Books Reviews & FAQs

Tarbiyya Hausa Novel Complete

🌲🌲TARBIYYA🌲🌲🌲*

 

*©NABEELA DIKKO*

 

*PEN WRITERS ASSOCIAON✍🏻*

 

_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM._

 

*GABATARWA* _Dukkan yabou da godia sun tabbata ga Allah ubangijin tallikai,Salati maras adadi zuwa shugaban mu Annabi (SAW) da alayensa da sahabbansa ba ki daya,Allah yaqara mana rai da lafia da ikon fadakarwa akan turbar Manzon rahma Ameen._

*TSOKACHI* _Wannan littafi na TARBIYYA na rubuta shi ne domin ilimantarwa, fadakarwa, da tunatarwa,Bugu da kari na tsara salonsa domin nuni da halaye masu kyau da maras kyau,wadanda sukaci karou da addini musulunci,Banyi domin wani ko wata ba,Labari ne kirkirarre kuma kagagge,Duk wanda ya ga ya ci karou da halayensa ko dabi’un sa to ya sani Arashi ne kawai._

 

*GARGAD’I* _Ban yarda wani ko wata ya canja min Labari ta kowacce fuska!,Matsawar ba tare da izinina ba!Duk wanda ya aikata hakan to ya sani shi barawoun fasaha ne,kuma Mai aikata aiki maras kyau,Allah ne gatana kuma shine wanda zai sakamin._

 

*SADAUKARWA* _Ga Iyayenah Abin Sona,Abin Kaunata, Abin Alfaharina,Rabbil izzah yaqara masu rai da lafia tare da nisan kwana,Ya rahman ya sadasu da rahmarsa, fatana Aljanna ta zamou mazauninsu na har Abada Amin._

 

*SHAFI NA D’AYA*

 

*SHIMFID’A* Da farko Ita dai *TARBIYYA* Abi ce mai muhimmanci a rayuwar Al’umma,A wannan zamani da muke ciki, Hakika *TARBIYYA* Tayi karanchi a rayuwar mu,Idan mukayi la’akari da tsantsar so da kauna da iyaye ke nunawa yaran su Ayau,Hakan agefen yara suna yawan ajiye halaye da dabi’un gidan su agefe suna aikata abubuwa son ransu….Anan na kanyi nazari akan shin meye *TARBIYYA?* Lalacewar ta da tabarbarewarta laifin waye? iyaye ko yaran?ku biyoni…ni ce taku Mai kaunar ku *Nabeela Dikko* domin sanin yadda zata kaya,Shakka babu *TSANSAR SO* ne ya sanyani nake subourboudou maku littafai masu ma’ana….Banda zabi akan ku masoyana *MATAN AURE* da ‘yan mata,na nesa da na kusa domin *MATA JIGON AL’UMMA* ne,Kuma su Abin girmamawa ne akoda yaushe,Ina baku shawara ku rike hakuri saboda halin *WATA RAYUWAR….* Domin *IDAN AN CIZA HURAWA AKE* Duba ga Ukuba irin ta wasu *DANGIN MIJI* Da sannu zata zo karshe,Kamar yadda *ALMAJIRANCHI KO AIKATAU* zai zamou labari nan ba da dadewa ba,Dama caan ita *BAK’AR AK’IDA* Abin gudu ce,Allah ya dauramu Abisa tafarkin gaskiya,Ya bamu ikon yiwa yaranmu *TARBIYYA* mai kyau Ameen.

 

______________________________________
“Sunana Nadiya Bello, Wanda akafi sani da suna Balarabe,saboda fari ne sol, kamar zubin larabawa.”

“Mafi yawan kawayena na firamare da sakandare sunfi Kirana da (Naddy Balarabe),”

“Tun Ina karamata na Tashi da nutsuwa gashi ,Allah yayi min baiwar kyau da farin jinin jama’a,shiyasa bakin mutane yayi yawa akaina,saboda tsabar kyau na,Iyayena akullum cikin zuba min addu’a suke, Kasancewar ni kadai ce, Allah ya basu a duniya!”
“Hakika iyayena sun inganta rayuwata, tun yarinta ta har kawowa girmana, suna bani TARBIYYA Mai kyau tare da bani cikakkiyar kulawa,”Shiyasa akullum nake alfahrin Samun su arayuwata,”

“Sunan mahaifina Mallam Bello, asalin sa fulanin Sudan ne, fari ne tatas Mai kyaun gaske gashi da kwarjini Duk inda ake neman dattako to idan aka sameshi ansamu,dalilin shi farine tas shine kowa ke kiransa da Balarabe,Amma sunan iya Nigeria ne, sanadin hakan sunansa na ainihi ya bace bat,
” Assultaan shine mahaifinsa ya mutu da dad’ewa bayan yayi wafati ne ya dawo Nigeria da Zama…,kasuwanci ne ya kawo mahaifina Nigeria,Har ya gidadan ce anan,duk yan uwan mahaifina suna caan kasar Sudan,Dalilin kasuwancin da yakeyi na sayar da gwanjou,”
“Watarana gurin tafiye-tafiyensa yaje cin babbar kasuwar nan ta garin kalgo da ke jihar kebbi,

“To anan ya hadou da Ard’ou dakin gari,daga nan suka kulla abota, Mai karfi da inganci tare da amanar juna atsakanin su,Balarabe ya zamewa Ard’ou aminin gaske,bayan wani lokaci Ard’ou yayi masa tsaye batare da binciken sanin Ahlinsa ba, ya baiwa Balarabe auren kanwarsa da ya ke riqou bayan rasuwar iyayensu wato fad’imatou(Innarei)wato mahaifiyata kenan.”Itama kyakkyawar gaske ce.”Shiyasa agefen uwa da uba na gado fari da kyau bana wasa ba.”Mamana da Babana suna zaune lafiya babu Mai jin kansu,Domin halayensu sun zou d’aya mutanen kirki ne sosai.”Shiyasa da suka sameni suke inganta rayuwata da TARBIYYA, Bayan tsawon lokacin da suka d’auka basu samu haihuwa ba,Duk da soyayyar da suke nunawa agareni bai Hana su kula Dani ba tare da hukunta Ni idan na aikata laifi,”

” Har yanzu mahaifina bai daina sana’ar sa ba wacce da ita muke ci da sha kuma acikin ta na kammala karatuna firamare na sakandare, Wanda Halin yanzu babana yana kokarin yaga na d’ane gurbin jami’a.”A kwalejin shehu shagari da ke garin sakkwato.”

“Dukkan mu muna rayuwa a jihar kabi,A garin argungu cikin unguwar tudun wada.”Na samu kulawa da Mai kyau awurin iyayena, ilimin islama da na zamani sunyi kokarin bani.”Haka suna saka min ido akan dukkan al’amurrana,da duk wani motsi na musamman Mamana,wacce komai nawa akan idon ta yake har alakata da abokaina duk mamana tana sane.Bana Komai sai da saninta ko Kuma izinin su, Domin akwai yarda da aminci atsakani na da su”

“Shiyasa na kasance abin so ga kowa, da kuma alfahari awurin iyayena da malammai nah,har ma da mutan unguwa Duka Kowa Nadiya.”Domin na zamou daga cikin Yan matan unguwa,”,masu nutsuwa ladabi da biyayya zan zamou ta daya, da zarar ka zAuna Dani na dakika zaka fahimciina da kirki da mutunci duka sun yalwatu arayuwata,”

“Nadiya..!Nadiya..!Kiran da Mama ke mani NE ya fargar da ni daga tunanin wacece Ni..”

“Da hanzari na amsa da na’am mama,gani nan.”

“Da sauri na fitou daga dakina zuwa Dan yalwataccen filin gidan mu, inda mama take zaune a tabarma,dake shimfide karkashin bishiya,rediyo ne ajiye gefenta tana sauraren gidan rediyon nan Mai farinjini wato Equity fm birnin KEBBI inda suke Shirin Nan na IN DA RANKA.”

“Fuskata mama ta duba, tana murmushi tare da rage karar rediyon…”ta ce ”yooo ni…Nadiya wai sai yaushe zaki daina kumshewa acikin daki kamar kunshin kaya ne!?…”

“Mama kiyi hakuri zan daina zaman d’akin..nace da alamun damuwa!”

“Ni kinga,idan ma kin cigaba ke zakita rub’a!”yanzu kije gidan lantana ki amso min sako.”Kice mata Ina gaidata, Nace ta baki sakon, ki kawo min,kuma karki Jima nasan dai mutuniyar taki na makaranta”inji mama

“To,mamana, an gama,nace Ina dariya domin idan da sabo na saba da sauraren fadan, yawan zaman da nake daki,,Wanda ya zame mani jiki..Nan dai na dauko hijab Dina,na fita zuwa makotan mu domin amso mata sakonta.”

 

Muje zuwa fans wasa farin girki🤙🏼
*Yar mutan Dikkawa ce*

*SHAFI NA BIYU*
______________________________________
Gidan su Hajiya Lantana(Kawar mamana) na nufa,da sallama na shiga gidan, hanyar da zata sadani da kofarta na nufa, da yake su biyu ne, A gidan ita da Abokiyar zamanta Laraba, sai dai ba wani zaman lafiya suke ba,zaman su irin zaman nan ne, na doya da manja,kuma laraba ce Mai matsala,”A tsakar gidan ko nasami laraba, tana daka a turmi tana wakokin ta na habaici,,duk da ta ji sallamata Amma sai tayi banza dani ta Cigaba da aikinta,Da sanyi na gaidata da girmamawa,sai dai wata uwar harara ta zabga min, Domin tasan inda wacce nazou wato lantana, shine bazata amsa min sllamata ba,”Sai ma Kawar da kanta da tayi gefe cike da masifa,”
“Shiyasa ma taki ta amsa min sallama ta da gaisuwa,Sum sum na wuce nikam,Harara ta bini da shi tana cewa munafuncin banza irin cuta da babu asali!”An kullo bala’i an kawowa oniga!”Komai nisan jifa dai kasa zai dawo..”
“Bance da ita komai ba nidai!Duk da naji zafi araina sai dai ba sa’an yina bace ina girmamata Kuma Abokiyar zaman qawar mahaifiyata ce, ita ce uwargida agidan tana da yara har jikoki,Bazan mayar mata da martani ba,Amma na lura Sam batasan ciwon kanta ba irin ballagazayen matan Nan ce Domin Bata daukar girman ta.”gashi dai ko yanzu ta nuna(Gaskiya ne akwai Mata masu halayen laraba basa Amsa Sallama muddin ba wurin su ajazou ba,A kiyaye Wannan dabi’,un jahilai ne)

“Daga cikin dakinta ta jiyo Ina jera sallama,Da fara’arta ta tarbeni sai da na hango haurenta na makka dake walkiya kamar zinare abakinta ya bayyana,da ladabi na gaidata, amsa min tayi, tana cewa Yawwa Nadiya,Ya Innarei!”Shigo daga ciki,kujera ta nuna min afalon na zauna.”Duk dai kuna lafiya Nadiya!?.”

“Lafiya qlaw,Hajiya da yake hakan yaran gidan ke kiranta.”

“Nace daman mama ce ta aikoni tace agaishe ki sannan kibata saqon..”

“Allah sarki,Dan Allah Nadiya ki ce mata tayi hakuri daman Ina jiran dawowar yaran nan, ne daga makaranta,Sai na basu sukai mata,Amma Ina zuwa…”Tashi tayi ta fice uwar dakinta….Dan madaidaicin falonta dake kallon Daman falon ta shiga,Wanda ke zuba kamshi komai atsare kamar wacce bata da yara,A raina Ina jinjinawa tsaftarta…”Dawowarta ne ya dawo da ni hankali na.”Murmushi nayi Ina sadda kaina k’asa.”

“Ta ce Karbi Nadiya kirga ki gani nawa ne!?”

“Amsa nayi a nutse na kirga su yan dari biyar_biyar ne,kimanin naira dubu goma.”Daga kaina nayi na dubeta nace Hajiya dubu goma ne cip.”

“Yawwa,Nadiya ki kaimata,ki gayamata wasu ne suka kawo mana tsaiko! basuyi zubin adashin su ba,ko yanzu ma ajikina ne na cika mata kudinta tunda lokacin kwasar adashenta yayi, kafin sukawo nasu zubin!”Kinsan Mutane basa da Alkawari!”Sai dai Hakuri kawai!”

“Murmushi nayi nace to Hajiya zan gaya mata,Allah ya sauwaqa ya taimaka, su Saudat ba’a dawo ba ko!”Na tambaya.”

“Ameen nadiya….Eh saudatu Bata dawo ba Abokiyar yawonki, ana can makaranta,jiya fa take kirana awaya waai anfara koya masu yadda zasuyi allura,nace lalle sai anyi malamar asibiti sarkin kaudi, sai ku shirya Nadiya afara koyo gareku mukam mun yafe…Hajiya tace tana dariya..alokacin da ta bude katou firijin din ta na kwance,wanda yake cike da kayan sanyi..kunun aya,da zobou da kunun zaki ta dauko min roba uku ‘yan talatin tasa a leda,ta miko min.”Tace Gashi Nadiyatu NAGODE ki gaida Innerie

“Da murna na amsa Ina godiya cike da ladabi saboda Hajiya akwai mutunci ga kyauta,Abinta na kowa ne,Shiyasa yan uwan miji,da makota duk ta amshewa laraba su wacce ke ganin maganin mallakar miji da Mutane ne tayiwa kowa ita yakeso da yaranta.”Batasan cewa kyautatawa nasa Komai arayuwa,”

“Har kofar gidan Hajiya ta rakani tana bani sakon gaisuwa wurin mamana.”Ni Kuma Ina kara gode mata tare da Bata sakon gaisuwana zuwa ga Saudat idan sunyi waya, saboda Ni ban ma taba rika wayar kaina ba asalima duk gidan mu Babana kadai ke amfani da waya.”Bare na Kira kawayena,”

“Gida na dawo Ina munna na mikawa Mama sakonta tare da nuna Mata alheran da Hajiya tayi min.”

“Mama tace Allah ya saka mata da Alheri…Lantana akwai mutunci Shiyasa zaman mu ya daure da ita akwai kirki, Kuma batada munafunci Shiyasa nake sonta…”Mama tace cikin harshen nan na hausarta da Bata gama zaunawa abakinta sosai ba,

“Ameen nace.”Amma Azuciata Ina tuna kazafin da Kishiyarta laraba tayi Mana,Sai dai Banda halin sanar da mamana komai akayi,Domin tun Ina karama ta horeni Akan k’aramar magana, da kawo Mata gulma da sauran kaji ka Gani, Sam Bata saurara kuma da zarar na fara fad’a Mata zata kwabe Ni tare da min fad’a akan ba halin kirki ba NE,”Shiyasa ko Yanzu nayi shiru nabar zancen Dan Nasan gwaleni zatayi,”

“Mama Tace”Bani zobou kinyi zaune kina tunani kamar Mai lissafi….”

“Murmushi nayi tare da kallon mamana cike da kauna.. ”

“Nan muka dinga shan zobou,Mama tace adashe ne na kwashe…Ina son in ba malam kudi aqara sayo min kayan Nan..”Saboda naga magi da mangyada sunyi qasa kinga babu dadi,azo sayen kaya babu su.”

“Haka ne mama Allah ya kara kawo kasuwa..”Nace Ina kurba kunun Aya,”

“Ameen,Ina son na baiwa malam dubu biyar ya qara wurin biya maki kudin makaranta.”

“Allah sarki Mama NAGODE,Allah ya bani abinda zan muku nima…”

“Kedai Kice Allah yaqara tufa asiri kawai nidai fatana kiyi karatu Kuma ki rike addini da *TABIYYAR* da muka baki.”Ko yanzu Mungode Allah domin daga ni har malaam,muna da sana’ar da muke tufawa kanmu asiri da ita Kuma akullum muna korewa bakin mu gudaji dai dai gwargadou…”

“Gaskiya ne,mama Allah yakarou arziki,Bari na d’aura sanwar dare naga lokaci na tafiya.”Nace tare da azamar tashi na hura wuta.”

“Mama tace”nima dai bara na kulla manja da magi da sauran kayan yajin nan kafin ki wuce Islamiyya.”Yau naga cinikin ma yayi sanyi yara sun dan tsakaita shigowa to babu kudi ga Mutane sai addu’a.”Inji mama

“Nace haka ne mama ko d’azu da safe Islamiyya mallam yace yanzu kusan mako daya Yana mita akawo kudi makaranta,Amma kowa shiru saboda gari yayi zafi!”

“Nan dai muka cigaba da aikin mu muna fira saboda mamana ita ce babbar Aminiyatah batayi karatun boko ba,Amma ta kwankwadi na muhammadiya,Shiyasa take da ilimi da wayewa na ainihi wayo Addini.”Domin macece da taso gidan malammai batada wata makosa arayuwarta,”Magana Daya da biyu ta ambaci sunan Allah ko wa’azi.”

 

Mallam Balarabe da abokinsa Mallam musa ne atsaye suna tattaunawa dangane da zuwan Nadiya makaranta da yake Dan gidan malam musa Yana aiki a jami’ar ta shehu shagari da ke garin na sakkwato.”Takardun nema min gurbin karatu na aji daya ne.”A hannun baba na.”Wanda Saddik ya kawo abaiwa Baba na shine mahaifinsa Mallam Musa yaba Babana.”Tare da gaya masa Saddiq yace “A tura ni makaranta mako Mai zuwa Domin kuwa dadewa daliban sun fara karatun zango na daya.”Lambar wayar Saddiq Baba ya karba Yana kara godewa Abokinsa Mallam Musa abisa namijin kokarinsu.”Daga Nan sallama sukayi Baba ya nufo gida.”

 

“Bayan sallar Isha,mun kammala cin abinci,Baba yace Nadiya shiga dakina kina ganin takardu ki dauko min su.”

“To,Na amsa da toh tare da cika umurnin Baba.”

“Na kawo masa yace”Ki karanta ki gani Takardun ki ne,jibi zakije makaranta.”Idan an kara shiryawa

“Da murna mama tace madallah, Allah abin godia Mallam wato yaron nan Saddiq ya samo mata adimishan (Admission)din!?”

“Ni kuma murna kawai nikeyi bakina yaki rufuwa sai jera Alhamdulillahi nakeyi azuciata.”Ina ta Duba Takardun fuskata awashe bakina kuwa tamkar gonar auduga.”Ina dariyar Mama

“Baba yace”Ay Innerie dazun Nan Mallam Musa ke bani su,Yace Saddiq din yazo to kai tsaye ne,Tare da abokan aikinsa ne sunzo ko wani taro ne a kwalejin can ta Adamu Augie.”

“Oho,na gane makarantar, Nan kafin akai asibiti babba ko,Inji mama.”

“Eh ita,Wai suna sauri ne Shiyasa, malam Musa ma yace saddikun yaso mu hadu Amma dai yace abani lambarsa da zamu Kira kuma yace idan Nadiya taje da ita zata iya kiransa.”

“Allah sarki gaskiya yaron nan akwai kirki….Inji Innerie,ta Kara da cewa to kinji ko Nadiya ki rikesa ki masa biyayya yayanki ne.”Kuma nasan ke da shi duk Kuna da hankali da sanin ya kamata Kinga bakisan Kowa ba sai shi,”

“To mama in shaa Allah.”Na Bata Amsa Ina murmushi.”

“Baba yace Kuma kunga cikin ikon Allah yace gwamnati ta biyawa dalibbai kudin makaranta,Yanzu kudin da zamu bata bazasu wuce dubu ashirin ba ayi duk abin ake buqata,”

“Mama tace Haba dai mallam masha Allah gaskiya naji dadi Allah Mai tufin asirin bawa, Nan ta kwance gefen Zanenta,kudi ta fito da su,ta kirga sannan tace malam ga wannan dubu biyar ne,akara ayi mata sayayyar daman dazu na kwashe adashena na gidan lantana da na fada make kwanan baya, wadannan ragowar kuma gobe kasuwa ayimin sayayyar kayan cefane kamar yadda aka saba Amma Ina da ragowar,kuka,kanwa,da barkono,su bada suba,Uw na manta da gishiri mallam”

“Dariya Baba yayi yace da kin barsu Innarei Ni kaina na hada dubu goma sha biyu Kuma Mallam Musa ya bani dubu uku tun shekaranjiya.”Ke ga sai ai Miki cefanen Sana’ar ki,”

“A’ah malam ba komai ai yiwa kaine da kai da kaya duk mallakar wuya ne, Allah dai yaqara tufa asiri.”shima mallam Musa Allah yasaka masa da Alheri.”

“Ameen nace Ina kallon iyayena cike da tausayin su…hawayen da nike kokarin hadiyewa ne suka kwanta a fuskata.”A hankali na share su kasancewar dare ne.”Nace Baba!”cikin sanyi naqara da cewa Mama NAGODE Allah ya sadaku da gidan aljanna yaqara tufa asiri.”ya bani ikon muku Biyayya,”

“Ameen,Sukace Dukkan su,Baba ya kalleni yace”Kinga dubu goma zan ba Innarei, gobe kije kasuwa kisayo kayan abinci da abubuwan da kike buqata.”Dubu biyar ki rike hannun ki,Dubu biyar Kuma naji ance malammai nacewa ku kawo kudin ko awut(handouts)sai ki dinga saye.”

“Dariya Baba ya sani Nace to Baba NAGODE,” Duk kudaden Mama ya baiwa ta ajiye,”fatan su Nan dai zuwa jibi na gama komai na wuce makaranta.”

“Tashi nayi na basu wuri suna ta hirar su.”Ni Kuma dakina na fada envelope din da nake boye documents dina na dauko na zuba Takardu na da baba ya bani.”sannan na kwanta Ina ta tunanin yadda zanyi rayuwa a jami’ar tare da tunanin irin halin da zan shiga saboda Ban taba nisa da iyayena ba idan dai ba hutu naje garin kakanni na ba dakin gari.”Kasancewar makarantar sakandare ta jeka ka dawo nayi anan Argungu.”Da hakan nayi addu’a kwanciya bacci barawo ya saceni.”

 

*’Yar mutan Dikkawa ce*

 

🌲🌲🌲 *TARBIYYA*🌲🌲

 

 

*NA*

*NABEELA DIKKO*

 

*PEN WRITERS ASSOCIATION*

 

_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM_

*SHAFI NA UKU*
_____________________________________

“Tunda misalin karfe goma na safe na shirya tsaf ciki riga da siket na atamfa super faro kalar miyan goro da fari kayan sun amshi jikina sosai,hoda da man baki na shafa da yake Ni ba ma’abociya son kwalliya bace,nayi kyau matuka,katon hijabina na islamiya na sa ruwan kasa tare da takalmina na roba,Kudi na amsa ga mamana da yake tun kafin baba ya fita kasuwa nagama lissafin komai da zan saye.”

“Shiyasa Ina amsar kudin na nufi hanyar kasuwa,Mama tayi min adawo gida lafia,Daga gida banyi wata wahalar tafiya ba, Na samu napep bakin titin makarantar nan shehu kangiwa.”Tsayarda shi nayi kana na Shiga, a hanya ya samu wasu yam mata biyu wanda da ba zasu wuce sa’a ta ba,sunci kwalliya, riga da wando ne sanye ajikin su Wanda suka kame jikinsu, sai Dan karamin gyale da kowaccen su ta yafa,Duk surar jikin su abayyane take,kallo daya nayi musu na Kauda kai!”Mai napep sai kallon su yake Yana washe baki Domin irin sune suke nema.”Daga ganin su suma dallibai ne Domin handouts ne rike ahannunsu sai jaka da suka rataya(Wankan gefe).”

“Tunda suka Shiga adaidaitan sahun muka gaisa da su ban kara bi takan su ba!”,firar su kawai sukeyi ba kunya bare tsoron Allah firar samari suke da malammai(lecturers)…Haka dai muke zaune dasu wannan tace ke yau wane ya sayo min kaza munci, wane yayi min kaza,Kice wane ya kawo maki abi kaza gobe…nikam mamakin su nikeyi kamar ba mata ba!?”

“Ba hankali bare nutsuwa da kamun Kai,Suna aikata zantuka banza kamar marasa *TARBIYYA* wata zuciyar nace min aykam basuda *TARBIYYA* da gani….wannan rashin kamun kai yayi yawa.”Allah dai ya shirya nace azuciata”…Dai dai nan aka ajiyeni babbar kofar ko kasuwar kudinsa na tambaya yace naira dari,kudin na bashi ya wuce da su..ko ajikin su suna fira suna shaan rake ga ledojin marhaba super market cike da kayan kwalaam ajikinsu,nikam da mamaki nabar wurin…”

“Addu’ar Shiga kasuwa na karatou kamar haka” _LA ILAHA ILLALLAHU WAHDAHU LA SHARIKAA LAHU LAHUL MULKU WA LAHUL HAMDU YUYYI WA YUMITU WA HUWA HAYYUN LA YAA MUTU WAHUWA ALAA KULLI SHAI’IN QADIR_”sannan na daura kafata na shiga a nutse na Fara abinda ya kaini har na kammala duk sayayyata.”Dan dakou na nemo ya tayani daukar kayana bayan na kammala sannan na nemi adaidaita na dawo gida.”

“Mamana ta Duba duk kayan da na sawo a kasuwa,daman su gari ne da indomie da sabulun wanka da ta wanki sai karamar tukunya da risho sakanhan na samo masu kyau na sayo, da sauran abubuwan da ba za a rasaba.”Ni da mama sai munna muke tana sa albarka.”Tace sai Baba ya dawo anuna masa Kudi sunyi albarka,nikam murna ce faal azuciyata.”

“Da yamma bayan na idar da sallata ta la’asar Kuma na gama aikina sarai shirin zuwa Islamiyya nayi.”

“Sallama nayi da mama na wuce,A hankali nake tafiya kaina kasa sai sauri nake saboda karfe hudu harta gota banaso na makara Domin Nice Amira wato (shugabar dalibai mata)Kuma malamar na kasa da ni, kusan aji biyu nakewa karatu bayan anyi min nawa.”Bana sanin inda nake jefa kafata saboda saurin da nake gashi daga gidanmu zuwa makaranta zanyi tafiyar mintuna goma da Dan nisa kadan.”A daddafe na isa ko da na Shiga ajinmu Mallam Yunus Yana karatu nan,Nima zama nayi ya karanta min batare da wani korafi ba saboda halin karya dokar makaranta ba hali na bane,Shiyasa yayi min uzuri.”Dalibai da dama suna cewa Mallam Yunus Sona yake Amma nidai ban yadda ba sai dai Ina da tabbacin Yana ganin mutuncina Kuma Yana kulawa da ni saboda hazaqa ta.”

“Malam yunus karatu yayi min, tare da bani umurnin naje aji biyu da uku na fada masu karatu,idan na kammala nazarin karatuna.”

“Lokacin Tashi yayi anan ne nake fadawa malam yunus jibi zanje makaranta a kwalejin shehu shagari da ke sakkwato.”

“Cike da damuwa malam ya dubeni yace haba Nadiya meyasa ba zakiyi karatun ki a Nan garin ba!?Naga dai duk makarantar daya ce meyasa zakije wani!?”

“A ganina ta cikin gari zata fiye maki sauki kullum kije ki dawo.”

“Murmushi nayi nace malam Ay ba laifina bane Baba ne ya nema min acaan din.”

“Sadda kansa yayi kasa Yana nazari tare da gyara zaman hularsa irin (tabanni kasha hadisi) Nan, yace to ba damuwa Allah ya Sanya albarka Amma munyi rashin daliba Kuma malama akusa da mu.”

“Wani iri naji Nan take idona ya cika da hawaye nace Amin malam nagode.”

“Bakomai Nadiya zan sanarda sauran malamman mu…Amma dai gobe zaki shigo mana bankwana ko!?”

“To gaskia da son nayi gobe na tsaya gida na shirya kayana Mallam, Amma zan shigo da yamma.”nace Ina gyara zaman jikata da ke rataye akafada ta kaina akasa,Domin Ina ganin girman Mallam arayuwata.”

“Masha Allah.”
“Allah ya kaimu kinji Nadiya.”

“Ameen,Nagode Mallam nace, Ina kokarin tafiya tare da yaran makotanmu da nake dawowa gida tare da su.”

“Daaaaaf!Da magariba muka shigo layin mu,Saboda tsayin da mukai da malaam lokaci ya tafi sosai…”Kamar daga sama naji mota tayo cikin mu….sai da mukayi saurin kaucewa!!”Tuni kura ta bademu na mintoci kafin muga gaban mu.” _Hasbunallahu wa ni’mal wakil_ Ita ce kalmar da ta fitou bakina…”Tsaye nayi Ina mamakin wanene wannan Wanda duniya tayi wa dadi!” har yake neman kisan rayuka!”A hankali na karkade hijabina tare da janye yaran gefen titi muka cigaba da tafiya Raina na kuna!”

“Caaan sai ga motar tana dawowa daga baya.”Matrix ce kalar jinin kare wadda tasha bakin gilashin,” oda ake mana…”ko kallon inda motar take banyi ba!”na cigaba da tafiya taa.”Duk da nasan akan mu ne ya dawo Yana fiiifiiitfit banza nayi da motar.”ko hakuri zai bamu oho Amma dai kowanene bamu yafe masa ba!” saboda ya shiga Hakkin mu musamman yaran sun tsorata!”Domin agefen titi muke tafiya amma ya nemi halakar da mu.”Jikina sai Bari Yake Dan fargaba!”

“Ganin ba zan tsaya ba yasa saurayin fitowa, da hanzari ya sha gaban mu da Mota, Yana min kallon sama da kasa!”Ya fito afusace!”

“Yace min ke yar gidan uban waye!?”Da zakiji ana magana ki share,Da hanzari na dago kaina Ina dubansa.”wando three quarter da red shirt ne ajikinsa sai katon madubi baki wulik manne a kyakkyawar fuskar sa,saman kansa suma ce baka wulik kwance wadda da ganinta tana shan gyara.”Baya da maraba da yaran arna!”Domin Sam baiyi kama da Ahlin Mallam Bahaushe ba!”

“Dariya yayi yace “Wow!Kice ke kyakkyawar ce Shiyasa kike wani yanga kina Shan kamshi.”Amma Kuma daga ganin wannan kodadden hijab naki na fahimci iyayenki basa kula da suturar ki!”Daga bana sai bad’in ba d’ad’a!”

“A hasale!nace Dan Allah bamu hanya…!”

“Anki abaki hanyar yar rainin wayo! wallahi naso na koyarda ke darasi sai dai ke Mai kyau ce,Kyaunki ya fansheki Domin yayi tasiri a zuciyar JAWAD,daman naga kina karkade wannan tsumokaran hijab din na kine wanda daga gani yasha omo da sabulu,Shiyasa nazo na baki Kudi ki yanko sabon yadi…Sannan ki sani da titi da gefen titi duk mallakin mu ne…saboda haka ki san inda zaki tafiya keda Allah ya daurawa tafiya a kafafuwa…”Kudi ya dauko a aljihun wandonsa Yana bani.”

 

“Amsa nayi Ina juya su sannan na dubeshi ahankali cike da kunar rai!Nace bakada abinda zaka bani Wanda ubangiji bai bani ba…na lura daga ganinka ba kasan muhimmancin Dan Adam ba KUma bakada TARBIYYA, Naga kana shiga hurumin Iyayena me sukayi maka da zaka zagesu,da kasan darajar naka iyayen na tabbata bazaka wulaqanta na wani ba!”Sannan titi na yadda naku ne amma kasani anyi gefen titi Domin irin mu bayin Allah…Ayshi arziki ba’a tutiya da shi,Domin na Allah ne, idan yaso yaba mutim ko Kuma ya amshe kayansa,Dan haka ka karbi tsiyarka bana bukata!!!!”Nace tare da watsa masa kudinsa a fuska Nan suka zube aqas, na juya na kama hannun yaran Raina abace muka wuce zuwa gida.”

“Kallona yayi tsaf Alokacin da nafara tafiya, kana ya kalli Jikinsa!” da kudin da ke kasa,mudubin idonsa ya cire Yana mamakin wacece Ni da na bashi kunya har Mutane na kallonsa suna shewa!”…..Idonsa suka kad’a sukayi jajur…zuciyarsa na masa suya!”A fili cewa yayi lalle kin tabo ruwan dafa kanki Ni JAWAD za akira da maras *TARBIYYA!?*”meye take nufi kensn taci bulus!?”

 

“Kudin ya tsallake ya barsu nan wurin, mota ya nufa ya fada cike da bacin rai!”Da matsanan cin gudu yabar unguwar @360 ya isa gidan su,Dakinsa ya fada Yana kaiwa da kamowa mafita yake nema yadda zai gasawa yarinyar Nan aya a hannu.”lalle zai nuna mata shi din maras *TARBIYYA* ne kamar yadda ta jefeshi da kalmar.”

“Bayan JAWAD ya wuce,mutanen da ke zaune gefen titin wadanda akai komai akan idonsu suna kallo,sune suka kwashe kudin suka raba,sukan gaba ta kaisu gobarar titi.”

“Ko da na karaso gida mamana tana alwala magrib,Kallon tuhuma ta bini da shi,Shiyasa na Dan saki Raina kar ta fahimci me nake ciki.”

“Addu’ar kammala Alwala naji tana karantouwa kamar hakan” _Allahumma ja’alni minal tauwabin waj’alni minal mutadahirrin Allahumma Amin_”

“Kallona tayi ta ce”Ina kika tsaya? meyafaru? naganki hakan?,Ajere mama ta jefo min tambayoyinta.”fuskarta adaure

“Sakewa nayi nace mama daman malam ne ya Dan Tsayarda Ni Ina gaya masa jibi zanje makaranta,shine yake min nasihohi har Lokaci ya kure min har fa nuna min yayi wai sai sun yi rashin dalibar da ke rage masu aiki!”Shi ne naji ba dadi Kuma Naga magrib ta gabato bana gida nasan zakiji ba dadi.”

“Ajiyar zucia mama ta sauke tare da gamsuwa da maganata,kana tace Allah sarki to Mallam yayi hakuri Domin koni zanyi kewarki Nadiya.”

“Murmushi nayi na Shiga daki kayana na ajiye na fito Domin Alwala yayinda mama ta tada sallah.”

“A kasan zuciyata haushi da takaicin Dan iskan yaron Nan nakeji maras *TARBIYYA*

 

“Toufaah kubiyoni Domin Jin yadda zata kaya😊 *Yar mutan Dikkawa ce*

 

Leave a Comment