IBTISSAM
( Heart touching story of love and destiny)
Story & written
By
Mss Lee
Littafina na kudi ne akan 500 kacal , banyarda wani yayi an fani da wani bangarena littafina ba, duk Wanda labarina yazo Daidai da wani abu na rayuwarshi a rashin sani ne.
🫧🫧🫧🫧🫧🫧
BOOK 1
(The beginning )
Season _1
THE UNITED STATE
NEW YORK CITY
COLUMBIA UNIVERSITY
Cikin babbar harabar hall dake cikin Columbia university,mutanene zazzaune kowa kaga fuskarsa zaka ga farinciki da annashuwa a cikinta, daga saman stage suma wasu mutanene sanye da suit a jikinsu black colour , daga sama kuma gown ce a jikin su na graduation . Cikin tsantsan turanci da ke fito dako Wana kalma ake kiran sunayen daliban , bayan kowa ya karbi certificate din shi aka fara kiran wasu daga cikin daliban Domin basu award dinsu. Zaune yake cikin shigar suit dinshi fuskarsa sanye da face mask ya dukar da kai sai gashinkansa daya sakko masa har wajan idanuwansa, time to time yana duba diamond watched din dake hannunsa kafun ya mayar kan dan kareriyar wayarsa kirar Samsung, “ADIL BIN MOHAMMED Al_TAUFEEQ”, gabaki d’aya kowa jira yake yaga me sunan ya tashi amma kwata kwata Har yanxu babu Wanda ya mike , wata babbar macece ta kara kiran sunan tana duban daliban “ the most talented person of the session,”ADIL bin Mohammed Al taufeeq,are you around please “, wani na gefensa ne ya dan tabosa “ADIL ,MAAH is calling you”, banza yayi wa na gefen nasa kamar be san da wani halitta a wajan ba , gabaki d’aya idanuwansa nakan wayarsa ,Akaro na uku aka kara kira sunan adil Mohammed Al-taufeeq, yanxu ba mashi da alama ko niyar tashi, “ YAYA PRINCE “, sunan da ya bayyana akan screen din wayarsa , “finally” ya furta cikin wani daddadan muryarsa kafin ya mike a hankali, gabaki d’aya hall din tafi aka fara bakajin komai sai raf raf raf din tafi dake tashi, da ihu aka kiran “ADEEL, ADEEL” Wanda ya mike din cikin wani irin taku ya karasa inda ake kiransa, wani medium box ne brown colour da akayi rapping aka mika masa, kafun matar ta nuna masa wajan mic, har yanxu kansa a sunkuye yake be kalli kowa dake cikin hall din ba, gabaki d’aya hall din shiru ya dauka kowa jira yake yaji speech dinsa,shi kuma ganin yanda kowa yayi shiru ne yasashi dauke kansa shima batare da yace komai ba kusan mintuna uku,”Little Boo”,kalmar ta sauka a kunnansa, da Sauri ya dago eyes dinsa da har yanxu gashi ya karesu,cikin sauri yake kallan mutanan wajan ko zea gansa, daga nesa dashi yaga an daga fingers guda biyu, murmushi ya saki duk da facemask din dake fuskarsa, a nutse ya fara bada speech din da ya dau hankulan mutanan wajan, gabaki d’aya cameras na kansa,yana kammala speech dinsa wajan ya kara daukar tafii da kalmar “ADEEL da ake ta faman kira, yana koma wa aka kara kiran sunansa as the most disciplined , dan guntun tsaki ya saki kamun ya koma, yana karba bece komai ba yayi wucewarsa, idanuwansa akan wajan da aka dago masa fingers dazu, so yake kawai yaga ankammala gabaki d’aya a ‘kage yake da ya bar wajan, akaro na uku aka kara kiransa , jiyay kamar ya make mekiran nasa , gabaki daya takaici duk ya kamasa,a karo na uku aka sake bashi wani gift din , Madam flora na kokarin bashi waje don yayi wani speech din ya bar wajan, a haka aka cigaba da kiran ragowar mutane 4 da zaa bawa gift suma, saida y karbi wasu gift din shima duk acikin student din ya fi kowa karbar gift din kowa ADIL TAUFEEQ zakaji yana kira kowa burinshi yayi hoto dashi, yana gani an gama ya mike da niyar barin wajan , duk yanda friends dinsa ke rokansa suyi hoto ba Wanda ya kula a cikinsu, cikin mutanan ya shiga kai tsaye amma be ga Wanda yake nema ba, kamar yayi kuka ya fita daga hall din, a tsaye ya hango wani black American sanye da black suits, idanuwansa rufe da ba’kin google, gabaki d’aya babu fara a cikin fuskarsa, da sauri ya karasa inda yake gift din hannunsa ya mika masa,cikin girmamawa ya amsa kafin ya sara musu,”captain” ya kira sunan mutumin, nuni mutumin yayi masa da wasu jerarrun motoci baka ke wuluk da suke zagane da wasu mutane masu kakin sojoji,batare da ya bari ya kuma cewa komai ba, cikin sauri sauri ya nufi wajan motocin, suna ganin sa suka sara masa,motocin ya fara bi da kallo yana jiran yaga ta ina zasu fito,daga bayansa yaji an furta “Little”, cikin wani daddadan murya, da mugun sauri ya juya tare da ware idanuwansa, beyi wata wata ba kawai ya Dane mutumin” yaya prince dina” shima Wanda ya ‘Dane rungumeshi yayi a jikinsa a hankali ya furta “ zaka karyani fa “, dariya ya saki yana sauka daga jikin mutumin, wani hadaddan guy ne fari tas dashi , kwata kwata rabin fuskarsa a kulle take sabida p_cap din data rufe masa rabin fuskarsa sai dan medium din bakinsa da ya fito pink dashi, kallan gefe da gefen mutumin yayi kafun ya furta “ basu dawo bako,” ya furta cikin sanyin murya kamar me shirin yin kuka , “why the pity face, so kake BIG BOSS da YAYA BOBO suyi farfesu nane, they’re at home fa”, kugu little ya rike kafun ya furta “ ka tabbata yaya prince”, girgiza masa kai yayi kafin ya furta “toh nayi maka karya , if you like kayi ta zama , ni am going “, yana kammala maganar sa wani black American ya bude masa mota ya shiga, da sauri ADIL shima ya zaga daya bangaran nan ma wani American guy ne ya bude masa kofa , da mugun gudu motocin suka fita daga cikin Columbia university suka hau kan babban titin New York , mintuna 15 ne suka kawosu hadaddan street din FIFTH AVENUE dake cikin Garin new york, gabaki d’aya layin shiru kake ji kamar babu wani halitta da ke rayuwa a wajan sai sojojin da ke wucewa time time, Daidai wani babban area da mafi yawanci sojojin suka fi yawa suka nufa, gabaki d’aya sojojin mikewa sukai tare da sara musu, da mugun gudu wasu soldier su hudu suka fara bin bayan motar har suka karaso dai dai wani babban gate me shegen girma da tsaho, ba bata lokaci aka wangale musu gate din motocin su suka shiga ciki, kusan tafiyar mintuna biyu suka kara zuwa wani gate din da ya fi na farkon tsaro , awannan karan sai da aka caje motocin ta waje saida aka tabbatar da lafiyarsu kafun a wangale musu gate dinshima,wata ni’imtacciyar iskace ta fara ratsasu sabida flowers din da suka fara cin karo dasu, a wannan karan tafiyan minti biyar sukayi kan dogon titin dake wajan, wata kafuwar gate ne da kanta take budewa, ta wani slide din waje motocin suka wuce bayan gate din ya aunasu.
Daga cikin motar ADIL ne ya dan kalli captain dake driving,” captain I give you 3 minutes ka karasar damu, if not zan fada wa big boss ya shigar da kai dakin duhu”, kafun prince dake gefensa yayi magana captain yaja motar da mugun speed “ azuciyarsa kuma yana auna irin horon da zai fuskanta idan ya karasa , sassaucin sama BOBO yayi mishi hukunci ba BIG BOSS ba, suma ragowar motocin suna ganin haka ko wannansu ya kara speed din motar, duk da sunsan dole su karbi hukunci wajan BOBO.ko gama parking ba ai ba Adil ya fito daga cikin motar ya arta a guje, masu tsaran kowa sunkuyar dakansa yayi cikin girmamawa, kofar babban masion din aka bushe masa , nan ma da mugun gudu ya shiga, wata kofar ya nufa me shegen kyau, yana shiga babban parlor ne ya bayyana me 4 set of designers , Aljannar duniya kenan gabaki d’aya falon sai ka dauka a wata nahiyar kake ba a duniya ba, falo ne da ya amsa sunan sa falo da ko me kudi be isa mallakar saba, naira tayi kuka ga wasu irin Logan modern stainless steel tiered crystal chandelier da ya kara haska falon, ko ina ka waiga haske ne tar, ga sanyin Ac dake busa ko ina na palour , cikin daga murya ya fara kiran “ UNCLE IRON MAN, YAYA BIG BOSS ,YAYA BOBO,Little is back”, yana maganar yana fincike mask din dake fuskarsa, fatabarakallahu ahsanin khalikin, kyakkyawa ne shi sosai da ya amsa sunan kyau, fari ne shi sosai duk da ba wani babba bane amma kyawunsa ya wuce misali, har yanxu bana iya ganin fuskarsa sabida gashin kansa da ya rufe masa rabin fuska sai kadan daga hancinsa da zaka gane dogone daya fito, sai dan karamin ba’kin shi pink kalo daya fito shima, Prince ne yashigo falon bakinshi dauke da sallama da sauri Little ya kalleshi duk da ba ganin idanuwansa ake sosai ba zaka gane hararar Prince yake, P_cap dinsa Prince ya saki, kyakkyawar sumar kansa itama ta sakko masa har wajan idanuwansa,gyara gashin nasa yayi kyakkyawar fuskarsa ta fito waje , ware idanuwansa yayi a kan little take eyes dinsa dasuka kasance ash colour suka fito waje sabida ware idanuwansa da yayi, shima kyakkyawa ne na ajin karshe , fadar irin kyawunsa ma bata baki ne, fuskarsa bame fadi bace sosai sannan ba doguwa bace, dai dai jikinsa ga dogon hancinsa daya kara fito da kyawun fuskarsa, dan madaidaici bakinsa ya tabe yana kara bin little da kallo ,cikin wani yare ya furta “Ni kake harara”kamar mace little ya rike kugu tare da tura masa baki, a guje prince ya bi bayan little, shima little yana ganin hakan yasa gudu suka fara zagaye falon,”stop there “ Prince ya fada yana jefowa little pillow , shima little pillow ya dauka tare da jefowa prince “ I won’t , ba kaine kace mun my loves sun dawo ba”, wani pillow Prince ya dauka ya jefawa little a fuska, ganin hakan yasa shima little daukan pillow, gabaki d’aya sun bata falon duk pillows din kujerun sai da suka sakko da shi kasa,wani pillow Prince ya dauka zai jefa wa little yaji saukar muryar data sashi faduwa “ If you dare “, da Sauri ya jefar da abunda ke hannunsu, Prince ma mikewa yayi shida little suka hade waje daya , kana kallansu kasan basu da gaskiya , Cikin 3 quarter din wandan sojoji da bakar armless ya karaso cikin falon, kakkarfa surar jikinsa da kallo daya mutum zai yi masa yasan yana daga karfe, kyakkyawa ne sosai da ya amsa sunan kyau, har na kasa banbance wanane yafi kyau a tsakaninsu duk da fuskar little ma rabi ce a bude amma kana ganinsu zaka ga kamannin da suke da juna har ya kwayar idanuwansa light gray ya zuba musu , “YAYA BOBO” little ya fada da niyar nufar sa, wani gigitaccen kallo ya jefa masa kuskarsa kwata kwata ba fara’a “ if you dare ka kara one step kaga yanda zan karya kasusuwanku “, narai narai little yayi da ido, shikansa Prince tsoran magana yake kar lefin ya dawo kansa baki d’aya ,kallansu mutumin yayi kafun ya nuna musu 5 fingers dinshi “ just 5 minutes na baku , ku tabbatar falon nan ya dawo yanda yake kafun ku karbi punishment dinku”, be karasa maganar ta saba suka fara gyara pillows din , jiya d’auke kansa yayi daga kansu kafun ya dakko wata roughly mobile phone army dake jikin 3quarter dinsa , number 3 kawai ya danna ko mintuna biyu ba aiba , su captain Suka shiga cikin babban parlourn, gabaki d’aya sara masa sukai ko kallan inda suke beyi ba, cikin kwarewa captain ya kara sarawa tun kafin BOBO yayi magana,
Cikin yaran turanci Captain ya furta “ reporting !!! Tukin ganganci a harabar gida hukuncin bulala dari tare da zagayen gida sau dari shine hukuncin mu”, ga baki d’aya sauran soldiers din suka hada baki wajan furta “salute”, hada ido Prince da adil sukai, cikin zuciyar sa prince yake furta “shikenan little ka kashe ni da raina, yanxu idan me kirar samu dawan nan ya dawo kan mu ai mummutu, “su captain suna fita Prince be karasa maganar zucin saba Bobo ya maida kallansa akansu, gabaki d’aya sunkuyar da kai kasa sukai, kan one sitter ya zauna kafun yayi crossing legs dinsa yana duba a gogo “ zagaye dari!!! Starts “ kamar zasuyi kuka suka fara zagaye falon gashi ba damar su bashi hakuri ya kara nunka musu wani wahalar, a zagaye na 20 suka fara layi kamar zasu fadi, a hankali suka fara tafiya yanxu, mikewa bobo yayi daga kan kujeran tuni suka manta da gajiyar tasu suka ci gaba da zagaye falon, da sunyi kokarin tsayawa zasu ga bobo na binsu da kallo, a 80 adil ya fadi kasa tare da fashewa da kuka “ yaya bobo please kayi hakuri, kamanta little dinka ne ni kuma yau graduation dina fa, “ shima Prince zubewa yayi a kasa cikin pleading ya furta “ yaya bobo we’re sorry “, babu Wanda ya kula acikinsu, “ zagaye hamshin!!! Starts”, sakin baki Prince yayi “ wani lokaci har tunanin tsakanin big boss da yaya bobo wanane yafi wani iya mugunta dan hukuncin big boss ya fi na kowa tsauri, ba karamin aikin sa bane yasa a jefaka caged din zakinsa kuma babu Wanda ya isa ya futar da kai sai ta Allah. Zasu mike wani mutumi ya shiga black American da shi, jikinsa sanye da kananan kaya shima, little na ganinsa ya kara fashewa da kuka “ Uncle iron man , please ka bawa yaya bobo hakuri kafata ciwo take mun”,kallan bobo mutumin yayi yaga ya dauke kansa, murmushi ya saki kafun ya karasa inda little yake “ kunyi lefi kenan, ku bashi hakuri idan ya ki hakura ku kira masa big boss sai ayi ya’ki kowa ma ya huta”, yanda suka zaro idanuwane yaso bashi shi dariya , zasu kara magana bobo ya nuna musu hanya dan hayaniyar su har ta cika masa kunne “ leave this place now”, ai be karasa ba ko wannansu ya arta a guje, yanxu kam kasa rike dariyarsa mutumin yayi saida ya dara kafun ya kalli bobo “ why are you punishing yourself, kai da big boss kunfi kowa jin zafin punishment din da kuke sasu amma hakan baya hana gobe insunyi lefi ku hukuntasu, ynxu da dan gwarzane sukai sai kunfi kowa jin ciwo, in wani kuma yayi gigin koda mintsuninsune tsaf zaku harbe mutum,please ku sassauta wannan zuciyar taku”.shafa keyarsa bobo yayi kafun ya furta “ok uncle”, girgiza Kai uncle din yayi kafun ya nufi wata kofa , shima bobo wajan elevator ya nufa da zea kaishi sama.
A bangaren Prince da little kuwa suna shiga dakin su kowa ya haye kan gadonsa yana maida ajiyar zuciya Dan ba karamun horuwa sukai ba, babu Wanda ya kula junan su ,musamman little da yake fushi, ko wannansu wanka yayi cikin kayan shan iska, duk yanda Prince yayi da little su sakko kasa yaki, ya ma ki yi masa magana kwata kwata sai ma Hayewa kan bed dinsa da yayi yana lullube kansa. Kusan tsawan 30 minutes yaji an bude door din, a tunaninsa Prince ne yace “ yaya Prince just leave me alone”, shirun da yaji ne yasashi kara furta “ please yaya Prince ka tafi, yaya bobo baya sona yanxu”yaye blanket din da akai ne yasashi waro ido ganin bobo tsaye hannunsa dauke da babban tray, akaran farko da kyakkyawar fuskar little ta fito, a shekaru bazai wuce shekara 21 ba dukda kyansa be gama fitowa ba kamar yan uwansa amma shima kyakkyawa ne na karshen karshe, dauke blue eyes dinsa yayi daga kan bobo zai koma ya kwanta “ stay still” cewar bobo, sunkuyar da kai little yayi kamar zeyi kuka , ajje tray din bobo yayi kan wani table me zaman mutum 3,kafun ya karasa inda little yake , a gefensa ya zauna shima kafun ya kama hannun little “ yaya bobo yayi lefi, am sorry kar a fada wa big boss ya harbeni “, dariya ce ta kwace wa little besan lokacin da ya rungume bobo ba, shima bobo rungumesa yayi kafun ya mikar dashi tsaye, dakansa ya dunga feeding ADEEL abincin da ya kawo masa shima ADEEL din na bashi abaki, saida suka kammala cin abincinsu kafin little ya kalli bobo” yaya bobo , big boss ya dena sona har yanxu ya ki dawowa fa”, bobo be ce masa komai ba sai wata karamar phone da ya dauko wasu number guda Hutu ya danna take a wajan aka dauka, little dake binsa da kallo, tsawan mintuna biyar Ba’ace komai ba kuma babu alamun za ayi magana ,”yaya” shiru yaji ba ayi magana ba “ Assalamu Alaikum “ ya kara fada kusan mintuna biyu kafun wata ratsatstsiyar murya ta daki dodon kunnansu “ Wa’alaykumussalm “, daga nan ba a kuma cewa komai ba “ Yaya” little ya fada kamar me rada “ little I will called you back!” “ kafun yayi kokarin yin magana aka kashe kiran gabaki d’aya ,” karbar wayar bobo yayi “ kaga yayan naka yana meeting and zai kiraka , so don’t worry, and ya bani gift dinta , and if you guys need anything ku duba dakina ko na big boss, but ba fa kyauta na baka ba , kana fara aiki zaka biyani kudi na “ rungumeshi little yayi cikin yaran larabci ya furta “ Ina sanka yaya bobo na ,” love you too “ yana gama maganar sa ya bar dakin.
Shima tittle wani choco ya dakko cikin sauri ya sakko downstairs, “yaya Prince “ yake kwallawa kira ,”Menene kake faman kirana ka gama fushi”, amaimakon ya amsa masa sai kashe masa ido daya da yayi “ yaya Prince wajan simba zaka rakani , yau kwata kwata banganshiba “,kallan tara saura kwata Prince ya bishi dashi “ dan iska ne Ance maka da zanje wajan wancan zagin, Kai da ka ga zaka iya ai sai kai tayi “, shima kallansa Adil yayi “ shikenan Allah sai na fada wa yaya bobo , shima big boss sai na fada masa “ da Sauri Prince ya riko hannunsa “ Haba auta, wasa fa nake maka zo muje wajan simba din”, fitowa sukai cikin babban mansion kafun su nufi wata kofa, duk inda suka wuce sojoji suna sara musu, cikin wani babban cage suka shiga , Prince da ya shiga karshe sai be kulle kofar cage din ba, “Simba!!! Simba !!!” AdIL yake kira,wani gurnanin zaki ne ya fara tashi me tsoratarwa, inda gurnanin yake fitowa adil ya nufa ba ko tsoro tattare dashi,”Simba “ ya kara kiran sunansa , wani katon zaki ne ya fito , yanda naga girmanshi nikaina sai da na razana, bakinsa ya bude kafun yayi wani kuka amaimaikon su gudu sai nufar kusan tosa da sukai kai, kansa Adil ya shafa “Simba yau duk ban gankaba “ Abun mamakin shima Zakin da aka kira da simba, gashin kansa ya karkada masa kafun ya daga hannayensa ya dora ajikin Adil, wani irin farinciki ne ya kama adil kamar Wanda ya samu mage haka yake wa zakin wasa, Prince na gefe sai faman vidoe yake musu, ganin lokacin sallahr magariba ya kusa ne yace wa Adil suzo su tafi kar yaya bobo ya ne mesu, ba musu kuwa suka bar cage din.
🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧🫧
ABUJA
ADEMOLA ADETOKUMBO STREET
Cikin wani babban gida dake cikin ademola , maza da mata ne ke faman shige da fice gabaki d’aya wajan fitula ya haska , ko ina ka duba zaka ga mace da namiji rabe da junansu, daga gefen gidan da akai wa lakabi da UWAR BARIKI, wasu kyawawan yan matane guda 4 da a kalla shekaru baza su wuce shekara 15 ba, ko wannan su ka kalli fuskarta zaka ga tashin hankali tattare da ita , d’aya daga cikin yan matan da tafi kowa shiga tashin hankaline ta rushe da wani saban kuka ,” shikenan na shiga uku, yanxu me zancewa UWAR BARIKI, na tabbata in bankai mata kudin yau ba kashe ni zatayi “ kallanta d’aya daga cikin yan matan da ita ma zaka ga tashin hankali tsantsa a fuskarta tayi kafun ta furta “ ki dena kuka ARWA nasan ABLA in tazo zata neman mana mafita “, girgiza Mata kai wacce aka kira da arwa tayi “ kinsan yanda uwar BARIKI ta tsani Abla fiya da kowa musamman yanda taki yarda tayi kudi da ita shiyasa tafi kowa shan wahala a cikin mu, yanxu idan Abla taji bansan me ze faru ba, kawai ina tunanin zan bawa wani kaina ne kamar yanda uwar BARIKI take bukata, ko hakan zaisa mu fita daga kangin rayuwar nan” saukar mari taji a fuskarta da yasa tadiye sauran maganarta, gabaki d’ayansu maida hankalinsu kan wanda tayi marin sukai, Wata kyakkyawar matashiyar budurwace tsaye a gabansu, gabaki d’aya wahala ta bayyana a jikinta ga wasu matattun kaya a jikinta daya fi na sauran munana sabida yanda suka mutu , gabaki d’aya hada baki yan matan sukai wajan furta “ABLA”.
IBTISSAM
(Heart touching story of love and destiny)
Story & written
By
Mss Lee
BOOK 1
( The beginning)
Season 2
ABLA !!!!! Wacce aka kira da Ablance ta kallesu cikin muryarta da bata fitowa sosai ta soma magana “ Saunawa zan fada muku duk wahalar da zamusha kada mu taba yadda muzubar da mutuncin mu, ya kamata mu yarda da kaddara, kome zasuyi mana mudunga kai wa Allah kukan mu su basu ita su cutar da mu ba , kar na kumajin wata magana irin hakan”, wacce aka marace ta kara sakin kuka “ Abla basu da kirki mugayene, idan bamuyi musu abunda sukeso ba zasu cutar da mu, “ ya’ken da yafi kuka ciwo Abla ta saki “ karki damu Allah na tare damu, nawane kudin naki da ya fadi “, share hawayenta arwa tayi kafun ta furta “ 170 ne “, kwance gefen dankwalinta Abla tayi taciro wasu matattun kudi, dari da saba’in din ta irga kafun ta bawa Arwa,girgiza mata kai Arwa tayi “ Abla kinsan matarnan ba mutunci ne garetava in na karbi kudin nan zata gana miki azabane “ bata kai karshen zancen taba daya daga cikin yan mata ta miko mata kudin da ta kudun dune “ Abla ni ki karbi nawa , ni se ayi mun hukunci”, kafun abla tayi magana ta gefen wacce ta miko kudin itama ta miko mata nata “ abla ki karbi nawa , ni se ayi mun hukunci ba sai anyiwa Anee ba “ girgiza musu kai Abla tayi “ karku damu bazan karbi kudin kowa ba , yanxu kunga dare yana karayi in bamuje kun kai mata kudin nan ba zata sa aduke kune , kuzo muje “ rungumeta sukai gabaki d’aya su ukun banda ta karshensu da sai faman harararsu take a fakaice , Sarai abla ta ganta shareta kawai tayi , Arwa ce ta kalleta “ husna ki taho mutafi mana “ girgiza mata kai husnan tayi a dan yake ta furta “ ku tafi zan taho daga baya “, bata jira cewarsu ba ta bar wajan, guntun tsaki Anee taja “ ni fa shiyasa kwata kwata bana shiga harkar husna , sai kace yar uban shugabankasa mutum sai fadin rai”, ta ukunsu ce me suna Ilham ta tabe baki “ matsalarta, ni bazan sawa kaina damuwar ta ba Wallahi”, shiru abla tayi musu dan itama ta fara gajiya da halin husna , a darare suka fara wuce mutanan wajan , Daidai bakin window suka tsaya ,gabaki dayansu tsoran shiga suke, basuyi auneba sukaji an shako rigar abla , da sauri suka juyo, gabaki dayansu razana sukai da ganin UWAR KARUWAI ga wasu mata guda uku a bayanta , “ tsinannun yara uban me kuka tsaya yi anan, wato kun tsaya muna furcin da kuka saba ko ,zinariyya ku dakko mun su” tana kammala maganarta taja abla kamar wata kayan wanki ga wuyanta da ta shake da kyar take iya shakar nunfashi, Wanda aka kira da zinariyya itama kan Anee ta janyo kafin ta tsinka mata mari tare da janta a kasa kamar kayan wanki, ragowar mata biyun da akallo daya zaka musu kaga manyan karuwai suma haka suka janyo Arwa da ilham, duk inda suka gifta sai dai a kallesu a dunga shewa. Can cikin wani daki da ya cika da tarkacan kwalaye Uwar karuwai ta jefa Abla take a wajan kanta ya bugu da Gini, bata gama shiga a zabar buguwar da tayi ba taji saukar mari dama da haku a kumatunta ,” shegiyar yarinya gwanda inkashe ki in huta babu abunda kuke tsinananun “, Daidai lokacin da ake shigo da su Anee suma, kallansu uwar karuwai tayi gabaki d’aya mummunar fuskarta a hade ta ke binsu da wani mugun kallo, katan hannunta da yaci uban Jan farce ta miko musu ba tare da ta furta komai ba , da Sauri gabaki dayansu suka saka mata kudadan hannunsu banda abla dake nishin azaba , “ ku d’auke su anan “ cewar uwar karuwai, ba musu kuwa suka d’auke su gabaki dayansu kukan da sukai ya bata musu fuska . Kallan ta uwar karuwai tayi ,”ina kudin ki” cikin dishashewar murya abla ta furta “ sun fadi”, bata Kai karshen zancan taba uwar karuwai ta hanbare mata baki take a Wajan bakinta ya fashe “Bansan asara ba , sannan bana daukar asara ,duk acikin yaran da nake hulda dasu kece tsagerarsu, in baki sani ba na tuna miki , ke din ba kowa bace face baiwa da ko dabba ta fiki gata , rayuwarki tana hannuna sai yanda nayi dake tukunna, dan haka ko kina so ko ba kyaso dole kiyi karuwanci ki kawo mun kudi” tana gama zancanta ta kwallawa zinariya kira “ ki kai ta dakin shirgincan, ki tabbata bata samu abunda zata kwanta ko lulluba akai ba ,abude winduna yanda sauraye zasu shiga ciki, banaso kuma naga kaske na yawa a ciki “.wani shu’umun murmushi zinariya ta saki kafin ta ja abla data gama galabaita zuwa wani dakin shirgi da ko mara gata sai haka , gabaki d’aya dakin dattine a cikinsa ga uban shirgin kaya a ciki sai faman wari yake , kamar yanda uwar karuwai ta umar ta haka zinariya tayi kafun ta kalli abla cikin lashe baki “ ki bani kanki kawai na dan dana zumarki, zansa uwar karuwai tayi miki sassauci “ ta karasa zancanta zata taba abla , cikin wani irin zabura abla ta hankade hannunta , gabaki d’aya ta gama galabaita “ karki sake kazamin hannunki ya kuskura ya taba fatar jikina, Ta Allah ba taku ba kuma mugaye azzalumai, kamar yanda kuke kokarin cutar damu insha Allahu munfi karfinku “, shake mata wuya zinariya tayi “ kar kiga ina binki ta lallami, ko kina so ko bakyaso sai kinzama mallakina, sai na dunga jin dadinki “tanakai karshen maganarta tasaki wuyan abla , sai alokacin wani irin tsoro da firgici ya kama abla ganin zinariya na kokarin barin dakin, bata gama shiga cikin firgicin ba zinariya ta kashe fitilar wajan tare da kullo ‘kofa. Cikin fita hayyaci abla ta soma magana “ A’a , A’a , ku budeni, banaso Wayyo ku budeni, duhu banasan duhu , duhu zasu kamani bana so , ku bude mun kofa , ku bude mun kofa “ a haukace ta soma dukan inda take tana kiran su bude ta , kara ta soma saki kafun ta fara dukan kanta kamar wata tababbiya, “ Dan Allah ku bud’eni bana san duhu” yadda nunfas yake sama da kasa kamar xai fita daga cikin jikinta, gabaki d’aya jikinta rawa yake take a wajan ta fara shakuwa kafun nunfashinta ya dauke gabaki d’aya a wajan.
✨✨✨✨✨
NEW YORK
FIFTH AVENUE
8:15pm Little ne zaune kan daya daga cikin ran tsatstsun designer cushions din falon , hannun sa dauke da system dinsa dayake game, Prince na gefensa dauke da waya shima , fitowar wannan black American dattijon da Akalla zaiyi shekara 50 a duniya ne yasa Little ajje system dinsa “ uncle Iron man ,” murmushi mutumin yasakar masa “ Na’am uncle little “, ba little ba hatta Prince dariyar kalmar uncle Little din daya fada suka saki , ganin lokaci na tafiya ne yasashi kallansu “ lokacin dinner yayi , let’s go and eat “, kashe system din sa little yayi kafun ya mike tsaye, “bari na kira yaya BOBO”, gyada masa kai sukai kafin su nufi wani rantsats tsan dinning , da in aka bar mutum bazai taba gajiya da kallan sa ba, iya haduwa dinning din ya hadu , ga wasu set din dinning daya ‘kara fito da haduwar wajan, kan d’aya daga cikin kujerun da mutane goma zasu zauna suka zauna batare da sunyi magana ba. A sama kuwa direct wani irin corridor Little ya nufa, yanda tsarin corrider din yake shikadai ya isa kallo, wani door me dan tsaho ya nufa kafun ya tura kofar babban door din, kayataccen falo ne me shegen girma duk da bai kai girman falon kasa ba , iya tsaruwa da haduwa falon yayi , wani kamshi turare ne ke tashi a cikin dakin ga sanyin falon da ya cika ko ina, ganin babu kowa a cikin falon ne yasa shi nufar d’aya daga cikin doors din kofar.Astagfirullah ya Allah , babban daki ne me shegen kyau a wajan, komai na cikin dakin brown colour ne , ga wani dan ubansun king sized bed me shegen girma da daukan ido, iya haduwa da tsaruwa dakin yayi kamar ba ‘a anfani dashi, shiga cikin d’akin little yayi bakinsa dauke da sallama, babu kowa a d’akin har ya juya zai fita wata ran tsartsiyar waya ta fara haske alamun kira ya shigo ciki, ganin yaya bobo baya d’akin yasa shima ya share zai fita ,sai kuma ya ‘kara dawowa cikin sauri zai dauki wayar aka turo wata kofa dake cikin dakin. Fuska a hade BOBO ya kalleshi babu alamun fara’a akan fuskarsa, “ what are you doing here “, rawa bakin little ya fara , kamar me ‘kin’kina ya furta “ Na dauka Yaya ne”, sakin fuskarshi bobo yayi kafun ya karaso inda yake “ you’re very stubborn little, gwanda yayan naka ya dawo ko kashiga taitayinka “, zaro masa ido little yayi zai marairai ce masa bobo ya harareshi,”my phone”, da Sauri Adil ya mika masa wayar, wata number bobo ya danna, kusan ringing biyu ba a dauka kiran ba, ana ukunne yaga kiran number ,da sallama abakinsa bobo yayi magana , shiru kusan tsawan mintuna biyu banji me akace masa sai kallan Adil da yayi “ your stubborn brother ya dameni, talk to him”, yana kammala zancan sa bobo ya mika masa wayar da sauri Adeel ya kar’bi wayar har wani dariya dariya na kwace masa “ Yaya big boss “, ya fada kamar me rada banji me aka ce masa ba sai kallan bobo da yayi kafun a shagwabe ya furta “ sorry yaya Assalamu alaikum,” kusan mintuna daya kafun ya furta “ Yaushe zaka dawo yaya nayi missing dinka , gidan ya rage dadi fa” kallanshi bobo yayi alamun zaka sani , ga baki d’aya Adil ya manta bobo na kusa dashi, gyada kan da Adil yayi ne yasa bobo gyara tsayuwar sa “ eh fa yaya ,yau graduation dina amma kaga yaya bobo yayi punishing dina , Kai nake jira ka dawo karamamun”, bai kara zancansa ba yaga bobo na dage masa gira ,”Innalillahi wa’inna ilaihi raji’una, na mutu na lalace yaya bobo daman kana nan”, kit aka kashe kiran daga can ‘barin, gyara tsayuwarsa bobo yayi “ ina punishing dinka ko, come over here , zo nan”, zaro masa ido Adil yayi “ Haba yaya bobo na kasan ina sanka , I’m sorry kaji “, not accepted cewar bobo, ja da baya little ya fara yana kokarin guduwa, hannu bobo yasa zai janyosa yayi saurin zillewa , cikin dariya ya furta “ nifa bazan bari ka kamani ba yaya bobo, nace fa ina sanka me and you one heart ne “ harararsa bobo yayi ,” come over here “, nace fa sorry yaya bobo, kace idan mutum yayi lefi kuma ya bada hakuri anaso mutum ya dunga yafiya”, murmushi bobo ya saki da yayi wa kyakkyawar fuskarsa kyau “ ni zakayiwa siyasa “, girgixa masa kai little yayi “ yaya nifa yunwa nake ji , kuma kai kadai nazo na kira kaji yayana , I love you “, gyada masa kai bobo yayi “ok let’s go”, da Sauri kuwa little ya karasa wajan bobon, be auneba yaji bobo ya kama kunnansa, saurin dafe kunnan little yayi , cikin dan kara ya furta “zafi yaya kunnena “ da sauri bobo ya saki kunnan nasa “ inane yake maka zafi”, kunnan little ya nuna masa ,”it’s ok zea dena” kama hannunsa little yayi “ yaya bobo,kayi mun alkawari fa ranar graduation dina zaka goyani “, kallansa bobo yayi “ as big as you are zan goyaka , so kake ka karyani”, shiru little yayi masa har ya kama tafiya bobo ya riko hannunsa “ hau mu tafi , kafin ka hana mu bacci “, da sauri kuwa little ya d’ane bayan bobo, har suka sakko falourn kasa Adil na bayan bobo kamar wani karamun yaro, murmushi uncle iron man ya saki, shi kuma prince girgiza kansa kawai yayi , “ sorry uncle iron man, sorry yaya Prince dina “, hararar sa Prince yayi , tun dazu yake jin yunwa da yake Adil dan iskan yarone ya barsa yana faman shiri rita, waje bobo da little suka samu kafin Prince ya danna wani button, cikin seconds din da bazea wuce d’aya ba wani soja ya shigo cikin falon, sara musu yayi kafun ya fara tanbayarsu abinda za a yi serving Dinsu, kowa fadar ra’ayinshi ya ke banda bobo da little ya zabar masa , yazo zea tafi Adil ya sakar masa murmushi “Thank you uncle James “, shima Wanda aka kira da james din murmushi ya sakar wa Adil kafun ya kara sara musu ya bar wajan.
Tunda suka soma cin abinci babu Wanda yace da wani kala har saida suka kammala cin abincin su, basu kara 50 minutes a falon ba kowa ya nufi bedroom dinsa. Karfe 2 da rabi Bobo ya fito daga part dinshi , direct dakin su Adil ya nufa ganin ko wannansu yayi bacci, gyara musu kwanciya yayi kamar wasu yara kafun ya kara yi musu addua ya totto fa musu, iya dum light ya bari a dakin kafun ya fito, haske kad’an ne a falon amma duk da haka sosai falourn ya kara kayatuwa,sai da ya zagaya ko ina na falourn kafun ya fito waje , awajan ma fitulu ne masu haske kamar rana da suka kara haska kyan gidan, sojojine birjik a tsakar gidan tare da wasu manya manyan karan sojoji da suke shawagi a wajan, duk inda ya gifta sai an sara masa, saida ya tabbatar da lapiyar kowa kafun ya koma part dinshi.
WASHE GARI
Washe gari ana kiran sallah asuba wata iriyar jiniya ta karade ko ina nagidan , gabaki d’aya kowana mahaluki na gidan ya tashi banda Prince da Adil da suke baccinsu,
Akaro na biyu Jiniyar ta karayin ‘karar da bata kai ta farko ba, pillow Prince ya dauka ya toshe kun nuwansa dashi tare da kara janyo blanket yana rufe har fuskarsa, Adil ma baccinsa yake hankali kwance, A hankali aka tura kofar d’akin, bakowa bane face bobo dake tsaye abakin kofa, hasken d’akin ya kunna kafun ya karasa inda Adil yake “ Adil!!! Get up lokacin sallah yayi”, ko motsi Adil beyiba, shafa gashin kansa bobo yayi “ get up now ,ok”, dan motsi Adil yayi kafun ya soma karanto adduar Tashi daga bacci a hankali, karasawa wajan Prince Bobo yayi , shima kiran sunansa yayi, amma ko gezau beyi ba, kara kiran sunan shi yayi akaro na biyu sai wani pillow da ya dauko zai toshe kunnensa, 2 fingers dinsa bobo kawai yasa ya dakawa Prince duka a gefen hannunsa, azabure Prince ya furta “ su wanene suke shirin yin yaki”, be karasa zancan saba yaga bobo tsaye a kansa, ga Adil dake faman kumshe dariyarsa. “Just 5 minutes na baku, if you like ku koma and see”, yana kammala zancansa ya bar dakin, bashiri kuwa sukai brush da Alwala ko wanka basu tsaya yi ba , a ‘kasa suka tarar da bobo da uncle iron man , gabaki d’aya masallacin dake cikin gidan suka nufa, sojojine suma cike a wajan suna jiransu, musulman ciki suka shiga masallaci, ragowar kuma suka fara motsa jiki. Ana idar da sallah kowa ya koma masaukinsa, su Prince ma basu tsaya a falour ba suka nufi d’akunansu , Prince ya zo zai kwanta Adil ya tsayar dashi,”yaya Prince kasan yaya bobo yana jiran muko , wallahi ka koma bacci babu ruwana kasan babu abunda zai hana a nunka maka wani motsa jikin”, yana kammala maganarsa ya shigo toilet, tsaki Prince ya ja kamar yayi kuka , Adil na fitowa shima ya shiga wankan, shaf shaf suka shirya cikin kayan motsa jiki, a tsaye suka tarar da bobo shima da nasa kayan motsa jikin , sa’banin nasu shi kayan motsa jikin sojojine a jikinsa, sakkowa sukayi inda yake kafun su sara masa” Salute”, shima hannunsa daya ya d’aga batare da ya sara musu ba ya furta “salute, kun ‘kara 2 minutes Menene hukuncinku “, gabaki dayansu sakin baki sukayi suna kallansa “ Yaya” eyes dinsa ya zuba musu , gabaki d’aya saurin sunkuyar da kai sukai kamar abun tausayi,girgiza kai kawai yayi “ let’s go” wata iriyar ajiyar zuciya suka sauke gabaki dayan su, cikin d’an gudu gudu suka fara tafiya , suna fitowa harabar gabaki d’aya sojojin suka sara wa Bobo kafun su hada baki wajan furta “Salute” hannu ya daga musu, kafun su Prince su fara motsa jiki , sai da sukayi 2 hours suna motsa jiki kafun su koma part Dinsu.
9:30am James ya serving Dinsu breakfast , Tunda suka fara Breakfast gabaki d’aya babu Wanda yayi magana saida suka kammala.
07041879581
MSS LEE
https://chat.whatsapp.com/GOZ7a2miBjZ4vUjRXdRdrA
IBTISSAM
( Heart touching story of love and destiny)
Story & written
By
Mss Lee 💖
BOOK 1
( The Beginning)
Season _3
3:00am nayi ko munti d’aya be gotaba aka bude kofar shirgin da aka kulle Abla, Zinariyya ce tashigo sai tangad’i take Ganin yanda Abla bata motsine yasa Zinariyya sanar da Uwar karuwai, umarni ta bada Akawo mata ruwa masu sanyi a fridge guda biyar, hakan kuwa akayi cikin d’an karamun roba Zanariyya ta juye ruwan masu bala’in sanyi. Dakin shirgin suka nufa ita da Zinariyya sai wata da ake cewa Yar shila , a yadda zinariyya ta barta a haka sukazo suka sameta, kar’ban ruwan uwar karuwai tayi cikin rashin imani ta juyewa Abla shi a jikinta.A gigice Abla ta farka tana Ambatan sunan Allah , gabaki d’aya jikinta rawa ya d’auka sabida wani irin sanyi dayake ratsa jikinta, kallanta uwar karuwai tayi a wulakance “ ku tashi ku fara aikin da kuka saba dan ba Hutu ne ya dace da kuba, matsiyata kawai”, tana kai karshen zancenta ta kalli ‘Yar shila “ jeki taso mun ragowar tsinannun yaran, lokaci kankani na baku su kammala ayyukansu, idan ba haka ba ku zanesu suji a jikinsu “ tana kai karshen zancanta tayi waje , a duniya idan akwai wacce ‘yar shila ta tsana be wuce Abla ba , shiyasa uwar karuwai na fitowa taja ta kamar kayan wanki , Daidai lokacin da Zinariyya ta fito dasu Anee suma ko wannansu a jike sai rawar sanyi suke . Cikin kuka arwa ta karaso Inda Abla take ,”Abla sanyi nake ji , ga yunwa ina ji, ga bacci da be isar mu, jikina duk ciwo yake mun ga wasu cunnaku dasuka cijeni “, kwallarta Abla tayi saurin gogewa “ wata rana sai labari, kafun su dawo ku tashi muyi aikin mu ko zamu samu in lokacin sallah yayi muyi kafun musamu na abincin, kunsan idan bamu kammala ba, bazasu ta’ba bari muyi sallah ba” gyada mata kai sukayi gabaki d’ayansu,Babban falon da ya baci da kwalaben barasa da abubuwan sigari suka fara gyarawa , gabaki d’aya falon wari yake amma duk da haka sai da suka gyara shi tsaf sai faman haki suke sabida galabaitar da sukayi, d’akuna Biyar da suke jere a kasa ko wannansu ya nufi d’aya da niyar gyarawa, d’akin da Abla ta shiga wani irin amaine ya taso mata sabida kazantar da ta dunga cin karo dashi a dakin, gabaki d’aya d’akin a har gitse yake , da kyar ta Samu ta gyara d’akin kafun ta nufi toilet. Tana shiga aman da take rike wa ne ya kwace mata Sabida karo da ta dungaci dasu condom gawani uban Kazan tar dake cikin nan dakin, da kyar ta samu ta wanke ban dakin, tana fitowa sai da ta jira su Husna suka fito Suma , ko wannan su a waji gace sai faman toshe hanci suke, sama suka nufa shima saida suka gyara falon tass da ya fi na kasa baci kafin su gyara rooms din cikin falon, lokacin da suka gama wani irin juwace ta soma kamasu ga kiran sallah da ake faman yi amma badamar suje suyi.Inda kwanukan wanke wanke suke suka nufa, sosai an ‘bata kwanuka haka suka zauna suka fara wankewa, sai wajan 8:30 na safe suka kammala wanke wanken, Dole su gyara kitchen din gidan ga tsakar wajan da zasu gyara shima , ga lokacin sallah na tafiya, murya a dusha she da ‘kyar take magana ta furta “ Lokacin sallah na tafiya , ya kamata muyi sallah “ a tsorace suka kalleta gabaki d’aya “ Abla kinsan hukuncin da zasuyi mana idan suka san munyi sallah ko”, manyan idanuwanta Abla ta saka musu,” kuna nufin mu zauna karmuyi sallah sabida hukunci “, da Sauri duk suka d’aga mata kai kamun ilham tafurta “ sai muyi sallar daga baya danni tsoron muguntar su zinariya nake “, same Arwa ma abunda ilham ta fada shi ta maimaita, Anee ce ta kalleta “ Abla Nima zanyi sallah , Taho muje “, kallan Husna Abla tayi ko zataje amma ko kallan inda Ablan take batayi ba, a d’arare Suka samu suka fita daga cikin gidan, saida sukai tafiya me Nisan gaske kafun su samu wani masallaci da suka ga butocin ciki da ruwa, Alwala suka samu sukayi kafun Suje bayan masallacin su tayar da sallar su, suna idarwa tsoran hukuncin da za ayi musu ya kamasu. Cikin fargaba suka nufa Gidan, tsallan kwado suka tarar ansaka ilham da arwa , fuskarsu gabaki d’aya ta baci da hawaye, yar shila tana ganin su Abla ta rufe su da duka da wata jungegiyar doruna,kafin suma akasu tsallan kwad’an, tun sunayi da karfin jikinsu har suka somayi a hankali kafun su fadi a kan tiles din suna nun farfashi, yar shila ta daga hannu zata kara zuba musu wani bulalan uwar karuwai ta fito cikin wankanta da kallo d’aya zaka mata kasan cikakkiyar karuwa ce, “ ya isa haka yar shila so kike ki kashe mun kasuwa ne , ga kosai can ko wanne ki basa guda bakwai kafun ku basu wankin da aka had’a kunsan yau akwai casu, ko bara banaso suje yau sabida akwai aiki”tana kammala zancanta tasa kai ta bar gidan, kosan yar shila ta dakko amaimakon ta basu kamar yanda aka umarceta sai ta bawa ko wannansu biyar biyar, tana zuwa kan Abla ta Wulla mata guda uku ba kamar sauran ba, Husna ce kawai babu a cikin falon, ayun wace suka fara cin kosan da ko rabin cikinsu be zoba , banda abla da take bun kosan da kallo, tayi wa kanta alkawari bazata kara cin abinda ya fito ta kazamun hanya ba , shiyasa ta rabawa su arwa kowa daddai, harda murnarsu suka amsa kuwa kafun a tulo musu uban wanki me shegen yawa, basu suka kammala ba sai wajan 2:30, anan ma satar hanya ilham da Abla sukai sukaje sukai sallah suka dawo , a wannan karan Allah ya temakesu ba aga dawowarsu ba, har lokacin su Arwa kuwa basuyi ko sallahr asuba ba duk yadda Abla take musu magana har ta gaji . Wata iriyar masifaffiyar yunwa suke ji , Ga uwar karuwai ta hana su zuwa baran da suke nemo abinci, La’asar nayi Abla takara guduwa wannan karan itama ilham bata bita ba. Tana idar da sallah ta ta’be jikin masallaci ko zata Samu sadaka amma har tagama bulayinta bata samu ko biyar ba , shiyasa ta nufi hanyar komawa gida abunta, tana shiga ta tarar da abunda ya tada mata hankali, da sauri ta karasa Wajan su tana tanbayarsu ina zasuje da wannan shigar, Anee na kuka ta soma magana “ Abla nagaji, bazan iya rayuwar yunwar nan ba, idan na kara awa d’aya banci abinci ba mutuwa zanyi , shiyasa na yadda da bukatar su Zinariyya, Sunce ba sex zasuyi damu ba, wasa ne kawai zasuyi, kuma zasu dunga biyan mu”, A firgice Abla ta saka salati “ Innalillahi wa inna ilaihi raji’un,me kuke kokarin yiwa rayuwar ku,bakusan hakan wata Babbar illace ba arayuwar ku, me zakucewa mahaliccin ku”, a kufule Husna ta kalleta“ Ya isheki haka IBTISSAM, ke komai kinfi kowa sani, ko ca’akai miki mu bamu da addinin ne, kullum mutum zai yi abu sai kin kawo naki, idan muka zauna da yunwa zaki bamu abincin da zamu dunga cine,ko zamu zauna kina hanamu abu yunwa ta kashe mu, na dad’e da fahimtar dama ba san cigaban mu kike ba , in baki sani ba ki sani yau bazan kara zama yunwa ta kashe niba , Nima dole na samu kudi, ga hanyar samun kud’i cikin sau’ki , idan ke bakya san rayuwar ki to mu muna so “ tana gama maganar ta taja dogon tsaki tayi wucewarta, Arwa da Anee ma bin bayanta sukai, ilham ce kadai ta Matso kusa da Abla “ kuncin rayuwar nan ta ishe mu Abla , Bamu da gatan da ya wuce mu samowa kan mu ‘yancin kai, bazan iya rayuwa cikin yunwa ba, duk da bamu dad’e da sanin juna sosai ba amma tabbas ke din Ablan muce me Kaunar mu, kin nuna mana soyayya irin yanda yaya take nuna wa kannanta” itama tana kai karshen zancen ta tabi bayansu Husna , zubewa Abla tayi a kasa tana faman nanata sunayen Allah, babu abunda bakin ta yake furtawa sai “ Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un” wannan masifa har ina,batasan lokacin da wani kukan ba’kin ciki ya kwace mata ba.

Leave a Comment