Ashe Ummi rahab ba shi ne asalin sunan taba Ashe Mahaifiyar Ummi Yar Nigeria ce Ashe Mahaifin Ummi ba dan ƙasar Saudiyya bane maye dalilin da yasa Ummi Rahab bata tare da iyayenta A halin yanzu Maye Gaskiyar maganar cewa bada aure aka haife Ummi Rahab ku biyo mu cikin wannan labarin domin jin cikakken Labarin.
Acikin wata hirar sirri da Kannywood reports tv tayi da ɗan uwan Ummi Rahab mai suna Yasir ya bayyana abubuwa masu yawa agame da Ummi Rahab, wadanda suka hada da Sunayen mahaifanta da kuma yadda aka yi Ummi tazo Nigeria tunda ba A Nigeria aka haife taba da bayanin yadda aka canzawa Ummi suna zuwa Ummi Rahab.
Da farko mun tambaye shi ya bamu takaitaccen tarihin sa sai yace Sunana Yasir kuma Ni dan Uwan Ummi ne ai haife Ni a kasar Saudiyya Kuma mafiya yawan Ƴan Uwana suna Saudiya.
Da muka sake tambayar shi maye dalilin zuwan ku ƙasar Nigeria tunda a Saudiyya aka haife ku sai ya amsa mana da cewa Hakika Ni da Ummi Ƴan Asalin Ƙasar Saudiyya ne an kawo mu Nigeria ne domin muyi karatu sannan mu samu tarbiyya irin ta Nigeria domin tarbiyyar Saudiyya da Nigeria ba iri daya bace acan Yaro na iya kai mahaifansa Kotu Hakan tasa tun da muna da Ƴan uwa a Nigeria aka turo mu nan domin mu zauna muyi karatu.
Da muka sake tambayar shi maye Gaskiyar maganar da ake yadawa akan cewa mahaifiyar Ummi ba ƴan Saudiyya bace Ƴar Nigeria ce, sai ya Amsa mana da cewa Eh gaskiya ne mahaifiyar ta Asalin ta Ƴar Nigeria ce Amman bata taɓa zuwa Nigeria ba.
Hakazalika da aka tambayi shi akan mahaifin Ummi shi ma ana zargin ba dan Ƙasar Saudiyya bane kamar yadda ake ta raɗe raɗi sai ya bada amsar cewa Kwarai shi ba Asalin dan ƙasar bane Mutumin Bangaladesh ne Amman kasan suna zuwa Saudiyya kuma idan suka ga macen da tayi musu suna auren ta.
Da Kannywood reports tv ta zake tambayar shin wai maye Asalin sunan Ummi ne sai yace Asalin sunanta Rahama Amman a ƙasar Saudiyya tunda su Labarawane suna Kiranta da Raham ana Nigeria ne Adam a zango ya sanya mata Rahab Amman Asalin sunanta Rahama ne.
Shin Yasir maye Gaskiyar maganar da ake yadawa akan cewa Ummi Rahab ba da aure aka haife taba, sai ya bamu amsa da cewa kaƙaddara haka ne to maye laifin ta Laifin wani baya shafan wani a gurin Allah mutanene kawai suke ta faman Suratu akai Wanda wallahi idan mutum bai wasa ba zai iya shiga wuta maganar gaskiya Iyayen Ummi Aure sukayi suka haife ta.
Shin maye dalilin da yasa ta fara Film?
Shin maye dalilin da yasa Har yanzu iyayen ya basu bukace taba ?
Shin maye Gaskiyar maganar da ake yadawa na cewar mahaifiyar Ummi Rahab ta rasu.
Shin maye Ummi Rahab take Nufi da zata tonawa Adam a zango Asiri ?

Leave a Comment