Maa ta taɓe baki tana aje cup ɗin hannunta.
“Ni fa ba zan iya da wannan kiyare-kiyaren naku ba, na riga da na saba da sunan Lami, don haka Lami zan ce ehe…”
Ya yi murmushi yana tuno da Lami ɗin. Lami ta kasance ‘yar aikin da take taya Maa aiki a gidansu dake Nigeria, ta jima tana aiki a gidan,kafin suka kamata da lefin sata, shi ne suka sallameta, kuma bayan sun sallametan ne Ram ɗin ya haɗa mata Humanoid android robot, wada ya ƙirƙireta akan girki da gyaran gida kawai, kuma tun daga lokacin ita ce take girki a gidan, har zuwa yau. Ita kuma Maa ta riga da ta saba da kiran sunan Lami a duk sanda take buƙatar a mata wata hidima, shi ya sa ko bayan da ya ƙera Kiyara robot bata dena kiranta da sunan ba.
“Maa!”
Wata murya sak irin ta Maan ta faɗi daga kitchen, kafin suffar silver humanoid robot ɗin ta bayyana a gabansu, a yanayin jikinta macace, kasancewarta macen, amma kuma jikinta babu kaya, da zallarƙarfen silver kawai aka yita, yanayin ƙirarta irin mutum ce, tafiya ce kawai ba ta yi, sai wasu tayoyi da ya saka a ƙasan ƙafafunta. Kuma cikin tafiyarta ta tayar ta iso gabansu tana kallonsu.
“Ki sakawa Feeq abinci a filas, zai tafi wurin aiki”
“Ok Maa!”
Har ta juya Ram ya kirata, jin muryarta ta fito kamar ganga ta fashe.
“Kiyara wait”
Kiyara ta tsaya kana ta juyowa. Miƙewa ya yi ya isa gareta.
“Me ya samu muryarki?”
Kiyara ta ci gaba da kallonsa da idanuwanta da suka kasance haske kamar tocila.
“Sashen magana… Na jikina… Ne… Ya lalace!”
Ta faɗi muryarta na ƙara hargitsewa.
“Bolbo kawo min screwdriver!”
Ram ya ƙwalla kiran sunan. Bayan shuɗewar wasu sakkani, sai ga wani abu ya fito daga ɗaya daga cikin ƙofafin dake falon, abun de gajere ne, kuma ba normal tafiya yake ba, gangarawa yake a ƙasa kamar ball, a kallo ɗaya de ba za ka iya fasalta yanayin suffar abun ba. Tsayawa ya yi a kusa da Ram, sannan fitar da wani dogon abu me kama da hannu, ya miƙawa Ram screwdrivern da ya buƙata, Ram ya karɓa.
“Thanks Bolbo1”
“You got it, Ram!”
Muryar abun me kama da ta kiriku ta faɗi yana komawa ɗakin da ya fito daga cikinsa.
Ram ya zagaya zuwa bayan Kiyara, sannan ya danna wani switch a bayan nata. Nan take hasken idon Kiyaran ya ɗauke, kanta ya sunkuya ƙasa, saboda switching off ɗinta da ya yi. Wani murfi ya buɗe a bayanta, ya yi amfani da screwdrivern hannunsa ya gyara wurin da ya samu matsala a jikinta, ya mayar da murfin ya rufe, sannan ya danna switch.
“Hello Kiyara H178rs9Q12!”
Ya faɗi yana kallon fuskarta.
“Hey RAFEEQ AHMAD MUHAMMAD!”
Muryar Kiyara da ta dawo dai-dai ta faɗi. Ram ya yi murmushi yana aje screwdrivern a kan danning.
“Yi sauri ki kawomin abincin”
Kiyara ta juya a kan tayoyin ƙafarta, ta shiga kitchen. Jim kaɗan ta dawo ta kawo masa wani flask me ɗauke da abincin da ta girka a ranar, Ram ya karɓa yana mata godiya, sannan ya saka a backpack ɗinsa ya yiwa ma Maa sallama, ya fita.
A ƙofar entrance ya tsaya yana kallon kekensa dake ake a gefen ɗan ƙaramin compound ɗin gidan. Kasancewar keke yake hawa idan yana USA, dan motarsa tana Nigeria, jakarsa ya goya a bayansa, sannan ya isa wurin keken, ya ɗauka, ya buɗe ƙofa ya fice, ya hau kan titi ya fara tsuga gudu.
Kuma bai dakata ba sai da ya iso GrowTech, haɗɗaɗɗen kamfanin sarrafa na’ura me ƙwaƙwalwa, Kamfanin ƙirƙirar robot, kuma Centre ɗin AI (Artificial Intelligence) da ake ji da shi a kaf faɗin USA. Ginin kamfanin ya kasance na beni me hawa 13, yanayin kyan ginin kaɗai ya isa ya tabbatar maka da muhimmancin ma’aikatar.
A parking lot ɗin dake ƙasan kamfanin ya aje kekensa, sannan ya nufi ƙofar entrance. Yana tura ƙofar wani abu ya zo ya wuce ta saman kansa yiffff, hakan ya sa ya kaucewa abun yana binsa da kallo.
“My bad Ram!… Sorry!”
Muryar Henry dake riƙe da remote control ɗin drone ɗin ta faɗi yana kallonsa. Ram da ya juya yana kallon dron ɗin da ya wuce shi, ya juyo ya kalli Henry ɗin. Kafin ya sakar masa murmushi yana faɗin.
“Ba komai”
Kafin ya raɓa Henry ɗin ya wuce. Shi kansa reception ɗin ma’aikatar abun kallo ne, robotics da harkar AI ce kawai za ka yi ta gani a wurin iya ka ganin idonka. Ko da Ram ya isa elevator shiga ya yi, sannan ya danna hawa na 10, inda office ɗinsa yake.
“Kai tun ɗazu ake ta jiranka amma sai yanzu ka zo?”
Abu na farko da Abdulrahman babban abokinsa a ma’aikatar ya fara faɗi kenan lokacin da suka haɗu. Ram ya sosa wuyansa setin inda tattoo ɗin sunansa yake, sannan yace.
“Wai me yake faruwa ne?”
“Wani tantirin aka samu ya datsi babbar na’ura!”
Ram ya kalleshi na wasu ‘yan sakkani. To wai duk akan an datsi na’ura shi ne ya ga ma’aikatar ta rikice?, shi ai a nan bai ga abun tada hankali ba.
“Ram! Mr. Rafeeq!”
Aka ƙwala kiran sunayen biyu daga bayansu, hakan ya sa su duka suka kalli wurin, Isabella ce ta iso wurin tana ta haki saboda gudun da ta yi.
“Sir Thomas yana jiranka a control room”
Ta faɗi tana juyawa, ba tare da Ram da Abdulrahman sun ƙara cewa komai ba, suka bi bayanta har zuwa control room ɗin.
“Na gode Allah da ka zo Ram!”
Cewar Mr. Thomas yana kallon Ram ɗin da ya shigo wurin. Ram ya shiga bin ƙaton allon glass ɗin dake sama.
“Gaba ɗaya na’urorinmu aka datsa, sannan ana ɗaukar bayanan mu na sirri zuwa wata computerr”
Cewar Isabella, Ram ya ja kujera ya zauna yana sauƙe jakar bayansa.
“Dan Allah Ram ka san abun yi, sun kusa kwashe duka bayananmu”
Cewar Mr. Thomas hankali tashe. A nutse Ram ya fito da laptop ɗinsa dake cikin jaka, sannan ya aje ta akan wani table yana buɗeta. Danne-danne ya shiga yi yana duba allon glass ɗin nan. Kowa ya yi shiru, ana jiran ganin warwarewar matsalar, saboda tun da ha Ram ya zo, komai ya zo ƙarshe. Cikin abun da bai fi muntuna uku ba, ya cire wani flash drive daga jikin laptop ɗinsa ya miƙawa Isabella.
“Ki yi sauri ki saka a jikin babbar na’urar”
Ta karɓa da sauri tana nufar wurin babban system ɗin, buɗewa ta yi, sannan ta saka flash ɗin. Daga nan kuma sai kallon kowa ya koma kan babban allon glashin nan. Sakan ɗaya… Biyu… Uku…
A sakan na uku ne, komai ya tsaya cak, duka naurorin suka ɗauke. Mr. Thomas ya buɗe baki zai yi wa Ram magana, na’urorin suka kawo wuta. Komai ya dawo dai-dai, na’urorin suka dawo under control ɗinsu.
Sauran ma’aikatan wurin suka sa ihu, har da masu tafi. Ram ya miƙe yana rufe laptop ɗinsa. Mr. Thomas ya dafa kafaɗarsa cike da alfahari, don zai iya cewa kaf ma’aikatar tasu babu wanda ya kai Ram fasahar sanin kan na’ura me ƙwaƙwalwa, haka robot.
“Ina alfahari da kai Mr. Rafeeq”
Ram ya yi murmushi yana sosa gemunsa.
“Godiya nake”
“Kwana biyu na lura da baka zuwa, fatan dai lafiya?”
Mr. Thomas ya tambaya, a sanda suka fito daga control room ɗin. Ram ya gyara zaman backpack ɗin bayansa.
“Ka san ina tsara ɓangaren karɓar bayanai na AI humanoid robot ɗin nan nawa, shi ya sa ba na fitowa”
“Shi ya sa na ga ka tara gemu?”
Ram ya yi dariya yana shafa gemun nasa. A lokacin kuma Mr. Thomas ya tsaya, hakan ya sa Ram ɗin ma tsayawa suka fuskanci juna.
“Zuwa gobe baƙin da muke jira za su zo, sun ce za su zo su ga device ɗin, kuma suna so su yi testing ɗinsa, idan har ta musu za a iya ƙera musu wasunsu, dan haka ya kamata ka zo”
Ram ya gyaɗa kansa, don ya gane wasu mutanene za su zo ɗin, mutanen da saboda su aka ɗauko shi daga branch ɗin GrowTech na Nigeria aka kawoshi na USA, don kawai ya haɗa musu device ɗin ake amfani da shi yasa mota tuƙa kanta da kanta, wato self-driving car. Kuma a zamansa na wata huɗu da ya yi a garin, ya samu nasarar haɗa musu device ɗin da yake saka mota a self-driving mode, duk da ba shi ne karo na farko da ya fara ƙera device ɗin ba, saboda ko motarsa tqna tafiya a kan tsarin self-driving ne. Kuma yanzu shi ne masu kamfanin motar za su zo don su duba device ɗin.
“Sai goben”
Mr. Thomas ya faɗi yana miƙa masa hannu, alamun su gaisa, shi ma miƙa masa hannun ya yi, suka gaisa sannan ya juya yana kiran Abdulrahman.
*
RAFEEQ AHMAD MUHAMMAD, wanda aka fi sani da RAM haifaffen ƙasar Nigeria ne. A asalin sunan mahaifiyarsa shi ne Salamatu.
Salamatu ta kasance ɗaya daga cikin fulanin tashi na rigar Shariga. A cikin yawon kafa rigarsu ne suka sauƙa a wani daji dake kusa da garin Nguru dake jahar Yobe. Saida nono ya kasance sana’a ga duka matan aure da ‘yan matan rigar. Hakan ya sa bayan sun sauƙa a dajin suka fara kaiwa tallar nono cikin garin Nguru.
Kuma a nan ne Allah ya haɗa Salamatu da wani buzun Niger me sunan Ahmadu. Tun farkon haɗuwarta da shi ya sanar mata da cewar shi maraya ne, kuma ci rani shi ne abun da ya kawoshi ƙasar Nigeria. Kan ka ce me soyyaya me ƙarfi ta ƙullu tsakanin Salamatu da Ahmadu. Har ta kai ga Ahmadu ya fara mata zancen aure. Hakan ta sa Salamatu turashi zuwa ga mahaifinta.
Ahmadu da limamin masallacin unguwar Hausari da Ahmadun ya sauƙa a gidan dake maƙotaka da nasa suka shirya domin zuwa nemawa Ahmadu auren Salamatu ɗiyar fulanin rifar Shariga.
Ko da suka je ba su samu tarbar girmamawa dag mahaifin Salamatun ba, don korar kare ya musu, tare da faɗa musu cewar shi ba zai aura wa ‘yarsa kaɗo ba ma bare a je ga wata ƙabila da babu irinta a Nigeria wai su buzaye, don haka kada ya ƙara ganin ƙafarsu.
Haka Ahmadu da limamin nan me sunan Zakar suka kwaso ƙafafunsa gwiwoyi a sanyaye suka dawo Nguru. Ba don Ahmadu ya so ba, sai dan ya zame masa dole haka ya haƙura da soyyayar Salamatu, ya ci gaba da gudanar da sana’arsa ta kayan miya a kasuwar Nguru.
Kwatsam rana ɗaya sai ga Salamu a rumfar saida kayan miyan nasa, ganinta da kaya ba ƙaramin ɗaga masa hankali ya yi ba, ko da ya tambayeta me yake faruwa sai take sanar masa da cewar ita ta gudo daga rigarsu ne don su yi aure, a lokacin sai ya shiga yunƙurin ganar da ita kuskuren aikata hakan amma saboda soyyaya ta rufe mata ido sai ta nuna masa cewar ita fa ta riga da ta yanke hukunci, idan yana sonta su yi aure kawai, idan kuma ba ya sonta zata shiga duniya.
Gudun rasata ya sa ya amince da cewar za su yi auren, ya ɗauketa ya kaita gidan Kawu Zakar, sannan ya tsara masa halin da ake ciki, hatta da shi kansa kawu Zakar ɗin sai da ya yi ƙoƙarin ganin ya nunawa Salamatu kuskurenta, amma ta ƙi yarda da abun da yace.
Washe garin ranar da Salamatu ta gudo daga rigarsu, aka ɗaura aurenta da na Ahmadu, a ka sakata a gidan da Ahmadun ke haya, wanda yake kusa dana kawu Zakar. Tun kafin aurensu, Ahmadu ya riga da ya sanar mata da matsalar ciwon zuciya da yake fama da shi, wanda ya yi gadonsa daga wurin mahaifinsa.
Kuma bayan aurensu da shekara ɗaya ciwon nasa ya fara ƙamari, tun yanayin ciwon a tattafe, har ta kaishi ga kwanciya, a lokacin suna da shekara uku da aure, kuma a lokacin ta samu ciki. Bayan doguwar jinyar da ya yi fama a ita ta tsawon shekaru Allah ya amshi ran Ahmadu.
Ba ƙaramar damuwa mutuwarsa ta saka Salamatu ba, don har sai da aka bata gado a asibiti, ga tsohon cikinta haihuwa yau ko gobe, bayan an tasota daga asibitin, kawu Zakar yace ta dawo gidansa da zama. Ta ci gaba da zama da matarsa da kuma yaransa biyu. Bayan wasu wattani Salamatu ta haihu, ta haifo kyakkyawan yaronta na miji, wanda yake tsananin kama da ita, a lokacin sumar kansa ce kawai irin ta Ahmadu.
Bayan haihuwarta da wata uku, kawu Zakar ya tisata a gaba suka tafi zuwa rigar Shariga, domin ta je ta nemi yafiyar mahaifinta. Sai de kuma kash, sun makara, don kuwa ba su tarar da kowa a rigar ba sai wani mutu ɗaya, kuma shi ne ya sanar musu da cewar ai mahaifin Salamutu ya rasu shekara ɗaya baya, mahafiyarta kam da ma ta daɗe da rasuwa. Ƙawarta Dija ce kaɗai ta rage. Kuma sauran mutanen rigar sun tashi, ko shi ma ya saida wasu daga cikin shanunsa ne yana jiran a bashi kuɗin, daga an bashi zai bi bayansu. Amma kuma ya sanar musu da cewar mahafin Salamatun bai rasu ba sai da yace ya yafe mata. Haka Salamatu ta sha kukanta ta gode Allah, kafin ta ɗauki ɗanta ta bi kawu Zakar zuwa Nguru.
Haka ta ci gaba da zama a gidansa, tana renon ɗanta me suna Rafeeq. A lokacin da Rafeeq ya fara tasawa ta fuskanci cewar nauyi ya yiwa kawu Zakar yawa, hakan ya sa ta shiga yin sana’o’i da ban da ban, duk domin ganin goben ɗanta ta yi kyau.
Rafeeq na da shekara biyar a duniya suka fara fanin alamun ciwon mahaifinsa tare da shi, kawu Zakar da kansa ya ɗauke shi ya kaishi asibiti, kuma a asibitin ne suka sanar musu da cewar ciwon zuciya yake ɗauke da shi,wanda suke kyautata zaton gadarsa ya yi. Haka suka jera musu tarin ƙa’idojin da ya kamata ace sun kiyaye ganin ɗan nasu ya samu sauƙi, don babu batun warkewa gaba ɗaya a ciwon nasa.
Salamatu da Rafeeq ke kira da Maa tun yana yaro, ta ci gaba da fafutuka wurin ganin ɗanta Rafeeq ya taso cikin gata da kuma turba ta gari. Tun Rafeeq na ƙarami alamun baiwa da hazaƙarsu suka fara bayyana.
Domin shi ba kamar sauran yara gama gari yake ba, akwai shi da wata irin ƙwaƙwalwa me kaifi da kuma saurin haddace abu, ga shi da sanin makamar ƙirƙire ƙiren abubuwa. Yana ss2 a makaranta ya ƙera wani jirgin helicopter na kwali, hakan ya sa malaman makarantarsu suka ɗauki jirgin zuwa local government secretaria, daga nan ya tafi zuwa government house, kuma a nan ne aka saka sunansa a jerin ɗaliban da za su tafi ƙasar America domin yin karatun gaba da sakandire.
A lokacin ba ƙaramin farin ciki suka shiga ba shi da mahaifiyarsa, don Maa har da hawayenta. Bayan Rafeeq ya kamlla secondary kai tsaye ya wuce ƙasar USA domin ci gaba da karatunsa na matakin jami’a, inda ya fara karantar fannin mechatronics engineering. Kuma ko bayan da ya gama degree be dawo ba sai da ya haɗa da masters. Ko a lokacin da ya na Universityn babu wanda bai san RAFEEQ AHMAD MUHAMMAD ba, kuma tsabar ƙoƙarinsa da sanin kan computer ne ya sa aka laƙabamasa sunan RAM, wato (Random Access Memory), wasu kuma kan kirashi da sunan ne domin su rage yawan sunansa, don idan ka kira sunan nasa a taƙaice RAM ɗin zai baka. Ƙwazonsa da hazaƙarsa ne ya sa bayan ya kammala makarantar manyan kamfanonin ƙere-ƙeren robotics da na software suka riƙa kawo masa dammamaki na yin aiki a ƙarƙashinsu.
Amma haka ya toshe kunnensa ya nuna sam shi ba ya buƙatar zama a ƙasarsu, ya fi so ya koma tasa ƙasar,domin su amfana a baiwar da yake da ita. Su kuma sam ba sa so su yi asarar ɗan baiwa kamar sa, hakan ya sa wani kamfani me sunan ‘GrowTech’ da suke da branch a Nigeria suka ba shi aiki. Kuma sai suka yi sa’a ya karɓi aikin. Daga nan ya tattara nasa ya nasa ya antayo Nigeria.
Sosai Maa ta yi farin cikin ganin tilon ɗan nata bayan shafewar tsawon shekaru, don tun bayan tafiyarsa ko sau ɗaya bai leƙo gida ba. Satinsa biyu a garin Nguru, ya ɗauki Maa suka shilla garin Abuja, a inda branch ɗin GrowTech ɗin yake, kuma da kuɗaɗen da suka ba shi ya sai musu wani madaidaicin kyakkyawan gida.
Sai de kuma a sunane yake ya bar USA, don har wa yau idan wani aiki ya tashi sai ya koma can ya je ya yi, hakan ta sa a can ɗin ma ya siyi gidan da zasu riƙa zama idan sun sauƙa a can US ɗin.
________
_Kun dai ji yanda tafiyar ta soma_
_Kun tuna da RAM ma’aikaci a ƙarƙashin KULIYA da ZAID?_
_To shi ne wagga_
A. ISAH CE✍️.
08131549317
°°°°°°°°°°°°°°°°
*💡️HASKE…️💡*
*©SALMA AHMAD ISAH*
TAURARI WRITER’S ASSOCIATION.
*Page 04*
~~~
*Ƙauyen Wagini, Batsari local government, Katsina state, Nigeria.*
*07:00 na safe.*
A cikin wani madaidaicin gidan ƙasa, wanda ya ƙunshi ɗakuna huɗu, uku daga cikin gidan, ya yin da ɗaya ya kasance a soron gidan, wata farar mata da a ƙiyasin shekaru ba zata wuce shekara 44 ba, ta fito daga wani ɗaki ta na hama tare da miƙa, ɗankwalin kanta da ya since ta kai hannu tanan gyarawa, a lokancin da idonta ya. Kai kan tilon ‘yarta dake zaune a rumfar da suka saba girki tana hura wuta. A lokaci guda ta saki murmushi.
“SALAME!”
Ta kira sunaun tana kallonta. A hankali matashiyar ta juyo tana aje maficin hannunta.
“Har kin tashi Inna?… Ina kwana”
Matar ta ƙarasa. Kusa da rumfar tana amsa gaisuwarta.
“Yayanki ya dawo?”
Salame ta ɗauki maficin tana amsawa da.
“Eh to, na ji motsinsa sanda na fito, amma ban sani ba ko ya ƙara fita”
Inna ta juya ta kalli hanyar soro, kasancewar ɗakin yayan Salamen a soron yake.
“Audu! Audu!”
Ta ƙwala kiran sunan yayan Salamen.
“Na’am Inna, gani nan”
Suka ji muryar Audu ta faɗi daga soro, kafin kuma ya shigo cikin gidan, har ƙasa ya tsugunna yana gaida mahaifiyar tasu, sai da ta amsa shi, tukkuna ya miƙe tsaye.
“Hamma Audu ina kwana”
Salame ta. Faɗi tana duban yayanta, da murmushinsa yace.
“Lafiya ƙalau Salma… Fatan kin tashi lafiya?”
Ya kirata da sunanta na gaskiya, kamar yadda ya saba kiranta da shi. Amsashi ta yi tana ɗora tukuyar ɗumamen dake aje a gefenta a kan murhu.
“Yau Muja lafiya?, Dan ban ga ya je masallci ba”
Cewar Audu yana duban mahaifiyarsu.
“Ah-ah, bai je masallaci ba kuma?. Sai da na tasheshi fa”
Inna ta faɗi tana duban ƙofar ɗakinta, inda ta san autan nata na ciki yana bacci.
“Ai kuwa bai je masallaci ba”
“Mts! Ba ri na je na taso shi”
Ta faɗi tana nufar ɗikinta. Yayin da Audu kuma ya nufi ɗakin babansu dake wani sashi na gidan. Salame kuma ta ci gaba da firfita wutar murhun dake gabanta.
“Inna na yi sallah fa”
Cewar Mujan da Inna ta samu nasarar koro ƙeyarsa daga ɗakinta. Ya fito sai murza ido yake. Salame ta kalleshi.
“Banda ƙarya auta, na san ba ka yi sallahr nan ba fa”
Salamen ta faɗi tana ci gaba da dubansa. Kuma a lokacin Inna ta fito daga ɗakin, ta ɗaga carbin da ta saba lazimi da shi ta cauɗawa autan nata a bayansa tana faɗin.
“Ai Wallahi Muja sai kowa ya ji kan mu ni da Kai a cikin gidan nan, in dai a kan Sallah ne, sai na yi maganinka, saboda iskanci irin naka, na tasheka dan ka je ka yi sallahr sai ka koma ka kwanta dan ka raina ni?!”
Tun bayan da ta samu nasarar cauɗa masa carbin ya finciki buta ya shiga banɗaki da gudu. Salame da Audu me za su yi in ba dariya ba.
“Ah-ah, ke Dija! A kan me za ki dakar min jika da safiyar Allah ta’ala!”
Cewar kakarsu Iya Abu tana ɗage labulen ɗakinta, tare da leƙowa kanta.
“Sallah ce fa be yi ba ”
Salame ta bata amsa tana dariya. Iya Abu ta ƙarasa fitowa daga ɗakin tana yatsina fuska.
“Kuma dan be yi sallah ba shi ne zata dake shi? Ai har yanzu Mujahid yaro ne, da sauransa, sai ana ɗaga masa ƙafa”
“Ban da abunki Iya, Muja fa ya kai shekara goma, idan be fara yin salah tun daga yanzu ba sai yaushe kenan?”
Inna Dija ta tambaya. Iya Abu na bata amsa, Baba ya fito daga ɗakinsa yana kallon Audu dake tsaye a bakin ɗakin. Audu na dariya suka ƙara gaisawa da maihaifin nasu, kasancewar tare suka je sallahr asuba.
“Iya kuma ma fa na yi sallahr, masanllacin ne kawai ban je ba”
Muja ya faɗi yana fitowa daga banɗakin, sai cuno baki gaba yake.
“Zo nan ɗan jikkallena, ai na san za ka yi sallahr, su ne ba su sanka ba”
Iya Abu ta faɗi tana miƙa masa hannu, a ɗarare ya gifta Inna ya isa zuwa ga Iya Abu, duk kuwa da ya san ba lalle Innan ta sake dukansa ba, tun da ga Iya abu da Baba a wurin.
“Ka zo ka siyo mana koko a gidan Marka”
Cewar Inna tana miƙa ma ɗari biyu. Iya Abu ta kai hannu ta fisge kuɗi.
“Kai Sa’adu! Wai ni kai ne ka ɗaurewa Dija gindi take bautar mi da jika?”
Baba dake tsaye a ƙofar ɗakinsa ya girgiza kai.
“Ni a wa? Kare da gudun layya, Wallahi Iya ban san zancen ba”
Iya Abu ta yi ƙwafa.
“Ke Salame sai ki tashi ki je ki siyo kokon, jikana bai ƙoshi da bacci ba, dan haka zai koma”
Ta ƙara she tana miƙawa Salame kuɗin. Salame ta miƙe, ta ja hijabinta na yadin tayabo yalo, dake rataye a jikin igiyar shanya. Ta saka hijabin, sannan ta karɓi kuɗin. Ta fita tana dariya.
Tana fita daga gidan suka haɗu da ƙawarta Karime.
“Salame in zuwa haka?”
Salame ta tsaya tana kallonta.
“Siyan koko zan je, yanzu Iya Abu ta tada balli da sassafen nan, wai auta ba zai je siyan koko ba”
Karime ta yi dariya yayin da suka ci gaba da tafiya, dan ita ma gidan Markan ta nufa.
“Iya Abu hoo… Yau za ki je yin ice?”
Salame ta gyaɗa mata kai.
“Kin san yau ranar kasuwa, baba da hamma za su je kasuwa, shegiyar ƙiwar auta ba za ta barshi ya je daji ba, dan haka babu me zuwan sai ni…”
Haka suka ci gaba da hira har suka kai gidan Marka me koko. A tare suka dawo bayan sun sai kokon, Salame ta shiga gidansu, yayin da ita ma Karime ta wuce nasu gidan dake ɗan gaba da na su Salame.
________________
*11:04 na rana.*
“Zo ka raka ni auta”
Cewar Salame tana zura hijabinta dake riƙe a hannunta. Auta dake zaune yana haɗa dokin kara a tsakar gidan, ya ɗago da kansa ya kalleta.
“Ina?”
Ya tambaya.
“Yin ice”
Ta bashi amsa tana dubansa. Inna dake zaune a kan tabarma tana tsintar shinkafa ta dubesu tana faɗin.
“Ba tare da Karime kika ce zaku je ba?”
Salame ta dubeta.
“Eh, ina so na yi itacen da yawa, kin ga ai sai ya tayani da ɗauka ko?”
“Kuma haka ne”
Inna ta faɗa tana meda hankalinta kan tsintar da take.
“Ko ba zaka je ba?”
Salame ta tambaya ganin Mujan ba shi da niyyar miƙewa.
“Idan ba zai je ba kar ki takurashi mana”
Cewar Iya Abu da ta fito daga banɗaki, hannunt riƙe da buta.
“A’a, zan je”
Cewar Muja da ya miƙe tsaye. Salame ta sashi a gaba suka fita.
“Kukula fa Salame!”
Cewar Iya Abu.
“In Allah ya yarda!”
Salame ta amsa suna ficewa daga gidan. Sai da suka biya ta gidan su Karime, kafin suka nufi daji dan yin ice. Ko da suka iyo icen Muja be bar Salame ta ɗauka da kanta ba, duka ya loda a kansa yana faɗin.
“Muje Adda”
Salame ta yi murmushi, duk ƙiwar Muja a kan Salame ba ta aiki, dan zai iya yi wa kowa ƙiwa, amma ban da ita.
*Makoko, Lagos State, Nigeria.*
*06:44 na yamma.*
DIYA SHOLA POV.
Tana dawowa daga wurin aiki ta shiga wanka, bayan ta fito ta sauya kayanta, a ‘yar rumfar dake gaban gidansu ta iske Papi zaune a kan tabarma kamar kullum, ya miƙe ƙafarsa me lafiya, yayin da guntilalliyar ƙafar tasa ke nan a yanda take. Ɗaki ta shiga, inda ta iske Gigi tana zuba musu eba da stew ɗin da ta girka.
“Yauwwa Diya, zo ki miƙawa Ekene nasa”
Cewar Gigin tana miƙa mata kwanon dake ɗauke da anbincin Ekene. Shola ta saka ɗan ƙaramin farin hijanbin data saba sakawa, sannan ta ɗauki kwanon tana faɗin.
“O dara (To)”
Fita ta yi daga ɗankin, ta wuce Papi dake zaune a kan tabarma.
“Ina zaki je?”
Ya tambayeta.
“Ekene zan miƙawa abinci”
Ta amsa masa tana juyowa, kansa ya gyaɗa mata sannan ta juya ta tsaya a jikin rumfar gidan kwanan su Ekene ta shiga ƙwala masa kira.
Asalin sunan Ekene shi ne Musa, musulmi ne kuma ɗan ƙabilar igbo, haifaffen wani ƙauye ne dake can Enugu. Tun yana ƙarami iyayensa suka rasu, kuma ya girma ne a hannun wani kawunsa da matarsa da yasha wahala a wurinsu, bayan ya girma ne ya gudo daga ƙauyensu ya iyo garin lagos.
Kuma tun bayan zuwansa Makoko Allah ya haɗa jininsu da Gigi da kuma Diya, hakan tasa ya zama kamar ɗan gidan, dan har kwanan gobe ba shi da ‘yan uwan da suka wuce su Gigi, sai abokansa da suke kwana tare.
“Musa! Musa!…”
Shola ta kira sunansa na gaskiya, jin har yanzu bai amsa ba balle ya fito.
“Mu kin cika mana kunne da kiran Ekene, ni ba kya nema na?”
Diya ta juya ta kalli gidan dake manne da nasu, dan ta san muryar babbar ƙawarta ce, FA’IZA. Kuma kamar yanda ta sani, ita ɗin ce ta leƙo daga tagar ɗakinsu. Sai wani murmushi take mata.
“Ni ban sanki ba”
Cewar Diya cikin harshen yarbanci. Fa’ee ta wurgo mata harara.
“Wata gulma ce kuma ta sauya harshen?. Malama ina za ki min hausa ki min, ni bana san gulma ehe!”
Fa’ee ta ƙarashe tana ƙara manna mata harara. Shola ta yi murmushi.
“Wasa nake miki fa, ina nemanki Allah, ɗazu kafin na fita ma sai da na tambayi Mama ina kike, tace min wai kin je aiki”
Ta faɗi cikin harshen Hausa, kamar ita kaɗai ce yaran da ta iya.
Fa’iza ta fito daga ɗakinsu tana taka katakwayen da suka haɗa gidansu da na su Shola tana faɗin.
“Wallahi, kin san ogan namu ne ba sauƙi, kana kuskurewa zai seta maka hanya”
ta ƙarashe tana tsayawa a setinta.
“Wai ina Ekene ne?”
Fa’ee ta tambaya tana kallon ɗakinsu Ekene. Nan take fuskar Shola ta rikiɗa zuwa damuwa.
“Yau da safe ma fa banganshi ba, sai Oliver ne ya fitar da ni, ban sani ba ma ko ba shi da lafiya…”
Ta ɗan dakata da maganar, ganin Lamu abokin Ekene ya fito daga ɗakin kwanansu, fuskarsa ɗauke da damuwa yake dubansu.
“Lamu ina Ekene?”
Diya ta tambaya, ko kafin ya bata amsa, Gigi dake zaune a rumfa ta fito ta tsaya kusa da su hankali tashe, dan duk abun da suke faɗi tana ji, haka Papi ma kallonsu yake, dan ya ji me ke faruwa da Ekene.
Lamu ya sunkuyar da kansa yana sosa hannunsa. Sannan ya furta abun da ya zama sannadiyyar haɗuwarsu da dalilin sauyawar rayuwar ɗaya daga cikinsu.
“Jiya da daddare muna zaune a rumfarmu ta ‘yan fito, ‘yan sanda suka zo suka rufamu da duka, daga bisani kuma suka ɗauki Ekene suka tafida shi!”
Nan take kwanon Ebar dake hannun Diya ya suɓuce ya faɗo ƙasa. Bakinta a buɗe hankalinta a tashe take duban Lamu. Ita ta san cewa Ekene bai aikata wani lefin da za’a kamashi ba, dole abun da aka saba yi wa sauran matasan Makoko ne ya faɗa kansa.
Wannan abun sababbe ne a yankin Makoko, gurɓatattun ‘yan sanda dake kusa da yankin Makoko, kan karɓi cin hanci daga hannun manyan masu lefi idan sun kamasu, daga nan sai su sakesu, su zo yankin makoko su kama matasan yankin, sannan sun jefa musu lefin. To bana kuma kan ƙaninta abun ya faɗo?!.
*Agha Mansion, Lekki Phase 1, Lagos State, Nigeria.*
TAUQEER POV.
“You’re like a ray of sunshine, Brightening my every day… You’re like a breath of fresh air, Filling my lungs with glee… You’re like a warm summer breeze, Making me feel free… You’re like a song that never ends, Always making me grin… You’re my everything, my dear, The joy that I live in…”
Waƙar da yake rerawa kenan. Waƙar me sunan Sunshine, na ɗaya daga cikin waƙoƙinsa da ya fi so. Tsaye yake a jikin dressing mirror yana taje sumar kansa irin ta asalin fulani, wadda ba ta cika tsayi ba, kasancewar tana cikin askin buzz cut.
Sanye yake da khaki trouser milk color, da kuma baƙar T-shirt, me ɗauke da makeken hoton fuskarsa a gaba, daga ƙasan hoton fuskar tasa kuma sunansa ne a rubuce ‘TAUQEER AGHA’ yayin da bayan rigar kuma ke ɗauke da rubutun ‘GOAT’ (Wato Greatest Of All Time). Rigar na ɗaya daga cikin kayansa da ya fiso a duniya. Ba wai dan rigar na da tsada ba, sai dan matsayinta gareshi. Ɗaya daga cikin masoyansa daga ƙasar south Africa ne ya turo masa ita, ranar da ya ƙara yake wani Birthday partynsa. Hakan ya sa yake matuƙar son rigar.
Juyawa ya yi ya ɗauki wayarsa bayan da ya gama taje sumar tasa. Sannan ya fita daga ɗakinsa yana nufar babban falon gidan dake down stairs. Yana karyo kwanar da ɗakunan samarin gidan take ya hangi mahaifiyarsa ta fito daga ɗakinta, hannunta riƙe da kwalbar zuma. Wadda ya san a shayin mahaifinsa za’a saka shi. Dan a lokaci irin wannan, mahaifinsa da ƙannensa sukan zauna su sha shayi. Da sauri ya ƙarasa kusa da ita yana rungumarta ta baya.
“Ya kike? Habibty”
Ya faɗi yana sumbatar gefen fuskarta. Umma ta yi murmushi tana kallonsa yayin da ya saketa.
“Lafiyata ƙalau Junior, ya gajiyar hanya?”
“Gajiya ta bi jiki Habibty”
Ya amsa mata yana karɓar kwalbar hannunta. Tare da ita suka jero har suka sauƙo ƙasa, inda ya iske mutanen gidan gabaki ɗayansu nan zaune. Daga can wani ɓangare na falon iyanyensu maza ne ke zaune suna shan shanyi kamar yanda ya sani, yanyin da a ɗayan ɓangaren kuma, iyayensu mutane ke zaune, kowa yana sabgarsa, daga wani ɓangaren kuma gabaki ɗaya yaran gidan ne ke tasu sabgar. Ɓangaren da iyayensu maza suke ya nufa, yayin da Umma ta nufi inda matan gidan suke, dan daman a wurin take zaune, Abba ya mata magana kan ta ɗauko masa zuman da ya saba sakawa a tea.
“Ya kake Habiby?”
Tauqeer ya tambaya yana ma Abba side huge. Murmushi kwance a kan fuskar Abba ya amsa masa da.
“Lafiya Junior”
Abban ya amsa kamar yadda ya saba, kafin Tauqeer ɗin ya shiga gaisawa da kawunansa dake wurin.
“Daddy!”
Ya kira sunan Daddy da ɗan ƙarfi, ganin ya kirashi har sau biyu bai amsa ba, kuma dama can shi haka yake, sau tari za ka ganshi ya zauna ya yi shiru yana tunani, kuma hakan ya samo asali ne sakamakon ɓatan matarsa ta biyu.
Firgigit Alhaji Tayyab Agha ya dawo duniyar zahiri ya dubi Tauqeer. Da ƙyar ya ƙaƙalo murmushin yaƙe ya yafa a kan fuskarsa, kamar yadda ya saba jifan sauran jama’a da irin murmushin. Saboda murmushin kan tsaya a kan laɓɓansa ne kawai, dan tun bayan ɓatan matarsa Rahila ya shiga yin irin wannan rayuwar.
“Tauqeer!”
Ya faɗi yana kallonsa. Tauqeer ya girgiza kansa yana murmushi, hakan ba wai sabon abu ba ne game da kawunasa.
“Na’am Daddy”
“Ashe ka dawo?, ya Abu Dhabi?”
“Wallahi Baffa, yau da yamma na Samu isowa”
Baffan ya gyaɗa kansa yana ƙara yin nitso a cikin kogin tunanin da ya saba linƙaya. Alhaji Muzammil Agha ya girgiza kansa yana murmushi.
“Hamma kenan”
Ya faɗi yana aje newspapern dake hannnunsa. Tauqeer na murmushi ya miƙe zai bar ɓangren nasu, maganar Abba ta dakatar da shi.
“Junior”
“Na’am Habiby”
Ya amsa yana juyowa.
“Fatan Munira (matemakiyarsa) ta faɗa maka meeting ɗinka da kamfanin GU Industry a gobe?”
Tauqeer ya gyaɗa kansa.
“Eh, ɗazu take sanar da ni, kuma insha-Allah zan halarta…”
“Tauqeer! Ɗazu na duba jadawalin shige da ficen kaya na watanan, amma ban ga na satin nan ba, kuma Yahaya ya ce min an turawa kamfanin Almak kaya a satin nan”
Cewar Alhaji Muzamill Agha. Tauqeer ya gyaɗa kansa cikin faɗin.
“Eh, an tura musu kaya, kuma jiya aka sake sabon jadawali, ban san yaushe ka duba ba”
Muzamill Agha da yaran gidan ke kira da Baffa ya gyaɗa kansa yana so sa girarsa.
“Eh to da yake shekaran jiya na duba jadawalin, shi ya sa ban ga na satin nan ɗin ba”
Tauqeer ya gyaɗa kansa.
“An sake sabon jadawali, zan tura office ɗinka zu wa gobe”
“Ok sai na jika”
Baffa ya faɗa yana dubansa, Tauqeer ya juya ya barsu suka ci gaba da hirarsu da suka saba.
Daga nan inda iyayensu mata suke ya nufa, ya gaida su ɗaya bayan ɗaya, Hajiya Zayya ta amsa tana wani murmushi da ita kaɗai ta san na miye, Mama ta amsa baki washe kamar yanda ta saba, Amma kuwa kadaran kadahan ta amsa.
Ya miƙe ya bar sashen da suke yana nufar inda sauran ‘yan uwansa suke. Gaba ɗaya yaran gidan suna wurin, idan ka ɗauke Deena da dama can ita bata zama a cikinsu kamar kowa, sai Jamal da baya gidan, kusan sati biyu.
Kusa da Saif ya zauna suna gaisawa, saboda kaf gidan babu wanda jininsu ya haɗu sosai da shi kamar Saif ɗin, duk da tsaurin halin Saif ɗin da kowa ke ga a gidan, ba ya nunawa Tauqeer, dan sosai suke shiri da shi.
“Hamma Taj ka ga makin da na samu a Homework ɗina da aka yi marking yau!”
Cewar Nimra tana nunawa Taj littafinta. Taj ya aje wayar hannunsa yana karɓar littafin nata.
“La la la la! Ai kuwa kin yi ƙoƙari mutuniyar”
Nimra ta ƙyalƙyale da dariyar jin daɗi.
“Nawa ta samu?”
Hammad ya tambaya yana matsawa kusa da su. Taj ya karkata masa littafin yana bashi amsa da.
“7 a cikin 10”
Hammad ya karɓi littafin nata yana ci gaba da dubawa.
“Suuuuu! Yarinya ta ciyo ta bayan Ronaldo!”
Gaba ɗaya suka kwashe da dariya, dan sak irin abun da Ronaldo ɗin ke yi a duk sanda ya yi nasara a wasansa ya gwada.
“Kai fa Aabis?”
Tauqeer ya tambaya. Da gudunsa Aabis ɗin ya miƙa masa littafin. Kuma tun kafin ya duba abun da ya samu, Aabis ɗin yace.
“9 over 10!”
“Give me five my friend”
Tauqeer ya faɗi yana miƙa masa hannu, Aabis ya ɗaga nasa hannun suna tafawa.
“Miƙomin ni ma na gani”
Cewar Nasir yana miƙo masa hannu. Tauqeer ya miƙa masa littafin yana faɗin.
“Next time ina so ka cin ye duka. Ni na san me zan baka”
Ya ƙarashe yana duban Aabis ɗin.
“Omoh! Wannan yarinyar fa tana wuta!”
Cewar Iqra, a sanda ta gama duba littafin Nimra dake zaune a gefenta.
Saif ne ya lura da Bobo da Khabir dake zaune a gefe suna zazzara ido. Zamansa ya gyara yana aje mug ɗin hannunsa.
“Bobo, Khabir! Ina naku homework ɗin?”
Khabir ya haɗiye yawu, yayin da Bobo ya ci gaba da cin meat pie ɗin dake hannunsa.
“Ba ku ji me nace ba ne?”
Ya faɗi yana tsaresu da ido, tuni suka shiga taitayinsu, dan da ma kaf gidan babu me zafin rai irin na Saif, kuma halin nasa shi ne ya banbanta shi da Taj.
“Nawa ku ka samu?”
Hammad ya tambaya, a sanda hankalin kowa ya dawo kansu.
“Ni… Ni… Ni 4 na samu”
Khabir ya faɗa.
“Kai kuma fa?”
Taj ya tambayi Bobo.
“2 na samu”
“Aikin kenan ai, har gwanda Khabir a kan kai Bobo, ban da ci babu abun da ka iya!”
Bobo ya turo baki gaba yana aje meat pie ɗin hannunsa.
“To yanzu Hamma Saif idan mutum bai ci abinci ba me zai ci?”
“Za ka ci duka!”
Haka suka ci gaba da yi wa Khabir da Bobo faɗa a kan rashin meda hankalin da suke a kan karatunsu.
A dai-dai lokacin Deena ta fito daga kitchen, hannunta riƙe da wani bowl me ɗauke da vanilla yoghurt, ɗayan hannun nata riƙe da wayarta tana dannawa. Tana sanye da pyjamas. Kwatsam ta ci karo da mutum, hakan ya sa yoghurt ɗin dake hannunta zubewa a jikinta.
Nan take jikin ‘yar aikin gidan me suna Aliya ya shiga ɓari, dan ta san wata ƙila yau tata ta ƙare, har ƙasa ta tsugunna tana bata haƙuri, tuni ta fara hawaye.
“Dan Allah Madam ki yi haƙuri, ki yi haƙuri dan Allah, na yi ta kauce miki, ke ce kika bangaje ni!”
Deena ta kalli jikinta, sannan ta kalli Aliyan dake durƙushe a gabanta jikinta na kyarma, hannunta ta ɗaga ta sharara mata marin da ya sa Aliyan ɗaukewa wuta.
“Shashasha talakar banza, ke har kin isa ki goga jikinki da nawa? Waye ibanki a Lagos? ”
Aliya ta share ƙwalla tana miƙewa tsaye, hannunta dafe da kuncinta.
“Ki yi haƙuri Madam, amma Wallahi ke ce baki lura ba!…”
Hannunta ta ƙara ɗagawa za ta ƙara mata wani marin, ta ji an riƙe hannun nata, ta juyo a fusace ta fisge hannun nata. Cikin matsanancin ɓacin rai ta ci gaba da kallon Saif da ya riƙe mata hannu, dan a duniyar Allahr nan, babu wanda ta tsana kamar Saif ɗin, dan shi ne wanda yake shige mata hanci da ƙudundune.
“Kai waye da za ka riƙemun hannu, SAIFUDEEN MAS’UD AGHA?”
Ta kira cikakken sunan nasa kamar yadda ta saba. Saif ya shiga goge hannunsa yana faɗin.
“Ni ne ya kamata na tuhumi kaina da na riƙe hannun mace mara sanin darajar kanta irinki!”
Deena ta yi murmushi tana ci gaba da dubansa.
“Saifudeen Agha kai ba sa’an yin faɗana ba ne, dan haka ba ni da lokacin ɓatawa a kanka, ka bari sai ka kai stage ɗin da nake tukunna”
Ta juya tana shirin barin wurin.
“A haka za ki ƙare babu mijin aure!”
Abba ne ya daka masa tsawa cikin faɗin.
“Wata irin magana ce wannan Saif? A matsayinta na ‘yar uwarka kuma ƙanwarka ya zaka na faɗa mata haka? Memakon ka yi faɗa da duk wanda zai faɗa mata haka sai kai kana faɗa da kanka? Ku kenan kullum cikin faɗa kamar kaji!…”
Deena ko juyowa ba ta yi ba ta haye sama. Shi kuma Saif ya sunkuyar da kansa yana bawa Abba haƙuri.
Tauqeer dake zaune saɓanin sauran mutanen falon da suka miƙe tsaye tun bayan fara faɗan Deena da Saif ya dafe kansa, dan ya san da ma dole abun ya gangaro zuwa kansa. Damuwarsa biyu ce a duniya, auren Deena da baya so da kuma halin da ƙaninsa ke ciki!.
“Dare ya yi, kowa ya je ya nemi makwanci!”
Cewar Mas’ud Agha cike da umarni, ɗaya bayan ɗaya yaran suka shiga watsewa suna nufar ɗakunansu.
Sai da kowa ya watse a falon, sannan Hajiya Zayya da aka bari ita kaɗai, ta cije leɓenta na ƙasa tana jijjiga kai, dole ne ta yi wa tufkar hanci.
___________
_Hello!. Salmanians!_
_Shin da wa kuke ganin Fa’ee da Diya za su haɗu?_
_Kuma shin wani hali ƙanin Tauqeer wato Jamal ke ciki?_
_Me nene a ran wannan Hajjiya Zayyan?_
A. ISAH CE✍️.

Leave a Comment