Books Reviews & FAQs

Hardness Of Heart Hausa Novel

HARDNESS OF HEART

 

( RETURN ) ……………..

 

 

 

_ BY _

 

MEERAH

 

 

 

ALHAMDOULILAH ! ! ! ! ! ! !

LITTAFIN TAURIN ZUCIYA ( RETURN ) YA ZAMA COMPLETE , ME BUKATAR SAYAN COMPLETE DIN LITTAFIN ZAI BIYA N600 KACAL , ME SON SHIGA PAID GROUP DIN KUMA N300 NE

VIA

8081129487

Khadija Sabi’u

Monie point bank

 

KO KUMA ZA KU IYA TURO KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER

Zain (Airtel)

07089503300.

 

 

 

 

 

 

A YI FOLLOWING CHANEL DI NA PLEASE

 

 

 

 

 

_ BONUS 🌙💞 _

 

 

 

 

 

「 PAGE______1 🕊❤💫 」

 

 

 

 

▪NEW ZEALAND 🌲🌲

 

 

 

▪WELLIGTOM ( ISLAND BAY )

 

 

 

Wata kyakyawar baturiya ce ke sauko stair din wani kyawatencen gida ba sai na bata lokaci na fada muku yadda gidan ya ke dan haka kowa ya yi aiki da brain din shi a nan

 

yarinyar kyakyawa ce gaskiya , fara kal da ita kamar ka taba jini ya fito , da ga gani wannan rainon madara da ice cream ce , a shekaru ba za ta wuce 16 years ba , ta na da kananan idanu farare kal kamar madara kwayar cikin su kuma brown ce , da wani dan karamin bakin ta lips din ta pink color ma su laushi sun sha lips balm

ta na da gashi sosai har tsakiyar baya brown color har wani shining ne ke da allamun ya na samun kula sosai , ya zubo mata har saman shoulder

 

ta na sanye da wandon jeans White color da wata yar t-shirt zuwa cibi white color ita ma , babu takalma a kafafun ta

ta na sauko stair din a hankali kai a sunkuye ta na latsa dankareriar wayar ta , murya kassa kassa ta na rera wakar Ed Sheeran ta Two step , ta ko iya wakar da wata yar siririyar Muryar ta cike da shagwaba

 

a haka har ta gama sauko stair din ta shigo parlourn gidan ta nufi doguwar sofa ta zauna ta na ci gaba da rera wakar ta

 

Ta na zaune a haka wani kawai na ga wani saurayi ya shigo parlourn , abun mamaki sai na jiyo ya na sallama kassa kassa hakan na nufin musulmi ne ?

kamanin shi daya da yarinyar nan da ga gani big bro din ta ne sai dai color din idanun shi ash ne mai kyau kamar mirror , a shekaru zai kai 30 or 31 years haka

 

ya na sanye da wasu suit brown color ma su mugun kyau da tsada sun zauna mishi sosai a jiki , ga shi ko ya na da murdaden jiki da allamun ya na yawwan motsa jiki

cikin nitsuwa ya karaso cikin parlourn ya zauna saman sofar da ke fuskantar yarinyar nan

da English ya ce mata ” Chuby , take me water please ”

 

ko motsi yarinyar nan ba ta yi ba sai faman latsa wayar ta ta ke ta na wakar ta

wani dan karamin tsaki ya ja kafin ya ja kafin ya dauki pillow ya tilla mata har sai da wayar ta ta fadi kassa

 

a dubu dari ta dago kai ta na yamutse fuska ta kai hannu ta cire earpieces din kunnen ta ta na turo dan bakin nan nata ta ce ” Jay-Zix , me na yi maka za ka buge min waya ta ? in screen din ya fashe fa ? ”

 

matse gera ya yi ya na fadin ” Chuby , ban son shirme , tashi ki kawo min ruwa ko kuma na fasa miki baki ba screen din waya ba ”

 

a hankali ta kai hannu ta dauki wayar ta da ta fadi kassa , ta na wani dan karamin gunguni ta tashi ta nufi hanyar kitchen ta shiga

 

ta na barin wajen ko wani mutum ya fara sauko stair din gidan ya na sanye da Trouser red color da t-shirt fara

ya lattijantaka gaskiya , a shekaru zai kai 55 years haka ya na kama sosai da Jay-Zix da Chuby da ga gani shi ne mahaifin su , wani abun mamakin ya na kama sosai da Nihal da Rayan dan har kalar din idanun shi ash ce kamar ta Rayan , shape din lips din shi na sama ya yi duhu kadan na kassa kuma ya yi pink kamar dai na Rayan da Zarah

 

fuskar shi babu yabo babu fallasa ya karaso cikin parlourn ya zauna saman sofar da Chuby ta tashi

ya na zama Chuby ta fito da ga kitchen rike da glass cike da ruwa sai faman turo dan bakin nan nata ta ke ta nufi Jay-Zix ta mika mishi glass din ta na kauda kai

 

a hankali Jay-Zix ya kai hannu ya karbi glass din ya na yi mata godiya

 

wata yar karamar dariya Mutumin nan ya yi ya na fadin ” wa kuma ya taba min My Angel ? ”

 

da sauri Chuby ta nufe shi ta zauna geffen shi ta rungume shi , cike da shagwaba ta ce mishi ” Daddy ba Jay-Zix ba ne , ina zauna kawai ya buga min pillow har waya ta ta fadi yanzu da screen din ya fashe fa ? ”

 

Daddy ne ya ce mata ” da ko ya saya miki sabuwa ”

wata yar karamar dariya Chuby ta na kara shigewa jikinsa kafin ta dago kai ta manna mishi kiss saman kumatu

 

murmushi mai dan sauti ya yi kafin ya ce mata ” shikenan yanzu je ki yi sallat lokaci ya yi ”

 

sakin shi ta yi ta na kauda kai ta na turo baki ta ce ” daddy ni gaskiya na gaji da yin wannan abun , ni ai ban taba ganin momy ta na yi ba , why mu za mu dinga yi ? ni gaskiya na gaji ”

 

cikin sigar rarrashi ya ce mata ” Right ba ki taba ganin momyn ki na yi ba saboda a lokacin da mu ka rabu ta daina yi , kin ga a wajen ta ki ka tasso shi ya sa ba ki ta taba ganin ta na yi ba , amma ki sani ke musulma ce , Sallat kuma wajibi ne musulmi ya dinga yin ta dan ita ce abun da ke banbanta mu da Christa , please kar ki gaji da yin Sallat ki tashi ki je ki yi please My Cutie pie ”

 

wata yar karamar dariya Chuby ta yi kafin ta ce ” tun da ka ce Cutie pie shikenan , zan je na yi Daddy , but idan na dawo za saya min chocolate ”

 

” duk abun da ki ke so my Cutie pie ” ya fada cike da so

da sauri ta tashi ta nufi stair ta haye ta na sakin murmushi

 

sai da ta bar wajen sannan Jay-Zix ya ce ” malam Ylies , lafiya ka ke ta murmushi kai kadai ? ”

 

wani cool murmushi Ylies ya saki kafin ya ce ” nothing , dazu Jason ya kira ni ya ce Next week zai dawo ”

 

a hankali Jay-Zix ya gyada kan shi kafin ya ce ” Daddy ka san wani abu , i saw photocopie din uncle Jason ”

 

cikin rudu Ylies ya ce mishi ” photocopie kuma ? ban gane ba ? ”

” wlh photocopie Daddy , da shi da uncle Jason kamar an tsaga kara har wadanan sexy blue eyes din nashi , na so na dauki pic din shi da na gwada maka , but next time idan na je zan dauko maka ka gani ” ya na gama fadar haka ya mike ya nufi stair ya haye

 

da kallo Ylies ya raka shi har sai da ya haye sannan ya bude baki cikin rudu ya ce ” photocopie kuma ? a sani Jason ba shi da yaro ko guda bare na ce yaron shi ne , ko da ya ke ba abun da Allah ba zai iya yi ba ”

ya na gama fadar haka ya yi wata yar karamar dariya kafin ya mike tsaye ya nufi dining room ya janyo chair guda ya zauna

 

 

 

▪NIGERIA ( KADUNA )

 

 

▪HAYAT 💦

 

 

A hankali ta ware idanunta da kalmar shahada a bakinta

ta na bude su ta fara bin wajen da kallo ta na kifta idanunta a hankali , a hankali ta mike zaune kafin ta mike tsaye

 

ta na mikewa ko ta jiyo Muryar Ash da ga bayan ta ya na fadin ” tun da kin tashi , sai ki je ki kawo min fruits ”

 

slowly ta juya ta kalle shi , ya na zaune saman sofa ya na faman latsa laptop din shi cikin konciyar hankali

” kar ki bari na sake maimaita abun da na ce ” ya fada ba tare da ya dago kai ba

 

ba musu ta juya a sanyaye ta nufi kitchen

da sallama a bakinta ta shigo , nan ta tardo Chef din da ke yi musu girki , wannan shi ne karan farko da ta tardo su ba ta taba tunanin duk maza ne su biyar duk sanye da Trouser na army da Shirt white color irin wannan na chef haka

 

su na ganin ta duk su ka shiga sara mata su na gaishe ta cikin girmamawa

a sanyaye ta ce musu ” don Allah ina mutanan gidan nan su ka yi ? ” ta fada da turanci

 

daya da ga cikin su ne ya amsa mata da cewa ” Madam sun tafi Abuja , zuwa yamma za su dawo but his excellency ya ce idan ki na bukatar wani abu ko fada min ”

 

nan take ta ji zuciyar ta duk ba dadi hakan na nufin sun tafi sun bar ta da Ash cikin gidan , wanda ba zai ji tausayin kashe ta ba in ta bata mishi rai

 

wasu yawu ta hadiye kafin ta ce ” don Allah ko za ka iya hada min fruits na kai mishi ” ta fada ta na nuna kofar kitchen din kamar akwai mutum a tsaye

 

ba musu wanda ke tsaye gaban counter ya juya ya nufi basket din fruits ya dawo ya yanka mata saman tray ya gyara gwanin burgewa , sannan ya daura glass da jug din juice a gefe sannan ya dauko shi ya karaso ya mika mata

 

wani dan karamin murmushi ta saki ta na yi mishi godiya kafin ta karba ta juya ynta fita kitchen din su kuma su ka ci gaba da aikin su

 

ta na fita wanda ya fara yi mata magana ya kalli wanda ya shirya mata fruits din ya ke ” Man , ba ka saka hular ka ba , a ka je gashin ka ya shiga cikin abincin ? ” ya fada dan ya lura shi kadai ne bai sanye da hula bayan ya san tsarin gidan ba a yarda su yi aiki ba su rufe kawunan su ba saboda gudun kar gashi ya shiga cikin abincin

 

ga shi ko Ash ya na da mugun kyankyami wata rana ya na cin abincin shi ya fiddo gashi a ciki sai da ya kwana ya na amai

 

duk chef din sai da ya ba su punishment har kuka wasu su dinga yi mishi duk da laifin mutun guda ne amma dukka sai da ya hada ya ba su punishment sai da Nihal ta yi zaune ta na rokon shi ya kyale su dan abu kadan ya yi saura ya kashe su , shi kuma ko a jikin shi

 

Ba tare da ya tsayar da aikin shi ba ya ce ” ai ina gani , ba abun da ya shiga ”

 

wanda ke tsaye kusan gas cooker ne ya ce ” kai dai ba ka sani ba , amma na san in har General za ta kai wa wannan fruits , a ka yi akasi gashin ka ya fada ciki to ka shirya yin jinya , ni dai kun ga tafiya ta ” ya kai karshen ya na nufar hanyar su ta fita ya tsere tun da ya riga ya gama aikin shi

 

haka kowane ya ci gaba da aikin shi amma duk zuciyoyin su na cike da fargabar abun da zai faru in a ka je Ash ya samu wani datti cikin fruits din shi

 

Hayat kuma ta na fitowa ta nufi Center table ta ajiye mishi fruits din ba tare da ta ce komai ba ta juya za ta bar wajen

 

ko taku biyu ba ta yi ba ya ce mata ” wa ya ba ki izinin tafiya ? ”

 

cak ta tsaya ta sauke wata yar karamar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta juya a sanyaye ta tsaya ta sunkuyar da kai ta riko hannayanta sai sake sake ta ke cikin zuciyar ta

 

ba tare da ya dago kai ba ya kai hannu ya fara daukar fruits din nan ya na kaiwa a baki ya na sha cikin konciyar hankali

slowly Hayat ta dago kai ta na son ta ga in ya gama ta tafi abun ta

ta na dago kai ko idanun ta su ka sauka saman wannan dan guntun bakin nashi

haka kawai ta tsaya ta na kallon lips din shi ya na motsa su a hankali ya na taunar fruits din kamar an yi mishi dole ya sha , duk sai ta ji ta kassa janye idanun ta da ga saman bakin shi ta na tunanin yadda a ka yi wannan dan karamin bakin ya iya tsawa da karfi haka , ga bakin dan guntun amma in ya bude shi kamar an ba shi speaker

 

ta na a haka kawai ta ga ya fiddo tongue din shi a hankali ya daura hannun a sama

 

shi ko ya na tsaka da taunar fruits din ya ji kamar wani zare ya shige mishi tsakanin hakwaren shi , a hankali ya kai hannu ya dauki zaren saman tongue din shi

ya matso shi saitin fuskar shi ya na kallon shi , nan ya ga ashe ba zare ba ne gashi ne

 

ai bai yi wani motsi ba kawai ya ji zuciyar shi na tashi

a dubu dari ya mike tsaye ya nufi hanyar kitchen da mugun gudu

ya na shigowa ya nufi wajen wanke dishes kawai ya fara kwararo amai

a tare duk chef din wajen su ka ji zuciyoyin su sun buga specially wanda ya yanka fruits din

su na kallon yadda Ash ke amai kamar diyan cikin shi za su fito har wani neman dunkusawa ya ke tsananin ya na shan wuya , idanun shi su ka jazir su ka ciko da ruwa

 

sai da ya gama sannan ya kunna fanfo ya kuskure bakin shi har uku kafin ya sauke wata yar karamar ajiyar zuciya

duk ma ya na jin zuciyar tashi na yi mishi zafi tsananin bacin rai

ji ya ke kamar kawai ya koma ya kashe Hayat dan wannan babban laifi ne ta aikata mishi , ji ya yi kamar ta yi kokarin kashe shi ne

 

cike bacin rai ya dago , a zafafe ya nufi knife ya zaro guda

su na ganin ya zaro knife kowane ya ja da baya ya na girgiza kai kamar za su yi kuka , shi ko ko ta kan su bai bi ba ya nufi kofar fita ya fice ya na taku da sauri sauri

 

bangaran Hayat kuma ta na nan cikin parlourn ko motsi ba ta yi ba , ta na tsoron ta motsa bayan bai bata izini ba yanzu ta shiga sabuwar matsala

shi ya sa ma kawai ta tsaya ta na tunanin ko lafiya ya tashi haka ga shi ko har gugu ya ke kamar wanda ya manta dahuwa saman gas cooker

 

ta na tsaye a haka kawai ta ji an zare mata hijabin ta ta baya da karfi har sai da ta dan daga kai sama

a razane ta yi kokarin juyowa , sai dai kafin ta juyo ya kai hannu ya damko gashin ta , dama ta nade shi da ribbon

lokaci guda ya sa knife din hannun shi ya yanke mata gashin har zuwa wajen ribbon din ya tilla mata gaban ta

 

idanun ta na sauka saman gashin ta saki wata razananiyar kara ta kai hannayan ta saman kan ta ta na shafawa ta ji Eh gashin ta dan va ribbon din da ta daure shi nan

a razane ta juya ta na kallon shi ta na zaro idanu ta na ci gaba da shafa kan ta

 

lokaci guda idanun ta su ka ciko da ruwa ta saki kuka ta na fadin ” me kuma gashina ya yi maka ? ” ta fada cikin kukan nata

 

a hankali ya dago hannu ya daura dan yatsar shi saman forehead din ta ya na dan bubuga shi da yatsar , cike bacin rai ya ce mata ” Next time , wannan kan zan cire ba gashin ba , stupid kawai ” ya na gama fadar haka kawai ya ji amai ya taho mishi

 

da sauri ya janye yatsar shi ya juya ya nufi stair da gudu ya Haye ya koma part din shi

ya bar ta nan tsaye ta na kuka , da kallo ta raka shi har sai ya haye sannan ta zube saman guyiwowin ta ta na ci gaba da kukan , ita ba ta ma san abun da a ka yi ba ga shi kuma ba ma laifin ta ba ne amma ita a ka bawa punishment

bisa yadda ta ke ji da gashin nan nata ji ta yi kamar rayuwar ta baki daya ya cire mata

 

haka dai ta zauna ta na wannan uban kukan hawaye na zubo mata bibiyu har da su majina

sai da idanun ta su ka kunbura su ka yi ja , kan ta ya fara yi mata ciwo sannan ta hakura ta fara rage sautin kukan

 

 

ta kai hannu ta dauki gashin ta , ta mike a hankali , duk jikin ta ya mace ga shi kuma kanta na yi mata ciwo har wani jiri ta ke ji ya na nema ya kwashe ta

amma a haka ta taka ta nufi corridor ta shiga , ta wuce part din Ummi kai tsaye ta wuce bedroom din su

 

ta na shiga ta ajiye gashin ta saman bedside drawer , ta zame hijabin jikin ta ta ajiye bakin gadon sannan ta nufi dressing mirror a hankali

 

a gaban shi ta tsaya ta na bin kanta da ido ,

 

( baiwar Allah har ta ban tausayi haka kawai ka cire wa yarinyar mutane gashi a kan laifin da ba nata ba , da sai ka fara tambayar ta mana , amma ba komai kanka ka yi wa 🤧🤧🤧 )

 

gashin nata ya koma dan kadan ko na Vedad ya fi yawa , dama duk sai ta matse shi sannan ta kame shi da ribbon , da ya tashi cire mata shi kai tsaye wajen ribbon din ya cire shi ya sa ya zama dan kadan

 

kawai sai ganin na yi ta kara sautin kukan ta ta juya da sauri ta haye saman gadon ta yi rub da ciki ta na kukan irin kukan nan mai cin rai ko

sannu sannu har ta share wajen good 20 minutes ta na wannan kukan

kafin ta fara rage sautin shi a hankali a hankali har ta daina baki daya , da ga nan kuma barci da ke tsaye a gefe ya na jiran dama kawai ya yi gaba da ita

Leave a Comment