Books Reviews & FAQs

Hatsabibin Tsibiri Hausa Novel

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

 

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

 

A lura dakyau – kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

 

Alura dakyau – manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

 

Alura da kyau – Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

 

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku

This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

 

Note that – we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

 

Note that – pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

 

Note that – our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT

 

This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[1/13, 12:05 AM] Mrsjmoon: HATSABIBIN TSIBIRI.
By Mrsjmoon.

Adabi Writer’s Association (AWA)

https://arewabooks.com/book?id=63a2e3d8821822a8402d8eb1

(Hatsabibin tsibiri kagaggen labari ne, ba’ayi shi dan wani ko wata ba in anci karo da abinda ya yi daidai da rayuwarka/ki alkalami ne ya zo da salon. Labarin zaiyi nutso ne cikin wata rayuwa mai ban al’ajabi na matsafa tare da wata ƙasaitacciyar masarauta da magajinsu ya shigo da salon da tun ginuwarta tayi hannun riga da lamarin. Duhu, Haske, Ƙarya,Gaskiya, Zalinci, Tausayi, Halarci,Butulci, Sadaukarwa, son mulki bakin rai bakin fama gami da tasirin riƙo da Addini duk na ƙunshe cikin tafiyar Mrsjmoon a cikin wannan labarin na Hatsabibin tsiri.

Ya Allah ka lamuncemin na rubuta abinda zai amfani al’umma. Allahumma Amin.

*Littafin baki dayansa sadaukarwa ce ga aminaina masu dubun karamci a gareni wato Khadija Candy da Rahma Kabir, Allahu ya ja wannan zumunta har zuwa gidan Aljanna mu zamo makwaftan juna Alfarman sayyidul sadati Manzon Allah S.A.W. Amin.*

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai, Allah ka karo dubun salatai marasa irga ga masoyinnan naka, shugaban Halittu baki ɗaya abin alfaharin salihan bayi, jagoran mabudin alkhairai, Abul Fad’imatul Zahra’u Sayyiduna Muhammadur Rasulullah S.A.W.

Page 01

Tekun Kabobo.

Teku ne mai faɗi da tsawo wanda ya ke cikin k’ungurmin dajin da ke yammacin Hatsabibin tsiri kuma gabashi da Masarautan birnin Mungaye.

Ruwan Tekun na da abin al’ajabi domin da safe zuwa rana kalansa blue ne amma idan marece ya shiga sai ya koma fari k’al wanda mai gani kan iya hango halittun da ke rayuwa a ƙasanshi na shawagi dan k’asansa na dauke da halittun da ke rayuwa a ruwa nau’ika daban daban, kama daga Kadoji, Kifaye da sauransu haka yashi da tsirrai koraye duk suna bayyana a fili ga duk wanda ke iya kawo ziyara da yamamcin.

Duk wannan girma da Tekun ke da shi gami da yawan ni’ima ya zamo hange daga nesa ga Fulani makiyaya domin basa iya isa gab’an shi balle tsautsayi ya kai dabbobinsu su shan ruwansa, hasalima basa biyo hanyar sai bisa makuwa inda suna farga da dimuwan da sukayi zasu sanja hanya tare da kare hanyar da dabbobin zasu isa zuwa gab’an Tekun domin jugewa samun asara dan duk wanda ya yi kuren isar bisashensa bakin Tekun zasu afka ciki tamkar waɗan da aka tura. Hatta da mafarauta ba kowa ke shiga dajin Tekun ya dawo lafiya ba sai in har ya kai kwaro wurin tsafi tamkar irin tsirarun jama’ar Hatsabibin Tsibiri. Sai kusan shekaru biyu da ya gabata Gimbiya Lina d’iya ga Sarki mai mulkin Hatsabiban Tsibiri ta maida Tekun muhallinta shi ya janyo matsafan sukayi nesa da Tekun domin girmama muradin mafi soyuwar Gimbiyarsu.

***
Guguwar iska ce ta turnik’e sararin samaniya dajin ya koma bak’ink’irin tamkar ruwan sama na daf da sauka domin ba sautin da ke tashi sai gunjin fitar iska wanda guguwar ta ke kad’awa da mugun k’arfi gami da tashin duk abin da taci karo da shi zuwa sararin samaniya, abin mamaki har da ƙananun duwatsu iskan sama ta ke yi da su tamkar ledoji. Ƙara gami da rugugi kawai ke tashi abinda ya haddasa rud’ewar tsun-tsayen da ke saman bishiyoyin da suka kewaye Tekun soma neman wurin tsira.

A daidai wannan lokacin Gimbiya Lina na zaune a saman ruwan Tekun Kabobo ta hard’e kafafunta saman kujera mai ruwan zuma tamkar ta hau saman dutse kamar yarda wurin da ta ke zaunen ya nuna babu alamun ruwa mai motsi balle igiyarshi ya wuce da ita ta zamo abin kalacin halittun ruwan.

Ga dai shi ruwan Tekun na tsiri gami da kumfa na gudu cikin murd’ewar igiyoyi sai dai kafin ya iso inda ta ke zaune ya ke sanja hanya ya zagayeta ya nausa gaba inda ke isa tsakiyar Tekun ya rufe dutsen da ke tsakiyarshi ruf zuwa wasu sakonni dutsen ya bayyana tamkar ruwan bai tab’eshi ba.

Murmushi ta saki cike da nishad’in ganin yarda ruwan Tekun ke wasanninsa, jin rugugin ya ƙi ƙararewa sai ta d’aga kai ta tsirawa sararin samaniyar ido na tsawon sekon goma sannan ta sauke kallonta kan fatar jikinta da ya ke bud’e ba sutura sai walwali ya ke yi cikin d’aukan ido tamkar jikin tarwad’a, sake kallon giragizan ta yi da suke k’ara yin duhu sai ta shafi fatar dantsen hannunta na hagu tare da kallon halittan k’irjinta masu ban sha’awa da cika domin ita kanta in ta kallesu suna burgeta saboda zubin da Allah ya yi musu na kyawu gami da jan hankalin duk wanda ya yi arba da su. Shafosu ta yi da hannun dama idanunta lumshe sumar idanunta na d’igar da ruwa na bin saman kuncinta. Girgiza kai ta yi sumar kanta ya yi tsiri sama ya fesar da ruwa sannan ya dawo ya rufe mata fuska zuwa saman k’irjin, ta yaye sumar da hannunta na hagu tare da sake kallon sararin samaniya a tak’aice ta kauda kai gefe cikin had’e fuska.

“Lima kenan, tabbas neman maganarki ya yi yawa, sam bakya son a zauna lafiya, kin addabi’a al’umma tsibiri kin kuma hanani watayawa a can, to ai shi kenan mu zuba mugani, domin jiya ba yau ba, Gimbiya Lina ta tumbatsa matuk’a, zata baki mamaki dan haka bari in nuna miki kaɗan ya ke Gimbiyar da bata kai a ambata mata sunar ba.”

Ta furta a hankali tare da jan tsaki mai sauti ta nuna guguwan da tafin hannunta wani haske ya soma fita daga tsakiyar hannunta na nufar iskan, aikam tamkar kiftarwar ido sai ga sararin samaniyar ya washe tangaras, ta sauke numfashi tare da share gumin da ya tsats-tsafo mata a saman goshi sai ta mike a saman ruwar ta yi nutso cikin Tekun, kujerar da take zaune ya zama walk’iya ya b’ace haka ruwan da ke sanja hanya a inda take zaune ya samu damar biyowa na kai da kawon shi.

Bak’ar tsun-tsuwa ce mai yarfin ja a fuska-fuskanta ta baiyana gefen Tekun zuwa can ta bud’e fuka-fukan ta soma shawagi a saman Tekun zuwa kimanin ‘yan mintoci sai ta zama bak’in hayak’i ta b’ace.

Gimbiya Lina da ta nutse cikin kogin sai da ta sami kimanin mintoci goma sha biyar sannan ta taso sama ta soma tafiya tamkar tana taka turb’aya dan yarda k’ura ke bin bayan takalmi idan ana tafiya a kan sa to haka ruwan ke tartsi na bin diga-digan Gimbiya Lina, wanda suke farare sol tamkar yarda fatar jikinta ya ke.

Tafiya ta keyi tamkar wacce ke filin gasar sarauniyar kyau dan cikin k’asaita ta ke takun abin da ya bawa mazaunanta da ke cikin siririn pant damar motsawa tamkar ba ita ce mamallakinsu ba dubi da yarda take mara k’iba su kuma gasu da fad’i gami da cika tare da fitar da shape na musanman tamkar wacce aka zana su a jikinta.

Ta yi tafiya har zuwa tsakiyar Tekun sannan ta tsaya jikin k’aton dutsen ta bud’e hannayenta tamkar walk’iya ta rikid’a zuwa balbela fara sol ta tashi sama zuwa wani tsauni da ke kusa da Tekun tana sauka ta yi girgiza ta dawo halittarta na Bil’adam ta yarfe yatsunta biyu saiga sutura ya baiyana a jikinta cikin shigar doguwar rigan yadin karan miski fari da ratsin ja tare da takalmin fata half cover mai launin Sarauta shima fari ta mik’a hannu jan gyale mai yarfin fari ya baiyana saman tafin hannunta ta nad’e kanta da shi ya zauna d’as, ta sake mik’a hannu kwalban turaren Company mai daraja mai suna LOST IN YOU ya baiyana ta fesa tare cilli da shi sama ya b’ace wani kwalban turare fari sol tamkar ruwa ya bayyana ta kai bakinta ta b’alle murfin ta kafa a bakinta ta shanye tas tare da cilli da kwalban ya zama walk’iya ya b’ace ta had’a hannayenta wuri d’aya ta manna a saman goshinta tare da kulle ido tana wani surutai saiga wata budurwa mai kama da ita sak tamkar an tsaga kara ta baiyana cikin shiga mai kamanni da nata, suka tsirawa juna ido kowa da karatun da ruhinsa ke kitsawa masa.

Gimbiya Lina ce ta kawo k’arshen shirun da cewa “Ba kya jin magana ko Lima? Shin wai har sai yaushe zan daina yi miki gargad’i akan shigomin yanki batare da neman izininta ba?”

“Baki isa ba Lina kuma bazaki tab’a isar ba, yankinki ko yankina? Ko kin manta ne in tuna miki? Ni ce mai k’arfin iko sama da ke dan haka kada ki sake yimin tsaurin ido domin zan hukuntaki tamkar uwar gijiya da baiwarta, dafatan kin tuna tazararmu da juna na sanin alkaliman sihiri.”

“Oh rigimar na ki ta nan ya b’ullo? To zan barmiki nan amma ki sani duk ranar da kika k’ara binciko inda na ke sai kin raina kanki domin yanzu ba da ba ne, na ga ba ya yi ga ba na baya kam sai tsintar hula sannan ina baki shawara ki koyi yarda ake magana da shugaba kada ki sami matsala nan ba da jimawa ba domin Gimbiya Lina ce gabanki sarauniyar Hatsabibin Tsibiri lokaci kaɗan mai zuwa.”

“Haka zalika nima Gimbiya Lima ce a gabanki wacce kowa na tsibiri ke tsoron karo da ita domin bata san wargiba aiki da cika ne takenta ko da kuwa ga jininta ne sannan magajiyar karagar Hatsabibin Tsibiri batare da wasi-wasi ba.”

“Na yaro kyau take bata karko amma bari in barki ki gama cika bakin naki sai ‘yar nanuniya ta nuna shugaban wani a tsakaninmu ba da jimawa.”

Dogon tsaki Lima ta ja tare da kaiwa kafadar Lina duka cikin cewa
“Ke dalla ni rufemin baki ki zauna ki sanarmin da inda kikayi b’atan dabo na tsawon shekara d’aya da rabi, kika barni da jidalin rabuwa biyu duk in Abun ya nemi ganinmu a lokaci d’aya domin bana son b’acin ranshi idan ya gano bakya Tsibiri zai iya sauke fushin a kaina.”

“Binciken ki ya bayyana miki inda na je tunda bazaki fita sabgata ba kamar yarda ba ruwana da naki sannan baruwana da fushin Abun dama Mah kika ce to na duba lamarin.”

“Idan kin isa ki cire hijabin da kika sanya a tafiyar naki kisha kallon tonon silili kamar yarda na tabbatar cikin jikinki da kika tafi da shi d’an kwanaki talatin da bakwai wanda kika b’oye haihuwarsa kuma fushin Abun ya dad’e bai dameki ba idan kinso kice ba shi ne makyen-kyashinki ba daga sama kika fad’o.”

Jim Lina ta yi tana kallon ‘yar uwarta zuwa can ta motsa labba ta ce “Lima sharrin da zakiyimin kena, na Haihuwa? A she tsanar naki har ya kai haka? Ni ce fa Linar da ta tsani ak’idarki na bilayi a gidan hutu, shin me yasa zaki jefeni da lamarin da kika san ban taɓa sha’awar aikatawa ba?”

Kinfi kowa sanin ban iya sharri ba domin abin da nake da tabbacin shi na kanyi zantuka a kansu sannan kin fi kowa sanin ina kan gaskiya, tabbas kin bar Tsibiri da ciki dan haka maza sanarmin ko ranki ya b’aci, yanzu na aikaki gaban Abun ba sutura ki fuskanci hukunci.”

“Zama bak’ar guguwar da kika zo a cikinsa ki b’acemin da gani ko in illataki sannan ki sani na wuce gaban barazanarki, jiya ba yau ba ce Lima na sake sanar da ke wannan kalman kuma ki saita harshenki kada ki fusatani na aikata miki abinda zai taɓa min domana ( rai).”

“Kome zakiyimin bazan kauce ba sai na san gaskiyan da kika b’oye kuma shi ne dalilin da yasa na rufa miki asiri ban sanarwa Abun labarin bakya cikin Tsibiri ba domin ina son na soma hukuntaki kafin ya yi miki
nashi.”

“Saboda na zama karyan maza irinki ba, mara yiwa kanta amfani?”

“Lina in magana kike son faɗamin kin makaro domin kaf sirrikanki a tafin hannuna suke dan haka ki biyoni mu koma tsibiri ko infasa kwai kowa ya san halin da kika kasance na yin cikin da baida sahihin uba sannan da ƙarfi akayi miki kika b’oye wanda yayi saboda kina yiwa jama’a bakin cikin samun ganimar jinin shi.”

“Ko yanzu lokaci bai k’ure miki ba maza tafi ki tona asirin domin ban shirya komawa Tsibiri yanzu ba ko wannan ganin da kikayimin wani dalili ya sanyani fitowa duniyar tsirrai dan haka yanzu zan koma dausayin sanyi na cigaba da rayuwa tare da hallitun ruwa masu amana.”

“Aikam kin gama komawa k’asan Tekun Kabobo Lina tunda ke ba aljanar ruwa bace haka ban san ta inda kika haɗa dangi da ‘yan ruwa ba.”

Dariya Lina ta bushe da shi tare da zama a saman wata kujera mai haske da ta bayya gabanta tamkar kiftarwar ido wanda haskenta ya kashewa Lima ido ta k’are da tafin hannunta tana ja baya, hannu Lina ta kai ta rik’o hasken tamkar igiya haka ya shige tafin hannunta sannan Lima ta samu damar dauke hannayenta daga saman fuskanta ta zubawa Lina ido wacce ke cin kayan lambu da suka bayya gareta cikin wani container mai d’aukan ido shima.

“Lina banda tsafi da muka gada kin koma ruwa biyu ce?”

Bata amsa ba illa murmushi da take dokawa cikin jijjiga kai.

“Wani Aljani kika samu ya baki sa’a irin wannan? Ko shi ne wanda ya yi miki cikin?”

“Lima idan baki daina ambatar cikin nan ba zan sab’a miki.”

“Zamu sab’awa juna dai Lina domin baki isa b’oyemin halin da kika fad’a ba kuma duk takunki ban k’yaleki sai kinyimin bayanin inda kika b’oye ko rayuka su b’aci.”

Kayan marmarin ta watso mata cikin fushi Lima ta yi sauri daga hannu suka tsaya cak batare da sun iso inda ta ke ba haka basu sauka k’asa ba. Numfashi su sauke a tare sannan suka ja baya ko wacce rai a haɗe zuwa can suka juya baya sannan suka juyo da makamai rik’e a hannunsu cikin gaggawa ko wacce ta nufi ‘yar uwanta da nufin halakawa. A ta ke k’azamin fad’a ya b’arke tsakaninsu, guguwa ya turnik’e ya rufesu ruf baka ganin kowa cikinsu sai fitar sautin takubba tare da walk’iyar hasken sukan da suke kaiwa juna. Bayan wucewar mintoci goma sha biyar sautin ya d’auke gami da washewar guguwar, wurin ya koma babu su sama ko ƙasa.

Takun ingarman doki ne ya ratso saman tsaunin da ya sanya itatuwar tsaunin soma fad’uwa ƙasa zuwa can wani gabjejen Sadauki ya bayya zaune a saman dokin ya iso ya tsaya a daidai wurin da Lina ta zauna yana bud’e k’ofofin hansa sai kuma ya diro ya shafi dutsen gefen da ta jingina da shi ya sunsuna ya soma waige-waige sai ya juya da hanzari sai ya kaiwa inda Lima ta tsaya duka sauti ya fita dum! Ya ja tsaki sai kuma ya zabura ya hau saman dokinsa ya nausa cikin tsaunin da mahaukacin gudu dokin na sakin haniniya wanda ya hargitsa k’ananun haluttun tsun-tsaye.

***
Lima ce ta soma bayyana jini na zuba a gefen kanta zuwa can itama Lina ta bayya dafe da kafad’arta jini na bin hannunta, a tare suka kalli juna ko wacce ta shafi inda taji ciwo a take ya koma babu alamun rauni suka sake kallon juna ko wacce taja tsaki tare da sauyawa zuwa halittar tsun-tsaye suka sula sararin samaniya.

Lina ta nufi kudu, Lima ta nufi yamma sai dai bayan wucewar mintoci uku Lima ta dawo saman tsaunin ta talli wata bishiya take ta tsage ta rabe biyu, ta bushe da dariya cikin cewa “Na san zaki dawo wurin nan Lina ni kuma na yi alk’awarin gano sirrinki tare da gano uban da yayi miki ciki kika b’oye bayyanarshi balle Kadojin kogin sihiri su sami abin kalaci kud’in shigar Tsibiri ya bunk’asa dan ina jiyowa da karfi ya ketaki sannan na yi alk’awarin bawa Kadoji jinin wannan mutumin domin barinsa a raye barazana ce ga lafiyar tsibirinmu mai dogon tarihi da ya barranta ga haik’ewa mata da ƙarfi.”

Tana ambatar hakan ta yi girgiza ta dawo yarinya karama cikin takun hawainiya ta isa gaban bishiyar da ta tsage ta shige ta koma ta kulle tamkar wani abu bai faru ba.

Daga can saman girgije Lina ta huro iskan bakinta zuwa kan bishiyar take kuwa ta b’ace b’at sannan ta sakko ta tsaya tare da kama k’ugu ta ce “Ni walkice daidai k’ugun kowa Lima, ki farka barci lafiya tare da mance kin ganni a zahiri domin nuna miki na wuce da saninki, yanzu ba da ba ce da kike shugabana a sanin alk’aluman sirihi da mugunta, ni yanzu shugabar kowa da ke HATSABIBIN TSIBIBI ne hatta kuwa da mahaifanmu nasha gabansu balle wancan basamuden banzan Buda wanda ke kan wahalar da kanshi, burina na daf da cika domin ba da jimawa ba zan kawo sauyi a tsibirinmu, Gimbiya Lina nan ta fe gareku ya ku jama’ar Hatsabibin tsibiri da samuwar cikar ‘yancin da kuke burin wanzuwar shi.”

Tana ambatar haka ta lula cikin girgije tamkar walk’iya bata sauka a ko ina ba sai saman Tekun Kabobo.

“Lina!”

Sautin kiran sunarta ya karad’e yankin bata waiwayo ba saboda ta gano muryan mai kiran nata sai kawai ta yi girgiza ta zama babban kifi ta yi nutso cikin Tekun daga can saman tsaunin Buda ya zaburi sihirtacce dokinsa ya daka tsalle zuwa cikin Tekun wanda yana fad’awa ruwan Tekun ya sanja kala zuwa launin yellow a maimakon fari k’al. Faruwar haka da seconds halittun cikin Tekun irin kifaye da kadoji suka soma fitowa suna yada zango a gefen Tekun wasu kuma na tseren hawa saman dutsen da ke tsakiyar Tekun.

A take kuwa Ruwan Tekun ya soma maik’o yana taruwa wuri d’aya tare da yin tsiri na feshi zuwa jikin bishiyoyin da ke kewaye da shi.

Mrsjmoon ce.

Ku daure ku buɗe Arewabooks👇

*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*

Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za’a cike Form ɗin kamar haka: –

*Enter your name:* (Cikakken sunanki)

*Enter your mail:* (Email ɗinki)

*Enter an username* (Sunanki)

*Enter your password:* ( misali 12341234)

*Confirm password:* (misali 12341234)

Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks.

*Continue with Google* – Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za’a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

*Register* – Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.
[1/13, 12:05 AM] Mrsjmoon: HATSABIBIN TSIBIBI
BY MRSJMOON

ADABI WRITER’S ASSOCIATION.
https://arewabooks.com/book?id=63a2e3d8821822a8402d8eb1 Follow me on Arewabooks.🖕

*Shafin sadaukarwa ce ga kafatanin member na Adabi Writer’s Association (AWA) Allah ya ƙara dankon kauna mara algus, Amin.*

Page 02

Juyi Lima ta yi cike da jin daɗin barcin sai ta jita a k’asa tim! daga saman gadon da ya ke da wani launi na daban da sauran gadajen da jama’a suka saba gani. A razane ta tashi zaune tana sosa bayanta cikin son tuno abin da ya faru amma ta kasa kamo komi tsaki taja ta dubi bangon d’akin tare da hura iskan bakinta sai ga Lina ta bayyana tana zabga murmushi yamutsa fuska ta yi tare da mik’ewa ta ja hannunta tana cewa “Nagaji da wannan wahalar narantse duk inda kike sai na nemoki domin hakan ya tauyemin jin dad’in rayuwata na tabbata Lina kin aikata min hakan ne dan murgunamin tare da hanani fita holewata amma duk ranar da na yi ido biyu da ke bazakiji da daɗi ba.”

Duk yarda taso jin basaja fushin da ke fuskanta ya koma irin murmushi fuskan fake Lina ta kasa saboda yau ta fusata sama da kullum, ga shi Abun bai nemeta ba taji son zuwa gareshi. Wani tsakin ta kuma ja tana dokawa dake Lima harara ita kam sai murmushi dake dokawa abinta.

“Wallahi ba dan rabi ruhina da ke nanne jikinki ba da yau na kasheki na huta.”

Gurnani tajiyo a bayanta ta juyo cike da masifa amma bataga komi sai sake jan tsaki zuciyarta na ƙara shiga ƙunci.

Fadar mahaifinsu ta nufa kai tsaye, tana shiga fadawan suka soma mik’o gaisuwa cike da tsoro ba wanda ta kula ganin haka suka watse aka barta da mai Tsibiri. Ta iso ta sunkuya gabanshi ya mik’a hannu zai dafata ta tashi da sauri tana dariya fake Lina da ke bayanta duk’e itama ta tashi tana dariyar girgiza kai Dattijon ya yi tare da kaiwa wani tulu duka a ta ke dake Lina ta nufi jikin Lima ta shige suka zama a bu d’aya, ya kalleta ta sunkuyar da kai ya nuna mata hanyar fita cikin fushi sai ta iso gabanshi ta zauna tare da kamo hannunshi.

“Kada kice komi Lima na jima da gano Lina bata wannan tsibirin sai dai tsawon lokacin na kasa gano inda ta b’oye duk da bincikena yana nunamin tana rayuwa cikin walwala da ‘yanci amma na kasa samun natsuwar ruhi akan inda ta ke da dalilin aikata mana wannan munafuncin sannan ina hango wani haske mai son maidani makaho a tare da ita amma a yau Buda ya gano mab’oyarta a k’asan Tekun Kabobo kamar yarda bincike ya bayyanarmin mintoci biyu kafin shigowarki, yanzu haka ina dakon isowarsu ne duk da ina shakkar isowar sa tare da ita.”

“Saboda me Abun kake shakka?”

“Lina ta soma bani tsoro da gaske ba wasi-wasi.”

“Abun me ya razanaka da ita haka, alhalin ko tsun-tsun Tsibiri bata iya kamawa saboda sokancinta da rashin amfani?”

“Kayya Lima, ki bi a sannu domin wannan sabuwar Lina ce mai cike da sadaukantaka ta fannoni da dama haka bincikena ya haskomi halin nan nata na tausayi shi ne zaiyi sanadin kawo k’arshen Hatsabibin Tsibiri mai dogon tarihi domin ba’a gina shi dan adalci da tausayi ga bak’i ba amma ita ce ta farko da zata shigo mana da sauyin da dole mu amsa kamar yarda taso yin nasara a baya.”

“Ta ina hakan zai sake faru Abun?”

“Ban sani ba Lima amma ina lalibo hakan a lokuta da dama tun kuwa kuna tsumman goyo shi Kaka Gunu ya keb’eki ya rik’a nuna miki sanin ilimin tsafi fiye da ita ya kuma raini ruhinki da rashin tausayi wanda kika rik’a wahalar da ita mahaifiyarku na yi miki kashedi kina watsi da kamarin saidai a yau na hango alamun ta samo sanin alk’aluman tsafi fiye da wanda kike tare da shi dan na kalli artabunku na d’azun duk da ta yi dubarar b’oyewa cikin iskan guguwa dan ta san zan gani sai amma ta makaro dan komi ya bayyana gareni tamkar kuna gabana.”

“Abun dama ba mafarki na yi na had’u da Lina ba har muka goge raini?”

“Eh ba mafarki ba ne, tabbaas kin had’u da Lina wanda hakan ya bawa Buda damar gano inda ta ke ta bayan b’atan dabon da ta yi na tsawon shekara d’aya da watanni ta hanyar jiyo k’amshinta wanda ta nan mafi akasarin jama’ar Tsibiri ke ganeku..”

“Abun me kake son sanar dani akan ‘yar uwata Lina?”

“Babu komi ‘yata illa hatsarin da Lina zata zame mana musanman ke domin zuciyarta ya ginu da tausayi ne ya yin da na ki ya ginu da tsabar mugunta, Kaka Gunu ya sanarmin d’abi’unki na kamanni da kakan-kakanninmu wanda shi ne silar samuwar Tsibirin nan wato Sarki Goma na farko.”

“Abun rabani da wannan zantukar gaibun na Kaka Gunu yanzu babban damuwata shi ne sanin gaskiyan abin da Lina ke b’oyewa.”

“Nafiki son gano lamarin da ta birne wanda bokayenmu suka kasa gano shi hatta kuwa da ni sarkinsu kuma jagorar wannan tsibiri.”

“Abun, shin yanzu Lina tafika k’arfin tsafi kenan?”

“Bata isa ba Lima.”

“To meye yasa ka kasa gyara Mata zama?”

“Har abada bazan tab’a fito na fito da ita ba saboda ina son ‘yata haka itama bazata tab’a yin gaba da gaba da ni ba domin girman da ta ke ganina da shi ya wuce tunaninki tana kawai nuna miki tafi damuwa da mahaifiyarku ce kamar yarda kika fi nuna damuwa da ni sannan zan baki aiki wanda na san akanshi kike wato na son gano lamarin Lima baki dayanshi na tsawon tafiyar da ta yi.”

“Ina saurarenka Abun.”

” ‘Yata Lima a yanzu nake son ki shiga bukkan Kaka Gunu kiyi wannan binciken.”

“Abun yau da kanka ka amince in shiga taskan sirrin Kaka Gunu wanda ya ke kulle tun bayan mutuwarshi?”

“Eh na baki damar shiga ya ke ‘yata, dama can gadonki ne dan ya tabbatar min ke kad’ai ya mincewa shiga bukkar amma bisa babban bincike shi yasa na baki umurnin shiga dan gano mana abin da Lina ta b’oye da kuma wanda ya koyar da ita dabarun ilimin sihirin da ya ke son doke wanda muka gada Kaka da kakanni.”

“To Abun kasan da wannan wasiccin ka barni ina ta wahala tsawon shekara d’aya da rabi akan wancan sokuwar yarinyar?.”

“Akul Lima! ‘yar uwarki ce bana son wannan tsanar da kike nuna mata wanda na yi imani shi ne silar b’oye miki sirrikanta ga shinan zai wahalar da ke a banza.”

“Abun bana sonta tunda Mah ta nuna da ita take yi ba ni ba.”

“Lima kin sanfa an raba ne ke ce nawa ita kuma na Mah ɗin ku.”

“Na barka lafiya Abun gobe da safe zan taho maka da bayanai wanda na amince tono sirrin Lina ce kaf d’inshi.”

Ta ambata tare da mik’ewa bayan ta subbaci bayan hannunshi.

“Baburdo ya taimakeki ‘yata.”

“A’a Abun ruhin Kaka Gunu ya bani sa’a zakace domin Baburdo Dodon gadin Tsibiri ne bai isa bani taimakon komi ba saima ni ce keyi masa alfarma na shaƙar ni’imar Tsibirin.”

“Haka ne Lima to ki fito lafiya cikin kiyayewar Ruhin Kaka Gunu.”

“Amin.”

Ta fice cikin sauri tana yarfe hannaye cikin salon mugunta inda yarfin ke fitar da iska na watsar da mutanen da duk ta ci karo da su a kan hanya wasu tsoffi ne da yara k’anana ya yin da masu ƙarfin tsafin ke kare kansu tun kafin ya iso inda suke, ganin jama’a na neman wurin buya saboda giftowarta sai tayi amfani da wuta da kunna a tsakiyar Tsibirin a take mutane suka soma kulle gidajensu masu sana’a suka tsere wutar ta soma bin kayansu tana lashewa, sai hakan ya wadata k’irjinta da nishad’i tayi ta zabga murmushi, batare da ta kula da illar da wutar takeyiwa jama’ar ba tayi gaba abinta tana dariya.

Ruwan ƙanƙara ne ya sauko a cikin minti ɗaya ya kashe wutar tare da ɗaukewa batare da sanin Lima ba hakan ya afku, jama’a suka dawo bakin kayansu suna tsinewa Lima a cikin zukatansu.

Tafiya mai tsayi Lima ta yi kafin ta isa bakin bukkan da ke cikin kogon wani dutse duk a saman Tsibirin.

WAIWAYE A DON TAFIYA.

*Asalin Tsibirin da mutanen da ke rayuwa a cikinsa.*

Hatsabibin Tsibiri, Tsibiri ne mai dogon tarihi domin sarakuna masu dama ne suka shud’e a cikinsa kuma dukkannunsu abisa turba d’aya suka ginu wato tsafi da kafurci domin basa da abin bauta balle wurin bauta, gasu nan dai kara zube domin ko Dodo Burda da ke TSIBIRIN basa bauta masa dan a mai gadi suka ajiyeshi ta hanyar yin bishara idan bak’o ya shigo ko samun wanda ya karya doka na yiwa mata fyad’e dan duk da wannan duhun da suke ciki suna kyamatar ketawa mata haddi.

Mafarin TSIBIRIN ya samu ne bisa jagorancin sarkin farko mai suna GOMA wanda aka ci shi da ya k’i inda ke mulkin al’uma masu yawa, sakamakon rashin nasarar da ya yi ne ya yi hijira da iyalansa ya yada zango a Tsibirin lokacin wurin sansanin miyagun namun daji ne da suka kashe dajin mafarauta da makiyaya suke tsoron haurowa samansa,.

Saukan sarki Goma ya sa suka koma gefen TSIBIRIN suka kewayeshi cikin yi masa mubaya’a domin k’arfin tsafinsa kad’ai ya isa zamowa bara zana ga rayukansu.

Sarki GOMA ya yi nasarasar k’awata TSIBIRIN cikin alk’aluman sihiri yarda kowa ya keto cikinta sai ya burgeshi kuma ya zamo ganimansa in ya so ya maidashi bawa in kuma ya so ya kasheshi musanman idan ya bincika yaga mai addini ne. A haka ya cigaba da shimfid’a mulkinsa tamkar yarda ya keyi a birninsa da yayo hijira sai dai ya k’ir-k’iro wasu ababe ya sanya su doka mai zaman kansa wanda d’aya da ga ciki shi ne sanadin yo hijiransa wato dokar ita ce ta hana mazaje haik’ewa Mataye wato yi musu fyad’e amma bai hana zinace-zinace ba abisa ra’ayin juna amma ayiwa mace da k’arfi wannan babban laifi ne domin duk wanda ya aikata hakan kafin macen ta kawo k’ararsa fadar Sarki Dodon Burda zai yi kuwwa mai razanarwa kuma a take kowa zai halarta gaban faɗar Sarki inda wanda ya aikata laifin zai fito da kansa tsirara mahunta lamarin su sanya takofi mai kaifi su datse masa al’aura tare da d’aukansa zuwa wata muguwar k’orama da Sarki GOMA ya k’irk’ireta na musaman domin hukunta masu laifi mai suna k’oranar sihiri, su jefashi ciki, wacce ba komi cikinta sai ruwa mai rai da lafiya tare da manyan Kadoji wanda abincinsu ya zamo manyan namun daji da mutane masu laifin aikata fyad’e da masu hayowa tsibirin dan ganin k’wam. Haka duk sarkin da ya hau sai ya k’ara inganta wurin da salon muguntarshi na daban inda kudin shigarshi zai sake ninka na sarkin da ya gabata.

Wannan doka na hana fyad’e Sarki Goma ya aiwatar da ita ce saboda ‘yarsa d’aya tilo wacce ya ke tsananin so da k’auna Gimbiya Aya da wani cikin jama’arsa ya yi.mata fyad’e lokacin da tafita shak’atawa bayan gari a sanadin ta rasa ranta sai gawarta aka kawo masa cikin jini babu kyan gani hankalinsa ya tashi ya bazama duban wanda ya aikata laifin sai ya baiyana d’an sarkin yak’insa ne ya aikata a ta ke ya sanya aka kamosa ya datse masa kai da hannunsa a bainar jam’a lamarin da ya haifar da k’azamin fad’a tsakaninsa da rundunar Sarkin yak’i inda Sarakunan da suke yammaci da na kudanci suka taho suka marawa Sarkin yak’in baya suka rufuma rundunar Sarki GOMA inda suka sami nasara akansa tunda ya fahimci kutunguilar da suka shirya na su sami nasara akansa su maidashi bawa sai ya silale da kafatanin ilalansa wanda suka had’a shi da matansa biyu da ‘yayansa biyar dukansu maza dama Aya ce d’iya mace tilo cikinsu. ‘Yayan ba wanda ya yi aure sai mutum d’aya wanda matarsa ke goyon jariran ‘yan biyu suma maza.

Cikin mabiyansa an sami wasu sun rufa masa baya sai ya sami nasarar tafiya da jama’a masu d’an yawa.

Dukkan kulawan Sarki Goma akan ‘yan biyun nan ne har suka samu isowa HATSABIBIN TSIBIRIN da yaga dacewar ya zamo fadarsa amma akan hanya ya yo fashin zuk’a-zuk’an ‘yan mata guda biyar wanda suma sukayo gudun hijira bisa jagorancin wani Sadaukin mayak’i inda ya amince zai tserar da su amma bisa sharad’in zasu zama matarsa a take kuwa suka amince shi ne ya biyo hanya da su bisa gudunmowar alk’aluman tsafi sai kuma ya yi rashin sa’a ya gamu da tawagar Sarkin GOMA ya ritsashi ya kasheshi ya kwashe ‘yan matan inda ya mallakawa ‘yayansa suka angwance a lokaci d’aya bayan kammaluwar gyaran Tsibirin wanda ya bashi suna da HATSABIBIN TSIBIBI domin bak’o bai tab’a shigowa TSIBIRIN ya fita ba fa ce wannan Dodon ya kamoshi ya bawa wad’an nan Kadoji sunyi watanda da Naman shi ko a maidashi bawa daga bisani ya zamo dan Tsibirin na har abada ya manta da Asalinsa balle burin komawa garesu. Wannan zalincin yasa mafarauta da sauran ma’abota shiga daji basa bin ko gefen TSIBIRIN duk kuwa sonsu da yankin saboda ababen tsoratarwa dake kewaye da Tsibirin yafi ƙarfin ji da ganinsu har gara kafin bayyanar Sarki Goma sukanyi shiri na musanman su hau, yanzu kam ba wanda ya san yarda TSIBIRIN ya koma balle ya bada labari dan duk wanda zai bada labarin an halakashi ko ya zama ganimar Tsibiri.

Leave a Comment