*ƁATAN DABO*
*BY: RIAMCOOL*
*Assalamu Alaikum my Habibties barkammu da sake haɗuwa a new Book ɗina Ɓatan Dabo,ina godiya ga masoyana dake bibiyar litattafaina kuna kasheni da love, Allah ya bar zumunci da ƙauna, a yanzun ma kar ku bari a barku a baya RIAMCOOL na ɗauko tafiyar da ban taɓa yi muku ba, nai muku ɗan baka zata ba a littafin Ɓatan Dabo me rikitattun abubuwa nazo da salon da ban taɓa yi ba, Ɓatan Dabo yai fintinkau ya sha bam_bam da sauran litattafaina,fatan Allah ya bani damar rubuta abinda Al’umma za su amfana*
*WRITTER OF*
*RUSHEWAR RAYUWA*
*BAYAN WUYA*
*KULU*
*ANYA UBA NE*
And Now
*ƁATAN DABo*
P.1&2
Daji ajiyar Allah’ dare mahutar bawa a lokacin da wasu suka yada haƙarƙarinsu dan hutawa wasu suke kan bautatawa Allah a lokacin ne ita take gudun ceton rai, gudun tsira da rayuwarta da son samun mafaka ko dan tseratar da rayuwatar daga neman kawar mata da numfashi da Azzalumai ke ƙoƙarin yi ,sai dai a bisa tsautsayi tai tuntuɓe da wani girkakken dutse tana faɗuwa, cikin fitar hayyaci ta ƙwalla ƙarar da ya janyo hankulan mutanen suka yo kanta
Kanta da goshinta tuni ya fara tsirtuwar jini, tana fitar da wani kalar numfashi mai sauti da sauke nishi a lokaci ƙanƙani, ta tabbatar da rayuwarta ta datse tunda suka cimma ta sai dai sam ba zata yi nadamar tafiya,ba sai dai abinda ke saka zuciyarta rauni wanda tunawa dashi ya sakata fashewa da matsanancin kuka anzo gaɓar da ba zata iya daurewa ba ” tun ba aje ko ina ba kin fara kukan ganin mutuwarki, sai dai taurin kanki da kafiya ya jawo miki rasa rayuwarki, mafitarki ɗaya ce ki bani faifan Video dake gunki” taji saukar furucinsa tare da fashewa da wata sheɗaniyar daria
Sai dai tamkar ya watsa mata garwashi a zuciya haka taji da rinannun idanuwanta waɗanda suka jiƙe da jinin sharkaf ta sauke kansa dukda duhu ne ba ganinsa take a wajen ba sai dai tai yaƙinin nan yake, busasshen fatar bakinta ta ɗaga tana faɗin “sam ba zan ba ka ba sai na tona maka asiri azzalumi kalarka be kamata ka rayu cikin salama ba, ƁATAN DABON da kayi tabbas sai na saka mutane ganeka,” ta faɗa da ƙwarin guiwa
Fuskarta aka dalle da fitila yayin da kamar haɗin baki taji muryoyi ukku suna sheƙewa da dariya, yayinda hasken ya koma ya zuwa fuskokinsu da ƙarfin gaske taja da baya tari mai tsananin gaske ya sarƙeta tana nuna su da yatsa cikin fitar hayyaci da mamakin daya lulluɓeta gani mutumen da ƙwalwarta bai kawo mata cewar zai shiga sahun masu aikata ƙazantacciyar ɓarna ba sai dai kash ashe ya shiga yai amfani da wasu damammaki da har yai mata ƁATAN DABO ya toshe duk wata hanya da zata bayyana shi
” kina mamaki ne?sai dai karki damu da abinda kika gani, saboda babu buƙatar yi miki bayani saboda adadin daƙiƙun numfashinki ya fara” Babban mutumen ya faɗa da katse mata tunanin da take tunkaro inda take yayi yana mai saka hannu ya falla mata marin da sai da taga wulgawar taurari har ta ƙwalla ƙara mai tsananin ƙarfi wacce sai da dajin yai amsa kuwwa, sai dai ihunka banza kururuwarka wofi taken jejin da ba lallai akwai koda wulgawar wani ɗan Adam ba, ballantana ka saka ran samun ceto
A lokacin da take tsakanin rayuwa ko mutuwa kalmominsa suka shiga dawo mata “Feenah da da Alƙawari mutuwa ba zata ɗauke ki ba tare da ni ba ina mai tabbatar maki a lokacin da Mutuwa za tazo a tare za ta ɗauke mu babu abinda ya isa ya rabamu, adadin ƙaunarki ba zata musultu ba, da ace ana bada fansar rayuwa to ni zan baki tawa ke ki rayu cikin salama” sai dai kash mutuwar tai mata shigar sauri ta zo mata a yanayin ɗan baka zata ba, ta zo mata a lokacin da yai nesa da ita ta zato ko tsammani bai wanzu akan adadin daƙiƙun numfashinta zai ƙare ba a hankali wasu siraran hawaye Masu zafi suka shiga zarya a fuskarta,da ƙarfin gaske suka rabata da suturarta tana ji tana gani
suka yaga mata rigar mutunci tare da mutumen da take martabawa take mishi kallon kamili kimtsatstse mutumen da take gani zai iya bada rayuwarshi dan ya ceci tata sai dai dashi aka keta mata haddin da take fafutakar ƙwatarwa wasu tana mai shiga ta fita kan ganin samarwa mata ƴanci sai dai gashi itama a yau bata tsira ba tun tana iya motsi har yakai ga adadin numfashinta ya riga daya ƙare a doron duniya,
**************
KANO
Babban gida ne wanda za a iya kiransa da gidan Gandu saboda yawan mutanen da ke ciki uwa uba yara da suka cika gidan da hayaniya ga yawansu ya ɓaci tamkar ƙudaje ko wanensu ya bi layin karɓar Koko Wanda bai fi ko wane a ɗiga mishi ludayi biyu ba, da ƙarfin gaske Huraira tazo kan mai raba kokon tana mai dangwarar da robar koko tare da riƙe ƙugunta kam tana girgizashi da ƙara turo ɗaurin ɗan kwalinta gaban goshi cikin masifa ta ɗaga fatar tsinin bakinta tana faɗin “Wai ni Rayya me kika ɗauke Ni da idan kika zo rabon koko za ki dinga tarhwa min shi kamar wacce na roƙo to billhillazi baki isa ba yanda kike taƙama mijinki ne ya kawo nima fa haka nake taƙama da mijina ne ya kawo geron Kokon ki ƙara min ko wllhy na danneki na ƙwaci bokitin Kokon nan”
Ta faɗa har ya zuwa lokacin bata daina girgiza ƙugu ba, cikin masifa Rayya ta miƙe tana mata kallon hadarin kaji tare da fatali da roban yaron data karɓa za ta zuba mishi koko “Huraira wllhy ba zan ƙara miki ba idan za kisha kisha idan kuma ba za ki sha ba na juye a ƙara da naki kason” ta ƙarashe cikin masifa
kanta Hurairah tayo tana mai kiciniyar ɗaukar bokitin nan fa dambe ya kacame a tsakaninsu
sama_sama ta fara jin hayaniya cikin baccinta wani wawan tsaki ta saki tana tashi tare da buɗe manyan idanuwanta waɗanda suka kaɗa su kai jajir, yunƙurawa tai ta tashi tare da yin Fito Manyan karnukanta dake kwance suka tashi daga kwancen da suke ɗakin ta yunƙura tana fitowa karnukan suna masu mara mata baya tunga taja ta tsaya tare da harɗe hannayenta a ƙirji tana zuba musu shanyayyun idanuwanta ba tare da tayi magana ba, ganin fitowarta yaran da ƴan kallo da suka tsaya tuni suka watse ya rage sai Huraira da Rayya dake faman kiciniyar ɗaukar bokitin Koko, sai dai jin Haushin karnuka a bayansu ya saka ko wace sakin ƴar uwarta da suka maƙure juna, wani yawu suka haɗiye tare da juyowa baya sai dai Abinda suka gani ne ya razana su, musamman manyan baƙaƙen Karnukan *SUMAIMAH* da suke kallonsu suna haushi tamkar za su cinye su ga harshensu sai zaroshi su ke yi, feɗuwa ta sake yi wanda ya saka karnukan yin wata sufa tamkar za su cafki su Rayya, tuni su Rayya suka faɗi kwankwasonsu ya bugu, Karnukan kuwa bokitin Kokon suka ɗauko suna ajiyewa a gaban Sumaimah “ku shanye Kokon inga ubanda zai ƙara magana a kanshi ballantana har ayi dambe a kanshi” ta faɗa da wata kalar Muryar mai nuna zallar ta’addanci, muƙut suka haɗiye wani yawun takaici ga shi babu halin magana sai dai ko wanensu ya ja mata Allah ya isa a cikin ransa
ganin karnukan nan sun shanye Kokon tas har bokitin sun lashe ga wata yunwa dake ƙaƙular cikin su Rayya basu san sadda hawayen takaici ya zubo musu ba Sai lokacin Huraira take jin ina ma ba tazo a ƙara mata ba
ganin karnukan nan sun shanye Kokon ya saka Sumaimah miƙewa tana tafiya suka mara mata baya, kiciɓis su kayi da Inna sai dai ta kawar da kanta gefe da niyyar raɓawa ta gefenta ta wuce “Ina kwana” ta furta duk da tasan ko tayi duk a banza ba lallai ne ta amsa ba sai dai bata damu ba domin tana mata martababben kallon sunan *Uwa*da ta amsa dukda ita har izuwa yanzu bata karɓeta a matsayin ƴa ba bata ci wannan sunan a wajenta ba, dukda cewar ita ce silar zuwanta duniya ita ce wacce ta tsugunna ta haifeta
wata doguwar ajiyar zuciya ta sauke tana mai shigewa ɗakinta Toilet ɗin da ta saka aka fidda mata a ɗakin ta shiga ta watsa ruwa, tana fitowa tai shirinta cikin wasu riga da wando, red T shirt sai crazy jeans sarƙoƙi ta saka a wuyanta tare da ɗaura baƙin scarf, sai a lokacin hankalinta ya koma kan wayar ta tana mai ɗauka tarin missed call ne da yawa sai dai a ciki kiran Barde tabi, bugu ɗaya aka ɗaga ba tare da tayi magana ba tai shiru har izuwa lokacin idanuwanta a lumshe “Shugaba daman na kiraki ne a kan cewar kayan nan sun iso sai dai ke ce wacce za ki yanke hukunci akan wa za a ba tun….” “Ka ga Barde bar ni na ƙara so yanzu kuna ina, ina son duk inda kuke ku koma Harabar nan mu haɗe a can” tana gama faɗin hakan ta kashe wayarta
Kamar yanda tace su haɗe a harabar haka suka haɗu su duka, waje ta samu ta zauna ankai kusan mintuna ba tare da ta ɗaga fatar bakinta ba, “Shugaba ga kayan nan sannan akwai tarin maganganun da za muyi a yanzu” Barde ya faɗa yana kallonta
Sai a lokacin ta ɗago da shanyayyun idanuwanta tana zuba musu su, “ba ni buƙatar jin komai a halin yanzu, abinda nake so daku kayan nan ka rabawa waɗanda suka kamata,ina son zuwa anjima muje karɓan yaran can,yanzu ba ni Allura ɗaya cikin kayan da aka zo dasu” ta faɗa da miƙa masa hannu
Kallon Aisu Barde yai, alamar ya bada Alluran ba ta su kayi ta saka a Aljihu “ban makullin mashin ɗin ka” ta faɗa da miƙawa Barde hannu, miƙa mata yai ta fice Mashin ɗin ta hau wanda tayi tafiya sosai kafin ta nufi cikin jejin da shigar shi zuciyarta ke rikiɗewa ya zuwa wani ɓangaren, bukkar da akai mata ado da jan ƙyalle da baƙi ta nufa sai a lokacin idanuwanta suka ƙara rikiɗewa ya zuwa jajir jijiyar kanta ta fito ruɗu_ruɗu da ace da akwai wani a kusa da ita zai ji sautin bugawar zuciyarta tamkar yanda Agogo ke bugawa Allurar tai saurin fitowa a Aljihunta tana mai miƙar da hannunta ta saketa a jijiyar hannunta tare da lumshe idanuwanta da suka fara mata yaji sautin buguwar zuciyarta ya ƙaru
Kanta ya ɗauki zafi tamkar ya tarwatse a gida biyu, sai a lokacin tayi jifa da Sirinjin Alluran bayan ruwan sun gama shigarta ɗaga ƙafarta tayi da zummar taka bukkar nan wani razanannen ihu ta saki tana dafe kanta
*************
*GOMBE*
gari ne daya tara ƙabilu musamman Fulani a ciƙin wani ɗan ƙaramin ƙauye *FUNNUKA’EH* da kwanciyar hankali da zaman lafiya yai musu ƙaura musamman mata da duhun magriba ya doso babu wata macen da za ta ƙara yawo ko dan tsira da mutuncinsu da kare martabar su ta ƴaƴa mata
gudu take ƙyalƙyalawa ba na wasa ba kallo ɗaya za kayi mata ka tabbatar da tana a cikin zallar tashin hankali musamman yanda bakinta yake zubar da jini, ƙafafuwan ta kuwa duk inda ta taka sai sawun jini ya bayyana tana zuwa inda mutanen garin suka taru ana shagalin auren ɗiyar mai gari, faɗuwa wajen tai tana sheshsheƙa ga numfashinta dake sama da ƙasa “ku taimaka wasu ne_ wasu ne…..” tai shiru saboda kukan da yaci ƙarfinta
“Wasu ne me Fatsime,shin sunyi miki wani abun ne?” Lariya ta tambaya da tashin hankali
“A a Hansai dai ce suka kama ni kuma suka biyoni ku taimaka ku ceto ta” Fatsime ta faɗa da wani marayan kuka
Tamkar waɗanda ta faɗa wa wani mugun abun da suma zai bayyana a kansu haka suka ja baya kowa yana ƙare mata kallo wajen yai tsit a hankali ta ɗago da idanuwanta tana faɗin “ba wanda zai cetota ne ku taimaka mata ko dan ta rayu a cikin Ahalinta,” Fatsime ta faɗa da haɗa hannayenta
Awurɗo ne ya dubeta yana faɗin “Fatsime sanin kanki ne duk wanda yaje ceto shirinsu na gaba a kanshi ne zai faɗa duk a cikimmu babu wanda zai iya sai dai mu jirayi lokacin da za su maidota idan sun gama abinda su keyi da ita” Awurɗo ya faɗa da kawar da kanshi gefe yayinda Fatse ta sake fashewa da wani marayan kuka tamkar za ta shiɗe
Busar da ta karaɗe ko ina ne ya saka Matan wajen watsewa da gudun a ciki kuwa harda Fatse wannan busar ta tabbar musu da za su Maido Hansai, mazan kuwa duk mai kallon gaba sai ya mai da kallonshi ya zuwa baya har lokacin da suka ji motsin ajiye Hansai a wajen wacce sai faman gunjin kuka take, bindigar da suka harba ne ya tabbatar musu da sun juya sun tafi
Sai a lokacin ne kowa ya juyo ya zuwa wajen da Hansai take da gudu mahaifiyar Hansai da Mahaifinta suka nufi wajenta suna tallafota jikinta kuwa duk ya ɓaci da jini “kar ta ƙara wasu Mintuna ya kamata a bar nan da ita ko ta tashi ta bar kauyen nan da ƙafafuwan ta kar ta sake jaza mana wani masifan tunda har a kayi zina da ita…………..
DOWNLOAD COMPLETE HERE 👉🏾https://shorturl.at/0xvDM
DOWNLOAD PDF HERE https://shorturl.at/0xvDM
*RIAMCOOL ce*
*Zan dinga posting ba kamar sauran Novels nawa ba da nake kullum, sau biyar zan yi posting a satin ma’ana Asabar da Lahadi ba zanyi ba*
*Share and commentt*

Leave a Comment