Books Reviews & FAQs

Lokaci Ne Hausa Novel Complete

1❤💛💚💜💙
Lokacine…
❤💛💙💜💚

® zuwairat (ummumaryam)

1⃣

Free page

Alhamdulillah…

Dedicated to my anty…

Cikin wata falo dake dauke da wasu Manyan mata akwatuna né na lefe akalla guda goma, sai budewa ake Ana yaba irin Kayan da aka zuba cikin akwatin,
“Oh wannan yaran da kashin arziki suke…ji wannan Kayan kaman bazaa mutu ba…” Inji wata middle age woman, wata mata ce ta sauko face dinta dauke da medical glasses ta saki murmushi for a second sai kuma ta daure face, da gani itace matar gidan but  am surprised why face dinta ke daure haka while wayanda ke duba lefe sai faman tofa albarkacin bakinsu suke, gefe daya ta koma ta zauna Tana latsa phone din hannunta Tana lumshe idanuwa, daya daga cikin matan da suke duba lefe ta Mike , da ganin matar kasan she’s her sister, dafa shoulder dinta tayi tace
“Wai sister meye haka?..Dan Allah ki saki ranki pls …kar a gane something is wrong with you..” Matar ta fada mata hannunta kan shoulder din matar gidan, idanuwa matar Ta lumshe tace
“Hmmmm wa ke bai San something is wrong ba?… Duk Wanda yasan ni yasan family din nan yasan something is wrong…” Matar Bata karasa ba ta Dora hannu kan lips dinta,
“Dan Allah ki bar cewa something is wrong…ki tuna wacce aka kawo lefenta ma is your daughter…me zata  ji if you show you’re not happy…” Ta fada mata cikin lallashi, matar gidan Dan Dora Kai Tana a hannunta sai hawaye, idanuwa sister dinta ta zaro yana cewa
“Pls ki Bari mana…pls ki Bari…nasan nan cikin mu babu bakuwarki amma pls me Aisha zataji.,she will feels you love Maryam more than her…” Matar ta fada cikin lallashi, sauran matan dake kallon lefe mikewa sukayi suka dawo kan matar dake kuka suka fara yi mata fada,
“Wai meye haka?.. Ke bakisan kaddara bane?… Duk sanda aka zo biki gidan nan sai kinyi wa mutane hauka…bakisan komai sai Allah ya yarda ba..” Wata babban mace Tafada mata cikin tsananin fada, ahankali matar dake kuka ta daga Kai ta kalli babban matar tace
“Yaya bazaki gane ba…mami wuya take sha a hannun kaka…Wallahi in har aka Kai mata wannan lefen ta gani sai tayi mata tas kaman ita ta Hana kanta mijin aure…Wallahi duk sanda ta ganta sai tayi mata gori…” Bata karasa ba yaya tace
“Dalla rufe mana baki… But taje tayi mata gorin mana..ai she’s her granddaughter..kuma Banda abinki gori har wani Abu né?… Yanzu kin zauna kina hawaye in mami ta shigo ta tarda ki haka sai tazo kuy tare kenan?… ” yaya ta fada mata, cikin kuka matar gidan tace
“Wallahi yaya na gaji…nan da wata biyu zan aurar da autata while yayarsu Tana zaune…Wallahi Sam bani da kwanciyar hankali har sai ranar mami ta bar gabana…” Matar ta fada cikin kuka, cikin rarrashinta wata yace
“Sister kiyi hakuri mana…kindai San babu irin kokarin da bamuyi kan almaranta ba…kullum cikin Rokan Allah muke kan wannan alamarin…sai mu jira muga ikon Allah…” Matar ta fada mata, shuru mai kuka Tayi amma tears basu daina fitowa ba, ba komai take tunani ba Illah first daughter dinta, her happiness her joy her pride, Tana mugun kaunar ta with her life, su biyar ta Haifa, the first born itace Maryam amma Ana kiranta da mami, she’s 32 Yanzu, followed by yazid Wanda Yanzu he’s 29 then asiya 26 Tay aure da yaranta biyu, sai Fatima 23 itama tayi aure da 1 child sa auta Aisha wacce is 21 one itace zatayi aure Yanzu amma ita first born din har yau bata yi aure ba, kome dai anyi, anyi sadaka, anyi adua anyi komai amma still shuru, bawai mazan basu Sonta ba, amma da Anzo wajen aure sai komai ya watse.  Horn akayi Kofar gidan matar dake kuka tayi saurin cewa
“Itace…” Tafada Tana mikewa da sauri, hanyar upstairs tayi da sauri while masu kallon lefe suka koma kallon lefen kaman nothing happened,

A bakin gate kam wata black Jaguar ce tsaye wata fara yarinya na zaune ciki Tana latsa horn, daga gefen ta kam bag dinta né sai farar riga irin ta doctors, face dinta dauke da glasses Dan siriri, face dinta look so beautiful and innocent, gaban goshinta kwance yake da wasu kananun gashi,  ganin tayi horn har sau uku ba’a bude ba yasa tayi relaxing cikin motar Tana cewa
” I know you heard my horn…ko me kake yi ka gama kazo ka bude…” Tafada cikin wani irin sexy voice, Tana lumshe idanuwan ta dake kama da na Mai Jin bacci, bayan kaman minti daya taga an bude gate din, Mai gadi né ke tura gate din kanshi daure da towel alaman daga wanka ya fito, Tana ganin an bude ta tada motar ta ta shigo ciki Tana tuki ahankali, Mai gadi ya dawo saitin glass din motar yace
“Hajiya kiyi hakuri Ina wanka né…” Yafada yana dariya, Dan murmushi ta saki Wanda yasa gefen cheek dinta lotsewa, wajen jerin cars ta samu available space tayi parking motar ta, bude motar tayi ta fiddo wasu Vincci slippers ta ajiye kasa Sannan ta zira legs dinta ciki ta fito rike da bag dinta, Maigadi dake maida gate ya kalleta tare dacewa
“Sannu da zuwa Doctor…” Ya fada mata yana kame mata kaman yanda ya sama as usual, kallon shi Tayi ta saki yar dariya before saying
“Ka bar wannan fadancin ban rago komai ba yau…” Tafada cikin dariya zolaya, Maigadin marairacewa yayi kaman zaiyi mata kuka yace
“Ai ba komai Doctor…da akwai gobe…” Yafada yana tale baki kaman zaiyi kuka, dariya Tayi tare da girgiza Kai  Dan koma bayan motar ta bude ta dauko wata Leda ta mika mashi, Da gudu middle aged man din yazo ya amsa yana cewa
“Anty na Allah ya biya maki bukatunki na alkhairi…Allah ya ya baki duk abinda kikeso duniya da lahira…” Yafada yana yaga ledar da hakorasa, dariya tayi tace
“Ameen…” Tafada Tana  kama hanyar falo, Maigadi da saboda dadin da doctor ke kawo mashi kullum yasa ko anyi Abincin rana aka bashi bai ci sai har Doctor ta dawo yaga in bata kawo komai ba sai yaci ya samu wurin ya zauna ya ware suyar data sha cabbage da su carrot ya lumshe idanuwa yana shakan kamshin Nama ya dauko daya ya Kai baki yana santi. Dan juyowa tayi ta kalleshi ta saki murmushi Sannan ta hau stairs uku ta isa varender, kofa falon ta bude walking like a princess Don ko kadan babu hayaniya tattare daita, she looks so calm and peaceful until she steps into the falo, dukkan matan dake falon juyowa sukay suna kallon ta some wearing a smile while others a wearing a sympathetic look, itama murmushi ta saki idanuwanta kan jerin boxes dake falon, gabanta né yayi mugun faduwa data tuna yau né za’a kawo lefen Baby wato Aisha, nan take face dinta ya Chanza but she’s trying to smile, karara abinda ke cikin ranta ya bayyana a face dinta,
“Mami har kin taso?..” Yaya elder sister din mom dinta ta fada, Dan murmushi ta sake saki Sannan tace
“Mommy Ina wuninku?..” Ta fada sounding calm, ni Kaina I was surprised danaji an kirata mami, alaman itace wacce mom dinta ke kuka kan she’s 32 amma ba aure, Nikam she don’t look 32 to me, duk da Tana da weight daidai and her height is average she look so beautiful and stunning,
“Lafiya lau ” suka amsa mata suna kallon ta, ita kuma ahankali ta shigo tsakiyar falon Sannan tace
“Mommies kuna Jin dadin ku…” Tafada cikin zolaya trying to look normal even though Tana tunanin Yanzu her last baby sister will be married in the next two months leaving only her and her immediate younger brother,
“Ke dai ce Mai Jin dadi…” Inji daya daga cikin su, dariya tayi Tana kokarin maida tears dinta tace
“Bari in hau upstairs and freshen up…zan sauko Yanzu…” Tafada Tana Kama hanyar stairs,  basu ce komai ba sai tausayinta daya cika ransu saboda sunga  what she’s trying to hide, Tana kaiwa stairs na uku  ta saki tears, kawai she just let them out freely like never before, da sauri ta wuce dakinta da gudu ta shige ta kulle kofa Sannan ta shiga bathroom ta zauna ta dinga kuka, kuka tayi like never before Don dukda Tana kuka almost every day because of her problems nayau yafi na kullum, she cried and cried and cried, she can believe her baby is getting married and, the baby she is eleven years older than, the baby da itace tamkar mom dinta saboda yanda take Sonta is getting married and still leaving her behind in their parents house
“Inna lillahi wa’ina ilaihi rajiun…” Tafada cikn matsanacin kuka,
“Ya rabbi meye laifina?… Ya rabbi why do you want me to be a laughing stock a cikin family…ya rabbi komeye laifina pls forgive me,,,this punishment is too heavy for me…ya rabbi ka garfata min…” Tafada crying very loud knowing too well that nobody will hear her cry, the bathroom has been a perfect pls to shed her sorrowful tears, kawai tunani take Yanzu in the next one year her baby sister will be a mother while she’s here yet tobe married, sai da Tasha kukan ta ta koshi Sannan ta sakarwa  kanta ruwa ta fito daure da towel, wata karamar box ta dauko daga karkashin gado ta bude ta dauki pills Tasha, it’s a pain reliever pills, duk yanda take Jin zafi a heart dinta data sha sai ta samu sauki, bayan ta sha ta koma bakin gado ta zauna duk gashnta a hargitse a face dinta, ahankali ta tura su baya ta Mike ta taka zuwa gaban mirror tayi tsaye Tana kallon kanta, ba yabon Kai ba tasan she’s beautiful, she’s so beautiful that she always thank Allah for making her this way, everything about her is moderate, ba’a ce mata short then you won’t call her tall, her skin color is so silky radiant, Tasan the problem is not from how she looks, at times Tana ganin matan da ko Rabin kyauwunta basu dashi d cute hubbies dinsu sai tace
“I wish me…” Take fada cikin ranta, ahankali ta Dan Shafa bismid cream dinta Sannan ta saka doguwar rigar material ta saka ta Dan kwanta saboda kar a gane tayi kuka, she’s so good in doing that, wato pretending nothing happened, pretending she’s alright even when she’s dying, Kara mikewa tayi ta je tayi unlocking door dinta Sannan ta kwanta, bayan kaman minti talatin da kwaciyanta aka Kira sallah asar, mikewa tayi feeling strong ta shiga bathroom tayi alwallah tafito tayi sallah tayi adua as usual Sannan ta tsaya gaban mirror ta karewa eyes dinta kallon ta tabbatar she looks alright Sannan ta fita kan babu komai, hanyar dakin mom dinta ta nufa tayi sallama Tana bude Kofar, mom dinta dake zaune kan praying mat looking weak ta daga Kai with a smile ta kalleta Sannan ta mika mata hannu Tana cewa
“My jewel har kin dawo?..” Ta tambayeta cikin so da kauna, ahankali ta taka ta zauna kusa da mom dinta ta Kama hannunta Tana cewa
“Yes mommy…Ina wuni?..” Ta gaisheta feeling so happy saboda duk yanda ranta ya bace in har zata gan mom dinta sai taji wasai, kullum tunanin is what will she have done without her mother, her mother never give up on her even for a minute, kullum she’s behind her, kullum cikin petting dinta take, at times Tana tunanin kilan saboda situation dinta take mata haka saboda kar taji komai amma kuma in taga yanda mom dinta keyi da sauran yan gidan kasan love is in her blood, she so much loves her children,
“Yau kin dawo da wuri..hope you’re alright…” Mom dinta ta tambayeta kaman  wata karamar baby,
“Mommy yau babu aiki da yawa…kuma Ai na Dan dade da shigowa…har nayi wanka nayi sallah…” Tafada hannunta cikin na mom dinta,
“Tou abinci fa?..” Ta tambayeta
“Mummy am not hun….” Bata Bari ta karasa ba tace
“Aa…muje…kici abinci…” Tafada mata Tana kokarin mikewa saboda kar taga tear dake taruwa idonta,
“Mum anjuma zanci…after magrub…” Tafada Tana jawo hannun mum dinta, komawa tayi ta zauna zata bude baki tayi magana akayi sallama tare da bude Kofar, yazid né ya shigo,
“Mommy and aunt…good evening…” Handsome cute guy din Yafada yana shigowa dakin, amsawa mom tayi wearing a lovely smile Sannan mami tace
“Sannu da dawowa…”
“Aunt ya akayi kika Rigani shigowa yau?…” Ya fada mata yana gefensu, he’s the only boy and ya Saba da zama cikin mata, kome zaayi tare dashi ake zama ayi, three years ke tsakanin shi da mami amma he calls her aunt, the whole entire family dinsu suna da Wannan respect din ga junansu, ko one month mutum ya baka dole ka saya sunanshi ka kirashi da aunt, yaya, brother da sauransu, family dinsu is among the largest and richest a family a Kano state, daka ce mai waazi family an San su, Maza har so suke su yi aure a family din Don su samu garagbasa saboda yanda suke hada yaran su da angon goma ta arziki,
“Kawai babu aiki sosai a office…how was your day?..”
“Hectic…na dawo kuma Yanzu am going out again…”Yafada yana lumshe idanuwa cikin gajiya,
“zuwa Ina kuma?..” Mom dinshi Ta tambayeshi
“Suhail né zai dawo…yace dole ni zan daukoshi daga airport…” Idanuwa mom dinshi ta zaro Sannan tace
“Wai har ya gama karatun?..” Ta tambayeshi
“Eh Wallahi…ya gama…”
“Oh ikon Allah kaman jiya fa ya tafi…Alhamdulillah…saidai Yanzu ganinka sai ahankali tunda besty is back…” Mami Ta fada,
“Ai I can’t wait to see him…dukda he’s angry at me wai banzo Lagos na tarbeshi ba kafin mu taho tare…”  Yafada yana mikewa,
“Kaci abinci né?..” Mommy ta tambayeshi,
“Aa Bari in naje chan zanci…” Yafada Sannan ya bar dakin, bayanshi suka bi da kallo both wearing a smile.

Marigayj alhaji Muhammad Mai waazi is a great man of honor, yana da mata hudu inda ko wacce mata sai da ta haifi yara goma plus, family house dinshi is well known by prominent people saboda shi babban mutum né Mai halin kirki kafin ya bar duniya, kafin ya bar duniya babu abinda ya fadawa yara shi sai dai kar su kuskura su bar zumunci nor matter what, Sannan in ba dole ba bayason duk zuriar shi suyi nisa da juna, and Alhamdulillah dukda bai duniya yaranshi da suka rage su 37 basu bar zumunci ba Don duk end of the month sai anyi family meeting inda ko Ina kake an nor matter how busy you are dole kazo da family Dinka, except in Baka country din zai wuceka, duk matan alhaji Mai waazi sun rasu sauran daya tal wacce suke Kira da kaka, wato mahaifiyar dad dinsu mami, she’s the youngest wife of alhaji Mai waazi, Yanzu she’s the controller of the family affairs, ko fada akayi a family itace Mai sasantawa, Tana zaune né a makeken gidan alhaji Mai waazi, duk yaran  suna respecting dinta tunda bata juyawa kowa baya ba, she takes all as her own amma don’t get in trouble with her, she’s as hot as fire Don duk family meeting da za’a yi a gidan akeyi itace a head table, dukda She’s old she knows how to handle duk Wanda yayi ba daidai ba hakan yasa duk tsoron yin laifi suke daga yaran har jikokin, duk family din zamansu is so sweet and suna supporting din juna sai dai matansu Wanda suka auro daga waje ke gulma da small talks Wanda ba’a rasawa a duk family.

A airport Karfe biyar jirgi ya iso daga Lagos, mutane suka sauko cikinsu har da wani saurayi Mai shegen kyau siriri dogo fari tas, rike da bag din puma, yana sanye da dark blue jean sai red polo Wanda ya amshi jikinshi kaman hauka, face dinshi dauke da glasses baki, tafiya yake cikin kwanciyar hankali, bayan ya fito daga cikin airport ya taho hannunshi daya rike da bag duk babe din data ganshi sai  ta sake kallon shi for the second time, wannan suhail kenan, the cutest of the waazi’s family kaman yanda ake ce mashi, yazid dake zaune bayan motanshi na ganinshi saurin direwa daga bayan motar ya nufo shi, suhail na ganin shi ya wani kauda Kai kaman bai San da kowa ba wajen, dariya yazid yayi yasan he’s angry at him
“Cutest meye haka Baka ganni bane?..” Yazid Yafada yana dariya, suhail cire glasses dinshi yayi ya kalleshi from head to toe Sannan yace
“Do I know you?..” Yafada yana rolling idanuwa kaman mace, dariya yazid ya sake yi yana cewa
“Wallahi Baka da mutunci…ko abinci banci ba …direct daga offfice na wuto daukan ka shine kake yi min haka?.” Bai Karasa suhail yaja tsoki before saying
“Do you think saying that will make me think am important to you?….you left me stranded in Lagos…” Yafada cikin wata husky and sexy voice, dariya yazid yayi before saying
“Wane irin I left you stranded…ai I never told you zanzo…” Bai karasa ba suhail ya katseshi dacewa
“You see?… Exactly why I said you don’t fucking care about me…na bar kasar nan for the pass four fucking years and na dawo bazaka iya zuwa Lagos tarbata ba?..” Dariya yazid yayi da karfi saboda yanda yake cewa fuck this fuck that Sannan yace
“Allah kaka taji ka kana wannan fuck din sai kaci ubanka…Dalla give me your bag…” Yafada yana Jan bag din daga hannunshi, rungume juna sukayi suhail yayi mashi kiss a wuyanshi yazid yayi saurin janyewa yana cewa
” kazama Dan iska Wallahi…Dalla mu tafi gida…” Yafada yana bude mota, shigewa yayi shima suhail ya  shige tare da relaxing.
“Wallahi I miss you…” Inji suhail
“Anya ka kaini?..” Yazid ya amsa mashi. Suna cikin hirar nishadi suka iso gida, horn yayi a bakin Kofar aka bude mashi gate, mutane né sunfi su shabiyar a compound din , mostly yanmata né daga family dinsu wayandan suka San da zuwan shi sunzo yi mashi Sannu da zuwa, yana fita daga cikin mota suka tafi riiii saboda yi mashi Sannu da zuwa, kaman wani yaro yayi saurin komawa bayan yazid,da yazid yayi step shima sai yay step, hannu ya dinga daga masu yana cewa
“Ji wannan yaran sun zama manya…abun ba wahala…” Ya fada yana leko su, sai kallon shi suke suna yi mashi Sannu da zuwa
“Weird fellows…” Yafada under his breath while smiling at each and everyone of them,.

Share
2❤💛💚💜💙
Lokacine
❤💛💚💜💙

 

® zuwairat (ummumaryam)

2⃣

 

Free page

 

Dedicated to my anty, lobi  you die

Haka ya dinga boyewa bayan yazid yana daga masu hannu yana murmushi while shi yazid yana dariya har suka isa falo, nan ma wasu families né zaune suna jiran shigowan shi, wata mata na gani Baka Mara tsawo sosai ta taho da saurin ta, da gudu suhail ya fada jikinta yana kissing face dinta, da sauri matar ta tureshi Tana goge face dinta Tana cewa
“Wallahi sai kaci ubanka…” Tafada but laughing dariya duk mutane dake falon sukayi yace
“Haba mommy shikenan haka zaki tarbeni?..” Yafada kaman zaiyi kuka, dariya Jin dadi ta saki ta mika mashi hannu alaman yazo, ahankali ya Kama mata hannu ya rungume ta,
“Mommy I miss you so much…” Yafada mata,
” Nima haka….ya kake ya hanya?..”
“Alhamdulillah mommy..” Ya fada mata wearing a lovely smile,  Dan juyawa matar Tayi taga yazid, nan take face dinta ya Chanza for a second Sannan kuma ta saki murmushi which is clear its not deep,
“Mommy Ina wuni?..” Yazid ya gaisheta
“lafiya…” Ta amsa mashi atakaice Sannan ta juya ga suhail tace
“Wai meyasa kaki azo daukanka?.. Wa ya daukoka?..” Ta tambayeshi kaman bata ga yazid rike da bag din suhail ba,
“Ai mommy besty ya dauko ni…wai Inna abba?..” Ya tambayeta,
“Bai dawo daga office ba…” Ta amsa mashi. Sauran family dake cikin falon gaisawa sukayi da suhail ya amsa masu looking so happy amma ko kadan bai son wannan never ending greetings,  bayan sun gama gaisawa ya shiga part dinshi tare da yazid yayi wanka sukaci abunci ya suka koshi Sannan ya kalli  yazid yace
“Muje gidansu humaira..” Mika yazid yayi yace
“Wallahi bacci nake ji…” Bai karasa ba suhail yace
“Aa babu wannan zancen..Dan Allah muje mudawo..I can’t wait to see her…it’s been a while,,,pls…” Ya rokeshi,  kaman yazid baiso ya Mike ya dauki mukullin motarshi suka fita zuwa gidansu humaira…humaira cousin dinsu ce, wato yar kanin baban yazid, daman dad din yazid da dad din suhail are not from the same mother, kowa da uwarshi amma dad dinsu daya, humaira is suhails love, suna kaunar juna sosai kaman they can’t stay without each other, a family humicute ake kiranta saboda suhail, suhail yaso ya aureta kafin ya tafi karatu abroad amma she’s just 16 lokacin, shi kuma 25, duk haukar da yayi dole ya hakura saboda family dinsu basu yarda su aurar da yarinyar da bata haura 18 ba, saboda hanashi aure da akayi yasa har yau yake Jin haushin kaka saboda itace tace bazaa yi ba wai dole subi doka,  bayan sun yi tafiya for like forty minutes yazid ya tsaya a wata gate yayi horn, Maigadi né ya bude ya shiga yayi packing suka fito, gidan na dauke da parts buda uku, babban ciki suka nufa, sallama sukayi falo suka shiga matar gidan da wasu family suna zaune
“Cute Yaushe ka dawo?..” Inji wata cikin mutanen falon,
“Yau…ban dade da dawowa ba…” Yafada cikin respect, basu dade da shigowa ba wata very pretty slim girls  dake sanyi da skirt da Riga na atampa ta sauko daga upstairs da sauri Tana cewa
“Yaya Sannu da dawowa…” Suhail daga  Kai yayi ya kalli budurwa for a moment Sannan yace
“Ashe kika nan?.. Ni I was thinking kinyi aure Wallahi…” Yafada idanuwanshi cikin nata, baki yarinyar ta tale kaman zatayi kuka Sannan tace
“Yaya ni ka fadawa haka?..” Tafada Tana nuna kanta, duk mutanen wajen dariya sukayi suna kallon su,
“Eh mana..bake kikace aure zakiyi ba?.. Kince tunda naki saurin dawowa wani zaki aura..what are you still waiting for…” Yafada cikin zolaya, da sauri yarinyar ta rufe face dinta saboda kunya Sannan mutane wajen are all looking at them especially mom dinta Tana mamakin rashin kunyashi ,
“Yaya yazid Sannu da zuwa…” Yarinyar Ta fada Tana turo baki,
“Yauwa humaira ya kike ya karatu?..”
“Alhamdulillah…” Ta amsa mashi Tana zama kan daya daga cikin kujerun falon, suhail kallonta kawai yake he can’t believe humaira ce ta koma haka, she’s so tall and beautiful,
“Bazaki basu ruwa ba?.. Ko sai an fada maki?..” Inji mom dinta, da sauri ta mike suhail yayi relaxing yana kallon yanda take tafiya kaman batason taka kasa, Bayanta yabi da kallo yazid yadan ta bashi tare dacewa
“Mom is looking…” Ya rada mashi, , murmushi ya saki tare da sauko kanshi, drinks ta kawo ta zubawa kowa ta mika masu in the process da zai amsa  ya hada da hannunta tayi saurin zarewa,  dariya ya saki ita kuma ta koma ta zauna, drinks suka sha bayan kaman minti ashirin suka Mike tare dayi masu sallama, da sauri humaira ta dauko vail da wayarta hannunta ta fito ta samesu a bakin motar yazid, suhail kallon yazid yayi yace
“Pls ka shiga mota…zamuyi magana…” Yafada mashi yana kallon humaira, Kai yazid ya girgiza Sanin halin besty and brother dinshi, shigewa yayi suhail yace
“Mine i miss you sosai,,.wallahi kullum cikin counting day nake all because of you…” Yafada mata sounding so cute, Dan murmushi ta saki Sannan tace
“I miss you too…” Tafada Tana turo mashi baki, kallon kawai yake ko blinking baiyi
“Baby you’re so pretty and big….am happy I choose you…nidai Yanzu baby no more delays..kawai zan yiwa dad maganar auran mu…lets see the excuse da kaka zata sake bayarwa…” Yafada sounding serious,
“Hmmm yaya Dan Allah kayi hakuri in gama school…besides you just get back today…pls yayana…” Ta fada mashi, daure fuska yayi yace
“Lallai ma….wato Inyi hakuri ki gama school…gaskiya I don’t want to take any Chances…kawai lets get married then you can continue…if we like kar ki haihu har sai kin gama nysc dinki…pls baby na…” Yafada mata cikin rarrashi,
“Haba yayana..yau fa ka dawo…” Bata karasa ba yace
“Pls kar in sake Jin wannan yau na dawo din nan….did I trek from England to Lagos or da kafa nazo daga Lagos?.. Nidai pls in kin San you’re no more interested in me tell me…am not getting any younger here…” Daga Kai tayi ta kalleshi tace
“Yayana why will you say such a thing?… Why will you say am not interested in you?..ni da kullum da tunanin ka nake kwana nake tashi…”Ta fada kaman zatayi mashi kuka,
“Tou baby am sorry you’re confusing me..,if really in damu kaman the way na damu dake you won’t want to spend one more second without me…nidai Yanzu zanyiwa dad magana yau din nan…or better still wurin kaka zani…I will tell her na dawo kuma Yanzu you’re 20… Kawai muyi aure…” Ya fada mata sounding so commanding, tasan if zancen nan yaje wajen kaka it’s over the moment she accepts, shuru tayi batace Komai ba kanta kasa,
“Baby pls tell…” Bai Karasa ba wayarta ya fara ringing, idanuwa humaira tayi rolling alaman she knows who’s calling, suhail tsayawa yayi yana kallon reaction dinta, ganin bata da niyyan piçking yasa yace
“Baby pick up mana…” Yafada trying not to get angry because he’s temper is the worst part of him, kaman bataso tayi piçking tace
“Pls I will call you back..am busy now…” Tafada atakaice bata jira response din caller din ba ta katse wayarta, surprise look suhail yayi mata yace
,”baby  who was that?..” Ya tambayeta kishi na forming cikin mind dinshi,
“Yaya it’s my course mate..” Ta amsa mashi not looking at him, he wants to say something sai kuma yayi shuru, yasan four years ba wasa bane, and a beautiful girl like her will have many suitors amma he believes she belongs to him,
“Pls soulmate if you’re having any relationship with ko waye stop it..na dawo…I promise I won’t blame you..Don haka ki katse duk wata dangantaka dake tsakanin ki dasu..if you’re thinking am not coming back for you and decided to get another one am back..kinji kou?..” Yafada mata sounding so calm, ahankali ta daga mashi Kai,
“Tou ubana..” Ta fada cikin ranta,
“Zan tafi…I bought something for you…yana gida..I was in a hurry to see you..she’s yasa na mance ban dauko ba…gobe zan kawo maki…” Yafada mata,
“Wow yayana na gode….” Tafada kanta kasa not looking at he’s killer eyeballs,
“Meye na godiya kuma?.. Ni Wallahi attitude dinki is changing…kaman an Chanza ki Wallahi?..” Ya fada yana tuna kafin ya tafi karatu yanda she’s so lively and look at him direct in the eye da kuma yanda lokacin komai har abunci suna ci tare, Tana zuwa gidansu duk holiday tazo part dinshi susha wasa and Allah ya taimakeshi he never does anything stupid with her, amma Yanzu she looks so cool and Allah knows bayason cold person,
“Ai yaya lokacin da Yanzu is not the same…” Tafada mashi kanta kasa,
“What’s the difference?..” Ya tambayeta yana tuna yanda ta rikeshi gam a Lagos airport lokacin da zai tafi,
“Ai yaya lokacin ban San ciwon Kai na ba…am a child…” Gira daya ya daga yana kallon ta,
“Yanzu kuma na girma…” Tayi adding,
“so you are telling me indirectly that duk abinda ya faru tsakanin mu is child’s play?..” Ya tambayeta sounding angry, horn yazid dake cikin mota yayi mash ganin anyi sallah magrub su basuyi ba, afusace suhail ya juyo yayi dakuwa yana cewa
“Am taking here” Yafada mashi da karfi sounding angry, agogo yazid ya nuna mashi daga inda yake zaune cikin motar,
“Go if you’re in a hurry…” Ya fada mashi atakaice, humaira murmushi ta saki kanta kasa, juyowa yayi gareta ya sake cewa
“So what happens kafin in tafi is out of childishness?…” Ya sake tambayan ta, ahankali ta girgiza mashi Kai Tana cewa
“Ba haka bane…kawai dai Abunda nayi a wannan lokacin I can’t do it now…” Ta fada mashi calmly,
“Like what?..ai gani nayi babu wani mugun Abunda mukeyi except play…” Ya fada mata sounding angry,
“Yaya kayi hakuri don’t miss quote me pls…” Ta fada mashi cikin respect,
“Ba komai…Yanzu zan tafi..sai munyi waya..” Yafada mata yana juyawa,
“Yayana..” Ta kirashi cikin zakin murya, ahankali ya juyo ya kalleta,
“Yaya pls kar kaje wajen kaka pls,,,ka Bari tukun na…” Ta fada mashi,
“Pls I need to hear one thing from you…do you still love me?..” Ya tambayeta Kai tsaye, ahankali ta daga mashi Kai, Sam baison wannan kunyar nan nata, gani yake zai kwaru if she continues like this,
“Then don’t ever tell me kar naje wajen kaka…do you understand?..” Ahankali ta daga mashi Kai,
,shikenan nan na tafi…” Ya fada mata cikin sanyinmurya yana kallon how she’s look at her phone alaman message just entered, shuru yayi ya shige mota amma deep down he’s angry, yazid dake tuki kallon yanda ya gumke baki yayi yace
“Cutest what’s going on in that thick brain of your?..” Ya tambayeshi while concentrating on the road, Dan tsoki suhail yaja ya harde hannunshi a chest dinshi tare da relaxing,
“Bazaka fada ba kenan?..'” Yazid ya sake tambayan shi,
“Kawai am angry né,,,bangane kan humaira ba…nikawai ka kaini gidan wannan masifaffar tsohuwar…Mara mutunci kawai…” Suhail ya fada yana Jan wata tsokin, dariya yazid yayi yace
“Kai Kay hakuri mana…matsalar ka kenan..lack of patience…you just get back today…” Yazid Bai karasa ba suhail yace
“Exactly what humaira is saying that is getting me angry…ku bar ce min Yanzu na dawo…kafi kowa Sanin bana son delay…one minute delay can cause regret of a lifetime..kawai take me to gidan wannan kakar…” Yafada face dinsh daure,
“Naji…amma kuma kasan too much saurin aikin shaidan né kou…”
“Kanka akeji…” Suhail ya fadawa yazid atakaice,
“Thank you..now tell me…what did humaira do? ” yazid ya tambayeshi
“Nidai Wallahi am thinking batasona kaman before…Wallahi besty bansan inda zan saka Kaina ba in har humaira ta gujeni….tunda na bar kasar nan ban taba complete one hour without the thinking about our moment together ba..amma now she’s telling me wai she’s was a child lokacin..gaskiya hakan brokes my heart…” Yafada kaman zaiy kuka
“Haba cutest…kasan humaira is yours fa… She loves you Sosai…in tayi two days batayi magana da Kai ba ni take takurawa tace I have to find out if you’re alright…so nasan humaira loves you more than she loves herself…” Yazid ya fada mashi cikin kwanciyar Hankali, idanuwa suhail ya lumshe tare dacewa
“Then why is she giving me cold attitude…Wallahi I was thinking she will run and hug me..amma sai tayi tsaye Tana cewa yaya Sannu da zuwa..mtwss…” Dariya yazid yayi har da rike ciki saboda yana suhail ya furta maganar
“Wallahi you’re so funny…haba Yanzu gaban parents dinta kakeson ta rungume ka?..”
“Ai am her brother…she should show me love…” Yafada sounding funny, dariya yazid yayi har da buga staring yana cewa
“Lallai…gaskiya Ina zargin turawa sun watsa ka…”
“Tab Allah ya Sauwake…” Ya fada mashi atakaice,

Kasa mommy da dr suka sauko tare, sisters din mommy basu tafi ba sai bayan sallah magrub, zama dr mami tayi ta kurawa waje daya Ido aka bude kofa, ahankali ta juya ta kalli door din Aisha ta shigo da alaman daga unguwa take, da gudu Ta fada jikin Doctor, itama hannu ta ware mata ta rungume ta Tana zaune kan kujera while baby na zaune kan kafarta, makale mata tayi gam ita kuma mami Tana Shafa kanta ahankali, sunfi minti goma ahaka Sannan Aisha ta daga kanta ta kalli lefen a aka kawo ta fashe da kuka,
“baby if you don’t want me to be angry at you right now ki goge face dinki…” Mami ta fada mata saboda tasan reasons dinta na kukan, she have been crying a lot lately, kullum cewa take she wish anty mami ce zatayi aure ba ita ba, at times har cewa take ita ba zatayi aure ta bar anty mami gida ba, ita kawai in Maza sunzo sai ta koresu, saida akayi da gaske ta amine zatayi aure,
“Anty…” Hannu mami ta Dora kan lips dinta tace
“Shuru…Yanzu baby ki tashi mu dubo lefenki…daman zaman da nayi kenan…” Tafada Tana kokarin turata daga kan kafarta, makale mata baby tayi Tana cewa
“Anty Ni Wallahi na fasa…” Da sauri mami ta buge bakinta Tana cewa
“Wato Yanzu baby baki Jin maganata kou?.. Gardama kikeson yi min?..”Aisha dafa bakinta tayi Tana kuka Sannan ta girgiza mata Kai Tana cewa
“Sorry aunt…ban karawa…” Ta fada mata, ahankali mami tayi kissing din kumatunta Sannan tace
“Tashi mu duba…” Dan mikewa baby tayi daga kafarta suka nufi inda akwatuna suke, kasa mami ta zauna gaban akwatuna ta mikawa baby hannunta zauna kan kafarta Sannan mami ta bude daya daga cikin bags din,
“Kai my baby tayi goshi…baby kayanki sun hadu…duk family babu Wanda kayanshi ya Kai naki kyau…my baby is a lucky princess…” Tafada Tana daga tilin manyan laces dake cikin akwatin, baby rushewa tayi da new tears Tana cewa
“Anty pls ki Bari….” Tafada cikin matsanacin kuka,
“Baby Dan Allah in ba so kike Nima Inyi kukan nan ba kiyi shuru…pls…” Tafada voice dinta na rawa, ahankali ta goge face dinta Tana cewa
“Anty bani son kiyi kuka…kawai anty Ina bakin cikin zanyi aure ke bakiyi ba…anty Wallahi nasan har in bar duniya bani da farin cikin daya wuce inga kinyi aure…” Yarinyar Ta fada cikin matsanacin kuka, idanuwa mami ta lumshe sai hawaye, tunda take bata taba kuka gabanta ba sai yau, she has always try to be strong, she has pretended that it’s nothing Ai after all meye cikin aure if not takura, but deep down she wants to feel what people are feeling, baby daga face dinta Tayi taga Tana kuka sosai,
“Way yo Allah na anty ki bar kuka,,,anty kiyi shuru…pls anty..” Baby Ta fada Tana rike da face din dr mami, yau kam batayi shuru ba, kuka tayi tayi har ta koshi, mom dinsu né ta fito daga kitchen rike da plate din abinci, Tana ganin su tayi saurin ajiya abuncin kan dining ta nufosu Tana cewa
“Lafiya?..” Ta fada jikinta na rawa, Don itama bata taba ganinta zaune Tana Tana kuka this loud ba, matar durkusawa tayi ta daga jaw dinta tace
“Jewel lafiya?..” Ta tambayeta cikin tashin hankali,
“Mommy…” Mami ta Kira mahaifiyar su,
“Naam…menene pls…”
“Zanyi missing baby…” Tafada diverting from the real fact,
“Haba jewel sai ki zauna kuna kuka haka?..Dan Allah ku tashi…” Matar ta fada mata knowing to well this is not her real  reason for crying, ahankali baby ta Mike daga kan kafar mami ita kuma mami ta Mike still crying, hanyar upstairs tayi mom dinta ta kalleta tace
“Jewel baki ci abuncin ba…” Ahankali ta juyo da wet face dinta ta kalli mom dinta Sannan tace
“Mommy bani da appetite…I can’t even swallow my own saliva…” Ta fada cikin sanyinmurya
“Anty kizo muci tare Dan Allah..nasan tunda kika dawo daga office baki ci komai ba…” Aisha Tafada mata.
“Baby naci Abinci…nasa an sayomin abinci dazun a office…kawai kije kici kinji babyna…” Tafada mata calmly,
“Tou shikenan Nima bazan ci ba…” Aisha ta fada Tana harde hannunta a chest dinta, dan murmushin Karfin Hali mami ta saki Sannan ta goge face dinta ta juyo, inda baby k tsaye taje ta Kama hannunta Tana cewa
“Kizo muci Abincin…” Tafada mata, dadi mom dinsu taji ta koma kitchen Ta sake debo abinci ta zuba masu saboda na farkon bai da wani yawa. Zama sukayi sukaci mami Tana feeding baby sister dinta, daman ko a baya inda mami tanason Aisha taci abinci sosai ita ke zama tayi feeding dinta, bayan sun gama suka hau upstairs dakin baby tace
“Ki zauna am coming right back…” Tafada mata Sannan ta fita, dakin mom dinsu ya shiga ya bude inda ta ajiye maganin da aka Kawo mata daga maiduguri ta debo ta zuba cikin cup dake kan fridge ta zuba madara ta dama Sannan ta fito, daman mom dinsu tace ta bar mata wannan aikin Don Aisha bata yarda Ta amsa tasha sai in mami ta bata, wani irin so sukewa junansu, first born da auta,  fitowa tayi ta shiga dakin baby tanacewa
,”na dawo sweetheart…” Tana ganin hannun mami ta tale baki Tana cewa
“Wayyo Allah antyna…banason wannan abun…” Tafada Tana buga kafa da kasa, Daria mami tayi Tana cewa
“Babyna bakisan wannan shi zai sa angon yaji babu kaman ki ba?..” Tafada cikin zolaya, da sauri baby ta rufe face dinta Tana cewa
“Wayyo anty am shy….Ki Bari…”
“Naji babyna…ki amsa kisha…” Ta fada Tana shiga dakin, kaman bata so ya amsa ta kafa Kai, sai da ta shanye tas Sannan ta daga Kai ta mikawa mami dake tsaye Tana Shafa Bayanta cup, ruwa ta dauko mata Tasha,
“Yauwa sweetheart..yi sauri kiyi sallah..Nima Bari Inje Inyi..” Ta fada mata Tana fita daga dakin rike da cup din.

 

Leave a Comment