{🌊Water gurl🫗🌊}
Yarinyar ruwa
Page 1
Zaune take bakin dutse tana rera wakokinta da tasaba jefa dutse take cikin ruwa
Juyawa naga tayi tana sauraren sautin zuwan jirgin ruwa tana cikin haka tsalle naga tayi tafada cikin ruwan tabuya
CIKIN JIRGIN RUWA⛴️
Shakalinsu suke hankali kwance ta ko Ina kida na tashi wani matashin saurayi na hango gefe yana shan coca cola kallonsu kawai yake yana jinjina shirme irin nasu
Wani daga cikinsune yataso yana kokarin janshi amma firrr wannan guy yaki yadda yatashi
FAHEEM mai duba na’urar jirgi yakirashi hankali atashe
Juya wadda zasuyi naga wani kyakkyawan saurayi hadadde kuma murdadden namiji
Fari soll dashi
Tana ganin jirgin tabi bayan jirji nandanan tashiga gefen jirgin tana lekonsu
can ta hangoshi yabada baya sai murmushi take tana kara leko duk da ba ganin fuskarshi take Yiba
Tana cikin haka taga zoben ta na haske alamane da kiran mahaifinta da sauri ta wintsilo sai cikin ruwan
Lumshe idanu yayi yana kallon ikon Allah yadda ruwa suka taso sukayo kansu
Page 2
Nan danan aka fara fidda kanannan jiragen ruwa🛶 kan kace mey har ruwan sunyo Kansu
Cikin gaggawa kowa yake fadawa karamin jirgin ruwan🛶 harzai fada jirgin ko mey yatuna oho🤷♀️ yakoma da gudu da baya yana zuwa tsakinyan jirgin yatsaya yana dube dube
Can ya hango Dan karamin dan kuikuyo dasauri yadakkoshi yajefa Cikin ruwa
Daidai wannan yarinya tasake fitowa ta tura karen da hannun ta wurin jirgi kafin takarasa gun saurayi jirgin har ya nutse tare dashi
Cikin tashin hankali takoma cikin ruwan tanata duba inda zata ganshi amma inah bata ganshiba
jirgin yana nutsewa yafara kokarin yin iyo amma ina yakasa Dan bakaramin ruwa banee
Jikinsane yasake yatafi can kasan ruwan saura kadan tariko hannunshi tayi sama da shi
Duk Abunnan da ake sarauniya fauza na kallonsu amadubin tsafinta
Bakin ruwa takawoshi amma ba numfashi atattare dashi cikin razana tafara danna kirjinshi
Page. 3
Amma inah ko alamar rai babu nandannan tasaka bakinta anashi tana jawo ruwanda yasha tanayi tana danna kirjinshi amma baitashiba
Cire bakinta tayi anashi tafara danna mishi kirshi da karfin gaske tana rera waka can saiga ruwa nafitowa ta bakinshi
Ajiyan zuciya tayi ta daga ajikinshi
Ahankali yake jiyo sautin wakar da take rerawa tare da kokarin bude idanun amma bishi bishi yake ganinta
Baikarasa bude idanuba yaga ta fada ruwa nan sojojin da ke nemansa suka karaso gareshi suna dagashi suka tafi dashi tasu masarautar
Koda takoma hannunta rike da agogon hannunshi murmushi tayi
FAHEEMA!!!
Naji ankira abayanta wata matace matashiya
bazasu wuce sa’a gudaba saidai ita faheema tafita koma daga halittar fuska harta jiki mah
Juyowa faheema tayi tace ya akayi mey ya kawoki nan ya akayi kikasan nan wurin ta tambayeta cikin alamar tuhuma
Faheema wannan abun dakike shirin aikatawa kuskurene ya za’ayi kiso wannan mutum wanda ba rayuwa iri daya kukeba
Taya zai iya rayuwa cikin ruwa faheema kinsan ambawa yarima khalil ke baikonku duka wata daya ne saura
Sanin kankine khalil bashida imani zai iya yin komai akanki zaishiga rayuwar mutuminda baimasan da muba
Ahasale faheema tayo kan abaya wuyanta takamo amugun hasale
Karki sake dangantani da wannan shedanin mutum har kike kokarin danganta wanda nake so fiye da rayuwata Takarasa a tsawace
Abaya na kokarin kwatar kanta amma ina takasa cikin mawuyacin hali ta fizge agogon hannun faheema
Bata ankaraba tajita kasa timmmm aguje ta tashi tareda sake agogon tayi fuuuuu ta wuce Dan wlh inta tsaya faheema zata kashe ta kan maganar
Sarauniya fauza dariya ta sheke tareda buga wani table dake kusa da ita
Faheema kinyi kuskure babba arayuwarki tason wani mutum ba dana khalil ba saikin gwammace baki taba sanintaba tare da kara shekewa da firgitacciyar dariya
Page. 4
Zama faheema tayi tare da rungume agogon kamar ta rungume mai agogon lol😂
Tunani take yazatayi itama kanta tasan tadibo abu mai wahalar gaske sbd koda kowa zai amince bata tunanin mahaifinta wato sarki zai amince
Yazatayi da matsananciyar soyayyar da ta tsinci kanta aciki
YAZANYI! YAZANYI!! YAZANYI!!! Takarasa cikin rauni inama mahaifiyata tana kusa nasan ita kadai zata fahimci halinda nake ciki
Tare da fashewa da kuka koda zan rasa rayuwata sai na rayu dakai
Zaki rayu da gawa dai inhar ina numfashi faheema ke tawace yakarasa tare da jawo gashin kanta da karfin gaske kokarin kwatar kanta take sbd azaba amma ina ko jijjigi hannunshi bayayi janta yake Tana turjewa shiko saikara janta yake.
NIKO NACE SAIKACE ABIN DOLE ANCE BA’AYI BAKA KYALETA LOL😂 toko dai wani abu yarima khalil yakeso wurin sarauniya faheema
Share & comment pls
✍️Writing by aishaalkali
Muhadu a page 5 muji yazata kaya 😌
shin mey yarima yakeso wurin sarauniya faheema? wacecec sarauniya faheena ?waye yarima faheem? shin faheem yanason faheema ?
Sarauniya fauza menene kudurinda kan fahima ?
Cakwakiya
Soyayya
Bandariya
Kiyayya
Mugunta
Izza
Tausayi
Tare da tsantsan nadama kudai kubiyomu muji yaxata kaya taku har kullum eshaalkali😉. { 🌊water gurl🌊}.
Idan bakuyi comment da sharing ba Zan cigaba da rubutu ba gaskiya✍️✍️✍️✍️✍️✍️✍️
📚📖AISHAALKALI PALACE📚✍️
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/DPpBhXyzIVKLbDQwVsQJX
Typing📲
Water gurl🌊🧝♀️
Yarinya ruwa
Page5&6
Jan hannunta yake da karfi kamar yasamu gwarzon namiji kamar shi
Bai tsaya ko inaba sai cikin dakinshi da shikadai yasan da zamanshi cikin masarautar tasu
Duk wannan abun dayake faheema ta dade da sumewa sbd matsananciyar azaba agogon ta na makale da ita.
Hankadata yayi sai inga wanda ya isa zuwa ya fitar dake balle harki kara ganin wancan mummunan mutumen
Sai asannan faheema tadawo cikin hayyacinta zatayi magana taci ta kasa kokarin magana amma inah abin da bazai yuyuba sbd
Yaciri kashin kanta yayi tsafi yacire murya sbd kada tayi yunkurin kiran mahaifinta
Kuka take iya karfinta amma ba halin magana shiko sai kallon Lip’s dinta yake. Allah yasani komi faheema tayi tana burgeshi
Shidai yana sonta koma mey tayi mishi
Yarima
Yarima khalil dane ga sarauniya fauza matar sarki wato mahaifi ga faheema
Mahaifiyar faheema tarasu faheema nada shekara 10 aduniya
Alokacin ita kuma sarauniya fauza takashe mijinta da hannunta khalil yanada shekara 16
Sarauniya fauxa takasance rikakkiyar masafiyarda ta amshi sunanta wani lokacin ita kanta saita sauya halitta
Taje ta holewarta da bayin masarauta maza
Ana haka mijinta ya kalu balanceta kan abinda take tabari kodon yaronsu yasamu Inga tacciyar rayuwa amma ina idanunta sun makance sai take gani kamar yanaso ya karbe dantane awurinta
Cikin Daren ranar mahaifin khalil ya mutu batare da ya shura ba farin ciki wurin fauza bako karami ba alokacin khalil yana wurin kakarshi acan yake rayuwa
Mutuwar mahaifinshi sarauniya fauza tasamu damar karbarshi awurin kakanninshi
Shima baisoba amma haka fauza ta tsafe dannnata sbd kada yayi gardama
Ahaka khalil yafara ganin abubuwan da mahaifiyarshi take saiya fara sha’awa tayi farin ciki sosai koba komai ynx tanada magaji
Wannan kenan bangaren sarauniya fauza da yarima khalil
Page 7&8
Sarkin ashib sarkine mai cikakken iko da karfin mulki izza sarauta cikin jinin jikinshi take sbd ta gadoce
Sarki ashib mahaifine ga sarauniya faheema mai jiran gado mahaifiyar ta itace kadai mata ga sarki
Auren soyayya sukayi kuma dama shi sarki bayada sha’awar mata barkatai soda yawa ana kawo mishi yaran sarakai Dan ya aura amma yace matarshi zainab ta isheshi
ana haka sarauniya zainab tayi shekara uku batareda ko barin wata ta taba yiba awannan lokacin mutane da dama sun yi zaton sarauniya zainab asiri tayima sarki sbd su basu dau tsafi wani mummunan abu Ba
Hasalima duk abinda zasuyi sai anhada da tsafi kowa zai iyayin abinda yakeso amma kuma abu dayane Sarki yafi kowa karfin tsafi shida sarauniya
Ananan hankalin kowa yatashi akan rashin haihuwar sarauniya zainab amma banda sarki ashib bayaso yanuna rauninsa har mutane su fuskanci haka
Anan cikin wannan yanayi aka bidi sarauniya Zainab amma ba’a gantaba duk inda akesa ran ganinta amma ina abu ya faskara hankalin sarki yayi matukar tashi nan take masarautar ta dauka kowa na tofah albarkacin bakinshi kan batan ta
Wata takwas kenan da batar sarauniya Zainab duk yanda akayi da sarki domin yakara aure amma yace shi bazaiyyi aure ba sbd Zainab nanan kuma takusa dawowa gareshi
Haka aka saka mishi ido sarki ynx gaba daya baya zama fada baya tabuka komai amasarautar kowa abinda yakeso yakeyi
Ranar wata litinin 1st November 2004
Sarauniya Zainab ta haifi yarta mace kyakkyawa fara tasss alokacin sarauniya zainab tana tareda mahaifiyarta wato kaka hajjo duk tsawon wannan lokacin tana tunanin halinda mijin nata yake ciki
Saida tayi arba’in sannan ita da mahaifiyarta suka fara shirin dawowa
Page9&10
Koda suka dawo masarauta sarki murna bibbiyu ga yarinyarshi ga matarshi alokacin hadda walima akayi a masarauta
Ana haka yarinya tafara girma hankalin yaran masarauta duk yatashi sbd koda tayi shekara takwas yarinya taxama macen asali
Wata Rana tafito daga cikin ruwa tana shan iska bakin teku ananne shikuma khalil ya fito mugunta sbd wannan lokacin ne masu jirgin ruwa suke wucewa shikuma
Yana matukar jin dadi yimusu mugunta ananne yafara ganin sarauniya faheema tun lokacin da idanunshi suka sauka kanta yakamu da matsananciyar soyayyarta
Water gurl by eshaalkali✍️
Ita kuma tana ganin jirgin tabi yasanshi jirgin bai tsaya ko inaba sai bakin masarautar jauro masarautace mai dinbin tarihi da al’adu ma bam banta
Faheema kidawo ammi nakiranki tajiyo sautin muryar abaya kwabe fuska faheema tayi tace abaya ganinan
Nan ta fada cikin ruwan bata tsaya ko inaba sai wurin mahaifiyarta
Abaya diyar kawar sarauniya Zainab ce wato indo tarasune wurin haihuwar abaya kuma mahaifinta ya mutu tun indo nada cikin abaya
Haka yasa sarauniya Zainab ta karbi abaya ta hada da yar ta take kulawa dasu atare kamar yan biyu
Wani abin mamaki tunda aka haifi faheema sarauniya Zainab bata kara koda barin wata bane
Tunda khlil yaga faheema yakoma yasanar da mahaifiyarshi dama abinda fauza ke jira kenan
Taku har kullum eshaalkali
KUBIYONI DOMIN KUJI YAZATA KAYA
Share &comment idan ba comment zandaina posting gaskiya
Water gurl🌊🧝♀️
Writing by aisha alkali✍️✍️📚Typing📲
Water gurl🌊🧝♀️
Yarinya ruwa
Page11&12
Alokacin da khalil ya fadama mahaifiyar shi cewa faheema yakeso ya aura bangaren mahaifiyar faheema tana yawan mafarkin khalil da mahaifiyar shi tayi alkawarin indai tana raye faheema bazata taba auran khalil ba koda kuwa tana sonshi
Fauza tayi bincike iya bincike amma abun yaci tura sbd haka ta yanke shawarar kawar da sarauniya Zainab aduniya sai ta maye gurbinta kunga ta jefi tsuntsu biyu da dutse daya
Na farko zata zama sarauniya mai karfin iko sannan zata cika burin mafi soyuwan dannata
haka sarauniya fauza tayi ta gwagwarmaya har tasamu nasarar raba sarauniya Zainab da duniya alokacin faheema nada shekara 10 aduniya tayi kuka iya kuka itada mahaifinta dama kakanninta
Wannan kenan…
Cigaban labari
Haka yaci gaba da azabtar da gimbiya faheema tun mahaifinta baya nemanta har hankalinshi yatashi wata kwarya yadauko wacce shi kadai yasan da ita
FAHEEMA!
yakira aiko saiga faheema cikin kwarya daure awani wajen hankali tashe yamike tsaye yana mamakin wanene yakeda ikon kama gimbiya har yayi mata irin wannan daurin
Bangaren faheem
Yatakurama mahaifi da mahaifiyarsa kan sai annemo mishi yarinyar da ta ceci rayuwarshi ba neman da ba’ayiba amma babu lvr
Shiko ya dau alwashin zai jirata koda tsawon rayuwa ce sbd yanaji ajikinshi cewa zata dawo nesa ko kusa
Haka duk lokacin da
Ya kwanta bacci saiyayi mafarkin tana kiranshi yataimaketa wani wajee mai hadarin gaske abin na damunshi amma ba yanda ya iya sbd shima yasan mafarki ba gaskiya bane
page13&14
Sarki ashib ranshi yayi mummuna baci alokacin da yagane da sa hannun Dan matarshi wato surukinshi awurin azabtar da yar shi daya tilo
Iska kawai mahaifinta ya hura saigashi daurin da akayi mata ya warware jin haka yasata kunkura zatayi kuwa amma saita kasa
Nan mahaifinta yagane ancire mata magana haka yakoma hura wani iskan saigashi ta furta ABIEE cikin wahaltacciyar muryar ta data dishe sbd wahala
Nan abaya ta bayyana agaban ta tana kuka itama kamar itace aka daure faheema bakijin magana na gaya miki kicire wannan mutumin acikin rayuwarki amma taurin kai ya hanaki
Shikenan tunda haka kika zabama rayuwarki faheema abaya tafada tare da juyawa zata bar wurin
ABAYA taji ankirata da sanyayyiyar murya idanu ta runtse tanajin wani zafi na ratsa ko wani loko na jikinta…
ba yawa kuyi hkr wlh yau banida charge shiyasa amma in sha Allah zanyi Post da dare amma gaskiya banyi alkawariba.
Water gurl 🌊🧝♀️
Writing by Aisha alkali✍️✍️✍️✍️
More comment more update✍️📚Typing📲
{Water gurl🌊🧝♀️}
Yarinya ruwa
“Page15&16”
Abaya kinsa wanene khalil kinfi kowa sani abaya kina tunanin idan na amince da khalil anya banyi wauta ba kina ganin yadda yake lalata yaran mutane kazama mai lpy marar lpy duk kusantarsu yake haka kike tunanin khalil zai iya canjawa bayan aurenmu??
Numfashi abaya ta fesar faheema ki gane
Dakata malama ynx dubamin ina khalil yake
Tafin hannunta tabude takira sunan khalil nan khalil ya bayyanan yanata sheke ayarshi da yammata ba daya ba ba biyu ba
Kauda fuska sukayi baki daya ni babban abinda yake batamin rai wai ace sarauniya fauza ita ke kaimishi bayi kuma wai sai wacce tayi mishi wlh bazan iya zabama yarana wannan fasikin amatsayin uba garesuba ;
Hakane amma faheema
Amma faheema mey takatseta ta hanyar mayar mata tambaya!
Kinsan abinda khalil yace zai aikata lalle zai aikata sannan duk abinda kikeyi mahaifiyarsa naganinki
Taya take ganina abaya
Wlh duk abinnan damuke tana gani kuma tana jinmmu
Wani abu abaya taciro daga jikinta kamar sarka tasaka mata awuya indai wannan abun yana tare dake bazata sake ganin motsinkiba…
“page17&18”
Faheem ne zaune bakin teku yana jefa dutse aruwa yana rerawaka. aduk lokacinda ya rufe idanunshi yana ganin bishi bishin fuskar ta !!
Saidai har ynx yakasa mantawa da ita abu daya yake wanda yake rage masa kewa shine rera wakarda ya jiya abakinta .
zaune take gefen mahaifinta fada yake mata sosai itadai sai hakuri take bashi FAHEEMA!!! yakirata da kakkausar murya !!
Nan da wata daya zan daura aurenki da khalil
Maganar mahaifinta haka tajita akunnenta kamar saukar aradu
Kwarai kuwa daki shirya da karki shirya duk dayane amma nariga na yanke hukunci
A wannan lokacin faheema kasa tabuka komai tayi sbd wata matsananciyar faduwar gaba sunan Allah take maimaitawa duk da batasan mey take cewaba
KO ita abakin faheem taji lokacinda yafara bude idanunshi!
Koba komai tasamu natsuwa ta hanyar ambatan Allah nda takeyi
Shuru tayi tacigaba da sauraren mahaifinta yana bata umarni duk abinda yace bata cewa a’a;
Haka gaban faheem yaketa tsinkewa baisan dalili ba yanaji ajikinsbi wani abu zai faru saidai baisan komai akan haka ba sbd haka yabarwa Allah komai shidai nashi addu’a da zubama sarautar Allah ido!!
“SBD koshi wani lokacn yana mamakin irin sonda yakema wacce baisan wace irin halitta bace dan ynx yadaina yimata kallon mutum;
lol faheem ashe kanada saura har ynx baka shirya tunkarar komaiba kenan…!
“Page19&20 ”
“Tashi tayi jiki ba kwari tatafi turakarta
Bangaren khalil kuwa sarauniya fauza ce take mishi barka kuma bangare daya tana mamakin yanda akayi ta daina ganin faheema gaba daya so dayawa takan matsa amma sai taga kamar tukunyar tsafin zata fashe inta cigaba …….
“MASARAUTAR SARKI ABDURRAHAMAN MASARUTACE TA ADDININ MULUNCI DA MANYAN MALAMAI MAGADA ANNANBAWA” sarki abdurrahaman mahaifine ga faheem su biyu Allah yawadata wa iyayensu faheem shine babba sai fahad da yake karami kuma auta agurin mahaifansu ;
Maryam itace mahaifiyar su faheem maryam macece mai rauni ta gefen iyalanta bata son wargi ko raini haka yasa bata fiye shiga harkar sarautaba sbd macece da batason rigima ko tashin hankali tanason duk abinda yaranta keso duk da haka bata bari tarbiyar yaranta ta lalace ba sbd tanaso suma su rabauta a duniya da lahirarsu;
Takan zaunar dasu tayi musu nasiha ta nuna musu abinda yadace duk dako sunsani haka baya hanata kara yimusu hasihar..
Sam faheem yatashi ne da dabi’ar mahaifiyarshi ta rashin son mulki kuma shine babban dan sarki amma bayason ko zancen mulki ayi mishi koda ya girma saiya nuna shi matukin jirgin ruwa yakeso yazama !
Saiya kasance dashi ake zuwa dauko kaya daga wata kasar zuwa wata acikin jirgin ruwa kaninshi kuma yana makaranta alokacin….
shin yazata kaya kuna ganin faheema zata auri khalil ..?
Shin faheem zai kara haduwa da faheema kuwa…?
Sainaji ra’ayinku a comment section zamu cigaba …
Water gurl by aishaalkali✍️✍️
bari muji yazata kaya shin comment section zaiyi zafi koko amma bari mugani dai hausawa nacewa gani ya kori ji …!Typing📲

Leave a Comment