Books Reviews & FAQs

Tayi Min Kankanta Hausa Novel Complete

TAYI MIN ƘANƘANTA*

*Zahra Surbajo*

*Sadaukarwa ga Ahalin Sharoo Gambo Yako,mazan su da matansu,alherin Allah yakai muku a duk inda kuke,nayi tawassali ga Annabi Muhammadu (SAW),Allah kai ruƙo da hannayena dan alfarmar ahalin manzon Allah (SAW)*

_Bissimillahirrahmanir raheem_

_wannan littafin nawa ƙirƙirarsa nayi banyishi dan wani ko wata ba,duk abinda kaga yayi dede da rayuwarka arashine_

_wannan daban yake da sauran,salonsa na dabanne,akwai abun dariya,zazzafar soyayya,tausayi,ƙiyayya,da ɗumbin danasani,karku bari abaku labari,kubishi sannu a hankali dan kwashe darasin dayake tafe dashi_

_surbajon ce de har yanzu,salo da basirar duk nata ne,nice da kaina ba saƙo ba,ga me_

*Ummu Aymana*
*Surbajo*
*Kano to jiddah*
*Karen bana*
*Sanadin kidnapping*
*Ɗan karuwa*
*Cin Amana Ko Fansa*
*Giɗaɗo ba Shege Bane*
*Allah Gatan Bawa*
*Ƴar Bautar Ƙasa*
*Aure Da Haihuwa*
Da de sauransu.ku kasance da wannan banufiya domin ci gaba da samun nishaɗi.😍

*1*

 

“Zahra’u ya kamata ki fito haka fa kizo ku wuce,tun ɗazu su hanne ke tsaye suna jiranki,bana son sakarcin banza fa”cewar wata dattijuya dake zaune kan kujerar zaman tsakar gida tana ɗaure nono a ledar siga.

Daga can cikin bukkar dake kusa da dattijuwar wacce aka kira da Zahra’u tace “Inna do Allah Do Annabijjo,ki barni in sa jambakina cikin kwanciyar hankali,ke bakisan in bakayi kwalliya ba ko kallonka ba’a yi?”

“aykin kawai,yo tun bara kike sa jambakin amma har yanzu ba mashinshini,se asarar kuɗin siya miki da nike yi”cewar inna daga wajen da take zaune.

Fitowa tayi daga cikin bukkar tana gyara ɗamarar da ta ɗaura a ƙugunta,ko ina a fuskarta kwallliyace irin ta fulani.
Laɓɓanta shafe cikin jan janbaki,yarinyace da bata wuce shekaru goma sha biyar ba.

“kede Inna kinada matsala,bakin ki be taɓa faɗin alkha’iri,se sharri,ni ɗoramin mu tafi”ta ƙarasa maganar cikin turo ɗan ƙaramin bakinta gaba.

Gammo ta ɗora sannan ta ɗora mata kwaryar nonon akanta,ta miƙa mata ledar viva da aka sa ludaya da ƙorai aciki,ta juya gun su Hanne dake tsaye zaman jiranta tayi murmushi kumatunta suka lotsa,siririyar hushiryarta ta bayyana atsakanin fararen haƙoranta masu kyan tsari,tace “na ɓata muku lokaci kuyi haƙuri,mu tafi kar mu sake ɓata wani lokacin”

Murmushi sukai mata,sannan suka rankaya suka fice bayan sunyiwa inna sallama.

Tafe suke suna hirar su ta yau da kullum,ɗaya daga cikinsu Me suna haule tace”wai duk ƙawancen nan namu muna aure inba riga ɗaya muke ba se ya ragu ko?”

Dariya Zahra’u tayi sannan tace,”Allah ya kyauta,ni aradu ko birnin sin naje aure bazan dena ƙawance daku ba,bare ma dukanmu muna ruga ɗaya ba inda zamu”

Hanne ce ta amshe zancen da cewa”ni Auran ma tsoro yake ban,kunga de Ma’u kamar abun arxiƙi Rabi’u ya Aureta amma ku dubi wulaƙancin da yake mata yanzu”

“shiyasa na shiga makaranta dan bazan yarda namiji yamin wulaƙanci ba,”cewar Zahra’u tana murmushi.

Da wannan hirar tasu suka ƙarasa fitowa daga cikin dajin falgore inda rugarsu take,suka miƙo tsawon titin zuwa inda barikin sojojin dake cikin dajin yake,sabida ankawo sababbin sojojin da ake ba training gurin acike yake da mutane kamar kasuwa,dan motocima in sun zo gurin da ƙyar suke wucewa sabida yawan sojojin.

Basu jima da zuwa ba kowa kayanta ya ƙare sabida ƙarancin abincin gurin,a hannu a hannu ake siyan duk wani abun ci na gurin.

gurin me saida burodi suka ƙarasa kowa ta sayi guda ɗaya sannan suka juya cike da farincikin sun sayi burodin da zasu ci yau agurin alibidin sunan Zina,wata ƙawarsu data haihu.

Karo suka ci da wani matashi sanye da wandon sojoji,hannunsa riƙe da bindiga,se riga tshits army green da hular sojoji,ba laifi kyakkyawane,raɓewa sukayi zasu wuce ta gefenshi yayi sauri yasha gabansu yace yana murmushi,

“don Allah kuyi haƙuri mu baƙi ne anan,kuma abinci mukeso mu ci,isowar mu kenan daga Abuja,amma mun rasa”

Harara Zahra’u ta galla masa sannan tace”amma dan baƙin hali ay kuna gani muka kawo tallan nono, in yunwar kukeji me ya hanaki siya?”

Murmushi yayi dan ya fahimci yarinyar akwai tsiwa,cikin taushin murya yace”Bamu lura bane ƙanwata,ayi haƙuri”

“to yanzu me kukeso muyi muku,tunda mude ba abinci bane bare ku cinyemu”cewar Zahra’u batare da tsoron komai ba,dan ita ba ƙaramin abu bane ke firgitata.

“in anan kuke don Allah ku taimaka mana, kuɗin cefane zamu baku ku dafo mana abincin ku kawo mana nida abokina,”

Shuru sukayi sannan hanne tace”gaskiya rigarmu da nisa nide bazan iya zuwa gida in dawo ba”

“yo inba wahalalle ba waye zeje gida yadawo nan”cewar haule.

“don Allah ku taimaka abokina yanada lalurar gyambom ciki be jure yunwa don Allah ku taimaka ku yi mana kamin yafara jin yunwa wallahi zamu biyaku ladan yi”cewar matashin kamar zeyi kuka.

Zahrau tsintar kanta tayi da tausayawa abokin nasa,sabida itama tana da lalurar gyambom cikin tasan azabar ziwon,dan haka tsintar kanta tayi da cewa

“kawo kuɗin,zan dafo muku,sede muna da nisa zaku iya jira?”
Da sauri matashin ya gyaɗa mata kai,sabida tun ɗazu yake neman wanda ze dafo musun amma be samu ba,ga abokin nashi shegen taurim kai shiba jure yunwa ba amma ko ze mutu baze ci abincin siyarwa ba,shiyasa duk yabi ya damu.

Hannu yasa a aljihu ya ɗebo kuɗin dashi kanshi besan adadinsu ba yabata,juya kuɗin take a hannunta tana mamaki,amma batace komai ba ta ɗauka da yawa suke so, dan haka ce mishi tayi”zan kawo ma insha Allahu ka tsaya a bakin titi de inda zan ganka da wuri”

Godiya yay mata sosai sannan yace”mu haɗu kawai anan,zefi sauƙi,sunana Capt Jameel Ahmad zan jiraki anan”

Bata ce komai ba suka juya suka wuce ita da ƙawayen nata,wanda gaba ɗaya haushinta sukeji,cikin fushi hanne tace.
“nufinki de bazaki gidan sunan ba ko?shiyasa kika amshi girkin gardawan da baki sani ba”

Batare da damuwar komai ba aranta tace”dan bakusan ciwon ulcer bane da kuma kun tausaya kun musu,nide zan musu sabida Allah”.tana kaiwa nan tai gaba ta ƙyalesu a baya.

Muje zuwa.

Surbajo for life.
[1/6, 10:15 AM] Zahra Surbajo:
*TAYI MIN ƘANƘANTA*

*Zahra Surbajo*

*2*

 

Gudu-gudu sauri-sauri Zahra’u ke tafiya zuwa gida,dan azahar ta kusa,
Tana shiga gida bukkar innarta ta shiga da sallamarta.
“wai har kun siyar?”cewar inna bayan ta amsa sallamarta,
Murmushi Zahra’u tayi sannan tace”wallahi inna mun siyar,yanzu ma wasu sojoji ne,suka roƙeni in dafo musu abinci,yunwa sukeji gashi suna da me ulcer acikinsu,shine na dawo in musu”daga haka ta kwashe komai ta faɗa mata,gami da bata kuɗin.

Sosai inna ta tausaya musu sannan tace”Allah miki albarka Batulu na, daɗina dake akwai tausayi, maza zo kije ki cefano abinda yadace ayi sauri ayi musu”

Daga haka miƙewa sukayi suka fito tsakar gida,inna ta bata kuɗin cefanen ta tafi.
Kamin la’asar sun kammala komai,abinci lafiyayye bame cewa daga rugar aka girkoshi,domin,harda,cincin,dublan,duka masu jimawa basu lalace ba kasancewar can cikin garin falgoren Zahra’u tazo cefanen,shiyasa tasamu komai.kasancewarta ƴar makarantar gaba da primary,kuma ɓangaren sciece yasa ta iya komai,sabida food and nutrition da ake koya musu.

Ga kaji da zabbi da suka soya musu rabi da mangyaɗa,rabi kuma da manja sabida me ulcer shima yasamu yaci,suyar sosai tayi kyau.a ledoji ta juye sannan ta zuba abincin a kular abincin baffanta,

A babbar roba ta zuba komai sannan tayi gammo ta ɗauka,inna ta bata canjin dubu biyar daya rage tace ta mayar musu,amsa tayi sannan ta juya ta nufi barikin.

Kusan mintuna arbain ta kwashe tana tafiya kamin ta iso bakin titin,sannan ta ƙarasa gurin da sojojin ke tare.
Inda sukayi dashi zasu haɗu nan ta ƙarasa,ga mamakinta yana tsaye agurin yana jiranta,yana hangota ya taho da sauri ya tarbeta yana murmushi.

Kama mata kayan yayi ta sauke,sannan tace”kuyi haƙuri wallahi gidanmu da nisa ne shiyasa”

Murmushi yayi yace”Ko kaɗan baki buƙatar bamu haƙuri,mune yakamata muyi hakan,mungode sosai,Allah saka miki da alkhairi,”

Canjin ta miƙo masa tace “ga canjin ku inna tace in dawo dashi,kuma tace tanawa abokin naka me ulcer ya jiki dafatan Allah ya bashi lafiya”

Sosai wani jin daɗi ya bayyana a fuskarshi,aranshi ya yaba da tarbiyyarta,cikin murmushi yace”ki maidawa inna kuɗin kice mungode”

Fafur taƙi amsar kuɗin,duk yadda jameel yayi da ita ƙin amsa tayi dole ya maida kuɗin aljihunsa,

“gobe in munzo talla zan tafi da kwanukan”tace sanda take ƙoƙarin tsallaka titi domin ta koma gida.

Sallama sukayi ta tafi,jameel yabi bayanta da kallo yana yaba natsuwarta da hankalinta.

Duƙawa yayi ya ɗauki,robar abincin ya nufi tantin da suka haɗa na tempol sabida ruwa da rana,kamin ay musu izinin shiga cikin barikin.

Zaune yake daga ƙarshen tantin,yana latsa wayarshi,hannunshi ɗaya,riƙe da bindigarsa,
Farine sosai yana da ɗan faɗin fuska kyakkyawa ajin farko,sede ko kaɗan ba fara’a fuskarsa.

Sanda jameel ya shigo tantin,a yatsine ya ɗago kyawawan idanuwansa ya kalleshi sannan ya amsa sallamarsa.

Robar abincin ya ajiye akusa da shi sannan ya shiga ciro kayan dake ciki,

Buɗe ledar soyayyun kajin yayi,sosai yayi mamakin ganin harda wanda aka soya da manja,

Ƙamshin abincin ne,yasa ya ɗago kansa da sauri yana bin ledar da kallo,da sauri ya matso kusa da jameel,yana faɗin”kunyi waya da mummy ne?”ya tambaya cikin zaƙuwa.

“me ka gani”jameel ya tambaya.

“itace kawai take soyamin kaza da manja sabida ulcer ta,shiyasa nayi zargin kunyi wayane”

“ko kaɗan,wannan wasu nasamu suka dafo mana,daga cikin garin nan,ka matso kaci abinci kasan tunda mukazo baka ci abinci ba tun ɗazu hankalina be kwanta ba sabida baka ci abinci ba”

Tausayin jameel ɗinne yakamashi ganin yadda yadamu dashi fiye da kansa,yasan duk ƙoƙarinnan yayine domin shi.

Ba musu ya matso yasa hannu ya ɗauki cinyar kazar yasa abakinsa,daɗin daya gauraye bakinsa sosai yatafi dashi,zagewa yayi yaci abincin sosai dan wannan girkin ma yafi na mommynsa daɗi.

Bayan sun gama cin abincin,su cincin da dublan din duk acikin jakun kunansu suka saka,sabida taimakon gaggawa,abincin kuma rufe sauran sukayi,sabida dare.
Se a lokacin suka samu natsuwa,Jameel ne ya dubi abokin nasa yace cike da kulawa”Gaskiya Hammad yarinyar nan ta iya girki,ba me cewa ita ta girka,ji abinci don Allah sekace a birni”

Cikin rashin fahimta,Hammad ya kalleshi,yace”dama yarinyace ta dafo abincin?”

“eh yarinya ce dan bata wuce sa’ar su surayya ba,ma’ana bazata wuce 14 to 15 years ba,nono suke siyarwa na roƙeta ta girko mana”

Sosai abun yaba Hammad mamaki dan shi de in ze iya tunowa ba ya jin ko gas surayya ta iya kunnawa bare ayi zancen dafa ruwan zafi,to taya yarinya sa’arta za’ace har tafi mummynsa iya girki,ta ya?

“Dan haka in munyi settling komai zan bita inga gidansu,dan mu dinga zuwa cin abincin can gidansu mudena sata wahalar kawo mana”jameel ya faɗi yana kallon Hammad ɗin.

“ba damuwa “Hammad ya faɗi yana nazarin zancen.

“innarta ma tace aymaka sannu gameda ulcer da take damunka “jameel ya faɗi yana murmushi dan yasan bazasu wanye lafiya ba.

A fusace Hammad ya dubeshi yace”Au kace bara kaje kayi da ciwon dake damuna,amma wallahi ka cuceni kuma ba inda zani wallahi bazan je gidan nasu ba”ya faɗi sanda ya miƙe ya fice daga tantin.

Muje zuwa

Surbajo for life
[1/6, 10:15 AM] Zahra Surbajo:
*TAYI MIN ƘANƘANTA*

*Zahra Surbajo*

*don Allah masu cewa asa su agroup ɗinnan kuyi haƙuri ni bana adding,haka kuma bana tura novel private,iyakacina posting a group,kar ki buƙaci ɗaya daga ciki ban miki ba kiji haushi,pls*

*3*

Har dare Hammad haushin Jameel yake ji,dan shi a duniya ba abinda ya tsana irin a faɗawa stranger yana da ciwon ulcer,aganinshi kallon mayunwaci za’a masa.
Haka suka ci abincin se cika yake yana batsewa.

Koda gari ya waye,basu wahala ba cincin sukai ta ci da dublan.

Wajen azahar Hammad yafara jin yunwa,duk yadda yaso ya daure ya kasa dole ya isa ga Jameel wanda shima tun ɗazu yake kallon hanya yanaso yaga ta ina zata ɓullo.

“ya kamata fa kasamo wasu yaran abasu kuɗin suje su girko mana abinci ni yunwa nakeji”hammad ya faɗi sanda ya isa ga Jameel.

“karka damu nasan yarinyar jiya zata dawo,tabani tabbacin hakan,mu ɗan jirata kaɗan”Jameel ya bashi amsa cike da kulawa.

Hammad Juyawa yayi ya nufi cikim tantinsu,Bayan yaba Jameel ɗin wayarshi ya riƙe masa.kamar jira yana barin gurin Zahrau ta ƙaraso gun Jameel ɗauke da kwaryar nononta,ɗaya hannun kuma ledar abincin data dafo musu,shinkafa da wake dafadukan manja taji alayyahu da albasa se ƙamshi take.

Murmushi tayi tace”duk da baku buƙata ba amma na dafo muku wannan,sabida me ulcer nan”ta faɗi tana miƙa masa ledar da kular abincin take.

Da Sauri ya amsa yace”mungode sosai wallahi,shima yanzu yagama tambayarki,nace baku zoba tukunna”

Murmushi tayi batace komai ba,Wayar da Hammad ya miƙo masa ya riƙe masa ya ɗaga yasa camera yace”yakamata muyi hoton tarihi ko ƙanwata?”

Zahra’u murmushi tayi batace komai ba ya fara ɗaukarsu hotuna,tana dariya wani tana murmushi,har seda yagaji ya dena ɗaukarsu selfie ɗin.

Kwanikan jiya ya bata,dan dama suna ajiye agefenshi,sannan ya ɗauko kuɗi masu yawa ya bata yace”ki ajiye wannan agurinki ki dinga yo mana girkin,in sun ƙare ki sanar dani zan ƙara miki,sati uku zamuyi anan mu tafi”

Amsar ƙuɗin tayi tana murmushi,ta juya tabar gurin ta ƙarasa inda suke siyar da nonon.

Ɗaukar ledar Jameel yayi ya nufi gun Hammad,da hanzari,dan yasamu yaci abincin.

Ganin jameel da abincin sosai ran Hammad yayi masa daɗi,matsowa yayi kusa dashi yana murmushi duk fushin da yake ya huce,yace”ta zone yarinyar?”

“Kana baro gurin tazo wallahi,yarinyar akwai kirki ga sanin ya kamata,kaga yau tun kan musa tayi tayo mana”

“naga alamar hakan”Hammad yace sanda ya ciko cokali da abincin ya danna abakinsa.

Lumshe ido yayi yana tauna abincin gashide ba nama akasa ba amma daɗin abincin ya wuce inda yake tsammani.

Jameel na janshi da hira ko sauraronsa bayayi ya maida hankali kan abincin seda yaji yacika cikinsa tab sannan ya ajiye cokalin.

Kamar daga sama suka fara jiyo ƙarar harbe harbe da guje gujen mutane ana ihu.

A hankali suka fito daga tantin ga mamakinsu ankashe mutane da dama agurin musamman ƴan talla da suka zo.

Harbin ne yafara yo ɓangarensu,da gudu suka nufi bayan wani dutse,hankali atashe,Jameel a firgice ya kalli hammad yace”ƴar filanin nan data dafo mana abinci tana gurin can,bari inje in taimaka mata kar wani abu yasameta”

Yayi yunƙurin zuwa harbin ya yawaita dole ya tsaya,guri yayi guri domin tankokin yaƙi aka fito dasu daga cikin barikin aka fara ɓarin wuta tsakanin sojoji da Ƴan bindigar da suka kawo hari garin,dan tuni sun shiga cikin rigagen sun ƙona komai sun kashe mutane,shine suka dawo nan bakin titin.

A gigice Jameel yaja hannun Hammad suka ruga da gudu zuwa cikin jejin domin su samu mafaka,sede ƙarar da jameel ɗin ya kwalla ce tasa Hammad tsayawa ya waiwayo yaga me ya samu aminin nasa,

Wayyo Allah harbinsa akayi agadon baya,rungumeshi yayi suka faɗi tare,ya tallafoshi yana ƙarajin kiran sunanshi,”No!!!!!!!! Jameel !!!!!!!! wake up!!!!”!!”yana ihun jijjigashi,Jameel wanda idonsa ke shirin lumshewa a hankali yace”ka kula da ƴarfilanin nan Hammad”yana kaiwa nan yafara salati jini na fitowa ta bakinsa.

A gigice yake jijjigashi amma ina jikinshi ya riga ya saki.

Ihu Hammad yake iya ƙarfinsa yana jijjiga aminin nasa,yana kiran sunanshi,amma shuru,

Harbin da ake yowa ta ɓangarenshine yasa ya miƙe da gudu,Ɗauke da Aminin nasa a kafaɗa ya ƙara nausawa cikin jejin,zuciyarshi na masa zafi.

Muje zuwa

Surbajo for life.
[1/6, 10:15 AM] Zahra Surbajo:
*TAYI MIN ƘANƘANTA*

*Zahra Surbajo*

*5*

Ƙara shigewa jikinshi take,sabida sanyin da takeji,a hankali ya miƙa hannu ya zagayeta,ƙara kwantar da kai tayi ajikinshi tana rawar sanyin.

Duk yadda Hammad yaso ya yaƙi zuciyarshi akan Zahrau ina shaiɗanne ya shiga ƙawata mishi ita a zuciyarshi..
A hankali yake shafa kanta,sannu a hankali ya zame ɗankwalin dake kanta,gashin kanta yake wasa dashi,

A zuciyarsa beson abinda yake matan amma shaiɗan yariga dayafi ƙarfinsa,

Ƙoƙarin kwance mata zani yake,se alokacin ta farga ta fara riƙewa,ƙarfi ya gwada mata ya rabata da zanin yayi fatali da ɗan wandon dake jikinta,

Sanda ya afka mata wata gigitacciyar ƙara ta saki sabida azabar datakeji,cikin kuka take faɗin”soja me ulcer ba kyau kar kayimin,don Allah ka tausayamin,kayi haƙuri,soja me ulcer!!!!!!”haka take kuka tana dukan gadon bayansa.

Hammad shima kukan yake,yayi iya yinshi wajen ganin ya kaucewa faruwar hakan amma ina ciwon da marainansa ke masa da shaiɗan su suka taru sukai galaba akanshi.

Be saurara mata ba seda buƙatarsa ta biya,Ya gangare gefe yana kuka,baiwar Allah kukan ma gaba ɗaya babushi a idonta ware ido kawai take cikin duhu,

A hankali ya miƙa hannu ya lalubota jikinshi ya janyota ya rungume yana cigaba da kukan,”Kiyi haƙuri da abinda nayi miki,sharrin zuciyane,kiyafemin nayi alƙawarin kulawa dake har ƙarshen rayuwata,zan miki gata in zamo katanga agareki,ina matiƙar ƙaunarki ƴarfillo”kukane yaci ƙarfinsa yayi shuru.

Lamo tayi ajikinshi bata ko motsi se hawaye dake biyo fuskarta,a haka suka kwana kowa be runtsa ba,shi zazzabi itama haka.

Ratsowar haske cikin bukkar ne yasa Hammad farkawa daga baccin daya saceshi,lokacin itama zahra’u baccin takeyi.

Kwantar da ita yayi aƙasa ya rarrafa ya fita daga bukkar,neman inda ze samu ruwa yana fitowa yafara laluben hanya,sabida duhu kawai yake gani,yana cikin tafiya yayi karo da bishiya ya yanke jiki ya faɗi ƙasa sumamme.

Zahra’u farkawa tayi taga se ita kaɗai a bukkar shi ya fice,se agogon hannunsa dake ajiye agefe,a hankali ta miƙe jikinta na mata raɗaɗi ta ɗaura zaninta tana kuka,agogon ta ɗauka ta fito da ƙyar daga cikin bukkar tana kuka.dan tafiyar da ƙyar take yinta.

Sojojin bada agajin gaggawane suka shigo cikin jejin,anan suka ci karo da Hamnad yashe aƙasa da hanzari suka ɗaukeshi suka fice dashi da gudu kasancewar sunga yana da rai,suna kaishi bakin barikin cikin motar ambulance akasa shi da sauran sojojin da suka samu rauni a kayi kaduna dasu asibitin 44.

Da ƙyar Zahrau ta ƙaraso bakin titin tana kuka,isowarta tayi daidai da isowar motar ɗibar ƴan gudun hijira,ganin ƴan ƙauyensu da yawa agurin harda ƙawarta Hanne yasa batai tunanin komai ba itama tashiga motar,guri guda suka zauna da hanne suka rungume juna suna kuka sabida itama hanne an kashe iyayenta.

Tunda motar ta taso bata tsaya ko ina dasu ba se sansanin ƴan gudun hijira dake Abuja.

koda suka isa tantina suka samu an kafa musu agurin.

Banɗaki Zahrau tashiga sabida ta wanke ruwan dake zubo mata tun da safe,ga mamakinta harda jini tagani gawata ƴar tsoka dake lilo kamar leda koda ta ja zafi taji dole tasaki ta wanke jikinta sannan tayi wankan tsarki ta fito,tana rawar sanyi sabida da ruwan sanyi tayi.

Gurin hanne ta koma ta zauna tana cigaba da kuka,yayin da azuciyarta take tsinewa soja me ulcer bisa keta mata haddin da yayi.

Muje zuwa

Surbajo for life.
[1/6, 10:15 AM] Zahra Surbajo:
*TAYI MIN ƘANƘANTA*

*Zahra Surbajo*

*Hindatou Auwal,wannan shafi sadaukarwane agareki,bisa dogon nazari da kikeyi kamin kiyi comments akan kowanne post nawa,nagode sosai Allah yabar zumunci*

*4*

Yana tsaka da gudu,yayi tuntuɓe da wani dutse beyi auneba seji yayi sun faɗi,kanshi ne ya bugu da dutsen amma be damuba ya miƙe sede ga mamakinsa,ko kaɗan baya gani,hannu yasa ya murje idanunsa sam basa gani duhu ne gaba ɗaya ya mamaye idanun nasa.

Tashin hankali baa sa maka rana,Hammad dirza idonsa yake iya ƙarfinsa amma ganinsa be dawo ba,
Faɗuwa yayi agurin yana kuka,yama rasa me zeyi,wannan wacce irin masifa ce,kuka yake me tsuma zuciya,a hankali ya miƙa hannu yana laluben inda Jameel yake, amma yakasa jinshi.

Rarrafawa yayi yana ci gaba da lalubawa,Amma be jiyoshi,ba,abinda be sani ba,inda suka faɗi kusa ne da wani ɗan tabkin ruwa,Jameel cikin ruwan ya faɗa.

A hankali ya miƙe yafara tafiya yana ci gaba da laluben hanya,yama rasa ina zebi haka yake tafiya,ya faɗi ya miƙe,haka ya nausa cikin jejin yana zubar da hawaye.

Zahra’u ko tunda aka fara harbe harben nan,tasamu ta falla da gudu hanyar rugarsu,gudu take kamar zata tashi sama,har ta iso,sede ga mamakinta gidan nasu gaba ɗaya a ƙone yake,ga gawar innarta kwance a harbeta a kai.

Ihu tasaka ta nufi innar tata tana kwalla mata kira amma ina,kifewa tayi akanta tana kuka me tsuma zuciya.

Kuka take kamar ranta ze fita,tunowa tayi da Jameel dan haka miƙewa tayi da wani mahaukacin gudu ta koma inda tafito da zummar yazo ya taimaki innarta.

Lokacin data iso titin ne yaƙin ya ƙazanta,dan haka tsallaka titin tayi da gudu ta nausa cikin jejin domin tasamu mafaka kamim komai ya lafa taje ga jameel ɗin.

Tayi gudu me yawa acikin jejin,ruwan da aka fara yi ne kamar da bakin ƙwarya yasa ta fara neman mafaka,dan batason dukan ruwan sama,wata tsohuwar bukka ta hanga acikin jejin dan haka da gudu ta ƙarasa cikin bukkar tana rawar sanyi.

Shigarta ba jimawa shima Hammad ya ƙaraso gurin,jin yataɓa bukkar ne yasa yafara neman hanyar daze shiga ciki,da saurinshi ya shige shima,ƙofar bukkar yashiga laluba har yasamu ya ɗauka ya rufe sabida feshin ruwan dake shigowa.gefe ya samu ya zauna,ga mamakinsa ji yayi ya taɓa mutum a hankali ya ƙara kai hannunsa yana faɗin”waye anan?”

Zahra’u wacce tunda ya shigo tsoro yagama cinyeta,tace bakinta na rawa “Batulun inna ce,sun ƙona gidanmu ne kuma sin kashemin inna ta,shine nazo kiran capt Jameel Ahmad yazo ya taimakamin”ta ƙarasa maganar tana kuka.

Cikin firgici,yace “kece ƴar filanin dake dafo mana abinci?”
Da sauri Zahrau tace “eh nice,kaine abokinsa me ulcer?”

Da sauri shima ya gyaɗa mata kai sannan ya shaida mata Jameel ya rasu,sakamakom harbin da akai masa.

Sosai take kuka kamar ranta ze fita,daga inda5 yake, yake bata haƙuri gamida rarrashinta.

Suna cikin bukkar har dare yayi,sosai ake xuba wani sanyi me rikita mutum,zahra’u se rawar sanyi take sabida zazzabin daya kamata,

Shiko Hammad addua kawai yake ruwan ya tsagaita ya fice daga cikin bukkar sabida shi irin mazan nanne masu ƙarfin shaawa koya sanyi ya taɓa shi gabanshi miƙewa yake kamar ze faso masa wando,ga zafin da marainansa suke masa.

Addu’a yakeyi azuciyarsa,Zahra’u wacce zafin zazzaɓi yasata neman inda zataji ɗumi a hankali ta matso jikin Hammad bakinta na rawa,tace “Soja me ulcer dan Allah ka lulluɓeni sanyi nakeji”ta faɗi sanda ta kutsa mazaunanta gabanshi ta kwantar da kanta a kirjinshi.

Wani abu ne ya tasowa Hammad tun daga tafin ƙafarsa zuwa kansa,runtse idonsa yayi gam yana ambato Allah sanda yaji mazaunan Zahra’u na gugar bananarsa.

Muje zuwa

Surbajo for life.
[1/6, 10:15 AM] Zahra Surbajo:
*TAYI MIN ƘANƘANTA*

*Zahra Surbajo*

 

*6*

“ƴarfillo!!!!!!!!!”ya ambata da ƙarfi sanda ya farka a gadon asibiti yana laluben ta,faɗowa yayi daga kan gadon yana ihun kiran sunan ta.

Da sauri sojojin dake kula dasu suka zo suka riƙeshi,dambe yake iya ƙarfinshi yana kiranta,”ƴarfillo kina ina,ki zo nan kusa dani,kar kimin nisa,don Allah kiyi magana injiki,kitaimakeni kiyi magana mana,nace kiyi haƙuri,ko baki yarda dani bane,nace zan kula dake,zan ɗaga darajarki fiye da ta kowacce mace me gata”sambatun da Hammad yake kenan sanda ya farka a asibiti.allurar bacci aka masa ko zaa samu sauƙin sambatun.

A can sansanin ƴan gudun hijira ko masu kawo sadakar abincine suka zo dan haka kowa da gudu yaje ya hau layi,banda Zahra wacce cinyoyinta ke mata mugun ciwo,zaune take ta kife kanta akan guiwowinta tana kuka,

Haka aka gama rabon abincin ita bata samuba,se hanne ce ta sammata nata.shima daƙyar ta iya ci sabida bakinta ɗaci yake mata.

Haka suka kwashe tsawon kwanaki uku,Zahra zuwa lokacin bata iya ko tafiya sede rarrafe,ga wani ruwa data rasa ko na menene dake bin cinyoyinta.tayi kukan tayi kukan har ta gaji.gashi ba suturar arziƙi ke garesu ba haka take zaune ƙuda na bin ta.hanne kanta yanzu ta gujeta sabida warin da zahran take.

Duk sanda zaa kawo abinci zahra bata samu sabida ƙyamarta da akeyi,hakan ne yasa take fita daga sansanin da rarrafen taje,bakin titi tayi bara dan ta samo abinda zata ci.cikin ikon Allah kuma tana samowar seta koma gefe taci ta ɓoye sauran.

Acikin sati biyu duk wanda yaga Batulun inna bazece ita bace,gaba ɗaya ta sauya,tazama abar tausayi.

Acan kaduna ko,lamarin na hammad ba sauƙi,dan gaba ɗaya kwakwalwarsa tasamu matsala,a birkice yake,arana seya kira ƴarfillo yafi so dubu,kuma yana dukan duk wanda yazo kusa dashi.

Hakanne yasa aka nemo iyayenshi sukazo aka basu shi domin suje su nema masa lafiya.

Allah sarki,a ɗaɗɗaure aka sashi a mota sabida dukan da yakeyi,shima seda aka masa allurar bacci sannan akai nasarar fita dashi.

Alhaji Nasir Abubakar shine mahaifin Hammad,me hamshaƙin me kuɗine,wanda sunanshi ya kewaye ko ina a ƙasar nan harma da ƙasashen ƙetare.ƴaƴanshi biyu Hammad da Surayya,se matarsa hajiya maryam,dukansu asalinsu ƴan gombe ne.

Alhaji ba abinda yakeso a duniya sama da ɗansa Hammad,duk wani buri nasa na duniya akan Hammad ya ɗorashi,lokacin daya ga halin da ɗan nasa yashiga kuka yake da idonsa kamar ƙaramin yaro.dan shi dama a dole yabar Hammad ya shiga aykin soja,dan kawai ya nuna yana sone.

Hammad matashine ɗan kimanin shekara 30 da haihuwa,bayan kammala karatunsa na secondry,mahaifinshi oxford university ya tura shi inda ya karanci gynocology,wato likitan mata,inda yasamu sakamako me kyau bayan kammala karatun.
Lokacin daya dawo gida nigeria,seya samu ƙasar na cikin yanayi na fama da rashin tsaro,ana kashe mitane basuji ba basu gani ba,wannan dalili ne yasa Hammad da Amininsa jameel suka faɗa aykin soja,wanda mahaifin hammad yasaki ƴan mazan kuɗi aka basu manyan muƙamai,bayan sun samu horo na musamman asansanin sojoji dake NDA kaduna. sunason taimakawa ƙasarsu da dukkan ƙarfinsu.

Wannan kenan.

Muje zuwa

Surbajo for life.
[1/6, 10:15 AM] Zahra Surbajo:
*TAYI MIN ƘANƘANTA*

*Zahra Surbajo*

 

*8*

A harabar gidan yayi parking,tun kan ya gama tsayawa Hajiya da Muhammad suka fito,cike da damuwa yafito daga motar,sannan yayi umarnin da a ɗaukota akaita boysquater dake gidan.

Ba musu masu tsaron lafiyar tashi suka ɗauketa kamar yadda ya buƙata,ba hajiya ba hatta Muhammad ya kaɗu dajin warin da takeyi,haka aka wuce da ita ciki.

Jummai da Asabe Masu aykin gidan hajiya ta kira bayan sunzo tace”ku kwashi kayan wanka maza kuje kui mata wanka,ku tabbatar da cewa komai na jikinta kun wanke ganinan zuwa”

Amsawa sukayi da sauri suka wuce aywatar da abinda tace.kallonta takai gun Muhammad wanda gaba ɗaya Babu annuri a fuskarsa tace”Muhammad bari inje in dubata bazan jimaba zan dawo”

“Mummy wannan warin fa ze iya cutar dake,gaskiya da aba direba ita yakaita asibiti,nan akwai matsala”ya faɗi cikin yanayin damuwa.

“karka damu bari in dubata ba abinda ze sameni”ta faɗi sannan ta juya ta bi bayan su jumman.

Se a lokacin Muhammad ya ƙarasa gun mahaifinshi yana murmushi ya ɗan rusuna yace “sannu daddy”

Dafoshi yayi yana murmushi yace “Yauwa ɗan gidan daddy ya hanya,ya kuma hajiya da jikin”

“hanya Alhmdllh,hajiya kuma ta warke sosai”

Daga haka suka shiga ɗan taɓa hira kaɗan suna jiran hajiya ta fito suji in agidan zata diba mara lafiyar ko asibitin zaa tafi.

Hajiya lokacin data shiga toilet ɗin kusan kukane yakusa kwace mata ganin yadda gaban mara lafiyar ke shirin lalacewa.

Safa tasaka sannan ta tara ruwa me zafi,tasa detol,sannan ta tsomata acikin ruwan ta fara wanke gurin,wayyo Allah na gurin yauƙi yake gashi har wani kore kore yake,ga uban wari.

Hajiya na fara wankewa tsananin azabar da zahra taji yasa ta farkawa daga suman da tayi ta kwalla wata ƙara.

A gigice Daddy da Muhammad suka nufi boysquater ɗin,sede suna shiga jummai ta dakatar dasu a falo ta hanyar shaida musu wanka ake mata.

Kimanin awa guda Hajiya ta kwashe tana sauya ruwa tana wanke gurin Zahra kuka take iya ƙarfinta tana kiran sunan Allah.

Kan kace me tuni wannan azababben wari ya tafi se ɗan wanda baa rasa ba,doguwar riga ta marasa lafiya hajiya tasa mata sannan suka ɗaukota zuwa ɗakin da hajiya ta ware domin kula da marasa lafiya na gida,ba abinda babu aciki.

Kan gado ta ɗorata,sannan ta fara wanke duk inda taji rauni sakamakon bigeta da mota tayi.seda tagama tsab sannan ta buɗe gaban nata ta kawo fitilar likitoci ta haska,sosai tausayinta ya kamata,wannan sashin ba ɓangarenta bane shiyasa bata fahimci ko matsalar menene ba.

Kashe fitilar tayi sannan ta rufeta,tasa jummai ta kawo mata abinci,ayko kamar tsohuwar mayunwaciya haka takecin abincin har ta cinye tasha ruwa,

Magunguna hajiya ta bata,sannan ta kwantar da ita ayko kamar jira bacci yayi awon gaba da ita,sosao tausayinta ya taɓa zuciyar hajiya,yarinya ƙarama amma ta haɗu da matsalar taɓin hankali,dan atunaninsu su dika mahaukaciyace.

Falo ta dawo gun su muhammad da Alhaji tace cikin damuwa “Alhaji ni nayi nawa,sede yarinyar nada matsala a al’aurarta,shine nake ganin ko de A kaita Hammad Hospital ne,kaga can akwai kayan ayki zata fi samun kulawa,tunda can dama na ɓangaren mata ne”hajiya tace cike da damuwa.

“wanne irin Hammad hospital,menene zaay mata acan wanda ɗanki Muhammad baze iyaba,ko kin raina kwarewarsa ne,da har kike cewa akaita wani guri bayan ga abu agida”cewar Alhaji yana duban Muhammad.

“Mummy zan dubata ingani insha Allahu baze gagara ba,abinda zaay mata a wancan asibitin nima shi zanyi insha Allahu”cewar Muhammad.

juyawa hajiya tayi yabita abaya zuwa inda Zahra take kwance tana bacci.

Safa yasaka a hannu sannan ya kunna fitilar likitoci ya matsa da ita gabanta hajiya ta buɗe masa gaban na zahra.

A Hankali ya duƙa yana kallon gurin,yasa hannu ya ruƙo wannan tsoka dake lilo itama ya ƙare mata kallo, tsawon mintuna arba’in ya kwashe yana karantar gurin sannan ya ɗago ya cire glass ɗin fuskarsa,sosai damuwa ta bayya na a fuskarsa idanunsa sukayi ja,tsigar jikinshi har tashi take yace “mummy fyaɗe aka mata,kuma a ƙalla ya kwashe watanni da yi matan,kuma anji mata ciwo agurin,wanda sanadin hakan ta kamu da yoyon fitsari,ga infection me ƙarfi daya kama gurin wanda in baayi da gaske ba ze iya rikiɗewa yakoma cancer”

.Salati mummy tayi sannan tace”oh ni jamaa yaushe zasu fara tsorom Allah ,yarinya ƙarama a haike mata wannan wanne irin cin zarafine”

“mummy muje inyi list na abinda zaa buƙata,dan akwai buƙatar ayi mata ayki yau ɗinnan ayi mata plushing ɗin infection ɗin sannan a ɗorata akan magani”cewar Muhammad bayan ya cire safar dake hannunsa ya wanke Hannunsa suka fito ransa Aɓace ya rasa dalili,ko kaɗan baya ƙaunar akawo masa yara an musu fyaɗe ransa ɓaci yake ji yake da ze ga wanda ya aykata musu ba makawa seya kasheshi .

Muje zuwa

Surbajo for life.
[1/6, 10:15 AM] Zahra Surbajo:
*TAYI MIN ƘANƘANTA*

*Zahra Surbajo*

*7*

*Bayan shekara ɗaya*

“Modibbo ɗiyata zata mutu a sansanin ƴan gudun hijira,kataimaketa!!!! kataimaketa!!! kataimaketa!!!!!!!!!”

A Razane ya farka daga baccin da yake,wani gumine ya karyo masa me zafi,gudun AC dake ɗakin ya ƙaro,sannan ya samu guri yazauna yana tunani gameda mafarkin da yake yi da Hauwa ƙanwarsa,wacce sanadin faɗan da akayi a garinsu yasa ta ɓace wanda sunyi cigiya har sungaji.

To shi wannan mafarkin da yake da ita me yake nufine,yau kusan kwana uku kenan seyayi mafarkin,ɗiyarta to dama ta haihune ko ya abun yake,a iya saninshi hauwa nada matsalar rashin haihuwa,kuma mijinta ankasheshi a faɗan da akayin.

Haka de yayi zugum shi kaɗai a ɗaki yana tunani,to shi wanne sansanin ƴan gudun hijira zashi,?taya ze iya gano ƴar da be san kamanninta ba,?to bama wannan ba shin mafarkin gaskiya ne?wainnan tambayoyi sune ke yawo a kansa da ya rasa amso shin su.

Haka ya kwana be runtsa ba,da gari ya waye bayan yayi sallar asuba ɗakin matarsa ya nufa,

Da faraarta ta taso ta tarbeshi,bayan sun gaisa ne,tace cike da kulawa”Alhaji naga kamar kana cikin damuwa?”

“Hajiya kwana biyu ina cikin damuwa,hauwa kullum se tazo amafarkina tana cewa in taimaki ɗiyarta,a sansanin ƴan gudun hijira ni na kasa gane kan wannan lamari wallahi”ya faɗi cike da damuwa.

“ka kwantar da hankalinka baban Muhammad,wataƙila akwai wani abu me muhimmanci gameda mafarkin nata nide ashawarata da ka fara duba sansanin ƴan gudun hijirar kagani ko wani taimako suke buƙata yasa hauwan ke zuwa ma a mafarki”

“kema kin kawo shawara hajiya,zanyi hakan in yaso duk week end na dinga zagayawa guraren da ƴan gudun hijirar suke,dan abun akwai ɗaure kai wallahi”

Haka de suka gama jajantawa modibbo ya miƙe ya fice zuwa ɗakinshi,wanka yayi ya kimtsa sannan ya dawo dinning suka ci abinci,agurin cin abincin ne yace “Munyi waya da Muhammad ɗazu ya shaidamin ƙarfe biyu na rana zasu iso, kuma hajiya babba jikinta da sauƙi,shiyasa ze taho,ki tanaji komai,ni zan fita,zan jima kan in dawo”

murmushi Hajiya tayi sannan tace”lalle Muhamnad yaci saa da hajiya babba ta barshi yataho,ita da tace se ta masa aure sannan ze dawo”

Dariya sukayi irin ta girma sannan yace”hala ta masa matar ne shiyasa tabarshi yataho”

Miƙewa yayi yana kallon agogon hannunsa yace”hajiya bari in ƙarasa office,zamuyi waya,in kuma naga da lokaci zan ɗan leƙa sansanin ƴan gudun hijira dake nan kusa”

A dawo lafiya tay masa sannan ya fice da hanzari,bodygurd ɗinsa suka mara masa baya.

Ƙarfe huɗu modibbo ya baro office,bayan yayi sallar la’asar,kai tsaye wani gidan abinci ya nufa, domin yaci abinci kamin ya wuce sansanin ƴan gudun hijirar.

A kan idon Zahra motocinsa suka faka,tana can ɗayan gefen titin,da ɗan saurinta ta taho tsallako titin dan tasamu tayi bara agunsu ko zasu taimaka mata,dan kwananta biyu yau bata ci abinci ba,agalabaice take ga ulcer ta data tashi,yanzu ko gabanta ya koma ciwo,yana fitar da wani wari me ɗaga hankali,ko giftawa kayi ta gunta se kaji warin,shiyasa duk inda tayi ake korar ta,hakanne yasa take samun kan bola tayi zamanta,gudun kar akoreta.

Cikin rashin sani mota tayi ciki ciki da ita lokacin da take ƙoƙarin tsallakowar.

Ƙarar burkin motar ne,yaja hankalin mutane da dama, ciki harda modibbo dake ƙoƙarin shiga gidan abincin.

Da gudu me motar daya bugeta yabar gurin be tsaya ba.
A Hanzarce Modibbo yayiwa bodygurd dinshi umarnin su ɗauko wanda aka buge susa a mota,

Hakan sukayi,sede warin da takeyi ne,ya hanasu kuma shiga motar da sauri suka ja baya har modibbo ya ƙaraso.

Warin shi kanshi ya ɗaga masa hankali,shiyasa be tuhumesu me ya hanasu shiga motar ba.

Tsayawa yayi shima yana nazari kamin ya ciro waya ya kira matarsa kasancewarta likita,tana ɗagawa yace”Hajiya akwai emergency yanzu wani ya buge wata mahaukaciya kuma ya tsere,in kaita asibiti ne zaki je yanzu ko in kawota gida?”

“Gaskiya ka kawota gida sabida muhammad be daɗe da dawowa ba bazan iya fita in barshi ba,amma in kukazo naga yanayin lalurar dole se anje asibitin semu tafi”.

Yana kashe wayar ya faɗa motar da kansa yaja,da gudu suka shiga sauran motocin suka mara masa baya zuwa gidan.

Muje zuwa

 

A daren duk abinda ze mata yayi mata,iya azaba zahra tasha ta,duk wanda yaganta seya tausaya mata,haka ya gama komai,sannan ya barota kwance kamar matacciya.

Ɗakinshi ya wuce kai tsaye kan kujera ya faɗa yana maida numfashi,wayarshi tayi ƙara da sauri yakai idonsa gurin,Amininsa kuma babban likitan mata na asibitin Hammad Hospital,shi ke kiransa.

Ɗagawa yayi ya kara wayar a kunne yace “ya kake?”
Daga can ɓangaren ya amsa masa “kaganni wallahi se yanzu zan bar office,tun safe ina asibiti har na gaji,”

“munyi ɗaya kenan,nima yanzu fitowata daga wani aykin gaggawa kenan?”

“Wallahi da naso in shigo gidanku yau sabida gobe weekend,inaso in je falgore dubo ƴarfillon nan inga ko zaa dace,to se kuma ayki ya riƙeni,dama so nike in ce ko zaka rakani”

Murmushi muhammad yayi me sauti sannan yace”na gaida na ƴarfillo,Allah de ya yanke maka wannan wahalar,”

Dariya dukansu sukayi,sannan daga can ɓangaren yace “aboki bazaka gane bane,wallahi ina matuƙar tausayawa yarinyarne shiyasa”

“Na jima da fahimtar hakan,kaga in Allah yasa ka ganota kuma kaga tayi kalata kaga shikenan seka aura min ita,adena cemin gouro”muhammad yafaɗi yana dariya.Dan yasan ya tsokano abokin nasa,ilai kuwa bece komai ba ya kashe wayar.

Wata dariyar muhammad yayi sannan ya ajiye wayar ya miƙe ya shiga wanka dan jikinshi duk ciwo yake,danma mummynsa na gurin tana taimaka masa.

Tsawon watanni biyu zahra ta kwashe Muhammad ke kulawa da ita,zuwa yanzu ƙafa tasamu tana tafiya kaɗan kaɗan.

Sosai take samun kulawa agurin mummy,safe darana da yamma ita ke mata wanka,ga ruwan zafi datake yawan sata aciki ta zauna.

Zahra farinta yasoma dawowa ga wata ƙiba da tayi kamar ba mara lafiya ba,yanzu komai takeso tana samu,sede ba uhm ba uhm uhm ido kawai take binsu dashi ko wanne lokaci.

Yau zaune suke ita da hajiya a falo tana bata kankana tana sha,Muhammad ya shigo falon,bayan sun gaisa da hajiya ya dubi zahra sannan yace “hajiya jikin yarinyat nan da sauƙi,yakamata akaita asibitin mahaukata aduba lafiyar kwalwalwarta,shurun tayi yawa”
Kamar jira yana saukewa zahra cikin muryar marasa lafiya tace”lafiyata ƙalau ni ba nahaukaciya ba ce”

Ba muhammad da hajiya ba hatta daddy dake ƙoƙarin shigowa falon yayo mamakin maganarta.

Muje zuwa

Surbajo for life.
[1/6, 10:15 AM] Zahra Surbajo:
*TAYI MIN ƘANƘANTA*

*Zahra Surbajo*

*11*

Muhammad tsawon sati guda ya kwashe ba inda yake zuwa sabida firgicin da yake ciki,sosai zancan auransa yasakashi,a damuwa,

Zahra sanda mummy ta sanar mata auranta da muhammad sosai taji daɗi,sabida taga ɗan uwanta ne,ze rufa mata asiri,dan haka bata da damuwar komai aranta.burinta Allah ya nuna mata lokacin.dan ita tun haɗa idonta dashi na farko taji ya kwanta aranta.

Sosai walwalarta da jin daɗinta ya ƙaru agidan ba mummy ba har daddy ya fahimci hakan,wani sanyi yakeji aransa sabida ya mata abinda takeso.

Mummy gyara zahra take da duk wani abu data san baze cutar da lafiyarta ba,,cikin ƙanƙanin lokaci zahra tayi wani kyau na musamman fatarta ta murje tayi fari har wani sheƙi take,gashi yanzu ba wata rama ajikinta,sema wata ƙiba data mulka,zahran inna kenan matashiya ƴar kimanin shekaru goma sha shida.kyakkyawa ajin farko,

Saura kwana biyu ɗaurin aure,muhammad na zaune a lambun gidansu zahra ta ƙaraso gurin,yana ganinta ya ɗauke kai kamar be ganta ba,murmushi tayi dan tasan baya sonta,ita ko sonshi take dan haka zatai haƙuri da duk wani halinsa har shima ya sota,gefenshi taje ta zauna,kamshin da take ne yasashi ɗago kai ya dubeta,sannan ya maida kansa gefe.

“yaya dama inaso in baka haƙuri ne akan auran dolen da zaay maka”
Ɗagowa yayi ya dubeta rai aɓace yace”au auran dolen ni kaɗai zaayiwa kenan ke banda ke?”

Murmushi tayi kumatunta suka lotsa tace”banda ni gaskiya,kai de za’a yiwa,ni auran nagani inaso za’a min,”ta faɗi a kunyace.

Tsayawa yayi,yana ƙare mata kallo,tattaro hankalinshi yayi gaba ɗaya kanta,hannunta ya kamo ya dibeta a tsanake yace”zahra ni kikeso?”yayi tambayar a tsanake.
Murmushinta me sanyi tayi sannan tace “Tunda naganka,naga kuma irin taimakon daka ba rayuwata da lafiyata,yaya muhammad naji ina sonka,wallahi da gaske nake har raina”ta ƙarasa maganar kamar zatai kuka.

Yatsun hannunta yake kallo,sannan ya ɗago ya dubeta yace”zahra to ya zakiyi in kika fahimci ba matsuguninki a zuciyata?”

“addua zanyi,wataran zaka soni”ta bashi amsa batare da damuwar komai ba.

Murmushin takaici yayi sannan yace”to in kuma ba kya cikin kalar matan da nake so fa?”

“Zanyi ƙoƙarin maida kaina kalarsu insha Allahu”tabashi amsa.

“to ay ni zahra gaba ɗaya kin min ƙanƙanta a aure,taya zan iya zaman aure dake?”

“wataran zan girma yaya,in zama babba,sede ko kace sauran wanine baka so,inaga shine kawai dalilin daze hanaka aurena”ta ƙarasa maganar tana kuka,

Runtse ido yayi maganar na masa ciwo a zuciyarsa,a hankali ya dubeta yace”to naji zahra tashi kije kar mummy ta nemeki,”

Miƙewa tayi a hankali,tabar gurin tana waigenshi.

Shima miƙewa yayi yaja motarsa zuwa Hammad hospital dan ya sanar da amininsa halin da yake ciki,dan barin kashi a ciki baya maganin yunwa.

Muje zuwa

Surbajo for life.
[1/6, 10:15 AM] Zahra Surbajo:
*TAYI MIN ƘANƘANTA*

*Zahra Surbajo*

*10*

Murmushi mummy tayi ta dafo kanta tace “ɗiyata sauƙi yasamu kenan?”
Murmushin itama zahra tayi ta sunkuyar da kai ƙasa,
Daddy ne ya ƙaraso gurin ya zauna sannan yace”dama wannan lokacin nake jira kuma gashi Allah ya kawo mu,zamu so ki sanar damu ko ke wace ce,dan musan taya zamu taimakeki ki koma ga danginki”

Hawayene ya zubowa zahra tasa hannu ta goge,sannan tace”ni bani da dangi,baffana yayi hatsari ya mutu,innata ƴan bindiga sun kasheta,tade taɓa shaidamin muna da ƴan uwa a gombe,kawu modibbo amma sun bar gomben kuma batasan inda zata gansu ba”

Kallon kallo suke tsakanin hajiya da Alhaji,bakinsu har rawa yake gun jefo mata tambayar”ya sunan innar taki na Aynihi?”

“hauwa’u sunanta”ta basu amsa.

Rungumota hajiya tayi jikinta tana hawaye tace”tunda nake kallon fuskarki naga kamar nasanki,amma na kasa gasgata hakan,ashe ko ikai fuskar hauwa nake gani ataki fuskar,Allah mungode maka”

Daddy sosai yake murna da ganin ɗiyar ƴar uwarshi,hotunan inna nada ya nunawa zahra ayko murmushi take tana faɗin”innata ce wannan dama kunsanta”

Daddy ya gabatar mata da kanshi da iyalinshi a matsayin dangin nata yamata bayanin komai,ayko itama kuka tasa najin daɗin ganinsu.

Shide Muhammad abun koma masa yayi kamar a film,daga neman shawarar akaita gidan mahaukata shikenan abu ya juye ta komo ƴar uwarsa.

Basu bar falon ba se da dare yayi sosai anata hira,sosai daddy yasaki jiki da zahra wacce yake kallo amatsayin sauran danginsa da suka rage masa a duniya.

Washe gari da safe bayan muhammad ya duba zahra,cire safar hannunshi yayi ya janyo kujera ya zauna yana fuskantarta,ita de tunda ta fahimci shine ke dubata kunyarshi takeji,da ƙyar take iya haɗa ido dashi.
“zahra kin bada labarin komai naki,amma baki sanar damu wanda kuma ya miki fyaɗe ba?wanda a matsayinmu na ƴan uwanki zamu so musani”muhamnad yace cikin tattausar murya.

Hawayene ke biyo idonta a hankali tace”na barshi a matsayin sirrina,don Allah karka kuma tambayata”ta faɗi cikin kuka.

Taɓe baki yayi sannan yace”bazan kuma ba,amma kisani in ni baki faɗa min ba dole zaki faɗawa mijinki ay”yana kaiwa nan ya fice daga ɗakin.

Hankalin zahra yayi ƙololuwar tashi jin furucin muhammad,tabbas dole zata sanar da mijinta wannan mugun labarin,duƙar da kanta tayi ƙasa tana kuka me tsuma zuciya.

A haka mummy ta shigo tasameta,sosai hankalin mummy yatashi janyota tayi jikinta tashiga tambayarta abinda yafaru,cikin kuka zahra tace”mummy yanzu rayuwata a haka zata ƙare kenan,bazan taɓa aureba,in ko zanyi auren dole sena cewa mijina anmin fyaɗe? inde hakane nida aure har abada”ta ƙarasa maganar cikin kuka.

Tausayintane ya kama mummy ta shiga rarrashinta da duk wata kalma me daɗi,da ƙyar tayi shuru.

Mummy ɗakin daddy taje tasameshi yana shirin fita,ganinta cikin yanayin damuwa ne yasa ya nemi guri ya zauna yace”hajiya lafiya kuwa?”

Cikin damuwa tace”Alhaji yarinyar nan na cikin damuwa gameda fyaɗen da aka mata, baka ganin akwai buƙatar a binciko ko waye a hukuntashi sannan asa shi dole ya aureta?”

Shuru Alhaji yayi na ɗan lokaci sannan yace”nemo ko waye beda wani amfani,fyaɗe de anriga an mata,ba abinda ze sauya hakan,kuma ni modibbo inde na isa da Muhammad to tabbas shine ze auri Zahra,dan shi kaɗai ze rufa asirinmu”

Mummy itama ta gamsu da bayanin na alhaji,dan haka kwarin guiwa ta ƙara bashi kan ƙudirin nasa,sabida Allah yasani tana tausayin zahra matuƙa.

Alhaji be samu zama da Muhammad ba seda dare bayan ya dawo daga gun ayki.
Lokacin daya sanar dashi hukuncin daya yanke akanshi da zahra muhammad kaɗanne beyi fitsari a wando ba sabida firgici,bakinsa har rawa yake yace”daddy don Allah kayi haƙuri kabar maganarnan,nifa bana sonta,gaba ɗaya zahra nawa take da har zaay batun aurenta,ni tayi min ƙanƙanta daddy pls”
Yafaɗi kamar zeyi kuka.

“muhammad ba shawara fa nake nema ba,hukuncin dana yanke nake faɗa maka,wannan duk raayinka ne,ba nawa ba,nan da wanne lokacine zahra zata iya warkewa gaba ɗaya” daddy ya buƙata cikin haɗe rai.

Jikin Muhammad a sanyaye yace “wata guda”

“nasa lokacin auranku nan da watanni biyu masu zuwa,na ɗauke maka komai,kaje ka fara shiri”daddy ya faɗi sannan ya miƙe yabar gurin.

Muhammad na zaune kamar wanda aka dasa,yama rasa me zeyi yaji sanyi aransa,da ace ze iya kuka to ba shakka kukan ze ta rusawa.

A Hankali ya miƙe ya nufi ɗakinshi jiki a sanyaye ya faɗa gado yana nazari,shide gaskiya tayi mishi ƙanƙanta a aure to in ya aureta yace ya auri wa?shi fyaɗen da aka mata ba damuwarshi bane kawai de shi yafi son mace ƙatuwa ne.

Leave a Comment